Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba." Armad najin tambayar ya tuno abinda Babara ya gaya masa akan yayarsa Hidaya wadda ke can tana yaƙar aljanu a wata duniya ta daban. Lallai kuma haka ne, tunda sai kana ganin abu zaka iya yaƙarsa. Armad ya girgiza kai alamun bashi da amsa, inda Babara yaci gaba da cewa, "To wannan shi ne dalilin da yasa na gaya maka cewa cikakken ma'aboci Izza bada idonsa yake gani ba. Kuma horonka na farko zai fara daga wannan." Babara na faɗar haka ya tsaya a tsakiyar dusar ƙanƙarar nan tare da kirawo waɗandu ɗalasimai a zuci, lamarinda ya bayyanarda aljaninsa. "Zaka fara horo da aljanina mai suna Ji-Inara." Aljanin ya kasance jinsin muridi, yana da farar haɓa doguwa da koren gashi wanda ya futo akan ƙahonsa guda ɗaya. Hannayensa kuwa ƙananu ne ƴan gajeru kamar na jariri sabuwar haihuwa. Amma ƙafunsa sunkai tsayin zira'i sittin. Yana sanye da farar alkyabba ta ƙasaita, kana ganin yadda yake ɗaukar kansa kasan wannan aljani yana ji da kyau. Koda rufe bakin Babara sai aljanin ya rusuna tare da miƙa gaisuwa. Sannan kafin ya ɓace wani ƙaton al'amudi ya bayyana a hannunsa. Babara ya numfasa ya ce, "Kada ka damu, bazai kashe kaba amma zaka sha wahala. Kayi duba izuwa Tsarin- ruhinka, yanayin me kake ji idan ka kalli Izzarka? Armad ya girgiza kai yana cewa, "ba wani yanayi da nake ji." Babara ya ce, "a'a dai ƙara dubawa da idon basira." Armad na niyyar cewa a'a amma wata zuciyar tace ya duba. Saboda haka ya rufe idonsa yayi duba izuwa Tsarin- ruhinsa inda yai tsinkaye da abubuwan nan guda uku: Izza da takobi da kuma wannan mutun-mutumi mai idanu ruwan ƙasa wanda shi ne a matsayin aljanin Armad da Uznu ya kashe. Armad ya maida hankalinsa akan Izzarsa domin jin wannan irin yanayi Babara yake faɗa amma baiji komai ba. Yana niyyar buɗe ido ya bayyanawa Babara sai yaji wata iska mai zafin gaske na tashi a hankali daga inda izzarsa take. Nan take ya fara mamakin shin dama wannan iska tana nan ne ko kuma yanzu ta bayyana, domin kuwa dai bai taɓa ganinta ba. "Naji iska mai zafi na tashi." Babara yai murmushi tare da cewa, "wannan iska ita ce yanayin Izzarka. Kayi sani cewa akwai yanayin izza da dama. Amma wanda aka fi sani sune yanayin zafi, yananyin hunturu, yanayin kaka, yanayin rani, da kuma yanayin damuna. Kamar kai kana da yanayin zafi ni kuma yanayin rani ne dani. "Irin wannan yanayi da kake ji ajikin shekarunka na Izza shi zaka yi ƙoƙari kaji ajikin wannan aljani nawa tunda baza ka iya ganinsa ba. Zan tafi nayi bincike akan sharrikan dake cikin wannan kurkuku da kuma hanyoyin da zamu iya ficewa, kai kuma zaka tsaya anan ka koyi jin yanayin Izza da aljani na Ji-Inara." Armad ya kyaɗa kai tare da amincewa. Lallai yasan cewa ba ƙaramin ƙarfi zai samu ba idan ya koyi wannan al'amari na Izza, domin hakan na nuna cewa zai iya faɗa da mutun ko aljan koda kuwa idanunsa a rufe suke. Indai zai iya jin Izzar dake jikinsu yadda yake jin Izzar dake jikinsa to lallai koda baya ganinsu zai iya sanin inda suke da kuma motsin da suke da kuma yadda zasu yi motsin. Ta haka babu wani abu da zai