Sai da ya Danganta da Goggo Halima yana mata magiya kan Shifa Da gaske sona yake Goggo Halima batayi kasa a Gwiwa ba ta gayamai Gaskiyan Cewa Ina da Mijin da Zan Aura Tunkafin na Fito Duniya kuma yana nan yana Jirana Da wannan mganar Goggo Ta Sahalemin Hisham Bayan Shi ma na samu Haren Haren Wasu Samarin Da Dama Nida Zafeera wannan Dalilin yasa muka Dawo kawai ba Shiri Saboda Sanin Halin Zain da Kishi,gashi ma yana Fushi da ita bai nemeta ko ta Wayar Goggo Halima ba Tunda suka zo Har suka koma.
Bayan mun koma Zafeera ta Rariyan Baki Taje tana Ba Su Umma da Nene labarin Abunda ya Faru a Gada karaf ya Fada kunnan Zain Ranar kuwa Yayi ta Bala"in ya kuma Tafi Gidan Alhaji Tsoho ya zauna mai kan Shifa Sai an Daura mai Aure da Matarsa,Dakyar Alhaji Tsoho ya Lallashe da Cewa ya bari Yaga Duka Iyayen nashi Suyi mgana Abunda suka yanke Shikenan Da Haka ya Hakura ya bar mganar,Bayan kwana Biyu Alhaji Tsoho ya Tara Duka Ya"yansa Dama suna Taruwa Duk bayan Wata Biyu Domin Tattauna Abunda ya Shafesu ya sako Mganar Zain da Bukatarsa Tun kafin ma Kowa yace komai Baban Kaduna yace bazai yuyuba Duka Duka nawa Zain din yake Shekarunsa fa 27 ne Karatunsa ma bai gama ba meya Tara mai ya ajiye..? Nan fa ya Fara Fadan Yace zai samu Zain din Maza ya bar wannan mganar Karatu zasu koma Dukkansu Shida Haddir din su kara Daukan Cos kan Abunda kowannensu ya karanta Jin haka yasa kowa yayi Na"am da mganarsa Shi da kanshi ya samu Zain din yamai Fata Fata kana ya Shiga Taitayinsa ya kuma ce in yasa Tsiya bazai Auri Halimar ba sai ta Gama Digree jin haka yasa ya bar mganar sanin Halin Baba kaduna kaifi Daya ne,Zareena da Haddir sai Dariya suke ganin yadda Zain din yazama Abun Tsausayi Sai Laifin ya Shafi Harda ita Zainar nasa Wajen Sati ya Dauka baya mata mgana ko Tayi mai mgana sai ya Dauke kanta wai Takan yace ta samu Abba tace itama Tana son ayi musu Aure yanzu Tace bazata iya ba Shikenan Fushin ya Shafeta Dakyar ta Lallasoshi ya Hakura aka wuce Wajen.
Bayan Haka sun Taba zuwa Biki Kano Bikin Babbar Diyar Inna Rukayyah mai Suna Asma"u Abunda yasa ma Taje harda Zain din yaje Daurin Auran Shiyasa ya barta Taje ammh sai da yayi Nadama da Wani Abokin ango ya makalema Halima awajen Lonching Ranar kuwa kowa yaga Kaunar da Zain yake ma Halima ko kayanta bata Daukaba ya kwasheta Suka koma Bauchi sai dai Su Zafeera bayan an gama Biki suka Dawo mata Dashi,Ko Tafiyarsa ma Mumbai Sai da aka Sha Daka da kuma Tarin alkwarin da Nene ta Daukan mai na Kula da Duk wani Motsin Zainar nasa kada wani yazo Daga baya ya Batamai Shirinsa,Da kuma Tabbacin da Alhaji Tsoho ya bashi kan ko Bayan Ransa yasan Ya"yansa zasu so su Cika Wasiyyan Maryama kan Auransa da Halima Dalilin Dayasa Hankalinsa ya kwanta kenan ya Tafi ya bar Zainar Nashi Zuwa Lokacin da zai Dawo Ta kamallah Secondry Sch Dinta sai mganar Auran.
