Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wanda ke nunawa Armad, kamar basa buƙatar suji abinda yaji. Ba jimawa Armad ya haɗa ɗaya biyu, ya kuma gane cewa lallai akwai yiwuwa wani daga cikin wannan mutun uku nada Izzar da take iya duba abinda ke cikin kan mutane. Kuma akwai yiwuwar anyi amfani da ita akansa, a wannan lokacin. Wannan tunani na shiga kansa ya ɗaga ido ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Yana zuwa kan wannan budurwa ya tsaya. Ba dan komai ba, saboda wani abu a jikinsa na gaya masa cewa tabbas, koma mai ya faru ita ce, musamman idan ya tuno da yadda yaga samarin biyu sun kalle da farko. Armad ya gayawa kansa cewa koma dai mai ya faru, lallai a wannan lokaci basa buƙatar ya gaya musu wani abu, domin kuwa gashinan a gabansa ana tattauna ta wacce hanya yafi kamata a kashe shi, wanda hakan ya bashi dukkan tabbashin da yake nema. Abin al'ajabi mutanen da basu daɗe hira dasu ba amma gashi suna tattauna ya zasu halaka shi a gaban idonsa kamar ma baya wajen; babban nasu ya ce kawai su ɗaureshi su cillashi acikin ruwa, ƙaramin ya ce kawai su sare masa kai da takobi a wajen, macen kuma bata ce komai ba da farko. Sai da taga sun rasa wacce zasu zaɓa aciki, har suna neman jefa ƙuri'a, sannan ta dubi babban nasu tace, "ahhh, mai zai hana, a haɗashi da yaya Kiru su fafata, in yaso idan suka gama faɗan sai ku san mai zaku yi dashi daga baya." Kamar wadda take tsoron kada suƙi yadda da shawararta, sai tayi sauri taci gaba da cewa; "Badan komai ba, saboda inason naga faɗan Yaya Kiru, da kuma sabuwar fasahar da kace ka koya masa!" Tana rufe baki babban nasu yai murmushi gami da girgiza kai, ya ce, "a'ah, ki bari idan munje gida....." Amma ina tun kan ya rufe baki ƙaramin da ta kira da Yaya Kiru ya miƙe tsaye gami da duban babban nasu ya ce, "Yaya Hasanu, kullum kana gaya mana wataran mu zamu kare Burja, kuma wataran mu zamu tsaya a gaban filin daga mu jagoranci yaƙi ko, to ina roƙonka daka bani wannan dama na nuna maka Izza ta!" Yana gama faɗa ya sunkuyar da kansa ƙasa, amma tun daga nesa zaka iya jin yanayin marmarin yaƙi na tashi daga jikinsa. Babu abinda yake jin tsoro face Yayan nasa ya ce a'a. Amma yana cikin wannan hali yaji yayan nasa ya ce, "tohhh! "Nuna min na gani! Kai sani ina sa ran ganin abinda zai faranta min rai!!" Amma yana cikin wannan hali yaji yayan nasa ya ce, "tohhh! "Nuna min na gani! Kai sani ina sa ran ganin abinda zai faranta min rai!!" Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 9: Farar Takobi Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Armad ne da Kiru a tsaye su na fuskantar juna, kowa da tasa takobin a zare! Tun dai ƴan mintuna da suka gabata, Hasanu wanda shi ne babban wannan tawaga ya kwance Armad ya kuma bashi takobinsa. Abinda kawai ya rage shi ne Kiru ya nunawa Hasanu da wannan budurwa, wadda ta kasance ƙanwarsa, irin sabuwar fasaha, da ya koyo. Fuskar Armad bata canja ba ko kaɗan, tamkar babu abinda ke faruwa, yana riƙe da ƙotar takobinsa. A wannan lokaci ne Kiru yayo kan Armad, yana zuwa ya ɗaga takobinsa ya kawo masa wani wawan sara. Wata ƙara mai kashe kunne ta tashi sama yayinda waɗannan takubba nasu