Zaina ido kafin Ta Daga baki ta Kirata Ta Juyo tazo Tana zuwa ta kara kallonta kafin tace mata Ki dinga cin Abinci kinji ko Sa"adiya Da Toh ta amsa kafin Tace Tatashi Taje Tana Tashi Mom Iklima Ta kalli Umma Tana Fadin"hmm wai ke Hajiyar Allah da kike kokarin Raba wannan Auran ina zaki kai Cikin Jikin Sa"adiya..?
Gabadaya Falon sai ya koma kan Mom Iklima Cikin mamaki Umma ke Fadin"Ciki kuma..?ke Uwar Amin wata Sa"adiyan ce ke da Ciki Zaina..? Mom iklima tayi Mirmishi Tana Fadin"Toh da wace Sadiya garemu..Ita fa Wlh Ciki gareta.."Ido Umma da Nene suka kwalalo Umma Cikin Wani yanayi tace"Wai wani irin Ciki..? Badai na Haihuwa kike Nufi ba..?
Mom iklima Tace"Shima fa gareta..Kina ina baki gane ba..? Yayi Wata uku in ma bai fi ba Wlh.."Nene ta washe baki Tana Fadin"Alhamdulillah.."
Umma kuwa Tagumi Tayi Tana Fadin"Wlh bansani ba...Ban taba lura ba..Mau ciki da Rama kalleta fa ki gani.."Mama Safiya Tace"Nima Wlh mgana ne kadai Banyi ba ammh Tun Lokacin da Naganta Sai dai naga alamun Ciki Tare da ita.."
Mom iklima Tace"Ai Indai Kasan alamun Ciki kana ganin Sa"adiya kaga mai Shigar Dan Ciki ajikinta.."Umma Ta saki Numfashi Tana Fadin"Wlh ban taba Lura ba..Naga sai Uban Rama Take,ammh Nima alamomin cikin sai yanzu na Fahimta Domin Kwana Take kwanaki cikin zazzabi,Ga Amai komai taci sai ta dawo Dashi Ni ban kawo komai ba Tunanin kila Saboda Damuwa ne.."
Mama Safiya Tace"ai mata kala kala ne...Wata Zaki ga Ciki ya Sakata kiba Tundaga Farkon Laulayi wata kuma Daga Farkon zata Rame sosai sai Cikin ya Girma sai ta Murmure.."Nene Ta Daga Hannu Sama Tana Fadin"Alhamdulillah..Sai aba ma yaro na Matarsa yanzu.."
Umma Ta Sauke kai kawai Tana Fadin"Umh...kawai batare da ta kara mgana ba Su Mama safiya suka Cigaba da Tattauna mganar suna gayama Umma Tayi Hakuri kawai ta maida Zaina Dakinta Abunda ya Faru ya Riga ya Faru Mama Safiya tace"Nifa addu"ata Allah sa in Yarinyar chan tatashi Haihuwa Ma yaron ya mutu tun aciki kowa ya Huta.."Duka suka ce Ameen Wlh Umma dai na Jinsu bata kara mgana ba ta Shiga Kogin Tunani.
Dakyar Zaina Ta iya karisawa Dakin Hajiya Mama saboda Fargaba da kuma Tsoro a kunnanta Taji mganar Mom iklima Da mganganun su Umma Labe ba Dabi"arta bane ammh Jin Abunda Mom iklima Tace ne yasa Gabanta ya yanke ya Fadi Shikenan Abunda Take Boyewa ya Bayyana Shikenan Umma zata Rabata da Firstlove Lokaci Daya Kuma Ta Rabata da Abunda ke Cikinta Wasu Hawaye suka Zubomata Lokaci Daya Tana Dafe Cikinta Saurin Goge Hawayenta Tayi Ganin Zafeera Ta Fito Tana nemanta Tayi kokarin Shiga Cikin su Ta nuna komai ba komai bane ammh Cikin Ranta cike da Fargaba da kuma Tunanin Taya ya zata Tseratar da Cikin Jikinta Domin Tana Sonshi Tana ma jin aduniyar nan Shine Kadai Wani makusacinta.
