Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fasaharka, amma kafin lokacin zan fara da koya maka dabarun amfani da takobi da kuma fasahar aljanu. "Kaga dai amfani da aljanu yana buƙatar shekarun izza. Kuma iyakacin yawan shekarun izzarka iyakacin ƙarfin fasahar da zaka iya amfani da ita. Da shekarun izza hamsin da ɗaya da kake dasu baza ka iya wuce mataki na farko ba daga cikin matakai shida na amfani da aljanu. Kuma indai...." Armad na cikin bayani yaji wani yanayin-izza mai tsananin ƙarfi da buwaya ya tunkaro shi ta baya. Tunda Armad yake bai taɓa jin irin wannan yanayin izza ba. Idan a misali zai iya kwatanta girman yanayin-izzar duk daya taɓa ji a matsayin kofin ruwa ɗaya to wannan izzar takai girman tekun maliya. Bawai kuma girman izzar ne yasa Armad ya fara gumi ba, tsananin zafi da muni da azabar dake cikin izzar ne yasa Armad yaji tamkar ruhinsa zai fashe. Kafin Armad yai wani motsi Inara ya faɗi ƙasa sumamme. Yana juyawa bayansa wani ƙatoton hankaka baƙi-ƙirin mai ido kwaya ɗaya tak ya kawo masa wafta. Armad ya manta da cewa zai iya juyewa izuwa walƙiya ya baje a ƙasa wannan hankaka ya wuce. Kafin ya miƙe hankakan yayiwo kwana. Cikin sauri Armad ya kirawo Hannun-Aradu ya fuskanci wannan hankaka. To amma bisa mamaki sai hankakan ya tsaya cak yana kallon Armad sama da ƙasa tsahon lokaci kafin daga bisani ya juya ya ɓace. Abu na farko daya fara zuwa ran Armad shi ne wani labari da mahaifiyarsa ta taɓa bashi akan wata ƙabila wadda aka manta da sunansu. Wannan ƙabila sune asalin tsafin Sanyin-Babban-Sihiri. Dukkan tsafinsu suna yinsa da baƙin aljanin-hankaka wanda ake kira da HANKAKAN- MUTUWA. Acewar wannan labari hatta sarki Eyriyon Wilbafos da sarki Kuyurussa'ayi Ururu baza su iya sawa wannan hankaka ya durƙusa musu ba. Shi yasa suka haɗa ƙarfi da ƙarfe suka halaka wannan ƙabila. Kuma tun daga wannan rana babu wanda ya ƙara ganin Hankakan- mutuwa a doron ƙasa. Amma indai Armad ba mafarki yake ba lallai yau yaga hankakan-mutuwa da idonsa. **MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 96: Shiga Fada Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Koda Armad yaga wannan baƙin hankaka na neman ɓace masa saiya buɗe ƙofar zobensa na sihiri ya cilla Inara aciki. Sannan yayi amfani da fasahar Kaban'shísu ya ɓace daga inda yake tare da bayyana acan nesa dai-dai ƙasan inda hankakan ke tafiya a sama. Hankakan na ganin haka ya sha kwana tare da ƙara azama wajen iyo akan iska yana ƙoƙarin gujewa Armad. Amma murmushi kawai Armad yayi tare da barin hankakan yayi nisa kafin ya ƙara yin amfani da ɗalasimin Kaban'shísu ya bayyana a ƙasansa. Sannu a hankali Armad yana bin wannan baƙin hankaka sai kawai ganinsa yayi a kusa da fadar sarki Bihanzin mai dauwamammen sara. Abin mamaki sai wannan hankaka ya ƙara shan kwana yabi jikin katangar wannan fada ya nufi yamma. Armad nada ragowar ɗalasimai biyu kacal saboda haka ya