Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Jama"ar Dakin Kallo Daidai Lokacin da Zain ya Dago kansa Daga Kafadar Hajiya Mama suka Hada Ido Hudu Da Dina. Wani irin yanke gabansa yayi ya Fadi Lokaci Daya ya zaro Ido yana kallonta ita kuma sai ta lamgwabe mai kai ta wani Rausayar da idanuwanta,Zakiya ce ta Damke hannunta Lokaci Daya tana Sakin Mirmishi ganin Gabadaya idanuwansu yana kansu ne,Zain kuma da Sauri ya kauda kai yana kokarin Daidaita  Natsuwarsa Haddir ne ya Dago kansa ya Sauke su kan Su Dina da mamaki yake kare musu kallo bai samu Zarafin mgana ba Yaji Alhaji Tsoho Dake Kishingide Cikin Wata Farar Jallabiya Muryansa ta Dan Shake alamun Mura yace"Maraba sannunku da zuwa..Ke Hannatu ku basu Wajen zama mana.." Yafada yana kallon Inna Hannatu dake Zaune kasa,Bata mike ba illah kafanta Data jaye Tana Fadin"Ai maraban nake musu Alhaji Tsoho Sannun ku da zuwa ga waje ku zauna Duka iyayan naku sun zaune kujerun.." Tafada Tana yar Dariya Da Sauri Zakiya Tace"La bakomai..Dama munzo Duba mai Jiki ne.."Tafada tana jan Dina zuwa Gaban Gadon Alhaji Tsoho Cikin ladabi Ta Rankwafa ta gaisheshi da Alhaji Tsoho da Jiki ya amsa Ganin haka yasa itama Dina Tayi hakan ya amsa Cikin Sakin Fuska yana ta saka musu albarka Zain dai Gabadaya bai da Natsuwa Hajiya Mama dake gefensa Tace"Kai kuma lafiyarka sai Hada Zufa kake Kamar wanda yake jin kashi..! Tafada Tana kallonsa Dariya ta Kubcema Haddir ya saketa har yana Dukawa yana kallon Zain wanda ya Hade rai yana wani Hura Hanci Cikin Son Basarwa yace"Ina Ruwanki kedai ji da wannan Tsohon Mijin naki gawa taki Rami kawai.."Haddir sai Dariya yake Hajiya Mama na Tayashi Dina kuwa sai nacin kallonsa Take yaki yarda su Hada Ido Zakiya kuwa kowa awajen take karema kallo su Baban kaduna dai suna ma Hirnsu ne haka ma su Nene Gwara ma Inna Hannatu da Umma hankalinsu na kansu Suna Nazaratansu. Alhaji Tsoho ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Yau kuma Aminatu Keda Megidan naki ake jin kanku..? Haddir yayi Saurin Fadin"Tsoho Daman ai Megidan na Bugi ne..Nine kadai Megidan gaskiya.."Hararansa Hajiya mama tayi Lokaci Daya Tana maida Hankalinta kan Zain wanda ya Fito da wayarsa yana Dannawa ji yake kamar Ahalinsa sun san Abunda yake aikatawa Shiyasa ya kasa Sukuni Sai Hada Zufa yakeDafoshi Tayi Tana Fadin"Kaji Juyo gareni Megidana Zainullahi kyale Hadiru ni kam Bani son Shi baya Cefene."Saurin Ture hannunta yayi yana Fadin"Jeki na Sakeki..Ko ki koma wajen Tsohon Mijinki ko kuma ki koma Ma Haddir din."kwabe baki Tayi Tana Fadin"Au ni zaka watsa ma kasa a ido..? Fuska ya Hade yana Fadin"An watsan wa ya ja.."Yafada yana matsawa kusa da ita nesa kadan Haddir da Alhaji Tsoho suna ta musu Dariya Dina dai da Zakiya suna Tsaye suna kallon Tsabar Shakuwa Tsskanin Jikoki da kakaninsu,Alhaji Tsoho ne ya an kare dasu,Dasauri ya kallesu yana Fadin"Af..Kunga mun Sha"afa da Baki..Sannunnku an gode ko..? Ammh Daga ina kuke ne...? Yafada Cikin Muryan Tsufa Lokaci Daya yana gyara zaman