masu albarka abun yayiwa doctor Husain Dadi ,dan yadda suhaima ta nuna damuwarta tayi matukar burgeshi , da ana samun kishiyoyi irinta da wasu matan basuyi bakinciki dan za'ayi musu kishiya ba .
tunda doctor da suhaima suka fara magana ya zuba musu ido kawai yana kallonsu jikinsa na rawa har suka gama bai iya cewa komai ba domin bai san abinda zai ce ba, ko yace ma zai magana muryarsa bazata fito ba ya lumshe idanunshi hakan ya baiwa kwallar dake cikin kwarnin idanunshi damar zubowa "farkon yayan da zai samu ya rasa, shi kaɗai yasan halin da shi da mama zasu shiga akan rasa ya'yan nan yana matukar kaunar ciki ko yace Allah ya jarabeshi da cikin , a hankali ya furta ya Allah ka bani wasu masu albarka ....
Doctor yace "ameen" muje ka kai ni naga yarana yayi maganar yana jin zafi acikin ranshi ,doctor ya Mike shima ya sauko daga kan gadon da kyar yake daga kafafunsa suka fita tare ..
Suna fita suhaima ta hau tikar warar shaku shaku tana jin farinciki mara misaltuwa, sai da tayi rawar sosai sannan ta kira number hajiya rahma "yayarmu albishirinki ? a can bangaren hajiya rahma tace "goro "ki tayani murna cikin wannan yar iskan ya zube ,a she ma yan biyu ne ,shi kanshi bai sani ba sai a yanzu "ke dai bari yayarmu yau ina ciki murna da farinciki mara misaltuwa kamar an sani a aljanna haka nake jina , can tayi shiru tana sauraron hajiya rahma sannan ta sake kwashe da dariya tana rawa da juyi "ke dai bari yayarmu ni dama an bar ma zance zuwa gurin malamin nan wannan makurcin ma ya isa wallahi "okya shikenan maje din ai zata sani ne sai tayi nadamar zamowarta kishiya agareni tana ji tana gani zata bar min mijina ,shima ɗan iska wai har da kuka yayi fa, ta k'arasa maganar tana kwashewa da wata dariya sannan tayi mata sallama ta fito da sauri tana neman inda suka shiga ..
Shiru yayi tsaye yana duban jariran ya'yansa waɗan da an gama halintta masu komai masu tsananin kama dashi sai dai sunyi kankanta da yawa , take wasu zafafan hawayen suka zubo masa jikinsa na rawa ya sake matsowa garesu sosai yana dubansu ɗaya bayan ɗaya yana jin soyayyarsu na sake shigarsa ,bai ma san yana tsabanin son baby's d'insa ba sai daya rasasu ,ya yarda da kaddara amman har da sakaci ummita ....
doctor husain ya dafa shi "kaga yadda sukayi kankata ko ?
Ya kada masa kai batare da yace komai ba "wannan kankantar nasu nada halaka da rashin kusantarta da bakayi da alamun tunda aka same su wani abu bai sake shiga tsakaninku ba ,ya sake yin shiru yana cigaba da kallon yaran yana hawaye bai taɓa yiwa abu kuka ba duk tsananin abu ya kan daure amman ya rasa dalilin da yasa ya kasa daurewa wannan rashi da yayi doctor yace "kayi hakuri ba kai ba koni naji rashin dadin komawarsu Allah dai ya bamu wasu masu albarka .
