Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
halartar Deniziyya Kurónikil. Wasu sune zasu shiga da kansu, wasu kuma ƴan rakiya ne, wasu kuma manyan baƙi ne. Tuni mutane suka fara bin layi, suna biyan kuɗin shiga inda za'a haɗa su da wani Badenize dake wajen ya faɗa dasu cikin ɗaya cikin ramikan dake kewaye dasu. Kowa ka gani sanye yake da kaya daban-daban, kai kasan daga ƙasashe daban-daban suke. Kafin jimawa da dama daga cikin waɗannan jama'a sun shige cikin waɗannan ramika, izuwa cikin wannan gari. Daular Denizawa zaka iyai mata kallon kamar wani ƙatoton gari ne mai tsananin girman ƙasa. Wanda acikinsa akwai birane manya guda biyar. Birane huɗu sune a zagaye da wannan gari guda ɗaya, wanda ya kasance a tsakiya, kuma ya ɗan haurasu girma. Sun tsara ginin kowanne gari ne, yadda zai zamo, a kewayen kowanne gari, akwai ƙaiyadaddun adadin ramika dake kewaye dashi, wanda kuma ta ciki ne, mutane ke ɓullowa bayan sun shiga ta waɗannan dajika na waje. A kewaye da waɗannan birane huɗu, dazuka ne kala-kala, iri-iri, wanda girman ƙasar da suka ci, shi kaɗai ya haura girman gaba ɗaya garuruwan nan guda biyar. Sannan kuma a kewaye da waɗannan dazuka kuma katanga ce, wadda akayi da wani sinadari na musamman, shidai ba ƙasa ba kuma dutse ba, ba kuma ƙarfe ba! Katangar nada girma sosai, tayadda baka iya gano ƙarshenta dama da hauni, sama da ƙasa. Acikin wannan gari dake tsakiyar garuruwan nan, akwai wani ƙaton fili wanda ya kasance a kewaye. Idan ka shiga cikinsa zaka ga cewa yama fi yadda kake tunani girma. Daga farkonsa a zagaye yake da kujerun zama na alfarma waɗanda yawansu bazai lissafu. Idan kai musu kallon farko abinda zaizo ranka shi ne, komai yawan mutane zasu iya ɗebe su. Daga cikin filin kuwa wasu ƴan ginannun wajaje ne ƴan ƙananu waɗanda suma suna da ɗan yawa kuma suna gaban waɗannan kujeru na farko. Daga tsakiyar filin kuma wani ƙatoton fili ne wanda akai masa tsarin filin danbe, kuma aka kewaye shi. Kai daka gani kasan wannan fili yaga fafatawar Mazan jiya. Domin duk da sabon mashimfiɗi aka lulluɓeshi dashi ta kowanne ɓangare, hakan bai hana kaji yanayi mutuwa na tashi daga jikinsa ba. Akwai fitilu na musamman dake kewaye da wannan filin na tsakiya suna bada haske mai ba sha'awa da sawa kaji marmarin yaƙi na tashi acikin ranka. Duk da cewa babu kowa acikin filin tsakiyar, daga cikin waɗannan ƴan ƙananun wajaje kuwa waɗanda basu da nisa sosai daga filin tsakiyar akwai mutane kusan acikin guda shida daga ciki. Kana gani zuciyarka zata baka cewa waɗannan sune mutanen da suka zo daga sauran manyan kabilun nan da sauran ƙasashe. Wani abu mafi ban mamaki da ba'a ambata shi ne, wani ƙaton gini daya tashi ta ɓangaren gudu maso yammacin wannan fili na tsakiya. Wanda ya kasance shi ne waje mafi kusanci da filin tsakiyar. Gilashi ne ke kewaye da wurin baki ɗaya, tayadda ana iya ganin komai dake ciki. Kuma a wannan lokaci zaka iya hangen kujeru na alfarma waɗanda yawansu bai wuce goma sha ba aciki. Akan waɗannan kujeru kuma dake zagaye da duk filin, mutane ne da dama, ana ta mayar da labari akan ire-iren waɗannan gasanni da suka gabata. Amma duk wannan kaɗan ne idan ka kwatanta da yawan mutanen dake tsattsaye a bakin ƙofar shigowa wannan waje. Babu abinda kake