kice ya barni har ayi suna "shikenna tana jin motsin shigowarsa ta kwanta da sauri tayi kamar mai bacci .
"assalamu alaikum ya shigo bakinsa ɗauke da sallama"wa'alaikum Salam "barka da yamma hajiya "barka ya aiki ?"alhamdullahi ya faɗa yana leka bayanta inda ummita take "ita wannan bacci me take da yamma ta tashi mu wuce gida ?
" tana nan har sai anyi suna ,ta faɗa tana haɗe rai ,yayi shiru yana kallon ummita dake kwance shi da yayi niyyar cin kaniyarta yau "ko ba zaka barta bane ka tsaya kana kallona ? "shikenna sai anjima "mujima dayawa yana fita ummita ta mike cike da jin dadi ta rungume hajiya umma "shiyasa nake sonki ummana, hajiya ummah ta shafa kanta karki damu diyata ki saki jikinki cikin yan'uwanki kinji karki damu kanki , babu abinda zai yi , tayi murumushi tana barin dakin..
Tun daga ranar mah'ruf bai sake takowa gidan ba ,haka bai kirata a waya ba ya tattarata ya watsar , ta soma damuwa duk ta kasa sakewa acikin mutane , sosai hankinta ya tashi da rashin ganin kiransa sai tayi kamar ta kirashi sai zuciyarta ta hanata , ta danne zuciyarta ta cigaba da shirye-shiryen sunah ..
Hajiya rahma taji shiru Alhaji Umar bai sake mata batun aurensa ba ,kwata kwata harkan gabansa yake dan haka ta ɗauka aikinta yaci ,tana zaune a kusa da mahaifiyarta kasancewar ita ke jinyarta tare da matar dake kula daita , ya kirata yace "zai yi tafiya zuwa dubai wata daya zai yi zuwa biyu ya tura mata kudi ta account dinta tayi fariciki sosai tana duba karamar wayarta da take ganin alert 500k ta gani ta lumshe idanunta tana narkar da murya "na gode mijina Allah ya kara budi ,allah ya kai min kai lafiya ya dawo da kai lafiya abinda aka tafi nema Allah yasa a samu "ameen ya faɗa yana mata sallama .. .
kullum sai mah'ruf ya sauke suhaima asibiti sannan ya wuce aiki haka zasu tasa mahaifiyarsu gaba suna kuka saboda surutan da take ya soma over , "suhaima rahma Kunga yadda na dawo ko ? " an yanke min yatsa sannan aka dawo kafata daga yanzu bani da idon sawu , tayi maganar tana dariya shikenna na dawo mai dungulumi bazan taka da kafafuna ba ,kuyi hakuri ya'yana ina nan tare daku bazan mutu yanzu ba sai naga auren jikokina da ya'yan auta tana magana tana tsotsa tsakiyar kanta da jikinta suna cikin haka kawar hajiyarsu ta shigo tana ganinta ta washe baki tana zazzaro ido "a'a hajiya hasana ! hasana ce ! hasana ce !! sannu da zuwa hasana ki zauna mana ga guri nan Kinga yadda na dawo ko ? "Na gani kawata Allah ya kare mu da lafiya ta fadi tare da zama , suhaima da hajiya rahma suka amsa da "ameen suna gaisheta "ya jikin zulaihat ance itama tayi karaya a kafa "wallahi amman ta soma jin sauki inji cewar hajiya rahma ta ɗan dade suna tautaunawa akan ciwon sannan tayi musu sallama ta wuce ..
Ranar suna baby yaci sunan kakan abdulshakur Muhammad Auwal ,suna yayi dadi sosai yan'uwa da abokan arziki sun hallara ,dangin abdulshakur sun yi bajinta, haka ma ta bangaren menal y'an'uwanta sun yi abun arziki babu wanda bai yi rabo ba, ummita tayi kyau sosai duk inda tayi idanu suhaima na kanta dan gano ko tana dauke da wani cikin duk sanda suka hada ido sai gaban ummita ya fadi yayinda suhaima ke sakar mata murmushinsa mugunta take ta shiga karanto addu'ar neman tsari daga sharrinta dan tsoro take bata sosai ..
