Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Haddir yace"Hmm koma miye kai ka sani Nidai ina Fadamaka nan ba London bane Bauchi ne Wlh Zain ina Jiye maka wani Tsoro ka dawo Cikin Hayyacinka Nidai nagaya maka Tuni nace ka sallami yarinyar nan Ta kama gabanta Ammh kaki In banda kana da Manufa miye na gayyato ta nan Tayi aiki Damu..? In gaya maka ina jiye maka Mtsala Ne..' Karamin Tsaki Zain yaja yana Fadin"Zato Zunubi Dai koda ya kasance Gaskiya ne..Kuma Hadisi ne guda Ka Rika kyautatama Dan"uwanka Musulmi Zato.."Daga haka ya wuce Ya bar Haddir nan Tsaye yana Binsa da kallon Tsausayi kuma Har acikin Ransa ya yarda da Zarginsa akan Zain ganin yadda yayi wani Wiki Wiki Dashi kada kai kawai yayi ya Bude Murfin Motansa ya Shiga acikin Ransa yana yima Zain Fatan Shiriya Zain kuwa har ya isa Office dinsa yana Juya Mganar Haddir Tabbas yasan gaskiya yake Fadamai ammh Taya zai iya yakice Dina..? Yayi iya bakin Kokarinsa wajen ganin ta bar Rayuwarsa ammh Abu ya gagara Shi kanshi yana Tsoron Wani abu ya Faru ya Tabbata Cikin Ahalinsa ba wanda zai mai Uzuri uwa uba kuma Zainarsa da wani ido zai Kalleta..? Haka ya wuni Sukuku kamar mara lafiya La"asar ya bar Cikin asibitin zuwa Gida Yaje yayi wanka ya kwanta yana ganin Kiran Dina yaki Dagawa sai ma ya Lalubi Zareena yace ta bama Umma wayar,bayan an bata sun gaisa ya Fara Complain din cewa Matarsa yaushe zata Dawo Umma tace suna Tafe Dole ya Hakura ya maida Wukar ammh Shi kanshi yasan yana Bukatar Matarsa ta Dawo Hakan nan Tunda Sukayi aure Bai Taba bari Taje wani Waje ta kwana Fiye da Biyu ba Shiyasa yake Jinsa Wani Iri. Ranar asabar su Umma suka Dawo Ta lagos suka Sauka nan Suka kara kwana Washegari Umma da Halima suka Bi Jirgi zuwa Bauchi Ita kuma Zafeera ta Hau Jirgi zuwa kano Taso Binsu Umma zuwa Bauchi Gabatowar Test dinsu yasa ta hakura ta koma kano sai sun samu Hutu,Zain bai ma san Ranar zasu dawo ba sai da ya Dawo Daga asibiti yaji Gida na Tashin kamshi,sai ga Zainarsa tazo ta Rumgumeshi Tana Murnan ganinsa Shima kamkameta yayi Yana Bayyana mata yadda yayi kewarta Ranar dai kwana sukayi Suna Bayyana ma Juna yadda Sukayi kewar Juna. Washegari kuma Monday ta koma makaranta Ranar kuma suka Fara Test ba zama Sai Hankalinta Duk ya koma kan karatunta Tunda Suna Tun karar Exams Din Second Semister ne,Don ma Allah ya Taimaketa Laila tayi mata Wasu Assigment din Da Data samu Gibi da yawa ba kadan ba. ***** Sannu Sannu bata Hana zuwa sai dai adade ba"a je ba Gashi Har Su Halima Sun kamallah Test dinsu na makranta Haka ma Su Zafeera,Shiryen Shiryen Fara Jarabawa suke yi nan da Sati Daya Gabadaya Hankalin Halima ya koma kan Makaranta da karatu bata ma samun Lokacin kanta hatta Gidan Umma da Gidan Alhaji tsoho Sai Ranar Sati Take samun Zuwa Saboda karatun Jarabawa bata da wata Natsuwa. In Ta Shiga Cikin makaranta sai yammah Take