Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta kare Jikinta kada Zainab ko Zafeera ko Umma wani gane kayan Jikinta ya Kirata,Allah ya Taimake ta har ta kusa barin Haraban Gidan bata Hadu da wani idon sani ba Tana Gabda Fita ne suka kusa cin karo da Haddir ya Shigo yana waya ganin Hankalinsa yayi gaba ne yasa sau Daya ta Waigo ganinsa yasa ta Juya da Sauri Ta na gyara Gyalanta Shi kuma sai da yace mata Tayi hakuri kana ya koma yana kallonta ganin yadda take wani Sauri kamar zata Tashi sama mamaki ya kamashi Ko dai Barauniya ce..? Ammh kuma kamar Dazu Da suka je gidan Abba yaga kamar wasu da kayan nan Dayake shi bamai wannan luran bane yasa kawai ya Cigaba da wayarsa ya Juya ya Nufi Haraban Gidan. Hankalin Zaina bai kwanta ba sai da Taga Ta Fita Daga Haraban Gidan Alhaji Tsoho kana ta Dago Ta kalli Gidan Ta kara kallo Hawaye na Zuba acikin Idanuwanta kafin Ta Furta"Umma ki yafemin..Abba ka yafemin...Goggo Halima kema ki yafemin...Firstlove da Ukti kuma ku yafemin.."Kafin ta Fashe da wani kuka mai cin rai adaidai kuma Lokacin ne Motar Zakiya Wacce Dina ke Ciki ta Faka nan kusa da Zainar bata ma Lura dasu ba Tana kallon Gidan Tana kuka sai Da Taji muryan Dina wanda ko Mafarki Tajita zata ganeta kana ta waigo Gabanta ya yanke ya Fadi Data gansu Saurin Juyawa Tayi Tana Rufe Fuskarta Lokaci Daya kuma Tana Tsallakawa Daga chan Dayan Hannu Da kallo suka Bita Dukkansu atamfa Riga da Sikat suka saka ammh fa kayan sun kamasu Zakiya ta Zubo attch din nan Dina dai bata saka ba ammh Itama gashinta waje ga wani mayafi kamar basu basu saka ba. Ta gefen ido Taga suna kallonta yasa ta Fara Tafiya da Sauri Da Sauri kamar wacce Zata Fadi Hannunta daya Damke da Sikat dinta da kudin Dake hannunta Ganin haka yasa Zakiya tace"Ita wannan fa..? Tana sauri kamar wata mara gaskiya..! Hankalin Dina naga Haraban Gidan Take Fadin"Miye naki..? Kila barayin nan ne da suke zuwa Sata wajen Biki..Tagama Diban Rabonta Zata kara gaba.." Ta Fada Tana kallon Bayan Zaina wacce ta Fara musu Nisa Cikin Wani yanayi kafin ta Kauda kai Zakiya ce Tace"Umh...Lalle ana Shagali kalli fa da Yadda Gidan ya cika da manyan Motoci kalli yadda Gidan ya cika fa Shine ke din acuceki sai ace ki zauna agida ke kadai.."Dina Ta saki Dariya Tana Fadin"Kyalesu...Ai na bar musu megadin gidansu yayi musu gadin gidansu..Nima sai nazo aci bikin dani nima ai na zama yar Dangi.." Zakiya Tace"Kwarai...Kuma ai mu ai abun kunya gaba muka bashi ba Baya ba..Kuma Tunda Dansu ya bari ya Shiga Tarkonmu sai Hakuri.."Dariya suka kara sakawa harda Tafawa Kafin Zakiya ta kashe Motarta su Fara Taku zuwa Cikin Haraban Gidan Daman Zakiya ce Tazo Gidan Taga Dina ita kadai duk sun watse sun barta Shine ta zugata kan ta Shirya Suma sai sunje Bikin Dama Dina nason Fita Ta gaji da zama waje Daya nan da nan ta Shirya suka bar Gidan,Megadi kadai suka bari agidan Hatta su Saudart Tun Jiya suna Gidan Alhaji