Farin Gilashin Idonsa Zakiya ce ta Murmusa bata samu Zarafin mgana ba Haddir yace"Wannan  anan asibitin Take aiki...Wannan kuma ina jin kawarta ce Domin ba'anan take aiki ba"Yafada yana kallonsu Zakiya Tayi yake kafin Tace"Eh ni Kawarta ce.."Tafada tana wani kallon Haddir din Kasa kasa yana Lura da ita ammh sai ya basar da ita,Alhaji Tsoho yace"Allah Sarki Sannunku fa Nagode Allah yayi albarka.."Sukace Ameen Cikin Dattakonsa ya kallesu yana Fadin"Duk wanda yazo gaisheni Ko daga ina ne baya Tafiya sai na san Sunanshi ko Sunanta.! Zakiya ta Murmusa kafin Tace"ni Sunana Zakiya Nuhu Daga Jahar kano.."Tafada tana kallon Dina Wacce take nacin kallon Zain Shi kuma yaki kallonta Cikin Sadda kai Tace"Dina Gaddafi Sheerif Nima Daga Kano.."Alhaji Tsoho ya kalleta Sosai bama Shi kadai ba Hatta su Baban kaduna sai da suka Dago Suna kallonta kafin Alhaji Tsoho ya samu Zarafin mgana Baban Kaduna yace"Gaddafi Sheerif Dai da muka sani kwamishinan kudi na Jahar kano.." Haddir ne ya gyada kai yana Fadin"Shifa Baba..Diyarsa ce.."Baban kaduna da Daddyn Abuja suka Hada baki wajen Fadin "Ikon Allah.."Shiko Alhaji Tsoho Mirmishi yayi yana Fadin"Masha Allah..Sannunki naji Dadin yadda kika Dogara ga kanki ba wa mukamin Babanki ba kika Tsaya kikayi karatu Domin Taimakon Al"ummah Allah yayi albarka.."Kansu na kasa Suna amsawa Da Ameen Alhaji Tsoho ya sake kallon Dina yana Fadin"Ammh yata Baki da wani Suna ne..? Naji kince Sunanki Dina kuma a sanina Sunan Kiristoci ne wannan Sunan domin in bazan manta akwai wata wacce mukayi aiki da ita a asibitin Dana Fara aiki a Bongcuf,Itama Likitar kwakwalwa ce Sunanta Dr Dina itama.."Dariya ta kama su Umma da Inna Hannatu Hajiya Mama tayi karaf tace"Yo in ban da Abunka Alhaji Yanzu yandda zamanin nan ya lalace Sunan ma Da zakaji an saka bashi da wani Ma"ana ayi ta kwaikwayon Arna wajen saka Sunaye Allah dai ya kyauta kawai.."Haddir da Alhaji Tsoho Suka ce Ameen Dina kuwa sai Taji ta Muzanta Kallonsu Alhaji Tsoho yayi yana Fadin"Nagode kwarai Allah yayi albarka..! Zakiya ta Rankwafa Tana Fadin"Allah kara lafiya da Nisan kwana.."su Inna Hannatu suka amsa da Ameen Ameen juyawa sukayi suna ma su Nene sallama Mama Safiya ce kadai ta amsa Mom Ikilima kallon TaraSaura kwata tayi musu Tana Fadin"Kai Nene wadanan yan mata basu da kamun kai kalli Shigarsu.."Nene ta Tabe baki Tana Binsu da wani kallo Haka Kurum Taji basu Burgeta ba,Suna Gabda Fita Daga Dakin aka Turo Kofa aka Shigo Zainab ce kan gaba ita da Maryama Din Inna Hannatu,Dauke da manyan Kololi a Hannunsu,Sai Zafeera da Zaina da suka Shigo Daga Baya Zafeera na Rike da Filet da cokali ita kuma Zaina na Rike da Katon Jug,Dukkansu basu ma Lura dasu ba Zafeera har Tana bangazan kafadan Zakiya kuma ko ta waigo Saboda Hankalinta ya tafi kan iyayenta Dake Dakin ne,Zakiya ta Juyo Tana kare ma Zafeera kallo Cikin baki isa ba ita kuma Dina Zaina ta kura ma ido ganin ta ta kara Kiba da Haske Alhaji Tsoho ne ke ta Fadin"Maraba da Amaryata Halimatu Sa'adiya mai