Bayan anyi suna mahruf yaki cewa ummita ta dawo, ita kuma tana jin tsoro komawa yaci ubanta ,dan haka ta cigaba da zama a bangaren Hajiya umma tare da menal sai duk abun duniya ya isheta tana kewar mijinta , ganin an tafi wajen kwana goma ga yanayin ummita ya nuna tana bukatar komawa ga mijinta, yasa Hajiya umma ta kira shi, bayan yazo ta dinga zuba masa ruwan bala'i a gaban ummita ta inda take shiga bata nan take fita ba "kiyi hakuri Hajiya "karka bani hakuri laifi kamin da zaka bani hakuri "ina lura da kai baka qaunar ganinta cikin y'an'uwanta dan tana aurenka sai akace maka bazatayi zumunci ba ? wallahi idan baka saki ranka ba zan hanata dawowa gidanka gaba-daya naga ta tsiya da gaba , daman ina bakinciki da zubewar da cikinta yake a koda yaushe ,ga jarabarka gata matarka ina dalili da me zataji ko dan kunga akwai ido an saka muku , dan Allah idan ta koma kayi mata wani abu kaga abinda zanyi ,ko kallon banza ban yarda dashi ba, ya dinga kallon ummita dake zaune tana kallonsa take ya dinga zabga mata harara "ki tashi kuje ko harararki yayi ki faɗa min..
Ta narke fuska cike da shagwa'ba tana rungume da abban abba sunan da suke baby dashi kenan , ta nuna shi da yatsan hannunta ɗaya "ai gashi nan ma hararata yake gara kawai nayi zamana , ta karasa maganar tana kuka , ya zaro ido yana Kallonta "kina hauka ne ? Ya buga mata tsawa" wallahi idan kika sake furta wani abu anan zaki ga yadda zanyi dake ",oho tun agabana ma ka fara nuna halin da zaka mata idan ta koma ke tashi ki shige uwar dakana kiyi kwanciyarki abunki ,jikin ummita yayi sanyi da jin abinda hajiya umma tace ta juya tana tafiya tana shafa bayan baby tana waiwayinsa kamar tace bazata shiga daki ba ,"haba hajiya wai me yasa kike biye mata ne ? ke kuma wallahi idan kika shiga sai na fito dake daga dakin ta karfin tsiya ki ajiye musu da mu wuce , "kayi tafiyarka kawai babu inda zata a dan rikice ya kalli Hajiya umma yace " babu abinda zan mata "da kyar Hajiya umma ta yarda suka fito ..
Ya shiga part din mama bata shiga ba ta nufi haraban gidan ,lallabawa tayi ta shige gidan baya gabanta na faduwa dan bata son wani sabon tashin hankali , kusan minti goma suna zaune babu wanda ya kalli fuskar wani sannan ya fito ya bude motar ya shiga suka bar gidan ..
Koda suka isa gida jikin ummita yayi mugun sanyi ta bude mota ta fita duk a tsorace take dashi sai data yi datasanin biyewa zuciyarta ,shima fitowa yayi ya biyo bayanta suna shiga part din ya zauna parlou'n ya daura ƙafarsa akan daya yana harararta , simi simi tashiga d'akinta ta cire mayafinta ta ninke ta soma share d'akinta ta shimfida haddaden zanin gado mai kyau da alfarma ta fito gyara parlou'n lokacin tuni ya fita , bata huta ba sai data gyara ko'ina ta fesa tuttarare kala dabam dabam ko'ina ya canza ya dauki kamshi ,ta shiga wanka ta fito tana goge jikinta tana addu'ar Allah yasa kar yayi mata maseefa doguwar riga ta saka ta shiga kitchen ta dafa jollof din wake da shinkafa , bayan ta gama ta shirya dining table sake shiga bayi tayi watsa ruwa tayi alwala ta fito tayi sallah magariba duk a tsoroce take dan gabanta sai faduwa yake ,a hankali ta zare hijab din jikinta ta haye gado ta kwanta ta lumshe idanunta tana jin wani irin yanayi mai cike tsantsar sha'awar mijinta bata jima da kwanciya ba wani bacci mai dadi ya ɗauke cike da tunaninsa ..
