yace " na fahimci komai amman ai abinda suhaima tayi ba laifi bane ? muryarta a cike da tashin hankali "nace maka laifi ne duk abinda zakuyi kuyi ina ruwana amman kar a sake min makirci a bangarena I can't take it..
"na furta mahimanciki gareni a gabanta na faɗa mata duk abinda zata soma miki ta gama dani kafin tai miki alhalin nasan hakan kuskure ne kuma abu mafi ciwo ga zuciyar duk wanda aka yiwa haka ,ta danne zuciyarta ta biyoni tare da yayarta ta bani hakuri har ke ,dan tayi kissing dina shine zaki d'aga hankalinki akai ?
"Nace dole Sai ka soni ? "Ko nace dole sai ka faɗa mata mahimacina a gurinka ? well ni duk ba damuwata bane wannan , karka sake cewa kana sona dan na ƙaryata wannan kalmar na godewa Allah da zuciyata bata kamu da soyayyarka ba ta karasa fada tana hura masa hanci haɗe da mikewa zata wuce ya mike jikinsa na rawa ya fixgota ya rungume ajikinsa tsam yana sauke numfashi a tsanake ya d'ago kanta yana girgiza mata kai sannan ya jingin bayanta da bango yana huci kamar wani zaki "Ke kadai ce a cikin zuciyar mah'ruf , da zan kasance tare dake muddin rai kin isheni karasa rayuwata, ki tsaya kiyi tunani da kyau ta ya zaki ƙaryata soyayyar da nake miki nasan kina da zurfin tunanina a koda yaushe ki tsaya kiyi tunani da kyau zuciyarki na makale da tarin qaunata zaki iya yin komai akaina amman baki isa ki nisanta gangar jikinki dani ba understand .
"kwayar idanunki da hawayen dake cikin idanunki da zuciyarki nasan duk nawa ne idanunki suna shiga cikin wani yanayi a duk sanda suka sauka akaina ,murmushinki shima nawa ne ya busa mata hucin numfashinsa yana shafa fuskarta zuwa lip's dinta da wannan gashin naki ya kai hannunsa ya shafa sumar kanta shima wannan nawa ne hatta kamshin jikinki nawa ne komai naki nawa ne muddin rai kalli cikin kwayar idanuna kice karya ne bakya sona ...?"Faɗa min qauna ta yaya zaki kasa fahimtata dan wannan karamar matsalar ?
'bayan ba yau ne karo na farko da suhaima ta taɓa kissing dina a matsayinta na matata ba , kema kinsan dole hakan yana faru a tsakaninmu "yana faruwa amman ba akan idanuna ba kuma kazantar da mutun bai gani ba tsaftace ta karasa maganar tana rushewa da wani sabon kuka ...
Ya sausauta rungumar da yayi mata "kinga idan zaki yi fushinki kiyi mai ma'ana karki daura min laifi bisa wani ra'ayinki , dukkaninku matana ne meye laifi dan tayi kissing dina a gabanki ? ya sake matsowa ya matseta kamar zai raba jikinta gida biyu ya daura bakinsa saman nata yana hura mata iskar bakinsa yana dubanta , idanunta cike da kwalla ta kawar da fuskarta gefe taki kallonsa sannan taki yin magana ya sake matsota yana zagaye hannuwansa da kugunta "kin yi shiru kiyi magana mana ko kina son na kasance mara adalci ne agurin Allah ya karasa maganar a fusace yana sake matseta a faffad'an qirjinshi "kiyi magana me yasa zaki min haka har da ƙaryata soyayyar da nake miki ...
