ta kurama waje Daya Ido Zuciyarta na Suya Cikin Tsausayawa tace"Ukti Tashi mu koma Dakin Umma..Bari na Kwashe miki kayanki.."
Cikin karfin Hali Zaina tace"Bani ma da wasu kaya Dogayan Riguna guda 3 ne Hijabi da yan kayan kwalliya suma na Zainab ne Umma ta bani Duka kayana suna Lowcost..'Zafeera ta gyada kai kawai Ta Bude Wardrope ta kwaso mata kayan kana ta Tattara kayan Shafan gaban madubi,Dama zainab Dakin da Zaferea ke sauka ne nata Bata kwanan nan Dakin Kowa ya sani Dakin Zafeera da Zaina ne Tun abaya...
Hannunta Zafeera ta Riko Har Dakin Umma ta Saka mata kayan sawan Cikin Wardrope kayan Shafan kuma ta Saka mata Kan madubi,Ta koma ta zauna Gefen Zaina wacce Tayi Tagumi kawai Haka itama Zafeeran Tayi Tagumin ganin haka yasa Zaina ta kalleta Cikin Sanyin murya Tana Fadin"Ya naga kin zauna..? Kin fasa Tafiyar ne..?
Zafeera ta Sauke Taguminta Tana Fadin"Ina zani na barki Cikin wannan Ukti..? Ni kaina da bani bace Mijina ya aikata wannan Lamarin ina jin Dacin Dawowar yarinyar nan Gidanan Baki ji Zuciyata ba.."Mirmishin Dayafi kuka Ciwo Zaina ta saki Batayi mgana ba Daman ance Hawaye Samun waje sukayi In Bala"i yayi bala"i kukan ma nemansa kake ka Rasa.
*****
Karfe 12pm da wani Abu na Rana Su Hajiya Maimuna da Hajiya Batula da Dina suna Zaune falon Gidan Alhaji Tsoho Tabawa ta Cika gabansu da kayan Ciye Ciye da Shaye Shaye,Hajiya mama na gefe zaune ta Fito suka gaisa da Hajiya Maimuna da Hajiya Batula ba Shakka kam Hajiya Maimuna ko Hausanta baya Fita Da ka ganta kasan Daga Chan ta Fito Dina kuwa Tana Gefe Ta lafe kan Kujera Tana latsa wayarta Taci Wata Doguwar Riga baka Wacce ta Dan kamata kadan sai Tayi Rolling din da bakin gyalen Abayar Ta kara Kiba Da Fari Daga gani Cikin ya karbeta Hajiya mama sai kallonta Take Tana mamaki Dakyar Ta iya Daga baki ta gaida Hajiya Mama Shima sai da Hajiya Maimu tayi mata mgana.
Bayan sun Sha Ruwa ne Hajiya Mama Tayi musu Jagora Dakin Alhaji Tsoho suka shiga suka gaisa sai alokacin Hajiya Maimu Ta kara ganin Kimarsa Sosai Take kuka Tana ta Godiya,Alhaji Tsoho yace Karta damu bakomai Kallon Hajiya mama yayi yana Fadin"Aminatu Ki Rakasu chan Gidan Usmanan Suga inda zata zauna.."
Kai Hajiya Mama ta gyada cikinn alamun gamsuwa.
Kallonsa ya koma kan Dina wacce Take ta kare ma Dakin kallo Tana wani Tabe baki yace"Zaki zauna Gidan Iyayen Zainullahi kamar yadda na Fada Daga Farko..Ina so kin san wani Abu zaki zaman neman gafaran Allah ne da kuma Jiran Wa"adin Haihuwan Cikin ki in kika Haihu ni kuma a Tabbatar da Tsarkin ki zan Daura miki Aure da Zanullahi ammh kuma baya Nufin zaki kara Wata Hulda Makamciyar wacce kukayi da juna abaya matukar kuna so ku Hallasta Auran naku."
Kai su Hajiya Batula ke gyadawa alamun gamsuwa Dina kuwa kai ta Sadda kasa Tana Fadin"insha Allahu Alhaji..Nagode.."Kai ya gyada kafin ya sallamesu Sukayi sallama kan cewa Dagachan zasu koma Domin ba kwana zasu yi ba.