suka haɗu a sama, lamarinda yasa dukkan tsuntsaye da sauran dabbobi dake kewayen fara guje-guje. Kan kace meye wata iska ta tashi daga kewayen su, inda ta bazu ko'ina, har saida ta kaɗa bangon ruwan dake arewa, wanda bashi da nisa da inda ake fafatawar. Kiru ya kalli takobin Armad idanunsa cike da mamaki, wanda a wannan lokaci fuskarsa taɗan canja, kana gani kasan haɗa takobin da sukai yasa ya rage kallon rainin da yake wa Armad. Duk da cewa yasan baiyi amfani da sama da kaso sittin, na ƙarfin Izzar sa ba, a yayin wancan sara, amma yanayin yadda Armad ya murza takobin tasa sannan kuma ya kare saran ba tare da wata damuwa ba, shi ne abinda ya bashi mamaki. Bama shi ba, hatta Hasanu sai da idonsa ya ɗan ƙifta. Armad ya ɗaga kai ya kalli Kiru ido cikin ido, lamarinda yasa Kiru yai tsaki, a lokaci guda kuma ya afkawa Armad da sara ta ko'ina. Cikin abinda baifi ƙiftawar ido ba, tuni sun kaiwa juna sama da sara ashirin. Aduk lokacin da takubbansu suka haɗu sai kaji ƙara mai kashe kunne ta tashi sama, sannan ƙura ta ƙara turnuƙewa, babu abinda suke sai kai-komo. Baya kimanin daƙiƙa sittin, dukkaninsu suka tsaya da kaiwa juna sara, gami da ja baya, kowa na kallon kowa, su na haki. Suma su Hasanu da Zahra kallonsu kawai suke, kuma harya zuwa wannan lokaci, Armad ya kula, babu alamar su biyun zasu shiga cikin faɗan. Wannan saurayi mai suna Kiru da suke fafatawa da Armad, zaɓaɓɓe ne daga daular Banfiriya, kuma ɗan sarkin garin Sisiya ne. Kuma yana daga cikin waɗanda mutane da dama suke yiwa kallon shugabannin gobe. Kuma saboda tarin kayan aiki na horo da zai iya samu aduk lokacin daya buƙata, da kuma manya-manyan malamai a garinsu, da duk suke so karɓe shi a matsayin ɗalibi na musamman, sannan kuma ga dangi na musamman da yake dasu, kai dama sauransu... Hakane ma yasa, a tsahon tarihin Kiru, tun daya taso, harya zuwa shekaru goma sha bakwai da yake a wannan lokaci, babu wani sa'ansa daya taɓa cin galaba a kansa a fagen fama. Saboda haka daga kansa har zuwa yayansa Hasanu, wanda shi ne Kwamanda na huɗu a ƙarƙashin wannan ƙungiya da akewa laƙabi da Burja, babu wanda ke da kokwanton Kiru zai samu nasara akan Armad ba. Kuma su na gani cewa, wannan kai-komo dake faruwa a tsakanin Armad da Kiru bata wuce motsa jini ba a wajen Kiru. Shi kuwa Armad duk da shi, ba zaɓaɓɓe bane daga kowacce masarauta ba, amma a dai-dai wannan lokaci da yake tsaye yana fuskantar Kiru, babu abinda yake gayawa kansa sai cewa, yanzu ya fara wannan tafiya tasa ta neman Tirifil Fakta, kuma lallai shima jarumi ne, kuma wannan faɗa kamar wata dama ce ALLAH ya bashi da zai fita daga cikin halin da yake ciki. Saboda haka babu abinda yake tunani face hanyar da zai kuɓuta daga waɗannan mutane koma su waye. Armad ba dolo bane, kuma yasan iyakacin ƙarfinsa, saboda haka nema tunda farko Armad ya gama lissafa cewa, a iyakacin ƙarfinsa a wannan lokaci babu yadda zaiyi da waɗannan mutane uku. Amma yana jin cewa da mutun ɗaya, zasu kara sai yaji daɗi, domin yasan akwai yiwuwar mafita. A dai-dai lokacin da yake wannan tunani kwayar idonsa ta motsa daga kan Kiru izuwa kan Hasanu. A lokacin ne yaji nan take tsigar jikinsa ta tashi da