Hannunta ta kai ta tokare qirjinshi dashi "ya mah'ruf dan girman Allah ka barni bana bukatar komai daga gareka , dan Allah ka barni bana son damuwa da tashin tsura mata kyawawan idanunshi yayi yana Kallonta cikin zallar bacin rai "me nayi wanda ba daidai ba ki faɗa min ina son sani ? ban taba expecting haka daga gareki ba qauna sai dai hakan yasa na fahimci makaryaciya zuciyarki dake nuna tana sona alhalin ba haka bane , na ƙaryata kulawarki gareni ya karasa maganar qirjinsa na dokawa da karfi idanunshi na kanta ya juya a fusace zai bar dakin har ya daura hannunsa kan handle din kofar ya tsaya batare da juyo ba "bakya son tashin hankali bakyason damuwa ki bar issue din ya wuce shine zaman lafiyarki dani ya bude kofa ya karasa fita kai tsaye gidan ya bari zuwa massalaci dan lokacin sallar magariba tayi ..yana fita ta durkushe a kasa ta tasa fuskarta a tsakankanin cinyoyinta tana wani irin kuka "bazan yarda da cin fuska ba "duk lokacin da kake tare daita bana shiga rayuwarku saboda bana son damuwar da zata damu zuciyata ,bazan ɗauki wannan salon ba kuma wallahi sai na fadawa ummah ta fadi haka a ranta tana cigaba da kukanta ...
Wata irin mahaukaciyar dariya hajiya rahma ta kwashe dashi tana juyi a tsakiyar parlou'n suhaima kamar wata mahaukaciya "kinga yadda ake biyowa yan iska irin su mah'ruf ko ? "a kullum bazan gaji da fada miki kalmar ki dinga daga musu kafa da kawar da idanunki akansu ba ,wallahi da makirci kadai zamu iya raba tsakaninsu ,kar na sake jin kinyi tari akansu ,suhaima ta daga mata kai "ki kwantar da hankalinki gobe zanzo da mus'ab yayi mana abinda boka ya bukata karki manta ki tabbatar da kim samu spam d'insa ko boxer d'insa ,"suhaima tace " duk wannan mai sauki ne aiki yayi "yama yi ya gama Bashir musali ne akanki kalli yadda ya dawo ni har tausayi yake ba shima wannan dan iskan mijin naki bayan ana tsaye akanshi da sai yadda kika yi dashi tana magana fadar haka ta fito suhaima na biye daita a baya suna magana kasa kasa ...
Da misalin karfe tara na dare ya shigo bangaren ummita bai isketa a parlou'n ba daman zuciyarsa ta faɗa masa bazata zauna zaman jiransa ba ya kulle ko'ina sannan ya nufi d'akinta ya murd'a handle ji kofar a buɗe numfashi da ajiyar zuciya ya sauke a tare sannan ya shiga dakin duhu dan haka ya soma laluben makunin wuta ya kunna haske ya haskaka dakin kwance ya ganta akan gado ta juyawa kofa baya.
karasowa yayi cikin dakin sosai ya kulle kofar ya soma ƙoƙarin cire agogon hannunsa ya ajiye a gaban mirrow dinta ya ciro wayoyinsa ya ajiye ya shiga bayi yayi wanka ya fito yana goge jikinsa ganin suna fuskantar juna yasa ta juya dayan bangaren, ya sanye vest da boxer ya gama shirin bacci ya fashe ilahirin jikinsa da turare mai sanyi kanshi ya hau kan gadon ya canza hasken daki zuwa dum light ya kwanta a bayanta yana janyota jikinsa , tayi saurin matsawa cikin zafin nama ya birkitota gabadaya ta zube jikinsa hancinta ya sauka a daidai inda yafi jin kamshin turarensa ta lumshe idanunta qirjinta na matsanancin dokawa ,ya zagaye hannunwansa duka a kugunta ya soma wasa da sansar jikinta kememe taki yarda dashi ta dinga mutsu mutsun sauka a jikinsa ya zare hannuwansa ya d'agota ya zaunar daita shima ya zauna ya kunna wutan dakin yana tsareta da manya idanunshi masu bugar mata da zuciya shiru yayi yana kallonta "lallai yayi saken da ummita ta rainashi dayawa kenan bataji abinda ya faɗa mata d'azu zai fita ba ? "Me ye haka ya faɗa yana tsareta da ido cikin bacin rai mara misaltuwa "me nayi ta bashi amsa tana hura masa hanci tare da kafeshi da nata idon "me nace miki d'azu ? Kinsa idan tsiya kike ji nafiki iya wa ko ? "Kayi mana ina ruwana.