Da Farko Motar da suka zo da ita wata katuwar Jeep Hajiya mama Zata Shiga sai ga Haddir ya Dawo Daga asibiti Hajiya Mama na ganinshi tace su bari Shi zai kaita sai su bisu abaya Ko Gidan Bata bari ya Shiga ba Ta gayamai Abunda ke Faruwa Kallon Kallon sukayi tsakaninsa Da Dina kafin ya Dauke kansa Motar ya koma Hajiya mama ta Shiga yayi Riverse ya Fice Daga Gidan Suma suka Shiga Mota suka Rufa musu baya.
Suna Zuwa Afalo suka iske Nene da Zainab,Umma kuma tana Dakinta ne Nene ce ta Mike tana musu Maraba Direbansu kuma yana ta Shigo da Uban akwatina kamar za"a Bude Shago kusan Rabin kayanta Dina ta kwaso,Mamaki ya kama Nene da Haddir Zainab kuwa Dinar take kare ma kallo ganin tana ta wani Bin Falon nasu da kallo Tana wani yamutsan Fuska acikin Zucityar zainab tace"Kan Uba wannann ai yar Bariki ce.."
Saman kujerun Falon suka yada Zango suka Fara gaisawa da Nene Sai ta Umarci Zainab Data Kawo musu Ruwa da abinci Hajiya Batula tace Bazasu Sha ba sun Sha Daga Gidan Alhaji Tsoho.
Hajiya Mama dai suna Zuwa Dakin Umma ta Shiga Tunda ta Tamnaya akace Tana Ciki Zuwa Tayi tace ta Fito ba yadda Umma ta iya Dole tabi Bayan Hajiya Mama hakama Zafeera sukabar Zaina ita kadai Cikin Tsinkewar Zuciya.
Sun kawo Falon Daidai Lokacin da Hajiya Maimu ke fadin"Nice kanwar mahaifiyarta Daga Sudan Sunana Hajiya maimuna kece Mahaifiyarsa..?
Nene na Shirin Tayi mgana Umma Tayi Saurin Fadin"Eh itace sannunku da zuwa.."Dagowa tayi Tana kallon Umma kana suka gaisa Nene kuwa bata samu ma bakin mgana ba Hajiya maimu Tace"Mahaifinsa baya nan ne..?
Nene Tace"Eh yadan Fita ne.."Hajiya maimu tace"Allah sarki..Mun fa Gode Allah ya saka da alheri Sai Hakuru Duk da Abun ba Dadi ammh Tunda an samu Fahimtar juna Shikenan ga Dina nan mum kawo muku ku Dauketa Tamkar yarku Don Allah kada ku saka mata Ido Duk Abunda ya kamata Don Allah akwaba mata Da na kowa ne mugu ne sai Mai shi..'Tafada kamar Tayi kwallah Nene kadai ta amsa da insha Allahu Umma da Zafeera Dinar suke kare ma kallo ganin ko ajikinta Sai ma Latsan waya Data keyi.
Hajiya Mama ce ta Kalli Nene Tana Fadin"Nene ku kaita masauki mana.."Mikewa Nene tayi Tana Fadin"Toh Hajiya mama..Na Dauka zasu ci abinci ne.."Hajiya mama tace"Akai musu cikin Dakin.."Da sauri Hajiya Batula tace"Mun gode Wlh..Muna kan Hanya ne yau zamu koma.."
Hajiya Mama tace"Ayyah ba laifi.."Nene ce kan gaba Suka Bita abaya Bayan Hajiya Batula ta kalli Dinar tana Fadin"Taso mana Dina.."Mikewa tayi Tana gyara zaman karamar jakar Hannnunta kafin tace"Kayana fa nan zan barsu Uwata.."
Yadda ta Fadi Uwata din gatsal ne ya bama su Umma mamaki Hajiya Batula tace"Za"a Shiga dasu mana.."Da Sauri Hajiya Mama tace"jeki za"a Shiga Dasu.."Bata da yarda zatayi haka tabi Bayansu Zuwa Cikin Dakin suna Shiga Hajiya Mama ta kalli Zainab Tana Fadin"Ke zainab dake da Zafeera kuja akwatimam nam kubisu dashi.."