ji sai hayaniya akan suna yen taurarin da ake saran zasu buga wannan gasa. Kuma ga dukkan alamu waɗanna mutane sun san taurarin nasu basa wajen, wanda hakan nema ya sasu fitowa bakin ƙofar domin kallon sanda zasu shiga. A dai-dai wannan lokaci saura ƙasa da awa ɗaya a fara wannan gasa, a yadda aka ƙayyade lokacin farawar. Ana cikin hakan ne wani saurayi ya bayyana, mutun bakwai na bayansa, dukkansu sanye da kaya mai fari da yalo. Tun daga nesa wasu daga cikin waɗannan mutanen daje jira suka fara nunashi. Koda jama'a suka kyalla ido suka ganshi, sai kuwa hayaniya ta ƙara tashi. Babu abinda kake ji sai, ''kai....... aikuwa da gaske ne!!! ''Kai..ka...kai....., wannan karan hardasu, lallai za'a sha fama. ''Wallahi shi ne!!!'' Can daga cikin taron waɗannan mutane, wani yaro mai ƙarancin shekaru, yana tsaye a ɓangaren arewa, babu abinda yake sai jan rigar wani dattijo Badenize, ya na tambayarsa, ''baba wanene? Baba wanene?'' Baban ya waiwaya, gami da cewa, ''ƴan ƙabilar Hán, daga doron ƙasa ta uku! ''Kuma ina kyautata zaton wancan yaron na gaba shi ne Hán-na-bakwai, wato Hán-Amuru, ko kuma sunansa cikakke Hanamúru Zulkiflu!!'' Kafin wannan dattijo ya gama bayani muryarsa ta fara rawa, kamar wanda yake tuno wata azaba. Kamar yaron ya fuskanci maike faruwa da sauri ya ce, ''shikenan baba na gane!'' A dai-dai wannan lokacin wannan tawaga suka zo suka wuce, suka shiga cikin wajen. To kamar yadda tsohon ya faɗa dai haka ne, wannan tawaga data wuce daga ƙasa ta uku suke, kuma wannan yaron shi ne, Hánamuru, wanda akewa laƙabi da Hán-nabakwai. Shima yazo wannan gasa, kuma tuni suka gabatarda adadin bayi dubu goma ga Jinzidal kamar dai yadda sauran ma daga sauran ƙasashe suka kawo. Ana cikin hakane waɗannan mutane suka ƙara ruɗewa zaka hango kusan tawaga har guda uku tana tafe. Kan kace meye wannan tuni shewa da ihu mai cike da murnar gani gwanayensu ta cika wajen. Kusan zaka iya cewa duk cikin garin nan ana jin wannan ihun. Nan take maganganu suka fara tashi, ''Shugaba yarima Bizaya!! ''Ah! ga Ikenga O. Bayajidda can ma!! ''Ga kuma hmmmm....Maikironomada!!'' Tawaga ta farko mai ɗauke kusan mutum sha biyar, dukkaninsu sanye da fararen kaya, ita mutanen keta nunawa suna murna gami da kiran sunan 'Bizaya'! Ya biyun kuma wadda ita ce mafi ƙanƙanta, mutane uku ne kawai, dukkaninsu sanye da kaya masu baƙi da ɗorawa. Kuma ita ake nunawa ana kiran sunan Ikenga. Sai kuma ta ukun wadda ke ƙunshe da kusan mutun goma, waɗanda mafiya yawansu kaya daban-daban suka sa. Kuma wani abin mamaki duk da irin girman wannan ƙabila ta Maikironomada, waɗannan mutane dake wajen basa nuna wani buri akansu. Hasalima tuni sun ɗauke kansu daga garesu, suna ta ɗagawa Bizaya da Ikenga hannu sunai musu fatan alkhairi. Bayanda aka gama sallamar tawagar Bizaya da Ikenga, kuma aka basu shedar shiga da kuma wajen da zasu tsaya idan sun shiga, sai da dama daga cikin mutanen nan dake tsaye suma suka juya baya suka rufa musu baya, ba tare da ko damuwa da ƙarasa kallon tawagar Maikironomada ba! Tundai abin baya damun ƴar tawagar, har takai wasu sun fara tsaki. To amma a dai-dai wannan lokacin ne wata tawaga guda biyu suka doso wajen, kuma duk da nisan da suke dashi kafin su ƙaraso, tuni ƴan tsirarun da suka