Akwatunan ki jera mim Cikin wannan Wardrope din Cos bana juran Daukan kaya Cikin Akwati and,kuma akwai Jakunkunana da Shoes dina suma ki samar musu matsugunni da kuma Kayan Shafa ne suma ki Jera min su..."..
Cike da Mamaki Zafeera ke kallon Dina kafin ta Nuna kanta Tana Fadin"Wai ni kike nufi..? Cikin Gadara Dina Tace"Yes..Ke mana..Ko agida bana aiki da kaina yan aiki kemin komai so nan Gidan naga kamar baku da Masu aiki ke sai kiyi min mana Kodin albarkacin Son or Dota Dinki Dake Cikina.."Tafada Tana Shafa Cikin,Zafeera Ta karkace kai Tana ganin Bariki kafin ta saki Mirmishi Tace"Lalle...Kin Fado..Allah rabani da zama Uwar Abunda ke Cikinki..Kuma wannan aikin Dakike mgana ki Daga waya ki kira wanda yayi Miki Cikin Shi sai yazo yayi miki Aiko Darajan Abunda ke Cikin naki...Idiot.."Daga haka kawai ta saki katon Tsaki ta Fita Daga Dakin Ta Bamgo kofa da Karfi Wata Dariyan Shakiyanci Dina ta saki Lokaci Daya Tana Fadin"Dole ko soshi..Tunda Jininku ya Digashi.."
Da wannan Takaichim Zafeera Ta koma Dakin Umma Ranta bace,Ta iske Zainab ta Shigo Da Farantin Abinci nan suka Hadu suka ci Zafeera na gayama Zainab yadda suka Kwashe da Dina Zainab Tace"Lalle nema...Gaskiya yarinyar Shegiyar kanta ce.."Zafeera tace"Allah yayi miki Tsari da zama da Karuwai Zainab...Yarinyar ta sangarce gata kyakyawa ammh Kyanta bai amfaneta ba Allah ya kyauta Gobe goben nan zan koma kano.."Zaina na Jinsu bata ce komai ba Zuciyarta Tatafi da wani Tunani Taya ya zamanta zai kasance acikin Gidanan da wannan Mara Tarbiyan..?lalle akwai zama kuwa indai Hakane..!
Hajiya Mama tajima kafin Tatafi sai da ta kara kwantar ma da Abba Hankali ta kuma Umarci Nene kan Karta damu da komai ta kula Da Dina,Nene ta amsa mata da Insha Allahu Umma tayi Tayi ta tsaya taci abinci ammah Taki Dole suka kyaleta Har Haraban Gidan suka Rakota kafin Haddir ya Dauketa Zuwa Gida Suna komawa ta Labartama Alhaji Tsoho Duk Abunda ya Faru ta kara da cewa"Ka kira Fatima ka Tsawatar mata gaskiya...Ka kuma gayamata ta bama Zainullahi matarsa kada Zaluncin yayi yawa..".
Alhaji Tsoho ya Murmusa Kafin yace'"In kirata nace me..?bayan Ta Riga ta Rantse so kike na sakata Tayi kaffara Aminatu..?
Hajiyaa Mama tace"Eh...Ai tayi gaggawa ne..Kuma gaggawa Dama ai yana Tare da Danasani.."Alhaji Tsoho yace"To bazan yi kuwa haka ba...Tana Ganin Girmana bazan bari ta Daina gani ba Duk da nasan in na Kirata da kaima zata janye mganarta bazan yi haka ba..Ki barta Komai tayi Daidai ne,ai Uwar Halima Take na kuma ji Dadi da Nuna ma Duniya ita Uwa ce mai Adalci da sanin ya kamata.."
Cikim Mamaki Hajiya Mama tace"Au Kaima kana goyon bayan Ta Raba auran yaranan..?
