Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nama, babban nasu wanda yayi magana a baya wanda kuma ga dukkan alamu yasan Hasanu a baya, ya buɗe baki cikin firgici, jikinsa na rawa, yana cewa, ”kai… yaushe….. ka kai matsayin Ótaki, Hasanu….yaushe??!?” Bai gama rufe bakinsa ba, mutun biyun dake bayansa suka zube a ƙas, inda wanda keda taurari biyu ya zarce kasa a sume, fatarsa a rufe da wannan ƙanƙara ruwan toka, shi kuma mai taurari uku ya fara faɗuwa bisa gwiwarsa fuska cike da mamaki, kafin daga bisani shima yaje ƙas. Waɗannan mutun-mutumi guda biyu na iska, dake tsaye a gefen Hasanu sukai ihu mara sauti, inda kafin Ƙilik yayi wani abu tuni sun cimmasa, inda suka ɗaga hannu kawai saiga wani dogon zare shima na iska, ya bayyana a hannunsu. Kan kace meye wannan sun gama naɗɗaɗe arnan daji Ƙilik dashi, sannan cikin tsananin sauri suka fito da wata jaka irin ta tsafi suka cillashi aciki. Kai ko damar yin ihu bai samu ba, kafin sun cillashi cikin jakar, sannan kuma daga bisani suka dawo gefen Hasanu suka tsaya. Dukkan abinda ya faru zai ɗau lokaci a wajen bayani, amma a zahiri ya faru ne cikin ƙiftawar ido da bismillah. A dai-dai lokacin mamakin dasu Nostalgiya da Kiru suke ciki yakai matuƙa, inda tuni ma suka manta da abinda ya gaya musu na cewa su lura zai koya musu wani sirri daga cikin sirrikan Sihri. ”Ku lura sosai, yanzu ne zan nuna muku abinda na faɗa!” Muryar Hasanu ta cika kunnuwansu da wani ƙarfi duk da cewa maganar a hankali yayi ta. Amma nan take suka dawo hayyacinsu suka kuma ƙura masa ido su na kallon wannan sirri da za’a saukar musu. Dukda cewa dukkaninsu sun san irin yadda ake ji da ƙarfin na Hasanu, bama a iya Sisiya ba, har iyakacin dukkanin Burja. Ko ba komai shi ne kwamanda na biyar a dukkanin jerin kwamandun ƙungiyar Burja. Amma duk da haka abinda suka gani yanzu ya firgita su saboda wannan bashi bane karo na farko ba da suka taɓa ganin faɗa da Ótakí ba, amma banbancin Izzar da suka ji a jikinsu yanzu tsakanin wancan da wannan tamkar banbancin sama da ƙasa ne! Hasanu ya ja numfashi matsakaici, kamar wanda yake zuƙar wani abu acikin sanyin iskar dake kewaye dasu, nan take idanunsa suka canja inda suka cika da tsananin imani da nutsuwa. Duk da kasancewar har a wannan lokaci gabansa yake fuskanta, wato tun bayan wannan taku guda ɗaya da yayi na farko, amma duk da haka saida suka ji ajinkinsu yanayin yadda fuskarsa ta canja. Wanda hakan yasa nan take suka fuskanci tsananin muhimmancin abinda zai gaya musu wanda yasa suka ƙara nutsuwa da tara hankalinsu. Har a lokacin da Hasanu ya buɗe baki ya fara magana bai waiwayo ya kallesu ba, sannan kuma bai ɗaga ƙafarsa daga inda ya ɗora ta ba tun farko sannan kuma dukkanin abubuwan da suka faru, waɗannan mutun-mutumi guda biyu dake tsaye a gefen Hasanu kansu a rusune yake tamkar waɗanda dukkan alamarinsu ya ta’allaƙa da kareshi komai wuya komai tsanani, ko kuma wasu bayi waɗanda suka kai maƙura wajen jin daɗi cikin bautar abin bautarsu, sannan kuma da wannan yanayi na sanyin-sihiri da yake kaɗawa acikin wannan jar iska, komai yana nan a inda yake bai motsa ba, bai kuma canja ba kamar yadda shima Hasanun bai motsa ba. ”Kuyi sani cewa duk wani Sihiri dake faɗin duniyar kafin ya zama kai ka zama shi, sai ka sadaukar da wani abu daga cikin sassan jikinka wanda yake motsi.” yaci gaba dai musu bayani, muryarsa a nutse. “Wannan abu da zaka