ajikinka?
" yawon bin mata ka fara bansani ba ?
"me na rasa ajikina ?
"Ko kuma me na rageka dashi da zaka soma bin mata "ki natsu dan Allah ba wani guri na kwana ba a gida na kwana ...
"karya kakeyi wallahi da a gidan ka kwana kai tsaye zaka faɗa min gaskiya saboda baka karya na sanka nasan halinka ...
Wani irin bakinciki ne mai hade da zallar bacin rai ya tokare masa makoshi "idan baki yarda da maganata ba ,sai ki yarda da hukuncin zuciyarki ya zagayeta ya zai shige d'akinshi ta sha gabansa tana huci ....
"kina hauka ne ko kin soma shaye shaye ne da zaki sha gabana ?
"Duka nayi , ba laifinka bane dan kaga ina mutuwar sonka ne ,amman kasani soyayyarka bazata rufe min ido na kasa kwatar yancina ba ,gefenta yabi ya shige d'akinsa
aiko cikin sauri ta biyo shi tana zuba masa bala'i iri iri "wannan zalunci ne da rashin daukata da daraja da kayi , idan ma a gidan naku ka kwana ai an san kana da mata da za'a daure maka gindin ka kwana a can , Allah dai yana gani kuma sai ya saka min ,soyayya ba hauka bane ban ga laifinka ba laifina ne ,wallahi duk wanda yake da saka hannu akwananka wani guri Allah ya tsine masa albarka .......
ta karasa maganar tana shako wuyan rigarsa tare da shigewa jikinshi tana kuka " duk maganunta suna shiga kunnuwanshi amman yayi mata banza yaki tanka mata saboda yasan bai kyauta mata ba ,amman ba zai dauki tsinuwa daga gareta ba ta bude bakinta da niyyar sake furta wani abu kawai taji ya zareta ajikinsa ya ɗauketa da wani gigitaccen mari Wanda yasa ta saki kara ....
ta d'ago tana dubansa tare da kankace idanu "ka mareni ?
"Yes ko zaki rama ne ?
"Bafa tsoronki nake ji ba da kike fadar duk abinda yazo bakinki ya karasa maganar yana shakota ya makata da bango "to be your last warning da zaki tsaya gabana kina faɗa min magana ko na miki kama da dan iska ko me neman mata ?
"Ko ki yarda ko karki yarda a gidanmu na kwanta a rikice ta soma kokarin kwatar wuyanta tana nishi da kyar "ban iya duka ba shi yasa bana son yi ya d'ago kanta yana jinjigata "idan bakya control din bakinki zakiji jiki a hannunsa saboda ni ba irin waɗan mazan bane bazan kyaleki ba , zan ɗauki mataki akanki ya karasa Maganar yana wurgi daita ya take wuyanta da kafarshi ..
Manage
TWO FRIENDS BSBD
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
MUHAMMAD AUWAL KANINA NA KAINA NAYI MISSING DINKA SOSAI SAURAN KACE NICE KANWARKA ..
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 42
..... bai ɗauke kafarshi ba sai daya fahimci numfashinta na ƙoƙarin barin jikinta sannan ya ɗauke kafarsa yana shureta ya nufi bayi "kafin na fito ki san inda dare yayi miki stupid kawai yaja tsaki yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya shige toilet ..
Kuka take sosai rike da wuyanta tabi bayansa da kallo tana sake fashewa da wani sabon kuka tare da d'aura hannuwanta duka a saman kanta "na shiga uku ta furta a fili sannan tayi kokarin mikewa ta bar d'akin cikin sauri tun kafin ya fito ya iske ya ninka mata wanda yafi na yanzu ..
Tana shiga d'akinta ta ɗauki waya ta kira hajiya rahma kira daya ta ɗauka tana jin ta ɗauka ta sake rushewa da wani kuka "yayyarmu na shiga uku ina cikin wani hali mah'ruf bai kwana gida ba jiya sai yanzu da safe ya shigo nayi hasarar nagani nan .....