Da Farko bayan Sun Dawo Nageria Baya mgana da Dina,Duka Hanyar da yasan zata Sameshi ya Dakileshi Saboda yana son Cikama Haddir Alkawarin Daya Daukan mai Sai dai me,Yayi kokarin ya Jure ya kasa Ya Rasa Dalilin Dayasa yake Kasa Rabuwa Da Dina Tun Yana Bauchi ya Fara Nemanta Suna Mgana Sama sama sai konawar sa Mumbai ta Sauya komai Domin Dina Tana kai mai Ziyara har chan su Sheke ayarsu son Rai ba Wanda ya sani Dama Haddir ne ke gayamai gaskiya kuma Basa Tare sai kawai Zain ya koma Ruwa Tsumdum Duk da wani Lokacin yana so ya Daina ko Domin Zainarsa ammh Kuma sai ya Kasa Gashi dai ya Daina Hulda da kowacce mace sai Dina Dinar ma yana iya bakin kokarinsa Wajen yakiceta ammh Ina tana kara Shiga Jikinsa ne Wanda ya Rasa gano Dalilin Haka.
Suna Shekara Daya Da Tafiya akayi Bikin Zareena,Wanda ta Auri Wani Bakatsine mai Suna Jawaad,Ma"aikacin kamfanin Shinfida Titina kuma Babba ne awajen,Allah Sarki Daga Haddir Har Zain ba wanda ya Hallaci Bikinta Har acikin Zuciyar Zareena Taji wani iri ammh ya zatayi Tunda ba Hali da sun zi bikinta ta sani Da Farko Katsina suka Fara zama bayan Wata Uku kuma Approving letter Dinsa ta fito ya samu aiki a Babban Birnin U.S America Da Wani Babban Kamfanin Shinfida Kwalti na kasar Da Farko Shi kadai ya Fara Tafiya bayan Wata Daya kuma ya Dawo ya kwashi Zareena suka Tafi Zama na Dindin Tunda Sun mai Takardan zama dan kasar Sun bashi Gida da Mota da komai na Bukatar Rayuwa,Dukkansu sukayi Sallama da Ahalinsu suka koma Chan da Zama,bayan komawarsu da wani Lokaci Zareena Ta kira waya tace ta samu aiki a gidan Radion Dake Shiyarsu Iyayenta suka Tayata Murna ainun.
Su Zain suna gabda Dawowa mukayi Candy Nida Zafeera da Umar Faruq,Lokacin Ya Saddiq Babba yana Abu Zaria inda ya Fara Masters Dinsa,Muna kamallah makarantar iyayanmu suka Fara Shirya Shiryan Aure na da Zain,kamar yadda sukayi mai alkawarin Tuni Sun kai Chan Gada da Sakon Lokacin yayi da zasu cika Wasiyan Maryama Goggo Halima Tafi kowa Murna da Haka Zain yana Mumbai aka saka Lokacin Bikin mu nan da Shekara Daya bayan ya Dawo Ya Fara aiki ya samu Muhallinsa Duk da wannan ba Matsala bane ammh Iyayansa sunfi son ya zauna da Kafafunsa Dagani Har Zain an Raasa wanda yafi kowa Murna wannan Auran Sai dai ni nawa na Boyeshi Saboda kunya Ammh Shi kam Daga chan kamar yayi Tsuntsuwa ya Dawo har yana ma Nenen korafin an saka Lokacin Bikin da Tsawo Tace karya Damu kamar Gobe ne.
Anyi Haka da Wata Biyar Haddir ya Fara Dawowa Tsskaninsa da Zain kwana Goma ne Shima ya Diro Abunda zai ba kowa mamaki da Hadin kayan Lefensa ya Dawo akwatunasa 12 yayi ma zainarsa da yan Kudaden da ake Ta Biyansu Tun Suna London To Dayake baya komai dasu Tunda komai Iyayansu sun Daukemusu wannan Nauyin sai ya Rika Tarasu Domin irin Haka kowa ya Jinjina ma Kokarinsa Sosai Nene sai Murna Take Yaronta yakara Hankali Umma kuwa Sai Shirin Aurar dani kawai Take Abunda kowa na Tututiya da Zai Aurar da Nashi.