Tsoho. Achan Haraban Gidan Alhaji Tsoho Kuwa Zain ne ke Ta neman Zaina bai ganta kuma Da Farko Zafeera ya Tambaya tace mai Tana Dakin Hajiya mama ya Shiga Ciki kuma Hajiya Mama tace yanzu ta Fita Tace zatayi sallama da Amarya Har wajen Yaje bai ganta ba Haddir ya gansa yana ta Neme neme yasa ya Tambayeshi wayake nema yace mai Firsrlove Haddir yace yaje wajen su Zafeera kila suna Tare. Wajen su Zafeera ya koma ya kara Tambayanta Tace mai Tana Ciki yace ya Shiga ciki ance ta Fito nan Haraban gidan Mamaki ya kama Zafeera Sai Ta Fara waigen Neman Zainar Tana Fadin"anya Hajiya mama Tana gani kuwa..? ukti bazata Fito Cikin wannan hayaniyar ba.." Zainab Tace'Eh mana mun ma ce..Ta Fito Taga Tafiyammu Tace Baxata Fito ba..Jakar ma Anty Zafeera yana Hannunta fa.."Zafeera Tayi Shuru kafin tace"Bari dai na kara Dubata Ciki.."Zain dai sai yaji gabansa na Faduwa Zafeera ta koma Ciki Har Dakin Hajiya Mama ba Zaina ba Dalilinta Ta Rude Lokacin bata ma Lura da Jakarta ba tazo Tana kara Tambayan Hajiya mama Zaina ita kuma ta Rantse mata Wlh Ta ganta Har sunyi mgana tace mata zata tayi sallama da Amarya. Sai kan Zafeera ya kara Daurewa ta Fito Haraban Gidan Tana kara Duba Zaina bata ganta ba sai ta Hango Zain din Tsaye Da Haddir Daga chan kuma su Zakiya na takowa garesu Zafeera ta Rike baki Cikinmamaki Take Fadin"Su kuma wadanan agayyar wa..? Kusan atare ita dasu suka iso ga su Zain,Haddir da zain baki kawai suka saki suna kallo su Dina Cikin wani Takaichi suma kallonsu suke cike da wani Mirmishi Zafeera Ta kallesu A wulakance kan ta saki Tsaki Tana Fadin"Ba kima.."Kafin Ta maida Hankalinta kan Zain tana Fadin'Wlh Ya Dakta bata aciki..Kuma Hajiya Mama ta Rantse min ita ta gani har sunyi mgana Tce xata je tayi sallama da Amarya..? Zain hankalinsa ya maida kan Zafeera ya ma manta dasu Dina yana Fadin"Bata chan wajenm..? Ko tana tare da Umma..? Yafada yana nuna inda Su Umma ke Tsaye suna Jiran Iyayen Hamdiya su sallameta,wasu Mutanen tuni sun Shigo Motoci Amarya kawai ake Jira ango ma Tuni Yayi gaba. Zafeera Tace"Anya.? Bata wajen Umma Ai kaya iri Daya kuma saka da tana Wajen dana hangota.."Haddir Da kansa ke gefe ya waigo Yana kallon Kayan Jikin Zafeera haka suma su Dina suna Tuna ai yanzu suka ga mai irin wannan kayan Haka Shima Haddir Cikin mamaki yace"Irin wannan kayan Dake jikin ki Zainar ta saka..?Da Sauri Zafeera Tace"Eh...Dani da Zainab da ita iri Daya muka saka kuma ga Zainab chan.."Tafada Tana nuna Jikin Motan da Zainab ke Tsaye Tana kallonsu ganin kamar hankalukansu ya koma kanta yasa ta Bar Jikin Motan ta Nufosu. Sai Lokacin su Dina suka Gane wa ake nema suka kalli Juna ita da Zakiya kafin suyi mgana Haddir yace"Indai kuwa wannan kayan ta saka Dazu Da zan Shigo naga wata mai irin kayan nan Tana ta Tafiya da Sauri Ban dai ga Fuskarta ba ammh har kusa Bangaxan juna mukayi Ta Rufe Fuskarta da gyalenta.." Gaban Zain da Zafeera Dana Zainab