?
"ko ba zakiyi hakurin ki fawwalawa Allah komai daya zartar akanki ba ?
A sanyaye kamar kazar da kwai ya fashewa aciki ta girgiza kai da sanyin murya tace " Alhaji na amince da qaddara ,Allah yayi masa rahma zanyi duk yadda kace gabadaya babu wanda bai tausaya mata ba daga haka baba Sarki ya mike tsaye "Allah yayi miki albarka sai anjimanku ta gyada kai da cewa " Allah ya kiyaye ya gyada kai yayinda yake karasa ficewa daga parloun'n inna ,Abba da injiniya na biye dashi ....
Kuka hajiya saudat tayi sosai tamkar ranta zai fita inna na rarrashinta ",kiyi hakuri nasan makirci ne kawai irin na mairo amman zanyi maganinta dan auren babana da yar banza yarinyar nan bazan amince ba, zamu hada karfi da karfi ni dake muyi komai gara ta zauna haka takare rayuwarta babu muji uwarta taji yadda kika ji .
"a'a inna ki bari ayi auren nan abinda rayhan ya bukata kenan ,ni dana rasa d'ana sukunta guda me kuma zan iya yi?
" ni yanzu abinda rayhan dina yake so shi zan yi daman ina kin ummita babu wani dalili yanzu wa gari ya waya ?
Cike da tausayawa hajiya inna ke rarrashinta ...
Ta dade zaune a parlour'n inna tana rarrashinta zuciyarta cunkushe da rashin danta ,ita kuwa Inna ta rasa yadda zatayi neman mafuta take akan al'amarin ,ita idan ba an fi karfinta ba bazata yarda da wannan hadin ba ,da kyar hajiya saudat ta taushi zuciyarta ta koma bangarenta .. ...
Bangaren ummita kuwa har lokacin tana cikin damuwa da kunci tattare da bakincikin mara misaltuwa haka ma mama tunda taga baba Sarki yazo gidan ta rasa abinda ke damunta ta kasa zaune ta kasa tsaye domin tun da taga sun kulle a bangaren inna tasan ba lafiya ba, da kyar ta samarwa zuciyarta salama ta nufi dakinta inda ummita ke kwance akan gadonta ,ta tambayeta ko akwai abinda zata ci tace "babu komai ,tasan har lokacin akwai damuwa a tattare daita dan haka ta zauna jigun a kusa daita tana tunani duk abun duniya ya dameta gabadaya duniyar ta tsaya mata cak saboda ganin tilon diyarta cikin damuwa ,cikin hk mah'ruf ya shigo d'akin ya gansu fuskarsu babu walwala ,take tausayinsu ya kamashi yasan mama duk tafi kowa shiga damuwa , shi kansa yana cikin damuwa tun daga lokacin da abubuwa sukai ta faruwa yake fama da matsanancin ciwon kai baya dai nuna wa kowa ne ,mama ta kafeshi da idanunu "sunnu baba da kokari , kana gida ashe ?
"Yanzu na shigo mama ya mai jiki ,?
"Da sauki gata nan dai taki cin komai tun safe nake fama daita taimaka min ko zata sakawa cikinta wani abu ,ya ɗan saci kallonta zuciyarsa na tsananta bugawa yaga wani guri take kallo , zuciyarsa yaji tana budewa da karbar wani abu mai sanyi da natsar da zuciya wanda bai san ko menene ba furzar da iska yayi sannan yace "ina abincin mama ?
"Bari naje na kawo ta mike cikin sauri "ki hado mata da ruwan zafi.
"to ta fice daga d'akin ,
Kujera ya janyo gabanta , sannan ya janyo kujerar mirrow din mama ya soma kokarin zama a gabanta tun kafin ya zauna jikinta ya soma rawa yayinda kirjinta ke dokawa da matsanancin karfi ya zauna yana kafeta da manya idanunshi masu bugar da zuciya "Malama ki samu natsuwa ,kina sane da shawarwarin likita akanki kou?
Tayi masa banza tamkar bata san da zaman mutu ba ,"ki taimaki kanki ki kwantarwa kanki da hankali, idan ba haka ba zaki mutu idan kika mutu mahaifiyarki kika yi domin sai tafi kowa shiga damuwa ,rayhan ya mutu babu wanda ya bishi duk son da muke masa haka muka hakura ,kema kina da tabbacin idan kin mutu babu wanda zai biki wallahi bancin mama da ni da kaina zan karasaki ki huta tunda kin gaji da duniyar....
ta d'ago da sauri ta tsura masa idanunta da suka fara ciccikowa da ruwan hawaye ta soma shesheka kuka yayi shiru yana kallonta kukanta na taɓa zuciyarsa batare da yace mata komai ba ..