Still bai ce masa komai ba juya ya nufi d'akin da aka kwantar da Ummita doctor husain bai yi kokarin biyosa ba
ya zuba duka hannuwansa cikin aljihun wandonsa ya tsaya a tsakiyar d'akin bayan ya shigo yana kallonta kwance daga nesa tamkar wata matacciya , alhankali ya dinga d'aga kafafunshi har ya k'arasa bakin gadon ya tsaya yana cigaba da kallonta da kyawawan idanunshi da suka koma ja yana jin kamar ya tasheta ya saka mata kuka ....
suhaima ce ta shigo ta tsaya kusa dashi tana faɗa masa kalaman rarrashinta na karya kafin daga baya ta janyo masa kujera "ka zauna habibi kar juya ya debeka bai yi mata mutsu ba , ya zauna batare daya ɗauke idanunshi akan ummita ba , "ka natsu dan Allah nan da wani lokaci zamu sake samun wasu ka sani ma ko nice zan kawo maka kyawawan baby's tayi maganar tana satar kallonsa domin taga reaction d'insa akan abinda tace , ya kai hannusa saman hannunta tayi saurin damkewa "na gode suhaima yayi shiru yana lunshe idanunshi sai a yanzu yake kaara sanin mahimmancinta arayuwarsa, tana tsaye akansa da alamuran gidansa shi kuwa me zai yi ya faranta mata ?
"Ka soni so na har abada habibi ,ina sonka son da ban ta'bawa yiwa wani mahaliki irin shi a duniya ba...
jin amsarta ya fahimci a filli yayi maganar ya sake damke hannunta gam cikin nashi yana murzawa ..
Jikinsa a sanyaye ya ciro wayarsa ya bugawa Abba ya sanar dashi abinda ya faru da Ummita ,abba yaji ciwon abun sosai dan shima ya kwallafa ranshi akan cikin amman tunda ga yadda Allah yayi ikonsa hakuri zaiyi , lokacin da mama taji har da kuka tayi a boye , hajiya Inna kuwa tamkar wacce akayiwa albishir da gidan aljanna daman kullum addu'a kenan Allah yasa cikin ya zube da cikin dan ita har lokacin bata yarda cikin na mahruf bane.
a parloun'n mama yan'uwa suka cika ana jajantawa juna , Inna kuwa na d'akinta tun da tace wa Abba Allah ya kyauta bata sake tofa albarkacin bakinta ba sannan bata tako part din mama ba ,duka gidan hankalinsu ya tashi hajiya umma tayi kuka sosai ba dan mahruf ya kasance d'anta ba saboda mama ne dan lokacin da zance cikin ummita ya fito taji dadi sosai mama zata sake samun zuri'a amman sai gashi sun rasa take ta soma magana "anya kuwa babu sanya hannu a fitar cikin nan ,jikina na bani akwai wani abu .. ?
Mama tayi saurin cewa "kai haba mufa muslimai ne bai kamata muna kawowa zuciyarmu irin wannan tunanin ba , Allah ya bayar kuma ya amshi abunsa , dole hajiya Umma tayi shiru ..
aunty ma data zo sai da tace akwai wani abu "ina jin tsoron dagin suhaima fa sam babu imani a zuciyarsu zasu iya aikata komai gaskiya ban yarda da zamansu tare ba gara ummita ta koma bangarenta daga kwana biyu har sunyi wata a guri daya .
mama tace " koma dai menene mu barwa Allah komai zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne muyi musu addu'a kawai "kunji matar nan wai muyi musu addu'a suwa kenan ..?
"Kinga ni diyata kawai na sani ,kuma ita kadai zan yiwa addu'a ba waɗan nan shedanun ba, kune baku da labari auren ita dayar yaya suhaimar ya dade da mutuwa wai mijin ya bude wordrob din kayanta zai dauki turare yaci karo da tukunyar tsafi shine fa yayi mata dukan mutuwa ya korota gida da takardar saki uku.."to Allah ya kyauta ya ganar dasu gaskiya suka ce "ameen daga nan suka shiga shirin zuwa asibiti .
Duk yadda suhaima ke rawar jiki akan ummita a banza dangin ummita suke kallonta har ta sha jinin jikinta ta kebe kanta gefe dan irin kallon tuhumar da suke mata babu sauki ..