Suna Dawowa ba Bata Lokaci suka Fara aiki na Dindin da asibitin Dayake zaman Jiransu Duk da sun samu Gayyace gayyace Daga asibitoci Dadama ammh Suka Ture wannan Bukatar sukace sun Yi karatun Likitanci Saboda su Cikama Kakansu Burinsa sun yarda sun kuma amince zasu aiki Tukuri a asibitin Dayake mallakin wanda yayi Sanadiyar kawo iyayansu Duniya ne koda bazasu samu komai ba Zasu yi Hakuri da Dan Albashin da asibiti zata Dinga Basu.
Dalilim Fara aikinsu yasa Suka Gayyato Likitoci abokan Karatunsu Domin suzo ayi Tafiyan Tare dasu Dr Imran abokin Karatun Haddir ne,Dr Peter kuma acikin asibitin suka zo suka Sameshi,Lokacin da Suka Fara aiki sai Haddir ya kama Wani Flat House nan kusa da asibitin Saboda Jeka ka Dawo Alhaji Tsoho yayi ta Ciwon bakin Haddir ya Dawo Wajensa ko Wajen Abba Usman ya zauna ammh yayi Biris da mganar.
Sun Fara aiki da Wata Biyar Bikin Zain da Zainarsa ya Taso aka Fara Shirye Shirye Sai ana Gabda Bikin ne Abba Usman ya Damkama Zain makullin Katon Gidan Daya gina mai a Federal Lowcost,Wanda zasu zauna Shida Halima Farinciki Wajensa Ba"a mgana su kuma su Umma suka Dauki masu Tsara Gidaje suka kai suka ga yanayin Gidan suka Saki kudi zuwa kawai sukayi Suka Tsara komai Duka Iyayen nasu suka Hadu suna Gudanar da duka Shiryen Shiryen yan Gada ma Abba Usman yace karsu Damu Daga Halimar Har zain Duka ya"yans kuma zai yi Abunda kowani Uba Nagari kema ya"yansa Dole suka Zuba ido suna ganin inda Tsananin karamci da Dattako ke aiki.
Anyi Auran Zain da Halima Tana Da Shekara 20 cif aduniya Shi kuma yana Cikin na 29wannan Bikin Ya Tara Dimbin Tarihi,Hatta Zareena Dake U.s Tazo Sadiq babba ma yazo Daga makaranta kaf Duka iyalan Baban kaduna da na Dadyn Abuja Inna Hannatu da nata Iyalan Haka ma Inna Rukayyah itama da nata Ahalin yan Gada ma Sunyi bajinta Mota Biyu Mota Daya na mata Mota Daya na Maza yan Daurin Auran da aka Daurashi a Gidan Alhaji Tsoho wanda Abba Usman ya zama Wakilin Amarya Yayinda Baban kaduna ya zama Wakilin zain kuma ya Biyamai Sadaki.
Ansha Shagalin Biki Haddir ne Babban Abokin ango yayinda da Zafeera ta kasance ta Hannun Damar Amarya sunyi Lonching Da Dinner wanda Hotunan Dinner ne suka dinga Yawo Har Zakiya Nuhu kawar Dina taci karo Dashi Wacce ta samu aiki a Hukunar Layin Mtn Anan Bauchi Take da Office,nan take Zaune Tunda Har ta Siya gida Da Mota,Dina bata da Labari Domin Duk Rashin Rike Sirrin Zain bai iya gayamata Zencen Auransa ba sai da Zakiya ta gayamata ta kuma Tura mata Hotunan Dinner Da taga yan"uwa sun Dora akafafan yada Zumunta Lokacin da Dina Ta Gama karatunta ta Dawo Kano Har ta Fara aiki a Mallam Aminu kano a matsayin Cikakkiyar Likitan mata.