Alhaji Tsoho yace"Ni ban ce ba...Dama waya isa ya Rabasu..?babu sai Allahn daya Hada Abun..Ki kyaleta Ta sauko yanzu Tana Cikin Fushi ne da Takaichin Abun kiyi mata Uzuri Abun yayi mata yawa Uwar Halima ce kuma Uwar Zainullahi in Ta Dauki Bangaran Zainullahi za"a ce saboda D'anta ne yanzu kuma Data Dauki Bangaran Halima sai muga Laifinta..? A"a ku rabu da ita ta Huce zuwa bayan Bikin Hamdiya ni da kaina zan saka akiramin ita Daga ita Har Usmanun Na sakasu Daki na Jawo Hankulansu yadda zasu Fahimta."
Hajiya Mama ta gyada kai alamun gamsuwa Tana Fadin"Kuma fa hakane..Allah ya kaimu ai bikin ma yazo Jiya da mukayi mgana da Hannatu tace nan da kwana Goma tana Tafe.."Alhaji Tsoho yace"Eh..dazu Aliyun ke Fadamin Sauran Sati Biyu munyi mganar kawo kayan Aure Da yace nan za"a kawo ma hanashi nace yabama yan"uwan ita Safiyan Dama suje chan Abuja su karba.."Hajiya Mama tace''Hakan yayi Allah sa alheri.."ya amsa mata da Ameen Ameen kafin su cigaba da Hira.
Haddir kuwa bayan ya Ijiye Hajiya Mama Gidan Zain ya wuce yaje chan ya sameshi Cikin Damuwa shi ya Dinga bashi baki kan yayi Hakuri Umma bazata rabashi da matarsa ba Cikin Tsinkewar Zuciya Zain ya kalli Haddir yana Fadin"Umma fa Har Rantsewa Tayi kan sai na saki Firstlove Haddir.."
Haddir yace"Kai kuma sai ka saketan..? Zain yace"Sai dai in tace Zata Tsinemin zan saketa ba Domin ina Tsoron Tsinuwan ta ba a"a sai Domin nasan bazan kara Wata Rayuwa mai tsawo ba Tunda ban Ji Dadin Duniyar ba gwara na Rabu da Iyayena lafiya In naje lahiran Allah ya bani Dacewa.."Haddir ya kallesa kawai batare daya Kara mgana Shi zai iya Dafa Qur"ani ya Rantse Zain yana yi ma Zaina wani So ne wanda bai san iyakarsa ba ya sanshi Farin sani kamar yadda yasan kansa Zain ba Bukatu da kuma muradin wanda yake Girmamwa Fiye da na Zaina wanda Abunda ya Faru zai Dorashi matsayin kaddara da Kuma Shiga abokai Barkatai.
Zaina kuwa Dasu Zafeera na Dakin Umma basu kara Lekowa ba Umma kuma Tana Dakin Abba chan zata kwana Nene ce keta Dawaniya Da Dina Da Daddaren Tuwo Zainab da Zafera sukayi Miyar Kubewa Danya Saboda Abba naso,Dama Tun bayan Rasuwar Maryama Su Umma basu kara Daukan wata mai Taimakonsu ba suka Hada Hannu suna Girkinsu ita da Nene Tun kafin yaransu su kawo Jiki bayan Girman Zareena ne ta karbi iyayanta Har Zuwa auranta Gefe Daya su Zafeera suma suka Taso,ga kuma Zainab,Mazan kuma dama ba wani aiki suke ba kuma Dukkansu ba anan Garin sukayi karatunsa ba sai dai indan Sunzo Hutu,Bangaran Girki bama su Rabashi Kowacce Yi take,Shashen Abba ne kadai suka Raba Tunda wannan ya zama Dole in Umma Tayi kwana Biyu Nene Tayi Biyu Shiyasa Gidan Abba babu Babban Teburin Cin Abinci ma"ana Dinning Saboda Koda wani Lokaci ba"a haduwa gabadaya sanda zasu kamallah na Rana yara na makaranta na Dare ma suke Taruwa suci afalo wani Lokacin Daga baya ma sai dai kowa ya Debo nashi barin ma da Gidan ya watse su Zain suka Tafi London da sauransu gaba gaba kuma suma su Sadiq suka Watse gidan duk sai yayi Rakwa Rakwa Kuma ba Dole bane sanda wannan ke gida wannan na nan Shiyasa basu Damu da Hadakan cin Abinci ba gaskiya Duk wanda yaji Yunwa yaje kitchen akwai a kula Abba ne kadai ake Shigar ma da nashi Falonsa Ranar kuma Dayake jin Nishadi abaje mai Darduma yaci a Falo Cikin Matansa da Ya"yansa.