Ummita bata farfaɗo ba sai cikin dare kuma har lokacin mahruf yana tare daita zuciyarsa cike da tausayinta, ta wani bangare kuma zuciyarsa na jin haushinta ganinsa har da gangancinta yasa suka rasa babynsu ..
A hankali ta bude idanunta sama tana kallon celling d'akin jikinta babu kwari ta waigo inda mahruf yake zaune kusa daita idanunsu ya tsarke cikin juna take ta gano inda take da abinda ya faru daita ,yadda taga ya dawo a cikin lokacin kankani yasa tausayinsa ya kamata musamman yadda ta lura yana son cikin jikinta addu'a ta soma yi Allah yasa bai rasa cikin ba , ta kai hannunta saman cikinta taji wayam babu tudun cikinta ta sake waigowa inda yake da saurin
Saurin kawar da fuskarshi yayi yana sauke numfashi da kyar , shiru yayi cike da d'acin zuciya alhankali ya soma magana "burinki ya cika tunda gashi kinyi sanadin da na rasa babyna ,daman kuma kin furta sai a zubar min dashi ,sai ki kwantar da hankalinki banda ma bakinciki irin naki ai kanki zaki yiwa yan'uwa amman kika bari gangancinki ya janyo aka rasa ....
ta tsura masa idanunta tana kallonsa ranta na kuna da kyar ta bude bakinta "ta nan kuma zaka biyo ?"Bata nan zan biyo ba ta sama zan biyo har suhaima nayi miki magana ki daina tsalle tsalle amman kika mata banza wa kika cuta yanzu ?" Ni ina da wata matar da zata haifa min yara kanki kika cuta wawiya kawai da bata san ciwon kanta ba ,ta yunkura da kyar ta mike zaune ta zuba masa idanunta dake narkar masa da zuciya sai dai yau babu abinda yayi tasiri acikin zuciyarsa illa haushinta da bakinciki "me yasa tun farko bata haifa maka ba ?
"Ko ita baka auratayya daita ne ?
"Kin min shiru da wannan banzar dakikiyar kwakwaluwartaki ,ko dan baki ga na rufeki da mahaukacin dukan hasarar ya'ya maza biyun da kika janyo min saboda bakinciki irin naki ,koda yake daman ba tun yanzu nasan da zaman kina min bakinciki akan duk wani abun farincikin da zai sameni a rayuwata ba ...
Bata san sanda ta riko hannunwansa duka cikin nata a gigice ba "yara biyu maza fa kace ?
ya galla mata katuwar harara yana ƙoƙarin fixge hannunsa cikin nata "ban sani ba ta narke idanunta cikin nashi tana girgiza masa kai "wallahi yaya ba da ganga bane , banyi maka ganganci ba ,ko zanyi ganganci ,bazanyi ganganci da rayuwata ba , wallahil azim kitchen zani domin dafa indomi saboda shi nake kwadayin ci kawai naji an turo ni ta baya amman nafi tunanin su....
"Shiiiiiiiiiii karki sake ki sako sunan matata ciki daman kina da niyyar aikata hakan kije ke da Allah dan bani da abinda zan miki .
jikinta na rawa ta sake damke hannunta cikin nashi "wallahi ba da ganga nayi ba babu sanya hannuna ka fahimceni wallahi turoni akayi ,ya soma ƙoƙarin zare hannunsa yana jan tsaki ta sake riƙe yatsunsa gam "shikenan koda bazaka yarda dani ba ka rufa min asiri dan Allah karka fadawa mama hankalinta zai tashi ,nasan muddin ka faɗa mata ɗauka zatayi da gaske ne da karfi ya fixge hannunsa ta koma ta kwanata sharaf akan katifa tana kuka kwakwalwarta na neman mafuta ranar dai karasa kwana tayi cikin kukan rasa ya'yanta yana zaune yana jinta yayi mata banza ..