Umma ma abangaranta Haka Abun yazo mata Shiyasa anayin isha"i Ta kira zaina tace su zo su Tafi Gida sai tace dasu Zafeera zata Dawo Umma Tace ta wuce su Tafi Tun a Mota Take Sharan Hawaye Domin tasan kwanan Zencen ai kuwa suna Zuwa Gida Umma ta Tusata Daki ta Tsareta da Tambayan da gaske ne Tana da Ciki..?
Tsoro ya kamata Ta Fara kuka Taki mgana Umma Ta kalleta Tana Fadin"Kukan ki ya Tabbatar min kin san dashi ammh Baki sanar dani bako..? Dalili kenan kika Hana muje asibiti ko kada ace kina da ciki naji ko..?
Da Sauri Zaina tace"Ban sani ba Umma..Ban sani ba.."Take Fada Tana kuka Umma Ta girgiza kai Tana Fadin"Miye na kuka kuma Halima..! Nifa yakin so kanki nake miki Wlh..? shi Zain din ya sanda kina da Ciki..?
Saurin Girgiza kai Tayi alamun A"a Umma Ta kada kai Tana Fadin'"Karki sake ki sanar dashi..Domin wannan cikin bazai sakani na Fasa Abunda nayi Niyyah ba Dole ya Sakeki..Cikin ma Zubar dashi zanyi.."
Umma Ta Fada Daga karshe Cikin Gatse ganin yadda Zaina ke kuka aikuwa kalmar Umma Ta karshe Ta saka Zuciyar Zaina Tayu wani Rugurugu,Da Sauri Ta Dago Tana kallon Umma Cikin Firgici da Tsoro Cikin Hararanta Umma tace"Eh haka nace..Ki bar kallona da wadanan Idanuwan naki kafin Ranki ya baci.."Dole Zaina ta maida kanta kasa Tana Danne kukanta Ranar kwana Tayi kuka Umma na jinta Tayi mata Banza Tana ganin ikon Allah Ya zama Dole ta Yi Kaffaran Rantsuwanta ta maida halima Gidanta kafin Watarana ta maida kanta Ji Daga mata gatsen Zubba da Ciki Ta kwana tana kuka,Su Zafeera basu dawo ba Chan suka kwana sai da Safe suka zo sukayi wanka,Umma Tun Safe suka koma Gidan Alhaji Tsoho,Zaina kuna sai da Zafeera ta matsa mata kana ta koma Ammh kowa ya ganta yaga Ta Rage Walwala kamar baya,Zafeera Tayi Tambayan Duniyanan Taki mata mgana Gabadaya Tagama Rudewa Tana Son Firstlove Tasana san Cikinta Bata za iya Juran Rasa Ko Daya ba Aranar har yanke Hukuncin Neman Zain Tayi ta gayamai komai ta Fito Haraban Gidan ko Zata ganshi bata Ganshi ba Ranar asibiti ma ya wuni bayan an tashi ya Tafi Gida ba Saboda baya son ganin Matarsa ba sai sanin Halin Umma Ga kuma Mutane sun Cika Gidan ammh ya Guduri Niyye Ranar Daurin Aure Sai ya saceta sun gudu wani waje sunyi sati basu nam kila Daganan Umma zata bashi Matarsa.
Washegari Jumma"a Aka Tashi Da Shirin Walima Baki kuma Duk sun gama isowa Baban kaduna ma Tuni ya iso,Basu da mataalan Wajen kwana Boysquaters suka Tare Dayake Yana gyarashi Lokaci bayan Lokaci Suma Ango da Abokansa sun sauka ammh Otel suka kama su.
Da yammah akayi Walima Wata malama aka kira anan Haraban Gidan tayi wa"azi kan Aure akaci aka Sha aka kuma yi Rabon Abubuwa Domin Zuwan Daddyn Abuja yasa mota Biyu tazo Ta Sauke Ruwan Gora da kuma Drinks kala kala Da komai na Bukata Bangaran Abinci Daman Oda akayi sai dai aka kawo shi adafe wannan aikin Abba ne shi ya Dauki Nauyin komai.
