Daga kan Gadon Daga ita sai Wata Doguwar Rigar barci mai Igiyoyi Gashin kanta Ta tattara ta saka aBand,Silafas dinta ta saka Ta Nufi Hanyar Kofa tana wani Taku Cikin Son Nuna ita din Watace.
Saukowa Take Daga kan Steps din Tana wani Lumshe idanuwanta Kamar mai Jin Barci nan kuwa Tunani Take Gata agidan Zain a matsayin Matarsa Shiyasa Take saukowa Cikin wani Rangaji da Karairaiya,Har ta Sauko Gabadaya Falon Inda kannenta Waleeda da Waleed ke zaune suna Buga game ganinta yasa Dukkansu Suna Hada bakin Wajen gaisheta"Gud Mrning Anty Dina.."
Kallo Daya Tayi Musu Ta kauda kai kafin Tace"Mrning Kids How are u..? Tare suka amsa da "We are Fine.."Daga haka ta jinjina kai ta Wuce kai Tsaye Dinning aRea Mai kama da alkarya guda,Kujera ta ja ta zauna Ta Fara Bubbude Kololin Gabanta tana Wani yamutsa baki kafin Ta Daga baki Tana Fadin"Zulai...Zulai.."
Da dan karfinta Da Sauri Wacce aka Kira Da Zalai ta Fito Da Gudu Daga ciki jikinta na Bari,Gabanta ta Durkusa Tana Fadin"Gani Hajiya ina Kitchen Ne Lokacin da kike Kirana.."Tafada Cikin Ladabi kanta na kasa ko Kallonta batayi ba Tace cikin yanga da Yauki."Soyamin kwai 3 karki saka Gishiri kana ki Soyamin Buredi da kwai.."
Da Sauri Zulai ta mike Tana Gyada kanta Cikin gamsuwa Tace"Angama Hajiya Bari naje na soyo.."Da sauri ta Juya ta koma Kicthen ita kuma Sai ta Kada kai ta jawo Fulas Din Ruwan Zafi ta samu karamin Kofi ta Tsiyaya Ruwan Citta da Na"a Na'a,ta Fara kurba sannu a Hankali Cikin kwanciyar Hankali.
Tana Cikin Kurban Tea din Taji Kamshin Wani Turare mai Dadin Shaka ya Ziyarci Hancinta Lumshe ido Tayi Kana ta Budesu kan Inda Take Jiyo kamshin Fes ta Sauke su kan Matar Mahaifinta Anty Batula Farar mace alkayabban mata Cikin Shiga ta alfarma.
Kai ta kauda ta wani Tabe baki Tana Jinta Tana mgana Dasu Waleed kafin ta Kariso Dinnig din Taja Kujera Ta zauna Tana kallon Dina Wacce ta Rausayar Dakai Tana Fadin"Gud Mrning Uwata.."Tafada cikin Wani Izgili Duk da Batula ta san da Tsageranci Dina ke Kiranta Uwarta,ammh Nuna mata take taFita iya Duniyanci Cikin Sakin Fuska da Fara"a Tace"Mrning Dota..? How was ur Nite..?
Cikin Basarwa Dina Tace"Cool..."Daga Haka ta Dauke kai Cikin Mirmishin Leben baki Hajiya Batula tace"Yayi kyau..? Yaushe zaki koma Bakin aiki ne..? Sarai Taji Tambayar nata sai kawai ta Basar da mgana Cikin Kallon Ido Cikin Ido Take ma Hajiya Batula sanda itama Take Tsiyayan Ruwan Na"a Na"an Tana wani Sakin Annurin Dake Fuskarta.
Cikin Dakiya Dina Tace"Uwata yaushe Daddyna zai Dawo ne..? Sai da ta Kurbi Tea din kana Ta kalleta Tana Fadin"bansani ba Kila dai Cikin Satinan...Kinsan in suka Tafi Abuja Tarurrukan nasu Yakan yi sati bai Shigo Gida ba.."Wani irin kallo Dina ta Jefata Dashi Tana Tunanin kalaman zakiya akan Yawan Tafiye Tafiyen Da Daddynta keyi
Saurin kauda wannan Tunanin Tayi Zuwan Zulai da Filet din kwai,Sai Dayan Filet mai Dauke da Soyayyan Buredi Da kwai kan Dinning Din ta ijiye mata Tana Fadin"Gashi Hajiya.."