Washegari tun da sassafe suhaima ta tashi ta haɗa break fast ta nufo hospital tana shiga ta isa gaban gadon ummita tana taɓa jikinta "sannu ummi ya jikin .?
Tayi mata banza batare data kalli inda take ba har tagama zuba surutunta ta samu guri ta zauna kusa da mahruf tana tambayarsa mai jiki "da sauki kawai yace atakaice ..
Yan'uwana suka cika asibiti banda mama domin duba jikin Ummita duk bayan minti ashirin mahruf zai shigo duba jikin ummita sai dai byn ya jiki baya sake cewa daita komai zai fice ,tun aunty na basarwa har sai da ta kirashi gefe "haba baba me yasa kake yin haka ?
"hakuri duk zamu taru muyi ka saki ranka ka nunawa matarka kulawa gaskiya bana jin dadin wannan shan kamshin da kake ,ya kake son yarinyar nan tayi ,ka kuwa san yadda uwa take ji akan ya'yanta idan ta rasa ? " A yanzu ita kadai tasan abinda take ji a zuciyarta , ya dai jita amman baya jin zai wani saurara mata a yanzu .
satin ummita daya aka sallamesu jiki a sanyaye ummita ta fito tana takawa aunty ta buɗe mata gaban mota ita da suhaima suka dawo gidan baya mahruf ya tada mota suka bar hospital zuwa gida bai tsaya akoina ba sai a tafkeken get din gidan yayi hon mai gadi ya bude musu, ya shigo kai tsaye inda aka tanada domin ajiye motoci ya nufa yayi parking daya bayan daya suka fito ummita na takawa a hankali sakamakon kafafunta da sukai nauyi saboda allurai da'akayita mata a asibiti ganin yadda take tafiya tamkar wace kwai ya fashewa a cikin ya tsura mata ido yana kallon every step of her wanda ke sashi jin wani irin sanyi a sansar jikinsa tuntube tayi sakamakon idanunshi dake yawo ajikinta "washhhhh Allah ta faɗa tana tsayawa haɗe da runtse idanunta aunty tayi saurin dafata "menene ummita ?
Ta runtse idanunta "kafata aunty " me kafarki tayi ?
"Ta rike bana jin zan iya takawa ..tayi maganar tamkar zatayi kuka a hankali ya k'araso ya tsuguna a gabanta ya rike daidai idon sawunta yana mammatsa mata kafar, batare daya kalleta ba ya dinga murza gurin , mutuwar tsaye suhaima tayi zuciyarta na tafarfasa tamkar ta kama da wuta kusan minti goma sannan ya d'ago ya sanya kwayar idanunshi cikin nata "how do you feel now ?
"Better ta bashi amsa tana rausayar da idanunta cikin nashi ya lumshe idanunshi tare da mikewa tsaye taku daya tayi ta sake tsayawa tana kiran "wayyo Allah bazan iya ta ... ..
bai tsaya jin abinda zatace ba ya sureta ya rungumeta ajikinsa ya soma tafiya daita a hankali take kallonsa tamkar wani sabon halitta a gabanta, yana jin yadda take kallonsa har ya isa bangarenta yana ƙoƙarin kwantar daita akan kujera a parloun, amman still bata daina kallonsa ba ya kwanto jikinta sosai har suna jiyo numfashin juna "kallon fa na menene ko na canza miki ne?tayi saurin runtse idanunta tana sauke ajiyar zuciya adaidai lokacin da aunty ta shigo haka nan taji gabanta ya fadi ta shiga bin parloun da kallo duk an gyara ko'ina, a hankali idanunta ya sauka a bakin kofar dakin ummita ta tsurawa gurin ido tana nazari kamar an fasa gurin , gabadaya yanayin gurin ya bambamta ,bata yi sanya a gwiwa ba ta ciro wayarta ta shiga neman layin malam musbahu ..