Data kariso Duka atare ya Fadi cikin firgici Zafeera Ta waro Ido Tana Fadin"Ka ganta kuma da irin wannan mayafin na Jikinmu..? Kallon gyalen yayi kafin ya gyada kai yana Fadin"Eh Tabbas Shine ajikinta.."Salati Zainab Ta saka Zain kuwa Hulan kansa ya Cire Cikin Tashin Hankali Da Sauri Zakiya tace"Indai kuwa Mai wannan kayan ne da wannan Mayafin muma muganta Tana ta Sauri sanda muka Tsaya da Motarmu." Da Sauri Zain yace"Tana ta Sauri Tabi ina kuma..! ? Zakiya tace"Bamu sani ba Tadai tsallaka Chan hannun daman Ta Fara Tafiya da Sauri Da Sauri.."Zafeera Taji wani Faduwar gaba kafin tace"Ina Ukti zata bata gayamana ba..? Ko gida ta koma tun Nan din Taga an cika Ga Hayaniya..? Da Sauri Zain yace"Muje Haddir mu gani..kila ma gida ta koma.." ya Fada yana yin gaba kamar zai Fadi Haddir ya Rufaamai Baya Suka Fada Mota suka bar Gidan,Su Zafeera kuwa ko Takansu Dina basu bi suka Fara Tambayan yan"uwa ko wata Taga Zaina matar Zain..? Kowa sai yace A"a Dina kuwa kallon Zakiya tayi yana Fadin"Allah yasa Ta bace kar aganta Har Abada..! Zakiya Tace"A"ah...Adai ganta Din bacewarta Gabadaya Tamkar Faruwar wani abu ne.."Da Sauri Dina Tace"Me kenan..!? Zakiya Tace"Kedai kada kiyi Fatan Ta bace har abada..Gwara dai ya saketa Tana Duniyarsa zai Fi.."Daga haka bata kara mgana ba suka nemi Waje suka Tsaya suna Bin Kowa da kallon Daya Bayan Daya Bangaran yan bikin kuwa babu wanda yama lura Dasu. Su Zain basu Dade ba sai gasu Sun Dawo Zafeera Ta Taresu Tana Fadin"Kun ganta Ya Dakta..? Bai iya mgana ba Saboda yadda yake jin wani Faduwar gaba Da wani irin yanayin da bai Taba ji ba,Haddir ne ya Girgixa kai yana Fadin"A"a babu kowa achan sai megadi.."Juyawa kawai Zafeera Tayi batare Da Tayi mgana ba Wajen ya Hautsine Lokacin Su Abba Sun gama Nasihansu sun Mika ma su Umma Hamdiya Zafeera Ta Kutsa Cikin matan Ta Riko Umma Tana Fadin"Umma Baki ga Ta Tafiya ba, Ba"a ga Zaina ba..! Umma Ta waigo Cikim mamaki kafin tace"Wani irin baki ganta ba..? Ba cikin gida muka barta ba Dakin Hajiyaa mama.."Da Sauri Zafeera Tace"mun Dubata Ko"ina bata Umma Ya Haddir yace yaganta Ta Fita Daga Gidanan..Kuma sunje chan Gida Bata Umma.." Umma Da Taji Gwiwanta Tayi sanyi Tace'"Bangane me kike nufi ba Zafeera ba..? Zafeera Tace,"Umma ba"ga Ukti ba..Bamu ga Zaina ba..Mun Dubata ko"ina bata ina Tsoron Faruwar wani abu.."Tafada Tana Fashewa da kuka Wanda yaja hankalin Jama"ar Dake wajen Mom iklima Tace"Subhanallah wani irin baku ganta ba..? Kun Duddubata ko"ina baku ganta bane..? Kuka yaci karfin Zafeera Ta kasa mgana karisowan Zainab ne yasa tace"Bata gidanan Domin an ganta ta Fita...Kuma an je gida bata nan gashi ita ba waya ba ballatana akirata.." Gabadaya wajen sai aka saka Salati,Umma ta Fara Sauke Numfashi kawai Nene ma Tana chan Tare dasu Zain suna gayamata itama sai Taji Tsoro ita Taje tagaya musu Abba suma suka Fara Tunanin toh ina zata ko Gidanta Takoma..? Da wannan Tunanin