mana zataje ta Tona maka asiri..? Wani irin Rugurugu yaji a tsakar kansa kamar Rugugin Hadari Kamar an Tsikareshi haka ya Tashi yana Layi ya nufi Mota yana Fadin"Bazan bari ki Tozartani ba Dina..Bazan barki ba."
Haka yake Fada kamar wani Zararre haka ya Tashi Motar ya Fita Daga Haraban wajen kamar zai Tashi Sama shi kadai kawai yake Fadin"Karki mun haka Dina..A"a don Allah karki Mim haka..!
Haka yake ta Fada kamar wani Wanda yayi gamo ko ya zauce..!
*Tanque so much Dearests..Allah ya bar kauna da Zumunci ZAINAZAIN BAND 1&2*
*Shakira..*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
_Budaddiyar wasika Daga Zainullahi Usman Abubakar Saulawa Mijin Halimatu Abdullahi Gada zuwa ga Tarin Masoyansa da makiyansa,yace na Fada muku Mussaman yan Group din ZAINAZAIN BAND 1&2, da kuma yan Group din Janaf Novella 1&2,da Sauran Group din da suke masa One love Rokon alfarma yake Don Allah don Annabi ku Taimakamai ku Koma bayansa ko zai samu wannan Bala"in Dake Tunkaroshi Da sauki a samu masu Rokar masa Firstlove Da kuma masu bama su Alhaji Tsoho baki Domin adaidai wannan Gabar dai ya Sare Ya riga ya Shiga kogin Nadama..Yace na gaya muku yana Godiya ga masu Zaginsa da Tsine masa albarka da wadanda ke Jin Dadin Faruwar haka da kuma Fans dinsa masu Jin ba Badi Dukkanku yace na ce muku yana Muku One love.._❤️😍🤣
1️⃣5️⃣
"Zain yana Fita Daga Gidan Dina GRA ya wuce kai Tsaye yana Tafe yana manganganu Shi Kadai kamar wanda ya Fita Daga Cikin Hayyacinsa.
Hon ya Dinga Zubama Megadi agigice kafin ya wangalemai get ya Sulalo da Motarsa Cikin Gidansu ko gama parking bai yi ba ya Bude Murfin Mota ya Fice da Sauri Gudu Gudu Sauri Sauri Zuwa Kofar da zata sadashi Da asalin Cikin Babban Falon Gidansu.
Abba na Tsaye a tsakar Falo yana gyara zaman Hulan kansa Nene na gefensa Dauke da karamar Jakar briefcase Dinsa Umma ma na Tsaye Dayan gefen,ayayinda suka sakashi a Tsakiya kenan Sai Zainab Dake gefe Itama Cikin Shirinta na kamala Domin har ta samu Gurbin Karatu a Jami"ar ATBU bauchi Ta Fara zuwa Aji Daya 7:30am na safe Take da aji Shiyasa Abba zai kaita tunda Ma"aikatansu na Gaban Jam"ar ne,Tunda har yanzu Motar da Abba ya Siya mata bata iso ba.
Sallama Abba yake da su Umma ya mika Hannu zai karbi Jakarsa Zain ya Fado Falo kamar Daga sama Gefe Daya kuma yana ta waige waige kamar wani mara gaskiya Gabadaya iyayan nashi Suka sakarmai Ido Suna kallonsa Cikin mamakin ganinsa Bashi da Natsuwa kwata kwata atare Dashi.
Cikin Mamaki Abba ya kalleshi yana Fadin"Kai Zain lafiyar ka kuwa..? Ka Shigo gida kamar a Firgice..? Yafada yana sake karantarsa Shi kuwa Sai da yagama Dube Dubensa bai ga alaman Dina Tazo Gidan ba kana ya Saki Ajiyar Zuciya ya kalli Su Abba yana Fadin'Bakomai Abba...Dama...Dama..!
Nene ta katseshi Da Fadin"Dama me..? Yarona Lafiya kuwa..? Ko wani abu ya Faru Da Zaina ne... ? Da sauri ya Girgiza kai yana Fadin"A"a Nene....Dama Dama zan Wuce asibiti ne shine nace Bari na biyo na gaisheku Komai lafiya Da yardan Allah.."Ya karishe Fada yana Faman goge Zufar Dake Tsatsafomai Daga saman Goshinsa Gabadayansa in ka kalleshi baida wata Natsuwa.
