Cigaba da Hiransu,Har barci ya Dauketa Kana Zafeera ta Fita ta barta acikin Ranta kawai Tana Jin Tsausayin Zaina Ranar da Yaya Dakta yace zai kara Aure akwai Daru.
Shi kuwa Zain sai wajen 3pm na Rana suka Dawo Cikin Asibiti suna Shigowa Suka Hade da Haddir wanda yamai kallo Daya ya kauda kai Shima Zain din Kai ya Daga sama yana wani Cin mgani,har sun Gotashi ya Daga murya yana Fadin"In ka gama Shashancin naka ka Kira Matarka ta Kirani tana Tambayarka tace Tayi ta Kiran wayarka baka Daga ba..'
Daga haka ya wuce ya barsa nan jin Haka yasa gabansa ya Fadi Dina Dake gefensa ta kalleshi bata samu zarafin mgana ba ya wuceta da Sauri kamar zai Tashi Sama ya Shige Office dinsa ya Rufe kofa sai da yazauna kana ya Lalubo Wayarsa Missedcalls din Firstlove Wajen 14 Ido ya Zaro yana Rawan Jiki ya Bi bayan Kiran Nata sai da yayi kira wajen uku kafin yaji Zafeera ta Daga wayar nan take cemai Zaina tana barci,Zafeera ce Tace"Ina ka Shiga ne Yaya Dakta..? Ukti Da kuka ta kwanta Duk ta Damu..?
Kai ya Dafe yana Fadin"Oh my God..Kuna gidan Umma ne..? Tace"Eh Tun dazu muka Dawo.."Daga haka kawai ya katse Kiran Ya tashi Da Sauri ya Lalubi key din Motarsa ya Fice Office Din Dr Aisha ya Shiga yace mata ta Duba Tiyata petient dinsu in basu Farka ba nan da 1hr ta kirashi Ta amsa da To Yana kokarin Fita Dina na Sawo kai Bai tsaya ma Kallonta ba ya wuce da Sauri kamar zai Tashi Sama Da kallon mamaki Hade Dana Kishi Ta bishi Dashi Domin Tana da Tabbancin Wajen Tsinanniyar matarsa Zashi In yaji Sunants yana Rawan Jiki kamar wata Uwarsa da Katon Tsaki ta rakashi kafin tace acikin Ranta"Lokacin ya kusa Zuwa..!
Yana Fita Kai Tsaye Motarsa ya Shiga Sai GRA,koda ya Shigo Falon Da Umma yaci karo Sama sama ya gaisheta ta kalleshi Cikin mamakin ganin Hanzarinsa tace"Kai kuma lafiya.? Yana Tafiya zuwa Dakinsu Zafeera yace'Lafiya lau Umma Firstlove naciki ko..? Bata ma samu zarafin mgana ba ya tura kofa ya Shige Dakin,Umma ta Rakashi da wani kallo kamar baya Cikin Natsuwarsa Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin Ta gyara zamanta Daman Tashar Sunna Tv take kallo Kawai sai ta Cigaba da kallonta Nene kuma Tana Dakinta ta Dan kwanta Zainab kuma Bata nan Tana Kaduna Da Baban kaduna yazo Ta bishi Suka Tafi Tare su Saudart kuma suna Makaranta basu Dawo ba.
Yana Turo Kofar Zafeera Ta Dago Tana kallonsa wacce ke Zaune gefen gado Tana Latse Latse Bisa Laptop dinta ganinsa yasa Ta Mike Tana gaisheshi Yana amsawa Hankalinsa na kan Zainarsa ganin Tana Barcinta cikin Salama Da Hannu yayi ma Zafeera alama da ta Fita ta bashi waje Mirmishin gefen baki tayi kawai ta Fice Dauke da System dinta aranta Tana Fadin ko bakace ba Dama Fita zanyi..'
Tana Fita ta turomusu Kofar Shi kuma yana ganin Fitarta ya Duka ya Sabule Takalmin kafarsa ya hawo kan gadon ya Ciccibota ya Daurata kan Jikinsa ya Rumgumeta kam yana Sakin ajiyar Zuciya Gefe Daya kuma na Zuciyarsa Tayi wani Rauni Yana Tunanin Abunda yake yi baya Ma kansa da Zainarsa adalci,Ya rasa ya zai yi ya yakice Dina arayuwarsa Idanuwansa sun Sauya launi Kamar ya Fashe da kuka.
