Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sake shi ta tsira, kodai taci gaba da riƙeshi su halaka tare. Amma ga dukkan alamu bata da niyyar sakarsa, koda kuwa wannan halitta zata cimmusu!! ''Hmmmm,'' yayi ajiyar zuciya, sannan kuma ya kalli idanun wannan budurwa wadda ke ta ƙoƙari iyakacin ƙarfin ta wajen zaroshi amma ina saurin wannan halitta yafi gaban misali tuni ta cimmusu. Tana kuma dab da taɓa jikin Armad! *** Shin kuna ganin zai yiwu, baka taɓa ganin mutun ba, amma kaji kamar ka taɓa ganinsa, harma kana tuno wasu abubuwa da suka faru a tsakaninku kamar a gaske??? Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos Dordor!! Wannan suna ne wanda jama'ar wannan zamani suka laƙabawa waɗansu halittu, waɗanda ba mutane bane, hasalima a zahiri fatalwowi ne. Sai dai kuma amma su na da irin sura ta mutane sak, in banda waɗansu banbance-banbance da suka raba. Girmansu ya haura na mafi yawancin mutane misali, tsaka-tsakinsu sune waɗanda girmansu yakai kimanin girman ƙarti biyu na mutane a haɗe. Kalar fatar jikinsu zata iya ɗaukar kowacce irin kala, kama daga kan baƙi, fari, ja, kore, shuɗi kai dama dukkan sauran launuka. To ɗaya dai daga cikin irin waɗannan fatalwowi ne, ya nufo Armad ta baya, da tsananin muguwar niyya taya halaka shi. Kuma shi ne wanda Hasanu ya gano yana tahowa tunda farko, kuma shi ne dai wanda Zahra/ Nostalgiya ta gani, lamarinda yasa take ta ƙoƙarin janyo Armad waje. A dai-dai lokacin da Armad ya waiwaya, sukai ido biyu da wannan fatalwa, mai suna Dordor, kamanninta suka shiga kwakwalwarsa. Nan take yasan cewa lallai a kowanne lokaci, mutuwa zata iyai masa sallama idan baiyi wani abu ba. Wannan Dordor dai daya Shuɗi ne gabaki ɗayansa; tun daga kan dogon gashin kansa wanda ke taɓo har tafin ƙafarsa, harya zuwa tafin ƙafar tasa komai shuɗi ne. Idan ka cire launin fatar jikinsu, wani banbanci da waɗannan fatalwowi suke dashi, idan ka haɗasu da mutane shi ne, adadin kawunan kowanne ɗaya a cikinsu. Duk da kasancewar yawanci waɗanda jama'a suke arba dasu, adadin kayikansu bai wuce ɗaya zuwa biyu ba, to amma akan gamu da masu kai uku a lokuta ƙalilan. Misali wannan shuɗin dake biye da Armad kansa ɗaya ne kurum, wanda hakan yasa yayi kama da ɗan-adam sosai, idan banda mahaukacin dogon gashin kansa da kuma shuɗiyar fatar jikinsa! Amma a zahiri da yawa daga cikin mutane sun san akan iya samun Dordor masu kai ɗai-ɗai har guda bakwai. Abin mamakin shi ne, watanni shidan ƙarshen kowacce shekara duk wata ƙasa dama duk wasu matafiya dake da burin yin tafiya akan Bangwayen ruwa guda biyu sai sun yi rijista, a wajen ma'abota Ururu, domin tafiya akan wannan ruwan. Hakan zaisa abasu shedar kariya daga waɗannan halittu masu laƙabin Dordor, wanda ta hakane kaɗai ake iya yin tafiya akan wannan bangwayen ruwa cikin kwanciyar hankali. A cikin littafin ''Halittun farko a duniya,'' da B. Zinariya ya wallafa, ya rawaito cewa, A farkon lokaci, al'ummar fulani mazauna yamma, sun yanke shawarar yin hijira zuwa gabas. Amma bisa ƙaddara akan hanyarsu ta tafiya, sun gamu da halittu masu firgici da dama, sai dai kuma mafi muni aciki, su ne waɗansu halittu da suka kira da suna Dódo. Karawar waɗannan fulani da waɗannan halittu shi ne ya zamo mafi munin abu da fulanin suka taɓa fuskanta. Domin