ya langwa'bar da kai yana dubanta haɗe da cizan lip's d'insa na kasan "kinsan halina sai dai ki bawa wani labarina bana daukar irin waɗan abubuwan kema yanzu ina binki a hankali dan nasan bake kadai bace , "kayi duk abinda zakayi I don't care dan halinka ya zame min man shafawata tana gama fadar haka ta sauko daga kan gadon ta nufi kofar fita ,saukowa yayi a zuciye ya cafkota ya juyo daita ya sauke mata yatsun biyar "kina hauka ne zaki fita ki barni ko wasa nake dake ? ta dafe inda ya mareta a gigice "ka mareni ?
"an mareki ko zaki rama ne ,ke ba mari zan iya miki abinda yafi shi matukar bazaki kwantar da hankalinki ba "me kike son nayi miki ki fahimceni ? kuka ta rushe masa dashi "kasan Allah tun daka mareni ka mari aurenka ta wuceshi a fusace ya murd'a key ya fito parlou'n zuciyarsa na kuna yana kallon hannunsa daya mareta dashi..
ta karasa gurin akwatin kayanta ta dauko daidai wanda tasan zata iya dauka ta k'araso gaban wordrob dinta ta bude ta dinga daukar kayanta tana zubawa ciki sai data cika akwatin ta rufe ta ɗauki zumbulelen hijab d'inta ta zira a saman rigarta ta soma jan akwati tana buɗe kofa suka ci karo dashi zai dawo dakin a gigice yake kallonta "oh my god subaia "wai meye haka ne ? me kike shirin yi taji kome ?
"kasan Allah bazan zauna ba yau a gidan ubana zan kwana sai kayi abinda yafi mari ta bi gefensa zata wuce ya fixge akwatin yayi jefa dashi ya rungumeta ajikinsa "you are mine subaia babu inda zaki "a ina kika koyi wannan dabiar yin yaji ? tunda kike da mama kin taba ganin tayi yaji ?"duk hargitsen da akayi a gidan mu wuya da dadi mama bata taba yin yaji ba me yasa zakiyi qauna ? ka rabu dani bazan zauna ba yau ka mareni gobe dukana zakayi "I have every right on you ban yarda ki taka ko nan da can ba " haka ne sai dai kasani komai yana canzawa , ya shiga girgiza fuskarta ki natsu ki fahimceni wallahi zuciyata bazata iya daukar wannan tashin hankalin ba ...
Ta zare jikinta ta faɗa saman gadonta tana kuka wayarsa ya dauko ya kira number mama Kira daya ta ɗauka da sallama "Assalamu alaikum "wa'alaikum Salam mamana barka da dare "barkanmu dana lafiya dai naji muryarka haka " kina bangarenki ne ko na abba "ina bangarena ta faɗa muryarta na rawa "okay gamu nan zuwa "Allah kawoka lafiya amman dai lafiya dai ko ?"lafiyar nan da sauki mama sai dai munzo ta katse kiran ya ya dauki jallabiya ya saka ya kamo ummita ya sauko daita ya rike tsintsiyar hannunta ya kulle ko'ina ya zare key ,ya nufi inda motarsa yake ya shiga ya yi wa matar key "ki shigo muje nan take tsoro ya kamata "ina ta faɗa a tsoroce "ban sani ba ki shigo muje jikinta na rawa ta shiga minti goma sha biyar kacal ya kaisu family house dinsu ..
