Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Fizgo Zaina ta Mikar da ita tsaye wanda yasa Zain ya Dago Idanuwansa Jajir yana Kallonta Cikin kaifin Idanuwan Uwa da Danta Take kallonsa Shima haka Cikin Karaya yace"Ummmaa..! Kai ta kauda Kafin Ta Kama Hannun Zaina kawai ta Nufi Hanyar dakinta da ita Cikin Murya wacce ba Sauti yace"Don Allah Umma ki yafemin...Ki yafemin ki bani Matata itace Rayuwata.."Cak Umma ta Tsaya sai kuma kawai ta Cigaba da Tafiya Har gadon Ta kai Zaina ta Zaunar da ita ganin Tana Neman Shidewa ne Saboda Kuka yasa Ta Zura mata ido Cikin Takaichinta Tana Fadin"Ko Na barki zaki Bishi ne..? Da Sauri Ta Girgiza kai Cikim Kuka kwafa Umma Tayi Tana Fadin"Toh ki kiyayeni Da min wannan kukan mara amfani..."Daga Haka kawai ta Fice Daga Dakin Harda Turo mata Kofa kan gado kawai Zaina ta Malale tana Sakin kukanta Zuciyarta ta Kasu kashi Biyu ne na Farko Kaunar Zain da Tsausayinsa na Biyu kuma Kishinsa da kuma Bakinciki Wanda yaki barinta Ta Kalleshi Lokacin Dayake kuka yana Rokonta Gafara. Umma kuwa Falon Ta koma ta Iske Nene Rumgume da Zain yana kuka Tana Lallashinsa Mirmishi Takaichi Tayi kafin tace"Nene ki gayama D'anki...Ba yata bace Rayuwarsa wannan Dadarion nasa Uwar Dansa ko yarsa itace Rayuwarsa Ita zai je ya Dauko tamai Duk Abunda Mata kema mijinta Dama ai sun saba.."Daga Haka kawai ta kada kai Zuwa Dakinta Zuciyarta kamar Tayi Bindiga in ta Tuna da Abun kunyar da zain ya Jawo musu. Zain ya gama Sarewa da almarin Umma cikin Karaya da Zubar kwallah ya Dago yana kallon Nene Lokaci Daya yana Fadin"Nene Umma ta Tsane ne kamar yadda Abba ya Tsaneni.."Kansa ta Shafa Tana Fadin"A"a kadaina Fadin Haka ka Tabajin Inda Uwa ta Tsani Abunda Ta Haifa da Cikinta?ko kuma Uban daya Tsani Dan sa wanda ya kasance mafi Soyuwa Garesa..? Da Sauri Zain yace"Nene yana Faruwa..Tun Ballatana Yaron in ya kasance yayi watsi da Tarbiyan da suka bashi da yardansu..."Yafada Yana Runtse Idanuwansa Cikin Kunar Zuciya Kansa Nene Ta Shafa Cikin Son Kwantar mai da Hankali tace"Ko Daya..Koda Ya kasance Haka yarona zasu mai afuwa Domin Shima Dan adam ne wanda Baya Wuce Kuskuransa..Basu Tsaneka ba Bacin Rai zai sakesu Lokaci Kadan Insha Allahu kaji ko..? Kura mata ido Cikin Samun Salama da kalamanta yace"Zasu yafemin Nene..? Kema zaki iya yafemin Abunda na aikata gareku naja muku Abun kunya Nene ni kaina ina Jin kunyar kaina da Abunda na aikata ."Yafada yana kokarin Durkusa mata da Sauri ta Dagoshi Tana Fadin"Basai ka Dukamin ba Ni Dama uwace mai afuwa gareka ammh kuma mai Kokarin Doraka hanyar gyara..?Meyasa ka zabi Yin Tarayyah da matar da ba taka ba yarona..? Wannan Dabi"ar Ba ita na Koya maka Tun kana karami na Karantar dakai Kallonka iya Halas Dinka ne ba Haram ba yarona.."Cikin Nadama ya Riko Duka Hannuwan Nene yana Fadin"Hakane Nene Wlh kina gayamin Ammh ban yi aiki Dashi ba..Da ace nabi mganarki da Abunda Addinina ya Hanene da Ba haka ba ammh sai na Bi Son