Mama ta hado mata irin abincin da likita ya bukaci ta dinga ci da flask din ruwan zafi akan dan wani madaidaicin tire .
Mah'ruf ya amsa tiren ya ajiye a tsakiyarsu cikin sauri mama ta juya ta sake ficewa tana addu'ar Allah yasa taci abinci sosai ..
Har lokacin idanunshi na kanta flasks ya ɗauka ya tsiyaya ruwa acikin karamin cup ya hada mata ruwan Lipton ya kai bakinta ta lumshe idanunta tana bude bakinta dan babu halin yin musu kurba daya biyu tayi ta kawar da bakinta tana sauke naunauyen ajiyar zuciya tana jin wani iri ajikinta sai daya tabbatar data sha ruwan zafin sosai sannan ya bude
Kular abinci , white rice ne ya bud'e k'aramin kular shi kuma farfesun dayen kifi ne a hankali ya zuba daidai wanda yake bukatar taci ya zuba miya sannan ya rufe yana maida idanunshi akanta, yana jin wani wani irin yanayi a jikinsa ya kai spoon bakinta still Bai ce mata komai ba tayi shiru tana kallonsa ita so take ko sau daya ne ya rarrashinta ya nuna tausayawarsa gareta amman yaki duk abinda yake mata tasani ba dan ita yake yi ba darajar mama ne ....
Taki bude bakinta tana jiran yace mata wani abu hawaye na zubowa daga cikin idanunta yadda ta tsura masa ido yasa ya dinga jin tsigar jikinsa na mikewa yayi kokarin dannewa, a hankali ta soma rera masa kukanta "oh my god ya furta a matukar fusace "ke ..ke wacce irin ma.....
sai kuma ya katse maganarsa yayi shiru yana tunanin abinda zai faɗa mata bayan kamar second biyu idanunshi da suka Kada ya dinga lumshewa sannan ya bud'esu yayi mugun kafeta da idanunshi yana huci ya sake kai spoon bakinta babu shiri ta bude bakinta yana kallonta yana dura mata abinci yasan halinta bata jurar kallon idanunshi na tsawon lokaci kusan minti goma ya ɗauka yana ciyar daita har ta kusan cinye rabin plet sannan tace na koshi cikin sanyayyiyar muryata mai matukar kashe jiki ,tuni jikknsa ya mutu ya janyo numfashi da kyar ya sauke yayinda ita kuma tayi baya ta jingina bayanta da pillow tana kallon yatsun kafafunta ,"ki shirya na kaiki gidan aunty .
batayi magana ba ta sauko ta ya zira junbulelen hijabinta batare data saka nikaf ba bare safa ya kalleta bai yi magana ba , take tabi jikinta da kallo dan tana fahimtarsa koda bai ce komai ba ,shiru tayi tana son gano ma'anar Kallon take kwakwaluwarta ta fahimtar daita "nikaf dina yana d'akina nan ma bai yi mgn ba , ya wuce ta biyoshi kai tsaye d'akinta ya nufa yana shiga ya tsaya jikin bango har ta shigo yana kallonta tana dube dube har ta gani ta saka nikaf da safa ta fito ya tasata gaba suka yiwa mama sallama ..
Ko a moto babu wanda yayi wa wani magana har suka kai gidan yana tsaida motar ta buɗe murfin motar ta fita a hankali shima ya fito ya biyo bayanta ..
Yana shiga ya ci karo da Ahmed da gudu ya k'araso gareshi ya ɗauke shi ya daga shi sama yana juyi dashi bai sauke shi ba har sai da yashiga parloun'n aunty sannan ya direshi a kan kujera hadi da manna masa kiss a goshi Allah bai yi shi da son mutane ba amman yana matukar so yara most especial ahmed.
aunty ta kallesu cikin qauna ta murmusa tace "kai baba kamar dama shi kadai kayi kewa ?
da sauri cikin dry ya duka gaban ita da mijinta ya gaidasu , cikin farin ciki suka amsa , tana jin dadin yadda mah'ruf ke da tsakanin biyayya ya fita daban cikin abokan watsanshi , zafi ta ji sosai a ranta in yadda taga duk sunyi tamkar basu ganta ba sai ta mah'ruf suke .
