ba..!
Yafada Cikin Alamun ba Wasa yake ba Abba ya Jinjina kai yana Fadin"Hakane Alhaji Tsoho..Kai Haddir maza ka Tattaro kayanka Ka zabi Gidana ko Nan Gidan ka Dawo ka Zauna Zamanka achan baida wani amfani Tunda Kana da Wajen da zaka Zauna.."Hajiya Mama ta karbe da Fadin"In yana so ya samu sakewa..Yayi Aure..!
Fuska ba Walwala Haddir yace"Toh Abba Dama Abunda yasa na kama Chan Gidan naga yafi kusa da asibiti ne.."Alhaji Tsoho yace"Wannan Ba Hujja bace..Da zai saka ka Zauna kai kadai..Sai Mutane surika Munana maka Zato Tunda ina da Tabbacin ansan kana da Mu anan garin Zamanka achan bai Dace ba kayi yarda muka ce kawai ."Kai ya kada yana Fadin"Shikenan Weekend zan yi parking..Zan dawo nan daman Wannan Tsohon matar naka Tana So tana kaiwa kasuwa..!
Yafada yana Hararan Hajiya Mama Shewa ta saki Tana Fadin"Ja chan Me zan Dakai..? Kaga Sabon Megida nan,Megidana akwai Cefane.."Tafada Tana Dafa Zain Dake gefenta Shima ya Dafata Harda Ma Haddir gwalo Abba yace"Hajiya mama Ayi ma Tsohon mu haka..?
Hajiya Mama tace"Me za"a Fasa..? Shima Tawaye yake neman yayi min da Halimatu Kullum sai tazo Gidan nan kaga Sun Hada kai suna ta kus kus in kuma bata zo Zata kirashi a waya ko Aikomai da wannan kawomai wannan Kaga fa in batazo ba ya Dinga Damuna da Fadin Oho Aminatu yau Halimatu Shuru ko lafiya..? Bari na Kirata..!
Abba na Dariya yace"Au Ramawa kikayi kenan kema kika kwace mata miji kenan..? Hajiya mama Tace"Eh mana Taji In Da Dadi itama.."Alhaji Tsoho yace"Hoho Aminatu...Ina Laifin Halimatu kinsan Bakin Tsoho sai da Gishiri Gishiri kuma Kus kus Din Da kikace munayi labarin Iyayenta nake bata Ina gayamata kyawawan Halayansu da na sani Lokacin da muka Zauna dasu Suna Raye..."
Allah ya Jikan Umaru da Abdullahi da Duka Musulmab da Suka Rigamu gidan Gaskiya.."Gabadayansu suka amsa da Ameen sai kuma Jikinsu yayi sanyi Alhaji ya Cigaba da Fadin"Haske da Rahma yakai musu..Bayin Allah ne masu Zuciyar Zinare Na Sha Gayama Halimatu Ta Debo Wasu Daga Cikin Hallayan Mahaifiyarta Maryama.."Hajiya Mama tace"Ba Shakka...Allah ya Hadamu a Aljannah Dasu.."Gabadayansu suka amsa da Ameen Ameen kafin su Cigaba da Hiransu Jefi Jefi Abba bai Jima ba yayi musu sallama ya Tafi Zain kuma sai da ya Tsaya Suka Sha Furan da Hajiya Mama ta Damama Haddir Duk da yadda ya Dage kan bazai Sha ba Bayan sun gama suka Tafi Kitchen suka gaisa da Baba Tabawa Wata Yar Dattijuwa ne aiki take Gidan Alhaji Tsoho Tun Tana Matashiyarta Har Girma ya kamata an Riga da an zama Daya Dayake Baba Tabawa irin yan gudun Hijiran ne ba wasu Dangi ne Alhaji Tsoho ya Zame mata Tamkar Uba Duka su Zain Agabanta suka Taso Ita tayi Wahala dasu In Aka kawosu Hutu Gidan na Alhaji Tsoho.
Bayan sun Fito ne sukama Su Hajiya Mama Sallama suka Fito Atare Haddir na Kokarin Shiga Motarsa yana Fadin"Wai ina ka Tsaya Jiya Zainarka ta kirani Tana Tambayana ko muna Tare..?