sadaukar ya zama wajibi ya zamanto kana da dukkan iko na sarrafa shi. ”Saboda wannan waje shi ne zai zama ma’ajiyar dukkan fasahohinka. ”Kuma yadda zaka iya sarrafa wannan ɓari na jikinka haka zaka iya sarrafa dukkanin sihirinka, yadda zai zamo wata hanya da zaka rinƙa sarrafa sihiri irin yadda kaga dama. ”Yanzu ku ɗauki misali dani, dukkanin sihiri na yana da alaƙa da ƙafata, wato dai kamar wannan jar iska da kuke gani. ”Ku kula kugani!” Yana gama faɗar haka sai ya ɗaga ƙafarsa ta dama wadda ya riga ya taka da ita tunda farko, ya dawo da ita baya. Faruwar hakan keda wuya, kamar a mafarki dukkan wannan jar Iska dake ta kaɗawa ta ɓace ɓat, sannan babu alamun waɗannan mutun-mutumi guda biyu babu alamunsu, sannan kuma babu wannan sanyi na babban sihiri dake kaɗawa, komai ya ɗauke cak tamkar ba’a taɓa samar dashi ba. Babu abinda ya rage banda, waɗannan Arnan daji dake kwance fululu a ƙasa a sume. Hasanu yaja numfashi sannan ya juya yai duba izuwa Zahra da Kiru waɗanda bakinsu yake a buɗe cike da mamaki, ya ce, ”wannan shi ne mataki na gaba da zaku shiga yayinda kuka gama kwarewa akan wannan mataki da kuke kai. ”A yanzu kawai abinda nakeso shi ne ku buga tambarin dukkan abinda kuka gani da abinda kuka ji a wannan rana acikin ranku, domin cikin shekaru masu zuwa zaku kai matakin da zaku fara koyar amfani da irin wannan sihiri, a lokacin zaku ga amfanin abinda na nuna muku yanzu.” Yana gama faɗar haka ya ƙara ɗaukan taku ɗaya wanda ya isar dashi gabansu. Yana isa cikin mamaki sai suka ga wata iska mai jan launi ta bayyana ta kuma zagaye su, inda kafin su buɗe baki suyi magana tuni wannan iska ta sure su tayi sama dasu, inda suka ɓace cikin samaniya suka kuma nausa cikin sauri izuwa garin Sisiya. Su na cikin tafiya acikin wannan iska Kiru ya kasa daurewa, inda ya haɗiyi yawu sannan idanunsa cike da ƙara ganin girman Hasanu ya tambaya, ”wato idan na fahimta, aljaninka na jar iska ne, sannan kuma sihirinka a ƙunshe yake acikin takun ƙafafunka. Tayadda idan kai niyya kawai ɗaga ƙafa kake da buƙata kawai kayi, domin ka bayyanar da aljaninka na jar iska?” Hasanu yai ɗan murmushi gami da kyaɗa kai alamun yadda da abinda Kiru ya faɗa. Kiru ya ƙara jan numfashi ga dukkan alamu kuma bai gama tambayoyinsa ba, gami da cewa, ”Shin Yanzu matakai nawa ne suka rage min na Izza kafin nakai wannan mataki?” Yayi tambayar ne fuskarsa da idanunsa cike da buri da kafiya na ranar da shima zata zo ya kira kansa ma’abocin irin wannan Izza. Hasanu ya ɗau lokaci mai tsaho su na tafiya ba tare ya bashi amsa ba, inda har ya fara tunanin ko bazai amsa masa ba. Amma daga bisani Hasanu ya ɗaga kai ya kalleshi gami da girgiza masa kai yana mai cewa, ”kada ka zamo mai hanzari acikin al’amarin Izza da sihiri. ”Komai lokaci ne, kuma hasali ma a yanzu mafi muhimmancin abu a gareku shi ne ku ƙure kuma ku kai matuƙa akan matakan da kuke.” Yana magana yana dubansu biyun kamar dukansu su ne sukai tambayar, idanunsa cike da ma’ana. ”Kunga saura sati uku kawai a buɗe *Non-toch-teka* dake birnin Maikironomada, kuma tuni ƙungiyarmu ta Burja, ta biya farashi mai tsadar gaske wajen kama muku babbar ƙofa, kunga wannan shi ne lokaci mafi dacewa da zaku tabbatar da horonku. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 16: Ido da ido da Daikirin Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . . ”S hekara uku!!” Armad yai ajiyar zuciya gami da ƙurawa wannan budurwa ido cikin mamaki. ”Ba zan iya yin shekara uku anan ba, saboda akwai abinda nake so nayi sauri nayi, na koma gida. Dan ALLAH yi min cikakke bayani naji abinda ke faruwa da wannan waje.” Kallonsa kawai tayi na ɗan lokaci, kafin daga bisani ta girgiza sannan ta ja dogon numfashi gami da ɗaga yatsanta na dama inda ta nuna masa filin dake gabas dasu tace, ”hanyar fita daga wannan waje tana can ɓangaren. ”Daga nan kuma zuwa wajen baifi tafiyar awa ɗaya ba. ”To amma kayi sani cewa gaba ɗaya wurin nan a zagaye yake da wani sinadari mai suna Negrinki. ”Wanda shi ne babban dalilin daya sa baka ga kowacce irin halitta anan duniyar ba. ”Kasancewar shi wannan Negrinki yana iya zuƙe ran duk wani abu mai rai. ”Kuma babban tashin hankalin shi ne iyakacin yadda ka kusance shi, iyakacin yadda zaka fuskanci ƙarfinsa. ”Mafi ƙanƙantar lokaci da aka ɗauka kafin wuce wannan mataki tsahon shekaru da dama, shi ne shekaru uku. ”Amma kaga yanzu acikin shekara ta ukun nan, a iya lissafin da nayi har yanzu ban wuce kaso sittin ba na wannan jarrawabar ba.” Ta kalleshi kallo mai ƙunshe da tambayar, ”ko ka fuskanci girman wahalar dake gabanka?” Armad ya gane meke ƙunshe acikin wannan kallo, saboda haka yayi mata murmushi a lokaci na farko tun bayan haɗuwarsu. Shi kansa bai san dalili ba, amma kawai sai yake jin cewa hankalinsa a kwance yake da ita, wato dai baya jin wata barazana ko kuma mugun nufi a tattare da ita. Ya buɗe baki yai kyaran murya sannan cikin girmamawa ya ce, ”baki gaya min sunanki ba, amma idan ba matsala zan iya kiranki yaya.” Kallonsa kawai tayi ba tare da cewa komai ba, sai dai kawai acikin idonta akwai alamu dake nuna lallai taji daɗin wannan magana da Armad ya faɗa, tamkar yana tuna mata da wani abu daya faru da ita. Maimakon ta bashi amsa, sai tace, ”naga alamun kamar baka fahimta ba sosai yanayin da kake ciki ba. ”Ina ga muje na nuna maka ka gani da idonka.” Tana gama magana ta miƙe gami da yi masa inkiyar ya biyo ta. Cikin ƙanƙanin lokaci tuni Armad ya saɓa takobinsa ya na murmushi yabi ta yana cewa, ”mai yasa kike kyautata min bayan baki taɓa gani na ba. ”Kuma da wuya inma ban zame miki wahala ba.” To amma tambayar tasa bata samu wata amsa sa ba, inda tayi kamar ma bata ji shi ba, kawai ta ƙara sauri suka ƙara dosar gabas. Da farko Armad yayi niyyar yayi mata shiru bayanda ya karanci cewa ba mai son magana bace sosai ba, to amma shi ɗin ya kasance mai nutsuwa da kamala, amma kuma hakan bai hanashi bin diddigi ba, kuma koda bai jima da sanin mutun ba, ya kan saki jiki suyi hira sosai dashi. A taƙaice zaka iya cewa Armad mutun ne mai saurin sabo da mutane da kuma barkwanci. Yanayin daya ke ji a ransa na cewa babu wata mugunta a ran wannan budurwa yasa ya ƙara sakar jikinsa ya ci gaba da janta da zance, ”hmm..” yai ajiyar zuciya, “kinsan kuwa kece mutun ta farko dana fara gani mai irin launin fatata tun bayan bari na garinmu? ”Kinsan shi ne dalilin da yasa nace in kin yarda, na kiraki yaya! Haka dai Armad yayi ta ƙoƙarin janta da hira amma ina ko ƙala bata ce masa, har dai ya gaji shima yayi shiru suka ci gaba da tafiya. Jim kaɗan bayan Armad yayi shiru, sai abinda tun bayan farkawarsa yake ta kai komo a zuciyarsa ya ƙara faɗo masa, inda ya shiga tunani akan fasahar da yayi amfani da ita ya halaka wancan Dordor, wato ‘Wilbafosiyan Siwod Dans!’ ”Har yanzu acikin ƙarnika goma dake ƙunshe acikin wannan hari, na kasa kwarewa akan koda kaso goma na ƙarni guda ɗaya. ”Hasali ma aduk lokacin da nayi amfani da wannan fasaha, saina rasa inda kaina yake, sai dai kawai na buɗe ido na ganni a wata duniyar kawai. ”Gashi yanzu bama tare da Baba Zaikid, ban ma san yadda zan iya ci gaba da koyon wannan fasaha ba! ”Hmmm..” yai ajiyar zuciya shi kaɗai acikin duniyar tunaninsa. Can alƙawarin daya ɗauka na cewa lallai sai ya cika burin mahaifiyar sa na ganin cewa ya nemo wannan mutun da akewa laƙabi da Tirifil-fakta kuma ya gabatar dashi a gareta, ya faɗo masa. Nan take idanunsa suka kaɗa da kafiya da kuma jajurcewa, wanda a wannan lokaci wani sabon tunani ya bayyana acikin kansa, ”na san cewa lallai duk da ban daɗe da zuwa wannan doron ƙasa ba, nasan cewa lallai a yanzu bana daga cikin jaruman gaske abin misali koda kuwa acikin sa’anni na, ina ji a jikina cewa da dama sun fini kwarewa ta kusan kowanne fanni. ”Duk da cewa a yanzu bani da masaniyar yaya wannan tafiya tawa ta nemo wannan mutun zata kasance ba, amma lallai nasan abu ɗaya; cewa a yanda nake ɗin nan bazan ko iya kare kaina daga cutarwa ba, ballantana wani abu. ”Saboda haka abinda ya zama wajibi a gareni shi ne na zama jarumi, ya zama wajibi a kaina na koyi duk wasu hanyoyi na horo da suke akwai a wannan ƙasa. ”A yayinda nake karɓar horo na sai kuma na ci gaba da bincike akan yadda zan cimma manufa ta. ”Bari muga… a doron ƙasa ta uku kowanne yawancin mutane koyarwar manyan gidaje suke bi a makarantunsu, hmm… ban sani ko nanma haka suke. ”Idan haka suke, to kawai sai na duba naga wanne gida ne yafi kama da nawa. ”Tunda ban tawo da wasu kuɗi ba, saina yi aikin ƙarfi na samu kuɗi na biya na shiga. ”Idan ma dai kuma ba wannan tsari suke bi ba, to koma dai yaya ne zanyi duk yadda zanyi, naga na cimma buri na shiga da kuma karɓar horon. Dama a gida ban taɓa samun damar shiga makarantar yaku-bayi ba, saboda haka ina ganin abu ne da zai bada ma’ana.” Yana zuwa nan a zancen zucin da yake, wani ɗan ƙaramin murmushi ya bayyana a gefen bakinsa yana mai ɗokin wanne irin sabon tsari zaije ya tarar, a doron wannan ƙasa. Yana cikin wannan hali sai yaga wannan budurwa ta tsaya cak inda shima ya tsaya gami da ƙura mata ido yana ƙoƙarin tambaya ko me yasa suka tsaya sai ta rigashi magana da cewa, ”munzo!” Armad ya ɗaga kai gami da ƙura ido amma a iya hangensa bai ga wani banbanci ba. Ya kalli kudu ya kuma kalli arewa amma duk da haka baiga komai ba. Yana niyyar ƙara yin magana ta ƙara rigashi da cewa, ”a ƙa’idar wannan waje babu wanda yake iya ganin wani, shi yasa duk da bani kaɗai na fara wannan jarrabawa ba, kuma duk da cewa dukkanin masu jarabawar a waje ɗaya suke amma babu wanda zai iya ganin wani. ”Badan komai ba saboda, duk idan wani ya wuce gaba ɗaya hijabin dake rufe hanyar na sinadarin Negrinki zai ɗauke gaba ɗaya. ”Shi yasa kowa dole ne yayi jarabawar sa a wajensa daban. Tana faɗar haka ta ɗaga hannu ta nuna masa can gabansu da ɗan yatsa, ta kuma fara tafiya gami da yi masa inkiya daya biyota. Har sun kusa ƙarasawa sai ta ja wani dogon numfashi, sannan ta ce, ”koma daga ina kake, kuma koma taya ya kazo wannan waje bai shafe ni ba, amma kayi sani cewa fitarmu daga wannan waje nada matuƙar wahalar gaske. ”Saboda ƙarfi da taurin hijabin sinadarin Negrinki, dake gaba lallai ni kaina yafi ƙarfin na iya wuceshi a shekaru da dama masu zuwa. ”Saboda