Cikin Barci Take jin kamar an Rumgumeta Sama sama ta Fara Bude idanuwanta ta Saukeshi a kansa Yana Rumgume da ita kamar zai Tsaga Jikinsa ya maidata Cikin Muryan Barci Tace"Firstlove...'
Jin Ta Kira Sunansa yasa ya Dagota Suna kallon Juna,Cikin Sanyin murya Zaina tace"Ina ka Shiga ka kyaleni ina ta Kiranka... ? Kara rumgumeta yayi yana Fadin"Bako ina Firstlove...ina asibiti ne Yau Mutane Biyu nayi Ma Fida Firstlove kema kinsan Haka kurum bazan kyaleki ba.."Ido ta Rausayar Tana Fadin"Na kira Ya Haddir yace min ka Fita Baka cikin asibiti..?
Fuska ya Hade yana Fadin"Ki daina ma Kiransa in kin kirani baki Jini ba..Ba Bangaran mu Daya ba Kowa da Barayinsa Kinji ko..? Bazai san na Fita ba ko Ina nan ba,kawai zai yanke Hukunaci ne batare Daya sani ba..Ni ina Cikin asibiti ba inda naje.."Kokarin mikewa take zaune Yayi Saurin Rikota ya Zaunar da ita kan Ciyarsa yana Shafa Fuskarta kafin yace"Kun Dawo lafiya..? Ya kuka baro su Goggo halima..?
Kai ta Lamgwabe saman Kirjinsa kafin tace"Duk suna lafiya..Kowa yace agaisheka."Kanta ya Shafa Lokaci Daya yana Zame mata Dan kwalin kanta Ya ci karo da Kitson shukun Da akayi mata achan Shafawa ya Farayi yana Fadin"Wow...Yayi kyau sosai Firstlove waya yi miki..?
Kanta ta Dago Tana Fadin'Matar Junaidun Goggo Halima taminshi Jiya.."Kiss ya sakarma kan yana Fadin"Yayi kyau Dole zan Biya wannann kitson.."Ya Fada yana Kure ta ido Kirjinsa ta Shafa Tana Fadin"Miye naga ka Kureni da ido..?
Kai Tsaye yace"Idanuwanki sun Tasa..kin yi kuka ko... ? Kara lafemai tayi Bisa Kirji Tana Fadin"ba kai bane..? Kuka nayi saboda Zuciyata tana ta Rayamin kana Tare da wata ne Shiyaasa ka Shareni.."Dam! Yaji mganar nata Cikin Rawan Jiki ya kara kamkameta yana Fadin"A"a Bana son wannan Tunanin Firstlove Taya ya Kike Tssmmanin zain dinki Wanda yafara Sonki Tun kina Cikin mahaifiyarki Taya kike Tsamanin zai kalli Wata mace Da sunan so..? A"a wannan ba Tunani bane karki kara Kinji Zainata.."
Ya Fada yana Shafa bayanta Zuwa Kugunta,ita kuma Tana Shafa Kirjinsa Cikin wata irin murya tace"bazan kara ba..Haka Ukti ma tace...Na Tsorata ne ganin ina ta Kiranka baka Daga ba.."Dago kanta yayi yana Fadin"Kin manta Mijinki Likita ne..? Akwai Ceton Rayuwanka Jama"a awuyansa Wani Lokacin Zaki rika Jin haka Firstlove plz kimin afuwa kinji ko..? Na saka Zainata kuka.."
Yafada yana Kokarin Hade bakinsu Waje Daya bata Mai gaddama ba ta Dago kanta suka Hade Lebensu Waje Daya Keyarta ya Riko ita kuma ta Riko Bayan Kansa tana Shafawa Cikin Wani Salo sun Dauki Dogon Lokaci suna Sumbatar juna kafin su saki bakin Juna kan Kirjinsa ta koma ta lafe tana Sakin ajiyar zuciya Lokaci Daya Tana Fadin"Firslove lalle nayi kewarka Har ina jin kamshin Bakinka ya Chanzamin..'"