Yana Sosa Gemunsa da Key din Motarsa yace"Na tsaya Cikin Asibiti ne Kuma Wayar tawa Tana Silent Shiyasa ban ji kiranta ba.."Kallon Sama da kasa Haddir yayi mai kafin ya Cije baki Cikin Tsarguwa Zain yace"Lafiya kake min wannan kallon..? Ko zan maka karya ne alkali Hadiru..!
Yafada Lokaci Daya yana Dauke kai Mirmishi Haddir yayi kafin yace"Kai dai ka sani..Ka kama kanka ne ammh ni wani kallo nake maka..? A koda yaushe bazan gaji da Fadamaka ba kaji Tsoron Allah..Ka kuma guji Ranar da Wata baraka zata Faru wacce Zata Zubar maka da kimarka Harda ta iyayenmu.."Yana Gama Fadar haka ya Bude Motarsa kiran Jeep ya bar Zain nan Tsaye yana Binsa da kallo Mganar Haddir din namai yawo a saman kansa yana Tsaye ya Fice Daga Haraban Gidan ya barsa ajiyar Zuciya ya Sauke kafin Shima ya Nufi Motarsa ya shiga ya Tasheta Shima da Gudu yabi bayan Haddir din.
Kusan Tare suka Shiga Cikin Asibitin..Kowa Bangaran Office Dinsa ya Nufa Saboda sun makara Sun san Fayels Din patient na chan na Jiransu da Uban Layi,illai Haddir yana Shiga Office ko zama bai gama yi ba yace First ya Shigo Shi kuwa Zain yana Gabda Shiga Office Dinsa Suka Hade da Dina ta Fito Daga Office Dinta kallo Kallo Sukayi ma Juna kafin Shi yayi Saurin Dauke kai ganin Tana Jifanshi da Irin kallon Data saba kashemai Jiki Dashi Fuska ya Hade kawai ya Tura kofar Office dinsa ya Shige yana Kiran Wata Nurse da Hannu Alaman ta Biyoshi.
Sai da ya Shige kana Dr.Dina ta Kada kai ta Murmusa tana Fadin"Kayi kuskure Dr.Zain in kana Tunanin zaka iya gujema Dina..Har Abada bazaka iya ba..Ban Fara sonka don na Daina ba kuma Ban Fara mu"amala Dakai don na Daina ba..Yanzu ma aka fara Wasan...!
Tafada tana wani Sakin Wani Shu"umin Mirmishi ta kada kai ta Wuce so take ta bar Cikin Asibitin Tunda Ta Duba patient 10 yau da Safe tace abarshi haka Sauran aturama Dr Imran Ita ZATA fita Ma"aikatan su Zakiya take son zuwa su Tattauna wasu Abubuwa sun kwana Biyu Basu hadu ba..!
*****
Fitowarsu kenan Daga Lecture Suna Gangarawa zasu Shiga Lap Duba wani Calculaton da aka basu Tafe suke suna Hira Sama sama Har suka Isa Libary Din Sai da suka samu Waje suka Zauna kana Halima ta Fito da Wayarta Tana Fadin"Kinga Laila kafin mu Fara Duba Assigment din nan Let me Call Firstlove Tukunnah na gayamai na Fito..!
Mirmishi Wacce aka Kira da Lailah Tayi,Itama Dim kamar Sa"ar Haliman ce sai dai Ita Fara ce Tas kuma kyakyawa ce,Kai ta kada Tana Fadin"Hmm kirashi Dama waya isa ya Hanaki Kiran Firstlove..'Halima bata Jita ba Domin tayi nesa da Ita Suna mgana da Dr.Zain tana mai Shagwaban Ta gaji,shi kuma yana Lallashinta Daga karshe yace in tagaji ta koma Gida Shima da wuri yau zai Tashi aiki nan dai suka Shiririce Suna Mgana Sai da Taji Shigowar Haddir da mganarsa kana Suka Datse kiran Ta koma Wajen Laila Tana Fadin.
"kawas afuwan..Na bata miki Lokaci.."Laila tayi Mirmishi Tana Fadin"Bakomai..ai na Saba Daukan Bata Lokaci indai akan Firstlove ne.."Dariya kawai Halima Tayi Batayi mgana ba Laila ta kalleta Tana Fadin"Ni kuwa Halima in bazaki Damu ba zan so na baki Wata yar Shawara..!