Dukkansu basu so ba suna Tura baki suna komai suka ja su suka Shigar mata dasu wajem akwatina Shida fa,Koda suka Shiga sun iske Suna ta mata Fada da Nasiha Nene daman Tuni ta Fice Dukkansu Falo Kowa ya Dawo ya zauna su Zafeera da zainab sun Buga Tagumi Umma Tayi Zugudi Nene ma Haka Haddir na Gefe zaune yana Latsa wayarsa Zain ya Tura ma sakon Zuwansu Dina sai shi kuma yamai sakon Abba na gida..? Yace mai A,'a cikin Sauri yace gashi nan zuwa.
Hajiya mama ta kalli su Umma Tana Fadin"Ina Baban nasu yaje ne..? Nene tace"Bai fadamana ba..Yadai ce zai fita Direban ya Daukesa kila Office yaje ko akwai wani Abu ya taso.."Hajiya mama batace komai ba sanin Ta sani Kawai dai yana Gujema Haduwa dasu Hajiya batula ne yana Jin kunyar a nunashi matsayin Mahaifin Zain Ita kuwa Dina ko ajikinta yadda kasan Cikin dam Sunna ne bana Shege ba.
Su Hajiya Batula ma basu Jima ba suka Fito zasu Tafi,Su Umma suka Mike suna musu sallama Ba wacce ta Rakasu waje sai Nene Hajiya maimun Tana ta Godiya da kuma Rokonsu alfaram suyi Hakuri Tanayi Tana Sharan kwallah Nene taji Tsausayinta Sosai Hajiya Batula kuwa Batace komai ba sanin dai Dina ba yar Goyo bace ako"ina sai Ta Nuna bata da Tarbiya.
Motarsu na Barin Gidan na Abba na Shigowa kilama sun Hadu a Hanya Yana Shigowa Falon yagansu Tsaye Cirko Cirko Ganin Hajiya mama ya Tabbattar da koma Miye Cikin Ladabi ya gaisheta Ta amsa Tana Kallon su Umma Lokaci Daya Tana Fadin"Wai ina yarintar nan Halima ne..? Tunda muka Shigo ban ganta ba..!
Umma tace"Tana Dakina..Chan nace ta koma Tunda Dakin nasu ya zama na zaman wata.."
Hajiya mama tace"Hakane..Ammh itama Alhaji yace Ki maida ta Gidan Mijinta zai fi zamanta anan Fatima..Sai fa hakuri Abunda ya Faru ya Riga ya Faru in muka sa Hakuri komai zai wuce ne.."
Da Sauri Umma Ta Mike Tana Fadin"A"a Hajiya Mama..Wannan karon ba Gaddama ko Jayayyah da Umarnin Alhaji Tsoho zanyi ba...Na Riga na yanke Shawaram Raba Auran ZAINULLAHI DA ZAINA..!!
DAM!DAM...! gaban ZAINA dake make Daga Kofar Dakin Umma Tana Jin Abunda ke Faruwa afalon sannan kuma Haka Gaban Zaina yayi wannan Bugawar Lokacin da yake sawo kansa Falon Nene,Abba,Hajiya Mama,Haddir,Zainab sai da suka Gwalo ido suna kallon Umma Banda Zafeera wacce ta Kada ido alamun Daidai kenan.
Kowa ya kasa mgana ba Illah Umma Data Cigaba da Fadin"Dama Lokaci kawai nake jira kuma yayi Lokacin..Saboda Haka ya kawomin Takardan Sakin Halimatu Bazan bari Ta kara zama dashi ba Ballatana Har Cin Amanarsa ya kasheta Lokacinta baiyi ba..!
Tafada Tana kauda kai Daga kallon Da Abba da Hajiya mama ke mata Muryan Zain suka ji wanda ba wanda yaga Shigorwarsa Falon Cikin Rauni kamar Cikin Muryan kuka yace..'
"UMMAAA....!
*Shakira...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
2️⃣6️⃣
"Gabadayansu suka Juya inda sukaji Tashin Muryan Zain din Yanayin da suka ganshi Dukkansu sai da ya basu Tsausayi Hatta kuwa da Abba Dayake Fushi Dashi.