ɓoye masa. Armad na cikin tunani Babara ya ɓace ya barshi da aljani Ji-Inaru. Koda ganin haka sai aljanin yai dariyar mugunta tare da ɓacewa. Abu na gaba da Armad ya sani shi ne saukar wannan al'amudi a bisa doron kansa, ba tare da yasan daga ina ba. Ƙarfin dukan ya tayarda iska wadda tayi cilli da Armad cikin dusar ƙanƙara. Yana tashi yaga jini na tsiyaya daga cikin kansa. Babu aljani Ji-Inaru babu alamunsa. Kafin Armad ya gane maike faruwa yaji wata gudumar ta sauka a bayansa. Nan take yaji wata ƙara mai nuni da cewa bayansa ya ɓalle. Ba shiri ya zare takobi ya fara kai sara ko'ina da ina amma a banza, ko sau ɗaya bai samu aljani Ji-Inara ba. Baya ganinsa ballantana yasan inda yake. Nan take Armad ya gane haƙiƙanin abinda Babara yake so ya koya. Inda ya rufe idonsa ya kuma yi ƙoƙarin jin yanayin Izzar dake tashi daga jikin aljani Ji-Inaru. Armad baiji komai ba a karo na farko, lamarinda yasa ya ƙara karɓar wata gudumar. Koda Armad ya tabbatar aljanin nan baida imani kuma zai iya karairaya shi indai baiyi da gaske ba, saiya ƙara zage damtse. A kwana na goma bayan kimanin kowanne ƙashi na jikinsa ya ɓalle sau kamar biyu sai kwatsam Armad yaji wani abu mai kama da ruwa sanyi yana tunkaro shi ta ɓangaren dama. Nan taje yakai sara ɓangaren. Ai kuwa nan take yaji ya daki ƙarfe, saiga al'amudin aljani Ji-Inaru ya bayyana. Armad yai ihun murna tare da ƙara rufe idonsa, yana neman wannan yana yi. Amma kawai sai ji yayi al'amudin ya ƙara sauka a kansa. Amma duk da haka Armad baiyi ƙasa a gwiwa ba, ya tashi tare da ci gaba da neman wannan yanayi na Izzar aljanin. A haka dai Armad yai ta fama, wani lokacin yaji wani lokacin yasha tafka har saida ya gane haƙiƙanin mai ake nufi da jin yanayin Izza. A haka saida Armad yai wata uku yana faɗa da wannan aljani kafin Babara ya dawo. Lokaci lokaci aljanin zai bayyana ya tausayawa Armad tare da koya masa abu ɗaya ko biyu akan Izza kafin ya ƙara ɓacewa yaci gaba da tafkarsa. Ba jimawa Armad ya gano cewa wannan aljani Izzarsa ce mai wannan yanayi na hunturu. Ana haka sai Babara ya dawo, ai kuwa abu na farko da Armad yayi shi ne fara jin yanayin Izzarsa inda yaji ta da yanayin kaka, gab da saukar damuna. "Lallai kayi ƙoƙari." Babara ya ce cikin farin ciki. "Na gano mana hanyar fita, amma lallai saika farkarda fasaharka zamu iya wannan aiki. Saboda haka yanzu abu na gaba shi ne farkarda fasaha." Armad yai murmushi tare da cewa, "muje zuwa." *** Sanarwa: Zamu fara chapter kullum amma duk chapter da comments basu kai 30 ba ba lallai nayi post ba washe gari ******* Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 79: Magajin Wilbafos Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos *** Tuni Babara ya zaunar da Armad a tsakiyar wani hatimi, a ƙoƙarin farkarda haƙiƙanin fasahar Armad. Armad na zaune ido a rufe, wasu ɗalasimai na haske suna kewayashi. Lokaci yaci gaba da tafiya a haka. Tuni hankalin Armad ya gushe babu abinda yake gani acikin kansa sai haske. Ana haka wannan ɗalasimai suka fara cinye ƙasar dake kewaye da Armad. Ba jimawa sukai wani ƙaton rami mai kama da