Shuru Dina Bata ce mata komai ba Kuma Idanuwanta na kallon Wani Gefe bata ma kalli Abunda Zulai din Ta kawo mata ba Hajiya Batula ne ta kalli Zulai Tana Fadin"Tafiyarki Zulai..Je ki cigaba da aikin ki.."
Cike da Girmamawa Zulai ta Rankwafa Tana Fadin"Toh Ranki ya Dade..."Daga haka ta Wuce Da Sauri Dina ta Bita da kallo mai kama da Harara Kafin ta saki Wani karamin Ajiyar Zuciya ta ja Filet din kwai ta Saka Fork ta Fara ci Cikin yanga Kamar Tana Tauna Madaci Hajiya Batula Ta Sauke Kofin Hannunta Tana Fadin"Wai yaushe zaki leka chan Sudan ne..? Naji ko kwanaki Babanki na Basu Hakurin kina Tafe Aiki ne yayi miki yawa.."
Kur Kawai Dina Take kallonta Kamar bazata Tanka ba Sai Chan Ta Nisa Tana Fadin"Uhm...Zanje Insha Allahu Nima Suna ta Kirana kan Bikin Diyar Anty Jiddo da za"ayi.." jinjina kai Hajiya Batula Tayi kafin Tace"Gaskiya kam ya kamata..Allah bada iko.."
Daga Haka ta Tsuke bakinta Ganin Dinar ta Mike ko Soyayyan Buredin bata ci ba ta dai Ci kwan Shima bada yawa ba,Batare da tayi mata mgana ba kawai ta Wuce zuwa sama Tana wani Taku Daya bayan Daya Kowani Gabanta na Girgizawa Cikin Kallon Tara saura Kwata Hajiya Batula ta Bita Dashi har sai da ta kule ma Ganinta kafin Ta Tabe baki a Fili ta Furta"Allah ya Shirya.."
Domin Duk Macen Da Taga Dina Da yanayinta zata mata Zargin Tasan Namiji,sai dai ita bata Shaidanta da Iskanci ammh kam wasu al"muran na Dina Suna Bata mamaki kara Tabe baki Tayi kawai Ta mike Daga Dinning Din ta Nufi Falon Inda Yaranta gefe Daya na Zuciyarta na Watsar da Sha"anin Dina ganin Mahaifinta ma bai damu da Bincikan Halin data ke Ciki ba,Ballatana ita da bai bata wannan Damar ba Ballatana ita kanta Dinar da bata mata kallon Uwa sai ma wani kallon Raini da Kaskasacin Data saba yi mata akoda yaushe.
******
Kamar yadda Dina ta Tsara Washegari ta koma Bauchi Kuma aranar ta Shiga Cikin Asibitin ta iske an kawo wata patient zata Haihu ita da Dr Aisha Sukayi Attempting Din Patient din ta Sauka Lafiya Gabd Mganariba Dina ta bar Cikin Asibitin Zuwa Gidanta a Hanya sukayi Clashing Da Zain Kila ya Fita ya Dawo ne,Tana ganinsa yayi mata Double Signa Zuciyarta kamar ta Fashe saboda Farinciki Bata Bi ta kansa ba Ta Take Motarta Tana ji ajikinta Dole zai nemeta Dolensa.
Kamar kuwa ta sani Tana komawa Gidanta tayi wanka tayi Sallah ta Sauya kaya zuwa Wasu Riga da wando iyakar Wandon Gwiwanta,rigar kuma Cibiyarta Bude Take,Kitchen ta Shiga Ta Soya kwai ta Dafa Ruwan Zafi ta Fito Falo Ta zauna kenan Sako ya Shigo Wayarta ganin Lambar Zain da tayi ma Saving da *LIFELINE..*
Yasa ta Ja Saman wayarta da Sauri Cikin Rawan Jiki Ta Duba Sakon Nashi Inda yace Mata" kina gida ne..? Kawai yace Cikin Sakon nashi,Wani kayattacen Mirmishi Tayi kafin Ta Maida wayarta ta ijiye,Tana wani kada kai kamar wata Sakarya,Zata Bi mganar Zakiya Dole me ta Koyama Zain Hankali Ko zai gane Darajarta.