Zuciyata Nene..Wlh Tallahi Neneta Daga baya nayi Nadama naso ya kiceta acikin Rayuwa sai Abun ya gagara na Rasa Dalilin wannan Bala"in.."Yafada yana Sakin Numfashin Nadama da Danasani.. Shuru Nene Tayi Tana kallonsa Tana wani Tunani aranta kafin  tace"Shikenan kadaina Kuka kuma ka Daina Damuwa kajiko..Ina Tare dakai Har Abada yarona kuma bazan Runtsa ba Sai naga komai ya Daidaita Karika Cin Abinci kaji..?kaci Ferfesun dana aika maka Dashi..!? Kai ya Girgizamata alaman A"a Cikin So da kauna ta Shafa Kumatunsa Tana Fadin"In ka koma Gida kaci kaji ko..? Ina wayarka..? Cikin Kasala yace"Tana gida Tun Ranar dana Kasheta ban kara kunnata ba.."Nene tace"Ka kunna wayarka Don in Rika Jin Lafiyarka kar ka kara Zuwa Tunda yace bayaso kaga bai da lafiya kada Hakan ya jawomai Wata matsala Zuwa gaba in komai ya Daidaita da kansa zai Kiraka kaji ko..? Cikin Kura mata ido yace"Nene Matata fa...? Umma ta Hanani ganin Matata..?cikin son kwantar mai da Hankali Nene tace"Itama din zata Dawo kaji ko..? Umma ta isa ta Rabaka da Halima ne..? Da sauri yace"Ko Mutuwa ce tazo Sai dai Ta Daukemu Tare In ba haka ko Ita bazan Taba bari Ta Daukemin Rayuwata ba Ta tafi ta barni ba.." Ya karishe Fada Cikin son Tabbatar da mganarsa ba Nene kadai ba Hatta Haddir Dake gefe sai da ya Dara Cikin Tsausayama Zain domin baya Tunanin Umma zata maida mai Halima sai dai indan Alhaji Tsoho ne ya tsawatar mata Abba ne kuma awannan karon bazai goyi bayan Dan nashi ba. Cikin Dariya Nene tace"Toh kagani..? Zata baka Matarka ko koma Gidanku kuci gaba da zaman Auranku.."Da sauri yace"Insha Allahu Neneta..Shiyasa nake matukar Kaunarki Uwata Kinfi kowa Fahimtata.."Yafada yana Kissing Din Hannunta kansa ta Shafa Tana Fadin"Allah yayi maka albarka...Ka rika addu"a kaji ko Domin Tsari Daga magautan Duniya kaji ko Yarona..? Kai ya gyada mata yana Fadin"Insha Allahu Neneta..Ammh zan Dinga zuwa koda Abba zai koreni ne..'kai Nene ta gyada mai kafin tace"Ba yanzu ba...kabari zuwa Jibi Haka Lokacin yadan Sauko kagane..! Jinjina mata kai yayi kafin yace"Shikenan Neneta..Zamu Tafi Chan Gidan Alhaji Tsoho.." Cikin So da kauna Ta Riko Hannunsa Tana Fadin"Muje na Rakaku Har waje...Hadiru muje.."Daga haka suka Rankaya Zuwa Haraban Gidan sai Lokacin Umma ta Juya zuwa Cikin Dakinta Daga Jikin Kofarta Inda Ta makale Tana Hangen Abunda ke wakana afalo Kwalla Take Sharewa Tana Sakin Mirmishi Cikin Takaichi tace"Maraba dake Salihar Uwa Nene...Nayi alkawarin Zan tsaya a Uwar Halima kadai Shiyasa bazan Taba bari wani ya Fahimci Raunina a kan Zainullahi ba..! Tafada Tana Ta Sharan kwallah Cikin Rauni da Sarewa Gefe Daya kuma Tana jin wani karfin Gwiwa kan Hukuncin Data yanke na Raba Auran Zain da Zaina wanda Har Cikin Zuciyarta Take jin Kunar Abun ammh bata da yarda Zatayi Ko don Zain yake Danta bai kamata ta bari Zaina ta kara Cutuwa ba Itama Ya' take gareta Shakikiya wacce ta sami asali Daga kaunar Datake ma Mahaifiyarta