abisa alƙaluma kafin su isa inda zasu je, sai da sama da biyu cikin uku, na jama'arsu suka salwanta. Bayan shekaru masu yawa, suka isa gabas. Amma sai suka ɗauki wata sabuwar al'ada ta rashin magana tsahon kimanin wata ɗaya, domin jimanta waɗanda suka rasa rayuwarsu a yayin wannan hijira. Bayan shekaru masu tsaho, zafin rashin da suka fuskanta yaɗan fara raguwa, ma'abota kwarewa ta fannin magana da salo wajen bada hikaya acikinsu, sai suka fara rubuta labarai domin fito da jarumtar mutanen nasu da suka fafata da waɗannan halittu, masu suna Dódo. A saboda haka kafin jimawa sunan Dódo ya bazu a sassa da yawa na duniya. Harma ya zamanto abin bawa yara firgici da tsoro; ''Wato idan yaro yayi abu sai kaji ance ya bari ko kuma a haɗa shi da Dodo." *** To wannan dai shi ne abinda yazo acikin wancan littafi. To da yake a gaba kaɗan acikin littafin anyi bayani akan su waɗannan halittu masu suna 'Dódo' da kuma siffofin su, waɗanda idan ka duba za kaga sunyi kama sosai dana waɗannan halittu da a wannan zamani, jama'a sukewa laƙabi da Dordor, to da dama daga cikin mutane su na tunani cewa akwai yiwuwar waɗannan halittun iri ɗaya ne ko kuma ƴan'uwan juna ne da waɗancan da suka fafata da fulanin a wancan zamani. *** Armad ya kalli idanun wannan budurwa ya kuma kalli irin yanayin yadda take ta ƙoƙarin kuɓutar dashi. Tuni har makarin fuskarta ya faɗi, amma duk da hasken dake tashi daga fuskarta ta bai hana ganin kwalla dake haɗowa acikin idanun nata ba. Armad bayan yayi ajiyar zuciya ya ɗaga ido ya ƙara kallonta, suka haɗa ido. Baice komai ba, ita ma kuma bata bashi amsa da komai ba, amma bayan wannan kallo guda ɗaya tak da sukai wa juna, Armad ya yanke shawarar cewa lallai bai kamata ya bari wannan budurwa ta halaka a wajen nan ba. Koba komai yana da buƙata ya tambaye ta yaji baki da baki, mai yasa yake jin cewa kamar ya taɓa ganinta, harma yana ganin waɗansu mu'amaloli da suka gudana a tsakaninsu. Waɗanda suke matuƙar kama da zahiri, amma kuma shi yasan a iya tunaninsa basu faru ba. To a dai-dai wannan lokaci tuni wannan shuɗin Dordor ya ɗaga hannunsa ya kuma kawowa Armad wafta. Wanda kuma a lokacin ne su Hasanu suka ƙaraso dab dasu. Idanunsu acike da rashin sanin yadda zasuyi, suka tsaya cirko-cirko akan Zahra. Kasancewar su na da cikakkiyar masaniyar cewa taɓa wanda Dordor ya taɓa tamkar taɓa Dordor ɗinne da kanka, wanda kuma hakan tamkar cakawa kanka wuƙa ne. Domin duk wanda ya taɓa Dordor, a take gaba ɗayan ruwan jikinsa ke ƙonewa! Saboda yana daga cikin sanannen ilmi a wannan zamani cewa ba'a taɓa Dordor da fata, saboda haka basu da damar taɓa wannan budurwa, a dai-dai wannan lokaci da take riƙe da Armad shi kuma Armad ɗin bai rage saura ɗan taƙi ba, tsakaninsa da shuɗin hannun wannan Dordor ɗin nan ba. To a wannan lokaci da kusan kowa acikinsu ya ɗebe haso a sannan ne abinda ko a mafarki basu taɓa kawowa zai faru ba ya faru ba. Wannan Dordor yana gab da taɓa Armad, a yayinda Armad ya fizge hannunsa daga hannun Zahra, ya guma zare takobinsa, sannan yana lilo akan iska ya juya ya kai sara ga hannun wannan Dordor da sauran ƙiris ya kama wuyansa. Koda ganin abinda ya faru, sai jikin Zahra ya fara karkarwa, ba tare da ta sani ba ma ta yunƙura da ƙarfin tsiya tare da miƙewa da niyyar riƙo Armad. Amma a