Dawowa Suna Chan Libarary ita da Laila da Sauran mates Dinsu Suna karatu,Hakama in ta Dawo Gida Zata Dukufa Sallah kadai ke Tashinta,Sai kuma wani aikin Daya Shafi Mijinta Shi kanshi Zain Din Tsausayamata yake yanzu ganin Ta saka Karatu acikin Ranta Sosai Shiyasa Girki ma sai Weekend take yi Musu Sai Breakfast kafin su Fita daSafe Da Rana kowa Wani Abu yake nema yaci Da Daddare kuma Kafin Zain ya Shigo Gida yake Biyawa wani Restaurant yayo musu Takeway suci Su kwanta Wani Lokacin Har sai ya kwanta ita bata kwanta ba Tana Falo Tana karatu Har sai ya Farka ne in ya Laluba yaga bata sai ya Fito Falo ya Tattara ta zuwa Ciki Toilet yake Turata Yayi mata wanka Wani Lokacin ma abinci sai ya Zaunar da ita ya bata take iya ci Ta Riga ta saba Da Abinci Shi yake Ciyar da ita da kansa Shiyasa Dagashi Har ita In Kowanne ya Tafi Laluransa Da Rana ba wani Abincin Kirki Suke zama su Ciki ba Saboda sun Riga sun Saba Da Ciyar da junansu. Bangaran Dina kuwa Ta Yarda da plan din Da Zakiya ta kawo mata Duk da Tana Tsoron Zubewar Mutuncin Mahaifinta ammh Zakiya ta Nuna mata Daga Mahaifinta har iyayen Shi Zain din bazasu zo mganar ta Fasu Waje Ba Tunda Dukkansu Suna da kima a idon Mutane zasuyi Abunda zai zama Rufun Asirinsu ne kuma Shine Aure Tsakaninta da Zain,Ta yarda da Shawaranta Sosai Shiyasa Ta Kudura acikin Ranta Six Month Din Datayi Alluran Planing Din Datayi yana karewa Bazata karayi ba In Allah ya Taimaketa Tsarinsu ya Tafi Daidai kamar yadda Suka Tsara,Acikin Zuciyarta Batason Faruwar hakan ammh ya zama Dole ne Tunda Tana son Son Zain kuma Tana Son Kasancewa Tare Dashi Har Abada Har yau har gobe In Tayi mai mganar Aure sai ya kara Maimaita mata bazai Taba Auranta ba Tunda bai Taba Cewa yana Sonta ba ya gayamata ba tun yau ba Mace Dayace Matarsa itace Zaina bazai iya Auran wata mace ba bayan Ita da irin Wadanan kalaman yasa Ran Dina ya kara Baci Batare da wani Dogon Tunani ba ta amince da Shawaran Zakiya ammh Bayan ta sun kara zuwa Wajen Bokan Zakiya na Hanyar kaduna Daman Zakiya ta kaita wajensa Shi yake mata aiki kan Alhazanta ta samu alheri akansu Yake kuma mata aiki in Taga wani Alhaji mai kudi a Tsaida mata Shi ta wanki Rabonta Da suka je mai da Bukatarsu ya Buga kasa yace musu in Sukayi Haka Auran nasu zai Tabbata sai dai yaga Duhu sosai acikin al"amarin Kamar yadda yagaya musu a Farko Suka ce bakomai Kowani Duhu suna Maraba Dashi Sun karamai Zubemai kudi kan ya kara Sakama Zain Din Fitinaniyar Sha"awar Dina Wanda bazai iya kwana bai Kusanceta ba Ko zasu samu Hakkansu ya cimma Ruwa yace karsu Damu anyi an gaba su Jira sakamako kawai Sai Dina tana Koran Zain ammh yana manne mata kamar wani Tsohon Maye mara Zuciya. Cikin Ikon Allah su Halima suka Fara Zana Jarabawar Karshen Zangon karatunsu na aji Daya,Chan ma Kano Zafeera suma sun Fara,Duk wani Masoyansu yana Tayasu ga