Ido Suka zubamai suna kallonsa kawai Cikin mamakinsa kafin Abba yace"Kai zain yaka nan..Daga ganinka baka Cikin Natsuwarka Meya faru..? Kada kai kawai yayi yana Fadin"Bakomai Abba Allah kuwa..Na Wuce asibiti.."Daga Haka bai basu Zarafin mgana ba kawai ya juya ya Fita a gaggauce kamar zai Tashi sama Dukkansu suka Bisa da kallon Mamaki har ya Fice Umma ta kalli Nene Tana Fadin'"Nene yaronki ba lafiya fa..?
Zainab ma tace"Allah Abba kamar yaya yana Firgice ne fa.."Abba ya jinjina kai yana Fadin"Nima Haka nagani..Ammh Tunda yace Bakomai mu barsa abakomai din Allah ya kyauta.."Nene tayi Shuru kafin ta Rausayar Dakai Tana Fadin"Naji Jikina Duk yayi Sanyi..Tunda Nake da Zain ban Taba ganinsa Cikin wannan yanayin Ba.."
Hanyar Fita Abba yayi yana Fadin"Komai miye Allah ya Saukakamai...Ni na wuce.."Dukkansu suka Bishi da Fatan Allah kiyaye Hanya Zainab Tabi Bayanshi Suka Fice Daga Falon Abun mamaki Zain yana Cikin Motarsa bai Tafi ba ya kasa Tuka Motar ma Gabadaya kansa ya Kulle Kiran Layin Dina yake yi kamar Mahaukaci Yana ayyana Faruwan Wasu Abubuwa Dadama Indai Dina ta Rusa plan Dinsa.
Abba ne ya kalli Motar Zain kafin ya Juya ya kalli Zainab yana Fadin"Dubamin Zain din yana Ciki ne.."?jin haka yasa ta karisa Jikin Motan ta Fara Knooking din Glass din Bai ma Jita ba sai chan yaji kana ya Waiwayo ya Sauke gilashin Motar Lokaci Daya yana Sakarmata Jajayen Idanuwansa,Cikin Tsoro tace"Abba ne yace na Dubaka ko kana Ciki..?
Sai da tace Hakane ya Juya yaga Abba Tsaye yana kallonsu Cikin Shakakiyar Murya yace"Kice mai yanzu zan tafi na Tsaya ina Waya ne.."Daga haka ya maida glass din Motar ya Rufe yayi ma Motar Wuta yaFice Daga Gidan Abba ya Rakashi da kallon Mamaki Lokaci Daya yana Nazarinsa Zainab ma Duk Jikinta yayi sanyi,Kada kai kawai Abba yayi Direba ya Budemai Bayan Mota ya Shiga Zainab ta Shiga gaba suka Bi bayan Zain Shi kudu yayi su kuma sukayi yammah Ammh agefen Zuciyar Abba yana Tunanin koma miye yake Damun Zain ba mai Sauki bane Tunda bai Taba ganinsa Cikin Irin wannan Rudewan ba.
*****
*Kano..*
Sabuwar kofa..!
Koda Karfe 10am na safe Tayi Su Zakiya suna Falon Gidansu Dina,Koda suka isa Dina Tun a Mota ta galabaita sun Fito basu karya ba,Sai suka tsaya Bisa Hanya Zakiya ta siya musu Dankali da kwai Ta faraci sai kuma Amai kafin su iso Duk Jikinta ya Saki haka Zakiya ta Shiga da Dina a Rirrike da Ita kamar wacce ta Shekara Tana Jinya.
Hajiya Batula tayi mamakin ganinsu ahaka,tayi ta Tambayan Zakiya meke Damun Dinar ammh sai taki Cewa komai,Daman ai Tasan Zakiya sosai,Nan Falon ta kwantar da Dina wacce ke kara Murkukusun karya Mahaifin Dina yana gari Ya tafi Office ne Cikin Hikima Hajiya Batula ta Kirashi a waya ta Fadamai Ga Zakiya kawar Dina Ta kawota Bata da lafiya yana Jin haka sai Hankalinsa ya Tashi yace tayi Maza ta Kira Family Doctor dinsu Gashi nan zuwa Zasu Shiga Meeting in sun Fito zai kariso Gida.