Zama yayi kusa da aunty Yana faɗa mata abinda ya kawo su ,
Sosai taji dadi saboda yadda ya sauke duk wani amatsayinsa yake bawa ummita kulawa ,amar ne ya shiga janta da hira kafin kace me tuni hira ta barke tsakaninsu tun tana maqale jikin har ta hakura ,shi kuma Mah'ruf hankalinsa naga Ahmed ,
aunty ta kalli maryam tace "toh baku kawowa ummita komai ba kun zo kuna ta zuba mata surutu, ku kawo mata abincin , da sauri Maryam ta mike ta shiga ta dauko abincin Mah'ruf dake gefensu yasan wahalar da kansu kawai zasuyi sai dai yayi shiru ya zuba ido.
Duk yawan uban surutun da suke bata fiyye cewa komai ba sai dai ta saki ranta ..
Kusan awa daya
Su maryam da aslamiyya
Suna zuba uban surutu kamar parrot , ko bakinsu bai gajiya da magana ne oho , cikin kosawa da surutun nasu ya miqe ",aunty zamu wuce "daga zuwanku ko abinci fa bata ci ba dan dai kai nasan ba ci zakayi ba amman ita ai ka bari taci wani abu ?
"itama a koshe take ya ɗan saci kallonta yaji ko zatace wani abu a daidai lokacin da itama ta kalli inda yake idanunsu ya sarke cikin juna take zuciyoyinsu ya buga da matsanancin karfi da sauri suka janye idanunsu .....
TWO FRIEND'S (BSBS)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~ *AYSHA SHEHU MAMAN 2 (MAI DADDAWA) IYA WUYA TAKWARA MUNA JONE*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 36
.......Akan hanyarsu ta komawa gida ummita ta juya masa keya tana kallon bangaren titi , haushin abinda tayi yaji dan kallo ɗaya Za'a musu a fahimci rashin ɗaukarsa da mahimmanci ne ya jawo haka.
take ya soma tunanin abinda zai mata dan ya dawo da fuskarta gareshi ko kuma ta maida idanunta ga kallon gaban motar ,
A hankali taji saukar muryarsa cikin kunnuwanta " kada ki jefa min uwa cikin fargaba da zullumi da wannan banzar tunanin naki.
"ita din fa mahaifiyata ce, kuma kowa yasan soyayyar dake tsakanin uwa da d'a , tayi maganar batare data juyo ta dubi inda yake ba .
"ko ma dai menene ki adana damuwarki ta tsaya iya kanki kawai batare da ta shafi mahaifiyata ba ..
Bata sake ce masa komai ba ta girgiza kai tare da ɗaukar goran ruwan roba dake ajiye tsakiyarsu ta kora tare da ƙoƙarin kawar da damuwar data soma bayyana a fuskarta.
a watanin baya ta hangi abubuwa dayawa a tattare dashi data rasa a sikilin da zata d'aura domin son sanin gaskiyar abinda ke tattare da zuciyarsa ,
sai dai a yanzu da take cikin halin damuwa ta sake fahimtar komai ,ta kasa amincewa kanta mah'ruf mai kaunarta ne kamar yadda mutane dayawa suka sha faɗa mata "ina ma rayhan bai furta abinda ya furta agaresu ba ...
Wasu siraran hawaye suka gangaro mata suna isa gida tun bai gama tsaida motar ba ta soma kokarin fitowa amman dole ta koma ta zauna saboda yayi lock din motar .
tana zaune ya gama daidaita tsayuwar motar haɗe da shareta har sai daya gama shan kamshinsa sannan ya yi unlock ta fito tana fidda numfashi..
duk da cikin hajib take hakan bai hanashi fahimtar kuka take ba "ya sallama ya furta a hankali "fat lion me yasa kuka baya miki wahala ?
"Me yasa kike son damun zuciyarki ?
"Banason kukan nan yana bala'in ci min rai ...
Ya fito yayi key din motar yana kallon bayanta kai tsaye part din mahaifiyarsa yaga ta nufa ,shi kuma ya nufi part din mama bakinsa ɗauke da sallama "Assalamu alaikum "
ya iske mama tana kokarin cin abinci ta kai spoon bakinta ta ajiye tana fad'ad'a fuskarta wa'alaika Salam "har kun dawo baba ?