Durkushe yake kan gwiyoyinsa Daga Kofar Falon Domin Tun Lokacin da Umma ta Furta Rabashi da Firstlove yaji kafafunsa sun Gaza Daukansa Gabadaya Nan ya zube Bisa Gwiwoyinsa Idanuwansa sun kala Sun Jajir Cikin Wata irin Murya mai Cike da Rauni yake Fadin"Ummaa..! Don Allah..! Don Darajan Ma"iki ki yanke min kowani Hukunci Ammh banda Wannan bazan iya ba...Wlh kikace na Rabu da Fisttlove na Tabbata Ranar da na Saketa Nima Ranar zaki Rasani na Har Abada..!
Yafada yana Sakarmata Idanuwansa Cikin Tabbatar da mganarsa Cikin Wani Irin Rauni da Tsausayi uwa kan D'anta Umma Taji kuka ya kwace mata ammh sai ta kauda kai da Sauri Cikin Daga Murya tace"Karya kake...Karya Kake Zainullahi...Baka son Halima da kana Sonta da baka aikata Abunda ka aikata ba,kaji ma Rantsuwan Dan Musulmi Wlh Tallahi Sai ka saketa Domin Har Abada bazata Cigaba da zama Dakai ba.."
Ba zain kadai ba Hatta Abba wannan karon sai da ya kara sakarma da Umma Ido Saboda Jin yadda ta karfafa Rantsuwarta Haddir ya Zaro Ido Cikin Tashin Hankali yana kallon Zain wanda yayi zaman yan Bori akasa Zaina kuwa Dake make kuka ya kwace mata In zata Fito ta Fadi gaskiya koda wannan Al"amarin ya Faru Kaunar Dake tsakaninta da Firstlove bata ma Girgiza ba Tana Jin in ta Rabu Dashi bazata iya kara son wani Da Namiji ba acikin Rayuwarta,Lokacin da Umma ke Fadin bazata koma Gidansa ba Ta Dauka Daga baya in Komai ya lafa zata ssuko ammh Yau kam ta kara Tabbatar ma da kanta Cewa da Gaske Umma take zata raba Auranta da Firstlove wanda Allah ne ya kulla wannan kaunar Junan Tun tana Cikin Uwa Gareta Maryama.
Cikinta Ta saka Hannu Tana Shafawa Cikin kuka da Hawaye da kuma wani kaunar Abunda ke Cikinta Ta kara Tabbatar ma da kanta Tana Dauke da Cikin Firstlove acikin mahaifiyarta wani Soyayyah da Kaunar Cikin nata suna kara kamata Har yau har Gobe Tana Son Uban Cikinta Shima Cikin Tana Sonshi ammh Taya zata Bijera ma Umarnin Umma..?Matar data Sadaukar da Farincikin Abunda ta Haifa Saboda nata Farincikin..?.har Abada bata jin zata iya Bijirema mganarta Taji tagani Duk Abunda ta yanke akanta Daidai ne, Koda Hakan zai sama Sillar Rasa Numfashinta ne ammh Taya ya zata Dauki Batun Rabuwarta da Firstlove kila Rabuwar nasu Tayi sanadiyar kaita Lahira ba wannan al"amarin da Umma Take hangoshi a matsala ga Rayuwarta ba.."
Kowa kallon Umma yake cike da mamakinta Barin ma Nene Data Bude baki kawai Tana kallon Umma Zafeera ce kadai bata wani Damu ba ammh ita kanta Rantsuwan Umma ya bata Tsoro Hajiya Mama ce tace"Haba Fatima wannan Uban Rantsuwan fa..? In rai ya baci Hankali ake sakawa ya Nemoshi ai...Dukkanmu nan Ahali Daya ne kuma Abunda ya Faru bamu isa mu Kauda Faruwarsa ba Haka Allah yake lamarinsa ya Fitar Da Rayyaye Cikin Mattace kuma ya Fitar da Mattace Cikin Rayayye Bai kamata ki Daga Hankalinki ba Tsakanin mata da Miji sai Allah ki maida Ta Dakin Mijinta sai kiga sun Daidaita koma yazo ya wuce Batare da an samu Wata Matsala ba.."