An Tashi Walima Kenan Sai ga Goggo Halima Ta iso Da matar Danta Isuhu,Zuciyar Zaina Ta kara Raunana ganin Goggo Halima Haka ta Rungumeta ta Fashe mata da kuka Dagota Tana Fadin"Ke kuma haka ake murnan sai kuka..?
Umma Dake gefe Sai Jikinta Yayi sanyi Hajiya mama ce Tace"Uwa mai Dadi tayi kewarki ne Hali Dubu.."Goggo Halima ta saka Dariya Tana Fadin"Haba dai Hajiya Mama mai uwa Irin Umman Zareena da Nene wani kewa zai yi kuma..? Ga salihin Miji Irin Zainullahi Wlh Sa"adiya bata da wata mtsala sai Godiyar Allah.."
Su Mama Safiya Da yan"uwanta da su Mom iklima suka ce"Hakane kam...Shagwaba ce kawai. "goggo Halima ta Tureta Tana Fadin"Ja chan..Banason Sarkaci Tafi wajen uwar taki kiyi Tabaran ita data Daure miki Gindi.."Umma ta Jawo Zaina Jikinta Tana Fadin"Taho nan Diyata...Ga inda ya Dace kiyi Shagwabar ki nan Bar Goggo Halima taji da Tsufanta.."Gabadaya aka saka Dariya ammh banda Zaina wacce ke Tunanin Abunda zai Faru gaba.
Nan Su Zafeera suka bar Duka iyayen yan matan kuma Harda Hamdiya da kawayenta wajen su Takwas suka Tafi Gidan Abba su kwana Sai gobe su dawo Tunda Gidan Alhaji Tsohon ya Cika da baki Goggo Halima chan suka barta Cikin su Umma sai kwamawa suke da Hajiya Mama daman abokiyar yinta ce.
Da suka koma Gida ba wanda ya Damu da Dina sai Zainab Data Shiga Wajenta Tunda Nene ta Roketa Ta Shiga ta Dubata,Tana Shiga sai da ta saka Ta Dafa mata kwai wai shi zata ci Ta isketa Zaune kan gado Tana kallo Cikin System dinta Harda cewa su rage Hayaniya Saboda Bata son Damuwa Dayake su kadai ne agidan Abba ma yana Gidan Alhaji Tsoho wajen yan"uwansa Harda Alhaji Tsoho wanda Shima yayi kaura Daga Cikin Gidan Saboda mata Zuwa nan Boysquaters.
Dakin Umma Su Zafeera suke Hamdiya kuma da gayyarta suna Dakin Nene Zaina sai da ta bari duk sun yi wanka sun yi Shirin kwanciya kana ta Zare Jiki ta Shiga Tiolet din,chan ta samu Damar yin kukanta ya Isheta da kuma Tunanin mafita Ta Dade kafin Ta yanke Shawara da kuma Hukunci Duk da Abun Da zata aikata bazai ma kowa Dadi ba ammh Shine mafitan Cikinta da kuma Auranta Uwa uba ta Gujema ganin Auran Firstlove dinta da Wata mace irin Dina...!
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
2️⃣9️⃣
Sai da Ta Tabbatar da kowa yayi Barci kana tayi wanka ta Dauro alwala Ta Fito Daga cikin Bayin Sadaf Sadaf ta iske su Zafeera sun kwanta Duk sunyi Barci Alamun gajiya nan Taga Hamdiya Amarya Itama Ta baro chan Dakin tazo ne ta kwanta Saman Cafet barci ya kwasheta Saboda Gajiya.
A hankali Ta Dauki Hijabinta Ta Zura Bayan Tunda a Tiolet din Ta maido Doguwar Rigar Abayan Dake Jikinta,Ta shinfida Darduma Ta Tada sallah Bayan Ta Idar ta Dade Tana addu"a Lokaci Daya Taji Natsuwa ya sameta,na game da Abunda Take Shirin aikatawa,Batare da wani Dogon Tunani ba Ta Mike Tanayin komai ahankali Saboda Kar Zirga Zirganta ya Tada Wata Daga Cikinsu.