rijiya, inda Armad ya rufta ciki. Amma duk da haka Armad bai buɗe idonsa ba. Daga nan sai kawai wannan ɗalasimai suka kama da tsawa da walƙiya wanda suka juye izuwa aradu. Ba jimawa wannan aradu ta fara cinye jikin Armad. Armad na zaune ko motsi baiyi ba. Hasalaima tamkar ba jikinsa ke ƙonewa ba. Ƙafafunsa ne su suka fara cinyewa izuwa toka, sannan sai gangar jikinsa, kafin daga bisani hannayensa da wuyansa da kansa. Armad ya ƙone ƙurmus acikin wannan rijiya amma ko tari baiyi ba. Shima Babara na zaune a wajen rijiyar bai motsa ba. Anma duk da haka wannan ɗalasimai masu bada walƙiya da aradu basu tsagaita ba. Hasalima juyewa sukai izuwa launin ja, sannan nan take walƙiyar ta fara tsiri tana sama har saida ta taɓo sararin samaniya. Ba shiri wani baƙin hadari ya taso mai ɗauke da aradu launin ja. Samaniya ta fara rugugi tana kaɗawa tamkar za'a saukar da ruwan azaba. Amma duk da haka Babara bai motsa ba. Nan take ruwa ya ɓarke tamkar da bakin kwarya. Duk bayan daƙiƙa biyar sai aradu ta sauka mai ƙarfin gaske. Ba jimawa wannan ruwa ya fara haɗuwa zafin aradun dake sauka suka fara narka wannnan dusar ƙanƙara data cika wannan kurkuku. Kwana uku cir aka ɗauka ana zabga ruwa kafin dukkan wannan ƙanƙara ta narke. Wannan kurkuku ta bayyana a fili. Ashe acikin wannan dusar ƙanƙara manya-manyan duwatsu ne na wuta wanda aka fafake cikinsu akai gidaje. Kana ganin wannan gidaje zasu tuna maka da ƙissar samudawan farko irin wanda akan bayyanasu da cewa suna ɗumamen safe da zafin rana. Waɗansu halittu ne sanye fatun namun dawa suka fara ambaliya daga cikin wannan gidaje na dutse da wani irin sauri tamkar na aljanun farko. Kafin ƙiftawar ido da bismillah sama da wannan halittu dubu uku sun bayyana sun kewaye Babara a inda yake zaune. Ga dukkan alamu ya tayar dasu daga baccinsu. Fuskokinsu a rufe suke da fatar farin zaki amma hakan bai hana tsananin ƙiyayya dake tashi daga cikin idanuwansu bayyana ba. Wata irin iska mai ɗauke da marmarin yaƙi na fita daga jikinsu. Sannan suna bada gunji mai amo kai kace samarin kuraye ne. Sahu-sahu sukai tare da tunkaro Babara a inda yake zaune, lallai babu ko tantama niyyarsu suyi watanda da naman Babara. Matsalar ɗaya na bayan ba lalle su samu ba. Amma duk da haka Babara bai motsa ba. Idanunsa na cike da imani da dogaro da fasahar da Armad Wilbafos zai farkar. Ba jimawa tokar naman jikin Armad ta fara haɗewa tana curewa waje ɗaya acikin wannan rijiya wadda tuni ta cika da ruwa. Ba jimawa wata tsawa ta sauka acikin rijiyar wadda ta ƙone duk ruwan dake ciki. Babu abinda yai ragowa acikin wannan rijiya sai tokar Armad. Ana haka wannan toka ta juye izuwa siffar Armad Wilbafos. Armad yai wani gunji mai firgitarwa wanda yasa dukkan wannan halittu jada baya. Wani taku irin na jaririn aljani ya fara fitowa daga cikin wannan rijiya. Inda daga bisani sabon saurayi ɗan kimanin shekaru sha tara ya bayyana daga cikin wannan rijiya, a jikinsa babu komai sai ɗan bante. Yana bayyana Babara ya buɗe ido tare da miƙewa ya kawo gaisuwa. Koda ganin haka sai waɗannan halittu suka fusata tare da rabuwa izuwa gida uku. Kaso