Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daga wannan kwanuka suka kalleta, "Idan kun gama akwai tafki na wanka mai cike da ruwan zafi. Kuyangi suna ciki suna jira suyi muku wanka." Cokali ne ya ƙara yin magana da ƴar kumburarriyar fuskarsa cike miya caɓo-caɓo. Lallai kallo ɗaya zakai masa ka fashe da dariya. "Wanka???!!! Iliyasis yaushe rabonka da wanka." Iliyasis ya harari Cokali, "Kai yaushe rabonka? Nusi ce kaɗai tayi a wannan satin, har gwanda nima nayi wancan satin. Kaifa?" Duk su ukun suka fashe da dariya. Ko a mafarki basu taɓa tunanin samun irin wannan daula ba, kuma lallai basu da niyyar yin tunanin daga ina wannan daula take har sai sunyi hani'an. Haka kuwa akai, kwata-kwata basu fara tunanin matsaloli ba sai washegari bayan sun tashi daga baccin awa ashirin da sukai akan wani katafaren gado na alfarma. Duk su uku acikin fararen kaya irin na bacci. Iliyasis ne ya fara tashi, sannan Nusi. Su biyun suka kalli ƙasaita ta cikin wannan ɗaki sannan suka kalli junansu cikin damuwa. Iliyasis ya numfasa ya ce, "ba dai abinda nake tunani kike tunani ba?" Nusi ta kyaɗa kai, lallai duk abu ɗaya suke tunani. Waye ya kawo su nan? Kuma maiya faru dasu Ɗan-darbejiya? Ina ne wannan gida da suka tsinci kansu? Ba jimawa suka tashi Cokali, fuskarsa cike da yawun bacci suka labarta masa cewa akwai matsala. Abu kamar wasa Cokali ya buɗe baki ya ce, "amma dai ba'a gidan yankan kai muke ba ko? Ba siyar damu akai ba? Ina ne nan?" Ba jimawa tsoro ya cika su duk su ukun, inda kafin kace meye wannan tuni sun cure a ƙarshen gadon suna leƙe- leƙe. Kafin wani lokaci tuni sun fara lissafe-lissafen yadda zasu tsere daga wannan gida. Suna cikin haka sai suka ji an buɗe ƙofar ɗakin. Suna tsammanin suga wannan farar kuyanga sai suka ga wani farin saurayi mai yawan gashi. Lallai tsayin gashinsa ya haura na mata da yawa a wannan zamani, domin kuwa yakai har gadon bayansa. Sai dai abin mamakin gashin nasa launin ja ne, jajawur. Yana sanye da baƙar alkyabba. Yana shigowa ya nemi waje ya zauna, sannan yayi murmushi a garesu. Duk su ukun suka ƙame a waje ɗaya, ko numfashi basa iya yi sosai ballantana magana. Saurayin ya fara magana cikin lafazi mai ɗauke da tsantsar Izza da kamala, "suna na Yarima Niyashi. Ni ne na ceto ku daga waɗancan mutane dake neman halaka ku. Sannan kuma ni ne na kawo ku wannan gida." "Y....yarima Niyashi?? Kai.... ne Yarima Niyashi?" Iliyasis ya fara magana cikin ƙinƙina, domin kuwa indai abinda yake tunani haka ne to kuwa lallai suna ganawa da ɗaya daga cikin waɗanda ake yiwa kallon su zasu iya mulkar duniya anan gaba. A duk faɗin ƙasa bakwai mutun ɗaya ne mai suna Yarima Niyashi wanda keda irin wannan jan gashin, saboda haka Iliyasis bai ɓata lokaci ba ya dubi wannan saurayi ya ce, "Yarima Niyashi, ɗan sarkin Jinzidal, Rafiya, na daular Infiriya?" Saurayin yayi murmushi, tare da kyaɗa kai. Alamun haka ne. Cokali ya ja rigar Iliyasis cikin tsoro, "Wane ne? Kasan shi?" Iliyasis bai kula da Cokali ba ya ci gaba da magana, "to amma mai kake yi a daular