Side Drower din Umma Ta Bude ta Dauko Littafi da Biron Umma wanda Take Rubuta wasu Abubuwa Gudun mantuwa Komawa Tayi saman kujeran Dake kallon Kofa ta zauna ta Yagi Takardan Ta Dora saman Littafin kana Ta aza Biron zata Fara Rubutu sai kuma Wani Sanyi Jiki da kasala da kuma Tunanin anya Abunda zata aikata Daidaine..? In tayi hakan Tayi ma Umma adalci.? Ko Tayi ma Iyalan Alhaji Tsoho Adalci Wadanda suka Fifitata Fiye da ya"yansu..? Toh ammh in fa Tana Son Cikin Jikinta da kuma Igiyar Auranta Dole sai Tayi haka Bata damu koma me zai Faru ba Ta Tabbata Watarana zai Wuce kamar bai Faru ba Hawaye Taji ya cika mata kwarmin Idanuwanta Har suna kwaranyowa da Sauri ta saka Hannu Ta Sharce Hawaye Cikin Juriya Ta Aza Hannunta Cikin kwarin Gwiwa ta Fara Rubutun.
Takai wajen Tsawon Mintina Talatin Tana Rubutun Tanayi Tana kuka,tana kuma yi Tana Tsayawa Domin wata zuciyar na sanyayamata Gwiwa ga aikata Abunda Ranta ya Rayamata ammh sai Tayi amfani da Zuciyar Dake Karfafa mata Gwiwan aikata Abunda Tayi Niyyah din har sai Da Ta kamallah Rubutun nata kana ta Ninke Takardam Tatashi Ta kaita Cikin kayan Umma ta sakata acikin Wardrope inda ma Hankalin wani bazai kai ba Umma kuma ta maida mata Littafnta da Bironta Inda ta Dauka Kana ta koma kan kujeran Da tatashi ta kwanta Kawai ba Domin Tana jin barci ba sai Domin bata da wata mafita sai na kwanciya.
Mganganun Dina da kawarta Zakiya nayi ta yi mata amsa kuwwa Gefe Daya ga Kudurin Umma,Abu Daya yafi Firgitata Rabata da Cikinta da Umma zatayi wanda Bata iya Jurewa ba Hannunta na Bisa Cikin Tana Hawaye Cikin Zuciyarta wani kunci ne,Domin Ta sani Dina Ta Rigata Daukan Kwan Haihuwan Firstlove acikin maranta kenan Gaskiya ne Ta Fita matsayi Tun Da gashi Komai ya Bayyana..? Kuka Take ahankali kada wani ya Jita takai wajen Misalin karfe 3pm na Dare bata iya Barci ba Tana Ta kuka Da kuma Tunanin Makomar Rayuwarta da Abunda ke Cikinta In har ta Yanke wannan Hukuncin Datake Shirin yankewa.
Bata san sadda wani Barci mai Nauyi ya kwasheta ba Sai da Taji Zafeera na Tashinta kan cewa Tatashi har an gama sallah Ta mike akasalance Idanuwanta Duk sum Kumbura sai da ta Shiga Tiolet ta Dauro alwala Ta Fito kana Zafeera Ta Luura Da Kumburin Idanuwan Zaina Cikin Mamakinta Take Fadin"Ukti meya Kumbura miki ido Haka..?
Da Sauri Zaina Tace"Bakomai...Idona ne Jiya Da Daddare ya Dinga Ciwo shiyasa..'Cikin Tsausayawa Zafeera Tace"Ayyah..Sorry bari mu Tafi sai asiya mgani ki saka..wlh ya kumbura miki Fuska Sosai kamar wacce Tayi kuka.."Yake kawai Zaina Tayi ammh acikin Ranta Tana Fadin ai kukan ne ma.
Bayan sun Idar da Sallah Zainab da Zafeera Suka Tafi Kitchen Neman Abun karyawa Dayake su Umma Duk chan suka kwana Harda Abba su kadai ne agidan Daman chan nan Zaasu zauna sai ana Gabda Daurin Aure zasu koma Chan Gidan Alhaji Tsohon Tunda ana Daura Auran zasu Tafi da Amarya kaduna.