Haddir da zain suka je chan gidan nashi Chamma Shuru bata nan Koda suka Dawo da labarin bata nan sai Hankula suka Tashi Aka Dakata da Shiryen Shiryen kai Amarya Alhaji Tsoho yace Kowa ya Shiga Cikin Gida,Bayan sun bama masu Daukan amarya Hakuri, Shima Cikin Gidan Su Abba suka Taimakamai ya koma Ya zauna Bisa Kujeransa Cikin Alhini ya kalli Zain yana Fadin"kun Dudduba ko Bisa Hanya baku ganta ba..? Haddir yace"Bata Alhaji Tsoho.."Goggo Halima da mamaki ya Cikata Ta kada baki Tana Fadin"To wai ina ma zata..? Me akayi mata..? Ba wanda ya iya bata amsa,Duka an Hadu waje Daya ana Ta Jajanta Lamarin Harda su Dina na Wajen ba wanda ma ya lura Dasu Zain na zaune kawai ya Dafe kansa Alhaji Tsoho yace Abba ya Kira Chan gada yaji koTa kira wani Daga chan aka Kira sukace bata Kira Kowa ba. Toh Ina Zaina Zata tafi..? Da Sauri Zafeera Tace"ko aje gidan kawarta Laila agani.."Batama gama mgana ba Zain ya Mike ya Fice kamar zai Fadi Haddir da Zafeera suka mara mai Baya,Suna Zuwa Gidansu Laila Ta Tabbatar musu da Cewa Rabon Da Taga zaina Tun Ramar da tazo Gidan Umma Ta Tabbatar masu batazo ba Zuwa Lokacin Zain ya Fara wani Tunani na Dabam Gabadaya Zuciyarsa Bugawa kawai take yi. Suna zuwa da Labarin Bata je chan Umma ta saka kuka kawai,Zainab ce tace a kira wayar Zafeera jakarta na Hannun Zainar,Zareena ita Ta Kira Wayar Zafeeran sai dai ana ta Kira Tana Ringing ba"a Dagawa,Hankula suka kara Tashi Zain ya Sulale yayi zaman Dirshan yana Fadin"Shikenan...Shikenan...Firstlove.."Haka kawai yake Fada kamar wani mara Hankali. Zainab ce Taji Fitsari ta Shiga Dakin Hajiya Ta yi Cikin bayinta Ta Fito kenan Ta ji karan Wayar Zafeera wacce Dagachan Falo Zareena ke kira Cikin mamaki Tabi Karan sai gata Gaban jaka Cikin Fargaba ta saka Hannu Ta Dauko Jakar Ta Bude Ta Dauko wayar Kenan sai Taji kuma Ta Taba wata Farar Takarda Tana Daukota Bayan Ta karanta Sunan Dake Jiki Ta Waro Ido jikinta na Rawa ta Kwashi gudu zuwa Falon Tana Fadin.." "Ga Jakar na gani Dakin Hajiya mama Da wayar..Ammh ga wata Takardan Daga Jikinta an Rubuta UMMA,ABBA,ALHAJI TSOHO,FIRSTLOVE,GOGGO HALIMA.." Tafada Lokaci Daya Tana Daga Jakar da wayar da Takardan lokaci Daya Gabadaya Ba zain kadai Daya mike da Sauri ba Hatta da Umma dasu Abba da kowa da kowa haka aka Mike ana kallon Zainab baki Bude da Fargaban Abunda Tace Tagani Jikin Takardan. _Nasan da yawanku wasu wannan Page din bazai musu Dadi ba sai dai ina so ku sani Bawa bai isa ya kauce ma kaddaransa ba Bayyanar Dina ga ahalin Dr.Saulawa ya kawo Rudani wanda ya kasa Daidaita Toh kila Bacewar Zaina ma wani Mafita ce zai kawo ahakan Kada ku manta Labarin nan Shashi na Daya muke bamu kai ga Shiga Shashi na Biyu ba Sauran Labarin da abubuwan da suka Faru Har su Daidaita suna Tafe,Ku karanta Cikin natsuwa ku kuma gane Labarin Tun Farko ya Tsaru ne...Nagode kwarai da Sharhinku Yan Amana Da yan Wattpad dina Allah ya bar kauna Ameen.._ *Janafty...