"Nayi missing last hope dina tunda aiki ba wani tasiri yake ajikinsa ba, ko ma yayi zuwa wani lokaci zai karye ki taimakeni yayyarmu karki barni haka "
Naunauyen ajiyar zuciya hajiya rahma ta sauke "shikenan ki natsu ki kwantar da hankalinki yanzu aka kirani zulaihat sun samu matsala da mijinta idan na dawo zamuyi waya "
Da sauri ta tsaida kukanta tace " matsala yayarmu to ko nima na taho ne ?
"A'a kiyi zamanki duk abinda ake ciki zakiji, idan kuma kinji zaki iya zuwa shikenan ki taho din mu haɗu a gidanta "ok gani nan zuwa yanzu ta katse kiran tare da faɗawa bayi tana tunanin irin kamun da zata sake wa mah'ruf , dan dole ta mallakeshi completely , sannan dan dole ya sawwakewa wacan tsinanniyar yarinyar tana bakinciki aurensa dake kanta ..
a lokacin ɗaya suka fito da mah'ruf ya tsaya jikin motarsa yana kallonta a tunaninsa yaji zatayi har zai shiga mota ya dakata ya soke hannunsa ɗaya cikin aljihun wandonsa yana nunata da keyn mota "wallahi ! wallahi !! idan kika yi kuskuren fita ko bakin get din gidan nan ne ki tabbatar da kin saku agurina , ba zaki sake dawowa rayuwa mah'ruf ba har abada yana gama faɗar haka ya bude mota ya shige ya bar gidan..
Dole ta juya ta koma ciki tana hura hanci "dani kake wallahi zaka san baka da mutunci ..
sai gurin goma ummita ta farka duk wata d'awainiyya ta gidan mahruf ne yayi da kyar ta iya yunkurawa ta sauko saboda gabobin jikinta da taji sunyi mata nauyi ga wani ciwo da suke mata uwa uba kasanta da take jin wani rad'ad'i tamkar ana tsagata , jikinta duk babu dadi ta dinga jin tamkar ba a gangar jikinta yake ba ,
kasa tafiya tayi , ta durkushe a kasa tana ciza lip's dinta.
a hankalin ta soma rarrafawa a daidai lokacin ya shigo d'akin jin motsin shigowarsa yasa ta koma ta zauna tana dubansa sanye cikin riga yellow da bakin wando ,saurin runtse idanunta tayi tana yatsina fuska,
da sauri ya k'araso ya tsuguna a gabanta ya kamo hannuwanta duka cikin nashi yana massaging ahankali "ya dai meke damunki?
yayi mata tambayar yana d'ago habarta tare da zuba mata manya idanunshi masu bugar mata da zuciya ....
Kawar da kanta tayi gefe tana matse hannuwansa cikin nata "wallahi gaba-daya ilahirin jikina ke min ciwo tayi maganar a shagwa'be hawaye na zubo mata bisa kuncinta ..
tausayinta ne ya kamashi kamar ya zubar da kwalla ya kamota ta kasa mikewa tsaye "na taimaka miki ?
Tayi shiru tana kuka hancky ya cire a aljihunsa ya kai goshinta ya fara goge goshinta zuwa kuncinta yana kallonta itama shi din take kallo tana cigaba da kuka , bai sake sauraratar ba ya maida hancky aljihunsa ya ciccibeta yayi bayi daita ya zaunar daita a bathtube ya tara mata ruwa mai zafi "ki gasa jikinki da ruwan zafi.
sosai ya matsota kamar zai shige jikinta ya kai bakinsa dai-dai kunnenta ya hura mata iska bakinsa sannan ya soma magana cikin rada "wannan yanayin naki kamar kinyi kokuwa da wani ciki bacci ......?
ya karasa maganar yana tsotsar cikin kunnenta
Tayi saurin kawar da kunnenta dake cikin bakinsa ta tsura masa fararen idanunta "haka ne ko ?
ta girgiza masa kai " ki dai kiyi tunani saboda gabadaya yanayinki ya nuna haka dan haka kiyi hado da wankan tsarki yana gama faɗar haka ya juya ya fita ta bishi da kallon mamaki zuciyarta cike da tambayoyi iri iri "mamaki maganarsa da kuma sauyawarsa take, gabadaya a cikin tamkar ba Mah'ruf din data sani ba ...