Yana jinta Tana Fadin Haka saboda ya kauda mata wannan Tunanin yasa ya Fara mata Wasu Abubuwan da bazata iya Jurrewa ba kawai sai ta bar mganar ta biyemai suna Farantama juna Rai da kuma nuna ma Juna yadda sukayi kewar Juna Ammh Tabbas yasani kamshin Man bakin Da Dina Ke yawan amfani Dashi ne,Domin ya Tuna koda suke Mota sai da ta kwakumeshi Ta sha Bakinsa tana Bala"in son Ta Tsotsi Bakinsa Shiyasa Zainarsa taji Kamshin Bakinsa nashi ya Sauya.
Kan Kirjinta ya Yada kansa yana Sauke Numfashi,sama sama ita ma Numfashin take Saukewa Chan Cikin Shakakkiyar murya yake fadin"Firstlove muje gidanmu.Nan gidan yamin kadan na Nuna miki yadda nayi kewarki ba.."Yana Fada ya mikewa ya Fara Daura mata Dankwali ya Sauko Daga kan gadon ya mika mata Hannu ta kama ta Sauko,Gyalenta ya mika mata ta Yafa Shi kuma ya Dauki karamar akwatinta yana Fadin"Ina karamar Jakarki...?cikin Sanyin Murya tace"Yana Dakin Umma..'
Gaba ya wuce yana Fadin"Muje Ki Dauka mu wuce gida ai nayi Kokari Sati Daya nayi ina Maraicin Rashinki Fistlove.."Tare suke Fita Falo ita ta wuce Dakin Umma ta Dauko Jakarta ta Fito Koda ta Fito har ma yakai Haraban Gidan Umma da Kalleta Tana Fadin"Sai anjuma Dota.Allah huta gajiya.."
Ta amsa da Ameen,Zafeera kuma Harara ta watsa mata Tana Fadin"Naga wariyan launin Fata Cewa fa kikayi ni zan Rakaki gida ammh yanzu kinga Yaya Dakta kin juyamin baya.."Dariya Zaina Tayi Kafin Tayi mgana Umma ta Rigata da Fadin"Kinga yi Tafiyarki yana waje yana Jiranki kinsan Halin Yaron Nene Wutar Ciki..."Jin haka yasa ta Fice tana Fadin agaida Nene in ta tashi Zafeera ta Bita da kallon mamaki ganin ta saki kamar ba ita ba.
Koda suka koma Gida Zain bai iya Daga ma Zaina kafa ba Sai ya ta Tabbatar da ya samu Natsuwa kana suka Shiga wanka Bayan sun Fito ne ya Shirya ya koma asibiti saboda ya samu Kiran Dr Aisha Ita kuma ta Zage ta Shiga Kitchen Domin Farantamana Mijinta Abun alfaharinta.
******
Kwanci Tashi babu Wuya awajen Allah gashi Har Su zaina sun cinye Hutunsu Dayake Hutun bamai yawa bane sosai iyaka Sati Hudu ne Ma"ana One Month kenan,Zafeera ma Tana ta Shirin komawa Ana gobe zata koma Tazo Gidan Zaina ta mata Wuni Tazo kenan ba Dadewa sai ga Laila itama ta iso Daman Tana Jin Labarin Ukti Zafeera wajen Zaina ammh bata Taba ganinta ido da ido ba sai dai ahoto Itama Zafeera Tana Jin Labarin kawar Zaina ta makaranta Laila sai Ranar suka Hade nan fa sukayi ta shan Hira Suna Dariya Dukkansu Ukun Tare suka Shiga Kitchen sukayi Girki Sukaci,Zain bai dawo Da Wuri ba,sai wajen biyar na yammh Lokacin Laila ma na Shirin Tafiya ne,Yayi mamakin ganinsu bayan sun gaisa yana ta Musu Tsiyan ashe sune suka zo suka saka Firstlove dinsa yau kwata kwata ta manta Dashi,Laila na karewa Zafeera dai Sai Mirmishi Sanin Ko da suka Taso Kai da kai Tare da Zaina Yaya Dakta bai Cika sakar mata Fuska ba Shiyasa itama Take jan kankantar ta da matsayinta awajen Matarsa.