A kwance ya shigo ya sameta tana sharar bacci hankalin kwance cike da tsantsar mamaki yake kallonta kafin ya duba agogo dake daure da tsintsiyar hannunsa karfe tara saura ya gani yaja tsaki "wato ma har ta samu damar yin bacci ? Ya tako ya isa bakin gadon ya tsaya yana kare kyakkyawar fuskarta kallo, take yaji duk bacin ran data haifar masa ya kau ,a hankali ya raba ya kwanta a gabanta ya shiga hura mata iskar bakinsa a saman idonta motsa ido idanunta ta fara yi har ta budesu fess akan kyakkyawar fuskarsa dake daf da nata tana hamma alamun bacci mikewa tayi a firgice tana haɗe hannuwanta duka ",dan girman Allah kayi hakuri karka min komai wallahi bazan sake ba ta karasa maganar tana hawaye alamun nadama, ya tsura mata ido kawai , kuka take har da majina tana rokonsa cikin zuciyarta tana addu'ar da kiran sunayen Allah "kayiwa alfarma Manzon Allah kayi hakuri karka hukuntani gabadaya ta bashi dariya ya kai hannuwansa wuyanta zai shaketa ta rungumeshi ajikinta ta rukunkumeshi , gashin kanta mai laushi da kamshi ya rufe masa fuska "karka ka kasheni dan kaima mutuwa zakayi idan bana raye ....
Jikinsa yayi sanyi ya zagayeta da hannuwansa ya matseta da karfi sai data saki ƙara cikin sanyayyiyar muryarta tace"am sorry ya zareta ajikinsa yana haɗe fuska "kinci daraja Manzon Allah da mahaifiyata wallahi da kin gane baki da wayo wai a gabana kika haye bayan wani kato kinsa yadda naji ? tayi saurin girgiza masa kai "kayi hakuri ta faɗa tana wasa da hannunta shiru yayi kafin daga baya ya mike zai fita ta sauko da sauri ta rungumeshi ta baya ta kife hannunta akan nipples d'insa ,cak ya tsaya yana fidda numfashi , tasan muddin bata sauko dashi ba tana ruwa dan gaba a zarce dashi "kayi hakuri mana bazan sake ba nasan nayi kuskure idan na sake kayi fushi fiyye da haka ya juyo yana fuskantartata "dan kinsan bana iya dogon fushi dake ko ? yayi maganar yana jan karan hancinta ta narke ajikinsa tana shafa kirjinsa gabadaya wani sanyi yaji yana ratsa sansar jikinsa ya rungumeta tsam, bai an kara ba yaji tana yawo da hannunta a jikinsa ya ɗan sausauta rungumar da yayi mata ta tallo'bo fuskarsa tana kallon kwayar idanunshi "i really miss you ta had'e bakinsu nan wasan ya canza salo suka zube kan gado tun daga rana basu sake samu matsala ba ....