Addu"an Fatan Nasara da Sa"a,Sannu sannu kamar yau suka Fara sai gashi Sun kamallah Zafeera sun Riga Halima gamawa a kuma Ranar bata kwana agarin Kano ba Sai Bauchi sai dai su Umma suka ganta Kwatsam Murna wajen su Zainab ba"a mgana Ita Tana gida Ta Rubuta jamb sai Farkon zango karatu Zata Fara zuwa makaranta itama Din ATBU bauchi Abba yace Zatayi bayason Tayi Nisa da Gida,Su Halima kuwa sai Da su Zafeera suka gama da kwana Uku kana suna Suka gama Farinciki Kamar me bakinta yaki Rufuwa,Sai da ta kai Laila Gida kana ta Wuto Gidan Umma Direct Daman Tunda Zafeera ta Dawo basu Hadu ba aikuwa tana Zuwa Suka Rumgume Juna Suna Murna kamar Wasu yara kananan Umma na Dariyan Farinciki Tana Fadin suyi a Hankali Nene kuma na Fadin Yaranki Umma basu Girma sai na Jikinsu. Bayan gaishe gaishe Dakin su Tun na yamatanci Suka Kule Ciki Inda yake matsayin nasu Har yanzu Tunda Zafeera batayi Aure ba,In tazo Hutu nan take Sauka Itama Halimar nan take wasu Abubuwan nata in tazo Ko Dakin Umma ko Dakin Nene Duka Basu da Shamaki da Dakunan Iyayen nasu. Hira ce ta Barke Tsakaninsu Cikin Hiran ne Zafeera ta kalli Halima Tana Fadin"Wai Ukti ba wani Bayani ne..?kusan fa Shekara kadan bashi a auranku keda Yaya Dakta..! Halima Ta gyara zama Tana Fadin"Bayanin me kuma Ukti..? Zafeera tace"Dillah na Haihuwa nake mgana Tun ina kano nake so nayi Miki Tadin munji Shuru ba wani Bayani me Dadi ko matar Likita Tana planing ne..? Halima Ta Daka mata Duka a Cinya Tana Fadin"Uwar planning Din kema kin zama Hajiya mama ko..? Haka wanchan Satin da muke je gaishesu ni da Firstlove take mana Fadan wai ko muna Tsarin Iyali ne Sa"o"in Auran mu Duk sun Haihu Har fa Tsohon can yana mana Nasihan Muji Tsoron Allah.."Zafeera tace"Wlh da gaskiyansu...Yadda Alhaji Tsoho ke Bala"in kaunarku keda Yaya Dakta Zai zo Ganin Ya"yanku kafin ya bar Duniya..' Tagumi Halima Tayi Tana Fadin"Wlh Nima ina so Ukti...Allah ne bai kawo ba Kinsan Allah ban taba Shan kowani kwaya ba kuma ban Taba Allura ba Firstlove ma baazai bari ba kinsani.."Zafeera Tace"To wani Taimako kuka nema..? Ta Sauke Tagumin ta Tana Fadin"Wani Taimako kuwa Kwanaki Dana Fara mai mganar sai ya Fara min Fada yaushe Duka Duka mukayi Auran Ballatana ace bamu Haihu ba..shi bayason Irin Haka Haihuwa Lokaci ne, in Lokacinta yayi Komai zai Wuce Daga Lokacin yace na bar mganar Babu Komai Dukkanmu lafiyanmu Lau Tunda Daga kowani Bangaran mun gaji Haihuwa.." Zafeera Na Dariya tace"Kuma fa Hakane mganarsa...In Lokacinta yayi Burum zamu ji Ukti na Faman Laulayin Ciki ana Tsirtar da yawu.."Ta fada tana wani yamutsa Fuska Duka Halima ta kaimata Ta Goce Tana Fadin"Kefa Ukti Saurin Hannu ne Dake ga Zafin Hannu Wani Lokacin.."Dariya Halima Tayi Tana Fadin"Kema din kwana nawa ne..? Alhaji Tsoho zan Zuga nace ya Aura miki Barrister Ahmed ko baki sonshi Kina Kano Sai da kiji Sakon kin