rage sun fara nunasu da hannu suna kwalawa, ''Kaiiiiii......kai wannan shekarar Infiriya Yarima Niyashi suka turo, lallai, wataƙila za'ai Deniziyya Kurónikil ɗin da ba'a taɓa yi ba! ''Wallahi shi ne!! Yarima Niyashi, mashin mutuwa!!! ''Kaiiii! Ku duba gefe ga tawagar Banfiriya can ma!! ''Dama su a duk shekara yarima suke turowa!!!! ''Kaga wannan shekara yarima Kiru suka turo!! ''Shi ne yayan gimbiya Nostalgia!! ''Oh...Zahra Kyau!! Kana tunanin kuwa tana cikin waɗancan Babysawan uku dake cikin tawagar tasa!!'' Kan kace kwabo, tuni irin waɗannan maganganu sun cika wajen. Kuma waɗannan mutane da da suka juya baya suka fara tafiya, yanzu sun dawo, wasu ma har gudu suke suna tunkuɗe mutanen dake shiryen-shiryen shiga ƴan tawagar ƙasar Maikironomada!!! Lallai mutanen wajen basu da wani gwani Maikironomada, ko mai yasa? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 31: Na daya dana karshe Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Koda waɗannan ma'abota Izza guda shida suka tsaya, sai kowa acikinsu ya buɗe baki tare da furta waɗansu ɗalasimai waɗanda suka shafi al'amarin Izzarsa. Dukkaninsu nada cikakkiyar amanna cewa lallai waɗannan ɗalasimai nasu sunfi ƙarfin kowa dake cikin zagayen karawarsu. Badan komai ba saidan cewa a wannan gasa zance ne na waye ya riga gamawa. Domin suna da cikakkiyar masaniyar cewa acikin waɗanda sukai nasara guda shida daga kowanne zagaye, guda huɗu kaɗai za'a ɗauka suje zagaye na gaba. Waɗannan kuma sune wanda suka riga sauran gamawa. Musamman duba ga cewa da dama daga cikin waɗanda suke kwabzawa dasu a rukunin nasu basu kaisu ƙarfin Izzarsu ba. Saboda haka mutun shidan nan suna da amanna sai sunyi nasara a rukuninsu, kawai dai kowa yana ƙoƙari ne ya riga sauran ƴan uwansa gamawa. Saboda ƙarar karan batta dake faruwa da ihun mazaje suna fafatawa a cikin dukkanin wajajen shida, babu wanda ya kula da abinda suke aiwatarwa, kusan kowa ya takansa yake. Kowa so yake ya samu nasara ko ya samu ya tseratsarda ƙannensa da ƴaƴansa da abokansa da iyayensa daga zama bayi. Domin rashin yin nasararsu tana nuna kason mutanen da suka kawo sun zama bayi kenan a wajen wanda yayi nasara. A dai-dai lokacin da waɗanann samari shida ke ƙoƙarin aiwatar da munanan hare-hare akan ƴan uwan fafatawarsu, kowa ka gani idonsa a rufe yake. Babu abinda nakan filin dagar nan suke sai saran junansu, jini na malala, kayika na tsalle sama. Amma tamkar ba ɗan adam ake kashewa ba, ma'abota kallon fafatawar nan kawai sai ihu da jin daɗi da shewa suke daga kan kujerunsu da suka zagaye filin wasan. Kai daka gani kasan sun saba gani kuma wannan ba wani sabon abu bane. Ana cikin haka saurayin dake rukunin E, wanda babu makami a hannunsa, ya tafa hannayensa guda biyu! Suma sauran samarin kawai sai wani shuɗin haske ya fara tashi daga jikinsu, lamarinda ta fara jan hankalin wasu daga cikin masu fafatawar da kuma da yawa daga cikin ƴan kallo. Abu na gaba kuwa da aka gani a kowanne rukuni ya bada matuƙar mamaki, wanda saida yasa dukkanin wanda ke kallon wannan gasa acikin wajen ko kuma a waje ta hanyar Ayrid mai nuna hoton bidiyo, buɗe baki da shiga mamaki mai haɗe da firgici. Bayanin dalla-dalla abinda ya faru ba abu bane mai yiwuwa ba, domin komai ya faru ne