Haka kuwa akayi Ta Kira Likitansu Dr.Bala Ta gayamai Cikin Abunda bai gaza Mintina Ashirin ba sai gashi Daga yanayin Tambayoyin Dayake ma Dinar tana Bashi amsa yasa Jikin Hajiya Batula ya saki Tayi Jagale Tana Bin Dinar da wani kallon Kurulliya bata dai ce komai ba Jininta ya Diba ya Tafi Dashi Lap dinsu na Asibiti yace Nan da Lokaci kadan zai Dawo da Sakamakon.
Faruwar Haka yasa Zakiya ta kama Dina ta Haura da ita saman Dakinta ta kwantar da ita kan Gado sai ga Hajiya Batula ta Shigo Gegen Dinar ta Zauna Tana Fadin'"Sannu Dota..? Allah kara afuwa..'
Dina ta amsa Tana yamutsa Fuska Zakiya na gefe Tayi Tagumi kamar ta Allah kallonta Hajiya Batula tayi Tana Fadin"Kinsan Abunda ke Damunta ne..? Tafada tana Kafe ta ido Domin haka kurum Taji bata yarda da ita ba,Shuru Zakiya Tayi bayan sun Hada Ido da Dina sai taSunkuyar dakai Tana Fadin'"Anty Mu jira Dawowar Doctor...!
Tana Gama Fadin haka ta kauda kai Domin bataso ta Fara mgana yanzu sai Likita ya iso da Sakamako Uwa uba kuma Daddy ya Dawo anan ne Zata Bude Baki Tayi mgana Sosai,Hajiya Batula Numfashi ta Sauke kawai ta mike tana Fadin"Allah yasa muga alheri."Basu amsa mata ba Har ta Fice Tana Fita Dina tace"Meyasa baki gayamata komai ba..?
Zakiya tace"Ba yanzu ba...Sai Likita ya kawo Sakamako in Tagani ita zata Kira Daddy ta gayamai Shi kuma zai Dawo Gida a Rude Daganan ni kuma zanyi Mgana..'Kai kaawi Dina ta kada Ta maida kanta Bisa Filo ta kwantar Tanajin wani Fargaba Na Abunda zai Faru in Daddy yaji Labarin Abunda ya Faru.
Dr.Bala sai da yayi wajen Awa Daya kana ya Dawo Hajiya Batula kadai ya gani afalo Ita ya Mikama Takardan Ta karba ta Bude Tana Fadin"Nifa ba gane wannan yaren naku na Likitoci nake ba Yimin Bayani Dr Bala..?
Kallonta yayi Cikin Wani yanayi kafin yace"Am sorry to Say Hajiya..Dina is Taking 5weeks Pregancy..! Ido Hajiya Batula ta Zaro Tana kallon Dr.Bala kafin ta saki Takardan HannuntaTana Fadin"Ciki Kake mgana..? Kai ya Gyada mata yana Fadin"Eh kwarai..Tana da Ciki na Tsawon Sati Biyar Harda kwanaki..!
Kirji Hajiya Batula ta Dafe Tana Fadin"Innalillahi Wa"inna Illaihirraju"un...Munshi uku wannan Wani irin Bata suna ne Dina ta Jawo mana..? Tafada lokaci Daya Taji kanta na Sarawa Dr.Bala dai kawai Jinjina kai yake yana Fadin"Sai Hakuri Hajiya.."Numfashi ta Sauke Tana Fadin"Biri yayi kama da Mutum..Dr Bala plz Wannan mganar ya zama Sirri Kar naji ta Fita waje..?
Mirmishi yayi yana Fadin"Haba Hajiya ai Famiy Doctor...Ba iya Likita ba ne Abokin Sirri ne Karki Damu a aikin mu Ba"a yarje maka ka bayyana Sirrin wani ba.."Cikin Gamsuwa tace"Naji Dadin haka...Mungode.."Daga haka taSallameshi ya fice ita kuma Kai Tsaye ta Rarumi Takardan zuwa Dakinta Wayarta ta Jawo ta Kira Kwamishina Alhaji Gaddafi Sheerif,Lokacin suna Meeting bai Daga Kiranta ba sai ta Turamai sakon ya Dawo Gida Ba Lafiya Daganan ta Fito a gaggauce sai Dakin Dina tana Shiga ta watsa mata Farar Takardan kan Jikinta Tana Fadin"Yanzu Fisabillahi Da Kuruciyarki baki Debomana Abun kunya ba Dina sai da girma ya kamaki..?