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *END OF BOOK 1*                 3️⃣0️⃣ "Zain ya Fara Takawa da Sauri Zuwa Wajen da Zainab Take tsaye sai dai kafin ya karisa yaji kansa ya sara,ya Saka hannu ya Dafe kansa ya Daga kafa zai Cigaba da Tafiya yaji kafafunsa na Rawa Jiri na Dibansa ammh ya kasa Hakura aikuwa Hajijiya Ta Debeshi zata Fadar dashi Allah yasa Baban Kaduna da Abba Dake kusa suka Tarbeshi Ganin yayi Gefe zai Fadi Cikin Damuwa da wani yanayi Abba yace"Subhanallah..Zainullahi..? Ya kira Sunansa Jin Ana Kiran Sunansa Daga sama yasa ya Bude ido ganin Abba Da Baban Kaduna yasa ya mike ga kafafunsa yana Dafe kansa Kokarin Cigaba da Tafiya Zain yake yi Baban Kaduna ya Rikesa Yana Fadin"Dakata..Ina zaka..!? Baka ganin Jiri kake gani kana neman Faduwa..? Cikin Raunin Murya yace"Baba zan karbo Takardan ne..Na Tabbata Firstlove ta Rubuta shi.."Baban Kaduna ya Jashi Ya zaunar Dashi Saman kujera yana Fadin"Zauna..kai Hadiru karbo Takardan chan muga kome ke Ciki.." Yafada yana kallon Haddir Ba yadda Zain ya iya Dole ya koma ya zauna yana Sharan Zufa Lokaci Daya Yana Sakin Numfashi Sama Sama Abba na kallonsa Cike da Tsausayawa Haddir ya Taka gaban Zainab ya karbo Takardan ya kawo gaban Baban Kaduna Cikin Umarni Alhaji Tsoho yace"Kai Hadiru Warwareta ka karanta Kowa yaji..Tashafi kowa Tunda ta Shafi Fatima da Usman dashi kanshi Zainullahin da kuma Goggonta Halima ka karanta Kowa yaji.." Cikin Bin Umarni Haddir ya warware Takardan sai ga Dogon Rubutun Zaina ya Bayyana Cikin Budewar murya yadda Kowa zai ji ya Fara karantawa Yayinda Falon ya Dau Shuru kowa na Sauraransa Hatta kuwa da Umma Dake kuka Amarya Hamdiya na Gefen Mom iklima Tuni Ta bar kuka Ta koma Jajanta wannan lamarin yayinda Dina da Zakiya suka saka kunni suna son suji wani sako wannan Takardan Take Dauke dashi _Assalama irin Ta Addinin Musulunci Assalamu Alaikum Warahamatullahi Ta"ala Wabarakatuhu,Nasan  zaku yi mamakin ganin wannan Sakon nawa ammh kuma ya zama Dole Kuma Ina da Tabbacin Lokacin da zaku ga Sakon nan na Riga nayi Nisa da Garin Bauchi,Shiyasa nace Sakon kai Tsaye ga Umma ne Da Abba sai kuma Firstlove,Alhaji Tsoho da Goggo Halima kafin nace komai zan Fara da Neman afuwanku Bisa wannan Hukuncin Dana yanke batare da nayi Shawara da kowa ba..Nasan Cewa Wannan Abunda na aikata bazai muku Dadi ba in kuka nemi kuka Raasa kuma kuka Fahimci Cewa na Bar ku ne,Da Farko zan Fara da Baki Hakuri Umma Don Allah ki yafemin Ba"a son Raina na Tafi na barki ba kuma ba Niyyata Na Bijerema Umarnin ki ba ko na saba miki ba..!ko na Watsa Miki kasa a ido ba..! Umma Tun ina Jaririyata na Rasa Duka iyayena kika Tallafeni kika zama Uwa gareni kika Fifitani sama da ya"yan da kika Haifa,Da ace mata da yawa zasu koyi da irin Halinki da sun Dace kin kasace Uwa Tagari mai maida D'an wani nata kin Soni Da Zuciya Daya kin Fifitani kan Abunda kika Haifa Saboda kina So