cikin rabin ƙiftawar ido kuma a tare. Sannan kuma ga wannan shuɗin haske ya ƙaru matuƙa tayadda ya haskewa mutane da dama idanu. Ga kuma wani wuta jajawur datai ƙuwa tare da tsalle sama ta kuma haske ilahirin filayen fafatawar nan guda shida. Lallai akwai ma'abocin aljanin wuta a ɗaya daga cikin waɗananan filaye. Bayanda wannan wuta da wannan shuɗin hasken suka gauraye suka bada wata irin kala mai ban tsoro, suka lafa, sai mutane sukai arba da filaye guda shida. Kowanne babu kowa a tsaye sai mutun ɗaya; A rukunin A, wani saurayi ne riƙe da wata doguwar takobi da tama fishi tsayi. Yana sanye da kaya masu zanen ɗorawa da baƙi. Fari ne mai yawan baƙin gashi. Idanunsa a tsaye suke, sannan kuma idan kayi duba cikinsu babu abinda zaka gani sai azabar tsana da kafiya, kai kace duk wata tsana da fushi da baƙin cikin duniya daga cikin waɗannan idanu suka samo asali. Fatar fuskarsa kuwa a ɗame take, kana gani kasan yayi shekaru da dama baiyi dariya ba. Kallon ɗaya zakai masa ka gane cewa a lokacin yana yaro kyakkyawa ne, kuma kuma har a wannan lokacin idan ka kalli yanayin zubin hancinsa da fuskarsa kasan irin kyan nan ne da baƙin ciki da ɓacin rai yake lalatawa. Kaf tsokar jikin wannan saurayi a murɗe take, kai kace basu taɓa motsi ba. Irin waɗannan mutananne da idan aka ce kayi bayaninsu a kalma ɗaya zuwa biyu, zaka ce, 'rashin imani', kawai ka rufe baki! Idan kuma ka kalli mutanen dake kwance a ƙasa acikin rukunin zaka tabbatar da haka. Domin kuwa dukkaninsu ƙirjinsu a cake yake da makamai, kuma abin mamakin shi ne, makamansu ne kuma hannayensu ne suka daɓa musu su a ƙirji. Kaf ɗinsu sama da mutun talatin gasu nan a kwance a ƙasa matattu! Wannan saurayi ba wani bane illa Ikenga O. Bayajidda! Ba jimawa ƙasar filin rukunin na A ya fara haske, kafin daga ƙarshe ya nuna alamun daƙiƙa ashirin da tara. Wato alamun cewa Ikenga ya gama a tsahon daƙiƙa ashirin da tara kenan. Koda wannan haske ya ɗauke sai Ikenga ya ɗaga ya ɗanyi wani murmushi mai cike da nufaƙa. Ɗaga kan nasa kuma ya ƙara bayyanarda wani ƙaton tabo a wuyansa. A rukunin B kuwa wannan saurayi mai riƙe da takobi wadda bata fi tsayin hannunsa ba, da kyalle a goshinsa shi-shi kaɗai ne a tsaye. Kuma idan ka kalleshi sosai zaka ga ba wani bane illa Armad Wilbafos. Wanda bai samu hankalinsa ya kwanta ba saida yasa kyalle ya rufe goshinsa duk da kuwa Miyurar tasa ta ɓace kuma baisan inda tayi ba. Amma kasancewar kyallen a goshinsa yana ɗan sawa yaɗan manta na ɗan lokaci. Tuni Armad ya yanke acikin ransa cewa duk ma inda wannan Miyura ta tafi lallai saiya nemo ta. Domin yafi kowa sanin amfanin ta. Koba komai tana ƙara masa ƙarfin Izzza, kuma da dama daga cikin fasahar walƙiyarsa suna buƙatar babbar Izza, wadda kuma bashi da ita. Amma ta dalilin wannnan Miyura bashi da matsala. A kwance a ƙasansa ragowar ƴan rukuninsa ne suke ta murƙususu amma babu wanda ke iya tashi, saboda haka bayan ƴan daƙiƙu shi ma wannan haske ya bayyana, wanda ya sa masa alamun daƙiƙa talatin da biyu, wato ƙarin daƙiƙa uku kenan akan na Ikenga. A rukunin C kuwa babu kowa akan gaba ki ɗayan filin. Dukkansu kamar ansa tsintsiya an sharesu zuwa ƙasa. Babu kowa sai wani saurayi mai yawan gashin fuska, riƙe da fafalo mai lanƙwasa. Sannan hasken dake