"Eh mamana ya ɗauki spoon din da take cin abinci ya kai bakinsa "ina ummita ?
Yayi shiru ya cigaba da cin abinci , itama shiru tayi tana dubansa "kada ki tada hankalinki mamana ta shiga bangaren umma har lokacin idanunta na kanshi "me kake gani akan ciwon ummita ?
"Babu komai mama komai normal ya sake kai cokali bakinsa
"mamana gurinki zan kawo suhaima ta koyi irin girkinki dan gaskiya girkinki babu karya "kai baba tace maka bata iya girki bane ?
"Mama dayawa fa yammatan nan basu iya komai ba sai fente fuska ni Kuma akan haka za'a iya samun matsala dani "ka jika kai da ba wani abinci kirki kake ci ba ,ya labarin jikin mamanta kuwa ?
Ya had'iye abinci ya kora ruwa sannan yace "taji sauki sosai dawowarce dai baza suyi ba ni addauta ma suyita zama a can karsu dawo , saboda aureta ma ya soma fita akaina.
"duk akan zaman jinyar ne kake fadan haka ?
Yayi shiru batare da yace uffan ba "kafa dinga hakuri baba uwa fa tafi ƙarfin komai "no mama ba akan shi bane akan wata yar matsala ne amman shima nayi solving dinta ki tayani da addu'a mamana .
"inshaallahu amman wuce matsalace wannan ?
"To ko akan batun aurenka da ummita ne ?
Ya girgiza mata kai dan baya son tashiga damuwa ko kad'an, mama bata yarda ba amman ganin yaki gaya mata dole ta hakura tayi shiru sai dai ta kasa samun natsuwa abinci ma tsakura ta koma yi ..
******
Acikin kwanaki ummita ta gama iddarta rana babu wanda bai yi kuka ba , mutuwar rayhan ta dawo musu sabo barin mahaifiyarsa da duniya tayiwa war'bar kunu, bata san iya son da take wa dan nata ba sai data rasashi ta fahimci duk cikin ya'yanta tafi son shi ..
Bangaren ummita bata sauya ba ganin damuwa tayi mata yawa yasa mahruf ya tausasa zuciyarsa akanta , yana son ya jawota jikinsa amman yanayin da yake ji ke hana hakan faruwa.
kayan marmari yasa mama ta kawo mata, bayan ya ta sata gaba taci abinci da ba wani na kirki taci ba ,ta dan zauna na kamar minti goma sannan ya turo mata kayan fruit " ki sha kafin ki kwanta yatsina fuska tayi amman ganin yadda ya haɗe rai tamkar hadari yasa ta soma sha , bayan ta gama sha sai da tayi minti goma sannan ta kwanta haɗe da kamkame jikinta guri ɗaya ,bargo ya janyo mata zuciyarsa na harbawa , lokacin da yayi kusa da kunnenta ya soma magana saboda ya gama karantarta tsaf rarrashi take buƙata daga gareshi " haba fatlion me yasa ba zaki sauya ba ,ki sanyayawa ranki, likita ya faɗa miki illar damuwa a gangar jikinkin .
"duk abinda kike so ki fada min ko mama numafashinsu ya nemi tsarke guri daya saboda kusancinsu da juna ,
yayi saurin mikewa ya zauna adaidai fuskarta idanunshi na kanta "wai ma menene abun damuwa fatlion I think before baki son rayhan ?
"Yaushe na faɗa maka bana son shi ?
"Idan ma bana son shi maganar da kenan, yanzu da zan ganshi zan soshi fiyye da komai dani kaina , tayi maganar tana lumshe idanunta tare da ƙoƙarin boye damuwar data bayyana a fuskarta .
ya ta'be baki yana harararta dan yasan duk gulma ce , "wa yasan alkibilarki ?
"Sai Allah daya halicceki zuciyarsa ta bashi amsa da hakan.
Da hillata da salon soyayyar da shi kanshi bai san yayi ba yasa ta soma samun sauki da sakin jiki amman har lokacin zuciyarta cike take da fargaban aurensa .....