Bayan sun gama Hada Breakfast
Din Zafeera ta Mika ma kawayen Hamdiya nasu ta kuma Dauki nasu zuwa Dakin Umma Zainab ce ta Dauki na Dina ta Shigar mata dashi Ko Da ta Shiga Tana Cikin Bargo Tana Barci Ijiye mata kawai Tayi ta Fice Dinar ma bata sani ba Ta koma Daki suka karya dasu Zafeera,Hamdiya kuma ta koma Wajen Kawayenta suka karya Tare kana Suka Fara wanka Suna Shiryawa.
Basu yi anko ba Kowa kayansa zai saka Zafeera da Zaina da Zainab Umma Tayi musu Atamfa Da Leshi Tun Shekaranjiya aka anso Daga Wajen Dinki ko Zaina dake gidan bata san da Dinkunan da Umma Tayi musu sai da suka Gani Ko kafin zuwa 10am na Safe sun gama Shiryawa Kowa yaci kwalliyansa ya Cakare Hamdiya Daya Daga Cikin kawayenta Tayi mata kwalliya Har Tayi ma Sauran kawayen dasu Zafeera Dama kunshi Da gyaran kai Daga Abuja Tayo Abunta.
Zafeera da Zainab anyi musu makeup dan daidai Ammh zaina Taki yarda ayi mata Dakyar ta tsaya aka Shafa mata Hodo akayi mata Dauri aka kuma saka mata man baki,Dukkansu ukun less Din suka saka mai Ruwan marun,Da Pick sunyi kyau sosai sai dai kayan yafi Cika Zainab da Zafeera Saboda ya kamasu ammh Zaina sai yayi mata Rakwa rakwa saboda Ta Rame kuma Inaga Measurement dinta na Baya Telan nasu yayi amfani Dashi.
An kawo musu Abinci Daga Gidan Alhaji Tsoho Shinkafa Friderice da Alala daman Drinks basu da mtsalanshi akwai agidan,Dukkansu Falo suka Fito Kowacce ta Cakare abunta suna Hira suna Dariya wasu kuma na gefe suna Hotuna irun su Zafeera Duk Rashin Son Kada Zaina Tayi Hoto sai ta matsa mata Zainab Ta Daukesu acikin Ran zaina Tana Tunanin kila wannan Hoton Shine Abunda Ukti zata Dinga kallo Tana Tunawa da ita.
Dina Bayan Tatashi Tayi wanka Ta Shirya Cikin Riga da wando na yan kanti Breakfast din Ta Tea kadai tasha Ta Tureshi Gefe Tashi Tayi ta Bude kofan Tana kallon Abunda ke Faruwa acikin Falon Daya Bayan Daya Take kare musu kallo su basu ma Lura da ita ba,Zaina Take kallo Zainab na Daukansu Hoto Ita Da Zafeera mamaki ya kamata na ganinta ko ajikinta Har da wani kashe Dauri kamar ta Fito Falon sai kuma Ta Fasa Ganin duka yara ne kuma Batason Hayaniya yasa ta Maida Kofarta Ta Rufe ta koma ta kwanta Domin Bata Gajiya Da Barci kamar Cikin Jikin nata Yana yawan sakata Kasala da Barci.
****
Bangaran Zain kuwa ya kwana da Gudurun yau ko ana ha maza ha mata ne sai ya Dauki Firstlove sun yi Nisa da garin Bauchi Bazasu Dawo ba sai Umma ta Sauya Ra"ayinta Tun safe suka Shirya Shida Haddir Tunda Daurin Auran 11am ne saboda angwaye Zasu wuce Da Amarya kaduna.
Dukkansu Shigar Farar Shadda sukayi Harda Babban Riga wanda Daddyn Abuja ne ya Dinga musu anko Dukkansu Harda Shi da Baban kaduna da Abba,Dukkansu kuma Harda Babban Riga sai suka saka Bakar Hula da Bakin Takalmi Booth,da agogon Fata baki na kamfanin Rado Dukkansu sunyi kyau Duk da Zain ya Rame ammh yayi kyau yayi Haske sai da Ramar Jikij kawai Kuma ita ta Shafi Zuciya ne.