fara tunanin hanyar da zaibi ya kama wannan hankaka idan bai tsaya ba. Yana cikin tunani ya hangi hankakan ya tsaya a ƙarshen katangar ta ɓangaren yamma. Har wani waiwayo wa yake yana kallon Armad tamkar yana jiransa. A fusace Armad ya yanke shawarar yadda zaiyi ya kama wannan hankaka. Ya buɗe baki ya kira ɗalasimin Kaban'shìsu amma a wannan lokaci saiya canja maimakon ya bayyana a ƙasa saiya bayyana akan katangar wannan fadar dai-dai gefen wannan hankaka. Yana bayyana ya miƙa hannu ya damƙe jelar hankakan tare da finciko shi da niyyar jefashi cikin zobensa na sihiri. To amma bisa mamaki sai Armad yaji tamkar ya finciki dutsen uhudu. Ko motsi wannan baƙin hankaka baiyi ba. Hasalima kaɗa jelarsa kawai yake ba tare da ya waiwayo ya kalli Armad ba. A fusace Armad ya sanya ƙarfin shekarun izza dubu a hannunsa ya finciko hankakan dashi. Amma bisa mamaki ko motsi baƙin hankakan baiyiba. Armad ya haɗe gira yana tunanin maiya kamata yayi domin dai bazai iya amfani da hannun-aradu ba a wannan hali. Koba komai duk wanda yaji ƙarar saukar aradu wajen zai taho yaga ganshi, wanda hakan zai tona masa asiri. Armad na cikin tunani yaji jelar hankakan dake hannunsa ta motsa ta fincike shi. Kafin yayi wani abu hankakan ya jashi ƙasa daga saman wannan katanga sun faɗa cikin babban gidan sarautar daular Sisiya. Saida suka kwashe daƙiƙu suna faɗawa sannan suka isa ƙas, badan Armad yayi sauri ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya ba da tuni ya karairaye. Kafin ya miƙe hankakan ya tashi ya gudu. Armad ya tsaya yana nazarin wannan katanga. Kaurinta yakai ƙafa goma, kuma dukkaninta da duwatsu aka sarrafa ta. A tsaye kuwa takai zira'i casa'in. Lallai koda kuɗi ɓarawo bazaiyi ƙoƙarin haura wannan katanga ba. Yana cikin haka yaji motsin tafiya daga nesa haɗe da maganganu wanda sukai kama dana masu tsaron fadar. Nan take ya rufe ido domin jin yanayin izzarsu da kuma adadinsu da kuma ta inda suke tahowa. Amma bisa mamaki abu na farko da Armad ya fara ji wata sanyayyar izza ce mai ni'ima da faranta rai daga can gefensa ɓangaren arewa. Ya waiwaya ɓangaren tare da buɗe ido. To amma wajen cike da yake da bishiyun goba dana inubi wanda sukai masa duhuwa tayadda baza'a iya ganin wanda ke ciki ba daga nesa. Amma bisa mamaki Armad ya gane waye aciki. Murmushi kawai yayi tare da nufar wannan waje kai tsaye. Ƙanshi ne ya fara yi masa sallama, ƙanshin da yasha banban dana turare. Wannan ƙanshi mutun ɗaya ne kacal yake da irinsa a duk faɗin duniya. Armad ya tsaya kimanin taku uku kafin ya ƙarasa. Nan fa zuciyarsa ta fara bugawa kamar zata fasa ƙirjinsa. Bashi da cikakkiyar masaniyar maike faruwa amma yaji gumi na ƙoƙarin kwace masa. Sanyayyar murya wadda Armad ƴasanta sarai ita ce tayi masa sallama. "Mai yasa ka tsaya?" Armad ya fashe da murmushi ba tare da yasan dalili ba, ya amsa da cewa, "Mai yasa kike tsaye a duhu?" Muryar ta amsa masa da cewa, "ka