dai-dai lokacin da take gab da faɗawa cikin ramin ne, su Hasanu da Kiru suka isa gareta, a inda Kiru yakai hannu ya riƙo ta, sannan kuma kafin kace meye wannan ya dawo da ita baya kuma a lokaci ɗaya duk su ukun suka yi tsalle sukai baya da sauri. Cikin daƙiƙa ɗaya tuni sun bada kimanin taku biyar tsakaninsu da Armad. To a sannan ne suka tsaya, sannan baki a buɗe cike da mamaki suka ƙurawa Armad ido. A baya basu samu lokacin mamaki ba, amma yanzu da suka ga sun ceto ƙanwar tasu wadda keta ƙoƙarin kwacewa daga riƙon da su biyun sukai mata, sai suka ɗan nutsu. A inda hatta Kiru da dakakkiyar zuciyarsa, saida ya sarawa Armad da irin jarumtar daya nuna wajan fuskantar wannan Dordor, gaba da gaba. Idanun Kiru suka ƙara kaɗawa da marmarin yaƙi babu abinda yake faɗa a zuciyarsa sai, ''kash! badan mutuwarsa tazo da wuri ba, ai daya taimaka wajan fiƙe takobi ta, domin ko badan komai ba ina son fafatawa da marasa tsoro irinsa.'' Shi kuwa Hasanu wanda ke riƙe da hannun hagun Zahra ƙam-ƙam magana yake aciki, ''hanzari ya kamata nayi na koma gida, na tabbatar da abinda nake kokwanto!'' Da yake tunda aka fara wannan fafatawar baice uffan ba, sai kawai nazari da kuma bibiyar abubuwa da yakeyi. Daga gefe kuma acikin abinda bai wuce daƙiƙa biyar ba, har Armad da wannan shuɗin Dordor, sunyi musayar sama da sara ashirin, a fafatawarsu a saman wannan rami. Duk da tsananin kyau kamar na ƴaƴan sarakunan manyan fararen aljanun farko, da kuma girman kai da ƙasaita da mulki irin ma'aboa maɗaukakiyar Izza, da Zahra take dashi, amma hakan baisa ta buɗe baki ba, idanunta cike da kwalla ta dubi Armad,kamar wani wadda take so ta bawa wanda zai mutu cikin ƴan daƙiƙu wasiya, amma ina takasa cewa komai. Nan take Kiru ya riƙe baki, yana mamaki; shi dai yasan irin buwaya da ƙanwarsa take dashi a fannin kyau da sarautaa dukkan faɗin ƙasa bakwai. Hasalima kusan ta kori sama da ƴaƴan manyan sarakuna goma, masu neman aurenta. Kuma tunda yake bai taɓa ganin ta nuna wani yanayi irin wannan ga wani ɗa namiji ba, komai kyansa, komai buwayarsa, kuma komai mulkinsa. Ballantana Armad, wanda yasan cewa koda ma wani ɗan babban sarkin ne, to yasan cewa bazai taɓa kama ƙafar manyan ƴaƴan sarakunan da suke neman auren ƙanwar tasa ba. Hasalima da dama zasu iya bayarda duk abinda suka mallaka, domin kawai rana ɗaya, sau ɗaya tak, ta riƙe hannunsu. Amma basu samu ba. Yana gama wannan tunanin, kawai abu ɗaya ya yanke acikin zuciyarsa, cewa LALLAI WANI ABU YA TAƁA AFKUWA TSAKANINSU; BANDA GAYA MANA DA TAYI TA CETO SHI DAGA CIKIN WANNAN GARI, LALLAI AKWAI WANI ABU, WANDA BAMU SANI BA! Can bayan wani lokaci kalmar kawai data fita daga bakinta ita ce, ''Ar...mad...'' A dai-dai wannan lokaci ne wannan Dordor ya buɗe bakinsa ya fesowa su Hasanu wani ruwa baƙi-ƙirin a dunƙule kamar ƙawanya daga bakinsa. Wanda kan kace meye wannan, tuni ya bayyana a gaban su Zahra, inda ya fara buɗewa yana ƙara girma tamkar wanda yake so ya haɗiye su gaba ɗaya. Kan kace meye wannan tuni wannan baƙin ruwa ya canja daga kimanin kamu ɗaya zuwa kimanin ɗaya. Bayanin yadda abubuwan suka faru zai ɗauki lokaci, amma yanayin yadda komai ya faru a zahiri baifi ƙiftawar ido da bismillah ba. Lallai duk wani mutum a wannan zamani yasan me wannan baƙin ruwa yake ƙunshe dashi, lallai