Koda 10 tayi na safe suna Gidan Alhaji Tsoho ana ta Shirye Shiryen Daurin Auran da zai Gudana nan da Lokaci kadan Zuwa goma Da Rabi komai ya kamallah Haraban Gidan Alhaji Tsoho an gama Tsara komai an Malale ko"ina da Manyan Cafet sun Kawata Haraban Gidan Dayake Gidan Babba ne ammh Duk da haka wasu Motocin awaje aka Fakasu Musamman ma na Abokan ango da Tawagan yan"uwansa da abokan aikinsa Sojoji,Suma Abba ga nasu gayyar na Mutanensu Hakama Daddyn Abuja da Dangin Mama Safiya Suwa Shima Baban kaduna Daga Barayinsa ko"ina ya Cika da Mutane gaisawa kawai akeyi ana Farinciki In kaga zain bakinsa kamar gonar auduga Saboda yau ya gaida Abba kuma ya amsamai Har sunyi musabaha da juna Zain ya ji Farinciki har sai da yayi kwallah Zuwa Lokacin Da Time din Daurin auran ya kusa sai Alhaji Tsoho Ya Fito ya zauna Bisa Kujeransa Daidai Lokacin kuma su Zaina Motocin da suke je Daukansu suka ijiyesu Daga Wajen Gidan,Kanwar Mama Safiya ita taje tazo da Amarya da kawayenta Haddir ta saka ya kaita Sauran kuma Motocin abokan ango ne.
Da kafa suka Taka zuwa Cikin Gida zaina Kamar ta Harde haka Take ji Sun saka mayafansu pick Zafeera da Zainab sun saka jaka kowannensu ammh Zaina Mayafin akanta ta sakashi Ta Jashi Sama saboda kada aga Fuskarta Daga Kugunta kuma Takardan Data Rubutu ne matse awajen Lokaci Bayan Lokaci Tana kai Hannunta wajen kada Takardan Ta Fadi.
Zain Dake Haraban Gidan yaga Zaina Domin koda Ga Tafiyanta ya ganeta,Sake baki yayi yana kallonta Domin Rabom da ya ganta Cikin kwalliya Tun suna gidansu baki da Hanci ya saki yana kallonta Ita kuwa bata ma gansa ba kanta na kasa Har suka Shige daman Amaryance agaba Anty Gaje rike da ita sai Kawayenta sai su Daga baya Shiyasa har suka Shige ma basu wani Daga gansu ba ganin maza sunyi yawa aharaban Gidan..
Dakin Hajiya Mama suka yada zango su kuma su Zafeera suka Fice gaida su Umma,Umma ta Dinga Kolasu Tana sun yi kyau Kowa yaji Dadin ganin Zaina ahaka Har Hajiya mama sai da tace ko kefa Hali Dubu Mirmishi kadai Tayi mata Diyar wajen Anty Zareena ta karba Tana Jijjigatamata Ganin Tana kuka ita kuma Tana Shiryawa ne,Kowa ya ganta sai yayi mgana Ita Goggo Halima bata Fahimci komai ba Tunda ba wanda ya gayamata ammh Dai ta Fahimci Halimar ta Rame sosai kamar wacce Tayi Cuta Ammh dai Ta bar ma Ranta da kila Cikin ne ya sakata Rama Domin Taga Shigar Ciki awajen Halimar Taso Ta Tambayeta Zain Sai kuma Tayi Tunanin kila zai shigo bayan Angama Daurin Aure.