wani irin tsoro, irin wanda rai ke fuskanta a dai-dai lokacin mutuwarsa. Ba komai bane ya janyo haka ba illa ratar ƙarfin Izza daya ji a jikinsa wadda ke tsakaninsa da Hasanu! Lallai yasan Hasanu ba sa'an sa bane. To amma a dai-dai lokacinda zuciyarsa take ɗarsa masa cewa, Kiru ba komai bane ba, Hasanu shi ne abin ji! Shima Kiru yaga kallon da Armad yayi wa Hasanu da kuma yadda ya tsorata dashi, saboda haka bai ɗau lokaci ba ya gano abinda Armad ke tunani a ransa. Wanda hakan yai matuƙar ƙona masa rai, ya ɗaga kai sama yai ƙaraji, idanunsa ja-jawur. Ba komai bane ya jawo haka ba, illa ji da yayi acikin ransa cewa Armad ya raina shi, yana gabansa amma bata tasa yake ba. Nan take ya maida takobin dake hannusa cikin kufenta, sannan ya fito da wata daga cikin kufen. Sai dai ita wannan ta biyun fara fat ce, babu abinda take sai matuƙar kyalli, idan rana ta haska ta sai kaga tana haske ido, haske na tashi kamar walƙiya. Ba tare da ɓata lokaci ba, cikin matuƙar fushi, ya afkawa Armad. Da farko Armad baiyi ko gezau ba, amma a lokacinda idon sa yakai kan wannan takobi, kyallin da take, ya daki idonsa, nan take yaji wata rawar-ɗari ta gifta ta jikinsa. Abinda yasa dukkan tsigar jikinsa ta tashi. Babu abinda zuciyarsa take ɗarsa masa sai alamun hatsari a tattare da wannan takobi. Bai ko ɓata lokaci ba yaja da baya, ya kuma zare takobinsa gami da karanta wasu ɗalasimai daya koya a wajen kakansa, waɗanda babban abinda suke shi ne ƙarawa takobi ƙarfi. Amma duk da haka Kiru yana ƙara matsoshi alamun hatsarin da zuciyarsa ke nuna masa a tattare da wannan farar takobin bai daina ƙaruwa ba. Baima ko gama karanta wannan ɗalasimai ba, alamun hatsarin da yake fuskanta daga takobin nan yakai ƙololuwa, bayanda ya fuskanci cewa wani farin haske mai kashe ido ya fara taruwa a gefen wannan farar takobin dake hannun Kiru! Kan kace meye wannan, hasken ya ƙaru matuƙa inda yake bada alamun walƙiya-walƙiya, wanda kuma a daidai lokacin ne ya iso gaban Armad, inda ya kawo masa wawan sara da takobin. Da kyar Armad ya iya kai tasa takobi ya tare saran. Wannan takubba na haɗuwa wata gagarumar ƙara ta tashi sama. Ƙarfin saran na Armad, ya daki takobin ta Kiru, inda wannan ɗalasiman daya karanta suka fara fita daga jikin takobinsa, kamar kibiya su na bi ta cikin takobin Kiru sannan su shige jikinsa. Wani mummunan zafi mai cike da gunji ya cika jikin Kiru, wanda acikin lokaci ƙanƙani yasa ya fara gani dishi-dishi. Wani tari na dole yazo wuyansa, wanda yayi iya ƙoƙarinsa kada yayishi amma ina Tarin na fitowa kuwa saiga alamun jini a jiki, wanda hakan ke nuna cewa lallai wannan ɗalasimai, sun jiwa wasu daga cikin kayan cikinsa ciwo. To amma a dai-dai wannan lokacin shima Armad ƙarfin saran takobin Kirun ya cimmasa, wanda yabi ta jikin takobinsa sannan ya shige jikinsa a kimanin abinda bai wuce rabin daƙiƙa. Abu na farko da yayi arba dashi shi ne, wani haske mai tsananin haskake ido, wanda yayi kama da hasken daya gani a farko wanda ke kewaye da takobin ta Kiru tun lokacin daya fara isoshi. Sai dai kuma amma wannan hasken da yake gani, yafi wancan ƙarfi sau da dama, domin yama fi kama da hasken WALKIYA. Bayan wani ɗan