Maryama. Nene Bata Dawo cikin Gida ba Har Sai da Taga Tashin Motarsu Zain da Fitarsu Daga Gidan Tana Shiga Falon suka Ci karo da Umma Wacce ta Fito Daga Dakinta kallon Kallo sukama juna kafin Umma Takauda kai Ganin Nene ta kura mata Ido Dakin Zaina Ta Shige gabanta na Faduwa Kada Nenen ta Fahimci Tayi kuka Mirmishin Takaichi Nene ta saki kafin ta kada kai Zuwa Shashen Abba Domin Taga Halin Dayake Ciki. Su Haddir kuwa suna Zuwa Gidan Alhaji Tsoho suka Iskeshi yau a haraban Gidan bayan an sakamai katuwar Darduma ammh Shi yana saman Kujeransa ne saboda zaman kasan zai mai Wahala ne,Jalal ne agefesa yana ta mai Gwarancinsa Shi kuma Alhaji Tsoho Muwadda Malik ne ahannunsa yana Dubawa Tunda Motarsu Ta Shigo Haraban Gidan ya Dago Daga karatun Dayake yana Kallonsu Har suka Fito Daga Motan Shi da Haddir suka Jero Zuwa Garesa Bakinsa ya Fara Motsi wajen Neman musu Tsari Daga Mutum da aljan Domin har yau har Gobe Haddir da Zainullahi Sune Sanyin Idanuwansa Soyayyar Iyayansu Gabadaya Ta Koma kansu. Har suka kariso yana Kallonsu Cikin karantar yanayin kowanensu Ramar da Zain yayi tafi komai Dagamai Hankali Jalal ne ya watsar da Tab din Hannunsa ya isa garesu ya Rumgumesu yana musu oyoyo Zain ya Riko Hannunsa yana Shafa kansa hakama Haddir har Zuwa gaban Alhaji Tsoho Gabansa suka Gurfana kamar masu Neman Gafara Zain kuwa Rauninsa ya bayyana yana ji Haddir na gaida Alhaji Tsohon ya amsa Rabin Hankalinsa na Wajen Zain wanda yayi Shuru ya Dukar da kansa kasa Yana Jin Kunyar Alhaji Tsoho Shiyasa ya kasa Dagowa su Hada Ido.. Cikin Dattako Alhaji Tsoho yace"Zainulallahi...! Jin ya kira Sunansa ya sa ya Dago Kansa yana Kallonsa kwallah suka Tarumai Waje Daya Cikin Mamaki Alhaji Tsoho ke Fadin"Subnallah Ciwon Har yakai Haka ne..?kaga yadda ka Rame ka lalace Cikin kwana uku Kachal.."Jin haka yasa kawai ya Fara Rarrafawa Zuwa Kusa da Alhaji Tsoho ya Rike kafansa Cikin Rawan murya kamar zai Fashe da kuka yace"Ka...ya...fe...Min Alhaji Tsoho..Ina jin kunyar Hada ido Dakai.. ka Yafemin batamaka Sunan Zuru"a Danayi na Tuba nabi Allah kuma Nayi alkawarin Bazan kara Sha"awa ko Jin ina son aikata Zina ba Insha Allahu.."Yafada Lokaci Daya yana Fashewa da kuka Saman Cinyar Alhaji Tsoho ya yada Kansa yana Rera kukansa kamar Wani karamin yaro Cikin Kukan ne yake Fadin"Kowa ya Daina Sona saboda Zunubai na..Abba na Fushi Dani naje gidansa ya Koreni Umma ma Taki Saurarana,Ta kuma Hanani mgana da matata Nene ce kadai Mai Sona itace kadai ta iya min afuwa da Tarin Laifukana Don Allah Alhaji Tsoho kada kaima ka Juyama Rokona Baya in kaki yafemin bansan Kuma wa zan kama ba.." Yafada Cikin Karayan Murya Shuru Alhaji Tsoho yayi Zuciyarsa na Sauka a hankali Ahankali Littafin Hannunsa ya Mikama Haddir Shi kuma da Sauri ya saka Hannu Biyu ya karba,Kana Alhaji Tsoho ya mika Hannunsa saman kan Zain ya Dafa  Cikin Muryan Tsufa yace"Bar wannan kukan Zainullahi...Bar wannan kukan..Domin bai kamaci Namiji