Kulle ya Tufka ya warware ammh yakasa gano Bakin zare yaso ya Tambayi Sadiq sai dai Rashin Samun Fuska yasa Ya kama Bakinsa..
Dr Imran na Fita zakiya ta Fito da wayarta Tana ma Dina Rada Tana Fadin"Yanzu Wasan zai Fara Daukan Dadi..Bari na Karisa Dayan aikimn."Mirmishi Tayi mata Cikim Kwarewa Ta Shiga Wsop dinta bayan ta Bude Data Ta Lalubo Lambar Zaina wacce Dina Ta Sato mata awayar Zain Tunda Wayarsa bata da matakan Tsaro,wasu Bad pics Take Turamata wanda Dina ta Daukesu ita da Zain cikin yanayi mara Dadin kallo Wajen guda Goma ta Tura mata Sai da Ta Tabbatar daya Shiga kana ta Fita Taje Bangaran Sakoninta ta Lalubo lambarta ta Tura mata sako Kamar haka...!
*Kina Bukatar sanin wani Abu game da wanda kika bama Amanarki Da Duka yardanki..? Toh in dai kin Ci karo da Sakon nan ki Bude Data dinki ki Shiga Wsop zaki ga na Tura Miki da sako..!*
Na Farko kenan na Biyu kuma sai Tace *Nasan zaki Shiga Rudu da Dimautuwa ko..?Kina kuma neman Karin Bayani..? Toh zaki sameshi Cikakke Harda ma wadanda baki sani ba..Kiyi Hanzari Kizo gidan Kakanin Mijinki zaki samu Duka Amsoshinki yanzu yanzu...*
Tana Gama Tura mata da Ta Tabbatar da ya shiga sai ta Kashe wayar Dama Sabon Layi ta Siya Kuma saboda wannan amfanin Tana gamawa ta Taka Kafar Dina Tana Fadin"All D Plan Done..Sai Abu Daya kawai ya Rage Tabbatar da Auranki da zain.."Tafada tana wani Juya ido Dina batayi mgana ba ammh Ranta kamar Farar Takardan Saboda murna
bangaran Alhaji Tsoho kuwa Dr Imran na Fita Alhaji Tsoho ya Juya yana kallon Kwamishina yana Fadin"Kayi Hakuri fa...Bawai don ban yarda da Abunda Kazo min Dashi bane..A"a ko Daya sai Domim kada mu zama Wasu Mutanen da Marabansu da Dabbobi kadan ne..Ko miye ya Tunkaromu mu Maida Hankalinmu mu Bincika in mun Gano Gaskiya kada mu Fusata..Mu Natsu mu yanke Hukunci Yadda ya Dace.."Kwamishina na jinjina kai yake Fadin"Hakane...Tabbas na yaba da Hikimarka.."Yafada yana jinjina ma Kaifin Basiran Alhaji Tsoho.
Kai Tsaye Alhaji Tsoho ya kalli Dina yana Fadin"Diyata...Wani Shaida gareki da zai Tabbatar mana Da cewa Zainullahi ne Uban Cikin Jikinki..?
Yafada yana kallonta kai ta Dukar kasa ganin Falon kallo ya Dawo kanta Zain kuwa Tunda Yaji Abunda Alhaji Tsoho yace kansa ya kara kasa kamar wanda zai Kifa Saboda Tashin Hankali,Zakiya ce ta Rike Hannun Dina tana Daga mata kai Shiya Bata kwarin Gwiwan Dagowa ta Fara mgana"Saboda Shine kadai Saurayina..Kuma Tunda Nake Shine kadai Namijin Danake irin wannan Mu"amalan Dashi.."
Dam...Gaban Kowa ya Fadi,Kowa sai ya saki baki yana kallon Dina Alhaji Tsoho ya Cije Abunda yake ji acikin Ransa yana Fadin"Ai bamu san haka ba Diyata..? Cikin Dakiya da Rawan Murya Dina Tace"Shi ya sani..Shi yasan komai...Yafi Kowa sanin Bayanshi bana Mu"amala da kowani Namiji..Tabbas Zain yasan wannan Cikin Dake Jikina ba Shakka Shine Ubansa..!