na farko suka ɗaga hannunsu sama, inda wasu masu, masu ci da wuta suka bayyana. Kaso na biyu kuwa bakunansu suka buɗe, inda suka fara yin aman ruwan narkakken dutse wanda zafinsa zai iya ƙona wuta ita kanta. Kaso na uku kuwa wani baƙin ruwa ne ya fara ambaliya daga hannayensu, idan da Armad yana gani zai gane ruwan irin ruwan da Dordor suke amai ne. Dukkaninsu sukai ƙaraji tare da sakar wannan hare-hare izuwa Armad. Babara yai tsalle da niyyar shiga tsakani amma Armad ya ɗaga masa hannu. Ba shiri Babara yai gefe. Lallai koda aljanun farko sai sun tsorata da wannan hari na wannan halittu, wanda ke ɗauke da tsantsar rashin imani. Domin kuwa idan ka kalli samaniya zaka ga masu, masu cida wuta sama da dubu, haɗe da guma- guman ruwan narkakken dutse sama da dubu, tare da wani baƙin ruwa mai alamun mutuwa. Kuma abu na farko da zai fara zo maka shi ne waɗannan hare-hare ana niyyar halaka gari ne dasu, babu wanda zaiyi tunanin wai mutun ɗaya ake so a halaka. Armad ko gezau baiyi ba, hasalima ko motsa ɗan-yatsa baiba. Yana tsaye waɗannan guma-guman azaba suka saukar masa. Wata ƙara mai firgitarwa ta tashi, sannan ƙura ta turnuƙe. Lallai ko wanda ke tsaye kimanin nisan tafiyar shekaru dubu zai iya jin wannan ƙara, kuma zai iya ganin wannan ƙura. Babara yai ƙaraji saboda ɓacin rai ya afka cikin wannan hargitsi domin ceto Armad. Amma ba jimawa yaji wani irin yanayin Izza mai firgitarwa irin wanda bai taɓa ji ba a duk tsahon shekarunsa. Ba shiri ya fara jada baya kaɗan da kaɗan kafin wannan yanayin izza ya ƙara dukansa, lamarinda yasa ya harɗe tare da faɗuwa a ƙasa. Haki sarkin duba Babara ya fara, badan komai ba sai dan saboda ƙarfin izzar da yake ji. Amma waɗannan halittu basu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙara fara shirin wani harin. Sai dai a wannan karan girman kaba'irar da suke nufin Armad da ita ya ƙaru. Domin kuwa kowa acikinsu girman harinsa ya ƙaru da sama da sau uku. Suna niyyar afkawa Armad sai ƙura ta lafa inda surar Armad ta futo fili. Sai dai ina, kwata-kwata ba irin Armad ɗin da aka sani bane. Babu komai a jikinsa face walƙiya. Amma abin mamakin bawai irin yanayin walƙiyar dake kewaye Armad bace a lokacin da yake amfanin da ɗalasimai irinsu Kaban'shisu. Wannan walƙiyar daga cikin tsoka da jinin Armad take. Hasalima zaka iya cewa naman jikin Armad ne ya juye baki ɗaya izuwa gundarin walƙiya. A wannan lokaci Armad ya zare wani mashi wanda ya nutse acikin ƙirjinsa. Amma babu komai ajikin mashin daya shafi jini ko fatar ɗan-adam. Lallai a wannan lokaci zaka iya cewa Armad wilbafos ya zama walƙiya, walƙiya kuma ta zama shi. Armad ya ɗaga hannusa sama ya dubi gundarin walƙiyar data haɗa hannunsa. Sannan daga bisani ya juyarda hannun nasa ya koma izuwa tsoka da jini. Sannan sauran jikinsa shima ƴa koma yadda yake. Koda ganin haka sai Babara ya zube a ƙas yana gaisuwa. "Ina ƙara jaddada mubayi'ata magajin wilbafos." Abin mamaki sai waɗannan halittu suka cire fatar dake rufe da fuskarsu inda suka bayyana a matsayin mutane. Sannan suka zube a ƙas suna gaisuwa tare da mubayi'a. "BARKA DA ZUWA