tashi na nuna daƙiƙa talatin dai-dai. Saurayin nada faɗi da yawan gaske, hakan nema yasa duk da cewa bawai gajere bane kuma ba dogo bane, amma da dama sai a ringa yi masa kallon gajere. Lamarinda bai masa dadi Ko Kadan! Amma kuma wani abu dashi shi ne, fuskarsa bata da faɗi sosai, sannan kuma baka buƙatar a gaya maka cewa tsatson wannan saurayi ma'abota sarauta ne. Domin a duk cikin waɗannan samari, da wuya ka samu mai yawan kyawunsa da kuma fitarda kamalar sarauta. Wani ƙarin abu ga fuskarsa shi ne, saboda yawan gashin dake fuskarsa sa, gashin girarsa ma a haɗe suke, wanda hakan ya bashi kamanni na daban, kuma da dama suna ganin abinda ke rage masa kyau kenan! Amma duk da wannan, babban abinda zaisa idan ka kalli wannan saurayi baza ka taɓa mantawa dashi ba shi ne idanunsa. Babu komai acikinsu face tsananin azabar masifar marmarin yaƙi!! Irin soyayyar nan da baza ka iya rabuwa da abu ba, irin ta sak zaka gani acikin idonsa, amma ba soyayyar komai bace ba illa yaƙi. Wannan saurayi ba wani bane illa Deniz Bizaya! Ɗan sarki Deniz Iluru. Saboda tsananin sansa da yaƙi, ance kullum yana cikin gwabzawa, har nemo abokan fafatawa yake a kullum ƙasa zuwa ƙasa, kuma hakan nema yasa suka saba da Ikenga! Idan mai Karatu bai mantaba an gano su suna fafatawa kwanaki kaɗan kafin a fara wannan gasa. Koya waɗannan giwaye suka ji, domin dai ga dukkan alamu basu samu damar haɗiye su ba. Tunda gasu acikin filin daga. A rukunin D kuwa, saurayi ne riƙe da mashi a hannunsa, kuma kana ganinsa, zaka san cewa ransa ɓace yake kuma acikin zuciyarsa akwai ɓacin rai na rashi! Amma kuma idan ka lura zaka ga wannan ɓacin ran baishiga cikin ƙashinsa ba kuma baikai irin ƙiyayyar dake zuciyar Ikenga ba! Fuskarsa babu gashi ko guda, kuma kyakkyawa ne, fari fat dashi kamar fulanin farko! Idan ka duba ƙasansa zakai arba da yuyar mutane kwance fululu! Amma abin mamakin da wannan rukuni shi ne, dukkanin waɗannan mutane dake kwance, idan ka lura zaka ga cewa da dama daga cikin waɗannan mutane waɗanda da suka kasance farare, amma a wannan lokaci suna ƙasa fatar jikinsu ta sauwa izuwa shuɗiya!! Sannan ragowar kuma waɗanda suke baƙaƙe, su kuma sun ƙara baƙi sosai matuƙa, tayadda kana ganinsu zaka gane cewa sun canja. Amma bisa mamaki, duk wannan abin hasken dake tashi daƙiƙa talatin da biyu shima yake nunawa, wato kamar na Armad. Babban wajan al'ajabin shi ne rukunin E, inda babu abinda kake ji sai ihun mutane waɗanda rashin sa'a ya tadda su, domin kuwa a wannan lokaci idan ka kallesu zakai arba da cewa acikin wata jar wuta suke muraran suna soyuwa!! Duk inda ka kalla sai kaga wannan wuta ce a jikin mutanen, sannan kuma sun kasa motsawa a wani yanayi na kamar ta ɗaure su da ƙasar wajen, ta yadda ko motsi basa iyayi. Kuma abin mamaki shi ne, hasken dake tashi yana nuna masa daƙiƙa ashirin da takwas ne, wato ƙasa dana Ikenga ma. Kuma duk da abinda ke faruwa, murmushi ne kawai a fuskar wannan yaro. Sai kuma wani abin al'ajabi idan ka kalli idanun wannan yaro mai suna Han Amuru wanda bai wuce shekaru sha shida ba, zaka alamun aljanin wuta yana balbali da wuta. Kai kace idanun sun ƙone gaba ɗaya. Sai dai kuma amma saboda wannan aljani nasa ma'aboci wuta, shi baya jin zafin wutar ko kaɗan. Ko kuma ace