Nene da kanta ta kaima Dina nata Farantin Dinner ammh Tana ganin Tuwo tace ita kam Batajin Tuwo sai Dai adafa mata Maroconi da Kifi Nene batayi kasa agwiwa ba ta saka Zainab na Tura baki Tana komai ta Dafa mata sai da aka gama tace Bata ma son kamshinsa Fura Take so Tashi Nene ta Fita ta bama Direban Abba sako Yaje ya amso mata kana ta Karba Tasha Umma bata man san Wainar da aka Toyaba sai da Safe Zainab ke basu Labarin Abunda ya Faru domin agabanta komai ya Faru mamaki ya kama Umma Tana Mamakin Nene wani Lokacin Datake Daukan irin wannan Iskancin.
Tun Safe Zafeera tayi Shirin Komawa kano Motar haya zata Bi,Tagama sallama da Kowa Har Abba ma ya sallameta Direban Abba ya Dauketa Zuwa Tasha Bayan tace ma Zaina sai Bikin Hamdiya zata dawo Da zata Tafi suka sarke Hannun Juna Zaina Harda Hawaye.
Ganin Abba ya Fito Cikin Shirin Office Zainab yake kwalama Kira Ta Fito su ijiyeta makaranta Tana da Test da Safanan,Sai ga Nene ta Fito Daga Dakinta Tayi Wankanta ta Shirya Cikin sakin Fuska Ta gaida Abba ya amsa yana kallonta,Daganan Dakin da aka Sauki Dina ta Shiga ta isketa Cikin Bargo Tana Sharan Barci Domin Ko sallar asuba ma batayi ba.
Tashin Tayi Tatashi Tana wani Tura baki Cikin Lallabi Nana tace Tatashi ta sa sauya kaya tazo Ta gaisa da Abba zai Fita Tunda Jiya basu Hadu ba kamar tace bazata jeba sai wata Zuciya ta kwabeta da Cewa Mahaifin Zain fa wanda ya Haifan miki Abun Sonki kuma ko Banza Taga Nene na kula da ita ba kamar Umma da Sauran kannen zain din ba
Tashi Tayi Cikim kasala ta Fata Tiolet tayi Brush ta Dauro alwala tazo tacr bari Tayi sallah Nene ta cika da mamakin karfe 8am na safe dan Musulmi ke sallah Lalle Duniya Sallar ma nata Yar faki ce Tayi kuma da Wani mayafi ta Nade jikinta kan Kayan Barcin Dake Jikinta Riga da Wando masu kauri,Nene taso ta sauya kaya ammh Dina taki Tama yi gaba ta bar Nene na Binta da kallon Mamaki.
Abba na Shirin Barin Falon Zainab na Binshi abaya da Jakar Briecafe dinsa,Umma na Falon itama Yaji Muryan Dina na gaisheshi Ya waigo yana kallonta Cikin mamakinta ganinta Tsaye sama da kasa ya kalleta kana ya iya ganeta Cikin Sauri ya amsa mata bai ma Tsaya Sauraran Nene dake mai wani Bayani ba yace sai ya Dawo Zainab ta Rufamai baya Umma kuma ta kada kai ta koma Dakinta Ta gani Zaina Ta Fito Daga Wanka Nene kuma Tayi Tsuru kawai Dina kuma Mika Ta saki kafin Ta Tabe baki ta koma Cikin Dakin Har Cikin Ranta Tana Jin Haushin Yadda Nene ta Takura mata ta katse mata Barcinta mai Dadi kan Gadon Ta koma bayan ta Cire Mayafin Data yane kanta Dashi Ta koma ta kara Lafewa bisa filon.