Maikironomada? Na tabbatar duk wanda ya ganka anan cewa zaiyi leken asiri kazo." Wannan saurayi ya ɗan numfasa tare da juyawa ya kalli Nusi wadda tai shiru tana tunane-tunane, ga dukkan alamu ita ma ta gane wane ne wanna saurayin. Kafin daga bisani saurayin yayi mata magana, "Tsahon lokaci ina nemanki, Nusi Djinn." *** 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 70 & 71: Cokali da ilyasis sun shiga Duniya Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ------- Nusi ta ƙara jada baya cikin tsoro, inda ta ɓoye a bayan ƙibar Cokali. A wannan rana ta gane cewa hatta ƙibar Cokali nada ranarta. A ranta tama kasa gane maike faruwa. Ta yaya za'ace wai ɗan sarkin babbar daular Infiriya yana nemanta? Wai tayaya ma akai ya santa? Dududu shekarunta shida kacal a duniya, kuma acikin waɗannan shekaru bata taɓa yin inda hanyar daular Infiriya take ba, ballantana ace ta gamu da ɗan sarkin dake mulkin wannan daula, harma ace wai yana nemanta. Lallai koma wanne laifi ta aikata yana da girman gaske, tunda har za'ace ɗan ɗaya daga cikin sarakuna biyar na Jinzidal ya taso ƙafa-da-ƙafa yana nemanta. "Kada kiji tsoro." Muryar yarima Niyashi ta shiga kunnenta tamkar ana busa algaita. "Banzo danna cuce kiba. Nazo ne danna taimake ki. Amma kiyi sani cewa a halin yanzu bani da ikon gaya miki tayadda akai na sanki ko kuma mai yasa nake nemanki, duk da kuwa nasan wannan tambayoyi sune suke yawo akanki. A halin yanzu wannan gida da muke ciki naki ne halak-malak. Bama gidan ba kaɗai, tare da duk abinda ke cikinsa. Sannan kuma akwai kuɗin Ayrid kimanin miliyan ɗaya dana bari wanda zaku yi amfani dashi zuwa sanda zan dawo. Na bar umarni mutanen cikin wannan gida zasu yi muku shaidar zama cikakkun ƴan garin nan kuma zasu saka ku a makarantar koyon Izza. Akwai mutanen mu wanda zasu kula dake har zuwa sanda zan dawo." Koda yarima Niyashi yazo nan a zancensa sai ya miƙe ya gabato izuwa gaban wannan gado dai-dai inda Nusi maƙale a bayan Cokali tayi kalar tausayi. Koda ganin haka sai Iliyasis yai tsalle ya dira a gabanta, wato ya shiga tsakaninta dashi. Iliyasis yai ta maza ya buɗe baki ya ce, "Bazan bari kayiwa ƙanwata wani abu ba indai inada rai." Abin mamaki saiga Cokali shima yai tsalle ya dira a gefen Iliyasis, inda gadon yai wata ƙara ƴana neman ɓallewa saboda nauyi. Hannun Cokali na karkarwa, ƙaton cikinsa na sama da ƙasa saboda tsabagen nishi, yana ƙinƙina yana cewa, "ni....ma... b...bazan bari k...ka taɓa taba. Kwandama ka tafi ko kuma ka tafi." Koda Cokali yazo nan a zancensa amma Niyashi bai tsaya, sai nan take haƙoransa suka fara karkarwa tamkar wanda aka tsoma acikin dusar ƙanƙara. "Baza ka tsaya!!!" Cokali ya kwala ƙara mai kama da kuka. Amma Niyashi yai kamar baiji shi ba yaci gaba da tafiya. Yana ƙarasowa saitin Cokali ya tsaya, inda ya juyo da kansa ya kalli Cokali. Abun mamaki suna yin ido-da-ido Cokali ya faɗi ƙasa sumamme saboda tsananin tsoro. Sannan ya tafi gadan-gadan zai faɗa ƙasan gadon. Haka na faruwa Niyashi yai sauri ya taroshi tare da fashewa da