Tafada Tana kallonta Cikin Wani Takaichi da Bakinciki Domin koda Dina ba yarta bace Taji Hankalinta ya Tashi da jin Wannan Labarin,Dina ta Dago kanta Tana kallon Hajiya Batula kafin ta waiga Tana kallon Zakiya wacce ta gyada mai kawai sai Dina ta Fara matsan kwallah Tana Fadin"Ba laifina bane Anty..Yaudarata yayi..!
Hajiya Batula ta saki baki kawai Tana kallonta kafin tace"Daman kinsan da Cikin kenan..? Da Sauri Zakiya tace"Eh..Jiya ne ta Kira Bata da lafiya sai nazo na Rakata asibitin Datake aiki aka Dibi Jininta aka auta,Shine yake sanar damu Tana Da Shigar Ciki na Sati5 da wasu kwanaki.."Tafada Cikin Nuna alhininta cikin Kufuluwa Hajiya Batula tace"Lalle...Shine kuma sai kika kwasio ta ita da Abun kunyar zuwa nan ko..?ina laifin ku Tsaya chan anemi Uban Cikin..Tunda nasan ta sanshi ko nace ko sun sanshi.."
Ta Karishe Fada Cikin Bacin Rai Zakiya ta Dukar da kai Tana Fadin"Ita ta matsa sai na kawota Gida...Kuma nayi Tambayar Duniyanan taki Fadamin ko waye yayi mata wannan aiki sai dai tayi ta kuka Tana Fadin Yaudaranta akayi.."Wani Dogon Tsaki Hajiya Batula Tayi kafin tace"Ita dai ta Yaudari kanta..Irin Abunda nayi ta Guda kenan,Da naga Alhaji ya sake ma Rayuwar yarinyar nan Dama na sani ita Mace ba"a sakar mata sai tazo da Abunda zai Bata Zuru"a gabadaya.."Daga Dina har Zakiya ba wanda ya kara mgana Ficewa Daga Dakin Hajiya Batula Tayi Tana Fadin"Sai mu Jira Dawowar Mahaifinki kila Shi in ya Tambayeki zaki mai bayani inda kika Samo Cikin Jiki ki..Aikin Banza kawai..!
Sai da ta Fice ne Dina Ta mike zaune Tana Fadin"Nifa ina Jin Tsoro Zakiya..? Ina Tsoron Faruwan waniAbu.."Zakiya ta Dafa kafadanta Tana Fadin"Dole daman Wani Abu zai Faru mana..Ammh ba yadda kike Tunani ba..Ki kwantar da hankalinki ina Tare dake.."Ita dai Dina Hankalinta yaki kwanciya komawa kawai Tayi ta kwanta Tana Tunanin wannan Abunda sukeyi ba wata Hanya bace ta Rusa Rayuwarta data iyayenta ba kuwa..? Da wani ido zata iya Kallon Daddy da Dan Shege...? Wannan Shine Sakamakon Irin Gata Da kaunar da ya nuna mata kenan...?
****
Zain Da ya bar gidansu Gidan Dina yasake Komawa yana Ta Bugawa kamar wani Mahaukaci Sabon kamu,Yakira Lambar Dina Sau Shurun matsaki Bai san Adadi ba,Ganin ba mafita yasa ya Shiga Motarsa kawai ya Dinga yawo acikin gari bai san ina zashi ba Idanuwansa sun kala sunyi Jajir so yake yayi kuka ammh ya gagara haka kurum yaje wani irin Faduwar gaba yana jin akwai wani gagarumin Mtsala Dake Tunkararsa.
Yayi ta Tunanin meyasa Dina tayi mai haka..?meyasa ta saba alkawari..!? Tuni wata Zuciyar ta an karar dashi Tayi hakan ne Domin Bayyana komai,baya Raba Daya Biyu Dina Kano Ta Tafi..? Tuna haka yasa sai da yaji wani Gigitaccen Faduwar gaba mai Dauke da wasu Rugajewar Abubuwa ajikinsa,Gabadaya ya Fita Hayyacinsa,yana ji yana gani ana ta Kiran wayarsa yaki Dagawa Firstlove tana ta Kiranshi Yana kallo Zata Tsinke ammh ya Kasa Daga Kiranta..? Da wata kalmar zai mata mgana..? Me zai ce mata..? Ayanzu bai da wani irin Kalma ko Mgana da zai iya kare kansa komai kuma ya kare mai..!