Halima na Fito da Note Book Dinta Da Handout Lokaci Daya Tana Fadin"Wata Shawara..? Ina Sauraranki Lailah..'Tafada Tana kallonta..'Laila ta gyara Zama Tana Fadin"Tunda muka Fara karatu a wannan makarantar muka Hadu Dake Halima muka kulla kawance Saboda Duka Abu Daya ya kawomu..Duk da Banta Aure ba ammh ina da Labaran Zamantakewar Aurarranki Da Dama Halima..Na Tabbata a Haduwata Dake zuwa yau zan Shaida Girman matsayin Soyayyah da Kauna Hade da yarda Da kike ma Mijinki Halima Kuma Hakan yana matukar Burgeni..ina jin Dama ace Nima na samu miji kamar naki Wanda zamu Dinga Gudanar da Rayuwarmu kamar yadda kuke gudanar da naku keda Firstlove dinki..!
Mirmishi Halima ta Saki kafin Tace"Bake kadai ba..Mutane Dadama Suna Fadin Irin Soyayyar Dake Tsakanina da Firstlove Tana Burgesu."Laila tace"Dole ne..Ammh Duk da Burgenin Datake Ina da yar Shawara gareki Halima..Kinga Da" Namiji Buhun kaya ne kuma Dan Hankaka ne gabansa Baki bayanshi Fari ina Tsoron yadda Kika gama Bashi Yardanki kada Watarana yaci Amanarki Zuciyarki ta kasa Dauka Har Abun yazo yayi affecting Dinki Halima..!
Tun kafin Ta karisa Halima ke Jefenta da wani kallo kafin tace"Bangane ba Laila..What Do U mean..!? Kai tsaye Laila tace"Ina Nufin ki Rage Wannan Zafin so da yardan da kika bama Mijinki ban ce ki Daina yarda Dashi ba Duka No ki Rage karki manta Namiji ne kuma Likita Likitan ma na Mata Yana Harka da mata kala kala kinsan Zuciya bata da kashi Ina Tsoron kada Wani abu ya Faru kika sa Jurewa Zuciyarki Zata iya Tabuwa a yadda na Sanki da Komai kankanta Abu Damunki ya...!
"Don Allah Dakata Lailah..!
Bata karisa ba Halima ta Tareta a Fusace Shuru Laila Tayi Tana kallonta Ita kuma Halima ta Fara Mgana Cikin Bacin Rai Tana Fadin"Kin bani mamaki laila Wlh Ban Taba Zaton keda bakinki zaki zo da irin wannan Zargin ga Firstlove ba na Dauka kowani Kikaji yana Fada sai inda Karfinki ya kare adai yadda muke Dake ammh sai gashi keda kanki ki ke Fadan Haka..Toh bari na gayamiki Abunda baki sani ba Firstlove Bazai Taba Cin Amana ta ba Domin na Yarda Dashi Fiye da kaina Banda Uwa Bani da Uba..Iyayensa Sune iyayen Goyona Sun Rikeni Tamkar yar da suka Haifa Tun Ranar da na Zo Duniya Firstlove Shi ya Fara Daukana kafin Innata da Babana Goggo Halima da Bakinta Take Fadamin Taga Soyayyata a kwayan Idanuwan Firstlove Tun Ranar dana Zo Duniya..Laila inda Firstlove zai iya Cin Amanata da Tun Tuni yayi..Domin tun ina da Shekara 9 a Duniya ya Tafi London karatu Cikim Jajayen Fata da Turawa masu al"adu da Dabam Dabam...Ammh bai Sauyani ba Ya Jirani Har na Girma Shima Lokacin ya gama karatunsa Auran mu Ya Tabbata Baki Tunanin wanda ya Tsallake zukan Zukan mata Harda Turawa ya Dawo gareni baki kyautatamai zato laila..?
Tafada tana kallonta Ido Cikin Ido Ajiyar Zuciya Laaila ta saki kafin tace"Nifa Baki gane mganata ba Ha...'! Nagane Duka Inda kika Dosa..So kike na Cire yardan da nayi ma Firstlove..Toh bari kiji na Yarda da Firstlove Aduk Duniya Shi na Fara yarda Dashi Tunda Ban yi Wayon sanin iyayena ba..Kuma ki sani Firstlove dina Bazai Taba Cin Amanata ba Har gaban Abada Saboda yafi kowa Sona da Sanin Raunina..!