Ba"a jima ba, Taji Tsayuwar Motarsa Tashi Tayi da Sauri Ta Bude Labulen Window ta Leka Daidai Lokacin ya Bude Murfin Motan ya Fito yana gyara zaman Tek tie din Wuyansa Cikin Wani irin kallo Take Binshi Dashi kamar ta Jawoshi Ta kwakwameshi Ganin ya Fara Taku Zuwa kofar Mashiga Flat din Nata yasa ta koma Ta zauna ta Harde kafa Daya kan Daya,Tana Kurban Tea din Hannunta Taji yana Knoking din Kofarta Sai da ta Sha iskanta tana Wani Hura Hanci Tatashi Bayan Ta Ijiye kofin Hannunta Saman Center Table Din Dake Tsakiyar Dakin Ta Fara Taku Cikin Wani Iya Bariki Ta isa Jikim Kofan Ta Bude Fuskar Zain Ta bayanna wacce baka isa ka gane yanayin Dayake Ciki ba.
Kallon Kallo Sukayi ma Juna Cikin Wani Yanayin kafin kowa ya Janye Idanuwansa yana Mganar Zucci Ita Dina Farinciki ne ya Cika ta kamar an sakata a Aljannah Ganin Zain ya Biyota Shi kuma wani Takaichi ne ya kumeshi yana kallonta yana Tunanin me Tafi Zainarsa..? Me Dina Take Jiyar dashi Da In ya kwana Biyu zuwa uku bai Kusanceta zai jishi kamar ba Daidai ba Baya Samun Kowani Natsuwa sai yazo Gareta..? Amsan Daya Gaza samun amsanta kenan Kuma Tuni Take yawo acikin Ransa.
Baya ta Koma Batare da tamai Mgana ba ta Bashi Hanya,Cikin Takun Jaruman Maza ya Taka ya Shiga Falon ita kuma ta maida Kofa ta Rufe ta Biyo Bayansa Tsakiyar Falon ya Tsaya yana Nazarin Falon kamar yau ya Taba Shigowa Ita kuma kai Tsaye wajen zamanta ta koma Ta zauna Tana Daura Kafa Daya kan Daya Cikin Wani irin yauki Ta Sunkuya Har sai da Nonowanta Ta sama Suka Bayyana Filet din Da ta saka kwan ta Dauko Zuwa kan Jikinta ta saka Fork din Dake saman Wajen ta Fara Tsakura Gefe Daya kuma na Zuciyarta Najin Kaifin Idanuwan Zain akanta.
Shi kuwa kallonta yake Cikin Mamakin Shareshin Datayi Cikim karfin Hali yace"Baki ga Sakona bane..?
Sai da ta Tauna Kwan Dake Cikin Bakinta Kana ta Dago Dararan Idonta ta saka Cikin Nashi kafin tace"Nagani mana." Tafada Cikin Wani lum da idanuwanta Cikin Kissa cikin mamaki yake Fadin"Kingani.?
Kai Tsaye Tace mishi"Eh nagani.."
Cikin Kufuluwa Yace mata"Me hakan ke Nufi Dina..?kinga Sakona kinyi banza Dani Nazo kuma kin kalleni kin watsar kamar baki ganni ba.."Dina ta saki Mirmishi Cikin Farinciki acikin Ranta Tace"me zan yi maka..? Dama ina da Sauran wani amfani ne awajenka ka manta kai ne ka Koreni Daga Office Dinka Ranar..? Ina Zainar naka..? Na Dauka zata Share maka Gurbin Dina acikin Zuciyarka kamar yadda kake ikirarin Ta Share ta kowacce mace.!
Wani Taku ya Fara Zuwa Gareta Ido Cikin Ido yake kallonta kafin ya saka Hannu ya Fizgota ta Mike Tsaye Filet din Dake Hannunta yayi Gefe Cikin Tsoro Take kallonsa Idanuwanta ta Zaro ganin Yadda Fararan Idanuwansa Suka Sauya launi Cikin Wata Irin murya yace"Dina baki da amfani awajena...Ba ki kuma da wani Kima acikin Zuciyata..Haduwata Dake Kaddara ne Haka ma Tarayyana Dake Tsakaninmu ma Kaddara ne Sai dai ina so Ki sani ba iya Kamarki Zaina ta Koremin acikin Rayuwata ba Irinki Dubu ma Ta Sharemin Su Tas..Ita Tauraruwa ce kuma Zahra ce Cikin Wata."