Tafada Idanuwanta na Cika da kwallah Gabadaya sai Falon ya koma Shuru Alhaji Tsoho ya Kalli Zain Cikin Kakkausan Murya yace"ZAinullahi...Kai Zainullahi..'Yafada yana Zungurinsa da Sandan Hannunsa Firgigit Zain ya Dago kansa Idanuwansa da suka Kada suka yi Jajir ya juyema Alhaji Tsoho Cikin Bacin Rai da kuma Lalama yace"Kaji Abunda Ta Fada..?
Kallonsa ya maida kan Dina Sukayi Kallon kallo na wasu Mintina kafin ya Janye idanuwansa Cikin Rawan Murya da Datsewar Harshe yace"Ehhh...Amm..."Hannu kawai Alhaji Tsoho ya Dagamai yana Fadin"Ba Ammh na Tambayeka ba..So nake nace Gaskiya ne Abunda Ta Fada da wanda na gani arubuce Cikin Dake Jikinta Na ka ne..?
Yafada yana Tsaresa da ido kamar yadda Kowa ya Tsareshi Da Ido Zuciyoyi na Bugawa,Kowa na Jiran yaji mai Zain zai ce shi kuma Ji yayi kamar kasa ya Bude ya Shige Ciki Wata irin Nadama da Danasani ne suka Lullubeshi,Jikinsa ya kama Rawa Zuciyarsa ta Fara Bugawa haka Yake kallon Duka iyayensa suna kallonsa Cikin son kada wannan Zaton ya Tabbata ammh Ina Bakin alkami ya Riga ya Bushe Haddir ya Kallah wanda ya Gyada mai kai alamun ka Fada kawai zain yau din Ranar Da nake Juyemaka ne Tazo.
Kansa ya maida kasa yana Jin Tahowar kwallah ganin Irin yadda Abba ke kallonsa da Alhaji Tsoho Cikin Nuna mishi Mun fa baka yarda Cikin Rawan Murya Dana Zuciya ya Bude Baki Cikin Kuka yace"Ehhjhhh...!Alhaji Tsoho Ba Shakka Cikin Dake Jikin Dina nawa ne..Ni nayi mata Shiii...Ta Fadi gaskiya Dani kadai take Mu"amala Gaskiya ne..!
Yafada yana Rufe Fuskansa da Tafukan Hannayensa yana sakin wani marayan kuka Kamar karamin yaro,Gabdaya Falon sai ya Rude da Salati da Salallami da kalaman Zain Dina da Zakiya kuwa Hannu suka Damke suna Sakin Numfashi Umma da Nene kuwa sai kuka Haka Zareena dasu Hamdiya Hajiya Mama da Inna Rukkaya Fadi Suke Hasbunallahi wani"imal wakil.
Baban Kaduna da Daddyn Abuja Hulunan kansu suka Cire suna Fifita cikin wani yanayi Abba kuwa kansa na kasa yana jiin Jikinsa Gabadaya yayi sanyi Alhaji Tsoho kuwa Sunan Allah kawai yake ta Kira,Duk da ya Zargi hakan zata Faru ammh Ya bama Zain Duka yardansa.
Daga Chan Bakin Falon sukaji Kara Da kuka Lokaci Daya da Fadin
"Innalillahi Wa'inna Illaihiraju"un....Lahaula walakuwatu Illahbilahi..."Zaina Take Fada Tana Daafe da Kirjinta Wanda yake Barazan nan Fashewa da jin kalaman Mijinta Abun kaunarta wanda tafi Kowa yarda Dashi Duk Duniya.
Hannu ta Daga Tana Nuna Zain Cikin Wani Fargici Shi kuma Tunda yaji kara da Mganarta ya Dago kansa Lokaci Daya ya Mike Zumbur Duka idanuwansa suna Waje
Laila Ke Riketa da Ita Itama kanta Cikin Rudin Take da Jin wannan mganar kafin Tayi wani Yunkuri Zaina ta Sulale kasa asume Bakinta na wani karkafa kamar Wata mai aljanu.
Ai Da wani Gudu kamar walkiya Zain ya Taka ya Nufi Zaina,Gabadaya Su Inna Rukayyah da su Umma suka mike afirgice suka nufeta.
Cikin Wata irin Murya mai amo Cike da kuka Zain yake fadin.
"FIRSTLOVE....".