Hali Dubu...Maraba da Zafeeratu Farar mace alkyabban Mata maraba da Zainabu Abu mai Tagwayen Suna Maraba da Maryama Allahu Akbar Allah yasa Ki yi koyi da Hali Irin Maryama Uwar Rikon Haddir da Zanullahi da Zareena uwa Shakikaya wajen Halimatu Sa"adiya Allah ya mata Rahma Ita da Abdullahi Da Mallam Umaru da Atine Allah ya Hadamu a Aljannah Firdausi.."Ya karishe Fada Cikin Alhini Duka Dakin suka Hada baki Wajem Fadin "Ameen Ameen ya Allah...Allah ya Haskaka kabarinsu.! Gaban su Umma suka yada Kololin Gabansu suna gaida Iyayen Nasu Daddyn Abuja ne yace"Sa"adiya me kika Dafo ma Tsohon naki ne?ya fada yana kallon zaina dama Sa"adiya yake Kiranta da Shi,Baban Kaduna ne kan kirata Halimatu su Mom Iklima kuma Dukkansu Zaina ne,Tana Dariya Tace"La..Daddy Tuwon Semo nayi muku miyar Kubewa Bushashiya Dukkanku Domin nasan Duka iyayen nawa sun yi Gado Wajen Tsohon nan na kwance.."Ta karishe Fada Tana Dariya Suma Dariyan Suka saka Mama Safiya tace"kwarai..Duka gidajenmu Gidan Daura Tuwo ne..Allah dai ya karama Alhaji Tsoho Lafiya..! Suka amsa da Ameen gabadaya Alhaji Tsoho yace"Dama ai kyan ya"ya su gaji Tsohonsu...Kunga wannan Tuwon Shi ke kara Muku Lafiya da karfin gani ba Ciyen Ciyen kayan Turawan nan ba.."Zain yace."Hakane Tsoho...Ina mamakin zamowarka Likitan kwakwalwa Ba Likitan Sanin Mutum har hanji ba.."Dariya suka sakamai Gabadaya kafin Hajiya Mama tace"Ke ta kwacen Miji zuboma mijina Tuwon yaci yasha mgani Tun Dazu yaki cin komai yana Jiranki.."Tafada Tana Hararanta Dariya kawai tayi ta Duka ta Fara zubamai Tuwon Zafeera na Tayata Zain na Daga gefe ya Dago kansa yana Fadin"Kinga Firstlove Da kin Sakama Tsohon nan Zubomin Ina jin yunwa.."Haddir ya kallesa yana Fadin"Lalle ne ma.Su Abban fa..? Harara ya Zabgamai zai yi mgana kenan suka Hada ido Da Dina Dake tsaye har yanzu basu Tafi ba Ido yazaro yana kallonta ganin Haka yasa Zakiya Taja Hannun Dina suka Fice su kansu basu san meya Tsaidasu ba ammh Ahalin na Gidan Saulawa Abun kallo ne Suna Da Fahimta Da kuma Kaunar Juna basu samu Zarafin mgana ba sai da suka Dangana da Office din Dina Zakiya kafin ta zauna sai da taKwankwadi Ruwa kana ta koma tazauna Tana maida Numfashi Dina kuma Takaichi ne Fal acikin Ranta da kuma Kishin Zaina Daya yi mata katutu. Dina kuwa zama Tayi kan kujeran Dake kallon na Zakiya Tana Fadin"Tsohon nan ya Cika Tambaye Tambayen Tsiya..'Zakiya tayi Mirmishi Tana Fadin"Likitan kwakwalwa ne fa...Tsohon Daga gani Lokacin Da yake kan ganiyar kuruciyarsa anyi Jajirtattace.."Ta karishe Fada Tana yar Dariya kafin ta Dora da Fadin"Baki mamakin yadda Shekarunsa sukaja Haka ba ammh kallesa Hutu da Jin Dadi Sun Boye tsufansa..? Dina Ta Tabe baki Tana Fadin"Ke ni bama Wannan ba..Wai kiji fa Cemin yayi Sunana irin na Kiristoci ne..? Da gaske ne sunana ba na Musulmai bane.'