Yana ganin Kiran Sadiq Babba,Shima ya kasa Daga Kiransa,Kansa ke Ciwo kamar ya Cire ya yar haka yaje ji Ganin zama ba nashi bane yasa kawai ya yanke Shawaran zuwa kano ya Nemi Dina,Har ya Juya kan Mota sai kuma wata zuciyar tace"wannan karon wannan yakin bazai yuyu kai Kadai ba zain..Koma Miye Shirin Dina na Tozartakane ko kaje kano ka sameta ba Lalle bane ta Saurareka..Ya zama Dole ka nemi Taimako ko agaji. !
Sitiyarin Motarsa ya Buga Cikin Muryan kuka yace"Wayyo kaichona...Yanzu Wa zan Tunkara da wannan mganar..? Wazan iya Tara na gayamai nayi ma Wata Ciki watan ma karuwa ba Matar Auransa na Sunna ba.."Yake Fada yana kuka Kamar karamin yaro ammh kuma ba Digon Hawaye saboda Tsabar Halin Dayake ciki.
Kamar amafarki ya Dakata da kukan Da yake yi Lokaci Daya yana Fadin"Haddir...! Yes Haddir ne kadai ya Chanchanta naje ma da kukana Shi kadai ne zai iya samamin mafita.."Da sauri ya karya kan Mota sai Asibiti kamar wanda ya Zare,yana Tafe yana Kiran Layin Haddir wanda Tana gabda Zata Katse Haddir ya Daga Kiran yana Fadin"Zain ya akayi ne..?
Cikin Shakewar Murya yake Fadin"Kana cikin Asibiti ne..? Cikin Mamaki Haddir yace"Eh lafiya naji muryanka wani iri..? Batare da Zain ya kara mgana ba ya Katse Kiran Daga bangaran Haddir kuwa wayar yabi da kallo yana mamakin Jin muryan Zain din Cikin Damuwa Da Dimuwa ba yadda yake ba ganin baida wanda zai bashi amsa ne yasa ya ijiye wayar ya Cigaba da Duba patient dinsa yana yi yana Dubaa gogon domin Jirgin da ya Dauko Inna Hannatu karfe 12:30pm zai sauka ta Kirashi Tun jiya ta gayamai zai zo Filin Jirgi ya Dauketa.
Haka ya Shiga Cikin asibitin kamar wani mahaukaci Sabon kamu Wayarsa ma amotar ya barsa,Haka Ma"ikatan asibitin keta mai sannu da zuwa suna gaisheshi ko tan kowa bai bi ba,Kai Tsaye Office din Haddir ya isa Bude Kofar ma Da yayi ba Cikin Hayyacinsa yayi ba Haddir Dake Zaune ya gama Duba patient din karshe Domin zai Fita ne Sai ga Zain ya Shigo.
Cikin mamaki Haddir ya Dago yana kallon Zain Wanda ya kariso Gabansa batare da Tunanin komai ba ya Zube gaban Haddir Lokaci Daya da kama Kafarsa yana Fadin"Na Shiga uku Haddir...Haddir na kashe kaina..Naki jin mganarka najin Shawaranka Dan"uwana yau gashi Dalilin Rashin Jin mganarsa yakai ni ga Fadawa wani Bala"i wanda nake jin kunyar kaina da Abunda na aikata.."Yake fada yana sakin Muryansa gabadaya cikin kukan da ba Hawaye.
Mamaki da al"ajabi ya Sandarar da Haddir Dake zaune da Sauri ya Janye kafarsa yana kallon Zain Cikin Tarin Tamboyoyi ya mike yana Fadin"Subhanallah Zain lafiya..? Meya kefaruwa..? Yafada yana Dago Kafadun Zain Daga Zaune zuwa Tsaye kawai sai ji yayi Zain ya Fado Jikinsa yana wani makyarkayata kamar wanda Shooking ke jansa Cikin Wani irin Faduwar gaba Haddir ya Rikesa yana Fadin"Zain meya faru.?Kasani Cikin Rudu ka gayamin Abunda ya Faru don Allah..!