lokaci da bazai iya ƙayyade shi ba sai yaga hasken ya ɓace ɓat. To amma kuma kafin ma yayi wani tunani dangane da yanayin daya samu kansa aciki, sai kawai ya fara fuskantar wata uƙuba irin ta musamman. Shi dai yasan lallai abinda yake fuskanta yafi gaban ace masa zafi, to amma bashi da taƙamaiman kalmar da zai kira shi, saboda haka ya gayawa kansa cewa wannan lallai uƙuba-ce-irin-ta-musamman. Babu abinda yake ji a dukkanin sashikan jikansa illa irin wannan uƙuba, wadda tasa yake ji tamkar kowanne ɓangare na jikinsa gab yake daya farfashe, ya kuma tarwatse. Baima san lokacin daya rufe idonsa ba, saboda tsanani zafin da yake fuskanta, wanda yasa yama manta cewa a tsakiyar faɗa yake. Can bayan wani lokaci da bazai iya ƙayyadewa ba, sai kawai yaji tamkar ruhinsa ya fara marmashewa tamkar busasshen yashi. Yana bin iska da ƙarfin gaske, wanda hakan yasa ƙura ta fara tashi. Dukkanin wannan abu da Armad yake fuskanta, yasan a mafarki yake jinsa, amma kuma lallai uƙubar da yake fuskanta yasan cewa a zahiri take. Babu abinda yake juyawa acikin idonsa banda wannan abubuwa uku; WALKIYA da FASHE-FASHE da kuma ƘURA. Yayi taga-taga, ya jada baya kamar zai faɗi, sannan bayan kimanin taku uku ya tafi ya nufi ƙas tamkar zai durƙushe akan gwiwowinsa guda biyu! Da kyar ya samu ya ɗan iya buɗe idonsa, inda ya cake takobinsa a ƙas, ya tallafi kansa da ita, lamarinda ya taimake shi bai je ƙas ba. Amma babu abinda ke fita daga bakinsa sai jini! Kallo ɗaya zakai masa, kasan yafi Kiru jin jiki a waccan karawar da sukai. Da kyar ya miƙe akan ƙafafuwansa ya kuma zare takobinsa daga ƙas. Ya ɗaga ido ya ƙara fuskantar Kiru, wanda tuni shima ya jada baya ya kuma tsaya daga ɗan nesa yana karanta abubuwan dake faruwa cikin haki, a zuciyarsa kawai yana auna ƙarfin abokin fafatawarsa ne, daga wannan haɗuwa da sukai guda ɗaya, musamman tunda gashi har tasa yayi tarin jini guda ɗaya. To a dai-dai wannan lokaci ne, Armad ya fuskanci cewa gaba ki ɗaya wajan da yake tsaye acike yake da ƙura matuƙa, domin da ƙyar ma yake hango abokin karawarsa daga nesa. Yana cikin tunani akan mai ya jawo wannan turnuƙewar ƙurar, wadda a iya tunawowarsa baya hango lokacin da sukai bata kashin da har wannan ƙura zata tashi haka. To amma a dai-dai wannan lokaci da yake wannan tunani ne yaji muryar Kiru, ''kayi ƙoƙari daka iya kuɓuta daga farar takobina. ''Kayi sani cewa ka shiga cikin kaɗan waɗanda suka cancanci suji bayani akan sirrin wannan takobi tawa! ''Sunan wannan takobi; Walƙiya-Tarwatsi-Ƙura! ''Da abinda kaji da kuma abinda kake gani na game da ƙura yanzu da idonka, duk zahiri ne bawai mafarki ba ne!'' Yana zuwa nan a zancansa ya ƙara taku ɗaya izuwa Armad, sannan yaci gaba da bayani, ''Duk sara guda daga jikin wannan takobi, yana tafiya ne da farin haske wanda waɗanda abin ya shafa sukan kwatanta a matsayin Walƙiya. ''Sannan kuma abinda zai biyo baya shi ne tarwatsewar abinda saran ya shafa, wanda hakan shi ne yake yin bayani ga kalmar tarwatsi dake cikin sunan.'' A dai-dai wannan lokaci ne Kiru ya ƙara ɗaukan taku ɗaya izuwa ga Armad, sannan yayi shiru, ya kuma kalli gefen Armad daga ƙasa, wanda a dai-dai lokacin ƙurar ta ɗan