kamar ka dashi ba..Tashi bari kaji ko" Yafada Cikin Sanyin Murya Cikin Salama da Yayewar Kunci Zain ya Tashi Daga Kafan Alhaji Tsoho yana Fadin'Ka yafemin..? Alhaji Tsoho yace"Ni daman bani kayi ma Laifi ba Zainullahi Ubangijinka kayi ma Laifi kuma Tunda kace kayi Taubatun nasuha...Shikenan Allah ya yafemana Gabadaya Allah kuma ya Tsaremu Da Imaninmu ya Rabamu Tabewa duniya da Lahira.."Cikin Farimcikin Zain da Haddir suke amsawa da Ameen Karo na Farko da Zain yaji Wani Sauki acikin Zuciyarsa Tun Faruwar lamarin. Cikin Son Sauke wata Salaman Zain ya kalli Alhaji Tsoho yana Fadin"Ina ta Rokon Allah Gafara Kan Zunubai na baya..Shin Allah zai Gafartamin...? Alhaji Tsoho yace"Sosai ma ai Allah Gafurun Rahimun ne Zainullahi Komai Girman Laifinka awannan Duniyan Allah mai Rahma ne kuma mai Jinka Kaga dai Girman Laifin Shirka ko..? Toh Shima Allah na yafewa matukar mutum yayi Tuban Gaskiya kuma ya Roki Allah Gafara,zai gafarmaka Saboda Haka Ka Cigaba da Istigifari Allah mai yawan karban Tuba ne Allah ya yafe mana.." Haddir da Zain suka amsa da Ameen wanda ya Zarce da Fadin'Allah na Tuba...Na Tuba.Astagafurulah..Astagafurullah.."Yake ta Fada Alhaji Tsoho na kallonaa yana gyada kai kafin Ya cigaba da Fadin"Shiyasa ako da yaushe ina gaya muku kuma zab kara Gaya muku..Komai kuke Arayuwar wannan kada ku bar Tafarkin Allah Domin Wanda ya Bijerema Allah zai ga samakon Haka Tun a Duniya..Zina Babban Zunubi ne da Allah yace Kada mu kusanceta Domin Ita Zina abace mai kawa mai kuma Dadi,Kusanta ta na Rage kima,Da rage Daraja Rashin kwanciyar Hankali Tana saka Rashin kunya tana saka Tabarbarewan Rayuwa da arzikima Gabadaya Kaga kenan Bata da wani amfani Ga Rashin Kwanciyar Hankali kullum Shedan na kawata mana ita ammh mai Kusantar Zina Bashi da wani kwanciyar Hankali Gwara kada mu Kusanceta Ma"ana mu kauce ma zama Cikin Shedanun matan da zasu Ribacemu aikata ta Allah yama na Tsari.." Dukkansu Jikinsu yayi sanyi Barin ma Zain wanda yayi Kasake yana Sauraran Alhaji Taoho kafin ya amsa da Ameen Cikin Rauni yace"in kagaya maka wata gaskiyata Alhaji Tsoho Zaka yarda dani..? Cikin Dattako Alhaji Tsoho yace"Saboda me bazan yarda dakai ba Zainullahi Ai har yau har gobe akwai yarda tsakanina Dakai fadi mganarka karka Damu..' Da Sauri yace"Wlh ban Taba Jin Natsuwar Zuciyata wajen aikata wannan Zunubin ba Alhaji Tsoho..Tun bayan Barinmu London Nadai na Neman kowacce mace Alhaji Tsoho ina Son Zaina Har cikin Raina ba kuma na Jin Dadin cin Amanarta aboye..Sai dai Bayan Dawowarmu gida Naji Komai ya Fita akaina ammmh sai me Sai na rika jin In ban Kusanci mace ba kamar zan Mutu macen ma bakowa ba Sai Dina Ita kadai nake jin im ban je gareta ba Zan iya Mutuwa..ammh Wlh Tallahi Na Daina na Tuba har Cikin Zuciyata.." Kura masa Ido kawai Alhaji Tsoho yayi yana kallonsa acikin Ransa kuma yana Fadin Haba Biri yayi kama da Mutum Koda Hali yasa Jikansa ya gamu da Shedancin mace Cikin Muryan