Ya karishe Fada ya Wani Mata wani Munafukin Mirmishi Cikin Takaichi Ta Juya Labbanta zatayi mgana ya Dakatar da ita Bayan ya Dora bakinsa kan Labban nata yayi mata wani Light kiss din Daya Sumar da ita Bata Dawo Daga Cikim Hayyacinta ba ya Radamata Cikim kunnuwanta.
"Kada ki Hada kanki da ita..Ita Ta Dabamce Awajen Zain..Ina mata Kaunar da Bayan Ahalina babu kamarta Ki kiyayi Harshenki Wajen Ambaton Abunda Zain yafi kauna Da Darajawa sai Ki Tsira da Matarbanki.."Cike da Izza da Dariyan keta yake gayamata Haka kuma bai bata zarafin mgana ba ya Hade bakinsu yana Bata wani Hot kiss wanda ya Rikita ta saki ajikinsa Lokaci Daya Tana karban Sakonshi Fin Minti Goma kafin ya saki Bakinta ganin yadda tayi Laishi ne yasa ya saki Mirmishi kafin ya Shafa Kumatunta bai Tare da yayi mgana ba ya Ciccibeta zuwa Jikinsa ita kuma ta kara lafemai Wutar kaunarsa da Kishin Halima na Cika mata Zuciya Da Kafa ya Daki Kofar Bedroom Din ta Bude ya saka kai Cikin Kan Gadon ya Wurgata Kafin ya Bita ya Danne yana Sumbatarta ta ko"ina Cikin Mugunta Cikin Ranshi Kuwa yana Tunanin Gwara yau yayi ma Dina Cin Kacha kila In yayi mata Ci mai kyau Bazai kara Jin son kasancewa Da ita ba.
Ita Kuwa Dina Farimciki ne ya Cikata da Sassafar take Rabashi da kayan Jikinsa,shima Cikin Saurin yake Rabata da kayan Jikinta,Achan gefe kuma sai Kiraya Kirayan Sallar Isha"i akeyi ayayinda wasu Mutanen ke kokarin yin alwala Domin Tafiya Masallaci Wasu suna chan Suna aikata Sabon Allah Wa"izubillah.
*****
Shudewar Awa Daya da Wani Abu Zain yana Caccakan Dina Kamar Allah ya aikoshi So yake yaji Kwadayinta da Sha"awarta Sun Kare acikin Ransa Ita kuwa Dina Duk da Yadda Jikinta ya gaji da Sabon Mu"amalanta da Zain bai sa ta Nuna gajiyawarta ba sai ma kara Daurewa Da tayi Tana Kokarin Bashi Hadin kai
Akallah ya Juye mata Abunda ke Maransa yafi Sau Uku kafin ya Sarara mata,ya koma Gefe yana Maida Numfashi Sama sama,Itama Dina Numfashin Take Maidawa Lokaci Daya kuma Tana Mirginowa Tana Rungume Zain din Ta Baya Ta Cikin Blanket din Da Zain ya Rufa musu Saboda Shi mutum ne Da baya son Ganin Tsaraicin Juna Gaskiya Tunda ta Fara Tarayyah Dashi baya yarda ya kalleta Ido Cikin Ido Ba komai ajikinta.
Tsawon Mintina goma Kafin ya yunkura ya Ture Dina Daga Jikinsa,Daga kwancen ya Jawo Boxers Dinsa Dake gefe ya Zura Duk da kyamar kansa ya kamashi ammh bai zai iya Shiga Toilet din Dina ba Yana Da Tsantsane da Tsabta da kyankyani,Abunda yasa ma yake Mu'amala da ita batare da kariya ba saboda yasani shi ne kadai Namiji kwara Daya da Dina Take Mu"amala Dashi Shi yasa ya bata yardansa a wannan Fannin.