dariya. Yana cewa, "Haha... lallai Nusi kina da wanda zasu kare ki ba saina damuba." Yana rufe baki ya shafa fuskar Cokali ya farfaɗo dashi ta hanyar ɗalasimai. Sannan ya juya ya fice daga ɗakin yana dariya. --------- Tun daga wannan rana basu ƙara ganin Niyashi ba, tun suna tsoron wannan ƙaton gida har suka saki jiki. Duk abinda suke buƙata akwai aciki, sannan idan zasu fita akwai bayi jarumai dake kula dasu. Ba daɗewa suka zama tamkar wasu ƴaƴan attajirai a wannan gari na Khan. Suka shiga babbar makarantar Izza dake wannan gari na Khan. Abu kamar wasa suna jira Niyashi yazo amma baizo, bashi ba alamunsa. Rani yazo, kaka tazo, bazara tazo, akai hunturu sannan damuna ta kewayo. Sannu a hankali har sunyi shekara ɗaya a wannan gida. Abin mamaki duk su uku tamkar an haɗa baki suka zamanto masu matuƙar ƙoƙari a makaranta. Sannu a hankali a kwana a tashi wata shekarar ta wuce. Iliyasis ya zaɓi ɓangaren takobi a makaranta, shi kuma Cokali ya zaɓi ɓangaren aljanu da zanunnuka. Nusi kuwa ta zaɓi ɓangaren Izza da dabarun yaƙi na daular Maikironomada. Sannu a hankali a wannan hali saida sukai shekaru tara cif, harma sun fara mantawa da labarin Niyashi. Ranar nan kwatsam sun dawo daga makaranta su uku sai babbar hadima mai yi musu hidima a gidan tace musu suna da baƙo idan sun shirya. Dukkaninsu sukai tunanin bazai wuce ɗaya daga cikin masu zuwa gida yanai musu karatu ba, saboda haka ko a jikinsu. Suka shige izuwa sashinsu sukai wanka suka kimtsa a hankali sannan can yamma suka bayyana a falon gidan. Nusi na sanye da doguwar riga samfurin daular Maikironomada mai ɗauke da bezar gashin zaki. Babu abinda take sai sheƙi. Kyawunta ya bayyana matuƙa a wannan lokaci, domin kuwa tuni Nusi ta cika ƴar shekara sha biyar da haihuwa a duniya. Ga dogon gashinta yana kwanciya akan kyakkyawar fuskarta mai ɗan duhu. Cokali ya ɗan rage ƙiba, amma duk da haka yana da tumbi da kuma da manyan gaɓɓai. Shi kuwa Iliyasis kamalarsa da nutsuwa ta ƙaru. Yana rataye da takobinsa launin ja. Abinda suka gani basu yi tsammani ba, domin kuwa ba kowa bane a zaune acikin wannan falo ba illa yarima Niyashi. Hannunsa ɗauke da jaridar kamfanin Maikiro ta wannan sati. Dukkaninsu suka gabato izuwa gareshi fuskokinsu cike da damuwa, duk da kuwa babu sauran tsoro a tattare dasu. Abu ɗaya da suka sani shi ne idan da Niyashi yaso halaka su da tuni hakan ya ɗaru tun shekaru tara da suka wuce. Yana ganinsu ya miƙe fuska cike da murmushi yana cewa, "Ahh.. duk kun girma. Nusi... dube ki har kin kamo ni tsayi. Cokali kaima....." Amma a dai-dai wannan lokaci da Niyashi ya ajiye jaridar data rufe masa fuska suka ga fuskarsa sosai sukai tiris suka cake a inda suke, baki a buɗe. Niyashi yana nan dai- dai da dai-dai yadda suka ganshi shekaru tara da suka wuce. Da daida girma ko kuma canji na kwayar zarra babu a fuskarsa. Hasalima sai kace sa'ansu ne koma sun girme shi. Musamman ma Iliyasis da yake da kamannin manya lallai zaka ce ya girmi Niyashi. "W...ane ne kai? Maike faruwa?" Wannan kawai shi ne abinda duk su