Bayan wata uku
abubuwa dayawa sun faru ciki har da warkewar zulaihat , da cigaba da bin bokayensu , yayinda jikin mahaifiyarsu ke cigaba da rurewa ta hanyar sababbin cuccutuka dabam dabam hauwan jini ,sugar Wanda shine dalilin da yasa a'ake yanke mata kafa ,a halin yanzu ma ciwon gaba yake suna zaune a parlou'n mahaifiyarsu zulaihat tace "yayyarmu har yanzu batun auren ya umar shiru? " an ce miki ni din ta wasa ce ai muddin ina raye bashi ba ƙara aure sai dai idan na mutu suka kwashe da mahaukaciyar dariya "ke ya labarin wannan tsinanniyar yarinyar kuwa ...? Hajiya rahma ta dubi suhaima aiki na tafiya yadda ya kamata ko ? "Kai bari yayyarmu mutumin nan ya iya aiki ,abu kamar maita wallahi muddin tayi ciki sai na gani sai dai idan bamu haɗu daita ba, shegiya kamar tasan halin da'ake ciki gudun haduwarmu take suka sake fashewa da dariya "ai haka zata kare baki haifa ba itama bazata haifa ba daga karshe ki korata da makirci matso kiji sabon makirci da zaki mata wanda nake da tabbacin wannan dan iskan mijin naki mai bakin kishin tsiya yana gani sai yayi gunduwa gunduwa daita sannan ya korata gidansu suhaima ta matso ta kasa kunne tana murna dariya ta fashe dashi lokacin da hajiya rahma tagama zayyano mata "kai yayyarmu kin kawo shawara wallahi haka za'a yi nan suka ci-gaba da tautaunawa akan tuggun da zasu haɗawa ummita ..
bayan sati daya da yamma ummita na zaune a parloun kan doguwar kujera tana kallo wanda azahiri ba kallon take ba tunani take mai zurfi gabad'aya zuciyarta ta amince mata da saka hannun suhaima gurin zubewar cikinta ba wai mafarki ne kawai ba akwai lauje cikin nadi duk randa tayi mafarkin suhaima sai cikinta ya fita kuma bata mafarkinta sai idan tana da ciki ,tayi shiru tunani yaki barin zuciyarta tana cikin wannan tunanin mah'ruf ya shigo ya wuceta a haukace bataga shigowarsa ba sai sautin muryarsa taji yana kiran sunanta "subai'a ta zabura ta mike jikinta na rawa tana furta "kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun saboda faduwar da gabanta yayi ta shiga d'akinta nan ta iskesa tsaye jijiyoyin kanshi da jikinsa duk sun mimike idanunshi sunyi jazir tamkar garwashin wuta yana zare ido.
cike da tashin hankali ya damki wuyanta "manufakar Allah muguwa me yiwa kanta bakinciki yau asirinki ya tono ta firgita tana ƙoƙarin cire hannunsa a wuyanta jikinta na wani irin rawa sai daya ga idanunta sun yo waje sannan ya sausauta rikon da yayi mata ya ingizata baya tayi taga zata fadi , Allah ya taimaketa ta tsaya bisa kafafunta tana fidda numfashi "lafiya me nayi maka ?
Tayi magana da kyar tana shafa wuyanta "ka dinga samun natsu..bata karasa ba saboda wani gigitaccen marin da taji ya sauka akan kuncinta kafin tayi wani yunkuri ya sake d'auketa da wani mai rai da lafiya a kyawawan fuskarta ,take ta gigice ta nufi hanyar bayi a madadin ta nufi kofar fita daga dakin .
yayi saurin janyota ta makake a jikinshi tana kuka "dan Allah karka sake marina kunnena zafi yake min ka faɗa min abinda nayi maka "kiyiwa mutane shiru munafuka shasha ya rike kafad'arta da karfi jikinsa na rawa "dan girman Allah kayi hakuri idan wani laifi nayi maka wallahi bazan sake ba ya turata baya ta faɗa saman katifa ya daura kafarsa daya gefen katifa yana zaro mata ido kana ya lalubo kwalin postonu 1 2 har 3 akan fuskarta "wannan maganin na mene ne ? a gigice ta mike ta ɗauki magani tana dubawa kana ta shiga girgiza masa kai dan bata fahimci komai ba "kin bani mamaki kin cuceni amman bani kika cuta ba kanki kika cuta kowa na tausaya miki ashe ke kinsan abinda kike kallonmu kawai kike yi muna hasarar hawayenmu ,wai yau kece kika shan maganin zubar da ciki saboda dakikanci wallahi dakikiyar kwalkwaluwarki bata faɗa miki gaskiya ba "da kinsa tsawon shekaru da mama da Abba sukayi suna neman haihuwa wallahi ko cikin shege kikayi zaki barshi bare dan halal.