MAGAJIN WILBAFOS, MAGAJIN SARKI EYRIYON, MAGAJIN SARKI ALDAIMA. Ka yafe mana rashin ɗa'ar mu, lallai mun cancanci kisa!!!" A dai-dai wannan lokaci duk wani wanda yasan sirrin dake ɗauke cikin jinin MAGAJIN WILBAFOS yasan an farkar dashi. *** Sanarwa: Zamu fara chapter kullum amma duk chapter da comments basu kai 30 ba ba lallai nayi post ba washe gari ******* Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 81: Kwangila Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Haka Lamarudu Wilbafos ya kai Armad cikin wani shinge wanda aka kewaye shi da manya-manyan jajayen duwatsu. Daga saman duwatsun kuma ruwa ne ke gudana zuwa ƙasa tayadda suka samarda wata ƴar ƙasaitacciyar ƙorama a ƙasa. Lamarinda yasa wajen yake bada wani irin sanyi mai inganci. Abu na farko daya fara zuwa ran Armad shi ne wai shin wajen horo aka kawoshi ko kuma wajen shaƙatawa. Amma kafin ya tambaya sai Lamarudu ya ɗora hannunsa akan wani dutse inda wasu hatimai suka bayyana suka kewaye dutsen. Nan take wata ƙofa ta buɗe a wajen. Lamarudu ya shige ciki sannan su Armad suka bishi a baya. Suna shiga wani ƙasurgumin daji mai kama da kasuwar muridan aljanu ya bayyana a gabansu. Babu komai sai manya-mayan bishiyun kuka wanda kowacce ɗaya tafi tsayin zira'i ɗari. Abin mamaki shi ne wasu manyan ƙayoyi dake kewaye da rassan wannan bishiyu a matsayin ganyayyaki. Lamarudu ya ce, "ga wajen koyar horo. Ga kuma ɗalasimin dazai fitar daku a yayinda kuka gama." Ya miƙa musu wata takarda mai ɗauke da hatimi. Har ya juya zai fita saiya waiwayo ya ce, "dajin nan an rabashi izuwa gida uku. Dajin kuma acike yake taf da jinsin Dordor dana aljanu masu cin naman biladama. Indai har mutun baya iya jin yanayin-izza to lallai bazai iya rayuwa aciki ba. "Kaso na farko na dajin yana ɗauke da abubuwanda izzarsu take tsakanin dubu ɗaya da dubu biyar. Kaso na biyu suna ɗauke da izza tsakanin dubu biyar da dubu goma. Amma kaso na uku duk abinda ka gani aciki izzarsa ta haura dubu goma. Lallai duk hatsabibancinmu bama shiga yanki na uku. A fito lafiya." Ya juya ya fice ya bar Armad da Babara a wajen. Bayan ya fita Babara ya tambayi Armad, "kaga irin kallon da wannan mutane ke yima?" Armad ya amsa da, "eh." Babara ya ɗanyi shiru naɗan taƙi kamar baya so ya faɗa amma daga ƙarshe ya ce, "Sunyi imani dakai kuma suna yi maka kallon zaka cece su. Hakan shi ne ma dalilin da yasa suka nuna maka waccan tsohuwar daula. Kada ka manta iyayensu sunyi wa kakanka sarki Eyriyon bauta, wanda hakan ne yasa aka ƙullesu. Cetonsu da zakai kamar ramawa kura aniyarta ne. Kuma idan ka yadda ka shiga cikin wannan daula zaka samu fasahohi da bayi na aljanu wanda zasu taimake ka a hanyarka ta zama cikakken sarki Wilbafos. Nidai ina ganin ya kamata ka shiga wannan tsohuwar daula." Armad dama yasan tuntuni Babara bai amince da rashin shigarsa wannan tsohuwar daula ba, saboda haka tuni ya tanadi amsa. "Duk na yadda da abinda kake faɗa amma kai sani cewa bazan iya sauka daga manufata ba. Kuma lallai indai ba ganin mahaifiyata ta samu lafiya nayi ba bazan iya tsayawa acikin wannna kurkuku ba. Saboda