Sakinsa Zain yayi kafin ya Riko Hannayensa Duka Biyun yana Fadin"Haddir na jawo ma Zuru"armu Abun kunya Abunda kake gujemin ne ya Faru Dani...Ni zain yau aka wayi gari nayi mata Ciki...Ciki fa Haddir Ciki na Haihuwa nayi ma karuwa ba Matata ba.."Ya karishe Fada yana wanin Kamar ya Kwanta akasa yayi ta Birgima yana kuka.
Ido Haddir ya kwalalo Waje yana Fadin"Ciki...? Wa kuma kayi ma Ciki Zain..?ya fada yana Girgiza kafadansa Cikin Fitan Hayyaci Zain yace"Eh Ciki dai Daka sani na Haihuwa..Ciki nayi ma Dina Haddir ni da kaina..Kaichona.."Baya kawai Haddir kawai ya fara ja yana kallon Zain Lokaci Daya yana Nunashi da Yatsa yama kasa mgana Ganin haka yasa Zain ya Duke kansa yana Sakin Kuka kawai Kamar wani karamin yaro.
Haddir kuwa sai da ya Dangana Da Bango ya Dafa kana ya iya Tsayuwa,Kansa ya Dafe lokaci Daya yana Maimaita"Hasbunallahi Wani"imal wakil...Allahuman Ajirni musibatihi...! Yake ta maimatawa yana Dafe da kansa Cikin Fitan Hayyaci ya Dago yana kallon Zain lokaci Daya yana Fadin"Dina..? Daman baka Rabu da Shedaniyar yarinyar nan ba Zain..? Innalillahi Shiyasa nake gaya maka Ka Rabu da ita ka rabu da wannan Shashanci Saboda gudun irin wannan Ranar Zain yanzu wa gari ya waya..?
Ya fada yana kallon Zain Shima Hawayensa sun cikamai ido kamar ya saki kukan Zain dake Zaune Dirshan a kasa ya Dago Yana kallon Haddir yana Fadin"Bansan Dalili ba..Ban kuma san ya akayi haka ba..Ko ina son Rabuwa da Dina sai naji na saka Wlh Har ga Allah ba"a son Raina nake Tarraya da ita ba Haddir ba"a son Raina bane ka yarda Dani..!
Haddir ya kalleshi Cikin Bakonciki Da Takaichi yace"Komai ya Faru kai ne Sila Zain...Tun farko Addininka ya Hanaka Kusantar ZINA kai kuma ka Kusanceta..Tunda ka Fara ta kaji Dadinta baxaka iya bari ba nasha Fada maka ka kori yarinyar nan Daga asibitinan ta bar garin ta koma garinsu kakijin mgana ne Abunda nayi ta Gujemaka ne ya Faru dakai..Yanzu ta ina zamu Tunkari wannan Mummunar kaddaran Data Fadomana..? Da wani ido Zamu kalli Danginmu da iyayenmu da wannan Labarin Mara Dadin Ji..?
Yafada yana Share Kwallar da Suka zubomai,Zain kuwa kansa ya Dafe yana Ta Jijjigawa yana Fadin"Kaichona na Cucu kaina..Na Biyema Rudin Abokai da kuma Shedan na Fada ga Halaka Hakika Duk wanda ya maida Zina Abun kawansa ya Jira Ranar da Zata Zama Silan Shigansa wani Bala"in da bazai iya Fita ba..Ya zanyi Haddir..? bani da kowa sai kai kai ne kadai Hop dina yanzu ka Fadamin Taya zan Tunkarin wannan matsalan Data Tunkaroni..? Yafada jijiyoyin kansa Sun Bayyyana Muryansa taDisashe saboda Tashin Hankali.
Batare da Haddir yamai mgana ba ya Juya ya Tunkari Kofa ya Murza Makulli ya Kulleta kana ya Dawo ya Dago Zain Daga kasa zuwa kan kujera ya zaunar Dashi kana ya zauna gefensa yana Fadin"Kaddaran ta Riga ta Faru Zain...yanzu sai dai muyi Kokarin Rufa wannan mganar Yanzu ina ita Dinar.?