tana tsaye mah'ruf ya fita ya bar part din zuwa na suhaima, Suhaima kuwa a parloun'n ta tsaya tana zaria tana ciza lip's dinta bakinciki kamar ta mutu, ranta duk babu dadi taji haushin daukar da mah'ruf yayiwa ummita, can tunanin shirinta ya fado mata a hankali ta gizgiza kai tana murmushin mugunta "wallahi kota karfin bala'i sai na fitar dake a gidan nan, ba dai kema kin iya kissa ba , babu fa abinda ya samu kafarta tsabar iskanci ne kawai , haka ta dinga zance zuci daga karshe ta sake yin murmushin mugunta "na gama cika aikina na farko yanzu zamu shiga na biyu da ni kike zance ,makircina na biyu banyi niyyar aiwatar dashi yanzu ba amman zanyi dan kuntata miki ,zan sa ki shiga haula'i ,zan sa kiyi kuka jini da idanunki ,zan yi abinda da bakinki zaki furta bakya auren mah'ruf tana cikin zance taji sallamarsa tayi sauri juyowa tana hadiye maganarta ta k'araso jikinsa ta rungumeshi "sannu habibi ta kamo shi ta zaunar dashi bari na kawo maka ruwa ka sha nasan ka gaji ta rikosa ta zaunar dashi, taje ta bude fridge ta d'auko ruwa mai sanyi ta tsiyaya a glass cup, ta dawo inda yake ta zauna tare da mika masa ka sha kaji sanyi nasan har yanzu kana tattare da damuwa, dan Allah ka bari komai mai wuce a zuciyarka , ya amshi ruwan ya sha kadan ba dan yana bukatar sha ba .
"Habibi ta Kira shi tana kallon cikin kwayar idanunshi shima ita yake kallo "dan Allah ka natsu ka daina yawon damuwa da damuwar ummita dan wallahi da gangan tasa mukayi hasarar babymu ,kawai dai ban faɗa maka abinda naji tana fadawa amina da tazo last week ba, dan banason haddasa fitina amma wallahi tana sane ta bari mukayi hasarar babynmu ya tsura mata idanunshi sosai hankalinsa a tashe yace "ki faɗa min me ya faru ?
"Banason haddasa fitina dan haka ba sai na faɗa maka ba kayi hakuri kawai ni zan sameta nayi mata magana ta karasa magana tare mikewa taku daya tayi ya fizgota da karfi ya kafeta da idanunsa "kina hauka ne ki faɗa min .......
ta sauke naunayen ajiyar zuciya tana jin dadi sannan ta kai hannunta ta janyo jakarta ta ciro wayarta ta kunna masa voice note din data nad'a a ranar da menal tazo , take ya soma jin magana kasa kasa hirar ummita da meenal ,meenal ke faman bata hakuri ita kuma ummita na cewa "gsky bana son cikin nan duk yadda zanyi a ciresa zanyi, yana gama ji yayi wata irin zabura ya mike kamar mahunwanci zaki jikinsa na rawa take zufa ya shiga tsatsafo masa kamar ana watsa masa ruwan zafi a jikinsa ya juya a fusace tayi saurin riko hannunsa da sauri jikinta na rawa "haba habibi kai kuwa ina zaka daga jin magana ?
"Ban faɗa maka dan kaje ka sameta ba ,na faɗa maka ne dan ka sani , sannan ka daina yawon damuwa akanta tunda tana sane ta zubar "ki barni naje na ladabbatar da jikinta sannan na sheida mata nasan abinda tayi .
"no ko zakayi wani abu ba yanzu ba ka bari sai aunty ta bar gidan nan dan yanzu kana zuwa zata ɗauka ko ...
"Ko me ?
"ni dai plz dan Allah karka janyo min bakinjini agurinsu azo ana jin haushina ni kuma banason na samun matsala da yan'uwanka kaga ita tasu ce duk runtsi duk wuya bazasu sa ta bar gidanka ba nifa ?