take ta soma ganin dakin na jujjuyawa daita idanunta suka dinga ganin biyu biyu jikinta na rawa ta sauko ta zube gabanshi "ka yarda dani yaya wallahi ban taba shan wani abu dan na zubar da ciki ba ,ban taba ganin wannan maganin ba sai yau na rantse maka da girman Allah ban san yadda zan zubar da ciki ba ..
Ya watsa mata harara cike da jin haushinta "yi min shiru me fuska biyu kawai kinsa na rasa cikin ya'yana na farko kin zubar min dasu duk yadda meenal tace karki zubar tayita baki hakuri sai da kika ga bayan rayuka biyu yanzu kuma kinata zubar min da ciki saboda bakinciki me nayi miki dana cancanci wannan hukuncin daga gareki ...?
"Inna Lillahi wa Inna ilaihi rajiun kawai take furtawa tare da sake daukar kwalin maganin tana dubawa "banga amfanin zamana dake gara na sawwake miki kije ki auri wanda zuciyarki ke so tayi saurin mikewa ta rungumeshi ajikinta "karka min haka yaya karka sakeni karka yanke hukunci cikin fushi Allah baya son haka ta rike fuskarshi da hannuwanta duka "ban taba kin hada zuri'a da kai ba ,kai din kamilin mutun ne mai daraja a idanuna ,me ye ribata Idan na zubar da gudan jinina da naka wallahi sharri ake son min bani da masaniyya da zubar da ciki ,yayi mata wani banza kallon cike da jin haushinta "ka yarda dani mijina kalli cikin kwayar idanuna subai'a tayi kama da wacce zata iya kashe kadangare ma bare dan mutun kuma jininka jinina "zan yarda tunda idanuna sun gane min kin hainceni kin zalunci rayukan da basuji ba basu gani ba ta sake kamkameshi ajikinta ganin zai zareta cikin sheshekan kuka tace "dan Allah ka ji tausayina ka tausayawa halin da mahaifiyata zata shiga idan ka sakeni "dan Allah kayi bincike kafin ka yanke hukunci saki akaina kada kazo daga baya kana dakasani ...
"Ya Allah ka fahimtar da mijina ya fahimceni wallahi bani da masaniyyar laifin da yake tuhumata kai "Allah duk wanda yake son had'ani da mijina Allah kayi gaugawan yi min maganinsa, Allah idan ina da sa hannu cikin zubewar cikin jikina Allah ...
Shiru tayi sakamakon fizgeta da yayi ajikinsa yana huci "kiyi min shiru makira maci amana ko mama taji abinda kika yi sai tsine miki tare da yin Allah wadai dake ya fice ya bar dakin zuciyarsa kamar zata tarwatse ..
Da sauri suhaima ta juya a guje ta koma part dinta tana hakin gudun datayi ya shigo yana mazurai "maganarki gaskiya suhaima wallahi naga kwalin maganin yarinyar nan ta dade tana cutata "ai kai ne ka yarda daita bayan wannan fa har maza take kawowa gidan nan duk randa kake dakina ita kuma tana tare da tsohon saurayinta bari na nuna ma ka gani .
ta kunna wayarta ta shiga vedio sai ga hoton hafiz almustapha ya bayyana yana zaune akan gadon ummita jikinsa babu kaya daga shi sai boxer Yana murmushi can sai ga ummita kwance da rigar bacci iya cinyarta yayi mutuwar tsaye jikinsa na rawa ,ta sake lalubo wani vedio still hafiz din ne yake sandar shiga part din Ummita wani irin ihu yayi tare da kwace wayar yayi wurgi daita akan tayis "kenan haukan banza nake cikin ma ba nawa bane yayi maganar itama yana damkar makoshinta "me yasa baki faɗa min ba "nima me gadi ya fadi min tana aikensa dan ta shigo dashi ,ka tambayi me gadi shi kuma yace tsoron faɗa maka yake ya wujijigata yayi jifa daita ya buga kanta da bango kamar itace Ummita ta dawo ta zube kasa take bakinta da hancinta ya fashe ta saki wani kara "sorry ya faɗa cikin tsananin tashin hankali "dole na rabu da yarinyar nan hakuri kawai mama zatayi , daman nasan batun yanzu zuciyarta hafiz take so ya sake fita. .