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
1️⃣8️⃣
"Shi ya Fara isa gareta da wani Gudu kamar zai kifa,Laila ce Ta tareta sanda zata Fadi Sakamakon Ta Rinjayeta sai Dukkansu suka Zube kasa Tare,Laila kuka ta Fashe dashi Tana Jijjiga zaina Lokaci Daya da Kiran sunanta kafin Zain ya kariso wajen gwiwa Biyu ya Duka agaban Zaina ya Ciccibi kanta ya aza Bisa Cinyarsa yana Kiran sunanta Cikin wani yanayi haka ma su Umma da suka Karisowa kowa ya Shiga mamakin ganinta da Abunda ya Faru Tunda basu san sadda tazo Gidan ba Balle har taji wannan al"amarin da kowa yasan Bazai mata Dadi ba.
Laila ce ke kuka Tana Jijjiga Hannun Zainar Tana Fadin"Na Shiga uku Halima ki Tashi Don Allah..Wlh da nasan Abunda zai Faru kenan da ban yarda na kawo ki nan da kika ce ba..Allah na Tuba.."Take Fada Tana kuka kamar An Tambayeta ta Cigaba Da Fadin'"Ni bansan me ya sameta ba Tun Dazu muka gama Abunda zamuyi muka samu Waje muka Zauna muna Hira Tana ta cewa na Tashi mu Tafi nace mata mu kara Zama na wani Lokaci Ni bansan meyafaru sai dai kawai naga kamar An Turo mata sako a wayarta ta Ciro wayarta Ta Duba Daganan ne sai ta Rikice ta Fara kuka Tana Dafe Kirjinta Nayi Ta Tambayanta Ko wani abu ya Faru ne taki min mgana,Sai cewa kawai Da Tayi na Rakota nan Gidan bata ma iya Tafiya na Rikota muka Fito Daga Cikin Makaranta muka Hau adaidaita zuwa nan..".
Ta Karishe Fada Cikin kuka Kamar wata karamar yarinya ba wanda ma yabi ta kanta ganin sun Rude ne sun Rasa yadda zasuyi yasa Haddir ya Shiga Kitchen da Sauri ya Dauko Ruwa mai sanyi yana Zuwa Ya sheka ma Zaina afuska Lokaci Daya ta saki Ajiyar rai Numfashinta ya Fara Tafiya Da Sauri Sauri,Zain Rumgumeta yayi yana Sauke Numfashi Lokaci Daya yake Fadin Alhamdulillah.
Dina kuwa da ZAkiya Juna suka kallah kafin Dina ta Dagama Zakiya Hannu Alamun Jinjina ita kuma Sai ta Daga mata kai Cikin Jin Dadin yabonta,Ganin Numfashin zaina ya Dawo yasa sai kowa ya fara komawa Wajen zamansa Aka bar Umma da Nene da Zareena kan Zaina wacce ke Rumgume Jikin zain,Sai Laila Dake gefe Rakube Cikin Alhini Da Damuwar Wannan Al"amarin Dayake Shirin Faruwa da kawarta ko ma Tace yake kan Faruwa.
Ahankali Take Bude Lumsansun Idanuwanta,Kafin Ta Fara Gani Dishi Dishi ahankali kuma ganin nata ya washe,Fes ta Saukesu kan Zain wanda ke Rike da ita Kura mai ido Tayi na wani Lokaci kamar kiftawan Ido Abubuwa suka Dinga dawo mata Tun Daga Hotunan da aka Turomata na Mijinta da wata karuwa Suna Halin Sirrarantan Juna Har zuwa Tambayar Alhaji Tsoho da kalaman Zain Tuni Idanuwanta suka Rufe Zuciyarta Ta fara wani Tsalle tana Bugawa Da karfin Bala"i ta Saki kawai ta Fashe da kuka Lokaci Daya tana Jaye Jikinta Daga na Zain Shima cikin Raunin Zuciya ya kara matsota yana Mika mata Hannu zai kamata Da wani Karfi Zaina ta Tattaro Jarumtar ta Tashi Tsaye Duk da Jirin Datake gani Idanuwanta na Zubda kwallah Tana kallon Zain ammh Ta kasa Furta ko kalma Daya.