shi bata aiki a kansa. Wannan saurayi shi ne yazo daga ƙasa ta uku. Wato mahaifar Armad kenan. Kuma daga ƙabilar Han, wato ƙabilar babban sarkin ƙasa ta uku kenan. A rukunin F kuwa wani saurayi ne tsaye da takobi mai hasken gaske, kai kace walƙiya ce saboda yadda take haskawa. Yana tsaye, kuma duk inda ka duba, idan banda wajen da yake tsaye akai, zaka ga ya rududduge ya zama gari, duk sauran abokan karawar tasa na ƙas. Wato dai a taƙaice shi kaɗai ne akan wajen da aka ƙaiyaje! Ya riga ya gama fashe ko'ina, kuma sauran abokan fafatawar tasa suna tsaye a zagaye dashi a ƙasa, amma haka zasu haƙura, babu abinda suka iya saidai kallo. Domin an riga an cire su saboda sun fita daga kan kewayen. Idan ka dubi wannan saurayi sosai zaka ga ashe ba wani bane illa Kiru Sisiyu, yayan Zahra! Kuma duk yadda akai yayi amfani da farar takobi. Wadda idan mai karatu bai manta ba ta kusa halaka Armad a baya. Amma fuskar Kiru bata nuna alamun komai, ko kaɗan. Wato dai bata nuna farin ciki, ba kuma ta nuna baƙin ciki, tamkar babu wani abu da yake tunani acikin zuciyarsa! Idan da Armad zai ganshi a wannan lokaci kuma ya tuna da yadda ya sanshi, to da lallai saiya sha mamaki. Hasken dake tashi daga ƙasansa na nuna daƙiƙa talatin da biyar. Bakin ƴan kallo a buɗe yaƙi rufuwa. Kai hatta shi kansa alƙalin wasan bakinsa a buɗe yake, idanunsa na cike firgici. Can bayan wasu ƴan daƙiƙu ya dawo hayyacinsa inda ya bayyana cewa, da Ikenga mai ashirin da tara, da HánAmuru mai ashirin da takwas, da kuma Deniz Bizaya mai talatin da ɗaya duk sun wuce zuwa zagayen kusa dana ƙarshe. Amma Armad da Kiru da Niyashi duk sun sami maki iri ɗaya wato talatin da biyar, saboda haka, abisa dokar Deniziyya za'a kawo musu Alkadar domin fitar da gwani. To a wannan lokaci ne aka tafi hutun lokaci, kafin a dawo a fitarda gwani a tsakaninsu Armad, sannan kuma a wuce izuwa gasar kusa dana ƙarshe. Kuma a lokacin aka bawa sauran manyan baƙi damar zasu iya zuwa su tattauna da waɗanda suka zo dasu. Kuma a wani lamari mai ban mamaki kawai saiga tawagar Banfiriya nan sun danno kai!!! Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 32: Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos . Wani abin mamaki, wannan tawaga ta Banfiriya suna zuwa suka nufi inda Kiru yake, kuma suka jashi gefe suna ƙus-ƙus. Babu wanda yasan mai suka tattauna, amma dai daga baya sun nemi waje sun tsaya a kewayen wajen da ake fafatawar, wato dai basu shiga wajen manyan baƙi ba. Ragowar sauran manyan baƙin kuwa irin su Asifu (wanda akafi sani da RUWAN BALA'IN), baima nuna alamun yaga shigowarsu ba, kawai hira yake. Suna tattaunawa akan Izza da ɗaya daga cikin mutanen da suka rako sarki Deniz. Wani Badenize da ake kira da Deniz Kalhari. To da yake idan ka duba gefen Armad zaka ga Nusi a gefensa. Kuma tunda ta fito daga cikin wajan manyan baƙi take yi masa bayani akan Alkadar. Ji take kamar wani babban jafa'i na dab da saukarwa Armad, saboda haka kwata-kwata bata saki jiki ba. Kuma tunda daman su Maikironomada gaba ɗaya basu fiya damuwa da tura wani babba zuwa wannan gasar ba, shi yasa da tace zata zo, da wuri ta zama shugabar tafiyar, tunda babu wanda yakaita matsayi acikin tawagar. Hasalima wannan shi ne babban dalilin da yasa Denizawa