Tana Gama Fadar Haka ta tashi ta Fara Tattara Takardunta Laila ta Mike tana Rikota ta Fizge Hannunta Tana Fadin"Stay Away From me Laila..Alaqata Dake bata yiyuba...Juz Leave me..!
Daga Haka ta kwashi Littafanta ta bar mata Wajen Laila ta Bita da Kallo Kafin ta kadai afili ta Furta..'Allah yasa Haka Halima..Rauninki na sani Shiyasa nake Tsausayinki Har acikin Raina ban kuma san Dalili ba ina Jin Wani abu acikin Raina mai kama da Tsoro..!
*Comments*
Share and Vote*
*Intelligent Writer"s asso*
*Janaftyshakira...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
0️⃣4️⃣
*#SHEKARUN BAYA..*!
"A kowani Fanni na Rayuwa akwai Cigaba akwai akasinsa Haka Zalika kamar yadda akwai Samu akwai Rashi akwai Nasara akwai Faduwa,kuma Duk Allah Subuhanahu Wata"ala yake Tsara Abunshi kuma ya Tafi yadda ya Tsarashin.
In mukayi Duba da wannan Rayuwar Tamu ta yau da kullum,Allah ya Hallicemu Dabam Dabam ne kuma Rukuni Rukuni Akwai Kasa kasa a Duniya akwai mu kuma Jaha Jaha,Kana kuma sai yazo yayi mu al"adu da kuma Harsuna Dabam Dabam..Sai kuma ya bama wasu Daga Cikinmu ikon Tashi Cikin Addinin musulunci wasu kuma Daga Baya ya basu ikon Zamowa Musulmai akwai kuma Wadanda Yake son ganinsu Haka kuma ahaka ya barsu Tunda Shi din mai Fitar da matacce ne acikin Rayayye kuma mai Fitar da Rayayye acikin matattu.
Kamar yadda muka gani ko yatsun Hannunmu ba Daidai Suke ba Wasu sun Dara wasu Toh Haka Abun yake in mukayi Duba da Rayuwarmu ta yau da kullum,Acikin mu akwai masu Tarin Dukiya wadanda bazamu iya Gogan Kafada dasu ba kama Daga wasu yan Siyasa ne wasu kuma yan kasuwa ne masu Tarin Arziki wasu kuma Suna Kasansu ne ma"ana masu Rufin asiri Daidai Gwargwardo Wadanda Suke fin karfin Gidansu Har da Nauyin wasu akansu Wasu kuma iya Nauyin kansu ma Suke iya Dauka yayinda da wasu kuma ko Nauyin kan nasu bazasu iya Dauka ba saboda Halin yau da kullum Ammh Duk da Haka basu Gaza ba ba kuma Suce Allah baya sane dasu ba akowani Hali na Rayuwa Sai dai Su Furta kalmar Godiya Ga Allah ALHAMDULILLAH..!
*Dr.Abubakar Bashir Saulawa* Haifaffan Garin Katsina ta Dikko Dakin kara ne,Kuma Haifaffan anguwan nan ta Cikin katsina mai Suna Saulawa,Abubakar ya Taso Dan Gata Cikin Dangi Duk da Tun yana karami ya Tsinci kansa amatsayin maraya ta Bangaran uwa da Uba sakamakon Hadarin Mota sai Rikonsa ya koma Hannun Baffansa Ma"ana Yaya Wajen Mahaifinsa.
Shi ya Daukeshi ya Hadashi Cikin ya"yansa Ya inganta Rayuwarsa Tunda alokacin Yana da Halin yin Haka Tunda ma"aikacin gwannati kuma yana Cin Lokacinsa Sosai Abubakar Tun yana karaminsa yake da Burin Zama Likitan kwalkwalwa Sakamakon Labarin Daya samu Kakarsa wacce ta Haifi mahaifiyarsa da Ciwon Hauka Ta Rasu Sai Abun ya Shiga Ransa ya Saki Tasiri Tun Daga Lokacin Yayi ma kanshi alkawarin sai ya zama Likita Ta Bangaran kwakwalwa kodomin Taimakama Talakawa Maraasa karfi Wadanda Suke karewa a Hauka Har su mutu basu samu mai Tallafamusu.