bani kunya daka kasa kama hankaka guda ɗaya tak." Armad ya fashe da dariya yana cewa, "dama ke kika turoshi. Nasan zaki aikata. Amma meye alaƙar ƙabilarku da Hankakan-mutuwa?" Muryar taja dogon numfashi tare da yin ƴar ƙaramar dariya sannan ta fito daga cikin duhun. Kyakkyawar sura wadda babu kamarta ce ta bayyana. Wato gimbiya Zahra wadda aka fi sani da Nostaljiya Nára. "Baka yarda zoben dana baka ba kenan." Armad ya kalli zoben dake hannunsa sannan ya ɗago kai ya dube ta ya ce, "kona mutu dashi za'a binne ni." Nostaljiya na sanye da doguwar riga mai kwalliya da bezar gashin farin aku. Jikinta kamar lokaci na ƙarshe da Armad ya ganta acikin wancan kogo haske kawai yake yana bada ƙawa da armashi. Gashinta na kwance har gadon bayanta babu abinda yake sai sheƙi da ƙanshi. Babu kalmar da tafi dacewa da wannan gashi illa mudubi domin tsaf zakai kwalliya kana kallon kanka acikinsa. Armad ya buɗe baki zaiyi magana sai yaji masu gadin fadar sun matso kusa saboda haka ya fara lisaafin neman wajen ɓuya. Koda Nostaljiya ta fuskanci haka saita jashi izuwa cikin duhuwar wannan bishiyu. Da farko Armad yayi tunanin ɓuya zasu yi har sai ma'aikatan sun wuce amma sai kawai yaga sun wuce izuwa wata siriyar hanya wadda ta ɓulle izuwa wani shinge mai kama da lambu. Baki a buɗe Armad yaci gaba da kallon ikon ALLAH a yayinda Nostaljiya take jansa izuwa tsakiyar wannan fada. Abin mamaki ko mutun ɗaya basu gani ba a hanyarsu. Amma idan akai duba da cewa wannan fada gidan Nostaljiya ce kuma anan ta taso to ba abin mamaki bane. Ba daɗewa Armad ya tsinci kansa a wani kewayayyan sashi mai dogayen ɗakuna wanda aka gina bangwayensu da gilasai da yaƙutu. Dukkan wajajenda suka wuce babu wanda yakai wannan waje kyau da armashi. Hatta ƙasar wajen da lu'u-lu'u aka shimfiɗe ta. Nostaljiƴa taja Armad ɗaya daga cikin manyan ɗakunan dake kewaye da wajen. Suna shiga Armad ya tsinci kansa akan wani farin gilas da ruwa garai-garai yana gudana a ƙasansa. Kifaye masu haske kyawawa suna ta wasa acikin ruwa. Daga can gefe kuma wani ƙasaitaccen ƙaton gado ne wanda zai iya ɗaukan mutun aƙalla hamsin. Armad yai duba izuwa manyan gilasan da suka kewaye ɗakin inda ya hango wani ƙasaitaccen lambu a bayan ɗakin. Wata iska mai armashi na ƙarawa yanayin ni'ima. Nan take Armad ya tabbatarwa kansa bai taɓa tsintar kansa a waje mai kyawu da armashi irin wannan ba a rayuwarsa ta duniya. MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 97: Sammaci Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** ** Nostaljiya ce fara magana. "Ka jira ni anan ina zuwa." Sannan ta fice cikin sauri, tun yana hangen jar doguwar rigar data saka har ya daina. Ajiyar zuciya kawai yayi sannan ya faɗa kan wannan hamshaƙin gado wanda tunda yake bai taɓa yin arba da kamarsa ba a tsahon rayuwarsa. Abu kamar wasa jikinsa na dira akai ya nutse cikin laushi ai kuwa sai bacci ya ɗauke Armad. Yayi ta sharar