haka ina gani wannan shi ne iyakacin taimako da zanyi maka.” A dai-dai sanda ta gama faɗar hakan sun iso wajanda suke iya hangen wani waje irin na musamman a gabansu, wanda gabaki ɗaya ya banbanta da dukkan sauran wajen da Armad ya gani tun shigowarsa. Kallon farko da Armad yayiwa wajen yaji zuciyarsa ta buga da ƙarfin gaske wanda sai da yasa ya ɗan ja baya. Ba komai bane ya janyo haka ba illa wani mutun mutumi dake tsaye kimanin taku ɗaya bayan an shiga wajen. Gaba ki ɗayan shashin dake gaban nasu a rine yake da launin shuɗi wanda yake garwaye da launin ja. Kama daga ƙasar wajen zuwa sama zuwa komai dake kewayen wannan launi ne dashi, face wannan mutunmutumi shi kaɗai. Wanda ke riƙe da doguwar takobi a hannunsa na hagu, wadda ke a ɗage tana nuni izuwa gabansa da ita, kai kace yana neman fafatawa ne da dukkan duniya baki ɗaya. Sanye yake da sulke sannan kuma akwai tambarin Miyura a goshinsa wanda ke ɗauke da wani yare da Armad bai sanshi. Gashi dai mutun-mutumi ne kawai, amma irin girman izzar da Armad yake ji tana tashi daga jikinsa yasan cewa babu wani abu dazai iya kwatanta tata dashi, kai bai ɗau lokaci bama ya tabbatarwa da kansa cewa baima kai matsayinda ko kuma kace baima cancanci ya ce zai auna buwayar wannan Izza dake tashi daga jikin wannan Mutun-mutumi ba. Amma a dai- dai wannan lokaci da Armad ya jada baya idanunsa suka kai kan idanun mutun-mutumin inda nan take mutun-mutumin ya buɗe idonsa ya kuma kalli Armad. Babu abinda Armad yake gani a ransa illa irin wannan kala data cika wajen dake gabansa cike acikin wannan idon. Babu shiri yaji tsananin ruɗani da firgici acikin ransa irin wanda bai taɓa ji ba. Kafin ƙiftawar ido da bismilla zuciyarsa ta tabbatar masa da cewa idan ya ci gaba da kallon idon wannan mutunmutumi zuwa daƙiƙu biyu masu zuwa, to lallai gabaki ɗaya jikinsa sai ya tarwatse gabaki ɗayansa. To amma tashin hankalin shi ne tuni yake ta ƙoƙarin janye idon nasa amma abin yaƙi yiwuwa tamkar ba’a jikinsa yake ba. A dai-dai lokacin da ya fara ɗebe haso daga rayuwa saboda tsananin firgici, a dai-dai lokacin ne wannan mutun-mutumi ya rufe idonsa, wanda hakan yasa Armad ya dawo cikin hayyacinsa. Amma kafin kace meye wannan ya jada baya kimanin taku biyar imda ya faɗi ƙasa gami da yin aman jini. Can bayan wani lokaci ya farfaɗo, yana buɗe ido yaga wannan budurwa tana riƙe dashi duk fuskarta cike da damuwa. Amma tana ganin ya farka saita sakeshi, gami tambayarsa mai ya faru. Baima tsaya tunanin wani abu ba ya gaya mata duk abinda ya gani. Yana ambatar cewa sun haɗa ido da wannan mutunmutumi, yaga fuskarta tayi matuƙar canjawa, wanda nan take ta cika da firgici gami da miƙewa tsaye tana kallonsa. Bayan ƴan daƙiƙu ta fara magana aciki, idanunta cike da hargitsi, ”waye kai!!! ”Kuma daga ina kake!!!” Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 17: Sadaukarwan Nusi Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . . N an take abubuwa da dama, musamman hikayoyi da suka shafi wannan mutun-mutumi dake wannan waje, suka fara kai-komo acikin ranta. Cikin tsammani ta buɗe baki da niyyar fara yi masa tambayoyi, to amma da yake shima kamar sunyi anko ne, domin babu abinda ke kai-komo a zuciyar ta, banda tambayoyin nan guda biyu; wai shin wanene wannan yaro da har ya isa ya ga mutun mutumin Daikirin, kuma daga ina ya fito? Hakan ne yasa duk su biyun sukai anko wajan buɗe bakunan su