Yayi shiru yana huci sannan ya koma ya zauna jagwab akan kujera yana fidda hucin numfash mai zafi ta dawo kusa dashi da kyar ta samu ta shawo kanshi..
Cike da sanyi jiki ya mike ya nufi d'akinsa ya faɗa kan gadonsa ransa duk babu dadi yana kwance ta biyosa ta kwanta jikinsa tana shafa kirjinshi ya mike "ki barni bana jin dadin zuciyata ya barta ya shige bayi ta girgiza kai kawai tana jin haushi "to ni meye nawa wallahi bazaka shiga hakina akan wannan shashar ba tayi tsaki ta fita , yayi wanka ya canza kaya zuwa kananan kaya riga blue da ratsin yellow duk ransa a bace yake hakan bai hanashi kyau ba kasa ya sauko bai yi mata magana ba ya wuce dining table , tana ganinsa ta mike ta zuba masa abinci ta turo gabansa ya soma cin abinci yana kallon agogon daya sha ado ajikin bango parloun'n dake walwali da hasken fitilu ya kara haskaka wa ..
Bai wani ci abinci kirki ba ya mike ya fita batare da yayi mata magana ba kai tsaye gidansu ya nufa ya wuce bangaren mama a parloun'n kasa ya sameta dan haka shima ya samu guri ya zauna suka gaisa "ya me jiki ?
"Taji sauki dazu muka dawo gida "to Allah kara sauki karka sakawa zuciyarka damuwa Allah daya bayar zai sake baku wasu masu albarka kamar ya fadawa mama ganganci da ummita tai masa sai dai ya share yana tare da mama har kusan magariba sannan ya wuce massalaci yayi Sallah ya koma gida part din suhaima ya wuce ..
Ranar dai bai sake daura idanunshi akanta ba sai washegari shima ya shiga ne saboda aunty dan yasan muddin ya fita bai shiga gurinsu ba zatayi magana , sama sama yayi abinda ya kai shi batare daya kalli inda take ba zai wuce gurin aiki ta dakatar dashi tana nuna masa abinda aka ciro "daga ina aka ciro wannan sharmen ? "a bakin kofar shiga dakin ummita gasu nan layu ne "to me ya kawo layu nan ?
"Kai da matarka za'a tambaya tunda kune a cikin wannan part din yayi shiru yana nazarin maganar idan dai zai fahimta zargin matarsa take ?
TWO FRIEND'S BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
*SUBSCRIBE TO MY CHANNEL HAUSA BAKWAI*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 57
cike da jin haushi ya juya yana ma aunty sallama "ni na wuce office , har ya juya tace "dawo ka zauna ina son magana da kai ya dawo jiki a sanyaye ya zauna yana
fuskantartata ,aunty ta numfasa kana ta soma magana a tsanake "wannan layun da aka ciro sihiri ne aka yi dan a shiga tsakaninka da matarka a hanaku zaman lafiya da juna, ina maka magana kana ƙoƙarin wuce wa saboda ka maida maganata banza .
Yayi shiru yana kallon aunty zuciyarsa na kuna da tafarfasa a dan fusace yace " aunty wa kike tunani zai yi asiri a gidan nan daga ni sai suhaima ne ,ita kuma nasan ba zata aikata haka ba ? yayi mata tambayar yana furzar da iska mai zafi .
" ni dai yanzu bana son wani dogon turanci ko wani tashin hankali ,
abinda nake so da kai ka sanya idanunka sosai a cikin gidanka sannan ka tsananta addu'a dan kai kanka baka tsira ba ,ko wannan matsalar data faru ta rasa bby's din da'akayi ba laifin ummita bane bare ka dinga jin haushin yarinyar mutane kana tsagwamarta babu garai babu dalili, babu uwar da zata ɗauki ciki ko na kwana uku ne taso ta rasa d'anta ko yarta bare har ya'ya biyu a lokaci daya , ko kai uban cikin baka kai ta son ya'yanta data rasa ba , Allah shi kaɗai yasan wanda yayi wannan mugun aikin kuma shi zai saka mata , amman kasa ido sosai Allah kuma ya tona asirin duk wanda yake da sa hannu tashi kaje Allah ya tsare ..