*Ina godiya da Sharhinku Both Wsop da wattpad..Keep it Up*
*Janafty..*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
2️⃣7️⃣
"Ranar dai Nene Tayi ta Wahala da Bukatun Dina wani Lokacin ma har da iskanci acikin Lamarinta ammh bata nunawa saboda Ita babba ce kuma Bazaka Biye ma Mara Tarbiya ba Ballatana sanin ya kamata ba.
Sai wajen 10am tatashi tayi wanka Breakfast din da Nene ta kawo mata bata ci ba Doya da kwai ne sai Tea da Dankali Tace bataci wai amai yake sakata Don Tsirfa waina Fulawa tace zataci Haka Nan Nene ta Fita ta Soya mata ta kawo mata ko kunya kuma ta karba ta Tsakura kadan Tabar kwanukan nan ta Tsallake ta koma kan gado Ta Fara Dannan waya Kayanta kuwa nan Gegen gado Ta Zubesu Data Bude akwatin zata Dauki Kayan da zata saka Ta saba agida komai zulai ke mata Shiyasa ta Tsallake ta bar komai haka Kila Tana Jiran Nene ko Umma su gyara mata ne Tunda Zafeera dai ta kara gaba Zainab kuma ta Shiga makaranta.
Zaina kuma Tana Dakin Umma ko Lekowa Falo batayi ba Umma ce kadai ke Zirga Zirga Tsakanin Falo da Kitchen,Misalin karfe 12pm na rana Umma Ta gama Miyar agushinta Sai Taji kanta na Sara mata sai ta bar ma Nene Tuka Tuwon Shinkafan Tace zata Daki tasha mgani ta kwanta,Nene ta mata Allah ya kara lafiya ta karbi aikin Tana Zuwa Daki ta iske zaina ta Tsiri aikin Saka mata goggun kayanta da Jiya mai wanki da guga ya kawo Cikin Wardrope taji Dadin Ganinta ta saki Jikinta Yau watarana zaina bata kuka Sannu da aiki zaina tayi ma Umma itama Tayi mata,Wayar Umma ce tayi kara Zaina na kusa da ita ta Miko mata Tana Fadin Zafeera ce.
Bayan Umma ta Dauka sun gaisa tace mata ta isa Tun dazu..Yanzu ma tana Cikin makaranta Fatan Nasara Umma Tayi mata kana suka yanke Kiran Tiolet Umma Ta Shiga Tayi wanka kana ta aiki Zaina Zuwa Kitchen ta Dauko mata Ruwa Ta sha mgani Ta kwanta,Bayan Zaina ta gama Jera ma Umma kayanta Cikin Wardrope dinta sai ta Rage mata Karfin A.C ganin ta Fara barci ganin kar zamanta ya Dameta sai ta saka wani bakin Vail Samam bakar abayan Dake Jikinta,Jiki ba kwari ta Fita Zuwa Falo wanda Tun Zuwanta Gidan batace ga Ranar da Ta fita ta zauna afalo ba.
Sai da ta Leka Bataji Motsin kowa ba Kana ta Fito Falo Tana kallon Kofar dakin da aka Sauki Dina Shuru kamar ba kowa agidan,Su saudart suna makaranta adofane ta zauna kan Daya Daga Cikin Kujerun falon Tana Raba ido Bata so Dina ta Fito Ta ganta ba saboda komai ba Sai Domin kauce ma Haduwarsu,domin Zuciyarta bazata iya Juran ganinta Dauke da Cikin Firstlove ba.
Cikinta ta kura ma Ido Tana Jin wani Shaukin Sonsa na kara Shigarta Da Tsausayin kanta Dana Firstlove wanda Tana da Tabbacin in Umma ta san da wannan Cikin bazata barshi ba ita kuma mai yunkurin Rabata Dashi Sai inda karfinta ya kare.!