Ciki ya Shiga Zainar ta Bishi Ta Taimakamai yayi wanka ya Sauya kaya Ta zubo mai abinci yaci kana ya sake Fita zuwa gidan Alhaji Tsoho,Domin yace ya kwana Biyu bai lekasa ba Daganan zai biya ya gaida Matan Abba Nene da Umma Bayan Fitansa ne laila Tayi ta ma Zaina Tsiyar ko sun samu karuwa ne Taga tayi wani Kiba ne Ta kara Cika kamar ba Ita ba Zafeera kuma Tana gefe Tana kare ma Zainar kallo Itama Tana Shaida Kibar Dataga Tayi ammh Tasan koma miye In Ta fasu zasuji.
Kusan Tare da Laila da Zafeera suka Fita Zafeera da Motar Umma tazo sai ta Rage ma Laila Hanya Ta kaita Har gida kana ta Wuce Gida,Tana zuwa gida taci karo da Ya Haddir ya kawo Zainab Daga Kaduna yake ya je Gaida Maman Wani Abokinsa sai ya Biya shine Baban kaduna ya Hadosa da Zainab sama Sama suka gaisa da zafeera daman Ita bata cika sakarmai Fuska ba tace ya cika Girman kai yaya Dakta ya fishi Sakin Fuska shima kallon Wata mai Girma kai yake mata Shi kuma bata sanshi ba Haka yake yafi Zain Miskilanci da Shariya.
*****
Misalin karfe 8:30pm na Dare Zakiya ne zaune kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon Da suka yi Ma Falon Dina kwanya itama Dina Tana zaune kan kujeran Dake kallon Wacce Zakiyan ke kai Dukkansu kananan kofuna ne a Hannunsu cike da madaran Hollandian suna Sha Suna Taba Hira,Yau din zakiya ce takawo ma Dina Ziyara Shima din ba Dadewa zatayi ba wani Alhajinta take Jira zai zo Gidan Dina ya Dauketa.
Sai da ta Hadiye Abunda ta kurba kana ta Tsurama Dina ido Tana Nazarartanta Ganin haka yasa Dina tace"Yane..?irin wannan kallo sai kace kin ga wani Tsohom kwartonki.."Dariya Zakiya ta saka kafin tace"Tsohon Kwarto ai ya gama aiki Dina...Rabani bana Harka da Duk Abunda ya zama Tsoho nafison Harkan da Abunda yake sabo ko banza zan Mori Quality dinsa kafin ya Tsufa.."Dukkansu Dariyar suka saka Cikin Nishadi kafin su Tsaigata Zakiya ce ta ijiye Kofin Dake Hannunta kan Center Table Din Dake Tsakiyar Falon Tana Fadin.
"In lissafina ya cika Daidai mun Riga mun Dana Tarkonmu Tun 3weeks da suka gabata.."Tafada Tana kallon Dina Mikewa Dina Tayi Dauke da Kofin Hannunta Tana Fadin"Eh mana..Kin manta ke ma ai sabuwar alluran taki Satinta uku dana Rakaki akayi miki ko..? Zakiya tace"Hakane..Toh sai ki Dage ba Daga Kafa mu samu Zomon mu ya Shiga Tarko..In ya Shiga Duka Burikanki zasu zama gaskiya ayayinda Zaki mallaki Zain mallaka na Har Abada..'
Kai Tsaye Dina Tace"in kuma plan din mu ya Kuskure fa..? Wani munafukin Mirmishi Zakiya ta saki kafin tace"Kin Rasa Zain har Abada Dina..In nace Har Abada ina Nufin har Abada bazaki Taba mallakansa a matsayin Miji ba kuma kila nan da Lokaci kadan ma Tarayyar Dake tsakaninku ta Wargaje gabadaya kedashi sai dai Hange Daga Nesa.."Ta karishe Fada Tana kallon Dina Ido Cikin Ido.