zama Amarya.."Ta karishe Fada Tana Dariya Fuska Zafeera ta bata Tana Fadin"Allah da ban Yafe Miki ba kuwa Ukti..Kinsan yadda Na Tsani Ahmed din nam kuwa..?Ko Sunansa aka ambata sai Raina ya baci.." Ta karishe Fada Tana Bayyana Bacin Ranta ga Mganar,Dafata Halima Tayi Tana Fadin"To wai Duk meyasa Ukti..? Yana da wata mtsala ce..? Zafeera tace"Ko Daya wlh in nace yana da Mtsala na Dauki Hakkinsa..Kawai dai bana Sonshi ne Shi kuma ya cika Takura Rayuwar nan fa ba"a Dole Ukti Tun Farkon Haduwata Dashi na gayamai ba yanzu Zanyi Aure ba sso na gama karatuna Ni Ra"ayina kenan da Farko kamar ya Rabu dani sai kuma ya Dawomin Tunda yayi Bincike ya gano Ni Diya nake Wajen Dadyn Abuja Shikenanan ya kama Bina Abunda yafi Bani Haushi Har da kawo kanshi Wajen Alhaji Tsoho Dan Shishhigi ko Uban wa ya aikoshi Bansani ba.." Ta karishe Fada tana wani Murguda baki Halima ta Saki Mirmishi Tana Fadin"Shikenan Tunda baki sonshi ammh ai Aure baya Hana Karatu Ukti..Bagashi ni nayi Auran ba kuma ina karatun nawa ba..? Zafeera tace"Ke Dabam ce..Daman Tun Tasowarki ke yar Gatace Miji gareki fa ahannu Tun kafin kizo Duniya Ukti Miji kuma na nuna ma Duniya Nima danasamu gatanki ai Tare zamu Shige Daga Cikn nan nima naji Abunda ake Ji.."Tafada Tana Daga mata Gira Irin Kin gane din nan Dariya Halima ta saka Tana Fadin"Allah Nima ina son Kiji Mazan nan Ukti Shiyasa nake so kiyi Auranki Tun yanzu ki Mori Kuruciyarki.." Zafeera tace"Allah ko Ukti..? Gira taDaga mata Tana Fadin"Ba"a Fadin Dayan Abun Ukti..."Hannu Ta bata suka kashe Lokaci Daya Suna saka Dariya,Nene ce ta Shigo Dakin Nasu Tana Fadin"Ku kuma yayan Umma me kuka samu ne kuke ta Dariya Harda Buga Shewa.." Zafeera ce tace"Nene Sirri ne.."Nene tace"Eh Sirrin a Fadamin naji.."Da Sauri Halima Tace"Kaji Nenen nan keda kike Shigewa Daki kina Kuskus da ya"yanki Kina gayamana ne..? Nene Tayi Dariya Tana Fadin"Abun na gori ne..Kwa ji Dashi Dai nasan Dai Tatsuniyar Gizo bata Wuce ta Koki..Muna zaune za"a zo agayamana.."Dariya suka saka mata ta Fice Tana Kiran Umma Tana Fadin Yayanta Sai Shewa suke Suna Dariya Duniya tayi Musu Dadi Umma tace Eh karfa a Takura ma Ya'yanta abarsu su Shakata Suna Daga Cikin Dakin su suna Jinsu sunayi Suna Dariya Hakika Rayuwar Gidan Abba Usman Rayuwace Abun Koyi ga Kowa baka isa ka Bambamce ya"yan Nene da ya"yan Umma ba sai wanda Daman yasan Komai Tun Fari. Nan Halima ta Kai yammah Da Taso Takai Dare Abba ya Dawo ya Kadata Gida Daman sunyi mgana Da Firstlove Lokacin yana asibiti yace in ya Tashi Daga asibiti zai Biyo sai su koma Tare Ta Share kafa kenan sai ga Abba ya Dawo ya Fattaketa Zafeera ma taso ta Bita Gidanta ta kwana Duka Abban ya Hana Yace zasu Shiririta ta bari zuwa Gobe sai Taje,Sai da ta koma Gida ta Kira ZAIN ta fadamai ta koma Gida Yaji Dadin hakan Domin yana Son ya Fara Biyawa ta Gidan Dina kafin ya Dawo