Lokacin Dataci karo da Hotunan Zain da Halima Hauka ne kadai Dina Batayi ba Sai da Zakiya ta Baro Bauchi tazo Tana lallashinta da bata baki,Washegari Suka koma Wajen malaminsu,Nan yake kara Tabbatar musu da cewa Daman ya gaya musu Tsakaninsu akwai Aure da Zuru"a Sosai,Itama Tsakaninta Dashi akwai Aure sai dai bai san yaushe ne ba bai kuna san Wani Turniku da Duhun daya gani acikin Lamarin ba,Hakuri ya Bata da cewa Taje ta Jira Lokaci ammh ya gayamata In dai Tana son mallakan Zain Har Abada Toh sai dai Ta daina Sukan Matarsa Wacce Duk Duniya ba wacce yake so bayan Iyayensa sai ita.
Da Haka Suka Tattaro suka Dawo Bauchin Ta koma Gidan Zakiya Tana Jinyar zuciyata Ita take ta aikin Lallashinta da bata baki karta Damu Zain bazai barta ba Tunda malamin ya Riga ya Tabbatar mata,da wannan Mganar yasa Hankalin Dina ya Kwantar Har ta Tattara ta koma Kano Saboda aikinta Lokacin Tuni Babanta ya zama kwamishan kudi na Jihar kanon Dabo.
Fadar irin gyaran da Nasha Wajen Umma ba"a mgana Tamin Abunda Ko aya"yanta bata Musu bata bama Tuna wai Danta zan Aura kawai ita Ni yarta ce zan Auri wani ne chan Dabam Wato Babban yaron Nene Itama Nene Tayi Rawar gani Sosai da Bajinta an kai Amarya Gidanta na Aure Tare da Nasihan duka Iyayan Rikonta da kuma Ahalin iyayenta na Gada Goggo Halima Tayi mata Nasihan Zaman lafiya da Hakuri da kuma yadda zata gyara zamantakewarta.
Anyi Biki lafiya yan"uwa Da Abokan arzuka sun Koma Gidajensu da Fatan zaman Lafiya ga Ma"aurata Fadar irin Daran Farkon Daya Gudana Tsakanin Zain da Halima Bata baki ne,Domim Shekara ashirin yayi Yana Dankon Jiran Ganin Wannan Ranar bai Tsausayamata Sai da ya Famshe wadannan kwanakin Yaji Halima Dabam acikin Sauran mata kamar yadda Take Dabam acikin Zuciyarsa wata irin Soyayyah da Zaman Amana da yarda Dakai suke ma juna,Zain ya Riga yagama Sangarta Halima da Salon Soyayyarsu Ita kuma Tagama yardan ma kanta Bata da wani Wanda zata yarda Dashi bayan ZAIN shine Duka Sirrinta Ganinta da Jinta Ta gama Bashi Duka yardanta ta ganin Shine abokin Sirrinta Shima Haka tana ganin Shine kadai yasan Rauninta Tana ganin Bayan Iyayenta ba wanda zai kai adadin kaunar da ZAIN yake mata Shiyasa itama Ta Sadaukarmai Da Duka kanta da komai nata Domin Biyansa bashin Dimbin kaunar Daya ke mata Bata Taba kawo ma kanta Watarana Zain zai iya Cin Amanarta ba Shiyasa Zuciyarta da Ruhinta suka gama Bashi Dukkan Wata yarda.