Yana fita ta mike bata damu da raunin da taji ba ta soma tikar rawa da shewa"yau yarinya dole kiyi kwana gida kwana jikin mah'ruf ya kare ta kira hajiya rahma yayarmu gobara fa ta kama da wuta a gidana "kice bom ya tashi "tashin ma babba ne yau dai na huta ,za'a koma gidan gyatuma "ke hirar waya bazata yi ba bari nazo "gara kam yau akwai kwaso shoki ta katse wayar tana kwanciya akan kujerar wayyo Allah dadi ..
part din ummita ya koma ya isketa tana risgar kuka "ki tashi muje dan idan na cigaba kallonki zan iya kasheki bata masa mutsu ba ta zira hajab dinta ta fito bakinta na ambaton sunan Allah kai tsaye gidan ya wuce yana parking ya fito ya shiga part din mama ita kuma ta wuce part din hajiya umma .
Mama na kwance akan kujera tana ganin shigowarsa tayi saurin mikewa saboda tsananin tashin hankalin da hango tare dashi da hanzarinta ta kamo hannunsa "lafiya baba ?
Bai iya amsa mata ba ya kife kanshi akan gwiwarta ya shiga kuka har da shesheka yana cewa "mama ummita ta cuceni ta hainceni taci amanar zuciyata "Baba me Ummita tayi maka kake fadan irin wadannan maganganu jikinsa na rawa ya d'ago da idonsa yana kallonta ,idanunsa da zafafan kwalla kansa kuwa wani irin sarawa yake tamkar ya rabe gida biyu, gabadaya ta sake rudewa ta kai hannunta tana goge masa hawayen dake zubowa a fuskarsa tana cewa "dan Allah ka faɗa min abinda ke faruwa hankalina yayi bala'in tashi.. ya sake watsawa mama jajjayen idanunshi muryarsa a kausashe yace "Ummita ............
TWO FRIENDS BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
SUBSCRIBE TO MY YOUTUBE CHANNEL *HAUSA BAKWAI*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 66
"Ummita na kama dumu dumu da laifin zubar da ciki ta hanyar shan kwayoyin , tare da aikata abu mafi muni da kaskanci arayuwar aurenmu gayyatar hafiz almustapha har cikin gidana da zumar keta haddin au ....
"Dakata ...
Hajiya Umma ta katse shi ta hanyar fadar haka tare da k'arasa shigowa parlou'n rike da hannun ummita dake wani irin kuka mai haɗe da shesheka "wannan maganarta banza ce kuma karya ce har abada subai'a ba zata taɓa aikata haka ba , makirci kawai ake son had'a mata tare da kawo wa rayuwar aurenta tsaiko .
"Yau kasan halinta da har dakikiyar kwakwaluwarka ta kasa ƙaryata wannan mummunar aika aika " ka sani na sani kowa ma ya san halin ummita ba zata taɓa aikata wannan mugun aikin ba ,tana budurwa ma bata aikata zina ba sai da igiyar aurenta "ko ba cikakkiyar buduwar ka sameta ba bai kamata ka amincewa zuciyarka ta aikata haka ba ,bare nasan karya ne kai ne ka fara saninta diya mace ta karasa maganar cikin fushi tana watsa masa kallon banza ..