Gida Domin yanzu Abun ya koma mai kamar wani Tsafi Duk da Tsafin ne,Baya iya Hakura da Kusantar Dina Kusan kowani Dare sai ya Biya ta Gidanta Sunyi watsewarsu kana yake komawa Gida Abun ya Fara Damunshi Saboda Ko Zainarsa yakan Daga mata kafa na kwana Daya ammh Dina yana jin a kullum in bai kusanceta ba kamar zai Mutu wani Lokaci Alokaci Daya sai suyi mayawa yafi Biyar Domin daya gama Kusantarta zai ji Sabuwar Sha"awarta ya kamashi,Da yasan Ba Haka yake ba ammh ya kasa gano Dalilin Hakan yayi Callaging Din Dina Ko mganin Mata take sha Tamai Rantsuwan bata shan komai,Ya yarda da ita,abunda yafi bashi Tsoro bayajin Haka akan Matarsa ta Sunna sai akam wata Karuwa Yana kuma da yakinin Wahala kawai yake bawai Don yana samun Wata gamsuwa ba Gamsuwa da Natsuwa awajen Zainarsa kadai yake samu Tuni yasan wannan Duk Nema neman matan Da yayi Lokacin suna London ba macen Datakai Dadin Zainarsa Ita Zainarsa Dabam kawai take,Abun yana Damunshi ammh Yarasa Wazai Fadama Matsalansa Ballatana ya Bashi Shawara Haddir ne kuma saboda Dina yanzu basu da wani Fahimta a tsakaninsu,Sakacin Zain Ya kasa ya gano Wani Abu Ballatana ya iya kai kukansa ga Allah Dina kuwa kakartace ta yanke Saka Wani Farinciki Take Fama Dashi na ganin Zain ya Fara zama nata Har Abada,Sau tari har Gwadashi Take in yazo ta nuna ita ta gaji ya tafi Wajen Zainarsa mana Tasan da abaya ne Bazai kara bi Ta kanta ba sai bayan wani Lokaci ammh Abun mamaki Haka zai zauna yana mata magiya kamar yayi Kuka Haka ta Kira Zakiya Tana bata labari suna Dariya Zakiya na kara gayamata aikin Bokan bana Wasa bane Sun Dade Tare kuma yana mata aiki Tana ganin Cigabansa nan da nan Dina ta yarda dashi 100%Alhalin da Da farko Bata yarda Da Harkan Bokaye ba Zakiya ma Fada suke kan hakan sai Gashi Dalilin Zain Komai nata yakara Tarbabarewa. Washegari kuwa Tun Safe Zafeera ta Shirya tatafi Gidan Yaya Dakta wajen Halima,Saboda Sammako ma Zain yana gida bai Fita ba Tazo Daya Fito ya ganta baki kawai ya Hangame kafin yace"Ikon Allah Wannan wani irin Sammako me kamar yaki..? Dariya Suka sakamai gabadaya Kafin Zafeeran ta gaisheshi Tare sukayi Breakfast suna Hira Sama sama kafin yayi wanka ya Shirya ya Fice zuwa asibiti,Bayan Fitarsa suka koma Falo Suna Hira cikin Hirar ne ma Halima ke gayama Zafeera sati mai Zuwa Zataje gada Tayi Sati Daya Saboda Bikin Dan Wajen Goggo Halima,Dakuma Duba Dangi Zafeera na jin Haka Ta Daka Tsalle tace sai Taje Halima tace Shikenan Daman Duk Zuwan Datake Tare da Zafeeran suke zuwa nan suka Wuni Tare Zafeeran ta Tayata tayi ma Abba da Alhaji Tsoho Tuwonsu Da Takwana Biyu Batayi musu ba saboda Makaranta Da suka gama komai suka sake wanka suka Shirya Halima ta Tukasu a Motarta Gidan Alhaji Tsoho suka Fara Zuwa suka kai mai Nashi yana ta ma Zafeera Tsiyam n Ta Dawo bata zo ta gaisheshi ba Hajiya Mama tace"Tana tsoron ka