yasan cewa ko mai za'ai kuma ko a bakin ransa to bai kamata ya bari wannan ruwa ya taɓa shi ba. Armad duk da bai taɓa arba da Dordor ba, amma yasan haka daga ilmin da yayi a rayuwarsa, su kuma waɗannan mutane uku dake wajen dukkansu ƴaƴan sarakuna ne, saboda haka sun san sarai mai hakan yake nufi. Armad bai san mai yasa ba, amma kawai yaji a ransa cewa bai kamata ya bari wannan budurwa ta halaka a wajen. Sannan kuma ya san cewa idan ya bari ta halakan, to lallai baya jin zai samu wanda zai iya bashi amsar abubuwan da yake so ya tambayeta. Kan kowa ya farga tuni Armad ya ɗaga takobinsa sama, ya numfasa a wani yanayi mai cike da yanke shawara, sannan ya saukarda saran takobin tasa da ƙarfin gaske gami da ambatar, ''Wilbafosiyan-Siwod-Dans!!'' Rufe bakinsa keda wuya wani haske ya fara feshi daga jikin takobin tasa, nan take komai ya tsaya cak; kama daga kan wannan baƙin ruwa dake gab da haɗiye su Zahran da kuma wannan Dordor dake biye da Armad zuwa ga dukkan ƙasar data rududduge. Wannan haske nan take cikin ƙiftawar ido yai matuƙar ƙaruwa ta yadda ya kashewa kowa ido, ko tafin hannu ba'a iya gani. Bayan kimanin daƙiƙa biyu hasken ya fara raguwa, kafin daga bisani ya ɗauke gaba ɗaya. Su Hasanu na tsaye inda suke, idonsu a gaba na ƙoƙarin karanta maiya faru. Abinda kuwa sukai arba dashi shi ne, babu alamun wannan baƙin ruwa, babu alamun shuɗin Dordor ɗin, sannan kuma bisa mamaki dukkan ƙasar da suke kai wadda da duk ta rududduge kuma su na gab da ruftawa ta dawo ta haɗe tamkar wani abu bai taɓa faruwa da ita ba. Dukkanin wannan abin mamakai ne da ban al'ajabi a garesu musamman ganin ƙasar da da ta riga ta rududduge ta kuma zaizaye, amma yanzu kuma ta dawo ta haɗe tamkar babu abinda ya taɓa samunta. To amma wani abu guda ɗaya daya fi ɗugunzuma hankalinsu sama da komai shi ne rashin ganin Armad ko sama ko ƙasa! Bayan ganin wannan fasaha da Armad yai amfani da ita, Hasanu ya ƙara samun nutsuwa kan abinda yake kokwanto, lamarinda ya ƙara sawa yaji akwai buƙatar ya koma da Armad garinsu maimakon kashe shi, duk da kuwa Armad ɗin yaji sirrin su, SIRRIN DAZAI IYA RIKITA DUNIYA BAKI ƊAYA. Shi kuwa Kiru, marmarin yaƙi ne kawai ya ci gaba da kaɗawa a idonsa, yana jin cewa lallai Armad ya isa su kara dashi. Ita kuwa wannan budurwa kana ganinta zaka san tana cikin jimami da ɓacin rai, saboda badan hannun Hasanu dake riƙe da ita ba, da tuni ta faɗi ƙas!! *** Wai me Hasanu yake kokwanto akan Armad, harda yasa ya fara ƙoƙarin fasa kashe shi? Anya kuwa babu wani abu daya faru tsakanin Armad da Nostalgiya, wanda bamu sani ba, wanda kuma shima bai sani ba, wanda kuma ga dukkan alamu ita kaɗai ta sani? Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 12: Ururu Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . . K wanaki huɗu bayan ɓacewar Armad bayanda yayi amfani da wannan hatasabibiyar hanya ya ceto su Zahra daga wannan baƙin ruwa da shuɗin Dordor ya harba musu. Zahra tayi shiru su na tafiya bata kuma yiwa kowa magana ba tun bayan tahowar tasu, duk da kuwa ƙoƙarin kwantar mata da hankali da Hasanu yayi tayi, kai hatta Kiru ma da ya nuna aniyarsa a fili ta so ya halaka Armad a baya, sai da ya sauko ya kuma fara lallamar Zahran yana gaya mata cewa shi dai bai gane mene ne a tsakaninsu ba, amma koma mene