Saukowa yayi Daga kan Gadon Sauri Sauri ya Maida kayan Jikinsa,Dina Data Dago kanta Cikin Blanket din Take Bin Zain da wani irin kallo na Tsantsan Farinciki,Tana kallonsa Ya Zura Hannu Cikin aljihun Wandonsa ya Fito da Wayarsa,Missed calls yagani Rututu Na Firstlove Dana Nene sai na Haddir Karamin Tsaki kawai yaja Lokaci Daya yana Daura Tek Tie dinsa,Cikin Hanzari ya maida Coat din Dake Jikinsa Batare Daya kalleta ba ya Juya ya Fice Daga Dakin Ko Waiwayota baiyi ba Karamin Dariya ta saki Cikin Wani Shauki Tace"Hmm Yanzu aka Fara wasan..!
Sai da ya Shiga Cikin Mota ya Daidaita zamansa kana ya Kunna Motar ya Fice Daga Kofar Gidan Dina da Gudu Daidai Lokacin da agogon Fatan Dake Hannunsa ya Nuna Karfe 9:20pm na Dare karamin Tsaki Yaja Yana Tunanin Dole zai koma Cikin asibiti Yayi wanka bazai iya zuwa gida ahaka ba In ya yi Wanka Firstlove zata Dora ayan Tambaya akansa Wanda kuma Faruwar Hakan kamar Faruwan wani Abu ne.
Cikin Asibiti ya koma Office Dinsa ya Shiga yayi wanka bai Fito ba sai da ya Tsaya ya Tsane Ruwan kansa da Karamin Towel Din Dake Toilet kana ya Fito Sauri Sauri ya kara Shiga Motarsa ya Fice Daga asibitin ya Nufi Hanyar Gida Daidai Lokacin Wayarsa ta kara Daukan Tsuwa Tana Gefensa ne ya Waiga yaga Firstlove ke Kiransa Da Sauri yayi amfani da Hannu Daya ya Dauki Wayar nasa ya Daga Kiran yana Fadin
"Hello Firstlove...!"
Dagachan Bangaran Halima ta Buga Tsalle Tana Fadin"Heyy Firstlove...Zuwa America Ya Tashi...Anty Zareena ta Haihu Yanzu Ummana ke Fadamin.."
Tafada Cikin Bayyana Farincikin Datake Ciki,Bakinsa ya Washe yana Fadin"Masha Allah...Me aka samu.? Cikin Murna da Farinciki Halima tace'"An samu Baby Girl Firstlove.."Zain ya Kada kai yana Fadin"Allah ya Raya ya amfana Jalal ya samu kanwa kenan..?
Halima Tace"Jalal Kuwa ya samu kanwa Firstlove yaushe zan Tafi ni..? Ko Tare da Umma zamu Tafi..? Fuska ya yamutsa kamar Tana kallonsa yana Fadin"A"a Firstlove ina kuma Zaki kin manta kun kusa Fara Test ne a makaranta..."Tura baki Halima Tayi Tana Fadin"Kai Firstlove...Kaifa kamun alkwari Sanda Umma zata maida Anty Zareena Lokacin kace na bari zamu je Tare dakai,yanzu kuma sai kace A"a bazani ba.."
Tafada Kamar Tayi kuka Mirmishi ya saki kafin yace"Naji..Ki bar wannan Tura Turan bakin sai na dawo sai muyi mgana.."Cikin Bata rai Tace"Yaushe zaka dawo Toh...? Da Sauri yace"Yanzu ina kan Hanya ne.."Batare da tayi mgana ba Ta katse Kiran alamun Ranta yana bace ne Wayar ya Sauke yana Mirmishi kafin ya Furta afili"Zaina Rigima.!
Sun Gama wayar kenan sai ga Kiran Zareena Da Lambar Waje Da Sauri ya samu Gefen Hanya ya Faka kafin ya Daga Kiran Nata yana Fadin"Abokiya Zareena Barka da Arziki..."
Dagachan Bangaran Zareena Dake Kwamce kan gadon Marasa Lafiya awani Daki na Musamman Cikin Wani kayattacen Asibitin kudi Dage U.S Babban Birnin America,Fara mace ce Wacce Ba inda ta Baro Nene a kama Sai dai afizge Tana Diban Kama da Zain,Rumgume da Jaririyarta sai Megidanta Dake Gefenta Jawaad da Yaronsu Dan Shekaru Uku da wani Abu Jalal.