? Ta fada Tana kallon Zakiya Ido Cikin Ido Wacce ta saka Dariya Tana Fadin"ina zan sani.? Ammh Tunda kikaji ya Fada gaskiya ne..Sai kiyi Hakuri Tunda Babanki ya Riga Da ya saka miiki baki da yarda zakiyi kuma..! Baki Dina Ta Bude Tana Fadin"Bangane ba.? Zakiya Tace"dama ai bazaki gane ba....Ke wai wata yarinyan ce ta Bangajeni Da zata Shigo Din nan.? Baki Dina Ta Tabe Tana Fadin"Ina zamnsanta..Banga Fuskarta ba  Matarsa kadai na iya Ganewa Sai Haddir sai Shi kanshi zain din gabadaya Cikin Dakin Banda su ban son kowa ba..! Zakiya tace"Soon zaki sansu Kawata...Nadai san na kan gadon nan Kakanininsu ne,Sai kuma Mazan Dake gefe sukuma iyayansu ne,Kin manta an gayamana Ya"yansa Biyar uku Maza Biyu mata,Kana ina kyautata zaton bayan Matan ya"yansa akwai ya"yansa mata Biyu a wajen."Dina tayi Tagumi Tana Fadin"Hmmm..Kina Nufin Harda iyayen Zain awajen..!? Zakiya tace"eh mana Surukan ki na Wajen..Kilama sune Wadanda da zamu Tafi mukayi musu Sallama sukabi da kallon Wulakanci.."Dina ta waro Ido Tana Fadin"Topha..Kada fa hakan ya bata mana Shiri fa..? Mikewa Zakiya Tayi Tana Rataya Jakarta Lokaci Daya Tana Fadin"Basu isa ba....Ki kwantar da Hankali Wlh bazan Taba Natsuwa ba sai naga wannan aikin namu ya tafi Sussufull ba wata matsala.."Dina ta sakar mata ido kafin tace"Kin Tabbata..? Taku Zakiya ta Farayi gabanta Lokaci Daya Tana Dafa Kafadarta Tana Fadin"Kin manta da kudinki kika Biyamin nayi Rigisteration na Shiga Jami"a Lokacin da Babana ya nuna Aurar Dani zai yi..?ni kuma nace karatu zanyi na Tssayu ga Kafafuna..? Ko kin manta Kina London kin Sha Turomin da kudin Abinci Dana Makaranta Har sai da na Shiga Aji Uku na Fara Raba ma maza Jikina Suna Bani kudi..? Ta fada Tana kallon Dinar wacce tayi Mirmishi Tana Fadin"Ni na manta...Bakuma nasan kina Tuna Baya.."Dariya Zakiya Tayi Tana Fadin"Zaki iya mantawa ammh ni bazan Taba Manta wannan Alherin naki gareni ba Dina..Shiyasa nayi Miki alkawarin bazan Runtsa ba sai naga Kin mallaki Zain kamar yadda kike Buri..! Ke baki Hango Yadda Fuskokin wasu zai sauya Daga Farinciki Zuwa Bakin Ciki ba..? Na Tabbata zasu Girgiza in sukaji labarin Abunda Dansu mafi Soyuwa garesu yake aikatawa Wlh inda ace Nasan inda zan samo Wasu Daga Cikin yanmatan Dayayi Hulda Dasu Har dasu zamu Saka Cikin plan din mu sai dai Kash..Bai yarda yayi Hulda da Ira iranmu bane Shiyasa Daya gane baida wayau..' Dina ta Saki Numfashi Tana Fadin"Na samu Natsuwa yanzu..Yaushe plan dinmu zai Tabbata kuma Wa zamu Fara. Tunkara.? Zakiya tace"Karki Damu...Komai na Tsarashi Daki Daki zan zo Gidanki Da Daddare akwai aikin da zan sakaki kiyi mana Shima yana Daga Cikin plan dinmu...Ni na Wuce sai nazo.."Da kai Dina ta amsa Kafin Tace"Shikenan sai mun Hadu.'Juyawa kawai Zakiya tayi ta Fice Daga Office din Tana wani Takun Daya Bayan Daya Dina ta Bita da kallon Tabbatar da mganarta. Bangaran Su Zain kuwa Duka nan suka wuni Cikin asibitin sai Dare kana suka Watse Hajiya Mama aka bari da Haddir zasu kwana da Alhaji Tsoho,Inna Hamnatu da Inna Rukayyah da su Baban Kaduna da Matansu Gidan Alhaji Tsoho suka yada Zango Daman nan suke sauka Iyalan Abba kuma suka Wuce Gida Zaina kuma da Zain suka ce Gidansu sai da safe kana