ne ta gane cewa, Armad ba irin mutanen da zasu mutu cikin sauƙi ba ne, ya kuma gaya mata da Armad ɗin zai iya mutu da wuri aida tuni ya rigaya ya halaka shi da farar takobinsa. Ya gaya mata hakan ne da wasa duk da niyyar ko zata ɗan saki fuska, amma ina ko kaɗan bata ma nuna ta jishi ba, idanunta kawai na nuna nutsawa acikin tsananin tunanin wani abu ne kawai. Tun da farko bata yarda sun baro wajan ba sai da suka kwashe awa ashirin da huɗu cir, tana kallon wajan da Armad ya ɓace. Babu yadda Kiru bai ba akan ta gaya masa menene tsakanin ta Armad ɗin ba amma bata ce komai ba, ”ba kamar ke ba, bai dace dake ba, ki faɗa cikin wannan yanayi ba, duk ina taƙamar ki da ji da isa ta tafi kuma yau. ”Ca nake gab da zamu taho kika ƙara korar ɗan sarkin Liha ba, wanda kuma shi ne na bakwai a layin ƴaƴan sarakunan da kika ƙi. ”Ji nake ke inba Yarima Deniz Bizaya ba sai rijiya!!” To haka irin waɗannan maganganu suka ringa fita daga bakin Kiru duk dan ya saussauta mata ƙuncin da yaga ta shiga. Wanda a gari banza ko mai zata bashi ba lallai ma taga dariya a fuskarsa ba, ballantana ma ya tsaya yana yi mata irin waɗannan maganganu. Amma saboda ganin halin da take ciki ya yanke shawarar hakan. To! Haka dai ya ci gaba amma ko a jikinta, inda daga ƙarshe ya gaji ya rabu da ita kurum, ya koma wajan Hasanu wanda ke kan dokinsa samfurin Kili, shima ga dukkan alamu akwai abinda ke damun zuciyar sa, domin ya natsa matuƙa a cikin tunani. To haka dai suka tashi suka nufi hanyar Sisiya akan dawakansu, inda suka shafe kwanaki uku su na tafiya. Kuma a wannan lokaci tafiyar data rage tsakaninsu da garinsu mai suna Sisiya, bata fi ta sati biyu ba. Kiru wanda ke tafiya a dama da Zahra, Hasanu kuma a hagu, inda saka ta a tsakiya, yai firgit ya ɗaga kai, kana ya dubi Hasanu idanunsa cike da kokwanto. Shima Hasanun kamar yasan abinda yake tunani ya ɗaga kai ya dubeshi. Su na haɗa ido Hasanu bai jira wani abu ba ya fara tambayar Kiru, ”dame-dame ka lura dasu a tattare da wancan yaro waɗanda baka fahimta ba?” Kiru yaɗan ƙifta ido kasancewar tambayar ta tabbatar masa da abinda yake zato na cewa lallai Hasanun yasan wani abu a tattare da Armad. Saboda haka bai tsaya ɓata lokaci ba, kawai ya numfasa ya fara bayani, ”na kula da abu biyu!” Ya ɗaga ɗanyatsansa na hagu guda ɗaya yana nuni da ɗaya. ”Na farko na lura ya iya tsaiwa akan iska,” ya ɗan dubi Zahra kamar wanda yake jira tace wani abu, kafin daga bisani ya ƙara ɗaga yatsunsa guda biyu sama sannan ya ci gaba da bayani, ”Na biyu shi kansa bai san cewa yana da wannan Izza ba ta iya tsayawa akan iska ba, badan komai ba sai dan cewa da fari yayi ƙoƙarin miƙa hannu domin ya riƙe tsandauri dan ya kuɓuta daga faɗawa ramin kamar yadda nima nayi, inda ba daban Zahra ta riƙoshi ba to da akwai yiwuwar ya faɗa ya mutu batare da ya taɓa gano cewa yana da wannan Izza ba.” Koda Kiru yazo nan a zancensa sai yai shiru ya kuma kalli ƙasa kamar mai jimanta wani abu, kafin can daga bisani ya ɗago kai ya ƙara fuskantar Hasanu, wanda ya taddashi yana kallonsa shima. Bayan ɗan jira da bai wuce na daƙiƙa biyar ba, Hasanu ya numfasa ya tambaye shi, ”wannan su ne abubuwan da kafi lura dasu?” Kiru ya kyaɗa kai alamun eh. ”Eh to! Ba komai ina ga kayi ƙoƙari, amma kamar kullum yadda nake ƙara gaya maka, yadda