ukun suka buɗe baki suka cewa Niyashi cikin mamaki da ɗimuwa. Amma Niyashi yai murmushi tamkar ba wani abu ya ce, "kada ku damu, sannu a hankali zan baku labari na. Amma ba yanzu ba. Kamar dai yadda kuka gani bana tsufa kuma shekaruna sun tsaya cak tun daga ranar da na cika shekara sha shida a duniya. Babu wanda yasan wannan labari daga ƴan gida na saiku. Kuma abinda ya kawo ni nan a wannan lokaci shi ne ina so kuyimin alƙawari cewa baza ku gayawa kowa ba. Baza ku gayawa kowa kun sanni ba, sannan kuma baza ku gayawa kowa wannan labari nawa na rashin tsufa ba. Idan kukai min wannan alƙawari to ni kuma zanyi muku alƙawarin taimakon ku a duk lokacin da kuke buƙatar taimako, sannan kuma zanyi muku bayanin komai akan dalilin da yasa nake neman Nusi da kuma dalilin da yasa bana tsufa idan lokaci yayi." Duk su ukun suka kalli juna suna mamaki wannan abu. Iliyasis ne ya fara magana, "To mai yasa bazaka gaya mana yanzu ba?" Niyashi ya amsa yana murmushi, "Saboda bazan iya ba." Nusi ta tari numfashinsa tace, "Zanyi alƙawari, amma idan kayadda cewa zaka amsa min tambaya ɗaya." Niyashi ya ce, "Wacce tambaya ce?" Nusi tace, "Ka gayamin, shin kasan mahaifina?" Niyashi yaja dogon nimfashi tare da sunkuyar dakai, baya so ya amsa wannan tambaya, amma ga dukkan alamu Nusi ta daɗe tana so tayi masa wannan tambaya, kuma baza ta amince da wannan alƙawari nasa ba idan bai amsa mata ba, saboda haka a ƙarshe ya buɗe baki yace, "Nasan shi. Amma bazan gaya miki komai akansa ba yanzu." ------- To daga wannan rana Nusi da Cokali da Iliyasis da Niyashi suka ɗaura wannan alƙawari. Niyashi ya daɗe acikin wannan gida suna tare a wannan karan, amma bayan ɗan ƙokaci ya ƙara tafiya ya koma daular Infiriya. Kuma tun daga wannan rana har zuwa sanda Nusi ta zama ɗaya daga cikin manyan ɗalibai masu hazaƙa a daular Maikironomada basu ƙara haɗuwa da Niyashi. Nusi tana ƴar shekaru sha tara ta shiga takarar jarabawar da zata bata dama ta zamo ɗaya daga cikin waɗanda za'a ɗaukaka matsayinsu a daular Maikironomada. Jarabawar da ta kaita inda suka haɗu da Armad a shekarun baya. Jarabawar da ta canja rayuwarta har abada. Nusi bata ƙara ganin yarima Niyashi ba sai a gasar Jinzidal. Tayi mamaki sanda ta ganshi yana nan dai-dai yadda ta sanshi shekaru goma sha da duka wuce. Kuma taso su gana dashi amma Niyashin bai amince ba. A cewarsa akwai kunnuwa a binne a ƙarƙashin ƙasa, da kuma idanu a kafe a sararin samaniya wanda baya so suji ko kuma su ganshi tare da ita. --------- Iliyasis na tsaye rataye da takobinsa yana kallon ƙaton mutun-mutumi na Al-yaya a bakin ƙofar garin Khan. A gefensa Cokali ne tsaye shima yana kallon wannan mutun-mutumin. Abin mamaki basu kaɗai ne tsaye suna kallon wannan mutun-mutumi ba. Mutane sama da ɗari biyar kallonsa kawai suke suna kuma kallon jaridun dake hannunsu. Babu abinda kake ji sai hayaniya. Wataƙila ace ba abin mamaki bane aga mutane suna kallon wannan mutun-mutumi ba, tunda sama da shekara ɗari mutun- mitumin gida shida ne a ƙofar garin na Khan, amma ƴan watannin baya