suka Dawo yau ma Zaina ta Dafo Abinci Farar Shinkafa da Miyar Ganye mai Kifi,da aranar Alhaji Tsoho ya matsa zai koma gida Dakyar su Abba suka Lallabashi ya kara kwana Tun Safe kuma yace sai Gida Dole aka bashi Sallama suka Tattara Zuwa Gida Tunda yaji Sauki Muran ma Tayi Sauki Ta Sakeshi. Washegari Kuma Inna Rukayyah Ta koma ita da Zafeera Inna Hannatu dai sai da ta kara kwana ta Jira Megidanta yazo ya Duba Jikin Alhaji Tsoho suka koma Tare nan dai suka bar Maryama Gidan Abba Tunda Sa"anin suke da Zainab itama sai wannan Shekarar zata Shiga Jami"a suma su Baban kaduna Duk Aranar suka koma Gidajensu su da iyalansu ganin Jikin na Alhaji Tsoho yaji Sauki kuma ga Zain da Haddir suna Kokaron Kula dashi Shi da kanshi ma yace Kowannensu ya Dauki Iyalansa ya koma Bakin aikinsa Shi ya samu Lafiya da wannan suka samu Natsuwan Tafiya su ma Su Nene sai Ranar suka samu Natsuwa agida. ******** *Bayan wata Biyu..* Bayan Wata Biyu da kwanaki Tuni Zaina sun Dade da Komawa makaranta sun Fara karatu ba kama Hannun yaro Tunda yanzu Suna aji Biyu ne,Zafeera ma Tana kano Tana Cigaba da Karatunta sai dai suna Waya Lokaci bayan Lokaci da Zainar. Bangaran Dina da Zain kuwa Tana iya bakin Kokarinta Wajen bata ga wani Baraka ya Shiga Tsakaninsu ba,Duk domin don plan dinsu ya Tabbata ammh Har Zuwa wannan Lokacin Shuru ba wani Bayani mai Karfi Zakiya Ta kagara kullum Cikin Zuwa Take ko Kiran Waya Tana Tambayan Dina bataji Wani Chanji Daga jikinta ba Tace Mata ita dai bataji Komai ba Har ta Fara Tunanin ko Zain yana amfani da wani matakin kare kai ne Daga barayinsa Ita Dina Tace bata sani ba ammh kusan kullum Suna Tare da Juna ya cita ya kuma Koma yaci Matarsa kamar wani Bunsuru. Har zakiya ta Fara sarewa da al"amarin ta Fara Tunanin nemo Wata Hanyar ita Aranta Take Tunanin kila Zain yana amfani da wani Abu agabansa na Tsikan Sparm kafin ya Shiga Mahaifar Dina ya Lalace,Ta riga ta gama Sanyi da Al"amarin ta kuma Fara Nema musu Wata Hanyar ganin wannan Taki Bullewa har yanzu. Yau din Dina ce takai Ziyara gidan  Zakiya suna zaune Suna cin Abinci A Saman Cafet din Dake Falon zakiya Indomie ne da kwai suke ci,ita Zakiya Dafa nata tayi Na Dina kuma Ta Soya mata sanin bata son Cin Dafaffen kwai Ammh Abunda yafi bata mamaki ganin yau Dinar tace bata ma son warin Soyayyah Dafaffen taci Ta barma Zakiya taci Soyayyah,Ita dai Zakiya sai kallon Dina Take Tunda Ga samam kanta Har zuwa kafarta ammh bata ga wani Chanji ba sai ta watsar da Lamarin kawai suka gama cin Abinci suka koma samam kujera suna Cigaba da Hiransu Ranar ma Gidan Zakiya Dina ta kwana sai da Safe ta koma Gidanta. Sakamakon yadda aiki yayi ma Zakiyar Yawa a office sai Suka kwana Biyu basu Hadu da Dinar ba,Sai da suka kwana Wajen Biyar kana Dina ta Kira zakiya Da wajen Misalin 3pm na Rana tace Tazo ta sameta agida tun Jiya bataje ko"ina bata jin Dadi Da Zakiya Taji Haka bata kawo komai ba Tana Tashi Daga Wajen aiki Ta wuce gidan Dina,Kwance Ta ganta Cikin Bargo Lokacin da suka Hada ido