Bata ji Shigowarsa ba ballatana Sallamansa ba Tadai ji kawai Kofofin Hancinta na Shako mata kamshin Turaransa wanda ko Mutuwa Tayi aka Dawo da ita zata iya Shaida mai irin wannan Kamshin Cikin Mamaki Ta Dago kanta Karaf kuwa Idanuwanta suka Sarke Cikin Nashi yana Tsaye agabanta Sanye da wasu Ubansu Ameriacan Suit Masu kalan Ruwan Toka ya matse Wuyansa da Nektie,mai Ruwan Toka kafarsa Tana sanye da bakin Takalmi Booth Hannunsa kuma Sanye da agogon Fata na kamfanin Rado Akallo Farko in kayi zaka ji kana marmarin kara kallonsa Saboda yanayin kyawunsa da Haiba sai dai in ka kura mai ido zaka Fahimci Baya Cikin Cikakkiyar natsuwarsa,Ya Rame Wuyansa ya Fito Haka ma Fuskarsa sai idanuwana da karan Hanci Kasumba ta Cikamai Fuska wanda abaya Saje ne kawai Zagaye da karamin Bakinsa Sabanin yanzu da ba gyara sai duk ya zama wani iri gashi nan ne.
Yau tun Safe ya samu Kiran Gaggawa Daga asibiti,Wata mata ce zata Haihu kuma Jini ya yanke mata ya isa ko Fara Duba patient din bai ba Allah yayi mata Rasuwa ita da Abunda ke Cikinta Domin ta Rasa Jini Sosai Abun ya Tabashi Sosai Haka ya koma Office dinsa ya zauna Sukuku Dama Jiya kwana yayi bai yi Barci ba,Sallah yayi bayan ya Idar ya koma Tuban ma Allah gefe Daya ga Zullimin nganar Umma da Abun ya kwana aranshi,Kawai yaji ba wacce yake son gani Sai Firstlove agogon Dake Hannunsa ya Duba ya Tabbatar da yanzu Abba ya Tsufa awajen aiki,Ya yanke Shawaran zuwa yau ko ta Halin kaka sai yaga Matarsa ko da Umma zata Dakeshi ne.
Shine yana Shigowa Falon kamar almara yaci karo da Zaina Zaune afalo ta kurama Cikinta ido,Farinciki yaje ji ko me bai sani ba kawai Ido ya Zuba Mata yadda itana ta sakar mai nata Idanuwan Hannuwansa na Cikin aljihun wandon Dake Jikinsa,kallonta yake da wani Managadisu Tare da Sonta da kaunarta kallon Ban Hakuri karki barni kallon Sha"awa kewa da kuma Muradi ita kuma Idanuwanta ne suka Tara kwallah kallon meyasa ka Cutar damu..?kallon Tsausayinsa kallon Soyayyarsa da kaunarsa kallon Girma kima Tare da wani kewa wanda Bata Taba Tsammanin zai yi Faruwa da ita ba.
Hannunta kawai Taji ya kama ya Mikar da ita tsaye Kur tamai da ido Tana kallonsa bai Tsaya Bata samu zarafin mgana ba Taga ya Fara janta suna Tafiya yana Rike da hannunta,Ganin sun Nufi Dakin Umma yasa ta Kwalalo ido Waje Cikin Tsoro da Rawan Jiki Tace"Umm..Umma...!
"Shiiii..." Ya Fada ba tare da ya Waigo ba sai ya sauya akalarsa zuwa Dakin Nene kamar wata Rakuma da akala haka Take Binsa Nene Dake Kitchen Taji kamar Motsi ta Fito kenan Taga Zain Rike da Hannun Zaina sun Shige Dakinta baki ta Rike acikin Ranta kuma sai Taji Dadi Cikin Sanda ta leka Dakin Umma Ta ganta kwance Tana Barci da Sauri ta Fito Tana Fadin"Haba...Naji Dadi ya samu Lokaci da zai gana da Matarsa..Haba Duk kin wani Takura ma yaro kin Hanashi kwanciyar hankali.."Tafada Tana kyafci Lokaci Daya Da komawa Cikin Kitchen din Ta Cigaba da Abunda Take yi.