Tare ta Da Sakon ka mata Miji.." Zafeera najin Haka ta Hade Rai Tana Hararan Hajiya mama Alhaji Tsoho kuwa cewa yayi"Bam ma ya"yana Dole ba Amina itama Bazan mata Dole ba ammh In ta zabi Ahmed a matsayin Mijinta zanfi kowa Farinciki.."Zafeera najin Haka ta Sulale ta Gudu Gida sai da Zaina tasameta Gidan Umma tana mata Dariya nan takai Dare Sai Wajen 10 Zain yazo suka koma Tare Motarta agida ta Barta Daman wani Lokacin Tana barinta agida In takai Dare Saboda Zain ya hanata Driving Din Dare. Da kanta ta gayamai Tare da Zafeera zata tafi Gada yaji Dadin Haka Daman Da Farko yaso Su Tafi Tare ne ana gama baki ya Tattarata su dawo Sai kuma ga wannan Halin Dayake Ciki Ta yaya zai Tafi wani gari Batare da Dina ba..? Wanda Nisa da ita kamar barazan Rasa Numfashinsa ne a koma wani Hali ne Shidai sai ya Rab'i da Dina yake jin Dadi Daman yana Cikin Tunanin mafita sai gashi Tace da Zafeera zasu Tafi sai yaji Dadin Haka yace zai kaisu ya Dawo Allah barshi in an gama Biki Taga Dangi tayi Sati Daya sai yaje ya Daukosu ita kanta Haliman Tayi mamaki Zain bai taba barinta zuwa wani Waje Tunkafin suyi Aure ta wuce kwana Uku zai ce ta Dawo Gida ammh sai gashi bai Nuna wata Damuwa ba da Farko Kamar zatayi mai mgana sai kuma ta watsar da Tunanin da Cewa Kila ganin Tare da Zafeera zata tafi Shiyasa. Shi yayi musu Dukan wani Shirun Tafiya da Tsaraba da komai Duk da Abba ma dasu Umma sunyi iya nasu Kokarin,Tun Ranar alhamis Suka Tafi Zain din yakai su Umma da Nene da Abba sai Ranar Daurin Aure zasu Taho,Tun Safe suka Fita Wajen Azahar suna Gada Abinci kawai Zain yaci yayi sallah yadau Hanyar Komawa bayan ya Cika Goggo Halima da Kudi Gudumuwa Na wajen Abba kuma Su Halima suka bata harda na Wajen Alhaji Tsoho da Hajiya Mama Goggo Halima sai da tayi kuka Ta Tuna da yar"uwanta Maryama da Dalilinta ne take ci Har yanzu Tana ta kwaromusu Addu"a Tare da Addu"an Allah yajikan Maryama da Abdullahi sai da ta saka Halima da Zafeera kuka. Cikin kankanin Lokaci Su Zafeera suka saki jiki aka Shiga Sha"anin Biki,Daman su yan Gida ne Kowa yaga Halima sai ya kara kallonta tayi kiba ta Cika Ta kara kyau da Fari Dangin Babanta Dana Mamanta kuma Sam Barka suke da Ahalin Alhji Abubakar Saulawa Domin Bazasu manta Alherinshi Garesu ba. Ranar Asabar Daurin Aure Abba yazo Shi da Dadyn Abuja da Mama Safiya da Umma da Nene Umarnin Alhaji Tsoho kena  yace Shima ba Domin Laluran kafa sai yazo,Basu kwana ba Suka Jiya,Goggo Halima Taji Dadi kwarai Har bakim Mota ta Rakasu Tana ta Godiya Su Zafeera kuma sai da sukayi Sati Cur kana suka dawo Bayan Ta Raka Halima ta Zaga Gidajen Dangi da yan"uwa ko"ina taje sai anyi mganar Rashin Samun Cikita ayi ta cewa ko suna Tsarin Iyali ne, Tunda sune Abun Sai ta Rantse da Babu Abunda Sukeyi Direban Abba yazo ya Daukesu da zasu koma Abun yabama Halima mamaki Alhalin Jiya da Daddare sunyi