ki inganta Rayuwata kin Kuntatama Abunda kika Haifa saboda ni Umma Sai dai ni na kasa Miki Hallaci bazan iya juran Rabani da Firstlove ba da zaki yi ba Umma Ina sonshi ina kaunarsa Shine Raunina Shi na sani Shine komai nawa Umma Shine Duniyata Zuciyata bazata iya Daukan abubuwa Biyu alokaci Daya ba..Umma ban yanke Shawaran yin nesa daku ba sai da naga kin Fahimci ina da Shigar Cikin Firstlove ajikina Wanda Duk da banje asibiti an Dubani ba ammh Duka alamomin masu Suna Bayyana ciki Gareni Nayi kokarin Na Sirrinta Abun kada ki sani sai dai hakan bai Faru ba, kin gano ina da ciki kuma Kin Fadamin zaki Zubar dashi Saboda Kina son Cigabana baza ki barni na Cigaba da Zama da Firsrlove ba Umma ina son Cikina naji ina kaunarsa Kuma nayi alkawarin zan kare lafiyarsa Muddin Raina Koda wajen Haihuwarsa zan Rasa Raina Na yarda na amince na Haifama Firstlove Wani Abu Daga Tsatsona Daga karshe Umma ina mai neman Gafaranki Don Allah ki yafemim kuma ina Rokon alfarman da ki yafema Firstlove koda wannan ne alfarma ta Karshe da zaki man Ummata..Sai Abba Kaima Zan Roke Gafara Domin kaima Uba ne gareni ka Rikeni Tsakani ga Allah ka Hadani da ya"yanka ka Inganta Rayuwata alhalin ni ba Kowan kowa bace Face Diyar Maryamai mai aiki da Abdullahi megadi ammh baku Duba wannan ba ka Rikeni kabani Dukkan gata Ina matukar Gode maka ka cika Uba nagari Abba ka yafemin Don Allah Kuma ka yafemin Firstlove Abun da ya faru Bawa baya wuce kaddaransa,Abba bazan cigaba da zama ina ganin kana Fushi da Firstlove ba Kana hanashi shiga gidanka ba Duk Saboda ni ba..Shiyasa naga Tafiya ta itace Mafita kaima Don Allah ka yafema Firstlove Na Tabbata Nadamarsa ta Gaskiya ce bazai kara aikata makamancin haka ba,Sai Kai Firstlove Mijina Abun alfaharina Bangona Majingina komai zaka min aduniyan nan na Riga nayafe maka Duniya da Lahira,Kayi Rayuwa cikin Jajayen Fata kaga mata kala kala Wadanda suka fini komai da komai ammh kace sai ni din nan Kamin komai aduniya ka nuna min kauna Ka soni Ka kaunace ni kuwa dame zam saka maka.? Zuciyata tayi Rauni Lokacin da Naga Wata amatsayin Wacce kake Rabamana na Rayuwa da ita naji Dama na iya Fincike sonka acikin Raina sai dai ina Bani ke Sarrfa Zuciyata ba naji na kasa sai ma karin kaunarka da Tsausayinka dakeCin Raina akullim ina kwana kuka ne ba Saboda komai ba sai saboda Tsausayina da Tsausayin kanka bazan Juri Raunin Rasa ka ba kuma bazan Juri Raunin wata ta sameka ba kuma Bazan juri Raunin Rasa Cikin Jikina ba Shiyasa na zabi na Tafi waje mai Nisa Zuwa Lokacin da komai zai Daidaita ka sani na yafe maka Nima ka yafemin Tare damin alfarman Barin Igiyar Auranka akaina Koda bazamu sake Haduwa ba...Nayi maka alkawarin kula da kaina da Abunda ke Cikina In har muna da Rabon Haduwa Shikenan in kuma ta yanke sai da nace Sai Wata rana..! Alhaji Tsoho Dattojon arziiki kuma Wanda ya Tara Zuru"a ta kwarai Babu Abunda zan ce maka kai da Zuru"anka