Cikin Jujjuya kai Zain yake Fadin"Bansani ba Haddir..Bansan ina Take ba.."Cike da Mamaki Haddir yake kallonsa yana Fadin"Bangane baka sani ba..? Cikin Damuwa da Nadama Zain ya Fara bama Haddir Labarin Abunda ya Faru Daran Jiya Har zuwa wayewar gari yau ya kara Da Fadin"Nayi ta Kiran wayarta a kashe...Gidanta kuma makotanta sun Tabbatarmin tayi sammakon Fita Haddir Ji yadda Zuciyata take Bugawa ina jin Kamar wani Abu Dina take Shiryawa akaina..'" ya fada yana Dora Hannun Haddir a saman Kirjinsa yana jin yadda kowani Dakika take Bugawa
Haddir ya janye hannunshi Yana Fadin"Ba kamar kana ji ba..Tabbas ta Shirya wani Abune..Abu kuma da bazai mana Dadi ba Dukkanmu."Zain ya Dago Araunane yana Fadin"Kamar wani Abu kenan..? Haddir yace"Bansani ba..Ammh ina Zargin Da gangan ta bari komai ya Faru..Ta Shirya Fasalla mganar Cikin nan ga Su Abba ne nifa atunanina.."Zain ya Mike Zumbur yana Fadin"Ina..? Bazai sabu ba Haddir..Bazan bari Dina Tayi min Wannan Illar ba..!
Yake Fada Kamar wani Zautattace,Haddir ya mike ya Rikosa yana Fadin"Wannan Surutan duk ba mafita bane...Ka zauna mu samu mafita.."Da wannan kalaman ya samu Zain ya koma ya zauna Shima sai ya koma ya zauna yana Fadin"Kasan Gidan kawarta din nan..?
Kuri Zain yayi mai da ido kamar mai Tunani kafin Da Sauri yace"Kana Nufin Zakiya..? Da sauri Haddir yace"Bansani ba..Wannan dai kawar nata dai Da suke Tare I think Zakiya din ne Sunanta.."Da Sauri Zain yace"Kssh...Sai yanzu na Tuna da ita...Ammh bansan gidanta ba sai dai Nasan a inda Take aiki.."
Da Sauri Haddir yace"Ina ne..? Zain yace"Kamfanin Sadarwa ta Layin Mtn...Office dinta na Babban Heaquater dinsu ta nan garin.."Batare da wani Tunani ba Haddir ya mike yana Fadin"Tashi muje..Na Tabbata ko kowa bai san inda Dina Take ba Ita ta sani.."Ba Gaddama Zain yabi bayan Haddir suka Fita Tare Sauri Sauri Gudu gudu suka isa Haraban Asibitin amotan Haddir suka Tafi Mintina ashirin da wani Abu yakai su Ma"akatan su Zakiya sai dai suna Shiga ciki suka Tambayeta aka Tabbatar musu da yau batazo aiki ba ta Dauki Excuse zata tafi Ganin Gida kano Sai Monday zata dawo ana Fada musu Haka Zain ya Rike Haddir yana Fadin"Na gayamaka..Sun Shirya wani Abu.." yake fada kamar zai Fadi Saboda Tashin Hankali Haka Haddir ya Rikosa zuwa Mota sai da suka Fara Tafiya kana Zain ya Dago Daga Kansa yana Fadin"Menene Abunyi Haddir..? Im mukayi Jinkiri Asirina zai iya Tonuwa..?
Haddir ya Sauke Numfashi yana Fadin"Tabbas...Ita da kawar nata suka Shirya komai ni Tsorona Daya bansan Ma"nar Abunda Suka aikata ba kuma ina Jin Tsoron wani tsari ne Tsarinsu na Gaba.."Zain dai ba baki sai Numfashinsa Dake kokuwa kafin yace"Mu Tafi kano kawai Haddir...Mu Je chan mu samesu sai ayi wacce za"ayi..'
Cikin Jinjina kai Haddir yace"A ina zamu sameta..? Zain yace"Gidansu mana..?Haddir yace"Zata je gida awannan Halin kake gani..? Shuru Zain yayi kafin yace"Muje dai...Gidan kwamishina ba boyayye bane..In bata nan sai mu samu Wata Hanyar ammh ina kyautata Zaton Tana chan.."Kada kai kawai Haddir yayi Daidai Lokacin da Wayarsa ta Dauki Tsuwa yana Fito Da ita Daga Aljihu ya waro ido yana Fadin"Kai...Abokiya Zareena Ta zo Nageria..!