kake maida hankali akan horonka na takobi haka ya kamata ka ƙara maida hankali akan karatu ma, badan komai ba sai dan ka ƙarawa ƙwaƙwalka ƙarfi ita ma.” A dai-dai wannan lokaci fuskar Hasanu ta nuna alamun muhimmancin maganar da yake yiwa Kiru da kuma sonsa da ace Kirun ya ƙara maida hankali wajan karatun da yake gaya masa. Bayan ya kalli farar takobin Kiru na lokaci sai ya ɗauke idonsa daga kan Kirun ya kuma fuskanci gabansa inda ya fara jawabi, ”tunda farko da naga wasu abubuwa hankali na ya fara ɗugunzuma, lamarinda yasa na sa masa ido. ”Amma bani da wasu cikakkun hujjoji, wanda hakan ne yasa na ci gaba da bin abubuwan da suke faruwa tsakaninku ba tare da na shiga ba, abisa tsammanin hakan zai kaini ga gano abinda nake tunani. ”Kaga dai abu na farko… shi ne wannan jan ƙyalle dake ɗaure a gaban goshinsa na musamman ne. Haske baya shugewa ta cikinsa, saboda haka indai baka fasaha ta musamman ko kuma ido na musamman baza ka iya ganin mene ne a bayansa ba.” Kiru wanda ke sauraro ya ɗaga kai cikin mamaki ya kalli Hasanu, ”kyalle kuma??” Hasanu ya ƙara numfasa wa sannan ya ce, ”ba kyallen bane abin daya ja hankali na sosai bama! ”Abunda kyallen ke rufe dashi. Domin ina kyautata zato, indai ba rafkanwa na samu ba, to lallai akwai irin wannan Miyura da akewa laƙabi da ‘Miyura Yinfinita’ ko kuma ‘Miyura Madauwamiya’, wadda bata taɓa ɓacewa tun daga sanda aka haifi mutum har mutuwarsa, maimakon kwana bakwai data kowa take ta ɓace. ”Kamar yadda ka sani abu ne mai tsananin wahala ka samu irin waɗannan mutane, kai harma yafi wahala ka samu raƙumi acikin kuratandu da ka samu irin waɗannan mutane musamman ma a wannan zamani. ”Wanda har yakai kawai mutane da dama suna tunanin kawai dai labaru ne irin na hikayun gizo da ƙoƙi kurum. ”To amma mu da muka fito daga Burja, munsan cewa yana daga cikin ɗaukakar shugaba Ibasi Burja, Jinnnafarko irin wannan Miyura. ”Abu na uku wanda shi ne mafi muhimmanci, shi ne wannan fasaha da yayi amfani da ita ta ƙarshe!! ”Har yanzu dai bazan iya cewa ina da kaso ɗari na tabbashi ba, amma lallai nafi kaso saba’in. ”Cewa na taɓa ganinta acikin wannan littafi na Jána Sisiyu.” Tuni Kiru ya shiga cikin ruɗani da zuciyarsa saboda abubuwan duk daya ke ji, abubuwa ne da duk da baya son bincike da karatu amma yasan tarihin Ibasi Burja wanda shi ne ma ya kafa kusan gaba ɗayan daular Banfiriya, mutumin da akewa laƙabi da Jinn-nafarko, inda daga baya ma aka kafa sabuwar ƙungiya da suka sakawa sunansa. Kuma sannan yasan littafin Jana Sisiyu! Kuma yana da cikakkiyar masaniyar manufar maganar da Hasanu yake yi!! Saboda haka ya shiga wannan ruɗani. Hasanu yai kyaran murya sannan ya ƙarasa zancensa da cewa, ”to koma dai meye, yanzu abu biyu ne suka rage mana; na farko dole ne muyi sauri mu ISA Sisiya, domin mu isarda wannan babba sirri da muka gano ga Shugaba!” Ya na faɗar haka ya waiwaya gefe ya kalli Zahra, domin yasan cewa wannan sirri, yana cikin kanta, tun bayan da ta karanta zuciyar Armad ta zaƙulo shi! “na biyu kuma,” ya juyo izuwa Kiru gami da ci gaba da bayani, “zarar muka isa Sisiya, DOLE NE ASAKA MANYA-MANYAN MA’ABOTA IZZA SU BAZAMA SU NEMO WANNAN YARO MAI SUNA ARMAD, duk inda yake a duniya, ko shi ko gawarsa!!” To a dai-dai lokacin da suka kammala tattaunawar tasu kuma suka