Zaune kawai mama take akan kujera jikinta na wani irin kyarma , hawaye kuwa tuni sun gama wanke mata fuska ,wannan hawayen da mahruf ya gani yasa jikinsa ya kama rawa ya shiga girgiza mata kanshi yana sake riƙe yatsun hannunta gam , tsoro da matsanancin firgici yaga ya bayyana a fuskarta yayinda a zahiri yake iya hango yadda zuciyarta ke bugawa da karfi , zare hannunta tayi cikin nashi ta shiga share hawayenta, muryarta na rawa tace " hajiya ummah karki ce haka karki karyata shi dan baki san abinda kwayar idanunshi suka gane masa ba dan......
"Dakata maryam banason irin wannan maganar da bata dadin ji , banason ji komai daga bakinki , tayi maganar da karfi wanda hakan ya janyo hankullan mutane dake cikin gida , kafin kace me duk sun hallara tare da yin zuru zuru fuskarsu dauke da alamun tambaya ....
A matukar haukace hajiya umma tayi kan shi tace "tashi daga gaban mahaifiyarta tantirin mara kunya da bai san abun arziki ba ,ta shi nace dan iska tayi magana jikinta na rawa tare da chakumo wuyar rigarshi ta mikar dashi tsaye bisa kafafunsa ta ɗauke shi da mari har biyu a jere tana huci tana kokarin kai masa wani marin mama tayi saurin mikewa ta rike hannunta "dan girman Allah ki barshi haka wallahi nasan haka kawai baba bazai fad'i abinda ya faɗa a yanzu ba akan ummita , ya kamata ki natsu ayi binkici domin a gano inda gaskiyar take bai kamata ki dinga yanke hukunci akan ra'ayi ki ba ..
"Maryam nace miki banason irin wannan maganar mai barazana da rayuwarmu ki daina ma tunanin abinda ya faɗa gaskiya ya faɗa tana girgiza mata kai bazan taba yarda ba wannan sharri ne da makirci aka mata .
naunayen ajiyar zuciya mama ta sauke tare tsura mata ido "wani irin soyayya hajiya umma ke mata ?"Ko uwarsu daya ubansu daya iyakar abinda zata mata kenan "Ki daina asarar hawayenki a banza dan ko bindiga za'a daura min a wuya bazan taba amincewa ba ,shi wannan ɗan iska zaki yiwa gargadi ya ƙaryata abinda ya faɗa yanzu kafin yasa zuciyata ta buga ganin yadda ranta ya ɓaci yasa hajiya mama ta kamota ta zaunar daita akan kujera tana huci ..
Ransa a matukar 'bace yake kallon mutane da suke tsaye agurin , Abba injiniya hajiya saudat mama da ummah "ga ta nan tsaye a gabanku ku tambayeta idan karya nayi mata , ku tambayeta ban kamata da laifin da nake tuhumarta dashi ba , ku
tambayeta karya ne banga maganin zubar da ciki a dakin ba?
" gata nan bata gayyato hafiz almustapha gidana da sunan aikata zi .......
Tass tas tass Hajiya umma ta tashi daga zaune da take ta sake dauke shi da wani gigitaccen mari har uku a jere "Idan ka sake danganta min yarinya da wannan kalmar sai tsine maka albarka .....
yayi shiru tare da juyo inda ummita ke tsaye tana wani irin kuka mai taɓa zuciya , fuskarsa cike da hawaye yake kallonta idanunshi sun yi jazir tamkar garwashin wuta, takowa yayi a hankali har inda take tsaye "akan idanunki ake ƙaryata abinda na tabbata da gaskiya ne ...
Zuba masa fararen idanunta tayi waɗan da suka kode tsabar kuka tana kallonsa tana jin zallar bacin rai na ratsata hawaye na sake gangarowa bisa kuncinta, ji take duk duniya mahruf ya gama tozarta ya gama wulakantata tun daya danganta da laifin zubar da ciki sannan da laifin aikata zina da aurensa ..."ta yaya zata aikata hakan gareshi ?
"Me take nema arayuwata da har
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 69 Chapter of 76