Hajiya inna ta zubawa mahruf Ido na tsawon lokaci kafin daga baya taja naunauyen ajiyar zuciya tace " babana me yasa bazaka gujewa auren nan ba tunda nasan kai ba son yarinyar nan kake yi ba ,kama rasa wace zaka aura sai matar da ciwon sonta ya kashe d'anuwanka ,da tunaninta da rayhan ya bar duniya , mata ya dubi inna zuciyarsa na masa kunci yace ",haba inna ki daina cewa haka babu wanda ya isa ya kashe wani , wannan maganar kowa yasani alkwarin rayhan za'a cika dan yarinyar bata sona ... ......
" Ina ruwana da rashin sonka da batayi ai abinda nake so kenan kai da ita karku so juna
ni dai wallahi wannan haɗin bai yi min dadi ba, ni kaf zuria ta bana son kowa ya aureta bare kai haka kawai ana son aka Kaba maka ita .
Haushi ya turnuke zuciyar mahruf ,amman ya ya saki fuskarshi sosai dan karta fahimci yaji haushi yace" dan Allah inna kada ki damu kanki daman ni ina sonta , kuma gashi ummah tana son had'in kowa ma yana so kema ke so kawai ayi auren cikin farinciki ...
"Amman ka cika babban munafuki shine kake nunawa mutane baka sonta "yaushe na nunawa mutane bana sonta ?
"Ko na taɓa faɗa miki bana sonta ?
Yayi magana yana tsareta da idanunshi
ta kad'a masa kai "duk abinda kake mata ai kowa yasan kiyayya ce zalla "anaki ganin ba amman ni nasan bamu ta'ba yin haka dake ba ya k'arasa maganar yana furzar da iska .
"aiko idan dai haka ne ka bala'in cin baya wallahi , ai gara auren sakina da dai ka auri secon-hand
"ko ma dai menene inna ina sonta a haka ,in dai son da kike kirarin kina min gaskiya ne to daga yau ki fara son fat lion a zuciyarki .....
"Allah ya tsareni gara na so wancan yarinyar da zaka aura wallahi akan naso jikar agumawa masu tallan kifi , yayi murmushi "to shikenan hajiya inna kiyi duk abinda kike so ai duk daya ne da suhaimar da fat lion agurina ..
"Kai dan Allah rufe mana baki, bakin munafuki kawai mai fuska biyu mayaudari kawai ..
"kai kai inna duk ni kad'ai Kar fa ki bari mutane sujiki fa "
"suji mana , kowa ma yaji mu wallahi in dai akan wannan auren ne,kuma wallahi gudunmuwar da zan bayar na fasa bayarwa ..
Yayi shiru yana kallonta Kullun cikin damuwa da fargaban auren ummita yake , kuma duk abinda ya faɗa mata ya dai faɗa ne ba wai hakan bane acikin zuciyarsa sai gashi yayi nasarar tsintar kanshi farinciki da nishadi ..
Ya gyara zama tare da haɗe fuska yace
"Shikenan tunda haka kikace nima zan saka kaina cikin damuwa da tunaninta daga karshe ciwon zuciya ya kamani ta sanadin soyayyarta na mutu kamar yadda rayhan yayi Kinga kinyi hasarar jikokinki biyu daga karshe ta rayu ta auri wanda ya fi mu komai .
Hajiya inna nagama jinsa ta rushe masa da kuka "yaya zanyi haka zan hakura na zuba muku ido, duk abinda ka shuka ai shi zaka gurba wala khairan wala sharran duk abinda uwarta take Allah na kallonta dan bata haifa dayawa ba ,shine zata dinga bin jikokina da bita da kulli ta cigaba kuka "kai inna ki daina kuka dan kukanki ma wallahi karamin kaunar fatlion yake abinda nake so dake kiyi hakuri kiyi mana addau kawai.
"Allah ya sanya alkhairi kuma Allah ya dawo da kai cikin haiyacinka ,
kada ka taba cutar wacan yarinyar ka sanya ido sosai a gidanka dan an rigada an shanyeka yanzu kowani irin zalinci za'a yi ba sani zakayi ba "yana murmushi yace " to hajiya inna zan kula na gode da addu'ar da kikayi naji dadi naji dadi da kin shiga zuciyata da zaki fi tabbatar da dadin danaji akan wannan addu'ar taki , ta kalleshi da sauri ",lallai an gama da kai tausayinsa ya kama inna, tasan Mah'ruf da kiyayyar ummita, ba'a son ranshi zai aurenta ba ,zai dai aureta ne dan an gama dashi da kuma wasihan rayhan.