A hankali ta samo zubawa jikinta ruwan zafi , kwakwaluwarta na tsanata tunani tana watsawa jikinta ruwa da kasanta da take jin wani azaɓaɓɓen zafi "lallai tayi kokuwa cikin baccinta ko mafarki zata ce , to amman ya'akayi shi ya sani ?
Ta yiwa kanta tambayar cike d'acin rai haɗe da bakinciki "baza'a yi wanka tsarkin ba ,ta furta tana furzar da numfashin tana tsotsa tsakiyar kanta "uhmmmm ummita tunda kina da tabbacin kinyi mafarkin mafi alkhairi kiyi wanka kawai da wannan shawarar tayi wankan tsarki , ta cigaba da zubawa jikinta ruwan zafi cikin ikon Allah yadda ta dinga ruwan jikinta ruwan zafi ta som a jin dadin da sanyi na ratsata daga karshe ma tashige cikin ruwan zafi gbdy ta dade sannan ta fito tana dingisa kafarta ...
ta shirya cikin wani had'ad'd'en atamfa riga da siket tana d'aura d'ankwali ya shigo kamar ya zame dankwalin yayita kallon gashinta yaji ,amman bazai iya ba "muje kiyi breakfast wani sabon mamaki ya kamata, tayi sororo tana kallonsa dan zuwa lokacin lamarinsa ya soma bata tsoro, bata gama mamakinsa ba ya k'araso inda take yana fuskantartata har numafashinsu na tsarkewa guri ɗaya ,
taji ya kamo hannuta "tunanin me kike yi, kin wani tsare mutane da waɗan idanun naki ?
Tayi shiru taki cewa komai , ya lumshe mata idanunshi muryarsa a kasalance yace "ki daina min irin wannan kallon mai cike da abubuwa ,
"dole nayi dan ka soma bani tsoro ta fadi a kasan ranta ..
"Ok mamaki kike yi dan na tausaya miki?
Ta hura masa hanci kawai batare data yi magana ba
" Bai kamata ki tsaya mamaki ba tunda haka ba wani sabon abu bane ba kuma shine karo na farko da zan taimaka miki ba " ke din tsoka ɗaya ce agurin mamana tun tana raye ta damka amanarki a hannuna duk da babu soyayya tsakaninmu bazan iya tsallakeki cikin hali na rashin lafiya ba , ya k'arasa magana yana sake matsota sosai yana shishina jikinta , tayi saurin ja da baya taji kamar numfashinta zai dauke , gabadaya ta rikice tare da yin kasa da kanta , bai san yadda akayi ba shi dai kawai ya ganshi a gabanta suna fuskantar juna kaɗan ya rage qirjinshi bai haɗe da nata ba , cikin tashin hankali ta kai hannunta ta tokare qirjinshi batare da tayi magana ba hakan yasa qirjinshi ya tsananta dokawa , ya tsaya shiru haɗe da kafeta da idanunshi, kallonta yake kamar wata sabuwar halitta a gabanshi kafin daga baya ya shafa sumar kanshi yana lumshe idanunshi haɗe da furzar da iska mai zafi kana ya ɗan ja baya kaɗan yana shafa goshinsa "menene haka kake yi mah'ruf you have to control your self , ya kake ƙoƙarin fito da felling dinka alhalin ba sonta kake yi ba ? Mikewa yayi tsaye yana
Yarfa da hannunshi sannan ya tura hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa "muje kiyi break sai na kai ki hospital , cike da karfin hali ta soma daga kafafunta tana dingisawa ya biyo bayanta yana kare mata kallo komai nata irin wanda yake so ne ina ma yana sonta ?