Alokacin ba wanda ya Dakatar Dashi kan kudirinsa sai ma Goyon Baya Daya samu Ana Cikin Haka yagama Secondry School Dinsa anan garin na Katsina Lokaci kalilan Baffansa yayi masa Cuku Cukun Samun Gurbi Karatu Awata Medicine School Inda ya Shafi karatun Likitan Kwakwalwa Wato Psychiatric kenan Dake Birnin Delhi India Chan ya Tattara ya Tafi Inda ya Kwashe Shekara Goma achan kafin ya Dawo kasar sa ta Haihu Shima Din Rasuwar Baffansa ne ya Dawo Dashi Tunda Shekara Daya kenan Da kamallah karatunsa da kuma kananun Cosa cosan Dayai ta Hallata Saboda Cikar Burinsa ya Fara aiki da wani Asibitin kwakwalwa Dake Bangcof a matsayin Psychiatric Doctor,duk da bashi da Burin aiki a ko"ina sai a kasar sa ta Haihu bai Hanashi Fara aiki Dasu ba Ba domin komai ba Sai Domin yana Bukatar Tsayuwa da Kafafunsa kafin ya koma kasar sa ta Haihu yaga kuma ta ina Zai Bullo Domin Cikar Burinsa na Taimakawa Talakawa ya Tabbata.
Ana yin Sadakan Bakwai ya Tattara ya koma Dama Bashi da gado Tunda Da iyayensa Suka Rasu da Abunda ya Gada aka Dinga mai Hidima koda ma Ragowa bai Damu Daya Nema ba alokacin Hankalinshi ya Karkata kan neman Halas Dinsa da kuma yadda Burinsa zai Cika.
Yayi gwargwarmaya Sosai kafin Cikar Burin nashi Tunda Sai da ya kara kwashe Shekaru wajen uku achan Bangcof kana ya Dawo Gida Nigeria ya yada Zango a Lagos inda ya Fara da Wani asibitin a Bangaran Masu Laluran kwalkwalwa,bayan nan yayi Tafiye Tafiye zuwa kashashen ketare da bai san iyaka ba Wajen kara sanin kam Abunda ya Shafi masu Laluran kwakwalwa yana Da Shekara 28 a Duniya komai na Bukatar Rayuwa ya mallaka Motar Hawa da Gidan kansa da kuma Wasu kadarori gefe Daya kuma yana Kokarin Taimakama yan"uwan da Dangi.
Sai da ya Shekara Talatin Yan"uwa suka Taso mai kan Mganar Aure Alokacin Shima bai kiba sai ya amince ya Fara Neman Aure sai dai Dayake Tun Farko ba"anan Hankalinsa ya karkata ba Sai ya kasa kawai Daga karshe sai ya basu Zabi Su kuma Suka Zabamai Aminatu Diyar Baffansa Wanda ya Rikesa bai yi gaddama ba ya karba,Duk da Amina itace auta Bai wani Wayeta sosai ba,Saboda Tana karama ya Daga Zuwa Delhi ammh bazai Taba kinta ba ba"a saka Lokacin Bikin da Tsawo ba Tunda Itana Aminar ta gama Secondry School Dinta kenan Mganar Tataso kuma bata ki Dan"uwanta ba Duk da Lokacin ana Ta so a Hure mata kunne ganin Abubakar din ya Riga ya Tazurance bai yi Aure ba ammh Taki Jin kowa Tunda dai Mahaifiyarta ta yarda da mganar kuma yan"uwanta Sun bata Goyon baya Sanin Dr Saulawan Samun kamarsa a wannan Marran sai an Tona.
Wata Biyu Tsakani aka Daura Auran Amina da Dr.Abubakar Saulawa,Direct kuma Gidansa Dake Lagos ya wuce da matarsa Tunda ba wani Sha"ani akayi ba Ta Samu Rakiyan yan"uwa da basu gaza Biyar ba,sukaje suka ga Inda Take suka kwana Biyu suka Dawo Suna Musu Fatan zama Lafiya na Har Abada.