Bayan Auransu da Wata Biyu Duk Yadda Zain yaso kada ya Neme Dina sai ya Nemeta,Saboda su kasance Tare yasa yayi mata Tayin aiki a asibitinsu Ba gardama ko Neman Shawara kawai ta amince kuma Da ta gayama Mahaifinta ga Ra'ayinta bai Tsaya Son Jin Dalilinta ba ya amince mata,Saboda yana Sonta kuma ya Riga ya bata Damar yin Abunda Taga Dama Haddir sai dai kawai Rana Tsaka yaga Dina acikin Asibitinsu Da Sunan Sabuwar ma"akaciya mamaki ya kamashi bai iya Shuru ba sai da yayi ma Zain mgana kan Meyasa ya gayyato Dina..? Ya barta Chan kano Inda ta Fara aikinta mana..? Ko ya Dawo Da Ita kusa Dashi Ne saboda su Cigaba daga inda suka Tsaya..? Nan sukayi ta ba Dadi Zain din ya Musa ma Haddir Zarginsa akaro na Farko yayi mai karya Ba Saboda komai ba Zain yana jin kunyar Haddir ya kara kamashi da laifin da yayi mai alkawarin ya Daina Uwa uba kuma ga Halima Wacce bata inda ta Rageshi,Auransu Duka Duka Wata Biyu ammh kuma Har ya Fara cin Amanarta..? Koshi yana son ya yakice Dina acikin Rayuwarsa Tunda ba Sonta yake ba ya Dade da gayamata bazai iya Auranta ba,Su Rabu ammh Abu kamar Zanen kaddara Tunda ta Shigo Rayuwarsa ya kasa yakiceta.
Tun Zuwan Dina asibitin Dr.Imran ya kyalla ido ya ganta Ransa ya Biya Dama mayen mata ne,Tuni yake taya Nurses Din nan Wacce ta bata kai Shikenan Yayi Kokarin Tusa kansa ammh Dina Taki bashi Fuska Har Fitomata yayi da Maitarsa ammh ta Watsa mai kasa acikin Ido,Daya gane Zain take so Shi kuma sai yana Zugata da Cewa Zain baya sonta kowa ya Shaida Mace Daya yake so Itace Firstlove in yana Fadamata Haka ji Take kamar ta Mangareshi Ya gaji da Maitarsa bata kulashi ammh Duk da Haka bai Hakura ba Tsakaninta kuwa da Haddir gaisuwan Sama sama ne kawai na Wadanda suke aiki awaaje Daya ammh Ta Riga ta sani Tun Farko Bata Burge Haddir
Wani Lokacin Zain yana kaucema Haduwarsu da Dina ammh Ita ke Hillatansa Zuwa Gidanta Chan su lalace,Ko a Office Dinsa baiso suka Fara wannan Mu"amalan ba Ammh Dina Tayi ma Zain Farin sanin Da tasan Hanyoyin Datake kunnosa,Shiyasa baya iya kaucema Tarkonta Sunsha yin Fada kaca kaca kan Firstlove dinsa Daga baya kuma su koma Su Dinke Likitoci Dadama su Na Dora Musu Zargi ammh Rashin Shaida yasa kowa ya kauda kansa Tunda Zain din kwata kwata bai da Sakewa Saboda nan ba Wata kasa bace Gida ne kuma Duk Abunda zai yi Mara kyau zai iya Taba Mutumtakansa Data Gidansu Shiyasa yake Kokarin Kiyayewa
Bayan Auransu ne Halima Tayi Jamb Taci ita Da Zafeera suka Rubutu kuma Dukkansu sunci,Dukkansu ABU samaru Zaria suka samu ammh Zain yace Zainarsa bazata ba,Dole Zafera kadai Tatafi itama Din An Sauya mata BUK kano Tatafi Tana zaune gidan Inna Rukayyah Tare suka Fara karatu da yar Autatanta mai Suna Shema"u, Shi kuma Faruq Ya Tafi Kasar Ketare Wato Chicago inda ya Fara karatun Digree dinsa achan Ayayinda Shi kuma Zain ya Sauyama Halima makaranta Zuwa ATBU BAUCHI ta Fara karantar B.SC Mathematics Tana Shekaran Farko ne,Lokacin ya Siya Motar Hawa Ita kuma Abba Usman ya Siyar mata NATA Saboda Zirga zirgan Tafiya makaranta Tunda Zain yana zuwa Wajen AIKI bai zama ba lalle Tafiyansu tazo Daya ba,Shidai Zain ya bata Gudummuwar Siya mata Tsaleliyar Waya sai ta bama Zainab Tsohowar Tata wacce Abba Ya siya musu ita da Zafeera tun suna gida
Tun Zuwanta makaranta Suka Hadu da Laila Adam,Course Dinsu Daya,Kuma Sai Halinsu yazo Daya Tunda itama Lailan akwai kokari anan garin Bauchin take da zama ita da iyayenta Duk ba masu Hali bane Suna Da Rufin asiri,Bayan Zafeera Laila ce kadai Halima ta yarda Ta sake kawa da ita Tunda Zafeera Tana makaranta sai dai in sunyi Waya,Duk wanda ya zauna da Halima Dole yasan Waye Firstlove agereta,Laila Taje har gidan Halima Tasan Zain Shima yasanta Tunda Yana zuwa Daukanta Wani Lokacin in bata je da Motarta ba,Har gidan su Umma Taje,Tasha kuma Raka Halima Gidan Alhaji Tsohi suje su gaishesu Yarinyar tana Da Hankali Shiyasa Har Zain ya yarda Halimar Tayi kawance da Ita.