sai da ta zaro ido ganin yadda Dinan tayi wani Fari kamar mai Hadawa da mai jikinta Duk ya Saki da Sauri zakiya ta yarda Jaka da Takalmi ta Hau kan gadon ta Cicccibo Dina Tana Fadin"Dina lafiyanki kuwa..? Kinga yadda kika Dawo..?. Take Fada Lokaci Daya Tana yaye mata Bargon Data Rufu dashi Daga ita sai Rigar Barci Haka take kare ma Jikinta kallo kafin ta Fizgi Tafin Hannun Dinar tana kallo Cikin Zaro Ido Zakiya tace"Dina yaushe kika ga period Dinki Last..? Yamutsa Fuska Dina Tayi Tana Fadin"Kinji ki da wata mgana Sau nawa zaki Tambayeni na gayamiki dis Month ne kadai ban yi ba ammh Last 2 month da suka wuce Duk nayi..! Kura mata ido Zakiya Tayi kamar mai son gano Wani Abu kafin Tace"Meke Damunki..?Dina ta wani Dafe kai kafin tace"Kaina ne ke Ciwo..Tun Jiya da Zazzabi na kwana ga Kasala da Dacin Baki komai naci bayamin Dadi.."Cikin Farinciki Zakiya Tace"Zain yazo Gidanan ne... ? Dina Tace"Yazo jiya..Wlh wani Abu yabani mamaki sam naji bana Sha"awar Sex Dakyar na bashi Hadin kai Bayan mungama Haka na Shiga bayi ina ta kwarara amai kamar zan amayar da ya"yan Hanji.."Bata bari Dina ta karisa ba Ta Fada Jikinta ta Rumgumeta Tana Fadin"Allah nagode maka our plan Was Sussefully Dina..! Cikin mamaki Dina Tace"Bangane ba..? Sakinta Zakiya Tayi ta Mike Da sauko Daga kan gadon Tana Fadin"Tashi zakiyi zama bai ganmu ba...Ina zargin Kina da Ciki Dina.."Ido Dina ta Waro Cikin Farinciki Tana Fadin"Da gaske Ina da Ciki Zakiya..? Tafada Cikin Sigar Tambaya Kai Zakiya ta Gyada mata Tana Fadin"Haka nake Fata kuma nake Zargin ya kasnce.."Aikuwa da Sauri Dina ta Diro Daga kan gado Suka Rumgume juna Suna Murna Kafin su saki Juna Zakiya tace"Tashi ki Rarrafa Ki Shiga wanka sanyi Jiiki ba namu bane..Zamu Shiga plan B din mu.."Dina najin Haka ta Daka Tsalle Tana Fadin"Yanzu kuwa.." Da gudu Ta Fada tiolet zakiya ta Bita da Dariya Ita ta Fito da kayan da zata saka a gurguje Dina tayi wankan ta Fito Ta Shirya Suka Fita amotar zakiyar basu zarce ko"ina ba sai wani Private Hop,baban Likitan Dake asibitin Saurayin Zakiya ne sunyi Soyayah Holewarsu Daga Baya Ta Rabu Dashi Shi kuma har yau har gobe yana Binta da nacin in ta yarda zai Aureta ya Killaceta ita kuma tace ba yanzu zatyi Aure ba Bata gama Bariki ba Shi kuma har yanzu bai Hakura ba acewarta In Tagama Barikinta Saurayi Uztas zata samu Tayi Wuf Dashi ba irinshi Da Suka Hadu a Bariki ba. Yana ganinsu ya Fara Rawan Jiki nan da nan Zakiya ta gayamai Abunda ke Tafe Dasu,Shi kuma ya kira wata Nurse Daga Lab tazo Ta Dibi Jinin Dina yace ta kaishi Lap yanzu yake son sakamakon Da Hanzari ta wuce Cikin Sassarfa Ita ko Dina sai Bin Zakiya Take da kallo Domin bata mata wani Bayanin Dalilin Zuwansu wannan asibitin ba Tana chan Suna Hira da Likitan Dagajin yadda suke mgana zaka Fahimci anyi kyakyawan zama tare. Shudewar Mintina Arba"in kana aka kawo sakamakon Sai da ya Bude ya Duba ya gani kana ya Mikama zakiya yana Fadin"Kawar naki tayi Aure ne..? Yafada yana Nuna Dina Fuska Zakiya Ta Hade kai Tsaye