Ganin yadda take takawa da kyar ya matsota ya ɗauketa ya rungumeta a jikinsa ta ware idanunta da mamaki tana cewa "no karka d'aukeni Ina da kafa .
Idanunshi na kanta yace "yau kafafunki basu da wani amfani dole na taimaka miki ta bude idanunta tace "no ..
Maimakon ya sake yin wata magana kawai ya cigaba da tafiya daita ajikinsa suka sauko parlour'n kasa ya ja kujera da kafarshi ya zaunar daita ya duko ya daura habarsa akafadarta tana jin yadda yake sauke naunayen ajiyar zuciya wanda tasa zuciyarta curewa guri daya kusan minti goma suna haka babu wanda yayi magana sannan ya zauna kusa daita ,da kanshi ya zuba mata abinci ya turo gabanta "eat "
zuciyarta ta sake cika da wani sabon mamaki abu kamar a farki ko dai har yanzu cikin dreaming take ?
"shi yayi girkin ko kuwa amso mata yayi agurin ummah ?
"Ke yanzu ina ruwanki ko shi ya girka ko amsowa yayi , ke dai kici kawai ?
duk motsin da tayi idanunshi na kanta daidai da cin abinci abun sha'awa ne ,sai juya karamin bakinta take a hankali ya ɗauki cup din ruwan zafi ya kai bakinshi ya kur'ba yana kallonta ta mike da kyar bai ce mata komai ba ta koma kan kujera ta kwanta , bayan kamar minti goma ya mike "tashi muje asibiti a dubaki ta yatsina fuska "na warke fa bana jin komai "ke banson iskanci ki tashi muje ko dan Kinga ina lalla'bakin kin ma yi wankan tsarki da nace miki ?
Jikinta a sanyaye tace "nayi ta yi mgn tana mai tsananin jin kunya " to ki tashi ki ɗauko mayafinki muje "
Mikewa tayi tana tafiya a hankali "ke tsaya ..
Cak ta tsaya a inda take, tana kallonsa ya haura sama cikin mintunan da basu wuce biyu ba ya sauko ya cilla mata hijab ya ɗauki jakarsa yayi gaba kulawa yake son bata amman yasan halinta batsare masa zata yi daga karshe suyi faɗa batare da ya kaita taga likita ba .
wani asibitin kudi ya kaita ya kebe da wata nurse yayi mata bayanin komai "dan Allah kisan yadda zakiyi aiki batare da gane komai ba, sannan ya had'ata da ummita , kallo ɗaya likita tayi mata ta fahimci bata samu wata matsala ba tunda tana iya takawa , amman duk da haka sai daya tayi mata yan tambayoyi yadda take jin jikinta tana bata amsa "ina ganin effetion ne yasa kika ji kasanki yana miki zafi ,kwanta na dubaki cike da jin kunya ta kwanta ta dubata babu wata matsala tayi mata allura tare da bata magani sannan ta sallamesu a kofar gida ya sauketa "ki tabbatar kin sha magani
Ta 'daga masa kai ta fita , ya ja motarsa ya kara gaba .
tana shiga bangarensu ta sake sulalewa ta kwanta tana mamakinsa , ta rasa a wani muhalli zata ajiye wannan sabuwar kulawar data samu daga gareshi zuciyarta ce ta soma mata magana cike da gargadi "ki daina mamaki kamar yadda ya faɗa miki ai ba yau ya fara taimaka miki ba, kuma duk abinda zai yi saboda mama yake yi ba saboda ke ko aurensa dake kanki ba.
"to ai ni ina son wannan kulawar daga garesa me yasa bazai min komai dan karan kanshi ba sai dan darajar mama ....?