"Bai isa ba..Bazai Taba yuyuba ya zama Dole na mallakesa ko yana so ko baya so.."ta fada Cikin zafin Rai dana zuciya Zakiya Ta mike tana Taku Daya Bayan Daya Zuwa ga Dina Lokaci Daya tana Dafa kadarta Tana Fadin"Shiyasa nace in baki son Hakan ta kasance sai kin dage sosai Kin kuma Danne wannan bakin Kishin acikin Ranki in ba Haka ba Duk sanda kikace zaki Rika bayyana Abunda ke Ranki Game da matarsa zaki lalatamana plan ne Domin zai gujeki kuma ni bana son Haka nafison ku kasance Tare har sai Hakanmu ya cimma Ruwa.."
Tafada Tana kallon Dina wacce ta sadda kansa Tana wani Tunani kafin ta Dago Tana Sakin ajiyar rai lokaci Daya Tana Fadin"zan yi kokarina..Ammh Wlh baki ji yadda na Tsani Diyar megadin nan ba in ya ambaci Firstlove ji nake kamar naje gidanta na Burma mata wuka in kuma ya ambaci Zainarsa din nan kamar na Kashe kaina nake ji.."Zakiya ta Kara Dora Hannunta saman kafadarta ta Hannun Hagu ta Girgiza da karfi Tana Fadin"Ki Daure kada ki lalatamana plan Dina na gayamiki.."
Dina tace"Insha Allahu muke da Nasara..."Zakiya tace"Ina saka Ran haka..."Ta fada tana wani Mele baki Kallonta Dina Tayi Tana Fadin"in plan din mu ya Tafi Daidai me kike ganin zai Biyo Baya..?
Sakin Kafadunta Zakiya tayi kafin Ta Sheke da wata Dariya irin na mugunta sai da tayi ya isheta kana ta Dakata Tana Fadin"Ke yanzu baki Hasoso mezai Faru gaba ba..? Ta fada Tana kallon Dina wacce ta sakar mata ido Tana kallonta lokaci Daya Tana girgixa mata kai alaman Bata sani ba Cikin Tafa Hannu Zakiya take Fadin"Ya kamata ki Hasaso wani Abu mana Dina Har kin manta Tare Dani DaKe muka biya kudi muka samu Labarin Tarihin Zain Tundaga Tushe..?ashe har kin manta..?
Da Sauri Dina Tace"Ban manta wannan ba meyasa kika ce haka awannan gabar..? Zakiya tace"Dalilai Da Dama mana..Bala"i ne zai Faru Lokacin da muka Fasa kwan...Za"ayi Kitimurmura fa,Ahali zasu Girgiza fa Kimarsu zata Raunana ba kadan ba,kinga wannan Matar nashi Dayake ji da ita kamar ransa..?hmm wannan Firstlove din da Zaina na zain ko.? Duka zasu kare Plan din mu zai saka Soyayyarasa ta Rikide ta koma Tsantasan Tsanarsa acikin Ranta Yan"uwansa da iyayensa zasu Daina yarda dashi kilama har Iyayensa Su kama Fushi Dashi Fushi mai Muni ma kuwa,..!"
Ta karishe Fada tana wani kallon Sama kamar tana ganin Abun na Faruwa agabanta ne.
Dina ta saki Mirmishi Tana Fadin"Naji Duk wannan ta ina nawa Burin zai cika..? Zakiya ta Dago kanta Tana kallon Dina Ido Cikin Ido kafin tace"Ta wannan Hanyar...Karki manta Sunan Kakansa Dr.Abubakar Bashir Usman Saulawa ya zaga garin Bauchi dama kewayanta Wajen Kimarsa da Dattakonsa da Son Talakawansa Na Biyu kuma Mutum ne mai Daraja wanda Al"umma ke ganin Darajansa Karki manta mai bamu labarin ya gayamana Duk Cikin Jikokinsa yafi son Zain da Haddir kuma yana kimantasu acikin Idanuwansa ya kike ganin in wannan Labarin ya Sameshi Da Shaida mai karfi..? Zai so wannan kimar nashi ta Zube..? Bazai Taba yarda ya Rasa Dattakonsa ba Dole mafita Daya ne Zasu bi koda Zain din yana so ko baya so Saboda Lokacin ba Mganarsa za"a Tsaya Saurara ba Domin bashi da wata Kima alokacin..'