Shima Mikewan yayi Yana Kokarin Nufarta Da Sauri Ta Fada Jikin Umma tana Sakin Wani marayan kuka wanda Duk wanda yaji wannan kukan zai san kukan ne Dayake Fitowa Daga karkashin Zuciyarta Rumgumeta Umma Tayi Itama Tana Kukan mai Hawaye,Gabadaya Falon Jikin kowa yayi sanyi Kowa kaga Fuskar ba Annuri kuma Cikin Tashin Hankali Masu kuka kuma natayi...
Alhaji Tsoho ne Da Tsausayin Halima ya gama Cikamai Zuciya ya Dago yana Fadin"Fatima kama ta Kuzo ku zauna.."Yafada yana kallon Umma ba Musu Umma ta Rikota suka zauna kusa Da Nene wacce Kanta ke kasa Tana Sharan kwallah Haddir ne ya Riko Zain ganin yana Neman zama Kusa da Umma Da Sauri ya Rikesa yana Fadin"A"a...Muje chan ne Zain..!
Yafada yana kallonsa ganin kamar Baya Cikin Hayyacinsa Dole yabi Haddir ganin Daga Umman Har Firstlove din Nashi Da wani Mugun kallo suke jifansa Dashi Wanda yake jin kamar ya kwanta a gabansu yayi ta kuka Gaban Alhaji Tsoho suka kara Komawa suka zazzauna Kafin Alhaji Tsoho ya Fara mgana da cewa,"Innalillahi Wa'inna illaihiraju"un..Hakika Gareka muke kuma gareka zamu koma Mu musulmai ne..Mun yarda Kaddara mai kyau da Mara kyau...Tabbas wannan Itace Jarabawa Wanda Allah ya Jarbacemu Sai dai muyi Fatan Allah ya bamu ikon Cinyeta kuma Allah ya karemu da Zuru"ar mu Gabadaya..!
Aka amsa Gabadaya da Ameen kafin Cikin wani irin Alhaji Tsoho ya kalli Zain yana Fadin"Ka Bani kunya Zainullahi....Ka Barar da yarda da Amanan da na baka acikin Zuciyata..Bantaba Zaton a matsayinka namai Hankali zaka iya aikata Laifi irin wannan ba..Wlh ina da yakini mai kyau akanka Zainullahi Ayadda na san Irin Tarbiyan da muka Baku Banta Zaton Watarana za"a samu wani Daga Cikin Zuru"ata da wannan aikin assha din ba...Naji matukar kunya..Kuma ka Bani kunya ka watsar da Kimarka Idanuwan Danginka da Iyayenka Da Matarka Zainullahi Bayan haka kuma ka kwashe kayanka Gaban Allah...Domin Zina Babban Zunubi ne Allah da kanshi yace kada mu kusanceta kai kuma sai ka Kusanceta..Dama kuma Wanda ya kusanceta zai Raba kansa da Kunya da Dattako Da kima Uwa uba kuma ya saka Rayuwarsa Cikin Wani Hali na Tabewa da kaskanci Kuma Daman Ko ba ji ma Asirinka sai ya Tonu Domin Ita Gaskiya Sunanta Gaskiya Karya ma Sunanta karya..Zainullahi ka Bama yardanmu da Tarbiyan da mukayi maka kunya..Naji Nauyin Mutane guda Biyu..Na Farkon Nauyin Ubangijina Na Biyu kuma Ina jin Nauyin kallon Idanuwan Matarka wacce Tunda tazo Duniya ka Fara Koya mata Sonka da yardanka Dashi Ta tashi ta Girma Ina Matukar Jin Tsausayin yadda zata Girmama wannan Shashancin naka Zaunullahi..!
Ya karishe Kamar ya Fashe da kuka Saboda yarda Muryansa ta Sauya Kowa afalon sai da Jikinsa ya karayin Sanyin Zaina kuwa Kuka kawai take ta ma kasa Mgana Haka kurum Takejin Zuciyarta na Fat Fat..kanta na Sarawa,Laila ma Dake gefe Hawaye Take Sharewa na Tsausayin Kawarta Gefe Daya na Zuciyarta na Fata da Addu"an Allah ya bama Zaina Ikon Jure wannan Jarabawan Rayuwan Daya Tunkareta.