Tsufa yace"Na yarda Dakai...Hakan yana Faruwa ne in muka Manta da addinmu muka Shige Cikin wadanda ke da Bambamcin al"adu da addinmu da kuma Cakuduwa Cikin Mata Wanda sam bai dace ba Shiyasa wani Lokacin Tsantseni da kamun kai Ba iya ga Mace ba harga Namiji ma yana da amfani..! Zain yace"Hakane Tabbas Alhaji Tsoho..Nima Harda zama Cikinsu da kuma Biyema Abokan Karatuna wadanda ba addinmu Daya ba.."Kai kawai Alhaji Tsoho ya gyada yana Fadin"Allah ya tsare mu.."Suka amsa da Ameen kafin ya kalli Haddir yana Fadin"Hadiru ku samo Wani Likita wanda zai maye Gurbin ita Dinar.." Kai Haddir ya gyada kafin yace"Ok..Shikenan.."Da Sauri Zain yace"Don Allah ina neman Wata alfarma Alhaji Tsoho..? Yana Kallonsa yace "Ina Jinka."Kansa ya maida kasa kafin yace"Ina so Don Allah ka bada izinin azubar da Cikin nan.."Da Sauri Alhaji Tsoho yace"A'"a badani za"ayi wannan Danyan aikin ba..Na Farko ance Cikin Kuskure ne Cikin ya Shiga shii kashe Rai fa..? Shi ai da gangan ne...Zata Dawo Gidanku ta Haifeshi Daganan Ta tsarkama sai a Daura muku Aure indai Ina da Rai ko bani Dashi zan bar ma Ubanninku Wasiyar haka.." Cikin Wani yanayi Zain yace"Toh Ta zauna Gidansu ta Haifa mana Alhaji Tsoho.."Dakuwa ya aika mai Dashi kafin yace"Gidan ku Zata Haifeshi Duk wa yajawo in ba kai ba..?kuma Gidan Usmana nace ba Gidanka ba.."Cikin kunyar kansa yace"Ni bana ko Son ganinta ne Alhaji Tsoho..". Cikin Tura Haushi yace mai"Allah yanzu kuma.? Dawa ya kai ka kake Jure kallonta Har aka kawo Yanzu..? Jin Alhaji Tsoho yace hakane yasa ya Runtse Ido yana Fadin"Kadda ra ce da Jarabawa..ammh Allah ne Shaidata Firstlove ce Kadai macen Da nake so kuma itace Rabin Rayuwata Gabadaya.."Hmm kawai Alhaji Tsoho yace Wanda Yasa Sai da Haddir ya Murmusa nan fa Alhaji Tsoho ya Cigaba da Musu Nasiha yana Nuna musu Illar kusantan Zina ba Zain kadai Da tayi ma Illah ma Hatta Haddir yaga illanta kuma ya Tsorata ma da kallon Abunda ba Halas Dinsa ba. Sun Dade nan wajensa kafin su Dunguma Zuwa Cikin Gida suka barsa Shi kadai ya Cigaba da karatunsa,Dama Jalal ne kuma Tun Dazu ya Ruga Cikin Gida,Acikin Gidan Itama Hajiya Mama zain ya Duka yana bata Hakuri ta Dagoshi ta Sharemai Hawaye tace bakomai Ya nemi Gafaran Allah,Sun dan Jima agidan ganin Zain din yadan saki Jikinsa,suna ta Hira da Zareena da Hajiya mama sai ga Tabawa Itama akayi da ita kafin suyi musu sallama suka Tafi Sun zo sun yi ma Alhaji Tsoho sallama ne ya Dago kai yana kallon Zain kafin yace"Gobe ka Shirya ka koma Bakin aikinka..Ka Cire damuwa Insha Allah bayan Bikin Hamdiya zan Daidaita komai.." Daga haka suka mai sallama suka Tafi Daganan Direct asibiti Zain yace su wuce kaawai Domin yana Jin yadan samu Salama kaso mafi Kadan,cikin Fargabansa ya Ragu acikin asibitin ma sai mamakin Ramar Zain ake nan dai yace bai da lafiya Daman Zain ya Shigar da Korafin Rashin Lafiyar Zain din Office din Haddir ya zauna bai iya Duba patient ko Daya ba sai Zuwa Gobe sai dai