tace"Ina Ruwanka..? Mallam bamu Sakamako muna kan Hanya ne.."Dariya yayi kafin ya Mika mata yana Fadin"Congarulation Kawarki Tana Dauke da 5weeks and 2dys Pregant...! Wani Farinciki ya Cika Zukatan Zakiya da Dina wanda sai da suka Rumgume Juna Cikin mamaki yake Binsu da kallo Sai yayi Tunanin kila tayi Aure ne ba kamar yadda yake Zargi Da Farko ba,Sai da suka gama Murnan kana Dina ta Juya Tana kallonsa Tace"Dacta Last Month fa nayi Mesis wannan Watan ne kadai ban yi ba Hakan ba matsala bane.? Yana yar Dariya yace"Likita Tana Tambayan Likita game da Abunda ta sani ko Duk Murnan ne..?karki damu Normal ne Mata Wasu Daga Ciki kuna Haka kila ki Dakata daga haka kila kuma Bayan kowani Wata Daya ki Rika ganinsa yadai Danganta Daga yanayinki ne.."Zakiya ta ja Jakarta Lokaci Daya da Hannun Dina Tana Fadin"Docta sai munyi mgana.." Daga Haka suka Fice Daga Office din Zakiya Dauke da Resuilt Din Cikin na Dina,Basu samu mgana ba sai da suka Shiga Mota Zakiya ta Ja suka Fice Daga asibitin Sai da suka Daidaita Tukin Bisa kwalta kana Dina ta waigo Tana kallon Zakiya Tana Fadin"Yanzu ina muka Nufa..? Hankalin Zakiya na wajen Tuki Tace"Saulawa Specialist Hop..."Ido Dina ta waro Tana Fadin"Bangane ba..? Wajen Zain zamu je..? Kai ta Girgiza mata kafin Tace"Ba yanzu ba...Wajen Saurayin naki zamu wama yake da Suna..? Wannan Bunsurun matan nake Nufi..? Cikin mamaki Dina tace"Wai Dr Imran kike Nufi..? Da Sauri Zakiya tace"Yauwa Shi nake Nufi.."Dina tace"Bangane ba..Miye Aikin Dr Imran awannan Plan din namu kuma.."? Zakiya tace"Bashi da wani amfani sai waje  Daya....Zamu je ne kan Baki da lafiya zaki ce ya Dauki Jininki a gwada ki kina Tunanin Maleria na Damunki.... Kinga In Sakamako ya Fito Irin na Dr.Yusuf ne,munhada Sakamako Biyu kenan Daga Mabambamta Asibitoci Ciki Harda Asibitin Dayake mallakinsu Koda zasu karyata Dr Imran zai iya zama Shadarmu.."Kai kawai Dina take gyadawa kafin tace"Daganan kuma sai yaya..,? Zakiya ta Bushe da Dariya ta saki Sitiyarin Motarta Tana Fadin"Daganan sai Ki kira Zain ki Gayamai kina Dauke da Cikinsa..! Dina tace"Sai kuma..!Zakiya tace"Daganan sai na Daukeki na kai ki Kano Sabuwar kofa.." Gaban Dina ya Fadi ta kwalalo Ido Tana Fadin"Gidanmu kuma... ? Tafada Da Sigar Tambaya Zakiya ta gyda kai Tana Fadin"Eh insha Allahu..! Dina Ta Dafe kai Tana Fadin"Miye manufar hakan..? Zakiya tana Zuba Hon abakin get din Asibitin Saulawa Ta Dago Tana kallon Dina lokaci Daya Tana Fadin"Manufa Shine Zan kai ki nace baki da lafiya..In Hajiya Batula ta Kirashi Ta gayamai Abunda ke Faru nasan zai ce akira Family Doctor dinku ya Dubaki..." Dina Tace"Kin kasheni Zakiya zai Fada musu ina da ciki fa..? Zakiya tace"Plan C din mu zai Fara Daga Lokacin.." Dina tace"Wani irin plan c kuma..ya zanyi in Daddy yaji Labarin ina da Ciki Zakiya..? Zakiya na Faka Motarta a parking space Tace"Zai ji ba Dadi mana Dina ai Duk Uba na kwarai ba zai so Gurbacewar Yarsa ba balle keda yake matukar so..Matakin da kowani Uba zai Dauka Shi zai