fara lafawa. Armad wanda ke gabansa, zare da takobi yana karantar abokin fafatawar tasa, yana kuma sauraran mai yake cewa, shima idon nasa ya motsa inda ya kalli gefen nasa daga ƙasa. Cikin tsananin mamaki ya jada baya, bama tare da ya sani ba, saboda abinda idonsa ya gani. Gaba ki ɗayan shatalen gefen nasa ya rarake yayi wani mummunan rami, tamkar wanda aka haƙe da ƙarfin gaske. To a sannan nan ne ya fuskanci cewa ƙurar na dake tashi daga wannan rarakakken rami take fitowa. Bai ɗau lokaci ba ya gane duk abinda ke faruwa kuma ya gane abinda kalmar ƙarshe ta sunan takobin take nufi, ''wato kalmar Ƙura wadda ke nufin ƙurar dake turnuƙewa bayan abinda aka sara ya tarwatse!'' Yana cikin tunani ya ƙara jin muryar Kiru wanda a daidai lokacin ne yayi taku na uku inda ya ƙara kusantar Armad, yadda ya rage baifi kamu biyu bane a tsakaninsu ba ''nasan zuwa yanzu ka riga kasan ma'anar kalmar ƙarshe dake cikin sunan takobi na. ''Kuma kasan irin sa'ar daka taka yadda ka tsira da jikinka a haɗe.'' Yayi wata dariya ta mugunta da gefen bakinsa sannan ya cike da cewa, ''amma nasan kasan cewa sa'a bata zuwa sau biyu a lokaci ɗaya a kuma cikin tsakiyar fafatawa ɗaya!'' Armad ya kalli gefensa yaga cewa babu inda ba'a rarakeba, inba ɓangaren da Kiru yake ba, kai hatta bayansa. Nan take yasan cewa babu wata hanya, ta guduwa ko kuma canja waje, abu ɗaya kawai daya rage shi ne su afkawa junansu. Yana cike da masaniyar cewa idan ya bari wannan farar takobin, ta ƙara cimmasa a irin lokacin haka, to ba lallai ya tsira da ransa ba! Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 10: Gimbiya Zahra Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga gefe, idanun Hasanu da wannan budurwa acike suke da mamaki, kuma zuwa wannan lokaci su na da cikakkiyar masaniyar cewa shima Armad, koma daga ina yake, lallai ya sami horo na musamman. Dukkaninsu sun san irin ƙarfin da farar takobin Kiru ke dashi, amma bisa mamakinsu Armad ya iya tare sara daga gareta kuma ba tare da yaje ƙasa ba. Hasanu ya ja numfashi sannan ya ƙara matsawa gaba, gami da ƙara ƙurawa Armad ido. Ya kalleshi sama da ƙas, sannan bayan wani ɗan lokaci sai kawai idanunsa suka canja, kamar wanda yake so yaga wani abu a tattare da Armad, amma kuma ya kasa. Yana shirin ɗauke ido daga kan Armad, sai idonsa yakai kan wannan jan ƙyalle dake ɗaure a gaban goshin Armad. Nan take ya ƙura masa ido tsahon daƙiƙu, kafin kwatsam idonsa ya cika da firgici sannan jikinsa ya fara karkarwa. Cikin ɗimuwa ya fara magana aciki, "madauwamiyar Miyura... ina ba abu bane mai yiwuwa... to amma... ''Hmmm.... ko madai ba ita bace a goshinsa ba, kashe shi a yanzu ganganci ne, ya zama wajibi na koma dashi Sisiya, in yaso na ƙara duba littafin 'Matsayin-Izza' na shugaba Jána Sisiyu, kafin na kaiwa sarki wannan babban labarin!'' Yana zuwa nan a zancansa ya ɗaga kai domin kawo ƙarshen wannan fafatawa dake faruwa, tsakanin Armad da Kiru da niyyar tafiya da Armad ɗin can garin Sisiya, wajan sarki. To amma a dai-dai wannan lokaci ne Kiru ya ƙara kawo wa Armad wani wawan saran. Amma abinda Kiru bai sani ba shi ne tuni ya bayyana ga Armad cewa lallai, idan ya bari suka ƙara haɗuwa