yana Zaune Haddir din na Duba maraasa Lafiyar sallah kadai ke Tadasu sai Xuwa yammah suka bar Cikin asibitin Zuwa Gidan Zain din Bayan sun Tsaya Bisa Hanya sunyi sallar mangariba. Ferfesun da Nene ta aiko da Zain Dashi Shi suka ci suka Koshi..Haddir yaja wayarsa yana Amfani da ita Shima Zain din Wayar nashi ya Dauko yayi ta ganin Sakonin mutane na Jinsa Shuru Sakon da yafi bata mai rai Shine sakon Dina Tana Ce mai wai Unborn yahanata Barci Saboda Bakinciki bai san sadda ya saki Katon Tsaki ba wanda sai da Haddir ya Dago yana kallonsa bai dai Tambayesa ba ganin ya Tashi yana Sakin Tsaki zuwa Cikin Bedroom dinsu ya Bishi da kallo kawai yana Fatan komai ya Daidaita kamar yadda Abun ya Fara Daga yau. ***** *Bayan Sati Daya* Bayan Sati da Daya da Faruwar Lamarin daya wargaza Farincikin Duka iyalan Dr.Saulawa Zuwa Lokacin Duk Wanda ya kamata yaji Abunda ya Faru ya Riga yaji. Bangaran Dina kuwa Tuni Umminta Maimuna ta iso Daga Sudan Wanda Kwamishina da kansa ya zaunar da ita ya gayamata Komai kuka ta saka Wiwi kuma ta bashi Duka Laifi Domin Lokacin sunyi Sunyi ya basu Rikon Dina yaki gashi ga Abunda ya Faru Abu Daya ya sanyayamata rai karban Cikin da Iyayen zain sukayi da kuma Komawarta gabansu ta Haihu ayi musu aure lalle ta Shaida Gidan Gidan Dattako ne da karaminci Ammh Tayi ma Dinar Zaga zaga kamaar ta Daketa Daga Karshenta ta kara Dorama Hajiya Batula laifin Rashin Rike amanar Dinar ita kuma tace Daga Mahaifinta ne ya Riga ya sakar mata komai Abunda Taga Dama Takeyi. Allah ya Taimaki Dinar Cikin nata bamai Laulayi ba ne Amai ba koda yaushe take yi ba sai dai yana Sakata Cin Abinci Sosai da Cin kwalama ta Kara zama wata Baturiya Fatar ta na Sheke Abunda ke Daurema Hajiya Barula Kai Ganin Ko Damuwa Dina Batayi ba na irin Mace Tayi Cikin Shege ta Damu a'a ita kam Ma wani Farinciki Take da Tattalin Cikin kamar na Sunna Ita kanta Ummi Maimun din Abunda na Dina Tsoro ya koma Bata Domin ko Fargaban nan Bata Dashi Harkan gabanta kadai Takeyi ko ajikinta. Kwamishina ya Roki Ummi Maimun kan karta koma ta bari Ta Raka Dina chan Bauchi Su Tafi Tare Da Hajiya Batula Jin haka yasa ta Dakata da Tafiya ammh Tayi Shuru Da bakinta bata Fadama Kowa Daga Chan Sudan Abunda ke Faruwa ba ko Bakomai Dina kamar yata gareta Tunda Sara kanwa take wajenta sai ta koma ta samu Mahaifiyarsu Sameena ta Fadamata Tunda bai kamata ita aboye mata ba,Hajiya Batula ita ta Taimaka mata suka Hadama Dina Duka kayanta Waje Daya Kan sun Tsaida Ranar Lahadi Ranar da zasu maida ita Dinar Bauchi Wajen Alhaji Tsoho kamar yadda aka Tsara komai. Bangaran Zakiya kuwa sun kara Dinkewa da Dr.Imran ta sakamar Jiki ganin Gayen yasan Hannunshi kuma yana sakarmata Kudi Shashancinta kadai Take acikin gari ba Ruwanta Suna waya da Dina Duk Abunda ake ciki tana sane,Dr.Imran yasio yaji wanda yayi ma Dina Ciki da kuma Abunda yakai mganar Gidansu Zain sai Zakiya tayi wasa da Hamkalinshi kan cewa a matsayin Alhaji