Tayi maganar a fili hawaye na zubo mata " shikenan ni haka zan kare rayuwata babu farinciki ?
"Ke kika so yin rayuwarki haka ai mijikn ne me yasa bazaki saki jikinki dashi ba ta yadda zai damu da lamarinki?
"Oh my goodness I need happiness from him ta fada cikin zuciyarta ta jima kwance tana tunaninsa hawaye na cigaba da bin kumatunta cike da sanyin jiki ta mike da kyar ta fita daga part dinsu zuwa nasu meenal ..
zubewa tayi a gadon meenal , ta kalleta "yar'uwa ya jiya kika kulle kofa nazo nayita bugawa har na gaji na dawo "wallahi wani irin mahaukacin bacci ne ya daukeni ban ma san ya'akayi ba sai farkawa nayi na ganni a dakina yanzu haka ma bacci nake ji ,ta juyar da kanta tare da daura akan pillow ,"bari na runtsa kad'an "okay inji cewar meenal " a hankali bacci ya d'auketa tare da tunanin mahruf .
yadda tunansa ya addabi ruhinta ,haka shima tunanita ya addabishi a office duk motsi sai ya jita acikin zuciyarsa,
barin aikin yayi ya tsurawa celling dakin ido take ya soma gani tana yi masa gizo wai gashi tana tahowa gareshi har ta shige jikinshi aiko bai san sanda ya rungume iska ,yayi mata riko mai karfi kamar za'a kwace masa ita sai bude idanunshi tayi yaga wayam rungume da jikinshi "meke damuka ne ?
You have to stop all this nonsense mah'ruf ,me yasa kake zurfafa tunanin yarinyar da bata damu da kai ba ?
" ka natsu mana duk kana neman saka kanka cikin damuwa plz control your self ya faɗa a bayyane yana mai dawo wa cikin haiyacinsa ..
wunin ranar gabadaya ya rasa sukuni , ummita ta sake tsaya masa arai wani lokaci yayi murmushi wani lokacin yaja tsaki, kowa ya ganshi yasan akwai wani farinciki dake tattare dashi daga gurin aiki kai tsaye gidan ya nufa yana taɓa kofar yajita a kulle dan haka ya nufi part din ummah dan yasan bazata wuce nan ba ,yana shiga daita ya soma cin karo suna kallo ita da meenal suna dariya suna ganinshi kowace ta shiga hankalinta ya k'araso ciki sosai ya zauna opposite din ummita , meenal ta gaishe "sannu da zuwa yaya ,
Ya amsa a ciki kamar koda yaushe .
itama batayi kwaron baki ba ta gaisheshi "ina yini ? ta ɗauke kanta
"Lafiya ya jikinki ya faɗa tare da d'ago kanshi a hankali ya tsura mata ido ,ta sake dawo da fuskarta taga ita yake kallo har lokacin yana cizan lip's d'insa dukkaninsu suka tsaya shiru suna kallon lumtsamsun idanun juna a hankali ta motsa bakinta "na..naji sauki tayi maganar muryarta na shaking .
Ya ɗauke kanshi adaidai lokacin da hajiya ummah ta fito daga d'akinta "waye bashi da lafiya kuma ?
Da hannu ya nuna mata ummita "shine baki faɗa ba kika zauna kallo da ciwo tun safe "naji sauki fa ummah, wallahi babu inda ke min ciwo yanzu "to shikenan Allah ya sauwake "ina yini hajiya?
"lafiya lau ya aiki ..?
"alhamdullahi atare ummita da meenal suka mike sukayi ciki ,nan suka soma hira da hajiya umma"wai har yanzu ba zaka yunkura akan tarewar ummita ba yau wajen wata uku zamu shiga na hudu kenan abun fa ya fara damuna gsky taja numfashi ta sauke " gaskiya kayi wani abu akai kowa ya kawo ido ya saka , mamanka fa ba zataji dadin hakan ba "hajia ku nake gujewa shiga damuwar hajiya inna " haka ne amman dan Allah kayi wani baba bana jin dadi ganinta zaune haka ita ba bazawara ba ita ba gidan mijinta ba "kamin alkawarin zakayi wani abu ..