haka inaga mu fara horo kurum." Haka dai Babara ya haƙura dole. Sannan ya zana wasu hatimai guda uku a kewaye da Armad kafin ya bawa Armad umarnin ya zauna a tsakiya, sannan daga bisani ya fara karanta wasu ɗalasimai. Can bayan sa'a ɗaya ana cikin wannan hali sai fuskar Babara ta canja, inda nan take ya daina karanta ɗalasiman ya garzayo gaban Armad inda ya ɗebi kaɗan daga jininsa ya zuba acikin wata kwalba mai ɗauke tsumi. Armad dai ya ji wani abu amma yai shiru baice komai ba ya ƙurawa Babara ido. Can Babara ya kalli Armad cikin alhini yana cewa, "dama nayi tunanin haka, amma ina ta addu'a ya zama hakan bata faru ba." Armad yai zumbur ya ce, "ban gane ba. Mai kake nufi da dama kayi tunanin haka?" Babara ya fara bayani, "labarin daka bani na ɓacewar Miyurarka bawai Miyurarce kaɗai ta ɓace ba, harda wani ɓangare na ruhinka. A sakamakon haka bazaka iya amfani da idanuwanka ba har sai ka nemo wannan ɓari na ruhinka." Armad ya zare ido. "Eh?!" Babara ya ce, "bari mu gani idan zan iya gano inda ɓarin ruhin naka yake." Nan take ya ƙara ɗiban wani jinin daga hannun Armad ya kuma yaryaɗar dashi akan ƙasa, inda ya zana wasu hatumai masu rikitarwa akansa. Can daga bisani jinin na Armad ya fara yin haske, kafin daga bisani ya kama da wuta. Nan take sukai tsalle gefe, amma kafin suyi wani abu tuni jinin ya ƙone ƙurmus. Babara ya dubi Armad ya ce, "ruhinka yana katange acikin wata sihirtacciyar ƙasa amma saboda ƙasar na kewaye da Tsari baza a iya gane wacce bace." Armad yama rasa mai zaice, domin kaf maganar a baibai yake jinta. Wai ruhinsa ya ɓalle? Bayan kuma gashi nan da rai da lafiya. A iya saninsa ma wannan ba abu bane mai yiwuwa ba. Yana cikin tunani yaji muryar Babara, "nasan mai kake tunani, kuma kayi sani nima wannan shi ne karo na farko da naga mutun ruhinsa ya rabe kuma ya ci gaba da zama da rai. Amma dai maganar tana nan cewa bazaka iya yin amfani da idonka ba har sai ka nemo ɓangaren ruhinka." Armad ya kalli zoben dake ɗan yatsansa inda mahaifiyarsa ke ajiye. Can bayan tsahon lokaci Armad ya yanke shawara, inda ya numfasa ya ce, "idan za'a fara bada tarihi na, za'ace na fara ne daga nemo ɓangaren ruhina daya ɓalle. Saboda haka inaga zaman mu a wannan kurkuku yazo ƙarshe, lallai inada mahaifiyata a gabana bazan tsaya neman suna acikin wannan kurkuku ba." Babara ya rusunar dakai alamun girmamawa sannna ya ce, "ya shugaba na akwai wata hanya banda idanuwanka da zaka iya bawa mahaifiyarka izza da ban gaya maka ba." Armad najin haka yai zumbur cikin murna ya ce, "ko? Kamar ya fa?" "Kamar yadda ka sani kowanne ɗan adam yana samun ƙayyadaddun shekarun izza lokacin daya farkarda izzarsa, kuma wannan adadi a ƙa'ida baya taɓa canjawa. Koda kaima dalilin da yasa naka suka canja daga hamsin da ɗaya zuwa dubu ɗaya dan kawai baka farkarda izzarka ta haƙiƙa bane da farko. "Amma akwai wasu hanyoyi guda biyu kacal wanda ake iya ƙara yawan izza. Hanya ta farko na riga na gaya maka ita. Ita ce ta amfani da sirrin dake cikin idanun ƴaƴan Wilbafos. Hanya ta biyu wadda ban gaya maka ba ita ce hanyarda ake kira da KWANGILA!!" --- Mai