dubi gabas, Zahra wadda kwanaki huɗu kenan cir bata ce komai ba tun bayan sanda ta kira sunan Armad, ta buɗi baki, kanta a sunkuye tayadda baza a iya tantancewa ko hawaye take ko kuma ba hawaye take ba, ta furta wata kalma guda ɗaya. ”Shi ne!!” Cikin mamaki duk su biyun sukai saurin juyawa izuwa gareta bakinsu a buɗe, kai daka gani kasan cewa magana ce mai yawa a bakinsu. Amma duk su biyun babu wanda ya iya furta wani abu bayanda suka ga yanayin ɗimuwa dake fuskar Zahran, lallai sun san cewa yi mata magana a dai-dai wannan lokaci bashi ba ne mafi kyawun abinda zasuyi ba. Saboda haka suka haɗiye abinda ke ransu suka ci gaba da tafiya ba tareda kowa yace ƙala ba. A haka su na tafiya su na yada zango, saffa-saffa har suka ƙara cinye wata tafiyar ta kwana uku. To a wannan rana su na tafiya suka iso cikin wasu manyan duwatsu masu yawan gaske, sannan kuma ga girma ta yadda kana gani kasan cikinsu zaiyi daɗin fakewa akai harin sunƙuru. Koda zuwansu nan, sai Hasanu ya bada umarnin su kwana anan in yaso da sanyin asuba, saisu shiga cikin duwatsun ido na ganin ido. Haka kuwa sukai, inda suka kafa tanti sannan suka kwana, asubahin fari suka ɗaura ɗamara suka shiga cikin wannan duwatsu. Abu na farko da suka fara arba dashi shi ne sauyin yanayi, inda su na taka ƙafa ciki ɗan hasken daya fara fitowa na asuba suka ga ya dusashe nan take, wani duhu na musamman ya maye gurbinsa. Sannan kuma suka fara jin wata iska mai sanyin gaske tana dukan fuskarsu. Kafin zuƙatansu su gama ankarewa da wannan sabon muhalli suka fuskanci wani sabon firgici. Inda suka fara jin wata kakkausar murya daga cikin dajin duwatsun na tasowa, ”kwamanda na biyar na rundunar tsakiya daga Burja, Hasanu! ”Ance yiwa ɓarawo sata bashi ce. ”Ba komai nake magana ba illa AYRID mai mataki na shida dake hannunka!! ”Ku bamu ku tsira da ranku, ku hanamu, mu kasheku sannan kuma mu ɗauka da ƙarfin tsiya.” *** Ururu A tsohon yaren Aldúrish, kalmar Urú tana da ma’ana biyu; ta farko tana nufin baƙin abu, yawanci ana amfani da ita ne, a abinda yake da alaƙa da jikin ɗan adam, sai kuma ma’ana ta biyu, wato adalin shugaba (yawanci mara dukiya da yawa.) Shekaru aru-aru da suka gabata (Before Amri, B.A), al’ummar wata tsohuwar ƙabila wadda babu wanda yasan asalinta a dukkan wannan zamani suka bayyana da wani abu sabo. Wanda ba’a saba gani ba; wato gabaki ɗayan idanuwansu baƙaƙe ne, baƙi ƙirin, babu ko alamar fari acikinsa. Saboda haka, sai mutanen wannan zamani suka fara kiransu da suna Uru. To amma, ga dukkan alamu wannan suna baiyi musu daɗi ba, saboda a cewarsu, lallai akwai ƙololuwar rashin kyautawa a ringa kiransu da kalmar da zata iya ɗaukan ma’anar sarki adali mara dukiya. Acewarsu wannan zagi ne ga buwayarsu da ƙarfin mulkinsu aban ƙasa. Saboda haka, ba jimawa aka maida wannan suna ya koma Urúrú, wato aka ƙara ‘rú’ a ƙarshe. Wanda ma’anar sunan ta baƙaƙen idanu amma na manyan sarakunan aljanu masu ƙololuwar girman kai waɗanda suka taɓa mulkar duniya, waɗanda kuma aka ce saboda tsananin girman kansu aka shafesu daga ban ƙasa. Domin kalmar ‘Rú’, indai anyi amfani da ita, to ana nuni da waɗancan aljanu ne. Wannan ƙabila sun daɗe suna mulkar bil-adama, babu zamani da yazo da bai tafi dasu ba, hasalima a dukkan littafan tarihi saika gansu, wanda hakan