Zain kuwa Hawaye ne suke Diga Bisa Cafet din Falon Alhaji Tsoho kalaman Alhaji Tsoho sun Kara sakashi Cikin wani irin Nadama da Danasani Shi yanzu Bayama jin ta kowa yafi Jin ta Firstlove wani irin Mataki ko kuma Hali zata Shiga Dalilin wannan Al"amarin Da son Zuciyarsa ya Jawo..? Kamar amafarki yaji Alhaji Tsoho na Fadin"Zainullahi ka Dago kanka Ka Bude baki gabana gaban Sauran iyayenka ka Fadamana Tunyaushe ka Fara wannan Shashancin bamu sani ba..?..
Yaji Tambayar atsakar kansa Kunya ta sa ya kasa Dagowa Toh yace me..? Yace Tun Tafiyarsa London..? Yace kafin Dina yayi Tarayyah da mata da yawa da baisan iyaka ba..? Ko iya Kunyar da yasha ta wannan mganar ta Isheshi baya Fatan ya kara Fuskanta wani kunyan Da Tonin asiri,Haddir ma Wuri Wuri ya Farayi da ido Jikinsa na Rawa Zufa na Ketomai Domin ya Tabbatar Da in aka Bi salsala Shima bazai Fita ba,Tunda yaasan komai Tunda Fari yana ta addu"an Allah sa kada Zain yayi mgana addu"ansa ta karbu Domin ko Dago kansa baiyi ba, ballatana yasa Ran zai yi mgana Yana Sauke ajiyar zuciya yaji Muryan Dina Tana Fadin"Alhaji ai Baxai iya Fada maka ba..Ni zan Fada maka komai tun Daga Farko Har karshe..'
Tafada Cikin Raunin Murya Lokaci Daya Tana Mikewa Kowa ita ya sakama Ido Haddir yaji Wani Zuu kamar ya kurmance Yana Bin Da Dina da kallon mamaki Zain kuwa Tsabar Gagara ma bai iya Dago kansa ba ya gama sama Ransa yau itace Ranar Tonon asirinsa.
Kai Alhaji Tsoho ya Daga yana kallon Dina Lokaci Daya yana Fadin"Muna Sauraranki..Ki Fadamana gaskiya Hakan zai sa Mu yanke hukuncin Daya Dace akan Lamarin.."Ya Fada acikin Zuciyarsa yana Tir da irin Tarbiyan Dina na Rashin kunya da Fitsara in Banda Fitsari ta na Cikin Wannan Halin har taga ta mgana Ko Dayake yana Tunanin Koda Laifin Zainullahi itama da nata Domin da bata bada Halin kai ba da haka Bata Faru ba..".
Cikin Wani yanayi na Takaichin zain Dina ta Fara mgana"Ni da Zain mun Hadu Ne a london Oxford Uni Tun Shekaru 7 da suka Gabata.."ai sai kowa ya saki baki kawai cike da mamaki Cikin Ajiyar zuciya ta Cigaba da Fadin"Kuma alaqar mu ta Faro asali ne Tun Farkon Haduwarmu..Allah ne Shaidana Duk da na taso Cikin Gata kuma ban Tashi gaban Tarbiya Uwa ba sai na Uba na Tsare kaina Har naje London ban yarda na Watsar da kaina ba..Sai dai komai ya Sauya Daga Haduwata da Zain..Wanda Allah ya Doramin makauniyar Soyayyarsa..Alokacin Zain bai Dauki mata abakin komai ba sai ababen Jin Dadi da Kore Sha"awa..Kafin ni Zain yayi Hulda da yanmata Kala kala kama Daga Musulmai zuwa Mabanbanta addinai."