Alhamdulillah Zamansu na Gudana Cikin kwanciyar Hankali Amina nada matukar Hankali da Natsuwa Shi ma Haka sai suke kokarin Sauke Nauyin Juna Dake kansu,Watansu Biyar da Aure ya Sakata a makaranta Tayi Diploma Dinta Shikuma alokacin yana taCikun Cikun Dawowa Arewa da zama Gabadaya Hakan bai samu ba sai da Suka Shekara Biyu kana Ya samu Babban matsayi a Asibitinn General Hospital Bauchi Ya Tattaro Amina Suka Dawo Garin Bauchi da zama Wanda ya zama kamar garinsu Ciki yayi ya"ya da Jikoki har kuma Babban Burinsa na mallakan Asibitin kansa ya Tabbata.
Suna Dawowa Amina ta Fara Laulayin Shigar Ciki Murna Wajen Dr.Saulawa Ba"a mgana yan"uwaa Suna Ta Murna Sosai Dama Ta gama Diplomanta Dayayi mata mganar Cigaban karatunta sai tace ya bari sai ta Haihu Shikuma sai ya kyaleta ganin Tana Fama da Lailayi.
Watan Cikin Amina na Shiga Wata Tara ta Haifo Santalelen yaronta Sak mai kama da Dr.Saulawa,Ranar Suna ya Ci Sunan Mahaifin Abubakar Wato BASHIR kuma basu mai wata alkunya da Bashir dinsa Suke Kiransa,Haihuwan Bashir kamar Tazo da wani Budi ne Tuni Sunan Dr Saulawa yayi Fice agarin Bauchi Da kewaye Duk inda ake nenan Likitan kwakwalwa Wanda ya kware a aikinsa Shi ake nema kuma yana Taimakawa gwargwardon ikonsa Ya Hallaci Seminar Seminar ba adadi,Kuma Sunansa yayi Fice Tunda Har ya goggayan Da manyan Likitoci,Tarruka na mussaman na karama Juna sani Duk yana Hallata Saboda Sanin irin gwazonsa da kuma irin yadda yake aikinsa da Jarjircya Hatta Asibitin na General ta san da zaman Dr.Saulawa Wanda Abubakar din ya bace sai dai kaji Ana Kiran Dr.Saulawa.
Bashir Nada Shekara Uku Duniya Amina ta kara samun Wani Cikin Lokacin ma Dr.Saulawa na Shirin nema mata makaranta ne sai kuma ga wani Cikin bai nuna komai ba Sai Jin Dadin Domin yace yafi son Haka yadda ya Dade bai yi Aure ba yana so kafin karfinsa ya kare ya"yansa Su more Lokacinsa Kamar kuwa ya amsa gaban yan Ameen Bayan Bashir Sai Kuma aka samu USMAN,Daganan Haihuwa ta Bude ma Amina ba Daga Kafa Daga Usman Sai Tayi ALIYU sai kuma ta Sirka ma Mata Tayi HANNATU sai kuma Tayi Autarta Ta karshe Wacce Daga Ita bata kara Haihuwa ba RUKAYYAHTU.
Da wadanan Ya"ya Biyar din Dr.Saulawa ya Godema Allah Suka Cigaba da Rayuwarsu Suna Tarbiyantan da ya"yansu Zuwa Lokacin Allah Duk Ya Dauki Sauran iyayen nasu Mata Sai suka Rumgumi maraicinsu Su da Amina Suna Cigaba da Rayuwarsu gefe daya kuma suna Bama ya"yansu Duka kulawansu.
*****
*Shekaru Talatin da suka Shude..*
Zuwa Lokacin Zan iya cewa Duka Buri da kuma Fata na Dr Saulawa ya Cika Domin ya Kamallah Ginin Kayattacen asibitinsa mai Suna SAULAWA SPECIALIST HOSPITAL BAUCHI...!
ya kuma Gina wani katafaren Gida a GRA gida ne Ginin zamani mai kyau da Tsari Tunda Duka yayansa Sun Girma Bashir Shine Babba Chemical engneering yayi sai Usman Wanda ya karanci Fannin Na"ura sai Aliyu Wanda Karanci karantun Lauya,,Hannatu da Rukkaya kuma kowace Tayi Aurenta Tana Cigaba da karatunta a Dakim Mijinta.