kaɗan na bakwai ya ƙaru. Lallai maza da mata zasu so suje suga wannan sabon mutun-mutumi da ake cewa na wani kyakkyawan saurayi ne. Sai dai kuma abin aljabin shi ne wannan sabon mutun- mutumi yana tsaye ɗaure a kansa da ɗan kyalle. A saman hannunsa na dama walƙiƴa ce take ta ci tana balbali. A hannunsa na hagu kuwa takobi ce tsirara. Idanun wannan saurayi sunyi kama dana jakadun mutuwar ƙarni na farko. Gashin kansa baƙi ne, wani a kwance wani a tsaye. Idan ka matsa kusa zaka gane cewa wannan yaro ba wani bane illa Armad Wilbafos. Kuma shi ne acikin shafin wannan jarida da mutane suke ta kallo suna hayaniya. A saman wannan hoto nasa ga kuɗi nan ansa har Ayrid sama da miliyan. Iliyasis ya dubi Cokali ya ce, "Lallai Ururu sunji labarin wannan mutun-mutumi shi yasa suka zabga wannan kuɗi akan Armad. Amma dai a halin yanzu ya zama dole mu nemeshi a duk inda yake, domin kuwa shi kaɗai ne zai iya gaya mana taƙamaimai inda ƴar uwarmu Nusi take. Amma na yarda da shawararka, mu fara zuwa daular Infiriya mu tuntuɓi yarima Niyashi muji ko yasan inda take." Cokali ya kyaɗa kai, "To mai muke jira, mu ɗau hanya kawai. Mu da dawowa wannan gari sai sanda muka ganta, ko kuma mu mutu muma nema, domin kuwa ita ma haka zatai mana idan mune muka ɓata." A wannan shekara Cokali da Iliyasis suka shiga duniya neman ƴar uwarsu Nusi Djinn. _____________________ Yarima Niyashi shi ne wanda Armad yaci galaba akansa a gasar Jinzidal, nayi tunani da nasa labarinsa a babi na baya zaku ce ya akai yake saurayi tun lokacinda su Nusi suke ƴan shekara shida, sannan kuma yake saurayi bayan sun girma har a sanda suka fafata da Armad. To ga amsar nan dai na faɗa, yarima Niyashi yana da sirrin Izza a jininsa tayadda baya tsufa. Yanzu tambayar ita ce mene ne alaƙarsa da Nusi? 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 73: Ikenga Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ______ Kwana biyu kun jini shiru Bani da lafiya ne shi yasa jiya na fara samun sauki, . --------- Ran Nusi a ɓace haka suka rankaya tare da Waziri, Saiza, da Galadima, Náru, da Sarkin Bai, Rayaya, izuwa garin Dula. Akan hanyarsu ne Nusi ta waiwayo izuwa waziri tana mai cewa, "amma nasan dole akwai mutanen da suke da damar keta wannan bango a sashin Ikwatora, ko kasan su?" Waziri Saiza ya ja dogon numfashi tare da kyaɗa kai yana cewa, "Eh, lallai akwai mutun ɗaya, babban sarkin Ikwatora, sarki Rainay Guguwa. Shi ne kaɗai sarki a ikwatora wanda tun shekarar da aka saukarda al'ummar biladama izuwa ƙasashen ƙasa yake mulki a sashin Ikwatora. Duk shekara tsibirin guguwa shi yake zaɓa a sashin Ikwatora dake doron ƙasa ta biyu. Ko a wannan shekara ma shi aka zaɓa. Wasu daga cikin mutane suna ganin cewa acikin baƙar guguwa aka haifeshi. To koma dai menene shi ne sarkin da yafi kowanne ƙarfin iko a sashin Ikwatora, kuma shi ne ya saka hannu a dokar hana ratsa wannan bango shekaru dubu da suka wuce, kuma shi kaɗai yake da ikon sauya wannan doka." Nusi taji daɗin wannan labari na waziri, inda ta juyo izuwa gareshi cikin