Halima Bata Taba ganin Dina ba Sai sau Daya Da Zain zai kaita makaranta Ranar Motarta ba Lafiya tana Wajen gyara sun Fito sai ya samu Kiran gaggawa Daga asibitin sai ya Fara Biyawa da Ita asibitin Har Cikin Office Dinsa awannan Ranar ne wasu Suga Firstlove dib Dr.Zain,Aranar zaina taga Dina Ta ganta Ido Cikin Ido Tunda batasan da zuwanta ba Ta Shiga Office din Zain din ne Ta ganta ganin Ta Tsaya Tana kallonta ne yasa Shi Zain din ya Gabatar da Halima ga Dina Itama Dinar ya gabatar da ita akan cewa abokiyar aikinsu ce Dr.Dina gaddafi Sherrif.
Hannu Dina Tabama Halima sukayi musabaha kowanne na Kallon kowa da Wani Tunani Dabam Ita Halima aganin Farko Taji Zuciyarta ta Fara rawa Akan Dina Haka kurum taji Matar bata kwantamata ba Duk Kokarinta na tayi mata Dariya kasawa Tayi sai yake,Shima Zain din bai yarda Zainar Tasa ta gano wani Abu ba,Ya Tattarata suka bar asibitin a Hanya da zai kaita Makaranta sai da Halimar tace ita Kuwa Taji Zuciyarta bai kwanta mata da Wannan Dinar ba,Da ta Fadi Haka yaji mamaki ammh sai ya Shanye mamakinsa yace mata Dama Haka Allah ke Abunsa ba kowa bane zakaji ya kwantamaka ba Ammh Dina Bata da matsala Daganan bai kara mgana ba itama Bata kara mai Zencen Wata Dina ba ammh Abun ya Tsaya mata arai Har Haddir ta Tambaya yace mata Karta Damu Juz kawai abokiyar aiki ne Shi ina zai yarda aji mutuwar sarki abakinsa ba Domin Har ga Allah Tsausayin Halimar yake ji Yana Tsoron Faruwar wani abu indai Sirrin Boye ya Fito Fili.
*******
Fitowa Tayi Daga Library Ranta a matukar bace da kalaman Laila agogon Fatan Dake Hannunta na kamfanin Gucci takai Duba Taga har pass 10 kuma sai 11am zasu Shiga Lectures Din Dr.Tafida ne Baya son Wasa ammh da ba Haka da gidan Umma zata wuce kawai.
Departement Dinsu ta koma ta Samu Waje ta zauna Ta Fito da Wayarta Tana latsawa Zafeera take son Ta kira sun kwana Biyu Basu yi mgana ba,gabadaya Walwalarta Ta Ragu akowani Dakika kalaman Laila gareta Suna Dawowa mata kuma Suna sanya mata Faduwar gaba da Wani Rauni wanda Ta Rasa Daga Ina yake Fitowa.
Ta kira Zafeera 2missedcalls bata Daga ba sai ta kyaleta Tana Tunanin kila itama Tana Class ne Tana kokarim maida Wayarta Cikin karamar Jakarta Laila ta kariso Wajenta bayan Ta gaji da nemanta Kafin ma Ta samu Zama Halima tayi Saurin Dagowa Lokaci Daya Tana Dakatar da ita Hannu.