Kowa kalaman Hajiya Mama yasa ya Kore Mganar Umma sai dai Umma kada kai Umma Tayi Tana Fadin"Hakane Hajiya mama ba naki jin mganarki bane..Na Riga na gama yanke wannan Hukuncin Tun Sadda abun ya Faru..Kawai kuce ya sakarmin yata yaje ya zauna da wacce ya zaba kawai.."Tafada Tana Dukar da kanta Daga kallon Da Hajiya Mama da Nene ke Binta.
Cikin Mamakinta Hajiya Mama tace"Ikon Allah..Fatima an Taba irin wannan kuwa..? Ki Dage kice Zaki Raba auran da bake kika Hada ba Fatima anya..? Umma ta Kada kai Tana Fadin"Na Riga na Rantse Hajiya Mama Sai ya saketa.."Da sauri Hajiya Mama tace"Tabdijam kya kuwa yi kaffara Fatima.."
Nene Tace"Tabbas kuwa..'Cikin Jin Haushin Umma Abba dai na Tsaye bai yi mgana yau kam Tsausayin Zain ya Shiga Ransa Shiyasa ma Tun dazu ya kasa Cewa komai ita Kuwa Dina Tana Cikin Dakin da aka Sauketa Ta gama Duba ko"ina Har Cikin Tiolet din sai da Ta leka taga Komai Tsab ita kanta tasan karyanta Ta Raina Gidan su Zain kan gadon Ta koma ta kwanta Tana Lunshe ido Lokaci Daya Tana Shafa Cikinta Cikin so da kauna Take fadin"Na fara kusanci da Babanka..Lokaci Kadan ya Rage na zama Rayuwarsa Gabadaya..'
Take Fada Cikin Farinciki Domin Kaf Rayuwar Dina ya Tafi ne kan So da kaunar Zain mallakarsa kadai ne agabanta Wayarta Ta jawo ta Kira Zakiya suka Fara mgana Tana gayamata sun iso Tun dazu Har su Hajiya Batula sun kama suna Cikin mganar take ta Jin Tashin Hayaniya Daga Falon ta basar ganin Abun na kara yawa ne yasa Tace ma Zakiya zata Kirata Tatashi Ta Bude Kofar ta Fita Domin Taga kuma Hayaniyar me ake kuma..?
Turus Tayi Daga Kofar Dakin ganin Zain Durkushe akasa ya Hada kai da gwiwa gasu Abba da Umma da su Nene tsatsaye,Kamar wani Abu na Faru mamaki ya kamata sai dai Zain kawai ta kurama Ido Cikin Tashin Hankalin ganin yadda ya koma Kamar ba Zain dinta ba Tuni Taji Hankalinta ya Tashi ta Fara Taku zuwa garesa Taji Muryan Nene Tana Fadin"Abban Saudart Don Allah ka Saka baki mana..'
Abba yana kallon Zain yace"Me kikeso nace Nene..?Tamin daidai ai mganinsa kenan komai ya Faru Dashi ai shi yaja ma kansa Daya Tsaya inda Allah ya Ijiyesa da Duk haka bata Faru dashi ba Bani da ikon Cewa wani Abu kan Hukuncin Fatima ayanzu haka Nene.."Jikin Nene Yayi sanyi Kawai sai ta Juya wajen Umma Tana Fadin"Don Allah Umma Zareena ki janye wannan Hukuncin ko don Tsausayin Halin da yaron nan yake Ciki..'
Umma ta kalli Nene Ido Cikin Ido kafin Tace"Yauwa Ki gayama Da"nki ko ki Tursasa ya sakarmin yata..In har ya bani Takardam sakinta ni kuma nayi mai alkawarin Ranar zan yafe mai..! Galala Nene tayi Tana kallonta Jin haka yasa Zain ya Dago kansa ya Fara jam kafa Zuwa Gaban Umma ya Rike kafafunta yana Fadin"A"a umma ba wannan Hukinci ba..Naji ki bani wani mai Wahala ammh wannan Fa Daidai yake da Barazan Rasa Numfashina.."