bacci tsahon lokaci har saida rana ta faɗi. A lokacinda yaji muryar Nostaljiya na tashinsa. Da kyar ya buɗe ido yana gani hazo-hazo har dai ya wartsake. Bayan Nostaljiya Armad ya kula cewa akwai wasu kuyangi guda bakwai duk sanye da kaya ruwan kasa iri ɗaya sunyi sahu suna ta shigo da kayan ci da sha. Ƙanshi ne kawai yake tashi a ɗakin. "Ka tashi kayi wanka kaci abinci. Mahaifina yana so zaiyi magana dakai." Da akwai ragowar bacci a idon Armad amma koda yaji abinda Nostaljiya tace saiya miƙe zumbur gami da fara gumi. Ko sirikinka yawon bola yake akace zaku gaisa dashi sai kaji zufa ballantana ɗaya daga cikin mafi girman sarakuna a duniya. Cikin sauri Armad ya tambaye ta. "Da gaske kike koda wasa?" Nostaljiya ta fashe da ƴar ƙaramar dariya wadda ta dace da karfin ikonta. Bangon ɗakin na ɗaukan sautin kyakkyawar muryar ta. Nan take Armad yaji tamkar sarewa ake kaɗa masa. Lamarinda yasa ya faɗa cikin tunani ya manta da cewa shugaba mai dauwamammen sara yana jiransa. "Ka tashi yana jiranka?" Koda Armad yaga ga dukkan alamu da gaske take saiya miƙe cikin damuwa ya ce, "lafiya dai ko?" Nostaljiya ta haɗe rai cike da shagwaɓa. "Nima ban sani ba." Armad yai ajiyar zuciya a karo na uku sannan ya fara tunanin mai Bihanzin zai ce masa. Lallai da matsala. "A ina zanyi wankan? Kuma ni gaskiya..." Nostaljiya tayi wa Armad wani kallo mai cike da tsokana tana cewa, "Kai gaskiya me? Ga ƙoramar wanka can ta musamman nasa an haɗa maka." Tayi nuni izuwa wani ƙasaitaccen tafki mai ɗauke da filawowi a samansa. Wani tiriri ne mai alamun ni'ima ke tashi daga saman ruwan. Kana gani kasan an shirya shi ne domin wankan manya ƴaƴan sarauta. Armad ya juya ya nufi ƙofa yana ta zulumi. Har ya kusa kaiwa ƙofar sai yaji muryarta. "Idan ka fita kasan ta ina zaka zagaya?" Armad ya juyo fuska a murtuke yana cewa, "to kizo ki rakani mana." Nostaljiya na ganin yadda yake magana ta ƙara fashewa da dariya tana cewa, "kaci gaba da ɓata rai saina kirawo maka yaya Kiru da yaya Hasanu yanzu-yanzu." Armad ya buɗe baki zaiyi magana amma ya kasa ganin Nostaljiya ta taho tana rangwaɗa irin ta ƴaƴan sarakunan farko. Kwata-kwata ya manta dasu Kiru da Hasanu. Amma a wannan lokaci ya tuno da fafatawarsu da Kiru shekaru da dama da suka wuce a sanda ya fara fitowa nemawa mahaifiyarsa lafiya. Can bayan Nostaljiya ta fara jan hannusa izuwa waje ya samu ya tattaro kwarin gwiwarsa ya ce, "Kiru da Hasanu? Da fatan suna nan lafiya? Na daɗe bamu haɗu ba." Nostaljiya ta amsa da cewa, "ba wani nan. Da yaushe rabon da ka tambayesu? Kai dai kawai tsoron yaya Kiru kake ji. Dan kasan yanzu ya ƙara kwarewa matuƙa a fannin takobi." Armad na niyyar cewa shima ya ƙara ƙarfin takobinsa Nostaljiya ta fara jansa da gudu suna sassarfa. Duk kwanar da suka sha sai sun haɗu da kuyangi suna hidima, kuma duk wanda duka gansu sai sun zube a ƙasa suna gaisuwa. Nostaljiya ko a jikinta, Armad kuma tun yana amsawa