Cikin Farinciki Da Jin Muryan Dan"uwanta Tace"Aboki Zainullahi Yauwa..Ashe ka samu Labari..? Yana Shafa Sumar kansa yace"Eh yanzu Mukayi Mgana da Firstlove Take Fadamun Ta Fara Rigiman sai Taje nace ta bari na koma Gida sai Muyi mganar.."Zareena na Dariya Tace"Wlh da gaskiyanta ita da Zafira ba wanda ya Taba zuwarmin gwamma kai da Haddir kun Rakoni Lokacin da Umma zata maidani Wannan Karon Tunda ba Gida na Haihu ba Ina Bukatar ganin Duka Ahalina.."
Zain yace"Insha Allahu karki Damu Abokiya Zareena ga Ummamki zata yi Kokari Taga Ta isa kan Lokaci.."Ya karishe Fada yana Dariya Zareena tace"Fadi ka kara Gobe Abba yace Min Umma zata tafi Lagos yama Mijin Inna Hannatu mgana zai nema mata Flight din da zai Tashi Da Daddare da Safiyar jibi zata iso nan din..'
Zain yace"Uhm kaji masu Umma...."Zareena Tace"Kwarai wanda Bai da Umma kuma Sai Jin Haushi.."Zain yace"A"a Fadi ma wanda bai Dashi Ni ina Da Neneta.."Dariya Ta saka kafin Tace"Yanzu muka gama mgana da Aboki Haddir yace min ya kiraka ka Baka Daga sai nace bari na gwada kiranka nagani sai gashi kuma ta Shiga..Gamu asibiti ammh yanzu za"a bamu sallama mu koma Gida.."
Zain yace"Eh naga Kiransa Ban Kusa da wayar ne..Allah Sarki Abokiya Zareena Allah ya Raya Jalal yayi kanwa kenan Ina angon Karni mijin Zareena.."Tana Dariya Take kallon Mijinta Lokaci Daya Take Fadin"Gashi a gefena..Ga Jalal mana yana gaida Uncle Zain,nidai Har kai da Aboki Haddir ku Taho Don Allah Kila sai ya samu Wata Yar Baturiya anan su Daidaita Tun Da naga alaman ya Fara zama Tazuru ba Aure.."
Zain ya Saka Dariya Yana Fadin"Wlh ai yama zama Tazuru kawai ya jira in Wannan Jaririyar ta Girma Sai ki bashi Ita ya Aura..."Zareena ta saka Dariya Harda Jawaad Dake gefensa Tunda Wayar a amsa Kuwawa aka sakata Zareena Tace"Kai mugu ne Aboki Zain Sai na gayamai.."Zain yace"Gayamai ko yaji Haushi nan da Wata Biyar musha Biki..Haddir fa ina jin Ko Budurwa bai da ita.."Zareena ta kada kai Tana Fadin"Zai yi ne in Lokacinsa yayi da yardan Allah.."
Zain yace"Allah ya yarda..Ba Angon karni Wayar mu gaisa..Nan ta mikama Jawaad wayar ya karba suka gaisa da Zain ya yi mishi Barka Daganan sukayi Sallama Bayan sun gama wayar ne Sai ya Kira Nene nan take Shaidamai Haihuwar zareenan yace sunyi mgana Daganan ya tada Motarsa ya Nufi Gida,Koda yaje chan Rigimar Zainarsa ya tashi kan ya barta Taje sunan Zareena ba yadda ya iya Dole ya amince Sai da ya koma Gida sukayi mgana da Haddir inda yace Daman Zareena ce tace ta nemi Wayarsa bata samu ba,Cikin Dakile Zencen Yace mai Sunyi mgana Daga Haka ya katse Kiran Saboda Bayaso Haddir din ya Jefomai Tambayan Ina yaje har ya Kirashi bai Daga ba.
Washegari da Safe kan ya Tafi aiki ya Biya Gida Ya gaida su Nene nan yaji Tafiyar Umma yau zata Bi Jirgi zuwa Lagos,Bai sani ba kawai Umma tace mai Tare da Zainarsa zata tafi mamaki ya kamashi Yace ma Umma"Umma na Dauka sai Zuwa Suna Sauran kwana Biyu Lokacin Jirgin da wadanda zasu Tafi Sunan ya samu..?