da wannan farar takobin ta Kiru, a irin karo na farko, tofa lallai sakamakon bazai masa kyau ba. Saboda haka tuni ya riga yayi wata sabuwar shawara acikin ransa. Yayi shawara cewa zaiyi amfani da wani hari na musamman shima, ya kuma afkar da wani gagarumin ɗauki akan Kiru wanda zai bashi dama ya ci nasara cikin sauri ba tare da bawa abokin karawar tasa dama ba. Saboda haka tuni ya gama shiri, a lokacin da Kiru yake ƙoƙarin afka masa da wannan farar takobi. A dai-dai wannan lokaci takobin Armad ta fara fitar da wani irin hayaƙi. Kan kace meye wannan gaba ki ɗaya kewayen Armad ya cika da irin hayaƙin, ta yadda da kyar ake iya hangoshi a tsaye cak a tsakiya. Dukka wannan baisa ko kaɗan Kiru ya dakata ba, illa kawai ƙara azaba da yai wajan afkawa Armad ɗin. Kamar ana ziga wannan farar takobi dake hannun Kiru, wani farin haske mai tsananin haske ido ya fara ambaliya daga jikin ƙarfenta. Sannan kuma idan ka lura ma zakaga kamar ta ƙara tsayi da kimanin kamu ɗaya To a dai-dai lokacin ne, su biyun suka haɗu kuma suka afkawa juna da sara, takubbansu suka haɗu a sama, ga mi da fitarda wata ƙara mai rikitarwa, wadda tasa saida Zahra ta rufe kunnuwanta da hannayenta. Iska mai ƙarfin gaske ta kaɗa, wadda tayi ƙoƙarin cilli dasu daga wajan da suke tsaye. Iskar ta ƙarasa ta daki bishiyun dake kewayen wajen wanda hakan yasa nan take reshinansu suka fara girgiza, kamar zasu cire. Kan kace meye wannan ƙura ta turnuƙe, har takai basa iya ganin koda tafin hannayen su. Babu abinda suke ji illa girgizar ƙasar da suke kai kurum. ''Dukkanin abinnan dake faruwa sara ɗaya ne kurum ya janyo, daga jikin takubbansu!!!'' ''Eh...'' Hasanu ya ja dogon numfashi, yayinda baki a buɗe, fuska a yamutse cike da mamaki ya bar ƴar uwar tasa, acikin ƙurar nan ya nufi cikin wajen da su Kiru suke fafatawa da gudun gaske. Ba wani abu bane ya jawo haka ba illa wata halitta da yaji a jikinsa ta fito daga cikin Bangon Arewa tana kuma gabato wajen da suke. Wannan halitta ba wata aba bace, illa ɗaya daga cikin fatalwowi na musamman dake cikin wannan waje. Kasancewar dama tunda farko wajan da suka kafa tantin nasu bashi da nisa da Bangon-arewar ta yadda zaka iya hangensa daga nesa. Akwai wani karin magana da kusan kowa ya sani a wannan zamani, wanda indai kaji shi, to kawai kasan ana magana ne akan waɗannan bangwayen ruwa biyu. Wannnan karin magana kuwa shi ne, ''Mafakar mutuwa!'' Wanda ya samo asali ne tun da daɗewa, saboda wani dalili guda ɗaya. Wannan dalili kuwa shi ne, da dama daga cikin al'ummatai na wannan zamani su na da fahimtar cewa, dukkan mutumin daya mutu anan ruhinsa yake fara yada zango kafin wani lokaci. Hakan kuma ya samo asali ne daga yawan fatalwowi da suke zaune akan wannan ruwa. Kuma babban abun mamakin shi ne, da dama mutane sukan ga fatalwar wani wanda suka taɓa sani a lokacin yana raye a wannan waje musamman a wasu lokuta na shekara. Babban tashin hankali ga al'amarin waɗannan fatalwi shi ne yadda suke cin naman mutun ɗanye wanda har takai sukan kifarda jirage, sannan su halaka fasinjoji. To amma a dai-dai lokacin da Hasanu ke ƙoƙarin isa wajen wannan fafatawa dake faruwa, Wannan haɗuwa da farar takobin