"Ameen ya furta haɗe da
mikewa cike da jin haushin ummita a cikin zuciyarsa, a ransa yace " sharri zata yiwa matarsa kenan duk abinda take mata bata gani , da sharri zata saka mata dashi ? tunanin matakin da zai ɗauka akan wautan da ummita tai masa da kuma sharrin data yiwa matarsa yake har ya qarasa office ,aiki yake amman zuciyarsa da gangar jikinsa na gurin ummita , wani iri ya dinga ji akanta ,qirjinsa ke wani irin mahaukacin dokawa da karfi duk saukar numfashinsa da tunaninta yake sauka da baby's d'insa daya rasa, zuciyarsa na matukar zafi ya tashi ya qarasa inda fridge yake ya buɗe ya ɗauki goran ruwa ya dawo kan kujera mai zaman mutun uku dake ajiye a office din ya kafa a bakinsa sai daya shanye tasss sannan yayi wurgi da roban ya dafe goshinsa da hannu daya yana furzar da hucin numfashi ,a hankali maganar aunty ke dawo masa ya mike tsaye ya rungume hannunwansa duka a qirji "daga shi sai suhaima ne a gidan shi dai yasan ba shi ya binne layun ba, haka baya zargin suhaima , yasan tana da tsananin kishi akansa amman kishinta bai kai ta dauki hakin rayuka biyu da binne wannan layun da aunty ta nuna masa ba ,"to wanene idan bashi bane kuma ba ita bace ta aikata haka? ya jefawa wankakkiyar kwalkwaluwarsa tambayar "lallai ya tabbata akwai mai kawowa rayuwarsa farmaki "to waye wannan ? ya tsaya cak a tsakiyar office din yana nazari da son gano wanda ke ƙoƙarin kawowa rayuwarsa hari shiru yana tsaye kusan minti goma sannan ya koma mazauninsa ya cigaba da aikinsa ..
Matakin farko da mah'ruf ya soma dashi shine shariya, ya share ummita iyakacin ya shigo bangarenta ya duba lafiyar jikinta ya kama gabansa ,wannan abu ya tsaya wa ummita a rai matuka ga kuma rasa ya'yanta har biyu data yi abun ya dameta kwata kwata taki kwantar da hankalinta kullun kuka, shima bangarensa dauriya kawai yake amman zuciyarsa da hankalinsa na kanta , aunty na iyakacin kokarinta gurin bata kulawa ta kowane bangare amman jikin ummita sai sake sukurkucewa yake babu wani cikowa da tayi , har tsawon kwanaki uku da dawowarta babu wani canji zuciyarta na tattare da damuwa, tana jin ciwo da rad'ad'in rasa baby's dinta da tayi, suhaima na shigowa jifa jifa duba jikinta da kawo mata kayan motsa baki sai dai duk abinda take idanun aunty na kanta sannan ko da wasa aunty bata yarda su ci abinda take kawowa ba , haka zai gama gantalinsa ta zuba a leda ta kai shara.
Zuciyar aunty ta kasa hakurin abinda idanunta suka gani , ta nemi hajiya umma tace " tazo su tautauna akan wata matsala , hakan ce ta kasance, Abdurrahaman ne ya kawo hajiya umma ya kama gabansa da zumar idan ta gama ta kirashi yazo ya maidaita gida , suna zaune a parlou'n ummita ,aunty ta tashi ta d'auko laya data adana a cikin flowers din dake zagaye da part din ummita ta nuna mata tare da yin shiru tana dubanta ,"menene wannan salama ? " Ki bude ki
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 59 Chapter of 76