Da Karfi Alhaji Tsoho ya Furta"Wa"izubillah.."Yafada Cikin karaya da wani Bakinciki Haka su Baban kaduna suke jifan Zain da wani kallon Kaskanci da Takaichi Dina bata Damu ba Ta Cigaba da Fadin"Da Farko dana samu wannan Labarin game dashi naso na Fita Batunshi sai dai kuma na kasa Son gaskiya nake ma Zain Dalilin Dayasa na kasa Rabuwa Dashi kenan Dalilin Takaichin Yanmatan Dayake Tarayyah Dasu yasa Na mallaka mishi kaina Yayi yarda yaga Dama Dashi..Na Rantse da Allah Shi ya Fara sanina a ya mace ban mai karya ba..Bayan nan kyakyawan alaqa ta Cigaba da wakana tsakanimu wanda Dakyar nayi Nasaran Rabashi Da Bin Sauran mata kuma wannan yakin Nasan bani kadai nayi ba Dan"uwansa ma Dr.Haddir gashi nan zaune Shima yayi Kokari sosai wajen Daidaita Rayuwar zain ammh Abu yaci Tura ni kaina ina gajiya Da wannan Abunda da muke aikatawa nakan ce mai Ya kamata mu Daina mu Tuba muzo muyi aure ammh Duk sadda namai irin wannan mganar da Fada muke Rabuwa Sai yace bazai Aureni ba saboda Shi yana Da matarsa...Ni kuma ina sonshi Shiyasa na kasa Rabuwa Dashi Har Barinsa London da Zuwansa Mumbai muna Tare nakan kaimai ziyara Lokaci Dayan Lokaci hakama Bayan Sun kamallah sun Fara aiki da asibitin su Shi ya gayyaceni Domin muyi aiki Tare da wannan muka samu Damar Cigaba Da alaqanmu aboye Acikin asibiti ne ko kuma agida Da Rana Ni Kamar matarsa nake Haka Da Daddare ne Zaina Take Matarsa Wlh Har araina bana Jin dadin Rayuwar da muke Gudanarwa ammh ba Laifina bane Laifin Zuciyata ce da kuma Zain wanda yake nuna Bazai aureni ba ammh zai Cigaba da Shashanci Dani..'.
Ta karishe Fada Wani kukan Kamar alokacin ne Zain ke Fadamata bazai aureta ba Tana kuka ne na Kishi Da kuma Soyayyar Datake ma Zain,Kamar yadda Take wannan kukan Haka zaina keyin Nata su Umma nayin nasu acikin Zuciya Kwamishina kuwa Sai da ya Share kwallah yana kallon Dina yace"Ba laifinki bane Dota..In ma kina da laifi Wlh naki kadan ne nawa yafi yawa..Allah na Tuba Allah ka yafemim..Wlh Sara in yau ta Dawo duniya bazatayi alfahari Dani ba...Na baki gatan Da Sanadinsa wannan Kaddaran ta Fadamiki Allah Mun Tuba.."Yake Fada yana Saddan kansa kasa Hajiya Batula na Bashi baki kasa kasa Lokaci Daya tana kara Nusar Dashi Kuskuran da yayi akan Rayuwar Dina.
Alhaji Tsoho Daya gama jin wannan labarin mai kama da alma"ara ya kada kai yana Fadin"Allah Sarki..Allah ka Rabamu da makauniyar Soyayyah...Meyasa kika Zabi ki Fallasa mganar Cikin Jikinki Tunda Naga ga Duk alamun kema kin Biyemai wajen Sabon Allh da Zunubin Da kuke aikatawa. ? Yafada yana kallon Dina wacce ke Share Hawaye kafin Tace"Saboda Bana so na sake aikata Laifi kan laifi..Ni da Zain daman mun yi ijiye magar bazan bari nayi Ciki ba..Dalilin Haka yasa nake karban allura Duk Bayan Wata Shida na planning,Wannan karon bansa ya akayi ba kawai sai gashi Ciki ya Bulla gareni wanda arude na Kira Zain gidana na gayamai komai ammh sai ya Rude da Tsoron kada Mganar ta kai kunnen Iyayensa Har nema yayi ya Illatani saboda yana zargin da gangan na bari nayi Ciki..Ina da Racoard din Abunda ya Faru Tsakanina Dashi Ranar zakiya kunna musu suji Da kunnuwansu.."Ta Fada tana kallon Zakiya wacce kamar Jira Take ta ciro Dayar wayarta Dake Cikin Jaka ta lalubo Recording Din Datayi na Zain da Dina ta kunna Ta kara Volume Saboda ma Kowa yaji Mp Ta Fito Dashi Dama saboda Haka tazo Da ita tayi Connecting sai ga Muryan Zain Radau ta karade Falon Tiryan Tiryan Komai yake bayyana Kowa naji Tun kafin agama Saurara Zaina ta Mike da wani Irin kara tana Toshe kunnuwanta Cikin Wata irin Murya Take Fadin..