Ya mike yana duban fuskar hajiya inna "to hajiya inna ni zan wuce sai wani lokaci kenan takaici da bakincikin ya turnuke zuciyarta ko kallonsa bata sake yi ba tace "jeka babana Allah ya saka mana har ya fice zagin mama take.. ..
Part din Abba ya zarce sun dade suna magana har suka gangaro kan aurensa da ummita Abba yayi masa nasiha sosai akan yayi adalci akan matansa kada ya sake ya cutar da suhaima dan ba yar'uwarsa bace ,Abba ya tamabayeshi "kamar nawa za'a bayar sadakin suhaima a bada dubu ɗari yayi ?
"Abba duk yadda kuka yi daidai ne, tausanyinsa ya kama Abba , Mah'ruf yaro ne mai tsananin biyayya yasan bada son ranshi zai auri diyarsa ba sai dan biyayya .
"to shikenan baba zan kira mahaifin ita yarinyar duk yadda mukayi zan nemeka Allah ya tabbatar da alkhairi ya amsa da "ameen " batun guri zama kuma kayi amfani da duka bangaren ,bangaren rayhan dana naka ita ummita sai ta zauna inda take , sai batun kayan lefe karka ita ba sai an sake yi mata ba tayi amfani da wanda na haɗawa rayhan y
kaje Allah yayi maka albarka ..
Jikinsa babu kwari ya mike ya shiga part din Hajiya ummah, suna gaisawa babu abinda ta fara tambayarsa sai "kunyi magana da abbanka kuwa ?
Ya gyada mata kai "zuwa nan da sati biyu za'a daura auren , tayi murmushi ta saki ranta sosai, ya jima tana yi masa lissafi kudaden da zai kashewa ummita "amman hajiya Abba yace bai sai na kashe komai ba ,tayi amfani da kayan rayhan "ina....
ta girgiza kanta" kayan rayhan daban naka daban zaka hada mata lefe kamar yadda ake wa kowa ,shi daya hada wancan shi zai sake hada wannan idan ma bazai yi kai dole kayi ,dan wannan auren naka ya fiyye min kowani irin aure ,duk auren da zakayi bazai kai kamar wannan a zuciyata ba dan haka kayi duk wani abinda zai sakani farinciki, idan ma baka da kudin ne ka faɗa min zan baka .
"a'a ina dasu zan je bank na ciro ya mike jikinsa babu kuzari kamar wasa yake kallon abu wai shine zai auri mata biyu ..
Cikin kwanaki mama ta kasa gane kan ummita kullum cikin tunani ,haka shima mah'ruf duk yabi ya rame , duk yadda taso ya faɗa mata abinda ke damunsa kin sanar daita yayi ...
****
A can bangaren suhaima iyayenta sunata shirye shiryen ba da wasa ba tsiyaya kuwa tayi kamar hauka tana bala'in son mahruf fad'ar kudin datayi tsiyaya dashi bata lokaci ne, tunda ta dawo kasar bai zo ba sai ana sauran sati d'aurin aure shima ita ta matsa akan yazo suyi shawarar yadda za'a gudanar da biki.
yana zaune sitroom cikin farin yadi mai shegen kyau da shara shara har ana iya hango farar siglet dinsa , ta shigo ta same shi taci kwaliyya cikin riga da siket na less wanda ya kama jikinta sosai har ya bulloko da saman dukiyar fulaninta waje wanda basu da maraba da na mace mai yaya biyu zuwa uku taimakon bra mai ciko da Kuma yanayin shigarta ya bulloko dasu ake ganinsu zunduma zunduma , tasa kayan ne dan ta burgeshi sai dai ba wani farinciki yayi ba , da kyar take juyawa saboda yadda kayan suka matseta dif yayi mata yaki cewa komai gabadaya ya sauya mata kamar ba mah'ruf dinta ba ,itace tayi ta surutunta daga karshe yace ta fadi abinda take buƙata shi dai babu abinda zai yi walima kawai ta wadatar ta marairaice murya kamar zatayi kuka "haba habibi haka zanyi biki babu komai bikin aure sau daya yake zuwa a rayuwar mutun.
ya daure fuska sosai yace "oho ashe bani kaɗai rashin lafiyar mahaifiyarki ya dama ba har dake ?
Tayi sororo tana kallonsa "Yes kina kallona ko ba haka kika faɗa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 76