harya gaji. Ga dukkan alamu zuwansa shi ne yasa aka kawo wannan kuyangi da yawa haka domin sanda yazo babu kowa a wajen. Suna cikin tafiya Armad yai ciki da wata tukunyar filawa garin ya kauce mata. Nan take ya fara jan hannun Nostaljiya yana cewa, "ki daina gudu. Wai wajen wankan nan tashi zaiyi ne? Kinga ban san hanya ba ina yi muku ɓarna." Amma Armad na magana Nostaljiya kawai ƙara jansa take tana dariya. "Komai ka fasa zan biya kar ka damu." Tun yana zuƙewa har ya saki jiki suka ringa zagayawa suna gudu acikin fadar nan suna shewa kamar wasu yara ƴan shekara goma. Bayan kimanin rabin sa'a suka iso wajen. Arnad ya waiwaya ya hango ɗakin da suka fito daga ciki sannan yaga hanyar da suka biyo, nan take ya gane cewa Nostaljiya na sane ta ringa zagaye dasu ba gaira ba dalili. Kamar ta gane mai yake tunani ta ce, "Eh mana. Ina sane na kewaya damu kaga yanzu kasan hanya baza ka ɓata ba. Kayi sauri ka shiga kai wanka tun kafin abba ya turo a ɗaukeka a tafi dakai." Armad najin wannan kalma ya fara azamar cire kaya zai faɗa cikin ruwan, amma a lokacin ya tuna tana wajen ya juya ya kalleta. "Anan zaki tsaya?" Nostaljiya ta haɗe rai. "Ko baka faɗa ba tafiya zanyi. Kawai dai kada ka nutse ka mutu ka barni." Armad ya fashe da dariya a karo na farko yana cewa, "kamar wata ke. Ɗan wannan ruwan ne zai kashe ni, mutuwa ta sai anyi shiri." "Nidai kayi sauri idan ba haka ba zan dawo na fito dakai." Nostaljiya ta juya ta fice. Armad ya jira yana murmushi har saida ta ɓace sannan ya ƙarasa cire kayansa ya afka cikin tafkin ya fara iyo. Ruwan ya kasance mai ɗumi dai-dai wanka. Sannan yana bada wani ƙanshi mai inganci. Filawowin kai kuwa na bada wani sinadari mai kama da sabulu wanda nan take ya wanke jikin Armad tas. Idan ta shawarar Armad ne kada ya futo daga cikin wannan daddaɗan ruwa har sai ya nutsu amma sarki na jiransa. Ba shiri ya fito ya maida rigarsa. Akan hanyarsa ta dawowa ya fara tunanin wanne kaya zaisa yaje dasu. Tambayoyi sama da ɗari suna ta yawo akansa akan menene dalilin da yasa Bihanzin ke nemansa. Kowanne dalili ya tuna sai yaji zuciyarsa ta buga. A lissafin Armad wannan ba wani abu bane illa sammaci. Cikin ƙanƙanin lokaci ya dawo ƙofar ɗakin daya kwanta aciki ɗazu. Yana shiga yai arba da Nostaljiya zaune tana jiransa zagaye da abinci. "Na baka minti goma ka shirya. Idan ka dawo kaci abincin." Armad ya zare ido cikin sauri yana cewa, "Yunwa nake ji fa." Nostaljiya ta canja fuska sannan ta fara magana cikin shagawaɓa. "Yana jiranka fa." Armad bai san sanda ya sanya kaya cikin ƴan daƙiƙu ba ya bita suka nufi nufi cikin fadar. Ranar da zaiyi arba da mai dauwamammen sara tazo. _______ Yekuwa Manazartar littafin Magajin Wilbafos Sarki Kurussa'ayi Ururu Sarki Bisa Doron Kasa na daya 1 yana Gaisheku ya kuma ya gaisheku Sannan yace a sanar daku cewa kwamitin Rubutun magajin wilbafos karkashin jagorancin Shuraih 99% sun canja tsarin