jin iko da ƙarfin mulki tana cewa, "mene ne matakin da ake bi wajen zama babban sarkin Ikwatora? Ko zaɓe ake yi? Domin koma me akeyi saina hau wannan kujera na kuma karya wannan doka. Babu ruwana da a ina aka haifi sarki Rainay Guguwa, ko kuma ƙarfinsa ko kuma alaƙarsa da Ururu. Abinda na sani kawai shi ne saina nemo abokina Armad da ƴan uwana Iliyasis da Cokali. Koda jin wanann magana sai duk su ukun suka ja linzami cikin firgici suna duban Nusi wadda ko a jikinta. Baki a buɗe sun kasa cewa komai, haka suka rankaya har zuwa fada ba tare da kowa yace uffan ba. *** A shekarar da aka gama Jinzidal abubuwa da dama sun afku. An siyarda Armad a matsayin bawa, Nusi ta ɓata sannan kuma Ikenga ya gudu bayanda yayi arba da Uznu Ururu. Armad ya rayu a hannun Ururu duk da kuwa uƙubar da suka gana masa, sannan ya farkar da babbar Izza a jininsa. Nusi ta rayu duk da raunin da Uznu yaji mata, sannan kuma ta tsinci kanta a sashin Ikwatora ba tare da tasan yadda akai taje ba. Shi kuwa Ikenga yana ɓacewa daga wannan fili ya bayyana a tsakiyar saharar dajin Ƙairus dake doron ƙasa ta biyar. Babu gida gaba babu gida baya, hasalima Ikenga shi kaɗai ne a tsakiyar wannan dokar dajin. Ƙuwwar iska da zafin rana da yashi yasa gumi ya fara karyo masa. Gashi tuni ya ƙarar da ƙarfin Izzarsa a fafatawarsa da Armad. Saboda haka dakyar yake tafiya. Sai dai kuma ana cikin haka yaji wata ƙara a bayansa. Yana waiwayawa yai arba da wasu manyan-manyan sadaukai guda biyu. Wanda kana ganinsu zaka tuna da tarihin daular samudawa. Saboda nauyinsu ƙafafunsu sun nutse acikin ƙasar da suka dira. Suna sanye da baƙaƙen kaya masu ratsin ɗorawa daga sama. Kowanne ɗaya acikinsu Izzarsa ta haura dubu ɗaya. Ikenga yana ganinsu ya gane su. Ba wasu bane illa biyu daga cikin kwamandu biyar dake aiki a ƙarƙashin Uznu Ururu. Ikenga yayi murmushi yana mai cewa, "dama nasan baza ku kyale ni haka ba." Ɗaya daga cikin kwamandun guda biyu ya miƙa hannunsa kan takobinsa yana mai cewa, "ka miƙa kanka salin-alin babu gardama. Dukkanmu izzarmu ta haura dubu, kana da ɗari kacal. Mai zaka iya yi face miƙa wuya." Ɗaya kwamandan wanda keda baƙar fuska da manyan ƙasusuwa masu kama da duwatsu ya ƙara da cewa, "kada ka zargi kowa ka zargi rauninka da lalacinka dana zuri'ar ka." "Hmmm....." Ikenga yaja dogon numfashi tare da murmushi yana cewa, "Idan zaku iya kama ni to ku gwada." Yana rufe baki ya tafa hannayensa guda biyu yana kiran waɗansu ɗalasimai da harshen Wilburish. Lamarinda yasa wani shinge na koren haske ya bayyana ya kewaye shi. Abin mamaki daga cikin wannan haske saiga wasu mutane uku sun bayyana. Babban abin mamakin shi ne biyu daga cikinsu kamarsu ɗaya sak da Ikenga, kai hasalima Ikenga ne kawai. Babu maraba koda kuwa ta kwayar zarra. Ɗaya mutumin kuwa wannan tsohon ne mai suna Kána, wanda aka gansu tare da Ikenga watanni kaɗan kafin Jinzidal, a lokacin da Ikenga ya jawo salwantar ruhin Armad. Waɗannan mutane biyu masu kama da Ikenga suka rikiɗe izuwa iska sannan suka shige jikin Ikenga. Haka na faruwa wannan