Karfe 11:10am aka Daura Auran Hamdiya Aliyu Abubakar Bashir Saulawa da Angonta Hafeez Muhammad Ikra,Daurin Auran da Shedu suka Tabbatar Dashi,Wan Baban Ango Shine Waliyin Hafeez Shi kuma Baban Kaduna ya zama Waliyin Amarya Masha Allahu su Alhaji Tsoho Suna Daga Cikin wadanda suka Shaida Daurin Auran ya samu Hallartan Manyan Mutane kama Daga Lauyoyi masu zaman kansu Abokan aikin Dadyn Abuja Da Tsoffofin abokan Alhaji Tsoho Da ya"yansu wasu Tsoffin Likitoci wasu kuma sun Taka wani mukami agwammati,Sai Abokan aikin Abba Dana Baban Kaduna Dangin Mama Safiya da wasu Daga katsina,Abokan Angon Shi kanshi Da kuma Tawagar Iyayensa da Yan"uwansa,Zuwa abokan aikin su Zain da kuma Makota Da abokan arzuka Hardasu Dr.Imran da kuma Dr.peter Sun Hallaci Daurin Auran Bayan an Gudanar da Daurin auran aka Fara Fito da abinci da Lemuka ana ta Rabawa kowa yana zaune kan Cafet yana cin Abinsa da Naman kaza ga Ruwansa agefe ana Korawa da Lemu Haraban Gidan Alhaji Tsoho kamar wani Restaurant Haka ya koma.
Daga cikin Gida Kuma ana Ta Shiryen Shiryen Tafiya da Amarya Nasihu Dama Tuni iyayenta sun mata su Umma dai ke karawa Da Hajiya Mama Alhaji Tsoho Daman Tun Daran Da suka iso yayi Mata nata Sosai,Kuka kawai Hamdiya Take ganin Da gaske Tafiya da ita fa Za'ayi Adaidai Lokacin kuma Zaina ta mika ma Zareena Yarta Ta koma Dakin Hajiya Mama Jakar Zafeera na Hannunta Ta bata ajiya Suna Chan Dakin Alhaji Tsoho suna Hadama Hamdiya kayanta.
Ba kowa adakin sanda ta Shigo Duk suna Falo ana Tsaye Masu Shirin Tafiya masu Rakiya ma na Tsaye Baban kaduna da Abba Sun Shigo Har gida suna Fadan su Shirya 12 suka ce zasu Mika Hajiya mama Ta Tsara masu Tafiya Kaduna Tace Umma zata Tafi da Mom lklima da Inna Hannatu da Inna Rukayyah sai Dangin Mama Safiya kanwarta Da Diyar wan babansu Sai Ya"yan yan"uwansu yan mata Daga Barayin nan kuma Hajiya Mama tace Zafeera da Zainab da Shema da maryama duk zasu Tafi Asma"u ma da Zareena suma Duk Dasu za"a je Hajiya mama tace Goggo Halima ma Da matar Danta zasu Tafi Da Farko tace bazata ba Hajiya mama tace sai Taje Umma na jin da ita za"a Tafi Ta kuduri Niyya da Zaina zata Tafi Sai ta Fara Nemanta ammh bata ganta ba Zafeera tace kila tana Dakin Hajiya Mama Umma Ta taka Kafa zata Bita Hajiya Mama ta kirata kan da ita da Mom Iklima da kanwar Mama Safiya zasu kai Hamdiya Tayi sallama da Alhaji Tsoho da kuma Iyayenta wannan Dalilin yasa Bata koma Dakin ba suka Dunguma zuwa Haraban Gidan Kaya kuma Tuni wasu an Fara sakawa cikin Mota kuma Daman an je Tuni anyi jere chan kaduna wannan aikin Mom iklima ce.
Zaina sai da Ta Tabbatar duk sun Ragu afalon kana Ta Tashi Daga Kofar Dakin Hajiya Mama inda Ta Labe Jakar Zafeera ta Bude Ta Taga kudi 3k sai ta Dauki 2k ta bar mata Sauran Lokaci Daya kuma ta saka Takardan Data Makale a kugunta Cikin Jakar Ta ijiye mata nan Gefen gadon Ta warware Daurin kanta Ta Rike kallabin Ahannunta Ta saka mayafinta Ta Yane kanta Ta zazzagoshi yarda bamai ganeta kuka Take kuka mai Cinrai hawayenta na Zuba Tana Sharewa Sikat din yadan mata yawa sai Tajashi sama Sai da ta Leka Daga Falon Taga duk ba wanda ya santa yawancin Dangib Mama Safiya ce Sadaf Sadaf Ta Fito Tana waige zata Fice Daga Falon Taji Muryan Hajiya Mama Da ta Fito Daga Dakin Alhaji Tsoho Tana Fadin"Ke waye nan zai Fita..?