Suna Shiga Dakin Nene Ya Saki Hannun Zaina ya Murza ma Kofar key Cikin Rashin Fahinta zaina ke kallonsa kafin ma ta samu Zarafin mgana Taji sa ya Fado Jikinta Cikin wani Irin Rumguma mai karfi ya Rumgumeta Saura kadan ta Fadi Dakyar ta iya Daidaita kanta Bayanta ta saka Hannu Ta Dafa Gefen gadon Nene...
Irin yadda ya sakata acikin Kirjinsa ya bata Tsoro,Matseta yayi ya Kamkame kawai Taji yana Sakin Numfashi Sama sama Kamar wanda zai Shide,kansa yake Tusawa Cikin Wuyanta Yana kara kamkameta kamar zai maidata Cikin Jikinsa,Tana Jinsa Kuma ta Fahimci Komai ban Hakuri da yarensa Numfashinta Take son Fizga ganin ya matse mata Wuya Yasa ta Fara mutsun mutsun Kwace kanta ammh yaki Sakinta sai ma kara Riketa Da yayi kam kam kamar wani zai kwace masa ita..
Ganin Ta kasa kwace kanta ne yasa ta Rabu Dashi kawai ammh Zuwa Lokacin Itama Rauninta ya bayyana Hawayenta kadai ke Zuba daga kwaryan Idanuwanta,Sai da suka Shafe wajen Mintina Goma ahaka kana ya Saussauta Rikon Da yayi mata Kafin kuma ya saketa lokaci Daya yana kallonta yadda Hawayenta ke Zuba Shima kukan Zuccin yake Domin Idanuwansa sun kala Sun Jajir kamar gawarshin Wuta.
Tattausan Tafin Hannunsa ya sanya ya Dauke mata Hawayen Cikin Wani Raunin murya yake Fadin"Haba Firstlove..? Me nayi miki da Zafi da yasa kika Tsane ni haka..? Kin manta Ni dake mun Fadama Juna kafin Dayanmu ma yayi Laifi mun Riga da mun yafe mai..? Amh Why ki ke azabar Dani alhalin kinsan duk Duniya ba wacce Nake so da kauna sama Dake..?
Yafada yana Rike da Fuskarta da Hannuwansa Duka so Take ta Bude baki tace me"Ita wacce kayi ma cikin fa..? Ba sonta kake yi ba..? Sai dai kuma ta kasa bakinta yayi mata wani irin Nauyin Data Kasa Furta komai,Runtse ido Tayi Hawayenta na Zuba kawai Cikin Fitan Hayyaci ya Jijjigata yana Fadin"Ki Bude idanuwanki ki kalleni kiga yadda na koma saboda Rashinki..Duk na Rame na Lalace Wlh Firstlove in baki Dawo Gareni ba kina gabda Rasani kin ji ma na Rantse miki.."
Da sauri ta Bude Idanuwanta Tana kallonsa Idanuwansu suka Narke cikin na juna cikin wani yanayi ya Cigaba da Fadin"Nasan Zuciyarki na Cike da Tsanata kan Abunda na aikata ko..? Me zan ce miki Firstlove Wlh Tallahi Har ga Allah ke kadai ce macen Da nake so kuma ke kadai nayi Burib ki zama matata,Dina tana Cikin Kaddara tane ammh ita kanta ta sani ban Taba Sonta ba...Ke nake so ke na kallo amatsayin Mace ke kadai ke sakani kukam kukan jin Dadi Firstlove Wlh Bata Fiki komai ba...Kin Fita komai Bata kai ki ba...Don Allah Firstlove Kada ki Dubi Tarin Laifukana Ki yanke min Hukunci Don Allah kiyi Hakuri kada ki bari Ummanki ta Rabamu plz...!