Kiru sukai da takobin Armad mai fitarda hayaƙi, ya haddasa wata mummunar girgizar ƙasa, wadda cikin ɗan ƙanƙani lokaci ta fara zagwanyar da dukkan ƙasar da suke kai. Abin ya fara ne a iyakacin kewayen ƙasar dasu Armad kekai, amma cikin daƙiƙa kaɗan ya fara bazuwa ko'ina. Kan kace meye wannan dukkaninsu sunyi tsalle sama izuwa kan ƙasar dake gabansu, domin kaucewa faɗawa rami, sai dai kuma bisa rashin sa'a, ƙafafunsu na dira kan ƙasar ita ma ta fara rududduge wa. Kuma kan kace meye wannan ƙasar da Zahra ke kai, ta rabe gida biyu kuma tana neman afkawa ciki. Lamarin da yasa cikin tsananin zafin nama Hasanu ya juyo da niyyar riƙota, amma tun kafin ya ƙarasa ya ji a jikinsa cewa wannan fatalwa data fito daga cikin wannan ruwa ta kusa cimma su Kiru. Nan take Hasanu ya ƙara azama, inda yai maza ya riƙo Zahra, ya hanata faɗawa wannan rami. Sannan kuma cikin sauri ya ajiye ta acan gefe guda, ya kuma juyo da niyyar ceto Kiru daga harin sumame da wancan fatalwa take neman yi musu. To amma abinda bai sani ba shi ne, tuni Kiru yasan abinda ke faruwa kuma ya yanke shawarar me zaiyi. Kan kace meye wannan, sunyi hannun riga, Kiru yayi yamma Armad yayi gabas, shi Kiru yana ƙoƙarin gujewa fatalwar, shi kuma Armad yana ƙoƙarin gujewa wannan ramika. Kan kace meye wannan, ratar dake tsakaninsu takai kimanin taku bakwai. Hakan kuma ya faru ne ba tare da saninsu ba, domin su kawai gudu suke suna tsallake rigiya da baya daga wannan waje zuwa wannan a tsakanin wannan girgizar ƙasa. Wani abu da duk su biyun suka fuskanta shi ne, lallai bawai kaɗai harin da sukai amfani dashi bane ya janyo wannan girgizar ƙasa ba, dole akwai wani abu a ƙas. Duk inda suka taka kafin ma su ajiye ɗaya ƙafar, shima ya fara zaizayewa, to amma daya ke dukkanin su biyu ba mutane bane wanda suka daɗe acikin duniyar horo ba, kawai yara ne waɗanda aka haifa da baiwa, wanda kuma hakan lallai bai kai a wannan lokaci yasa su tsere daga mahaukacin saurin da zaizayar ƙasar ke faruwa dashi ba. Hakan ne yasa bayan kimanin daƙiƙu shida ta cimmusu, ta yadda takai ƙafafunsu suka dira a dai-dai lokacinda itama ƙasar take cinyewa, saboda haka suka rufta ƙas ba shiri. To amma ga dukkan alamu sa'a tana tare dasu a wannan lokaci, inda wannan girgizar ƙasa ta tsaya a dai-dai lokacin da sukai amfani da hannayen su wajen riƙe ƙarashen ƙasar da bata ƙarasa rushewa ba. Hakan na faruwa suka miƙa hannayensu, suka kuma riƙe waɗansu tubalin ƙasa waɗanda suma sauran ƙiris su cire. Kasancewar kuma duk su biyu a gine suke da jiki murɗaɗɗu, kuma wajajen da suka riƙe basu da kwari sosai, bai ɗau lokaci ba kafin wajan da suka riƙe ya fizgine, su ƙara nufar faɗawa. Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne Hasanu ya isa wajen, inda ya riƙo hannun Kiru, ya kuma fara janyoshi waje. To amma a dai-dai lokacin ne idanunsa suka cika da mamaki saboda abinda yai arba dashi. Zahra, wadda bai daɗe da ajiyeta a can gefe ba, ita ce a kwance a rigingine, dai-dai wajen da Armad ke ƙoƙarin faɗawa inda hannunta na hagu ke miƙe a gabanta riƙe da hannunsa. Shima Kiru wanda yake jira a janyoshi waiwayawa kawai yayi, yayinda ya fuskanci inda Hasanu ke kallo. Armad