Dam!gaban Zaina ya Fadi tayi Saurin Share hawayenta kana ta Juyo Tana Fadin"Nice Hajiya mama..Zani waje naga Tafiya Amarya ne muyi sallama.."Hajiya Mama Da taci wani Ubansu Leshi Ta kariso Tana Fadin"Au Halima ce..? Eh gwara haka Kinga ke bai kamata ki Tafi ba gwara ki zauna in Uwar taki sun kaita sun Dawo sai ansan yadda za"ayi ki koma Gidan Mijinki.."
Cikin Sanyin Murya Zaina Tace"Toh Hajiya Ma..ma.."Ta Fada Muryanta na rawa ganin haka yasa ta Dafa kanta tana Fadin"Karki damu kinji ko..Ga Nene ai ba da ita za"a Tafi ba saboda kada abar gidan ba kowa ga Amanar yarinyar nan a Hannunsu Kiyi hakuri gobe zasu Dawo Dukkansu.."Tafada Cikin Sigar lallashi tana ganin kamar zaina ta Damu ne za"a Barta ita kadai Saurin kwakwalo Mirmishi Tayi kafin tace"Bari naje muyi sallama.."Hajiya Mama tace"Hanzarta.."Ko gama Rufe baki bata yi ba ta Fice har tana Tuntube sai da Hajiya Maman ta Bita da kallon mamakin ganin kamar tana Sauri kuma bata Cikin Natsuwarta.
Girgiza kawai Tayi ta koma Ciki,Achan Haraban Gidan kuwa Zaina na Fita ta Tsaya Daga Gefe,Tana Hango Hamdiya Durkushe gaban Alhaji Tsoho Da Abba Da Babban kaduna da Daddyn Abuja su Umma na Tsaye Daga Chan gefe kuma Tuni wasu ma Daga Tawagan anko sun Fara mikawa su Zafeera kuwa suna jikin wata Jeep Daga gani ita zasu Shiga Daman sun Taho Da kayansu Tun Daga Gida wajen ya cika da jama"a Shiyasa wani ma bazai gane wani ba an cika maza da mata Kamar an ce Ta kara Daga kai ta Hango Firstlove yana ma Zafeera mgana Bata san me ta gayamai ba Taga ya Nufi Wajen su Umma Kara Lafewa Tayi jikin Fulawan Dake Haraban Gidan tana kara Rufe Fuskarta Tana gani ya Rankwafa yana gaida Goggo Halima ta amsa Tana Shafa kanshi bakinta har kunni Daga gani albaeka Take sakamai Zuwa chan kuma ya mike ya Nufi Hanyar Shiga Falon gidan Sai Zaina ta kara Boye kanta Tana Danne kukanta ganin Firstlove ya Tada mata Duka wani Mikin Dake Zuciyarta,Wani irin Sonsa da kuma Raunin Rasa sa ya Bayyana Gareta Tana kallonsa har ya Shige Cikin jikinta ta Dafa Lokaci Daya wasu hawaye na Zubomata afili ta Furta"Nasan zakaji Ba Dadi in kaji irin Hukuncin dana yanke..Kada kadamu nayi hakane saboda Tseratar da Cikin ka da kuma Aurena Dake hannunka..da kuma kauce ma ganin wata Ta haifa maka D'a ko ya' ba ni ba da kuma kaucema ganin Wata a matsayin matarka..Ammh zan Dawo In da Rabo kuma nayi maka alkaawarin Kula maka da kaina da Abunda ke Cikina Insha Allahu.".
Kuka Ta fashe dashi kamar Wacce aka Duka Har sai da Ta Duke jin kamar Motsi ne Daga Bayanta yasa ta waiga Tana Toshe bakinta kada wani ya jiyota,Ido ta zaro Tana kallon Zain Daya Fito kamar yana neman wani abu Jikinta ya Fara Rawa Ta Tabbatar da ita yake nema ya kamata tayi ta Fice Daga Gidan nan kafin komai ya kwace mata,Tana ganin ya Nufi Wajen Zafeera Tayi Zuruf ta Fito Daga maboyarta Ta Bayan Mutane ta Dinga Bi Tana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 32