Yafada yana sakarmata kuka Nene da Zainab masu Saurin kuka Suma kukan suka saki na Tsausayin Zain ayayinda Zaina Take Labe Tana nata,Dina ma Cak Take Tsaye Tana sauraran Kowa Dake Falon da kuma kallon Zain dake wannan kukan in Ta Fahimta Daidai kamar mganar saki take jin anayi..? To wazai saka yake fadin Kamar Barazan Rasa Numfashinsa ne..? Firstlove wata Zuciyar ta bata amsa sai gabanta ya Fadi ashe an kashe maciji ne ba"a Sare kansa ba Yanzu ita Firstlove yake fadin in ya Rabu da ita zai iya Mutuwa daman tasan Za"a Rina Raba wannan Soyayar Ba abu bane mai Sauki Gyara Tsayuwa Tayi Tana so Taga Karshem Episode din.
Jaye kafarta Umma Tayi da Sauri Ta kauda kai bata son kallonsa kar ya karya mata Zuciya ganin haka yasa ya koma Gaban Abba ya kama kafarsa yana Fadin"Allah ne gatana Abba kai ne gatana..Don Allah ka tayani bama Umma Hakuri kada Ta Rabani da Firstlove.."Shuru Abba yayi yana kallonsa ganinsa yana kuka sai ya karyamai Zuciya Da Sauri kawai ya kwace kafarsa ya Juya Zuwa Shashensa yana Share kwallah Kowa ya Bishi da kallo Cikin alhini.
Yana Tafiya Hajiya Mama ta Duka ta saka Duka Hannuwanta Ta Dago Zain tana Kallon Umma Lokaci Daya Tana Fadin"Meyasa kike da kafiya da Taurin Zuciya ne Fatima..? Kalli yadda yaron nan ya koma..? Baki da Tsausayi ne karfa ki Manta Ke kika Haifi Zain da Cikinki ammh baki Taba Dubansa da Kallo Uwa da D'anta ba ko Sau Daya ba..?haba don Allah koda Aisha ke miki kara ai batace karki So Abunda kika Haifa ba ko... ? Yakamata ki Sausauta ma Zuciyarki Don Allah.."
Umma ta Dukar dakai Tana Fadin"Don yana D"ana saboda Farincikinsa sai na bari Rayuwar marainiyar Allah ta Gurbace..? Kun Taba Tunanin Wani Hali yarinyar nan take ciki game da Abunda ya aikata mata..? Kun taba auna ya Girman cin Amanar wanda kafi yarda dashi yake..? Tana matsayin matarsa fa wacce ta Dauki Dukkan wani Son Da kauna da yardanta ta bashi Rana tsaka ace yana Tarraya da wata Harda Ciki..? Taya a matsayinta na mace mai Rauni Zata Dauiki wannan..?yarinyar nan kwana take kuka bata Cin Abinci bata Barci Saboda shi..? Shikenan don yana Namu bazamu Nuna masa Kuskuransa ba..? Bazan janye maganata ba sai nabi mata Hakkinta ya Saketa Ta zama Bata da Nauyin Kowa akanta Shi kuma ku aura masa Dadironsa Tasa su Cigaba da zama da ita ya zaba.."Umma nagama Fadin haka Ta Raba ta Jikin Hajiya Zata wuce sai Suka Hada ido Da Dina Dake tsaye tana mata wani kallo Sai yanzu ta Fahimci komai kenan Nene ba Shakikiyar uwa take ga Zain ba Umma ce mahaifiyarsa kuma Uwar Rikon Halima Shine yasa zata Kirata yar zaman Dadiro Lalle nema Kallon kallo sukama Juna Kafin Umma ta kauda kai ta Wuce Dakinta Tana Jin wani irin Takaichi da bakinciki in Taga Dina agabanta.