A parlou'n suka iske mama zaune tana jiransu , tana ganinsu zuciyarta ta soma bugawa , guri ya samu ya zauna itama ummita ta zauna gabanta na fad'uwa dan tasan halin mama muddin taji abinda ya faru ita zata bawa rashin gaskiya "mama ga subai'a nan na kawo miki ki tayani bata hakuri nasan muddin kika bata hakuri da kanki zata hakura ? "Subai'a zan bawa hakuri akan wani laifin ? "me ka mata da har ka iya bata hakuri taki hakura ? " ita wacece ita mama tayi maganar jikinta na rawa tana kallon ummita dake zaune kamar wacce tayiwa sarki karya, ya furzar da iska mai zafi "wai akan.... ummita tayi saurin take masa kafa jikinta na rawa ya waigo ya tsura mata ido kanta ta shiga girgiza masa , mama ta cigaba da Kallonsu ranta a matukar bace, a fusace tace "ke har kin kai matsayin da mijinki zai baki hakuri kiki hakura sannan har ki hanashi fadar abinda ya hadaku ? "kai kuma kamar wani shasha shine ka wani tasota gaba yarinyar da zaka gaugarawa mari ta shiga hankalinta "no mama nifa ba faɗa na kawota kiyi mata ba hakuri zaki bata ni ne da laifi ai"mama tayi shiru tana dubansa cike da mamaki "lallai duniya mai juyi juyi mah'ruf ne ya dawo haka ? tayiwa kanta tambayar sannan ta girgiza kai "shikenna zan dai mata magana ba dai hakuri ba bani minti biyar kacal ya mike "dan Allah mama hakuri zaki bata ban da fada "inna lillahi wannan shirmen kake mata shiyasa ta rainaka "ya girgiza kanshi yana bar parlou'n mama bazai ki fahimci tasirin subai'a a arayuwata ba ..
Bayan fitar mahruf mama ta soma magana cikin fushi "ke yanzu irin wannan rayuwar kika zaba wa kanki mijinki yayi miki laifi har ya baki hakuri ki kasa hakura saboda gaki yar mai ? "ke kinsan halinsa wallahi ya fiki jin duk abinda kike ji dashi ya dai daga miki kafa ne saboda cikin jikinki bancin haka da kin gane baki da wayo sakariyar kawai ,daga yau sai yau karki sake irin wannan kuskuren , da zarar yayi miki laifi kika nuna fushinki ya baki hakuri shikenna sai ki hakura komai ya wuce idan kika saba masa da taurin kai, duk sanda yayi miki laifi bazai wahalar da kanshi gurin baki hakuri ba, zai barki da halinki haka kika ga suhaima nayi masa ? matar da ko shine da laifi ita ke durkusawa ta bashi hakuri "duk na makirci ne mama "koma dai na menene tayi kar na sake jin wani abu ya hadaku kina masa taurin kai shi namiji lalla'bashi ake tamkar jinjiri ki koyi hakuri da duk abinda zai miki ki saki ranki komai ya wuce Allah yayi muku albarka ta faɗa a daidai lokacin da mahruf ya dawo parlou'n yana sosa keyarsa "ɗauki matarka ku wuce dare yayi "na gode mamana babu kunya ya kamo hannun ummita suka wuce ..
A mota ya dinga janta da hira har suka kawo gida ya rungume tsam ajikinsa yana kissing din wuyanta zuwa qirjinta "Allah na gode maka da ka sanya mama cikin rayuwata Ina son mama fiyye da kowa "fiyye da kowa har ni ya daga mata kai alamun eh "a cikin soyayyarta na tsammaki ,ya kai hannusa mararta yana shafa "wayyo baby ko a wani hali yake ? Yayi maganar yana cigaba shafa marta a hankali ya soma tafiya daita ya kwantar daita akan gado ya zare hijab din jikinta ya tsura mata ido yana Kallonta "kina da rigima qauna Allah ya taimakeni kar yayana su dauko rigimarki gara su dauko komai na mama "tunda itace ta daukar min wahalar ciki ba? tayi magana a shagwa'be tana turo masa karamin bakinta ya matso da fuskarsa yana busa mata numfashinsa ya daura bakinsa saman nata ya tsotsa "sai na cije bakin rashin kunya ta mike zaune shima ya mike ta janyota jikinsa "Ina son komai naki "ba dai komai yanzu kagama cewa baka son yayanka su dauko rigimata bayan ni babu wata rigima da nake yayi murmushin gefe baki yana kissing din kunneta ....