Tsohi na ma mallakin asibitin yana da Hakki Ya bincikin Abunda ke Faruwa da Ma"akatansa da Haka Ta Rufe Bakinsa Domin Har Abada Tana Mutumta Sirrin Dina kamar yadda Itama Take Mutunta Nata,Zakiya ko Tana so Ta Tuban ma Allah sai taji ta Kasa ta saba da Harkan Bariki da Harka da maza da kuma kama Manya kudade Bata iya bari kuma dan albashinta Tana ganin bazai Isheta Ta Famtama ma Rayuwarta ba,infact ma Tana ganin Bata samu irin Namijin Daya Dace da Rayuwarta ba ammh Duk Ranar data samu zata bar Rayuwar Bariki Tayi Aure kodon Faratama Babanta rai wanda kullum Taje gida mganar kenan Zakiya kiyi aure kibar wannan Rayuwa bata dace Dake ba kuma bazata haifar miki da D'a mai ido.. Sai tace"Zan yi Baba...Ammh sai na gama Tsayuwa da kafafuna bana son naje na Dawomaka irin Auran su Sahura ne..! ****** Ta Bangaran Zain an samu Cigaba Domin ya koma Bakin aikinsa aikin ya Fara Daukemao Hankali Daga Damuwarsa ammh fa Duk ya Sauya ya Rame ya zama wani Silent kamar ba shi ba Dina kuma Tuni Wata Dr polina ta maye Gurbinta,An cigaba da bama asibitin Gudummuwa kamar yadda ya kamata Kuma Kowa ya Tambayi Dina sai asanar dashi Ta ijiye aiki ne Da Ra"ayin kanta. Bangaran Abba ma ta Sauya Tunda yaji sauki Shima ya koma aikinsa sai dai game da Tsakaninsa da zain Ta na nan Jiya iyau,In Zain yaje gidan sai dai in yana Office ne ranar kuwa Daya Dawo ya ganshi ba zaman Lafiya Nene ce kadai ke kulashi sai Zainab dasu Saudart Zareena Bata nan Mijinta yazo ya Dauketa sun Tafi Katsina Umma da Abba Ko ya gaishesu basu amsa mai Zaina kuwa Bayan Ranar Ya kara Cin sa"a Umma na Kitchen ya Fada Dakin Tunda indai yazo bata bari yaje inda Take ya sameta kan gado kwance ya Bita ya kwanta Kusa da ita ya Rumgumeta yana Ta bata Hakuri ammh Zaina taki mgana sai kuka Ganin Taki yin Shuru ne yassa Ya Hade bakinsu Waje Daya Duk Kokarinta na ya saketa yaki Saboda yayi mata Riko na Sosai Dole Jikinta ya saki ta koma ta kwanta Tana kallonsa yana yadda yake so da Bakinta. Umma ce Ta shigo ta gansu Cikin Wannan Hali Ranar yaga Tashin Hankali Da Fushin Umma wanda bai Taba gani ba Tsawa Ta Dakamai Abunda yasa ya Gano ta Shigo Dakin kenan kuka kawai ta Fashe Dashi ludayin Miyan Dake Hannunta ta kwalamai agadon Baya Dama Tana Miyane Zuciyarta Ta bata Wani Abu ganin ta Fito bata ganshi a Falo ba kamar yadda yake zama kamar wani maraya gabanta na Faduwa ta Nufi Dakin sai kuma ta ganshi ya kwakwume mata y"a Cikin Hargagi Ta Rakashi Falon da Ludayin Tana Bugamai Tana hadin"Kasheta zakayi..? Na samu Ta Daina kuka Tana samun Cin Abincin Shine zaka zo ka maidata Gidan Jiya ko..?ka Rumgumeta Ubanka zatamaka..?ina Dadironka ko nace karuwarka kaje wajenta mana Wlh kar na kara ganinka kusa da yata Domin ita mai Tsafta ce ba Kazama ba irinka.."Tana gama Fadin haka ta koma Cikin Dakin Fuu Zain ya Bita da kallo yana Sosa inda ta Dakeshi da Ludayi Cikin wani yanayi yace"Samun Kamar Uwata aduniyanan sai An Tona..Mai Maida