Kowa afalon sai Lokacin Yaga Dina Bayan kuma mganganun Umma sun kashe musu Jiki Zain ma ya ganta Kallon kallon sukayi ma Juna cikin wani yanayi itama mai kallo So da kauna da kuma Muradi mai Girma Shi kuma yana Binta da wani kallin Tsana wanda yake jin yana Fitowa Daga karkashin Ransa Da farko Baya Jin yana Tsanar Dina ammh Tabbas yasan ba sonta yake ba kuma Wata Cikakkiyar Sha"awa game da ita baya Jinta sai dai kawai wani Abu ne da zamu kirashi kaddara Daga baya ya Fara Sha"awarta Sosai wanda in bai je gareta ba yake jin kamar zai Mutu ammh Tunda lamarin nan ya Faru yaji komai ya Fara Fita kanshi,Baisani ba Tun mganar daya Fadama Alhaji Tsoho ya Fahimci Dina bata bar mai Jika Haka Kurum ba, ya Dage da addu"a kuma Shima ya gayamai ya Daina Sakaci da addu"a wannan Dalilin Shi ya Raunana Sihirin Jikin Zain wanda Alhaji Tsoho ya Lalatashi Domin Zain yazo Wajensa yana bashi Ruwan addu"a wanda akayi Acikin Ruwan zamzan yana Sha,ayanzu ma Haka maimakon yaji wani Abu Daga gareta sai kawai yaji wata sabuwar Tsanarta Tana Huda Birnin Zuciyarsa yana Tunanin komai ya Faru dashi ayau itace Silan komai.
Kowa Bin Dina yake da kallo Haka kowa da nashi Tunanin akanta Itama Tsaye take tana kare musu kallo ko kunya bata Jiba,Haka ma Zaina Dake Labe Take kallon Dina Sai dai bayanta Take gani Tunda tabama Fuskarta gaba ne ba Baya ba Haka kurum Taji cewa itace Tunda ita kadai bakuwa awajen Ballatana yadda Taga kamar Zain na kallon Barayin Datake Duk da kallon na Tsana ne ammh hakan bai saka Zaina ta iya Fahimtar komai ba Tana kallonsu Hawaye na Bulbulowa Ta Cikin Idanuwanta bata da kwanan Amin sai dai kawai ji Tayi Umma ta sakar mata Rankwashi atsakar kanta kana ta Dago a Firgice Taga Umma gabanta Tana Auna mata da Wata Uwar Harara Kanta ta Dafe Tayi Kasa da kanta Tana Hadiye kukanta.
Cikin Takaichinta Umma tace"Uban wa kike leke..? Kuma kukan mi kike..? Saboda nace ya sakeki kike labe kina kallonsa kina kuka...?
Da Sauri Zaina Tace"Ah..Ah Allah ni bashi..Bashi nake kallo ba.."Cikin Bacin rai Umma tace"Uhm...Kin zata bansan Halin da kike ciki bane..? Ina Kokarin kwato miki yancinki kina Kokarin ni kuma ki bani kunya ko kuma nace ki Nuna min iyakata ko..? Zan cire Hannuna akan Lamarinki Sai ki je chan ki koma Mai ni kam ba Ruwana Tunda Har yau har Gobe bai bata miki ba ahaka kike kukan Sonsa da Tsausayinsa.."Umma Ta gama Fada Cikin Sababinta.
Da Sauri Zaina Tace"Allah Umma ni ban ce zan baki kunya ba..Kuma zan karbi Duka Abunda kika Yanke da Hannuna Duka Biyu kece Uwata Harda Ubana Umma Taya zan Baki kunya..? Zaina Ta Fada Tana kuka Umma Taji Dadi ammh bata nuna mata sai kawai ta Shige Cikin Dakin Tana Fadin"Ki koma ki samu wuri ki zauna ki koma maida wannan Hawayen naki Don banga Dalilin Fitarsu ba..Yanzu zan kawo miki abinci kici ki kwanta Allah sa kuma ki Cigaba da kukan naki..."
Sum sum Zaina ta wuce ta zauna kan Wata Kujera kwara Daya Dake dakin Umma ta maida kanta kasa Tana Hadiye kukanta Lokaci Daya da Share Hawayenta Kallonta Umma Tayi kafin ta Girgiza kai ta Bude Kofar Tiolet ta Shiga ta Rufo.
Achan Falo kowa ba wanda yabi ta kan Dina sai Nene wacce ta kalleta Tana kakalo Mirmishi Take Fadin"Kina Bukatar wani Abu ne yata..?