Dauka Dina karki Damu..! Dina na Sakin Numfashi Sama sama Tace"Nidai Don Allah ki Fitar dani Duhu Zakiya Wani irin mataki zai Dauka..? Hakan yana da alaqa da Cikar Burina ne..? Zakiya tayi wani Mirmishin Kin Cika matsala afili sai ta Furta"Naso ki bari mu bi komai Daki Daki ne ammh Tunda kin matsa Shikenan..Matakin da zai Dauka Shine Zai Fara Tambayanki wayayi miki ciki..? Ke kuma sai ki Bashi amsa da ZAINULLAHI USMAN ABUBAKAR SAULAWA,Ki kara da cemai ya Ribace ya yaudareki da kalmar zai Aureki ya Lalatamiki Rayuwa Tun kuna London Yanzu kuma Daga karshe ya Nuna bazai Taba Auranki ba.." Dina ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Naji sai kuma yaya..? Ta ina zamu Fara tunkarar Ahalin Zain..? Zakiya tace"Daddy da kansa zai Dauko ki ya kawoki har garin Bauchi A gaban Iyayen Zain zai Zayyane musu Dan"su yayi ma yarsa Ciki kuma bazai yarda ba yana Neman Hakkin Yarsa.." Dina ta Saki baki kafin tace"Kai...! Zakiya ta Bude Murfin Mota Tana Fadin"Naki wasa ne..Komai na Shiryamai..Kinga Haka na Faruwa plan D zai Fara aiki..Yayinda Duka Zuru"arsu zasu Tattaru waje Daya Domin Yima Abun Tufkan Hanci.."ta fada Tana Dariya Jinjina kai kawai Dina keyi itama ta Bude Murfin Mota Ta Fito Tana Fadin"Burina fa Yaushe zai cika..? Zakiya tace"Acikin plan D zai cika..Domim Daddy zai ce bai yarda ba..Zai kai kara Kotu Su kuma iyayensa zasu nemi Sulhu..Daganan kuma Za"a ce Dole zain sai ya Aureki Saboda Rufuwar Abun kar ya Hadu a Duniya..Ammh Shi kanshi Daddy Barazana zai yi musu Domin Shima ba zai so Wannan labarin ya Fita ba ko Domin Siyasarsa...! Hannu kaawai Dina ta bama Zakiya suka Tafa Lokaci Daya Tana Fadin"Aikin ki na kyau Tawan..! Jinjina Zakiya tayi ma Dina kawai kafin su Fara Takawa atare zuwa Cikin asibitin Zakiya na kara Gayamata Yadda Tsarin Plan dinsu zai Tafi har zuwa matakin Nasara. *Ina Godiya da Sharhin ku kan wannan Labarin Keep it up...* *Shakira...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*              1️⃣4️⃣ "Shigarsu asibitin basu Hadu da kowa ba sai Dr.Aisha da Dr.Peter suma din sama sama suka gaisa Dr.Aisha ce ma ke Tambayarta Lafiya Jiya bata Shigo Asibiti ba yau ma Haka Fuska a Tamke tace mata bata Jin Dadi ne sannu kawai Tayi mata sukayi sallama su suka Wuce Office din Dr Imran ita kuma ta Wuce Femele Word Kila zata yi Dubawar yammah ne. Dr.Imran na Tsaye acikin Office Dinsa ya gama Abubuwan Dayake Shirin Tashi ma yake,sai ga Dina da Zakiya sun Shigo mamaki ya Kamashi Da ganinsu ,Ya Riga yasan Wacece Zakiya awajen Dina Tunda kamar yadda Kowa ya san Dina a Ma"aikatan Da Zakiya take aiki Haka zalika kowa yasan Zakiya kawar Dina ce Acikin Asibitin. Bai iya cewa komai ba har suka samu Waje suka zauna Zakiya ce Ta kalli Dina itama ta kalleta sai ta kada mata kai,Ganin haka yasa Ta Juya Ta kalli Dr.Imran wanda ya sakar mata Bunsuran Idanuwansa Cikin Wani kallon Bariki da kwarewa Cikin Basarwa tace"ah..Zauna mana..?Ko baka Maraba da zuwan namu ne..? Cikin yake ya zauna yana

Chapter 14 of 32