ya dubeta idanunsa cike da yanayi na rashin fahimta. Nan take ya shiga wani yanayi mai tsananin ban mamaki da alajabi. Irin wanda bai taɓa fuskanta ba a rayuwarsa. Hannunta na taɓa nasa, yaji wani a jikinsa cewa lallai ya taɓa ganin wannan budurwa, kai bama iya haka ba, har wasu hotuna yake gani acikin kansa wanda suke nuna masa wasu mu'amaloli da suka faru tsakaninsa da wannan budurwa a baya, lamarinda yai matuƙar ɗimauta hankalinsa. Ya cika da mamaki, domin kuwa yasan lallai duk waɗannan abubuwa basu taɓa faruwa ba. Hasalima bai taɓa ganinta ba, sai a wannan lokaci. To amma bisa mamaki, abubuwan da yake ji, sunfi gaban ace mafarki yake. Domin kuwa a zahiri yake ganin abin, kamar ma bai daɗe da faruwa. Dukkan abin daya gani, bai haura daƙiƙa biyar ba, amma shi yana jin kamar ya kai daƙiƙa dubu a jikinsa. Ya buɗe baki zaiyi magana, to amma duk da cewa akwai samada tambayoyi dubu da zaiso ta bashi amsa, amma bisa ya kasa cewa komai! Kafin ya iya rufe bakinsa kawai sai wata kwayar hawaye ta fito daga idanun Zahra ta kuma nufo idanunsa. Kuma saboda yanayin yadda suke a lokacin, kai tsaye hawayen ya ɗisa acikin idonsa. Lamarinda baiyi wani abu naya hanashi faruwa ba. Babu abinda yake ta kai-komo a ransa sai tunanin a ina ya taɓa ganin wannan kyakkyawa?? Zahra ta buɗe baki kenan zatai masa magana, fuskarta acike da murmushi, sai kawai yaga murmushin fuskarta ta ya dusashe a lokaci ɗaya, sannan kuma an maye gurbinsa da tsananin tsoro da firgici. Kafin yayi wani abu tuni Zahra ta saka dukkan ƙarfinta wajan ƙoƙarin janyoshi waje. Idanunta nakan wani abu dake doso wajan da suke ta baya. Bai ɗauki lokaci ba ya fahimci cewa akwai wani abu mai hatsari dake kusanto shi ta baya. Kafin ma ya ƙarasa juyawa muryar Kiru wanda tuni Hasanu ya fito dashi, suke kuma nufosu da gudu, ta isa cikin kunnensa, yana kwala ƙara kamar maƙokwaransa zai fashe, ''Kinsan cewa idan fatalwa ta taɓa shi kina riƙe dashi har kema abin zai shafa, KI CIKASHI!!!'' To a dai-dai wannan lokacin ne Armad ɗin ya juya ya hango wata siffa mai tsananin firgitarwa tana nufoshi daga nesa da wani mugun sauri mai kamar walƙiya. ''So kike yi ki mutu, saboda wannan yaron da ba kowan kowa ba!!'' Inji Kiru wanda ya ƙara azama a ƙoƙarinsa na isa wajanda suke. Shima Hasanu wanda fuskarsa ke cike da rashin-fahimta da mamaki, da kuma ɗimuwa, musamman ma yasan shi alhakin kula da ita ke kansa, ya fara roƙonta, ''kinsan muhimmancinki a gurin mahaifinki, dama dukkan al'ummar ƙasar Sisiya, kada kiyi haka, koma me kike tunani akansa, kuma ko meye dalilinki!!'' A dai-dai wannan lokaci saboda tsananin saurin da wannan halitta ke tafiya dashi tuni ta iso inda Armad yake, wanda har a sannan Zahra bata ƙarasa janyo shiba. Nan take ya gane mai maganganun su Hasanu suke nufi, ya kuma fuskanci dukkan abinda ke faruwa, kasancewar duk da bai taɓa ganin irin waɗannan fatalwowi a gaske ba, amma ya taɓa karanta su a littafi; Ya fahimci cewa saurin da wannan fatalwa take yi, yafi wanda su Hasanu keyi, kuma tabbas kan su ƙaraso wajen da suke, wannan fatalwa zata rigasu. Saboda haka komai yana hannunsa da wannan budurwa, mai suna Zahra, kodai ta

Chapter 6 of 33