"Menene abinda kafi so da tsana tare dani ? Ya sake yin murmushi yana Kallonta da kyawawan idanunshi "Abinda nafi tsana a tare dake taurin kanki , abinda nafi so sauƙin kanki dan bakya shiga lamuran mutane muddin basu suka shiga naki ba , tayi murmushi " ni da kai kadai muka fahimci halin da zukatanu suke ciki zan so sace zuciyarka gabad'aya mallakin subai'a ce " idan dai ba kasheni zakiyi ba ai....
tayi saurin kai hannunta bakinsa tana girgiza masa kai idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye "kasan yadda naji kuwa ?
ya riko hannunta yana murzawa yayi mata kyawawan masauki a cinyarsa "faɗa min abinda kikaji "karka sake min batun mutuwa yayi murmushi "mu fa muslimai ne mutuwa kuma dole kowane muslim da yayi imani dole zai kawo wa rayuwarsa mutuwa....
Wasu tsiraran hawayen suka gangaro mata a hankali tace "plz yaya ya kai hannunsa yana shafa sumar kanta "shikenna na amince duk duniya babu wanda ke sona kamarki ya faɗa idanuwansa na kanta , murmushi tayi dake kara mata kyau ya kai bakinsa cikin kunneta yana hura mata iska "faɗa min abinda kika so atare dani da abinda na taɓa miki wanda ya tsaya miki arai har kika kasa mantawa ya matsota sosai yana goge mata hawaye "uhmmmmmmm bana son kuka ina sauraronki numfashi ta sauke da kyar sannan ta soma magana a natse "zaka tuna ranar da mama ta aikoni d'akinka har ka tsareni a bayan kofar parlou'nka kace duk namijin daya aureni ya cuci kanshi ya aurar wa kansa matsala da tashin hankali har ma .......
yayi saurin rufe mata baki yana zaro ido haɗe da Kallonta cike da mamaki yadda bata manta komai daya faru ba a wancan ranar , ta cire hannunsa daga bakinta ta daura bakinta akan lip's d'insa tana tsotsa wani irin abu yaji yana yawo a gabad'aya ilahirin jikinsa wanda ya haddasawa qirjinsa bugawa ta tsaida idanunta cikin nashi "ban taba jin bakinciki irin na wannan lokacin ba kuma shine abinda yafi komai taba zuciyata da tsaya min a rai ...
"Na yarda kuma na amince da hukuncin Allah shine daidai ga bawansa duk abinda kaga Allah yayi akanka shine daidai a lokacin idan wani yace min zamu kasance ma'aurata zan ƙaryata sai gashi yau mun wayi gari tare cikin tsananin kulawa da juna ,nasan a lokacin kayi furucin ne ba daga kasan zuciyarka ba ,you just say it ,ajiyar zuciya ya ɗan sauke yana zuba mata idanu batare daya cire idanunshi cikin nata ba ya kwanta flat akan katifa ya kwanto daita jikinsa,lafewa tayi ajikinsa saboda abinda take ji ,lip's dinsa na kasa ya ciza da karfi yana jin haushin abinda yayi mata a baya wanda shima tsintar kanshi yake da aikatawa ba dan ransa na so ba .
a hankali ya soma yawo da hannunsa a jikinta ya dinga shafawa yana mammatsa mata jiki , kissing d'inta yake sosai tun daga wuyanta har zuwa boobs d'inta ya zare yar rigar bacci dake jikinta ,baki yasa yana tsotsan kan nipples d'inta a hankali ya cigaba da romancing d'inta cikin mawuyacin hali ta kai bakinta kunnenshi "ban gama magana ba kake neman canza hira "abar wannan hirar wannan yafi shi mahimmanci ya cigaba da saukowa bai tsaya ko'ina ba sai gonarsa she's wet dan haka kai tsaye bata lokaci ba ya ɗauki hanyarsa kusan raba dare suka yi suna morar juna .....