"Ya isa...Ya isa....Ya isa....! Take Fada tana wani Barin Jiki,Hannuwanta Dafe da kannuwanta kafin ta kwashi Gudu Zuwa Dakin Hajiya Mama kamar wata zararriya Zain Daya Dago kansa yana kallonta yana Hawaye ya mike zai Bita Umma Ta Daka mai Tsawa da karfi Tana Fadin"Karka sake ka Bita Zainullahi...!
Tafada Cikin Kakkausan Murya Lokaci Daya Tana Mikewa Cikin Zafin Nama ta isa Gabansa Tana kallonsa Sau Daya ya kalleta ya maida kanshi kasa Idanuwansa na Zubda kwallah Cikin Mintina Goma Ta gama Kallonsa Cikin Wani Bakinciki Da Takaichi irin na Uwa da Danta Kawai sai Ta Cira Hannu Yau Rana ta Farko Ta zabga Mai Maruka guda Biyu Da sai da ya Durkushe Cikin Kuka Ta Nunashi da yatsa Tana Fadin"Me zaka Fadamata..? Babu..Kada ka kara kokarin zuwa Kusa da Zuciyar da Ka Riga ka Bata Rauni Zainullahi...Ka kiyaye Fushina akanka."Daga haka kawai ta Wuce Cikin kuka ta Rufama Zaina Baya,Haka zain ya Duke kawai yana kuka Hawaye na Zuba Alhaji Tsoho na kallo yama kasa mgana Baban kaduna ne ya mike afusace ya isa ga Haddir ya Mikar Dashi Tsaye Sai ji kayi Shima ya bashi Fayau Fayau har guda Biyu Sai da Shima ya Duka Cikin kunar rai yace"Kaima ka bada Gudummuwa wajen Faruwan komai..Meya hana Tun Farkon Wannan Lalacewar ta zain baka Kirani Ko Ni Ko Aliyu ka sanar mana ba In bazaka iya Fadama Usman ba..Don Ubanka ...?
Dagajin yadda yake mgana zaka Fahimci Yadda Ransa ya baci Hajiya Mama na Sharban Hawaye Tana Fadin"Bafa Hadiru bane Abun Duka ga Abun Duka chan...Kai Zainullahi Ka cucemu ka cucu kanka Wlh.."Waje ya Fara Daukan mgana Inna Hannatu da Idanuwanta suka kala sukayi Jajir ta kalli zain Tana Fadin"Baka Fara kuka ba Zain yanzu zaka Fara Tunda kasa iyayenka kuka da Bakincikinka..'Sadiq kuwa Tuni ya Fice yana kuka ganin yayansa Cikin Wannan Halin Zareenaa ma kuka take kamar Ranta zai Fita Haddir kuwa Kasa ya Duka yana kuka yana Fadin"Don Allah kumin aikin Gafara..Nasan zaka ga laifina ammh ban Boye wannan mganar Saboda komai ba sai saboda Rufamana Dan"uwana asiri..Kuma Har ga Allah bansan Har Dawowarmi suna Tare da Dina ba Tunda Tun muna London yayi min alkawrin Dainawa kwata kwata..Ku yarda Dani Wlh Allah bansan komai ba yadda kukaji komai nima Haka naji.."Ya karishe Fada yana Rike Kafafuwan Baban Kaduna wanda ya Fizge yana Fadin"Rufemin baki Shashenshan banza..Ai gashi nan garin Rufamai asiri ka barshi ya saka kansa Cikin Bala'i da mu kanmu iyayanku Dukkansu sai kunci Ubanku kunjima na Rantse..".
Ganin Abun na neman yayi yawa ne yasa Alhaji Tsoho ya Dakatar yana Fadin"Bashir koma ka zauma..Yanzu ba Lokacin wannan bane...Mu zauna mu samu mafita Tunda mai aukuwa ta auku..'Da haka kowa ya koma ya zauna Alhaji Tsoho ya gyara zama yana Fadin"duba da Duka Abubuwan da suka Fara Da Shaidan gani da ido dana ji da kuma amsan ZAIN na cewa ya yarda Cikin nan nashi ne..Toh zanyi ma Abun Duban Fahimta na Farko bazamu bari mu kara aikata wani kuskuran ba..Mganar azubar da ciki bata Taso ba Dole Yarinyar nan zata Haifi Abunda ke Cikinta..!