Rukayyah Tayi Aure agarin Kanon Ta Dabo ne,Tana Auran wani Dan Siyasa ne sai Hannatu Wacce ta Lula garin lagos Tana Auran wani Dan Canji ne Dukkansu sun gama Degree dinsu Basa dai aiki ammh kowacce Tana Kasuwancinta ta Tsaya da Kafafunta.
Dr.Saulawa yaso Dayan Burin nashi ya Cika Na samun Daya Daga Cikin ya"yansa wani ya gajeshi ya zama Likita koda ta wani Bangaren ne ba Bangaransa ba Ammh kana naka Allah na nashi ne,Hakan bai samu Tunda Duka ya"yansa Nashi basu da wannan Ra"ayin sai ya kyalesu ya Binne abun Aransa yana Tunanin inda da Rai da Rabo Allah zai cikamai Burinsa ko ba akan ya"yansa ba akan Jikokinsa da zai samu ta Tsatsansu Tunda shi karfinsa karewa yake bawai Raguwa ba.
Asibitin Daya Gina ya samu karbuwa Domin ya samu Shawara da kuma Taimakon manyan Likitocin Duniya musamman Likitocin kwakwalwa Shashi Guda aka Bude acikin Asibitin Saboda masu Wannan Fanni Dr. Saulawa da kansa yake Attending Din patient dinsa Sauran Bangarorin kuma ya kawo Likitoci Masu kwarewa Da Taimakon Abokan aikinsa da Abokan karatunsa da kuma yan"uwansa Harda Taimakon ya"yansa Dana Matarsa Tunda Da Farko yana ganin kamar bazai iya ba Sai kuma gashi Da Taimakon Allah da kuma ganin Niyyarsa komai ya zama Sai Tarihi.
Dr.Saulawa Mutam ne nagari kuma Mai Daraja acikin Idanun Mutane da suka sansu su kuma San Labarinsa,Game da ma"aikatan Gidansa Shi mai Kirki game da Likitocin Dake aiki Dashi asibiti Mai kirki ne kama Daga ma"ikatan lafiya zuwa masu matsayin Aikin Share Share da goge goge da kuma Masu kula da Shige Da Fice Duka Sun Shaida Dr Saulawa mai Kima ne Haka game da patient dinsa zakayi mamakin ganin yadda yake Tafiyar dasu ba kyama ba wani Girman kai Zai koma Kamrsu Suma Ya Shiga Cikinsu Domin mema musu lafiya Shiyasa Lokacin kalilan indai Haukan naka bq Tuburan bane Dr Saulawa zai Taimaka wajen Dawowa Dakai Cikin Hayyacinsa awannan Fanni Shi kwararre ne kuma Haziki ne.
Dr.Saulawa yana da Wani Megadi Wanda yake gadin Gidansa Mai Suna Mallam Umar Gada Wanda Dan asalinsa Haifaffan Garin Gada ne Dake Jahar ta Sokkoton Shehu,Talauci da kuma neman kudi ya barosa da Garinsa da ya"yansa zuwa Garin Bauchi yayi gadi a gidajen masu kudi Dadama da yan Siyasa bai ji Dadi ba Sai da Allah ya Hadashi da Likitan kwarai likitan Takalawa Wato Dr.Abubakar Bashir Saulawa Ya Bugeshi da Mota Lokacin yana Kokarin Komawa garinsu ne wajen iyalansa Abun ya Faru,Dr Saulawa ya Dinga Kula da Mallam Umar a asibitinsa Duk da bai wani ji Rauni ba Karaya ce da Gocewar kashi,Dashi da matarsa Hajiya Amina Wacce Mijinta da ya"yanta ke Kiranta Hajiya Mama Sunsha Dawainiya Dashi Bayan an sallameshi Dr.Saulawa da Matarsa Suka Dauki Mallam Umar har garin gada suka sadashi da Danginsa da Iyalansa.