"Wai bana ce miki ki kyaleni ba Laila..? Don Allah ki barni Dazu najure kin Fadi maganganu Son Ranki Buh by now Zuciyata bazata iya Jure waba gwara ki Kyaleni kamar yadda nace Simple...! Tafada Lokaci Daya Tana Mikewa Cikin Bacin Rai da Sauri Laila Tasha Gabanta Tana Fadin"Naji zan kyaleki Halima..Ammh plz ya kamata Ko Sau Daya ne kima mganata kyakyawan Fahimta ba Nufi...!
"Ya isa Laila..Sai yanzu na gano Inda kika Dosa Wato Kina son mijina,Shiyasa kika Fito da wannan Hanyar da Rashin Jituwa zai Fara Shiga Tsakaninmu saboda ki samu Wata Dama ko..? Tafada tana Watsa mata wani kallo Waro Ido Laila Tayi kafin Tace"Wa...? Innalillahi Wlh banzata ba Halima Banzata zaki min Wannan kallon ba..Ammh komai ya Faru ba laifinki bane ni naja..Allah ya baki Hakuri Insha Allahu haka bazata kara Faruwa ba kuma ina so ki sani yau ko Mutuwa kikayi bazan iya Cin Amanarki ba Ballatana Kina Raye Halima..!
Ta karishe Fada Idanuwanta na kawo kwallah kafin ta Juya Ta Fara Tafiya Halima da kalaman Laila suka kashe ma Jiki ta Daga Kafa Tana Tafiya ga Lailan Tana Fadin"Haka zalika kamar yadda Ko Da bana Raye bazaki iya Cin Amanata Haka ma Firstlove Ko Gawata bazai iya Cin Amana ba Laila Ballatana Da Rai na da lafiyata Bazan Taba yarda Dake ba..Domin Firstlove ya Fara Min Kauna ta gaskiya Tun ina Cikin Mahaifiyata..!
Cak Laila Ta tsaya ammh bata Waigo ba sai Halima ce Tasha Gabanta Tana Fadin"Nima am Sorry In mgana ta bata miki Rai I did Mean to hurt u..! Tafada Tana Riko Hannuwanta Mirmishi Laila Ta saki kafin tace'Na Fahimceki Kawata..Samun Wannan kaunar ta Firstlove dinki gareki sai An Tona Irin Labaran da muka Sha karantawa ne English Novels Da Hausa Banta Tsammanin akwai Ira iransa a xahiri ba..! "
Halima Ta saki wani kayattacen Mirmishi Tana Fadin"Gashi kin gani Wajen ZAINAZAIN..! laila ta Jinjina kai Tana Fadin"Kwarai kuwa na Shaida wannan kaunar Daga Allah ce.."Dariya suka Saki Lokaci daya kafin su Fara Tafiya Tare Hannayensu na Cikin na juna suna mgana Sama sama Wanda duk wanda ya gansu zai Fahimci Suna da kyakyawan alaqa akwancensu.
Cafteria suka je suka Sha Lemo da Snacks kafin su Wuce Class sai 1pm suka Fito Daga lectures Daganan Halima tayi ma Laila Tayi Zuwa Gidan Umma bata yi musu ba Ta Bita ammh Bayan ta Kira mamarta Ta gayamata Suna zuwa Gidan Umma su Saudart suka Fara Ihun Murnan ga Anty Halima ga Anty Halima Tun kafin ma Tagama Daidaita parking Dayake suna Haraban Gidan ne sai ga Zainab ta Fito suka Rumgume juna cikin Ladabi Take gaida Laila wacce Darajan Halima yasa Duka yaran ke Kiranta Anty Laila.