da niyyar yiwa juna tambaya, amma a dai-dai wannan lokaci ne kwatsam babu tsammani idanun Armad suka rufe ruf, sannan babu alamar rai a tattare dashi, ya faɗi kasa da ƙarfi a sume. Kallo ɗaya kacal zakai masa kasan yayi zazzafan suma ne irin wanda bashi da nisa sosai da mutuwa. Cikin tsananin mamakin abinda ke faruwa da Armad tayi firgit ta matsa daga kusa dashi zuwa nesa, inda ta zauna tana haki. Ta dubeshi cikin mamaki da firgici zuciyarta cike da tunanin maike faruwa ne, kuma mai ya kamata tayi? To amma bata ma gama tunanin nata ba, Armad ya ɗan farka, inda ta dubeshi fuskarta cike rashin sanin mai ya kamata tayi. To amma a wannan lokaci yana farkawa nan take ba tare da ya cika cikakkiyar daƙiƙa ba, ya ƙara faɗawa cikin suma. Sannan kuma jikinsa ya fara jijjiga. Tana dubansa ta tabbatar da cewa lallai wannan shi ne lokaci na ƙarshe da zata yanke shawarar kota taimaki wannan yaro da bata taɓa sani ba a rayuwarta, ko kuma ta bari ya halaka! Badan komai ba sai dan cewa wannan suma na ƙarshe da Armad yayi, ya bayyana ƙarara a fuskarsa da jikinsa cewa ruhinsa gaba ɗaya bazai iya ɗaukan wahalar wani suman ba, kuma lallai idan haka ta faru to lallai zai halaka, wato dai dukkan alamunsa sun nuna ya kai iyakacin ƙololuwar juriyarsa. Fuskarta ta yamutse cikin tunani, kai daka ganta kasan cewa tana cikin ruɗani ne da ruhinta, akan cewa ta rasa wanne mataki ya kamata ta ɗauka. Bayan sama da daƙiƙa talatin ana cikin wannan hali, a wannan lokaci jikin Armad ya fara karkarwa irin wadda duk baiyi ba a baya. Nan take fatar jikinsa ta fara tsufa tamkar wanda ya wuce shekaru aru-aru a ɗan wannan lokaci, kai daka ganshi kasan ya tashi daga wannan ɗan yaro mai yawan murmushi da barkwanci, zuwa wani tsohon mutum mai yawan shekaru. ”Yanzu haka zan bar doron ƙasa ba tare da kammala alƙawari na, na nemo Tirifil-fakta ba?” Wannan ita ce tambaya ɗaya dake gilmawa acikin zuciyar Armad, yayinda yake tsaka da wannan suma nasa. To amma a dai-dai lokacin da rayuwarsa take cikin tsananin hatsarin salwanta… Sai kawai yaji wani abu ya shiga bakinsa. Bama shida ƙarfin taunawa, amma jim kaɗan sai yaji ya narke a bakinsa, ya kuma wuce maƙogoronsa, inda ya zarce zuwa cikin cikinsa. Haka na faruwa, cikin abinda bai wuce daƙiƙa ɗaya ba, Armad yaji wani mahaukacin ƙarfi ya bayyana acikin kwakwalwarsa inda nan take yaji lurarsa ta ƙaru matuƙa sama ma da da kafin ya fara suman. Nan take wannan haske ya daki idanunsa inda suka buɗe tarai. Hasken ya wuce ya daki zuciyarsa da hannayensa da ƙafafunsa da dukkan kayan jikinsa. Kafin kace meye wannan dukkan tsufan da da jikinsa ya fara yi ya ɓace ɓat, inda fatarsa ta dawo kamar yadda take ada. To, duba da irin halin faran-faran da barkwanci na Armad, yana farkawa ya fara murna , inda yayi dogon numfashi gami da cewa, ”hmmmmm!”Yana faɗar haka yana miƙa hannunsa na dama yana share gumi a goshinsa. Duk da bashi da cikakkiyar masaniyar mai ya faru, amma zai iya cankar cewa wannan budurwa tana da sa hannu aciki, saboda koba komai irin wannan taimako a irin wannan waje da wuya ya faɗo daga sama. Nan take ya fara dudduba damansa da hagu yana nemanta. Can idanunsa suka kai kanta daga ɓangaren arewa maso gabas tana zaune ta haɗa kai da gwiwa. Dud da bai kalli fuskarta ba, amma wannan kallo ɗaya ya isa yasa yaji irin jimamin dake tashi daga zuciyarta. Nan take sama da tunani goma sha, da wataƙila su suka