Umma Ta kalleshi Tana Fadin"A" a Tare Da ya'yana zan Tafi...Ta kano zamu Tashi Zuwa Lagos Zafeera nachan na Jiranmu."Mamaki ya kama zain kawai sai ya Fara Tura baki yana Fadin"Nifa Umma ban amince Tatafi yau ba gaskiya.."Umma bata kulashi ba Ta kalli Nene Tana Fadin"Nene Gayama D'anki Da yata zan Tafi Yaji da wai ma.."Daga Haka Tayi Shigewar Daki Ta barsu nan Nene ta Lallabashi ya yarda,Dole ya Kira Zaina yace ta Shirya zata Bi Umma Ta Fara Murna tana Tsalle Ta Fara Shirya kayanta ta Kira Laila ta gayamata Ta kuma ce ta Dinga saka mata Atendence kafin ta Dawo Da haka sukayi Sallama,Saboda Zumudi Ko Ta Jira Zain din ya Dawo batayi ba ta Hado kayanta zuwa Gida,Sai da tazo Taji Labarin Harda Zafira zasu Tafi ta fara Murna Nene da Umma na Musu Dariya Zain yana asibiti Halima ta Kirashi kan zasu Tafi Suna Gidan Alhaji Tsoho baro asibitin yayi yazo Sukayi sallama Daga Halima sai Umma Direba ya Tafi Dasu kano,Wajen La"asar suka isa,Salloli kawai sukayi suka Nufi Airport Dama sun ci Sa"a sun samu Jirgin Azman wanda zai yada Zango a Birnin Ikko Suka Shiga Bayan Inna Rukayyah ta Rakasu har Airport din Tana musu Fatan Dawowa lafiya Domin bazata samu zuwa ba Inna Hannatu ce Zata tafi.
Jirginsu ya yada Zango A Murtala Muhammed International Airport Dake Birnin Ikko,da Misalin 7pm na yammah Direban Gidansu Inna Hannatu yazo ya Daukesu Zuwa Gidanta Dake Victoria island,Nan sukaci Abinci sukayi Sallah Ba zencen zama Domin Jirgin Karfe 11:30pm na Dare zasu bi Zuwa U.s Babban Birnin America.
Koda 11pm Tayi a Airport Tayi Musu Daman Mijin Inna Hannatun ya Riga yayi musu Bucking Tunda Tafiyar Harda Ita Lokaci nayi kuwa Jirginsu ya Daga Basu isa ba sai Washegari da Hantsi Dama Tun Suna Lagos Sunyi waya Da Zareena sun gayamata Lokacin Hawan Jirginsu ita kuma sai ta Kin Taci Lokacin Saukarsu Suna Sauka suka ga Jawaad da Dansa Jalal Sunzo Daukansu a Filin Jirgin nan suka Rankaya sai Jerin Estate din da Ma"akatarsu su Jawaad ta basu Umma ce kadai Ta Taba Zuwa Lokacin Da Zata maida Zareenar Bayan Jawaad din ya kawota Gida Ta Haifi Jalal Lokacin ya samu Hutun Karshen Shekara ne sai suka Tattaro Gabadayansu Zuwa Mahaifarsu Sai bayan Ta Haihu Tayi Arba"in kana suka Dawo Da Rakiyar Umma da na Mama Safiya Matar Dadyn Abuja,Tunda Daman Tun Dawowarsu kasar ba wanda ya Taba Zuwar mata sai wannan Zuwan Wanda Bakin Zareena yaki Rufuwa Saboda Murnan ganin Ahalinta.
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
1️⃣1️⃣
"Sai da su Halima suka kwashe Wajen kwana Goma a kasar ta U.S kafin su Dawo,Kwanansu Hudu da zuwa akayi Suna Yarinya taci Sunan Umma Wato Fatima,Suna Kiranta little Umma Washegarin Suna sai ga Baban Kaduna da Mom Ikilima Sun Biyo Sun ga Zareena da Bby kwana Daya sukayi suka Wuce Cyprus Wajen Sadiq karami Chan Yake Degree dinsa Yana Shekara ta uku achan.