Wannan Abun Da yayi ma Mallam Umar Shi ya karamai kima adanuwansa da kuma na Danginsa dana iyalansa Bakinsa ya Dinga Fadin Alherin Dakta Garesu,domin Da suka maidosa Gida bai barsu Haka ba sai da yayi musu Sha Tara na arziki balle ganinsu Cikin Halin Talauci da Wahalan Rayuwa Abun bai Tssya nan ba kowani Lokaci in Dr Saulawa ya samu lokaci zai zo ya Duba Jikin Mallam Umar kuma baya zuwa Hannu Rabbana kafin Mallam Umar ya warke yaga karammawa da kuma Karancin Irin na Likitan Mai Hangen nesa da Taimakon Takalawa ba Shi kadai ba yan"uwansa ma Suna yaban Hallin kirki irin na Dr Saulawa da matarsa.
Bayan Mallam Umar ya Warke sai Dr.Saulawa yazo ya zauna Dashi anan ne ya Fahimci ba wata kwakwaran Sa"ana da kuma Dalilin Daya kaishi Garin Bauchi Jin Haka yasa sai Dr Saulawa yace in bazai Damu ba yazo Gidansa ya Zauna Shida iyalansa Da matarsa Allah barshi sai ya Dinga Mishi gadi matarsa kuma ta Rika Shiga Tana Taimakama Amina Tunda Bai yi karatun Boko ba Ballatana ya Taimakamai ta wani Fannin.
Wannan Albishir din yafi komai yima Mallam Umar Dadi Yan"uwansa ma Sun Tayashi Murna,cikin Abunda bai fi Sati Daya ba Dr.Saulawa ya Turo Mota aka kwasheshi Shida Matarsa Atine da kuma Dansa kwara Daya Daya mallaka Abdullahi Zuwa Bauchi Gidan Dr.Saulawa aka kuma Saukesu a Shashin Boysquaters Inda Aka Jikasu da komai na Bukatan Rayuwa Mallam Umar da Matarsa Atine suna kuka suna ma Dr Saulawa Godiya na Irin karamcinsu garesu shi kuma yana Fadin karsu Damu.
Mallam Umar shi ya Cigaba da gadin Gidan Dr.Saulawa awanchan Lokacin bayan ya sallami megadinsa Dama Buzu ne, zai koma garinsu,Cikin Jin Dadi da kuma Cigaban Rayuwa ita kuma Atine ta zama yar gida Tunda Ta zama yar Dakin Hajiya Amina kusan a Shashensu Take wuni Abdullahi kuma anyi anyk a sakashi makaranta Boko yaki wai karatun allo yake so ganin Haka yasa mallam Umar ya Tattarasa ya maida gada inda chan aka kaishi argungu yana Makarantar allon Dayace Ita yake so.
********
*Bayan Shekaru Biyar..!*
Abubuwa Dadama sun Faru Cikin Gudun wannan Shekarun Ciki kuwa Harda kamallah Duka karatun Ya"yan Dr.Saulawa Duka Zaratan mazan nasu Wadanda Dukkansu suke da Qualification din Masters dinsu Wato Bashir ne Babba wanda ya Samu aiki agarin kaduna A Refenaring,sai Usman Wanda Ke Bimasa Wanda Shi ya samu aiki a anan garin Bauchi a wata ma"ikata Inda Suke Wallafa Littafan karatun na makarantu Dabam Dabam a matsayin Manajansu sai Karamin su Aliyu Wanda Shine Lauya Mai zaman kansa.
Dukkansu sun yi Aure Sai Dai Aliyu ya Rigasu yin Aure da Matarsa Safiya,suna Zaune agarin Abuja,Sai Usman Wanda Dr.Saulawa ya Aurama Mata Biyu arana Daya Wato Fatima da Aisha kuma Dukkansu yan garin Bauchi ne Wadanda Dr.Saulawa yayi zaman Amana da iyayensu,kuma yaji yana Sha"awar Hada zumunci da ya"yansa da Farko Fatima ce ta Usman Aisha Ta Bashir ce wanda ko kafin Dr.Saulawa ya gabatar da ita ya Riga ya gabatar da matar da zai Aura Iklima Wacce itama yar Kaduna garin gwammace Koda Dr.Saulawa ya Kawo maganar Aisha sai Bashir din ya Nuna Ita Iklima din yake so sai ya kyaleshi Ganin ya Riga kuma ya Furtamai iyayen Ita Aisha sai ya Nemi Usman din Daya Hadasu Duka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 32