faru har ya samu sauƙi, suka gifta ta cikin kansa. Kafin kace meye wannan fuskarsa ta canja inda ya nufi inda take cikin zafin nama. Yana isa ya durƙusa a gefenta inda daga bisani bayan ya kalli yanayin da take ciki ya yanke shawarar kada yayi magana a lokacin, wato ya ɗan jinkirta. Nanfa ya zauna a gefenta inda bayan wani ɗan lokaci ya juyarda kansa daga ita ya sunkuyi da kansa inda nan take juyayi na tunanin meke faruwa da kuma maiya kamata yayi, suka cika masa kai. Tun rana tana tsakiya suke zaune babu wanda yace uffan acikinsu har saida rana ta kusa faɗuwa inda a wannan lokaci ne wannan budurwa ta ɗago kai ta dubeshi, wanda a wannan lokaci zuciyarsa tuni ta gama gano masa mafi yawaicin abinda ke faruwa. Ta numfasa gami da fara jawabi, ”Suna na Núsi Djinn. ”Mutane na na ƙabilarmu da muka rage a duk faɗin doron ƙasashe bakwai bamu da yawa. ”Kuma a wannan zamani bamu da ƙasa ta kanmu, hasalima da dama daga jama’armu basu da taƙamaiman wajen zama, sannan kuma kamar muma da muka samu muhalli muna iya ƙoƙarin mu wajen ganin cewa mun ɓoye sunan Djinn ɗin dake nasabarmu. ”Kuma saboda wannan hali da muke ciki nema muka samar da hanyoyi da dama, waɗanda indai ɗaya daga cikin mu yaga ɗan uwansa na ƙabila nan take yake ganeshi!” Tana faɗar haka ta ɗago ido ta kalli Armad, irin kallo mai cike da ma’anar cewa; ”nasan kai ba ɗan ƙabilar Djinn ba ne, (ba Armad Djinn sunanka ba)!” Armad dama tunda farko yasan ba Djinn ɗin bane shi, amma kamar yadda tsarin danginsa yake, bazai baƴyanawa kowa sunan gidansu ba. Armad ya juya ya kalleta gami dayi mata yaƙe idanunsa a rufe, fuskarsa cike alamun bata haƙuri. Bata ce masa komai ba, kawai sai ta ɗauke kai kuma taci gaba da bayani, ”Djinn ƙabila ce data bada gudunmawa ta musamman a babban yaƙi mafi girma daya faru a duniyar aljanu shekaru aru-aru tun kafin al’umma su fara rayuwa akan ƙasashen ƙasa. Koda tazo nan a zancanta sai ta ja numfashi gami ajiyar zuciya, sannan tayi murmushi mai ɗauke da alamun zurfin tunani.’ Ta rufe jawabinta da cewa ”Wannan shi ne wani abu daga cikin labari na, manufa ta da kuma ƙudiri na aban ƙasa, wannan wani abu ne wanda bazan iya gaya maka ba!” To haƙiƙa duk da cewa Armad yana da ƙarancin shekaru, amma ba dolo bane. Domin tun daga lokacin daya farka ya kuma ga yanayin data shiga da kuma yadda ta fara bashi labarin kanta kwatsam, yasan cewa akwai wani abu dake damunta. Musamman yanayin yadda take bada labarin a wani yanayi irin mai kama da bankwana, ko kuma ɗebe haso. Saboda haka duk da cewa labarin nata ya motsashi, kuma zaiso yaji menene manufarta da ƙudirinta, shin itama neman Tárifil-faktan take, ko kuma tana tare da waɗancan mutane su Gimbiya Nostalgiya, ko kuma nata ɓangaren daban yake. Amma zuciyarsa tana kan tambayar dake cikin zuciyarsa. Inda ya numfasa idanunsa cike sanin ya kamata ya ce, ”Yaya Núsi, me ya faru ne wai?” Bayan ɗan lokaci sai tayi murmushi, sannan ta ɗaga kai, ta dubi wannan ƙasa mai launin ja haɗe da kore a jikinta, tace, ”bamu da wani tsammani na fita daga wajen nan yanzu.” Sannan ta ƙara wani murmushin tana cewa, ”ALLAH mai iko, ban taɓa tunanin rayuwata anan zata ƙare ba!” Idanun Armad suka kaɗa da ruɗanin rashin fahimtar mai take faɗa, inda cikin sauri yace, ”wai me kike nufi ne? kiyimin bayani yadda zan gane!” Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 18: Mutumin dayafi kowa yawan makiya a duniya (tirifil fakta) Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos . Núsí ta kalleshi kallo mai zurfi, wanda acikinsa akwai alamun tausayi, tsahon daƙiƙa goma, kafin daga bisani ta fara wata dariya mai matsakaicin sauti, kai daka ji kasan akwai tsananin ciwon rai acikin wannan dariya. Kana daga bisani ta numfasa tace, ”Mangwaron Negrinki! ”Zaka sha wahala matuƙa, kuma abu nema mai kama da samun jaki mai ƙaho, kafin ka sami wani abu guda ɗaya dake da muhimmancin Mangwaron-Negrinki wajen ƙarfafa ruhi da inganta Izza, kai hasali ma akwai hikayoyi da dama da suka rawaito cewa idan ka samu adadi mai kyau ka kuma yi amfani dasu ta yadda ya dace, to zaka iya tashin matacce daga kabari da ƙarfin sihirin wannan mangwaro. ”Hakan nema yasa mallakar wannan mangwaro abu ne mai tsananin wahalar. ”A misali; a sama da shekaru goma da nayi a birnin Maikironomada nayi ayyuka na kwadago da dama kuma na samu dukiya dai-dai gwargwado. ”Amma a lokacin da zan fito wannan jarrabawa wadda nasan bazata taɓa yiwuwa ba idan mutun bashi da wannan Mangwaro ba. ”A saboda haka na tattare dukkan tari na, na tsahon rayuwa ta dan na sayi wannan mangwaro, amma a ƙarshe ban iya mallakar sama da guda biyu ba. ”Bayan zuwa na nan wurin acikin shekaru uku da nayi anan, na ƙarar da guda ɗaya aciki. ”Saura guda ɗaya, wanda kuma shima yanzu babu. ”A duk lokacinda kake fafatawa wajen ƙoƙarin wuce wannan hijabi idan ka samu rauni, to fa baka da wata hanya mafi sauƙi face kayi amfani wannan mangwaro, wajen warkar da ciwon naka. ”Babban sharrin sinadarin Negrinkin dake wajen nan, shi ne ciwon da yake yiwa jiki baya warkewa da wuri, ɗan ƙarami ma yakan ɗauki shekaru da dama. ”Amma da taimakon wannan mangwaro zaka iya rageshi zuwa kwanaki. ”Dukkan waɗannan dalilai ne suka sa babu ta yadda wani mahaluƙi, zai iya wuce waɗannan wannan mataki ba tare da wannan mangwaro ba.” Tana zuwa nan a zancanta ta girgiza kai gami da cize haƙora tana cewa, ”naso na fita daga wannan waje. Armad ya ƙura mata ido yana sauraren ta cikin mamaki. Tun kafin tazo nan a zancenta Armad ya gama haɗa lissafin duk abinda ke faruwa, kuma ya gane inda ta dosa; wato wannan abu daya ji a bakinsa ba komai bane illa mangwaron-negrinkin nata guda ɗaya daya rage. Kuma wannan yanayi na ɗebe haso daya bayyana a fuskarta ba komai ya jawoshi ba, illa rasa wannan mangwaron sihiri da tayi. Bayan ya gama fahimtar komai, sai nan da nan yaji kyautayi da ƙaunar wannan budurwa ta shiga ransa. Irin ƙaunar dake zuwa rai ga wanda ya taimake ka a lokacin da kafi buƙatar taimako. Armad yana wannan tunani ne hankalinsa a kwance, babu ko alamun ayar tashin hankali a tattare dashi. Duk da kuwa duba da cewa babban abinda yafi ɗagawa ita Núsín hankali shi ne rashin hanyar da zasu fita daga wajen. Hakan nema yasa ta dago kai ta dubeshi idanu cike da mamaki, tayadda duk da bata ce komai ba ya bayyana ƙarara a idonta cewa mamaki take da hankalin Armad bai tashi ba duk da cewa kuwa ta gaya masa a fili cewa basu da hanyar fita daga wannan waje. Armad yai murmushi gami da cewa, ”kamata yayi a mayarda alkhairi da alkhairi, wato ina nufin baki sanni ba amma kin yarda dani kuma harkin sanar dani labarinki. ”Nima ina ganin ya kamata na gaya miki dukkan labari na a zahiri, kuma ina baki haƙuri dana ɓoye miki a baya.” Nan fa Armad ya kwashe dukkan labarinsa tun daga dalilin fitowarsa daga doron

Chapter 9 of 33