Baban Kaduna yace"Ta haifa fa kace Alhaji Tsoho..? Ammh dai ba"ana ba ko..? Ina zamu kai wannan Abun kunyar..? Cikin Mirmishin Takaichi Alhaji Tsoho yace"Anan kuwa..Kuma agidan Iyayen Zainullahi zata Haifa Abunda ke Cikinta.."Kowa Alhaji Tsoho ya zubama Ido Harda Dina da Zakiya Cikin Dattako ya kalli kwamishina yana Fadin"Kwamishina kamin afuwa zanyi maka wani karambani..Abun nan ya Riga ya Faru bamu da yarda zamu sai dai Fatan Allah ya kyauta na gaba..Naji Dadin yadda ka nuna min kai Mutumin kwarai ne wajen Dauko wannan yarinyar ka kawota nan naji Dadi..Nima zan yi amfani da wannan Damar Mu Taru mu Rufama Juna asiri kai dan Siyasa ne Fasuwan wannan mganar matsala ne ga Kimarka,Saboda Haka na yanke Shawaran Yarinyar Wajen naka zata Dawo Nan Bauchi da zama agidan Mahaifin Zainullahi karkashin Kulawa iyayansa Mata Nene da Umman Zareena zasu kula da ita Har ta sauka Lafiya Daganan ta samu tsarki da zasu iya yin auree Bayan haka ni Dakaina in ina Raye zan Daura Auran yarinyar nan da Zainullahi in kuma bana Raye ga ya"yana nan insha Allahu zasu Cikamin wannar Wasiyar Tawa.."Gabadaya Falon sai D'au Shuru Dina kuwa Tun sadda Alhaji Tsoro ya Furta kalmar Aureta Runtse ido tayi Tana jin kamar tatashi Ta Taka Rawa ita bata ma Damu da Cikin jikinta da akace sai ta Haife ba,Domin Soyayyar Zain yasa Take matukar son Cikin Jikinta,ita kuwa zakiya a kunne ta mata rada.
"Finale MRS ZAINULLAHI USMAN SAULAWA.!
Mirmishi Dina ta mata Tana kallon Zakiya kamar ta Goyata su Baban kaduna kuwa basu ma iya mgana ba sanin In Alhaji Tsoho ya yanke Hukunci Shikenan Zain kuwa Kallon Alhaji Tsoho yake cikin Wani yanayin ya zakamin Haka Abba kuwa Kansa na kasa Ko Dagowa bai yi ba,Ballatana ma agane wani Hali yakeciki.
Kwamishina kuwa saboda Murna Har kasa ya Duka yana ma Alhaji Tsoho Godiya Alhaji Tsoho yace"Bakomai..Kada ka Damu..Abunda ya Hadamu bamai Dadi bane..Ammh da yardan Allah zai zama mai Dadi Watarana Ina kuma Fatan Allah ya Shiryama Zuru"a Gabadaya.."Yadinga amsawa da Ameen kafin yace"Ina so zan koma da ita zuwa Sati mai zuwa Sboda zuwan kanwar mahaifiyarta Daga sudan..Zan zaunar da ita na gayamata komai Tunda ya zama Dole tasani kamar uwa Take gareta..Allah barshi bayan Haka ni Dakaina zan kawota wajenka Ranka ya Dade.."Alhaji Tsoho yace"bakomai..Allah ya nuna mana.."
Agogo Fatan Dake hannunsa Kwamishina ya Duba 3pm na Rana ta wuce da Sauri ya Mike yana Fadin"Subhanallah munja Lokaci..Ko Sallar azahar bamu yi ba..Zamu wuce yanzu Alhaji..Nagode kwarai Daka Fahimceni Allah ya kara Kiyayewa.."Alhaji Tsoho ya amsa da Ameen yana Fadin"Dukkamu mun Shiga Rudani bamu san Lokaci ya Tafi haka ba..Allah ya Tsare yakai ku gida lafiya..!
Da Ameen ya amsa Bayan ya Bashi Hanmu sunyi Musabaha Haka yabi su Baban kaduna suma yayi musu musabaha suka karba Fuska ba Fara Abba ne ba"agane wani yanayi yake Ciki Mikewa Hajiya Batula tayi Dasu zakiya,Hajiya batula nayi musu sallama suka amsa Fuska ba Walwala Mama Safiya ce ma ta Amsa da Allah
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 32