Yafada Kwarmin Idanuwansa na Cikowa da Hawaye,Tuni Zaina ta saki kukan Data ke Rikewa Tana neman Dukewa a kasa Saboda kuka ya saka hannuwansa Duka Biyun ya Tareta Lokaci Daya ya sakata Cikin Jikinsa,ganin irin kukan Data keyi ya Rurumai wutar wani Abu acikin Ransa Kawai sai ji tayi Ya Tallabo kanta Idanuwanta ta kara Runtsewa saboda jin yadda ya saka Bakinsa yana lasan Hawayenta kafin ya Dire Bakinsa kan Lebenta yana Sucking Cikin kwarewa da kuma Rawan Jiki kamar yadda Itama Zaina Jikinta ya Fara wani irin Rawa Kana ganinsu kasan Gabadayansu Suna Cikin wani yanayi Batare data sani ba ta Bude baki ta yi Ihu kawai Taji ya Zura Harshensa Cikin Bakinta ya Fara mata wani irin Sumba Sumbar da bai Taba Mata ba yawo kawai yake da Harshensa,Lokaci Daya yana kara Riketa gam acikin Jikinsa ganin Tana nenan Faduwa Ammh Duk da Haka Jikinta ba Karfi sai ta kara yin wani luu ammh haka ya Bita suka Tafi suka Zauna saman Cafet din Dakin Nene yana kamkame da bakinta gam yana mata wani irun Sumba Yana kuma kallon Idanuwanta Cikin wani Shauki.
Ya Damke Bakinta ganin bata iya kwace kanta yasa Kawai ta Sakarmai Ragaman komai,ganin ta Saki ne yasa ya Saka Hannu ya Janye mayafin Data yane kanta Dashi Kalaban Dake kanta Suka Zube Duk da Kitson ya Tsufa Domin tun kafin Faruwan hakan Tayi shi Ammh kuma Tana wankeshi Saboda yayi mata Nauyi har wani Tashin Tashin Warin Daula yake yi ammh Shi bai Damu ba sai ma Shinshina kanta Daya Farayi da Hancinsa ammh ya kasa sakin bakinta sai da yaga Dama kana ya Saki bakin nata Bayan yaja Leben nata kamar zai Tsinka matashi Kirjinsa kawai ta Fada tana maida Numfashi Shima Sai ya Rumgumeta yana maida Nunfashi Lokaci Daya yana Shafa Bayanta Zuwa Kugunta Kokarin Tashi Take daga Jikinsa yaki sakinta Sai kawai ta Shammaceshi ta Turashi baya yayi kamar zai Fadi ta Fizgi kanta ta Mike da Sauri Shima ya Mike ta Duka Zata Dauki mayafinta Taji Hannuwansa Dumu Dumi kan Boobs dinta ya Rike da karfi yana wani matsa matsawa Cikin kwarewa da kuma wani irin Muradi mai Girma...
Mikewa Tayi tana kokarin kwace Kanta ammh sai ma ya samu Damar saka kansa Tsakanin Wuyanta Lokaci Daya yana Matsan Boobs Dinta Da karfi Karfi Kuka kawai ta Fashe mai Daahi Har Muryanta na Fita Ita Tsoronta Daya kada Umma Tazo ta gansu me zata ce mata..? Umma bazata Kara yarda da ita ba Ga kuma Abubuwan daya ke mata Suna Rikitata so yake ya saketa Ammh yaki Sakinta Har sai da ya kara kaita kasa bata Fargaba Taga yana Kokarin Zare mata Rigar Jikinta kana ta Daddage ta Gantsaramai Cizo a Kirjinsa wanda yasa ya saketa da Sauri Ganin ya saketa Ta Yunkura Tatashi da Uban Sauri ta Rarumi mayafinta ta koma Gefe Tana Kuka,wani kukan mai Tsuma Zukatan mai Sauraro.
Inda ta Cizeshi ya Shafa yana mata Wani irin kallo kafin yace"Baki Taba min irin wannan Cizon ba Firstlove..zo ki yi Ta Cizona indai zaki Huce kuma ki biyoni mu koma Gidanmu.."Yafada yana Mikewa Kamar zai kamota Tayi Saurin Ja baya Tana wani irin kuka Kura mata ido Yayi kafin ya mika mata Hannu yana Fadin"Taho...Taho Firstlove don karki kiki Tahowa gareni..Taho mu koma Gidanmu..Na Yarda Muna Zuwa Gidanmu ki kulle ni acikin Dakina kiyi ta Dukana Har sai kin Huce indai zaki Barni kuma Ki zauna dani na yarda na amince.."