"Karki damu inshaallahu zanyi komai dan faranta ranku , ki bani lokaci "shikenan Allah yayi maka albarka Allah ya tsareka da tsarewarsa "ammen ya rabbil alameen.
Bai koma gidan ba sai bayan sallar isha'i yayi wanka ya fito sanye da farar riga da boxer can iya cinyarsa ,ya zauna akan dining babu komai akai , sai gwangwanin milo da madara flaks da cups da bread da wasu abubuwa amfani , tsawon minti goma yana zaune sai gata ta fito tana cika tana batsewa, idanu ya zuba mata yana kallonta ta wuce shi ta zauna kan daya daga cikin kujerun parlourn ta canza tasha zuwa zeeworld ,bai taɓa especting zata iya sharesa ba ,da kamar bazai yi mata magana ba sai dai yayi karfin halin cewa " ina abinci ?
Ya tambayeta yana sake tsareta da manya idanunshi "banyi ba ta bashi amsa atakaice tana yatsina fuska .
"akan wani dalili kenan bayan ga kayan abinci birjik a gida ko akwai abinda babu ne ?
Ya sake tambayarta yana kallonta ,
"ko ɗaya akwai komai ta mike tana jijjiga jiki tana tahowa inda yake "kaje inda ka kwana jiya kaci dan ni ba baiwarka bace , auroni kayi bazai yiwu na wuni ina kokarin ganin nayi maka abinda zai faranta maka ba amman kai kullun cikin bakanta min kake ," kunnenki da jikinki bai ji abinda da na faɗa miki da safe kafin na fita office ba kenan ?
" Bansani ba abinci ne dai bazan sake girkawa acikin gidan ba, idan kace kaine nima nice wallahi nafika tashanci kawai makewa nake dan a zauna lafiya, amman tunda iskanci ne abun mu zuba ..
"gidan kika zo dan nafiki iyashi suhaima idan kin sake girki a gidana baki haifu ba cikin uwarki da ubanki ba ,ya mike ni za'a kawo iskanci acikin gidana ?
" idan kin hanani banzan abincinka inda wata matar da zata bani naci na koshi ...
,"oho kace dama can kake lalla'bawa gurin wannan laananiyyar yarinyar mai siffan aljanu yar ...
Saukar yatsunsa ya sa ta katse maganarta ta da kuncinta "kika sake zaginta sai na miki dukan mutuwa , mara mutunci kawai ....
"Ni ba sakaran namiji bane dole kiyi abinda nake so ,wallahi ki kuka da kanki tunda kika bari na fahimceki ,a fusace yake magana "girki kuma dole kiyi tunda ina da halin da za'a girka koda ba zanci ba sai kin girka..
a matukar zafafe ya nufi d'akinsa yana huci tabi bayansa da kallo tana rike da kuncinta ..
Ya faɗa saman gadonshi tare da runtse idanunshi maganar mahaifiyarsa ya shiga dawo masa ya tuna damuwar daya gani akan fuskarta lokacinbda take masa maganar ummita dan dole ya nemo mafuta domin ya faranta zukatan iyayensa ...
Da sauri tashiga dakinta number hajiya sadiya ta kira, kiran bai kareta da komai ba illa bakinciki dan mugun labari taci karo da shi mijin yayarta zulaihat yayi mata saki uku bayan ya mata dukan mutuwa sakamakon tukunyar tsafin daya ci karo dashi acikin kwa'barta tukunyar ta fadi ne tare da fidda hayaki wanda yasa take ya dawo haiyacinsa "ki bari miji da abinda ya sanyo kai kisan yadda zaki lalla'bashi kafin mu san abun yi , akwai matsafi da hajiyarmu zata kwatanta min inda yake a ijesha cikin satin nan zamu ki lalla'bashi yanzu kije ki kwantar da kai ki bashi hakuri ki nuna masa kinyi nadama "shikenan yayarmu zanyi yadda kikace ta katse kiran bata tsaya bata lokaci ba ta nufi hanyar d'akinsa .