da'irar haske ta ɗauke, amma Izzar Ikenga nan take ta canja daga ɗari zuwa duba ɗaya, sannan ta ƙara rikiɗewa daga dubu ɗaya zuwa dubu goma. Gashin kan Ikenga ya rikiɗe izuwa fari fat, sannan kuma ya ƙara tsayi har zuwa gadon bayansa. Fatarsa jikinsa tai fari fat tamkar an zuƙe jinin dake jikinsa. Wata sabuwar nutsuwa ta bayyana a tattare dashi. A wannan lokaci idan baka sanshi sosai ba baza ka gane shi ba. Ana haka saiga aljani Gal-iyyu ya bayyana ya fito daga jikin Ikenga ya zube a ƙas cikin biyayya. Shima wannan tsoho Kána a ƙas ya zube yana mai cewa, "barka da dawo wa, sarkin duniya." Su kuwa waɗannan kwamandu guda biyu buɗe baki sukai cikin firgici suka fara jada baya, amma ina tuni sanyin babban sihiri ya sauka a garesu. Wannan ƙanƙara ruwan toka mai ɗauke da ƙarfin Izzar Ikenga ta ratsa ƙashinsu, sannan ta rusa ruhinsu. Kan kace meye wannan waɗannan kwamandu masu Izza sama da dubu sunyi bindiga sun faɗi ƙasa matattu. Ikenga ya juyo izuwa Aljani Gal-iyyu da tsoho Kana yana magana a nutse tamkar ba shi ne ya halaka ma'abota Izza sama da dubu ba. "Kunga yanzu duniya zatai tunanin ƙarfinmu bai wuce na Izza ɗari ba. Za suyi tunanin cewa ƙarfin Izzarmu bai wuce na mu kara da wannan yaro ɗan zuri'ar Wilbafos ba. Hakan zaisa baza a saka mana ido ba a lokacin da muke gudanar shirye-shiryenmu ba." Ɗan tsoho Kána ya amsa da cewa, "wannan haka yake ya shugaban mu. Zanso naga fuskar yaron nan Armad a sanda zai gane cewa da ɗaya bisa ukun ka ya fafata amma ya kasa samun nasara. Hasalima saida ka raba izzarka gida ɗari sannan kai amfani da kaso ɗaya." "Armad?" Ikenga ya tambaya cikin girman kai da jin Izza tamkar bai taɓa jin sunan Armad ba, sannan ya ɗora da cewa, "Ah... sunan sa kenan." 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 74: Miyura (1) Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos -------- A wani gari nisan kimanin shekaru hamsin daga inda Armad tsaye, a wani tsiburi dake tsakanin doron ƙasa ta farko data biyu, wasu yara ne ƴammata guda biyu ke wasa a gefen wani kogi. Kana ganin ƙirar yaran da kayan jikinsu zaka san cewa lallai ƴaƴan sarauta ne. Dukkan idanunsu farare ne fat babu ko kwayar baƙin dake cikin ido. Kai ka rantse makafi ne. Amma zaka gane cewa suna gani tar-tar kamar kowanne ɗan adam a yayinda ɗaya daga cikinsu wadda ta kasance fara mai gashi roɗi-roɗi ta ga wani mutun a kwance a gabanta ruwa ya koroshi. Ba shiri taja rigarta sama, ta kuma fara kiran ƴar uwar ta, "Suwee! Suwee!! Suwee!!!" Ƴar-uwar tata ta juyo izuwa gareta. Asalin sunan ƴar uwar shi ne Suwainah, amma ƙanwar tata mai suna Zeera ta fiso ta ringa kiranta da Suwee. Zeera ta nuna mutunin dake gabanta tana cewa, "Kizo kinga wani ma, ina ragowar ukun?" Suwee ta zare ido cikin firgici tana cewa, "Wani ne ya ƙara bayyana? Waɗancan baba ya tafi dasu wajen sarki." Zeera ta buɗe baki cikin mamaki,"Baba kuma? kina nufin baba da kansa! To gaskiya ne kenan abinda ake faɗa cewa daga wata duniyar aka jefosu!" Tun kafin ta rufe baki yayar tata mai kimanin shekaru sha