yasa mutanen wannan zamani da dama suke tunani kodai dama wannan duniyar tasu ce su kaɗai. Sunga jiya, sunga yau, kuma ga dukkan alamu babu abinda ya isa ya hana suga gobe. Su suka ƙirƙiro da Amri, kuma su suke da yaren Aldurish, sannan kuma su suke tsarawa dukkan mazauna ƙasa bakwai tsarin rayuwarsu, a wata hanya da suke cewa Rukunan Urúrú! Sudai waɗannan Rukunai, guda uku ne asali, amma daga baya saboda wani dalili da ba’asan ko menene ba, suka goge Rukuni na uku, ya dawo saura rukunai biyu kawai. Rukuni na farko, shi suke kira da Jinzidal! Yana magana ne akan yadda mutane zasu yi rayuwarsu, cewa dukkan mutane sai sun zama iri biyu. Kaso na farko sai sun zama Bayi, wato su aikinsu bauta kawai! Na biyu kuma su ake kira da Béligi, waɗanda su kuma aikinsu yaƙi. A ƙarƙashin wannan tsari, duk shekarar duniya sai anci gagarumar kasuwar cinikin bayi, wadda akeyinta a bisa tsarin da ake kira da suna Jinzidal. *** Jinzidal shashi ne mai zaman kansa acikin wannan littafi, wamda za’a zo kansa na bada daɗewa ba. Inda zaku ji yadda Ururu suka ɗaurewa cinikin bayi gindi. *** Shi kuwa rukuni na biyu, shi ake kira da Izza Ristirikta! A ƙarƙashin wannan tsari, dukkan wani ɗan adam dake rayuwa abisa doron ƙasa bakwai, idan ka cire ƴan ƙabilar Ururu, saiya karbi jarrabawar daga Ururu, idan dai yana so ya haura daga matakin Izza na ɗari zuwa sama. Haka daga na ɗari biyu zuwa sama, haka haka, wato duk bayan shekaru ɗari na Izza, sai ka karɓi wannan jarrabawar kafin ka wuce gaba. Wannan jarrabawar ba wani abu bane illa, Ruwan wuta da za’a saukar maka daga doron ƙasa ta farko kai kaɗai. Idan ka wuce shi ka rayu, to kaci wannan jarrabawa, amma idan ka mutu shikenan. Kuma duk bayan mataki ɗaya, wahalar daɗa ƙaruwa take. Wanda hakan nema yasa kaɗan ne suke iya ci gaba da ƙarawa Izzarsu yawa zuwa wani mataki, indai kai baɗan ƙabilar Ururu bane. A ƙarƙashin wannan Rukuni akwai abubuwa da dama, waɗanda Ururu ke amfani dasu wajen tabbatarda cewa babu wani mahaluƙi daya kuɓucewa wannan jarrabawa. Wannan abubuwa za’aji su anan gaba kaɗan. *** Wannan shi ne kaɗan daga cikin girman iko da Ururu ke dashi a ban ƙasa a wannan zamani. To wannan sirrin dai da Armad yaji a wajen su gimbiya Nostalgiya, yana da alaƙa da rukuni na farko, wato Rukunin Jinzidal (cinikin bayi), dama kuma wani ɓangare na Rukunin Izza Ristirikta. Sabida haka, ko’a wannan lokaci da iska tayi cilli dashi zuwa wata duniyar, kafin hankalinsa ya gushe abinda ya fara faɗo masa kenan. Lallai yasan cewa akwai babban tashin hankali, koma kuma mummunan yaƙi dake gabatowa indai aka aiwatar abinda yaji. To amma mai ya kamata yayi? Wannan ita ce tambayar daya kasa bawa kansa amsa. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 13: Wacce shekara muke Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Magajin Wilbafos Babi na sha Uku 13: a Wacce shekara muke wannan Marubuci:- Dr Abdullahi Muhammad Posts by Shuraih Usman Daga:- Taskar Magajin Wilbafos . T un bayan ɓacewar Armad daga wannan waje, hankalinsa ya dusashe ta yadda shi kansa bayan farkawarsa bai san a inda yake ba, bai san kuma tayadda yaje wajen daya farka ya tsinci kansa ba, sannan kuma bai san kwana nawa yai ba, tun bayan dusashewar hankalinsa ba. Amm abu ɗaya da yake iya tunawa

Chapter 7 of 33