Yake Fada kamar yayi mata kuka,Tana Kallonsa Tana ja da Baya Cikin Kuka Da Tsausayinsa Take Fadin"Aah....Bazan iya ba..ba zan iya ba.."Tafada Lokaci Daya tana Juyawa Ta Bude Kofar Tiolet ta Fada da Sauri ya Bita sai dai yayi Rashin Sa"a Ta Riga ta Saka Makulli Jikin Kofan ya tsaya yana ta kwalamai Kira tamai Banza ta Sulale nan Kasan Tiolet din Tana sakin kukanta Bazata iya Binsa ba Ba saboda Laifinsa ba sai domin Umma uwa wacce Tayi mata Dukkan Hallarcin Duniya bazata iya watsa mata kasa acikin Idanuwanta ba.
Tana Jinsa ya gama Kiran Nata da Buga Kofar Ya Taka ya Fice Kuka ta kara sakawa Tana Jin kamar ta Bude Kofar ta Bishi sai ba Hali,Kukanta tayi ta Sha abunta Kuka ne na Soyayyah kauna da kuma yanke kaunar duk Lokaci Daya.
Shi Kuma zain yana Fita Cikin Wani irin kasala ya Fara Taku zai bar Falon,Yaji Kiran Nene Daga Bayansa ya waigo Cikin Saurin Basar da yanayinsa Kura mai Ido Nene Taayi kafin Tace"Me ya sameka..?
Yana Shafa kafansa yace"Bakomai Nene..na shigo kina Kitchen.."Nene ta kada kai Tana Fadin"Eh...Naga Zaka Fita baka Shiga ka Duba yarinyar nan ba.."Cikin yamutsa Fuska yace"Wata yarinya kenan Nene..? Cikin Takaichi Nene Ta mai Dakuwa Tana Fadin"Bansani ba...Toh wacce ka Kakabamana Dole mana Ai kana sane jiya iyayenta suka kawo ta.."Sosa keya yayi yana Fadin"Nene don Allah kyaleta..ina da aiki asibiti Na Tafi.."Baki sake take binsa da kallo Har ya Fice bata samu zarafin mgana ba sai da ya Fita kana Ta kada kai Tana Fadin"Uhmm..!
Nene bata koma Dakinta ba sai da Ta gama Kulla Duka Tuwonta cikin leda ta saka Cikin Wata katuwar Kula,Jin ana ta Kira kiran sallah yasa ta koma Dakinta ta watsa Ruwa Tayi sallah sai taga Zaina na sallah sai Lokacin ma ta iya Tunawa da ita Kada kawai tayi ta Shiga Tiolet tayi wanka Koda ta Fito Zaina ta bar Dakin Nene ta Murmusa Tana Fadin"Ta gudu Dakin uwarta kenan.!
Umma kuwa sai da Zaina ta koma Dakin kana ta Tashi kan ya Saukar mata Ta Shiga ta Dauro alwala tazo Tayi sallah bayan Ta Idar ne ta Zura ma Zaina ido ganin Tana ta wani Dukar dakai kuma Fuskarta ta kumbura kamar tayi kuka Cikin Mamaki tace"Meke damunki..?
Da Sauri Zaina Tace"Ba...Bakomai Umma.."Kuri Umma Tayi mata da ido Tana Nazartanta kafin ta mike tana Fadin"Ke dai kika sani..In ma Kukan nace zan rabaku ne Wlh sai dai kiyi tayi har Hawayenki ya kare bazaki Koma gidansa ba.."
Daga Haka Umma ta Sabule Hijabinta ta Fice ta bar Zaina na Kokarin maida Hawayenta acikin Ranta Tana Tunanin da Umma ta gansu yau ai da ta kade har ganyenta.
*****
*Bayan Sati Daya..*!
Haka abubuwan sukayi ta Faruwa,Acikin sati Dayan bangaran Dina kuwa iskancinta sai Karuwa yake yi kayanta Data Zube sai dai Nene ta saka Zainab ta gyara mata ta Shiryamata kowanne ta ijiye abangaransa,Banda Nene kuma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 32