Da sauri Zain ya kallesa yana Fadin"In jiwa..? Wayarsa ya nuna mai yana Fadin"Gashi ta Kirani da Lambarta na Gida ba na chan U.s ba.."Dakyar zain ya iya Hadiye wani Miyau mai Daci Shi kuma Haddir ya Daga Kiran yana Fadin"Abokiya me zan gani haka..?badai kin Diro Ba Labari ba..?
Dagachan Bangaran Zafeera Dake Falon Gidansu Su Saudat sun Zagayeta,Umma na Zaune kusa da ita rike da Takwaranta Jalal kuma na Kan Cinyar Nene Bakinta Har kunne tace"Eh mana So nake na baku mamaki..Gani afalon su Umma gasu ma kusa dani Dana Sauka nayi ta Kiran Lambar Aboki Zain Tana Ringing bai Daga ba Kawai sai na Kira Abba ya Turo Direba ya Daukeni Daga Katsina nake Tun Shekaranjiya muka sauka Nida Abba Jalal yana chan sai an kwana Biyu zai Bullo..'
Haddir yace"Masha Allah..Sannu dazuwa..Zain kuma Muna tare dashi Wayarsa ya barta amota gamu nan zuwa muyi Sannu da zuwa dakyau asha Hirar yaushe gamo.."Tana Dariya tace"Yauwa Abokaina na Hakika ina Jiranku.."Daga haka suka katse Kiran Zain yana kallon Haddir bai samu Zarafin mgana ba yace mai"Zuwan mu kano yau baazai yuyu ba sai dai Mu Jira gobe..?
Cike da Tashin Hankali Zain yace"Saboda..?ammh kasa."Bai ida mgana ba wayar Haddir ta Kara Daukan Tsuwa Cikin Dafe kai yace"Innalillahi ai na Sha"afa.."Zain yace"Mun Shiga uku menene kuma..?Haddir yace"Wlh Inna Hannatu ta Kirani Tun safe tace min gata zata Hawo Jirgi nan da 12:30pm nazo Filin Jirgi in dauketa..'
Ido Zain ya kwalalo waje yana Fadin"kuma..? Me hakan ke Nufi Zafeena tazo ga Inna Hannatu ma zata zo Haddir..?Haddir na Shafa kansa yana Fadin"Bama ita kadai ba..Kowa dakowa zai zo Zain..Akwai Gagaruman mtasala kuwa indai Hasheshena ya zama gaskiya.."
Cikin Fitan Hayyaci Zain yace"Bangane kowa da kowa zai zo ba..?kai tsaye Haddir yace"Ina Tunanin gobe Asabar din Karshen wata..In lissafina yayi daidai wannan watan Shine Watan Taronmu na Family kuma kasan wanchan watan ya Kamata ayi ba"a samu yi ba ina Kyautata zaton Gobe ne za"ayi Zaman.."Dafe kai kawai Zain yayi yana Fadin"Qalu inna Lillahi..Haddir na Mutu Shikenan Asirina zai Tonu Wlh.."
Shima Haddir Yana Cikin Tashin Hankali ya kalli Zain yana Fadin "Bari muje mu Dauko Inna Hannatu Daga Filin Jirgi Allah zai kawo mana mafita.."Daga haka Haddir yaja Mota Suka Nufi Mallam Aminu International Airport.
Suna Zuwa suka iske Har Inna Hannatun tasauka sai Fada take tana Fadin Tana Kiran wayar Haddir bai Daga ba Haka ma Zain,Saboda Tana Fadan ne yasa Bata Fahimci basa cikin Natsuwarsu ba har gwara ma Haddir ya Tattaro Natsuwar Zain kuwa Zaro ido kawai yake yana kifta idanuwa Jira kawai yake ace kyf ya zura da Gudu.
Gidan Alhaji Tsoho suka kaita Suna Shirin kara Zillewa tace sai sun Shigar mata da kaya Domin kaf a Ya"yan Alhaji Tsoho da ita da Baban kaduna ne mafadata,Suna Shiga Zain yaci karo da Zainarsa Cike da mamaki take kallonsa tana Tambayansa bai Tafi Gomben bane..?
Ganin Baya Cikin Natsuwarsa ne yasa Haddir ya Bata amsa da bai samu Tafiyar ba Abun ya bata mamaki ganin Firstlove baya ma iya Hada ido Da ita kamar Alhaji Tsoho ya sann Suna Cikin Uzurin son Tafiya ya Hanasu ya Zaunar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 32