Kai tsaye Dina Tace"Wata mafita ce..? Ta fada tana Kallon Zakiya da neman karin Bayani ta Bude baki zata yi mgana kenan Wayarta dake Cikin karamar Jakarta ta Dauki Kiran Neman agaji Hannu ta kada mata Tana Fadin"Kin cinye lokacinki Alhajina ya iso.."Tafada tana Karisawa kusa da Jakar nata ta Dauka ta Zageta ta Dauko Wayar nata Har Kiran ya katse Tana ganin mai Kiran Ta Dago Tana kallon Dina Wacce ta Sakar mata Ido Tana Jiran amsanta Dariya ta saka Tana Fadin"Sorry kawata Lokacinki ya kare...Ammh ki bani Bashi zan baki amsa in muka Hadu.."
Bata bari Dina ta samu Zarafin mgana ba ta kama Hanyar barin Falon Daidai Lokacin Da wayarta ta Sake daukan Neman agaji Ta Daga Ta kara akunne lokaci Daya ta waigo Tana kallon Dina Tana Fadin"Zan bar Motata awajenki Zan dawo na Dauka..."
Daga haka ta Bude kofa ta Fice Cikin yanga da Takun Yanmatan Zamani Wadanda suka san kan Duniya Dina Ta rakata da kallo mai kama da Takaichi kafin ta koma kan kujera ta zauna Tana Dafe kanta.
******
Washegari iyalan Dr.Saulawa suka Tashi da alhinin Rashin Lafiya Alhaji Tsoho Wanda Mura da Zazzabi ya Sarkeshi Cikin Dare Numfashinsa ma baya Fita sama sama kamar zai Sheka Dalilin haka yasa Haddir Da Hajiya Mama suka Rankaya Dashi Zuwa Asibitin Dayake mallakinsa Wato Saulawa specialist Hop,wajen Misalin uku na Dare,Dr.Imran Haddir ya Kira Tunda Shi ke kusa da asibitin Kafin su iso ya iso Cikin asibitin Tare dashi Da Dr.Peter suka bashi Taimakon gaggawa Har Numfashinsa ya Dawo ya Daidaita ashe majina ce ta Tushemai Kirji yasa baya iya Numfashi,Duk da Dare ne alokacin ammmh akwai Nurses masu Duty din Dare suna ta kai da kawo ganin Dr.Saulawa da kansa aka kawo ba lafiya.
Daki na Mussaman aka kaishi Wanda Dama Dakunan na Family ne in wata mtasala ta Faru,Sai wajen asuba kana Haddir ya samu natsuwa ganin Alhaji ya samu Barci Hajiya mama Tasha kuka Haddir nata Mata Tsiyan Shima kanshi ya Shiga Rudu nan ya barta ta Shiga Toilet ta Dauro alwala Domin ana ta Kiran Sallar asuba Shima Fita yayi zuwa masallacin Cikin asibitin Yayi alwala yayi Sallah sai da aka idar kana ya Tuna da Abba da Sauri ya Fito da waya ya Kirashi ya gayamai Abunda ke Faruwa Hankalinsa ya Tashi Dama lokacin Dawowarsa masalaci kenan Su Nene suna tsaye Sun Firfito Jin Salatinsa sai da Ya gama wayar kana yake gaya musu Suma Duk Sun Rude sanin sudai Basu Taba ganin Alhaji Tsoho yayi ciwon Daya kwantar Dashi Haka ba.
Kafin wayewar gari Labarin Ciwon Alhaji Tsoho yakai kunnan Duka ya"yansa Dalilin Dayasa Zafeera ta Fasa Tafiya kenan Zain ma yana Gida Nene ta Kirashi ta Shaidamai Hankali Tashe Shida Zainarsa suka Nufi asibitin,Hakama Abba Da su Umma da Nene da Zainab da Zafeera su Saudat suna makaranta Kafin karfe goman Safe Hatta Baban Kaduna da Dadyn Abuja sun iso Inna Rukayyah ce ta Kira tace tana Hanya Inna Hannatu kuma ta biyo Jirgi Itama Duka Hankalinsu ya Tashi Lokaci Daya Hatta su Zareena Dake Kasar U.S Haddir ya Kira Jawaad ya Fadamai sai Kira Zareena take tana Tambayan Jikin na Alhaji Tsoho.