Zumbur ya mike i yana kallonta fuskarta Shabe Shabe da hawaye idanushi sun rikide sunyi jawur tsabar bakinciki "maza ki barni daki kafin na taso ta soma buga kanki da bango uban me ya dawo dake ?
Saurin durkushewa tayi kasa ta hade duka hannuwanta guri ɗaya tana kuka "kayi Allah da Manzonsa kayi hakuri nayi realize din mistake Dina nasan ba halinka bane amman Dan Allah kayi min uzuri na tuba bazan sake ba duk abinda nayi na yi ne dan tsananinn kaunar da nake ma ka yafe min saukowa yayi daga kan gadon "You have fall ya faɗa sannan ya nufi fridge ya bude ya dauko ruwan roba ya kafa abakinsa ya sha sosai sannan ya rike ragowar a hannunsa "kin fadi warwasss suhaima ni kika kalla kika dinga fadawa son ranki ,wallahi kin sa zuciyata tashiga kwankwanto akanki naji gabadaya nayi danasani aurenki na ɗauka mai tarbiya na aura ashe tantiriya yar tasha na kawo gidana ban sani ba ..
"Nayi dana sanin aurenki dana yi amman nasan abinda zan yi zan datse au......
cikin hawaye ta matso gareshi ta rike kafafunsa "na shiga uku karka sakeni gara ka kasheni akan ka furta wannan kalmar wallahi nayi nadama idan ka sakeni ban san yadda zanyi ba ,na tuba bazan sake ba wallahi bazan kara ba sharrin sheidan ne"bazaki canza ba koda na yafe miki saboda asalin boyayyen halinki kika fito dashi wannan shine halinki na asali ,halin da kike nunawa yanzu na munafurci ne dan haka gara kawai na ...
Da sauri ta mike tsaye ta dauki alqur'anisa dake ajiye akan Dre's mirrow ta daura akanta "wallahi na daina bazan sake ba take jikinsa yayi sanyi ya tsura mata ido yana kallonta cike da tausayawa "ka yarda dani bazan sake ba idan na sake na yarda kayi komai lumshe idanunshi yayi ta zube ta kife kanta bisa kafafunsa tana wani irin kuka a hankali ya kai hannunshi ya d'agota ya rungumeta ",is okay na yafe miki komai wuce ya shiga shafa bayanta ta kamkameshi ajikinta....
Tun daga wannan lokacin bata sake shiga lamarinsa ba ko me zai yi ido ne nata , yayinda ummita ta kauracewa part dinsu ta dawo part din hajiya Umma saboda tsoron daya soma bata , dan kusan rana day day ne bata felling ana yi wani abu daita ,duk da tafi tunanin mafarki ne ,hakan da tayi ya kawowa mah'ruf cikass dole ya hakura daita sai dai kullun zai zo safe dare da ,da safe ne kawai yake samunta a a part din amman da zarar dare yayi zata gudu part din hajiya umma ...
******
A wata safiyar asabar ummita ta tashi da zazzaɓi mai zafi sai dai bata , faɗawa kowa ba har abbanta bata bari ya sani ba sannan ko bangaren hajiya umma bata shiga ba , ko daya shigo bai kalli inda take ba ya kwana tare da ciro system dinsa ya da'ura akan Centre table ya soma aiki ko yar gaisuwar da take masa batayi ba ,kanta ke matsanancin sarawa da cikinta , jiri ya dinga dibarta duk da kasancewar a kwance take tana felling ,a hankali ta dinga jin aman
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 41 Chapter of 76