basu kula dasu ba a baya, saboda a matsayinsu na babbar daular tsohuwa, bai kamata ace basa taɓa turo wani babba ba, kai koda matsayin ɗan majalisa kawai. Wanda hakan yasa Denizawa suke ganin raini ne yasa. Nusi ta gama yiwa Armad bayani kenan tana niyyar komawa wajen manyan baƙin, kawai taga ƴan Banfiriya sun tsaya saboda haka ita ma ta tsaya. Acikin wajen manyan baƙin nan kuwa tuni sarki yasa aka wadatashi da kayan ci da sha, sannan bayan wani lokaci ya ƙara komawa gefen Uznu'Ururu, wanda har wannan lokaci idanunsa a rufe suke, yana isa ya dubi Uznu tare da cewa, ''ina fatan yaran suna ƙayatar dakai! ''Kaga yanzu duk wanda suka futo matakin zagayen kusa da ƙarshe kyautar da zan basu ita ce Ayrid mai mataki na ɗaya guda hamsin hamsin sannan kuma da ƙusar yaƙi guda ɗaya ga kowannensu. "Wanda yazo na biyu kuwa, Ayrid guda ɗari da kuma ƙusar yaƙi guda biyar. "Amma ga wanda yazo na ɗaya kuwa kyautarsa ita Ƙusar yaƙi guda goma da kuma Ayrid mai mataki na goma." "Wato ni da kaina zan basu wannan kyauta, saboda haka ya zamo zai iya yin nutso a wannan fage na Izza kamar yadda kowanne Badenize zaiyi. Duk wannan kyauta kawai zan bada ita ne a matsayin nuna jin daɗi ga ƙasashen da suka taka rawa a wannan gasa acikin ƙasa ta. Kaga idan aka haɗa da kyautar bayi ga waɗanda sukai nasara ɗin, to kaga gobe kowacce ƙaramar ƙasa babba ko ƙarama zata so ta taka rawa a Jinzidal idan za'ai a gari na na Seerisha." Sarki Deniz Iluru ya ƙarasa bayanin sa da kurɓar wani ƙayataccen fari lemo dake hannunsa. Sai dai kuma Uznu Ururu shiru kawai yai masa baice masa komai ba, sai can wani lokaci, tuni Armad da Niyashi da Kiru sun hau kan ɗaya daga cikin sababbin filayen da akasa domin gudanar gasar mutun-mutumin Alkadar, sannan acikin wata murya ƙasa-ƙasa ya ce, "Abubuwa masu muhimmanci sun taso, na farko bayyanar Magajin Wilbafos, wanda kasan ba batu bane da Ururu take ɗauka da wasa ba. "Na biyu, muna da isassun hujjoji dake nuna mana cewa akwai masu san tada ƙayar baya akan Rukunin Jinzidal, nan bada daɗewa ba!!" "Na uku, akwai ƴan ƙabilar Djinn, waɗanda suma suke ƙoƙarin komawa garin Shaedníza da kuma ƙara yaɗa abubuwan da suka afku a wannan shekara, domin mutane suji. Kaga ta haka, tunda abin ya haɗa da Tirifil- fakta, mutane zasuyi ca akai, kaga tashin hankali zai afku." Wannan mutun mai suna Uznu'Ururu yaci gaba da bayani cikin mulki da isa da ƙarfin Izza. "Amma mafi muhimmanci akwai abinda nayi shekaru sama da ɗari tara ina nema. Kuma nayi duba izuwa taurari bakwai dake saman ƙasa ta farko. Wanda suka tabbarmin da cewa wannan abu da nake nemo zai bayyana a wajen wani yaro dazai taka rawa a wannnan gasa. "Duk waɗannan dalilai, su ne suka taso ni nazo wannan gasa. Da fatan kuma Denizawa zaku bamu haɗin kai domin kautarda asarar rayukan da ba dole ba." Yana gama jawabinsa, bai jira wata amsa daga sarki Deniz Iluru ba, kawai ya juya kai, idanunsa a rufe, ya kuma ci gaba da fuskantar filin fafatawar nan. Wato dai zaka iya cewa, koma sarkin ya yarda koma bai yarda ba, wannan shi ta shafa, domin a iya saninsa, su ma'abota Ururu, su na da ikon aikata duk abinda suka ga dama, kuma a duk lokacin da suka ga dama. Dama dai taƙarƙashin ƙasa, shima sarki Deniz yaji waɗannan abubuwa, cewa wani