Washegari suhaima da sassafe ta tashi tayi duk abinda zata yi tana ganin mah'ruf ya fita , ta kira number hajiya rahma ta ɗauka "yaakayi suhaima "lafiya yayarmu daman nace na faɗa miki ya fita "kina jina ? "Ina jinki yayarmu "zuwanmu yau bazai yiwu ba, yanzu dady ya bugo min hajiyarmu babu lafiya yanzu haka ina kan hanya gida "mun shiga uku me kuma ya sameta? " ina ganin ciwonta ne idan na karasa zan kiraki ,ta katse kiran ,ta cigaba da tuki ,tana shiga gidansu hankalinta ya tashi saboda canzawar da kamanin mahaifiyarsu yayi a kwana ɗaya tal daman duk ta kare ta rame gashin kanta duk sun fara kakkabewa ta isa inda take kwance tana ta tambayar mahaifinsu" gata nan wai babban yatsan kafarta ke mata ciwo daga susawa ya kumbura babu abinda ba'a sa mata ba sai kara kunburi gurin yake duka last week ne abuya faru ,jiya bamu runtsa ba saboda ihunta "sannu hajiyarmu yauwa rahma ta faɗa da kyar numfashinta na fita basu bata lokaci ba suka nufi asibiti ita ..
Bayan sati jikin mahaifiyar suhaima yaki dadi dan har surutai ta soma ga babban dan yatsan kafarta ya soma fitar da wani ruwa mai wari dole likitoci suka ce za'a yanke , suna kuka suna komai aka yanke babban dan yatsun mahaifiyarsu ,mutane arzikinsu sunata zuwa dubata sai dai basa bari an ganta saboda surutan da take dan da zarar kace mata ya jiki zata fara zubo zance kamar wata zarrariya mutanen gidansu mah'ruf sunje dubata suma basu damar ganinta ba ..
Karfe tara na dare ranar ummita ta shigo d'akinsa a daidai lokacin daya fito daga bayi ,ya matso kusa daita zai rungumeta, tayi saurin ja da baya ai kuwa ya yarfa mata ruwan jikinsa haɗe da cewa zaki gane baki da wayo ne ba dai guduna kike ba ?
Cikin shagwa'ba tace " daman nazo na maka sallama ne ka shirya kayi baccinka kai kadai dan a yau a dakina zan kwanna , yayi murmushi "kamar da gaske idan kin koma d'akinki naki zaki iya bacci ?
"zan iya mana menene aciki dan na kwanta ni kadai ? "Nothing ya faɗa tare da tsayawa gaban mirrow ya fara shirya kanshi ta tsura masa ido kawai tana kallonsa , kallonta yayi bayan ya saka rigar bacci me budadden gaba har ana iya hango gashin dake kwance a qirjinshi a hankali yace "ya kika tsaya kina kallona baki wuce ba ko da magana ne ?
Ta rausayar da kwayar idanunta cikin nashi tana juyawa "to bari na wuce , yayi saurin riko hannunta ya juyo daita ta fadawa qirjinshi ya soma yawo da hannunsa a sansar jikinta yana tafiya daita har ya isa gaban wordrob dinsa ya zare rigar jikinta" bana son wadan nan kaya sun yiwa matata nauyi , tayi saurin rufe idanunta zuciyarta na harbawa , koda yaga tayi haka sai ya girgiza kanshi ,yana zira mata riga daya dauko mai shegen kyau wanda ya bayyana sansar jiki ,iya gwiwa rigar ta tsaya mata , tasbihi ya shiga yi a zuciyarsa saboda ganin irin kyawun da tayi yajata zuwa bakin gado ya kwantar daita yayi addu'ar ya rufe kofar part haɗe da kashe kwayakon lantarki na ko'ina sannan ya dawo ya kwanata a gefenta ya musu addu'a ya rungumeta ajikinshi daga shi har ita sai da suka sauke ajiyar zuciya ta lafe a qirjinshi tana shaƙar kamshinsa son shi na sake huda zuciyarta "qauna ya kira sunanta muryarsa a raunane ,tayi shiru taki amsawa illa zuciyarta data shiga dokawa da sauri "zuciyata ta kasa hakuri, ina son jin wata kalma mai mahimmanci daga bakinki sai careles kike dani kina batsawar .