sai Godiya Allah ya saka muku da alheri,Kamin Nasiha na ki Jin mganarka nasan zakaji zafin wannan Hukuncin Dana yanke ammh kuma Shine daidai awajena Katayani Bama goggo Halima Hakuri kuma Don Allah komai zataji kan Firstlove kada Tayi Tir Dashi Ta Dubi mganar da Fuskan Basira,dangina da yan"uwa na Gada da kuma Ukti,Faruq,Anty Zareena da kowa da kowa nasan bazaku ji Dadi Ba Dake zainab Ammh don Allah ku yafemin ku sani Duk inda zani zanyi matukar kewarku..Kada kusha Wahalan nema na nayi Nisa Na Tafi bansan Inda zani ba ammh kuma In da Rabo zan Dawo Insha Allahu Zuwa wani Lokaci in kuma ba Rabon ganawarmu sai nace Allah ya Hada Fuskokinmu a Darussalam..masallam_! Gabadaya Falon ya Dauki wani irin Shuru kafin kuma ya Kaure da Salallami da kuma Koke koke Umma kasa ta Durkushe Tana Fadin"Innalillahi...Wayyo Ni Fatima me na aikata..? Nayi sanadiyar Yata ta bar gida ina zata..! Wlh koda na Rantse zan Raba wannan auran Daga Baya nayi Nadama har cikin Raina kuma nayi Niyyar maida ta Gidan Mijinta na yarda zanyi kaffara Saboda haka,Kuma mgana Ciki Wlh harga Allah Shine Shaidata Ba Har raina na Fada ba gatse nayi mata ganin tana kuka ashe ashe ita Ta Dauka Da gaske ne.."Ta karishe Fada Cikin Kuka Hajiya mama na Sharan kwallah Tana Fadin"Kinga Abunda kika aikata Ko Fatima..? Dama na gaya miki Abunda Hakuri bai bamu ba Wlh a kasasin bazai bamu Ba gashi yarinyar Tabar gida yanzu wani Hali zata Fada bamu sani ba.." Abba kansa kawai ya Dafe Yana Salallami Baban kaduna ma Haka su Mama Safiya Kowa dai afalon Sai salati ke tashi Zafeera da Zainab kuwa sai kuka Suke Dina ce kadai Take Farinciki Sosai Zuciyarta Kamar farar Takarda,Alhaji Tsoho kai ya Sadda kasa yana Kiran Sunan Allah,Goggo Halima kuwa Da ta Shiga Rudi Da kuma Rashin Gane ina aka Dosa ta kalli Hajiya Mama Tana Fadin"Hajiya mama me ya Faru ne..? Halima Tayi gangancin me ya Faru da zafi da zata yanke irin wannan Hukuncin Tana yarinya karama ga Danyan Ciki Tare da ita kai Innalillahi.." Hajiya Mama Ta girgiza kai Cikin Sharan Hawaye Tana Fadin"Bari kawai Halima Mganar mai Tsayi ce sai mun zauna.."Hajiya Mama bata gama Rufe bakinta ba Zain ya Mike Tsaye da karfi sai Lokacin ya samu Damar mikewa,Tun Sadda Haddir yake karanta Takardan Gabadaya Muryan Zaina ke mai yawo a kunnuwansa gabbansa sun saki Kafafunsa sun gaza Daukansa bai Kara Shiga wani irin Rudewa ba sai da ya fahinci Zaina Ta tafi Ta barshi Sannan kuma Tana Dauke da Cikinsa ajikinta Tundaga Lokacin bai kara Fahimtar komai ba Domin Jinsa Da ganinsa ne ya Dauke alokacin sai yanzu yaji kamar ya Dawo Cikin Duniyar. Gabadaya aka Zubamai Ido ana kallonsa ganinsa yana Nuna Hannu yana so yayi mgana ya kasa Runtse ido yayi wasu Zafafan Hawaye suka zubomai Cikin Rawan murya kamar mai In ina yace"First...L..O..v..e...Ta..tafi...Ta..barni.Kuma..Ta...na...Da...Cikii...naaaa...!bai ida karisa mgarsa ba Kawai ya Sulale ya Fadi nan da Karfi