daga cikin manyanmanyan ƙusoshin duniyar ƙasa bakwai, yana so ya tada zaune tsaye akan Rukunin Jinzidal (wato cinikin bayi da ake.) Sannan kuma bayyanar Magajin Wilbafos, abu ne da kowa ya sani, amma ba'asan ko waye ba, duk da kuwa kusan kowa farautarsa yake. Sai kuma batun ƴan ƙabilar Djinn, wanda shi ne kaɗai sabon abu, a abubuwan da yaji. Sai dai kuma babban abinda ya ɗagawa wannan sarki hankali shi ne, da abu na ƙarshe da Uznu Ururu ya faɗa akan abinda yake nema. Wanda nan take Deniz Iluru ya shuga tunani akan ko menene. Hakan nema yasa tunda Sarki Deniz yaji wannan batu, ilahirin annurin dake fuskarsa ya ɗauke, kuma bai ƙara cewa komai ba. Hasalima daka ganshi zaka san idanunsa ne kawai acikin filin gasar, amma tunaninsa yana wata duniyar. Lallai yasan wani bala'I yana kan hanya. Badan komai ba sai dan girman ikon Uznu Ururu da ya sani. Koda kuwa acikin ma'abota Ururu yasan shi ɗin mutun ne mai darajar gaske. Tun bayan sanda ya zamanto mutun ɗaya daya dawo daga wancan fafatawa data faru a shekaru da dama da suka wuce. Wadda tayi sanadiyyar samun shi kansa Littafin-Takobin. Saboda haka zai iya turo wasu ma'abota Ururun ma dake ƙarƙashin ikonsa. To amma mai yasa yazo da kansa?? Kusan tunda manyan baƙi daga Banfiriya suka tsaya a kusa da Kiru, kuma suka ƙi tafiya, itama Nusi ta dawo, dukkanin ragowar waɗanda ke tafe da waɗannan mazaje ma'abota Izza guda huɗu suma sun sauko ƙasan. Wato idan ka duba zaka ga mutanen Maikironomada tare da Armad, mutanen Banfiriya da Kiru, Mutanen Infiriya da Niyashi, mutanen Hán, daga ƙasa ta uku tare da HánAmuru, sai kuma Denizawa waɗanda suka fi kowa yawa, dan sunkai kusan su goma sha biyu, a tattare da Deniz Bizaya. Saurayi ɗaya wanda babu kowa a tare dashi shi ne Ikenga! Kuma idan ka dube zaka san cewa kwata-kwata hakan bai dame shiba, hasalima ko a jikinsa, kawai kansa ne a ɗage yana kallon sama acikin matuƙar nutsuwa, tamkar wanda yake kallo wani abu da baya so ya wuceshi, ko kuma wanda yake karanta tafiyar taurari!! Ana cikin wannan yanayi ne, wanda kowa ke ƙoƙarin gayawa nasa abinda ya kamata yayi da kuma ƙara nuna musu muhimancin samun nasara, kawai alƙalin wasa ya sanar cewa, sarki Deniz Iluru ya bada damar a sanar da kowa kyaututtukan wannan shekara, abinda ya ƙara rikita wajen! Domin kowa yayi tunanin kawai kyautar bayi za'a samu kawai kamar yadda aka saba. To amma ga dukkan alamu gashi sarki Deniz Iluru ya ƙara wasu kyaututtukan. Amma wannan alƙalin wasa bai tsaya ɓata lokaci ba ya zayyana dukkanin kyaututtukan da suke akwai, kamar yadda sarki Deniz ya gayawa Uznu'Ururu. Jin waɗannan kyaututtuka yayi matuƙar hargitsa ƴan kallon gaba ɗayansu, kai bama su ba kaɗai, hatta waɗannan manyan baƙi dake tare da waɗannan samari shida saida alamun mamaki suka bayyana ƙarara a fuskarsu. Kai hatta Asifu dake cikin wannan waje yana tattauna al'amuran Izza da wannan Badenize, saida ya juya ya kalli Sarki Deniz cikin mamaki. Kai gaba ɗaya wannan taro, wanda idan ka lissafa, sama mutun dubu ɗari suna cikin wajen, amma saida aka shiga shiru na ƴan daƙiƙu kamar mutuwa ta gifta. Kai hatta masu kallo wannan gasa a sauran garuruwan Denizawa, suma saida suka shiga mamaki! Wataƙila mai karatu yana buƙatar ɗan ƙarin

Chapter 15 of 33