Bude Bayan Mota tayi ta Dauko Cake din suka Dunguma Cikin Gida Da Umma suka Fara cin karo Halima Tatafi gareta ta Rumgumeta Tana Fadin Tayi Kewarta Itama Rumgumetan Tayi Tana Fadin Itama Tayi kewarta Nene na gefe Tana Fadin Ayi dai mugani Umma tace anyi kuma Sun gani Laila na gefe Tana Dariya Cike da Sha"awan wannan ahalin Kafin Halima ta saki Umma Taje ta Rumgume Nene tana gaisheta ta Shafa kanta tana saka mata albarka Laila ta gaishesu suka amsa Cikin Sakin Fuska Suna Tambayanta karatu Daganan zainab Ta Shiga nuna ma Halima da Laila Vidio da sukayi ma Su Umma da Safe Lokacin da Zain yake yanka Cake sai da suka gama gani Halima tace kowa yazo suyi nasu Shagali Yanka Cake din akayi kowa yaci Halima Ta Diba Dayawa tace Na Alhaji Tsoho ne da Hajiya Mama su Umma nata Dariya Sallah sukayi sukaci Abinci kana Laila Tayi musu Sallama Tatafi Gida Saboda Mamarta zata Fita tace ta Dawo Da wuri Tunda kannenta Duk kanana ne suna Makaranta Gidan ba kowa.
Sai da Halima Tayi La"asar kana Ta bar gidan Shima Firstlove ya Kirata yace ta koma Gida Hakanan Daganan Gidan Alhaji Tsoho ta Biya ta gaishesu Shi da Hajiya Mama da Tabawa ta kuma basu nasu Cake din Hajiya Mama naci Tana Fadin"Shidai Zanullahi dan gata ne..Kowacce Shekara sai munci wannan Abun mai Dan karen Dadi da Sunan wai Bazday dinsa..!
Gabadaya Halima da Alhaji Tsoho suka sakamata Dariya Halima na Fadin karta Damu zata Shiryama Alhaji Tsoho ammh sai ya Cika Shekara 100 aduniya kana Zata Shiryamai Suna Ta Firansu suna Dariya Bata Jima ba tayi musu sallama Tatafi Alhaji Tsoho na kara Jadaddamata ta kula ta Dinga Tuki a Hankali tace Insha Allahu akoda yaushe tana Alhafari da Alhaji Tsoho Domin Tana kallonsa kamar kakanta ne ya Kure mata Dukkan Rashin kakanni Shi da Hajiya Mama.
Daganan Motarta Ta Shiga Ta koma Gida ta Fara Tunanin me zata Dafa musu na Dinner ita da Firstlove gefe Daya kuma Lokaci bayan Lokaci kalaman Laila na Dawo mata Ganin ta saka Abun Aranta zai Dameta sai ta Watsar da wannan Tunanin ta kwabe kaya ta Shiga tayi wanka ta Saka Saukakkun kaya na Zaman Gida Riga da Wando ta Fada Kitchen.
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
0️⃣8️⃣
"Dina na Fita Daga Cikin asibitin bata Zarce ko"ina ba sai Dan madaidaicin Gidanta wanda mahaifinta ya Siya mata take zaune aciki Daura da asibitin yake ba Nisa Wanka Tayi ta Sauya kaya zuwa Wata Doguwar Rigan Abaya baka tayi Rolling din Vail Din gyalen Bisa kanta kana ta Dauki Wayarta Ta kira Zakiya tace mata Tana Office ne ko Tana gida..? Nan tace mata Tana Office,kawai sai ta yanke Kiran Wani Hill din Takalmi ta sakamai mai Tsawo Ta zari key dim motarta Wanda ke Hade Dana gidanta ta Fito ta Kulle kana Ta Fada Motarta ta Bata Wuta kai Tsaye Babban Ofishin Kamfanin Sadarwa Ta MTN ta Nufa Zuciyarta Cike da Tunanin Yadda zatayi Da Zain Domin bata Jin zata yi Sanyi kamar yadda yake Bukata agaresa.
Tana zuwa ba wani Neman izini Domin Duk wanda yasan Zakiya acikin ma"aikatan Dole yasan Dina Saboda kawaye ne na Sosai koda ba Bangaran
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 32