ya"yan wasu nata..My Mommh is Differnt and Special..' Ficewa Yayi Daga Gidan Batare ma Da yayi ma Nene sallama ba Kada Abba yazo ya ganshi ya jawo wani Matsala Umma kuwa Daki ta koma Wajen zaina ta sameta ta Takure kan gado Tana kuka Lebenta na mata wani Zugin Tsotsan zain yayi musu Gefe Daya kuma Tsausayinsa da Sonsa ya mamayeta Domin ayanayin yadda ya kamkameta yana Tsotsan bakinta na Tsabar yayi kewarta ne,Tunda Tanaji Jikinsa na Bari nan da nan wata Zuciya tace"Ke zaina dawo Cikin Hayyacinki kin manta Har ciki yayi wata ma karewarta..! Kika sani ko Daga wajenta yake..!. Tuna haka ne yasa ta kara Sautin Kukanta Umma na Shigowa itama Batayi Wata wata ta maka mata Ludayin Miyan Abayanta Tana Fadin"Rufemin Baki sakarya kawai Shashasha...! Gum Zaina Tayi da bakinta Tana Sosa inda Umma ta Daketa Cikin Hararanta Tace ganin Tana Kallonta"bar kallo na da wadanan kwalalan Idanuwan naki kafin naci miki Mutumci anan wajen..Ke sakaryace ace bansani ba ina nan ina miki yaki ki samu yancinki ammh baki sani ba ko..? Kina manne mai ko..! Tafi Chan wawiya karya yake da yana sonki da ganin Darajanki bazai barki kina Matarsa yaje yayi ma Wata Yar iska Karuwa ciki ba Harda bayan ya maidake sauna Daga baya yazo yana kwakwumarki.." Cikin kuka Zaina tace"Allah Umma bani na Kirashi ba ina kwance na naga ya shigo.."Cikin Bacin rai Umma tace"Ja chan meyasa baki kurman mai ihu ki kirani nazo naci mai Mutumci ba.? Wato kinyi mukus da bakinki kema kina so badomin Allah ya kawoni ba Kin kwakumeshi Don Ubanki har kin manta da Bakincikin daya Kunsa miki ko..!? Ita Zaina bata kara mgana ba Har Umma Ta gama Fadanta ta Fice Ta Bita da kallo Bakincikinta Daya yadda Umma Taga Laifinta alhalin ita bata ma san dashi ba Ganinsa kawai Tayi ya hau gado Ya zatayi Dashi..?kwalla kawai take Sharewa Ranar wuni Umma Tayi Tana Jin Haushinta Tayi banza da ita Ko irin Lallabanta Datake taci abinci yau din ko kallo Ta dai kawo mata abinci ta Dunkure mata nan Da taga Tana kuka baki ta Rike Tana Fadin"Ikon Allah don na miki Fada yasa kike kuka..? Yi hakuri In yazo Gobe ki bisa ku tafi..Ni nawa ido ne.." Jin tace haka ne yasa ta Marairaice Tana Fadin"Kiyi hakuri Umma kina Fushi Dani.."Kallonta batayi ta Fice ammh Ta Dan saki Fuskarta Shi ya sa ma Zaina taci Abinci Sosai ammh ko Rabi bata ci ba sai amai haka take fama kuma taki yarda Aje asibiti ita Kuma Umma bata son bata mata Rai Shiyaasa ta kyaleta. ***** Washegari ta kama asabar ne Tun safe sai ga Laila kawar Zaina ta Dira gidan tace Tunda ta Koma Gida Tayi ta Kiran Layin Zaina Tana Ringing ba"a Dagawa Kwana Biyu Daga Biyu kuma sai takejin wayar tana Kashe Dama zata Fadamata ne sun Fara Test tun Ranar Monday,Ganin Shuru Shuru ne yasa Taje chan Gidan Zainar megadi ya Tabbatar mata da Bata nan wajen Sati Daya Shiyasa ta yanke Shawaran zuwa Nan Domin tasan bata wuce Wajem Umma... Bayanin Da Laila ta korama Umma kenan ita kuma Umma sai

Chapter 25 of 32