Dina Bata sani ba sai da Ta Shigo Cikin Asibitin Taga yadda Asibitin ya Cika ga yalwar Motoci a parking Space,Ta faka Motarta kenan tana Shirin Fitowa Misalin 12pm na Rana sai ga Motar Haddir ta Shigo Cikin Asibitin Inda ya Dauko Inma Hannatu Daga Filin Jirgi ita da Autarta Maryama,Agaban idon Dina suka Firfito Daga Motan zuwa Cikin asibitin Gabanta ya Fadi Domin Taga Tsantsan kama da Zain din akan Fuskar matar sai ta Fara Tunanim ko mahaifiyarsa ne..?
Cikin asibitin ta Shiga sai kuwa suka ci karo da Dr Aisha ita ta Tambaya take Fadamata Mai asibitin aka kawo ba lafiya Kakan Zain da Haddir Dr Saulawa Ido Dina ta kwalalo Tana Fadin"Kai don Allah Tun yaushe..?
Dr Aisha tace"Tun Cikin Dare..Su Dr Imran sukayi Attempting Dinsa ammh yanzu da Sauki Tun safe Jikokinsa da ya"yansa suka Cika asbitin nan.."Dina tace"Allah sarki Allah bashi lafiya.."Dr Aisha tace Ameen harzata wuce Dr Aisha tace Mata"Ki shiga ki Dubashi mana Yana Family Side Dinsu.."Kai kawai Dina ta kada mata Jikinta asanyaye ta wuce Office dinta tana Jin wani Sanyin Jiki Taya zata Hadu da Ahalin Zain bayan kuma suna kam Shirya wani Abu..?
Haka ta isa office dinta sukuku har ta zauna bata da Natsuwa patient din ma sama sama take Dubasu Duka duka goma ta Duba ta kira wata Nurse tace ta kwashe Sauran Folder din ta kaima Dr Aisha batajin Dadin Jikinta ita kuma ta maida kanta ta jingina da kujera ta Dauko Wayarta ta Doka ma Zakiya Kira Don Ta bata mafita.
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
1️⃣3️⃣
"Koda ta Kira Zakiya ta gayamata Abunda ke Faruwa karamar Dariya Zakiya tayi kafin Tace"Sai me..? Kema Dangin ki ne nan da Lokaci kadan zaki zama Daya Daga Cikinsu So ya kamata ku Hadu Duk yana Cikin plan dinmu ne..!
Dina Ta saki Numfashi Tana Fadin"Zan iya kuwa Zakiya..?ina jin wani iri zuciyata tana Rawa Taya zan Fara Tunkararsu yanzu..? Zakiya tace"Karki Damu ki Jira zuwa nan da 3pm zan tashi Daga office zan biyo nan asibitin zan Rakaki sai muje mu gaida inlaws dinki.."Ta karishe Fada Cikin Dariyan Shakiyanci kashe wayarta kawai Dina tayi tana maida Numfashi Har acikin Ranta tana jin Wani iri bayan Haddir da Zaina adagin Zain bata taba Haduwa da kowa ba Zuciyarta na Rawa Tun yanzu kafin ma su san Ita din Wacece a wajen Zain.
Haka kuwa akayi Misalin 3pm na Rana sai ga Zakiya tazo Cikin Asibitin Lokacin Har Dina ta koma Gida tayi wanka ta Sauya Shiga Zuwa Wata Abaya mai Ruwan Coffea,Ta yane kanta da Vail din Abayan wacce ta Bayyana Suran Jikinta,Kafarta sanye Cikin Wani Damdamalin Takalmi Fuskarta ba kwalliya ammh Sanin Dina mai kyau ce ko Batayi kwalliya ba kyanta yana Haskawa Ita kuma Zakiya Doguwar Atamfa ce ke jikinta wacce ta kamata sosai Daga mazaunanta,Kanta ba Dankwali Sai da ta yafa wani Vail a Kanta zuwa Saman Kafadarta Takalmin kafarta ma mai Tsini Ne sai wani Glass Data Toshe Fuskarta,Hannunta Dauke Da karamar Jaka lokaci Daya kuma Tana Kada key din Motarta akallon Farko in kayi musu sai ka kara Domin Sun amsa Sunansu na Mata masu aji da Baiwar iya Taku da isa da kuma Haiba Iya Sarrafa Jikinsu.