kuke tunani ake nufi da fasahar KWANGILA? ** Note ------- Fasaha/Technique Farkarda fasaha/Awakening Sido-Urúrú/Pseudo-Ururu Hatimi/Ancient runes Dalasimai/spells etcMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 83: Bango Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ____ Duk da gudun dokinsa Ubbaru saida Armad yai kwanaki goma sha ɗaya yana tafiya sannan ya fara hango Bangon arewa. Gangar ruwa iyakacin ganinka ta shafe kudu da yamma gabas da arewa, tana ta kwaranya izuwa ƙasa amma babu ko halitta ɗaya a samanta. Koda Armad ya hangi wannan sai yaja linzami ya tsaya, inda ya buɗe zoben sihiri da Nostaljiya ta bashi domin ya futo da mahaifiyarsa. Babara ya gaya masa duk bayan kwana biyu akwai wani tsumi da zai ringa bata har zuwa lokacinda zai samu wannan shekarun Izza ya bata. Shi dai wannan tsumi shi ne abinda Babara ya ringa bata tsahon shekarunda Armad yayi bayanan kuma har ya dawo ya same ta cikin ƙoshin lafiya. A lissafin Babara mahaifiyar Armad tana buƙatar aƙalla shekarun izza dubu goma kafin ta warke. Wannan shekaru ba wani abu bane a wajen sarakunan jinzidal masu fasahar kwangila, saboda haka Armad ya gama yanke shawara kai tsaye wajen Nostaljiya zaije. Kuma tunda a hannunsa akwai wani ɗalasimi daya karɓa daga wajen Babara wanda zai iya gano masa inda ruhinsa yake zai iya yin aiki biyu a lokaci ɗaya, yana neman ruhinsa kuma yana neman Nostaljiya. Amma koda wannnan tunani ya gilmawa Armad a rai saiya tuno cewa ai bama abu biyu ba, lallai abu uku zaiyi a lokaci ɗaya. Domin kuwa akwai alƙawari daya ɗauka na kawarda cinikin bayi a ban ƙasa, wanda kuma bai manta dashi ba. Koda tunanin haka sai Armad ya buɗe ƙofar wannan zobe ya shiga inda ya samu waje ya rubuta sha huɗu ga wata tara shekarar 1855 Bayan Amri. Wato dai a wannan rana ce Armad ya fara shirinsa na rusa rukunin Jinzidal. Bayan ya gama kallon wannnan kwanan wata saiya juya izuwa ɗakin daya ajiye mahaifyarsa, inda ya shiga ya same ta a kwance, idanunta a rufe kamar tana bacci. Mahaifiyar Armad tana bada yanayin kwarjini matuƙa wanda saboda haka ba kowanne ma'aboci izza bane zai iya tunkararta ba a hakan da take a sume. Gashin kanta na nan baƙi, kuma kamar yadda wannnan cuta ta izza take a har kullum alamar kawai shi ne mutun zai zamanto a sume, amma banda haka babu wani abu dazai nuna rashin lafiya kamar irinsu tari ko zazzaɓi. Koda zama a gefenta sai kawai wani hawaye ya fito daga idonsa, babu abinda yake tunawa sai lokutan da yana yaro da kuma lokaci na ƙarshe daya ganta da lafiya. Tsahon lokaci a haka kafin ya buɗe bakinta ya ɗisa mata wannan tsumi dake cikin wata ƴar kwalba. Sannan ya taso ya futo idanunsa cike da kwalla. Lallai akwai abubuwa da dama da yake so ya tambayeta idan ta farka. Saboda haka babu wani abu dazai tsaya a gabansa. Har Armad yaje bakin ƙofar wannan zobe zai fita sai ya tsaya ya juyo inda ya durƙusa yayi alƙawari, ƙololuwar alƙawarinsa cewa a wannan fita kozai rasa ransa bazai dawo ba sai mahaifiyarsa ta warke. Yana fitowa ya rufe ƙofar wannan zobe sannan bayan yaci abinci ya mayarda Ubbaru cikin zobensa