mgana da Firstlove ya Tabbatar mata Shi zai zo ya maidosu ammh Kuma sai taga bashi bane kuma Tun Suna Hanya Take ta Kiran Wayarsa Baya Dagawa Tuni hankalinta ya Tashi Zuciyarta ta Fara Tsinkewa zafeera ma ne ke ta bata Baki Har suka iso Bauchi. *Sannunku da kokari ZAINAZAIN BAND 1&2...naga Sharhin ku Allah ya bar Zumunci..Yan Janaf Novella 1&2 ku kuma Kun kyauta Tabbas kun kusa daina ganin Update kan Zainazaina sai dai ku karantashi Chan Waje...* *Shakira...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*            1️⃣2️⃣ "A lokacin da Zaina ke ta Kiran Zain yana gidan Dina suna ta Lalacewarsu da suka saba,Dama Tun safe yayi Shirin Tafiya Chan Gada ya Daukosu sai kuma ya samu Kiran gaggawa Daga asibiti an kawo Wata patient zata Haihu ammh kuma Kafar jaririn ne ke Turo kai Dr Aisha tayi iya bakin Kokarinta Abun ya Faskara sai anyi mata C.S Dinar ce ma ta Kirashi Ta gayamai wannan Dalilin ne yasa ya bar Tafiya Daganan shirya ya Tafi asibiti,Bayan yayi ma Matar C.s An Fitar da Abunda ke Cikinta ba Rai sai kuma ga Wani Case din makamanciyar irin Haka sai dai ita Biyu ne acikinta Daya ya Danne Daya ganin Zasu sake Shiga Theater Room ne yasa ya Daga waya ya Kira Nene yace Ta Tura Direban Abba ya Daukosu yana Busy ne Bayan Haka ma Asibitin Ranar ta Rikice Saboda akwai wasu yan Daurin Aure da zasu shigo Bauchi Suka samu Hatsari Yawanci Duk asibitin Aka Yo da masu Raunin,Su Dr Imran ke kula da wannan Barayin Bayan sun Fito Daga Tiyatar ne Dina ta Ribaceshi Ta Jashi Gidanta,Da Farko gida yaso ya koma yayi wanka ammh Ta Hillaceshi ya bar Motarsa Cikin asibiti ta Tukashi Zuwa Gidanta Chan suka Tube Ta Hillaceshi da Salonta suka Gama Tambadewarsu a Tiolet kafin Suyi Wanka su Fito Bayan sun Fito Tayi musu Girki Sukaci Ta kara Hillatanshi Suka koma Ruwa Tana Dariyan keta Domin Ita ta Saka wayarsa a Silent Saboda Bata so wani Abu ya Katse mata Jin Dadinta Abun Takaichi Dukkansu ba Wanda yayi Sallar azahar ita batayi ba kuma bata barsa yayi ba Shiyasa Halima keta Kiran Wayar nashi Baya Dagawa. Wajen Biyu na Rana Suka Iso Gidan Umma suka yada Zango da Tsaraban Gada Sukayi Sallah suka ci Abinci,Shuru Firstlove bai Kirata ba Hankalinta ya kara Tashi Tayi wani Sukuku da ita Zafeera ce ta Lura da Halin Data ke Ciki Ta Kalleta ganin ta da waya a Hannu Cikin Sigar Tambaya tace"Wai har yanzu bai Daga wayar ba...? Tafada Tana kallonta Kai ta gyada mata kafin Ta zabga Tagumi Tace"Wlh Ukti Hankalina ya Fara Tashi Anya Lafiya..? Zafeera bata samu Zarafin mgana ba sai ga Umma ta Fito Daga Dakinta ganin yadda Halima Tayi ne yasa ta zauna Gefenta Tana Fadin"Ya"yana meke faruwa ne..?nga kamar kuna cikin Damuwa ne..? Zafeera ce Tace"Ukti ne ke ta Kiran Ya Dakta Tun muna Hanya bai Daga ba yanzu ma Ta kara Kira Still bai Daga ba kuma bai Kira ba.."Takarishe Fada Cikin Sigar Damuwa tana kallon