shida wadda kuma ta bata shekaru uku, ta taho wajen da take da gudu domin taga wannan mutun da ƙanwarta take nuna mata. Tana zuwa ta rufe ƙanwar tata da faɗa, "ba baba yace mu daina faɗa ba, so kice wasu suji. Yana ina?" Zeera ta nuna mata wani yaro kwance a gefen kogin, duk taɓo ya shafe masa jiki da fuska. Amma duk da haka idan kalura sosai zaka ga cewa akwai ɗaurin jan kyalle a gaban goshinsa. Kuma lallai idan kasan Armad Wilbafos mamallakin tambarin Miyura zaka gane cewa shi ne ba wani. Suna tsaye suna tunanin ya zasu yi kawai sai suka ji hayaniyar sauran ƴan matan daga nesa suma suna kusanto wannan kogi. Zeera ta dubi ƴar uwar tata cikin sauri tana cewa, "Yaya to ya zamuyi dashi, ga mutane nan!" Nan take Suwainah ta fito da wata ƴar ƙaramar jakar tsafi a cikin rigarta ruwan hoda, inda ta bawa ƴar uwarta ta. Suka kuma fara tala wannan jaka har saida takai dai- dai tsayin yadda zasu iya zira Armad aciki. Ƙanwar ta miƙa hannunta domin ta fara saka kan Armad aciki, amma a lokacin al'amari ya canja. Domin kuwa tana taɓa jikin Armad hannunta ya shige cikin kansa tamkar babu komai a wajen. Cikin sauri ta zaro hannunta ta kuma ƙara taɓawa dan ta tabbatar, amma hakan dai ta ƙara faruwa a karo na biyu. Nan da nan ita ma Suwainah ta miƙa nata hannun ta taɓa ƙafarsa, amma taga itama hannunta ya shige tamkar babu komai a wajen. Cikin tsananin mamaki suka fara tunanin ko mafarki suke. Amma maganar ƴan uwansu matan dake ƙara matsowa ita ce ta tabbatar musu cewa ba mafarki suke ba. Nan take suka fara bin duk wata hanya domin zira jikin Armad acikin wannan jaka, amma ina. Kuma suna cikin haka ne ɗaya daga cikin matannan masu ƙarasowa ta hango su, ai kuwa nan take ta fara kwala musu kira, tare da tahowa inda suke. Nan take Suwainah ta yanke hukunci tana mai cewa, "Zeera jeki ki gano inda baba yake. Idan da dama ki gaya masa abinda ke faruwa a ɓoye ba'a cikin mutane ba. Zanyi maganin abubuwa anan." Tana faɗar haka ƴar uwar tata Zeera ta rankaya a guje ta nufi gabas. Suwainah tayi duk wata dabara da zatai ta ɓoye ruhin Armad amma abin ya gagara. Tana cikin wannan hali wannan ƴammata huɗu suka iso wajenda take tsaye. Tai kasaƙe tana jira su tambaye ta wane ne wannan mutun dake kwance a bayanta amma ba suce komai ba. Hasalima tamkar basa ganinsa. Wanda hakan yasa Suwainah waiwayawa cikin zafin nama tayi duba izuwa inda tabar Armad amma babu shi babu alamunsa. Tana cikin diri-diri taji muryar ɗaya daga cikin wannan mata dake gabanta. "Suwainah me kike anan ke kaɗai? Saura kwanaki bakwai a rantsar da ma'abota Ururu na wannan shekarar, kije ki rubuta sunanki ki hau layi." Suwainah ta kyaɗa kai tana cewa, "Eh hakane. Dama nazo wanka ne kuma bansan an fara rubuta suna ba. Yaya tsarin yake?" Ɗaya daga cikin ƴan matan taja dogon numfashi kafin daga bisani ta kyaɗa kai tana cewa, "fafatawa za'ai kawai. Duk wanda ya farkar da Ururun dake idanunsa zai shiga cikin ma'abota Ururu. Ragowar kuma zasu ci gaba da zama anan sai wata shekarar. Sannan kuma acikin waɗanda

Chapter 26 of 33