Cikin wani irin kallo Dina Ta Rausayar da kanta kafin tace"Nop..Sai dai ina Bukatar hollandian mai sanyi Domin bana iya cin Komai in ba ita ba..Komai naci bai zama acikina sai na amayar dashi.."
Tafada Cikin wani Salo Lokaci Daya Tana Shafa Cikinta Tana kuma kallon Zain Lokaci Daya Tana wani kashe mai ido Daya Kowa kuma ya ganta Haddir Dake zaune bai ji wani mamaki illah wani sakaran kallo Daya Bita Dashi Zain kuwa Takura yayi ya mike kamar zai yi mgana sai kuma ya fasa Kawai ya Juya da Sassarfa ya Fice Daga Gidan Haddir ya Tashi zai Bishi Hajiya Mama tace"Kai ina zaka tafi ka barni..? Dawo yanzu zamu tafi.."
Bai yi mgana ba yace"Ki sameni a waje kawai.."Yafada Lokaci Daya yana wucewa da Sassafar Duk Saurinsa bai cimma ba Zain ba yana Fitowa Haraban Gidan Motarsa na Ficewa sai kawai ya koma Jikin Motarsa Yana Latsa wayarsa ammh Cikin Ransa Damkan da Damuwa da kuma Tunanin wani zama zai Gudana da Dina da su Umma acikin gidanan.
Nene ce kadai tace"Allah Sarki..Bari a samo miki ai sai a hankali.."Tafada Lokaci Daya Tana kallon Zainab kafin tace"Zainab jeki ki Dubata Cikin Fridge din Kitchen Nasan baza a rasa ba.."Ba yadda Zainab ta iya Dole ta mike zuwa Kitchen kana Dina Ta Juya Tana Fadin"Ta kawo min ina ciki..Plz ta Hadomin da Cup..."
Tafada Tana Juya mazaunanta Zuwa Cikin Dakin Har ta Shige suna Binta da kallo sai da ta Shige ne Hajiya mama tace"Tabdijam...Allah ya Shirya..! Nene tace Ameen Zafeera kuwa baki Ta Tabe Tana Fadin"Dama duk wanda ya sai Rariya Daman yasan zata Zubda Ruwa.."Daga haka ta mike Zuwa Dakin Umma ta samu zaina Inda Ta zauna Tundazu ammh Ta Daina kukan sai na Zucci Tana ganin Zafeera ta sakarmata yake Tana Fadin"Tafiyarki inaga sai gobe ko..?
Zafeera tace"Eh mana...Kinga na manta Dazu ban dauko karamar Jakar da nazo da ita ba achan Dakin.."Zaina tace"Kije ki Dauko mana.."Zafeera Ta mike Tana Fadin"Yanzu kuwa ina Umma..? Zaina tace"Tana Kitchen inaga.."Daga Haka Zafeera ta Fice sai da ta Fara Lekawa Kitchen Taga Umma ne ke Zuzzuba abinci Cikin Kololi Zainab kuma na Gefenta Tana Taimakamata kenan har ta kaima Hakimar Sakon nata,Falon Ta kallah ba Kowa Hajiya mama na Shashen Abba Nene kuma Tana Dakinta Juyawa Tayi zuwa Dakin da sallama Ta Shiga lokaci Daya Tana Tura Kofar Zaune kan Gado Dirshan ta isketa tana waya Gefe Daya ga karamin Farantin da Zainab ta Doro mata Holladian din da Kuma Karamin Cup.
Dagowa Tayi Tana kallon Zafeera da Manyan Idanuwanta Itama ta sakar mata nata Batare da Tayi mata mgana ba ta Nufi Wardrope ta Bude ta Dauki Karamar Jakarta Gabda Zafeera Zata Fice ne ta Saka baki Tana Fadin"Hy ji mana.."
Da kamar bazata Waigo ba sai dai ta waigo Tana kallonta Cikin yanga Dina ta katse wayar datake da Hajiya Maimun ta Kirata Taji ko sun kai tace suna Hanya ammh sun kusa,Lokaci Daya Tana Fadin"Arm...Zaki Kwashemim kayana dake cikin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 32