Zakiya Tayi ta kara ma Dina karfin Gwiwa Tunda ita ta Sare,kuma ganin Kowa nata zuwa gaishe da Alhaji Tsohon zakiya ta nuna mata in bataje Ba, Zain bazai ji Dadi ba Da wadanan kalaman Ta kara jan Ra"ayinta Ta jata suka Nufi Family Side na Cikin Asibitin.
Duk wanda ke asibitin Dr.Saulawa ya san da wannan Shashin,Shashi ne wanda Dr.Saulawa tun yana da karfinsa yasa aka samar Dashi Saboda iyalansa da yan"uwa da abokan arzuka nan ake Attempting Dinsu har su samu lafiya Shashi ne mai matukar Girma da kawatuwa,Koda yaushe Cikin Gyarashi ake da Sauyamai Fasali,Duka iyalansa ba Wanda bai da Fayel acikin asibitin Saboda Halin Rayuwa Dr.Saulawa da kansa yayi ma Shashin Lakabi da Fanmiy Side.
Daki na Mussmman Mai dan Girma ne Alhaji Tsohon ke Ciki Kofar tana Rufe ne ammh Kana jin Hayaniyar mutane kadan Kadan Daga Ciki Zakiya ce tayi Knooking Din kofar kafin ta Tura ta Fara Shiga da karamar Sallama Hannunta jaye da Hannun Dina Wacce Take jin Wani irin Faduwar gaba kamar ta arce ta gudu,Suna Shigowa Dakin Gabadaya kallo ya Dawo Garesu Sai da suka kariso Tsakiyar Dakin zakiya Taja ta Tsaya Itama Dinar sai ta Tsaya cak,wanda yaji kayan alfarma kamar ba asibiti ba kama Daga Cafet,Kayan kallo kujeru Da kuma Abun Sanyaya Daki A.C,Fridge, Sai gadon Mara lafiya Dake gefe chan Shima din Wani Tsararra ne,Wanda ba Daya yake da Sauran gadajen Dake Cikin Asibitin ba Daga gani na Musamman ne kamar yadda Barayin Ko Shashin yake na Musamman.
Baban Kaduna da Daddyn Abuja sai Abba Usman Suna zaune kan kujeran Dake Gefe,Yayinda mai kallonsu kuma Mom Iklima da Mama Safiya sai Nene ke zaune akai,Daga gefe kuma kan Wata Farar kujera Inna Rukayyah ce zaune,Daga Saman Cafet din kuma Umma ce da Inna Hannatu,Daga saman Gadon da Alhaji Tsoho ke Kishigide Bayan an karamai Filo abayansa kuma Hajiya Mama ce ke zaune gefensa Itama Daga gefenta Zain ne zaune ya yada Kafadarsa Bisa Kafadarta Suna mgana kasa Kasa Daga Tsaye kuma Haddir ne Wanda ya coge Hankalinsa kaco kan yana kan Wayarsa ne,Daga tsakarwajen kuma ga manya manya kololi nan Baje na Abinci sai manya manya Ledoji na kayan Marmari,Daga yanayinsi zaka Fahimci Tabbas Ahalin ya Cika Ahali kuma Ahali ne na Girma Da Dattako.
Da yin Sallamarsu Dama Wajen yayi Tsit duk da Farko Hira na Tashi Sama sama,Gabadaya ido Suka zuba musu suna kallonsu Sama sama da kasa Duk da Baki sun Ta shigowa wasu ba saninsu sukayi ba wasu Likitoci Asibitin ne wasu kuma Nurses ne da Sauran Harda ma"aikatan Asibitin Ba"a barsu abaya ba,ganin Sun Coke ne sun kasa karisowa yasa Inna Hannatu ta Washe bakinta mai Dauke da Hakorin makka Tana Musu Maraba sai Lokacin Dina ta iya Dago kanta ta Kare ma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 32