"wace kalma kake son ki ? ta tambayeshi tana sake shigewa jikinsa take ta tsokano masa sha'awarsa jijiyarsa tayi wata irin haniniya ,
Ya kai bakinsa cikin kunneta "love .....ya faɗa yana sake rungumeta ajikinshi "i want hear from you "wannan ai kauyanci ne ban da abunka , zuwa yanzu kasan matsayinka dan haka ka daina damun kanka, yayi shiru yana sauke numfashi "wato duk abinda yayi sai ta tunatar dashi , ya tuna lokacin da rayhan yake furta mata kalmar yana sonta , shine da kanshi yace kauyanci ne furtawa mace kalmar so , ka nuna mata a aikace kawai shine wayewar , kallonta yayi yaga har ta soma bacci ya kai hannusa daidai kasan mararta yana shafawa a hankali daga nan shima bacci yayi gaba dashi...
Bayan sunyi sallar asuba ya soma lalubarta duk yadda taki haka ta hakura ta barshi yayi shagalinsa .
******
Shad'aya daidai hajiya rahma ta shigo gidan bata tsaya a ko'ina ba sai bakin part din suhaima ta fito tana bawa mus'ab umarni shima ya fito yana karewa gidan kallo har suka shiga parloun gidan "ka zauna ina zuwa ta shige ciki dakin suhaima ,kasa zama yayi saboda idanunsa daya hasko masa hoton mah'ruf makale a bango yayi shiru yana tunanin in daya sanshi," tabbas yasan fuskar amman ya manta inda yasanshi ganin ya kasa tunowa ya samu guri ya zauna yana jiran yaga fitowar matar da zai yiwa aiki ...
TWO FRIENDS BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*AUNTY RAHMATUN CAPTAIN*
SUBSCRIBE TO MY YOUTUBE CHANNEL
*HAUSA BAKWAI*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 63
"yayarmu zuciyata na cike da matsanamcin tsoro da fargaba kina ganin yaron nan bashi da matsala ? " ba zai kawowa rayuwarmu tashin hankali da barazana ba ?
"Suhaima ya kamata ki natsu ki karfafa zuciyarki daga yau bazaku sake had'uwa dashi ba, an tabbatar min da bashi da wata matsala ta wannan fanni ,muddin bashi yayi ra'ayi mace dan kanshi ba , idan kin daina kishin mijinki ,sannan zaki hakura matarsa ta cigaba da ɗaukar cikinsa tana haihuwa kina zaune bai da matsala sai ki hakura yanzu naje na sallemeshi ya kama gabansa tana gama fadar haka ta juya zata bar d'akin.
cikin matsanancin tashin hankalin jin abinda hajiya rahma ta faɗa ta k'araso gareta tayi huging dinta gabanta na fad'uwa, sai data sanyawa jikinta jarumta sannan tace "shikenna yayarmu kiyi hakuri karki yi fushi dani duk abinda kika shirya haka zan bi "danku nake wannan tashi fadin a kullum hajiyarmu burinta ku mallaki mazajenku ke da zulaihat kamar yadda na mallaki Umar da taimakonta , murmushi suhaima tayi tana cewa "thank you my lovely sister Allah ya barki da ya Umar .
Hajiya rahma ta dade a dakin tana shirya mata yadda zata biyowa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 65 Chapter of 76