ya kuma nufi wannnan bango a ƙafa. Yana isa gaban wannan bango wata izza irin wadda bai taɓa jintaba ta dakeshi tayi cilli dashi gefe. Yana faɗuwa yaga jikinsa ya fara narkewa, fatarsa tana ɓanɓarewa. Nan take Armad yai sauri ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya. Wanda hakan ne ya cetoshi tunda hatta wuta bata isa ta ƙona walƙiya ba. Nan take Armad yai murmushi tare da cire zoben dake hannunsa ya cilla a baki sannan ya ɗaga hannunsa sama ya kirawo ɗaya daga cikin ɗalasimansa daya daɗe baiyi amfani dasu ba wato Kaban'shisu. Idan mai karatu bai mantaba wannan ɗalasimi ana iya amfani dashi ayi tafiya acikin lokaci daga wani waje zuwa wani. Matsalarsa kawai ita ce sai ɗaya kacal ake iya amfani dashi a shekara. Tuntuni dai Armad yayi tunanin amfani da wannan ɗalasimi ya fice daga cikin wannan kurkuku to amma bai gama abinda ya shigo dashi ba, sannnan kuma baya son yabar Babara anan. Nan take ya ƙaddamar da wannan ɗalasimi, inda ya ɓace daga inda yake. To amma a wannan lokaci maimakon ya tsinci kansa a bayan wannan bango sai kawai ya ganshi acikin tsakiyar bangon, kewaye dashi wani ruwa ne mai tsananin danƙo. Abu na gaba daya biyo baya wasu abubuwa ne manya-manya guda biyu suka bayyana a gaban idon Armad. Ɗaya daga cikinsu yana kama da wata daren goma sha uku, ɗaya kuma yana kama da rana saidai dukkaninsu baƙaƙe ne wuluk. Waɗannan abubuwa suka ƙura masa ido tamkar wasu idanun mayunwaciyar kurar da taga abinci. Nan take Armad yaji ya fara rawar ɗari. A lokacin ne ya fuskanci cewa gaba ki ɗaya jikinsa ya narke babu abinda ya rage face ƙoƙon kansa. Kuma wai a hakan ma dan ya riga ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya ne, lallai da tuni ya tsinci kansa a lahira. A wannan lokaci ya fuskanci abubuwa guda biyu. Na farko dai bawai a waje ɗaya yake tsaye ba, hasalima mugun gudu yake acikin wannnan bangon saboda ɗalasiminsa na Kaban'shisu. Wanda hakan ya nuna masa cewa saɓanin fahimtarsa da ɗalasimin bawai ɓacewa yake yiba a lokacin da yayi amfani dashi, kawai dai saboda tsananin sauri ne kawai yake ganin kamar ɓacewa yayi. Abu na biyu daya fuskanta shi ne wannnan abubuwa guda biyu dake kama da rana da wata ba wasu abubuwa bane illa idanuwa guda biyu na Ururu. Kuma hatta rawar ɗarin da yake ji daga su ne. A take Armad ya gane cewa lallai koda ya taho da Babara lallai bazai iya wucewa dashi ba. Domin ba daban jikinsa na walƙiya ba da tuni ya mutu aƙalla sau ɗari zuwa wannan lokaci. Sannan kuma ya gano cewa yayi dabara daya saka zobensa acikin bakinsa domin da tuni ya narke. Ana cikin haka wannnan idanuwa guda biyu suka fara haske suna fitarda wani yanayi mai firgitarwa. Ba shiri Armad yaji tamkar ana caccaka masa allurai acikin kansa. Abin mamaki sai kawai ya ganshi ya tsinci kansa a tsakiyar filin yaƙi, kewaye dashi sarakunan Ashura ne guda goma. Kowanne acikinsu yana riƙe da baƙar takobi. Kafin Armad yai wani motsi su goma sunyi tafiya acikin lokaci sun cake masa wannnan takubba acikin ƙirjinsa. Ko motsi baiyi ba ya faɗi matacce. Abin mamaki a gaske ma a wannna lokaci

Chapter 28 of 33