sai kaji Tim nan da nan Idanuwansa suka kafe ba Numfashi Cikin Tashin Hankali su Abba dasu Daddyn da Baban Kaduna da Haddir suka Rufu kansa Cikin Rudewa da wani Tashin Hankali Haddir da Baban kaduna Suka Tallafeshi suna Kiran Sunansa ammh ko Motsi Abba Dake gefe ya Rikice Hakama Su Umma sai kuka ya kara Tashi Dina Dake gefe ganin Zain baya Motsi ya Tada hankalinta Ta nufi Wajenshi Tana Zuwa Ta ture Haddir Dake Rike da kansa Baki ya saki yana kallonta Cikin Tashin hankali ta Rike Hannunsa Tana Fadin"Na Shiga uku plz zain don"t do this to me..Kada ka Tafi ka barni da Cikinka.In ita bata Sonka ni ina Sonka Zan zauna dakai nayi maka Duk Abunda take maka Don Allah ka tashi.."Sai kuma ta saka kuka Galala kowa ke kallonta sai Lokacin ma Su Umma suka ganta Cike da mamaki Wadanda basu san Labarin Dina ba suka saki baki Cikin mamaki irin su Goggo Halima. Kowa ya kasa mata Mgana Sai Baban Kaduna ne ya Fizge Hannun Zain din yana Fadin"Ke miye haka..? Wannan wani  Rashin Hankali ne..? Baki ganin Halin Dayake ciki..? Ya Fada Cikin Takaichi kamar ya maketa Kuka ta kara sakamai Zatayi mgana Zakiya tazo Ta jata Tana Fadin"Kuyi Hakuri Don Allah..Ta saka Control din kanta ne Da Halin Dayake Ciki ne.."Inna Hannatu Dake Gefe ta Lailayo Ashar Tana Fadin"Kaza kazan Halin Data ke ciki.. Duk son data kemai Takai mahaifansa ne..? Nace baga uwarsa nan da Ubansa ba Me kika ga sunyi..? Sai ke karan kada Miya Matsa ki bamu Waje Maras kunya"Sumi Sumi Zakiya Taja Dina Dake kuka suka koma Gefe Zakiya Ta kalli Dina Cikin Takaichi Tana Fadin"Ki Natsu Dillah..Kina da mtsala wani Lokacin.."Dole Dina Ta natsu ammh hankalinta na wajen Zain wanda Daddyn Abuja yace aje asibiti Alhaji Tsoho ya Dakatar dasu yaje su kawo Ruwan zamzam Hajiya mama ta kawo yayi addu"a ciki ya bama Baban kaduna yace su Shafamai afuska Cikin Ikon Allah yana Shafamai sai gashi Ya sauke ajiyar Zuciya Kafin kuma ya Fara Bude Idanuwansa. Ganinsa Akan Cinyar Haddir gasu Baban kaduna sun zagayesa Gefe Daya gasu Umma komai ya Dawo mai Zumbur ya Mike su Abba na Rikoshi Yayi Saurin Cire Baban Rigan jikinsa yana Fadin"Ku sakeni naje na Nemota..Wlh bazan iya Rayuwa bata ba...Bazan iya ba"Yake Fada kamar wanda ya Zare Baban kaduna da Haddir ke Rikesa Abba kuwa Da Daddyn Abuja kwalla suke dama sune masu Raunin ganin yaki yarda ya zauna yasa Alhaji Tsoho ya Daga baki ya Kirashi Sunansa. "Zainullahi...kai Zainullah yaka nan."Jin Alhaji Tsoho na Kiransa yasa ya Dakata da Neman Fitan Dayake ya Zubamai Ido yana Hawaye Cikin kuka yake Fadin"Alhaji Tsoho kagani ko..? Zainata Tatafi ta barni sai da nace ku bani matata aka ki bani..Ku barni na Taje na Nemota.."Alhaji Tsoho ya kalli Haddir yana Fadin"Hadiru zaunar Dashi.."Haddir ya zaunar Dashi Kan Kujera Dakyar sai Sambatu yake,Kana Alhaji Tsoho ya kalli su Umma da Nene dasu Zafeera Dake kuka yace"Kuyi hakuri kubar kukanan..Aminatu Tafi Da Goggo

Chapter 31 of 32