Tafiyar Halima Ta saka Dina Tayi amfani Da Wannan damar Kusanci ya kara Shiga Tsakaninta da Zain wanda take iya bakin kokarinta Koda yaushe suna tare acikin asibiti ne gidanta ne,Ita take Dauke mai Kishiruwan Zainarsa,Duk da baya Jin Dadin Hakan dayake yi Ammh kuma bashi da wani Zabi,Haddir kuwa Ransa ba karamin kuna yake ba in yaga Zain da Dina suna Tare Saboda ya sani Shedaniya ce Kuma bawai ya yarda da kalaman Zain Din bane bama Shi kadai ba Mutane Da Dama suna Dora musu Zargi,Ganin Abun nasu yayi yawa ne yasa ya yanke Shawaran zai yi ma Zain din mgana Tunda yanzu har Fita Suna Tare da Dinar Wani Lokacin da Motarta wani Lokacin da Motarsa Cin Abinci kuma Tun Farkon Tafiyarsu Umma yake zuwa Wajen Nene yana Ci ammh yanzu sai dai Dina Ta jashi Zuwa Waje Su je chan suci Abinci ko kuma ta Jashi Gidanta Su je chan suyi Watsewarsu in Sun gama ta Sulala musu Ko Indomie ne Suci Su Dawo Cikin asibiti Abubuwa dai gasunan ba Tsari Wanda Haddir din yake Tsoron Faruwar waani abu.
Ranar sun Dawo Daga Resutarant Cin Abinci Bayan sun Faka Motarsu a parking Space,Sun Fito Motar Dina ce ita ke Driving Din Motar Dukkansu Sun Fito Suna Dariya Fuskarsu na Bayyanar da Annurin Da Suke Ciko karo Suka ci Da Haddir ya Fito Daga Cikin asibitin zai Fita da kallon Mamaki ya Bisu Dashi Daga Zain Din Har Dina,Zain kuma kallon kallo Sukama Juna kafin Zain din ya kauda kai Dina kuwa Data gaida Haddir Kin amsata yayi sai ma kallon Tsana Daya watsa mata yana kallon Zain Lokaci Daya Yana Fadin"Zain ina son mgana Dakai..!
Yafada Cikin Kakkausan Murya Juyowa Zain yayi yana kallonsa Kafin ya kada kai ya kalli Dina yana Fadin"Shiga ciki gani nan Tafe.."Daga haka ya Juya ya Bi bayan Haddir wanda ya karisa Wajen Motarsa yana Bin Dina da wani kallon Tara saura kwata Ita kuma kai kawai ta gyada kafin ta wuce zuwa Cikin asibitin Tana wani Takun Isa.
Zain na karisowa Kusa da Haddir ya karkace Kai yana Fadin"gani Lafiya ka ke son ganina..? Ido Cikin Ido Haddir yace'"Meka yi kenan Zain..? Kasan Ma"nar haka kuwa..?
Gyara Tsayuwa Zain yayi yana Fadin"Me kenan..?bangane inda ka Dosa ba Mallam.."Haddir ya Murmusa yana Fadin"Karka Raina ma kanka Hankali Zain..Kagane inda na Dosa ina mgana ne kan Wanchan yarinyar Dina,miye yake Hadaka Da ita..? Muharamanka ce..?na lura dakai kwana Biyun nan kun wani kulle ne wanda kuma Nake zargin Ba ta alheri bace..!
Zain ya wani Cije baki kafin ya fara mgana"Bangane Kaga mun kulle ba..?wannan wata irin mgana ce Karfa ka manta Dina Bayan Abokiyar aikina Abokiyar karatuna ce kuma Kawata ce akwai illah ne Don kaganmu Tare..? Kuma wani irin Ba alheri bane kake Fadi Me kake son Fadi...?
Kai Tsaye Haddir yace"Kafini sani..Ina Zargin kun koma Ruwa Kaida Ita kuma Faruwar hakan kamar Barazana ne ga Zubewar mutumcinmu Da naka gabadaya.."Da sauri Zain ya Tareshi Yana Fadin"Tsaya mallam kasan kuwa Zaton Zina... ? Ko kutu akaje Sai ka kawo Sheda Hudu suma sai sun ganin ma Idanuwansu Turmi da Tabarya kana da wannan Shedar ne..?Mganarka kawai kake wanda kuma Ra"ayinka ka Fada mallam Ni babu komai Tsakanina da ita sai na abokiyar aikina ce Fakat.."
Ya karishe Fada Cikin Son Nuna Bakomai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 32