Zaina wacce ta Yi kamar ta Fashe da kuka,Kallonta Umma Tayi kafin Tace"Inaga aiki ne yamai yawa..Domin Shi ya Kira Nene da safe yace atura Direban Abbanku ya Taho Daku aiki yayi mai yawa a asibiti.."Da Sauri Zafeera Tace"Kinji ko Ukti Don Allah ki kwantar da Hankalinki Insha Allahu Komai Lafiya.." Umma ta Dafa kanta Tana Fadin"Karki Damu Ya'ta..yaron Nene yana lafiya kinji ko..? Kai ta Dagama Umma Lokaci Daya da Kwakulo Mirmishi Wanda iya Saman Fuskarta ne bai kai Zucci Domin Haka kurum Take jin Wani Tsinkewan Zuciya Hira suka Fara sama sama da Umma Sai kawai ta Fara Hamman karya Umma ta kalleta Tana Fadin"Barci.? Maza jeki kwanta kafin an juma ki wuce gida.."Daman Abunda Take so kenan Tatashi ta Shige Dakinsu ta Fada kan Gado Tana jin Zuciyarta na Rawa Wani iri Taji ba yadda ta saba ji In Firstlove ya Tafi asibiti ba. Lambar Ya Haddir ta Lalubo Ta Kirashi Shima sai da Ta katse kana ya Kirata bayan sun gaisa ta Tambayeshi Zain yace mata Bai sani ba gaskiya ammh Yana Tunanin bashi acikin Asibiti kamar ya Fita,Gabanta Taji ya Fadi ammh Bata bari ya gane ba Tamai sallama ta kashe Wayarta Tana Tunanin Ina Firstlove yaje Daya kasa Daga wayarta Ta Tabbata ko Duba Marasa lafiya yake in ta Kirashi yana Daga Wayarta In ya Shiga Tiyata ne kadai bata samunshi kamar Wasa wata Zuciyar tace mata toh in yana Tare da Wata ne fa..?kuma watan tafiki Matsayi da kima awajensa fa..? Wannan Tunanin yasa Taji ta Fara jin Jiri Tana Daga kwance,Kwallah ya Cika mata kwarmin Idanuwanta Cikin Wannan Halin Zafeera ta Shigo Ta sameta Ganinta a Haka yasa ta Zauna Gefenta Tana Fadin"Ukti Damuwar ne..? Ko zaki Shirya muje cikin asibitin ne muga ko lafiya..? Tashi Zaune Tayi Cikin Wata kasallaliyar murya tace"Ba bukata yanzu muka gama mgana da Ya Haddir ya Tambatarmin Firstlove baya Cikin asibiti ya fita.."Kallonta Zafeera Tayi kafin tace"Ikon Allah ina yaje .? Ko gida ya koma ne...? Zaina Ta Kada kai tana Fadin"Bansani ba Ukti..Bansani ba.." Tafada Lokaci Daya Hawaye na wanke mata Fuska Cikin Mamaki Zafeera tace"Lafiya..? Haba Ukti miye Abun kuka..? Kai   kawai ta yada Saman Cinyar Zafeera Tana Fadin"Bansani ba Ukti..Haka kurum naji Zuciyata na Zafi Wata kuma na Fadamin kila yana Tare da wata ne Ukti..! In ba wata ba taya Firstlove yake kin Daga wayata Ukti..? Tafada Hawaye suna Kara Kwaranyomata. Cikin Tsausayawa Zafeera ke Shafa Kanta Tana Fadin"Kina Tsammanin akwai wata mace Datafiki Daraja awajen Ya Dakta ne..?babu Ukti ke kadai ce ba baki da Na biyu Wlh kowa ma Shaida ce.."Tafada Tana Share mata Hawaye Mikewa Zaina tayi Tana Fadin"Hakane kila Ya tafi Waje ne Da ba'a san Daga waya ko.? Da sauri Zafeera Tace"Eh hakane mu barsa ahaka Ukti..zai kiraki da Zarar ya samu Sarari.." Da haka Zafeera tayi ta Lallashin Zaina tana bata baki har ta Sauko Hankalinta ya kwanta ta saki Jiki suka

Chapter 12 of 32