Posting, A yanzu za'a runga posting Kullum sabanin zamanin baya da sai sati sati, A kowane Rana za'a runga yi maku post Daya, . Sako daga shalkwatar Ururu ta doron kasa na Uku, Sa hannun sarki Kurussa'ayi Ururu, Dhul ururu,Yarima Dumakisu Ururu,Uznu Ururu, Haruta Ururu,Maruta Ururu,deniz ururu ______ dafatan za ku bamu hadin kai 99% Babi na 98: Armad da Bihanzin ** Haka Armad da Nostaljiya suka yita keta cikin wannan fada suna wuce manyan gine-gine masu fasali daban- daban. Nostaljiya na ƙoƙarin yiwa Armad hira amma hankalinsa baya wajen harta gaji tayi shiru. Bayan wani ɗan lokaci suka iso harabar wani ƙaton ɗakin taro da aka kewaye da mutun-mutumin mutane kala-kala. Nostaljiya ta nuna ƙofar ɗakin tana cewa, "shiga ka jira aciki ina zuwa." Armad ya nufi ƙofar ɗakin ita kuma ta kewaya tabi hanyar da tabi ta bayan ɗakin. Ɗakin nada madaidaicin girma amma abubuwan dake cikinsa basu da yawa. Wani ƙaton teburi ne kewaye da kujeru a tsakiyar ɗakin. Ga dukkan alamu wannan ɗaki kullum acikin kula yake domin ko ƙura ɗaya babu. Komai kyalli kawai yake, shi kansa teburin na gilashi ne. Armad ya ja kujera ɗaya ya zauna yana jiran shigowar mai dauwamammen sara. Ba jimawa saiga Hasanu Sisiyu, yayan Noltaljiya, ya shigo. Fuskarsa babu murna kuma babu ɓacin rai. Ya dubi Armad ya ce, "kwana da yawa. Da fatan kana lafiya." Muryar Hasanu na nan ɗauke da ƙarfi da girma irin na sarakuna. Fuskarsa ta ƙara cika da kamala, kana ganinsa kasan ba'a zaune yake ba. Armad ya amsa da cewa, "ina nan lafiya. Da fatan na same ku lafiya?" Hasanu ya nemi waje ya zauna sannan ya dubi Armad ya ce, "bari na baka shawara a matsayi na na abokinka. Kada kayiwa mahaifinmu ƙarya domin duk abinda zaka faɗa zai san gaskiya kake faɗa ko ƙarya." Armad yai murmushi. "Ai dama bana shirin yin ƙarya." Hasanu ya girgiza kai kafin daga bisani yai murmushi sannan su koma hirar takobi. Hasanu yayi ta yiwa Armad tambayoyi akan fasahar takobinsa shima Armad yana masa har dai suka ji an buɗe ƙofar ɗakin. Wani babban mutun sanye da doguwar riga ƴar shara ya shigo cikin ɗakin. Nostaljiya na tafe a bayansa. Yana shigowa Hasanu ya miƙe tsaye tare da durƙusawa, shima Armad ya miƙe ya bashi girmansa. Mutumin na tafiya kamar ba tafiya yake ba, ƙafafunsa na motsawa cikin isa da iko irinta sarakunan aljanu. Idanunsa tsaye suke kan Armad yana nazarinsa. A tsaye zaka iya cewa wannan mutun ragowar samudawa ne domin aƙalla yakai zira'i ashirin. Wanda hakan ya ninka tsayin Armad sau wajen takwas. Yana shigowa ya nufi kujerar da aka tanada domin sa wacce ke gaba da dukkan sauran kujerun. Yana zama Hasanu da Nostaljiya suka fice suka barshi da Armad. Wannan mutun dai ba wani bane illa Bihanzin mai dauwamammen sara, ɗaya daga cikin sarakuna biyar na Jinzidal. Mutuminda akai ittifaƙi takobinsa tafi kowacce takobi ƙarfi a duniya. A wannan lokaci Armad ya nutsu tare da tsayawa yayi wa Bihanzin kallo na tsanaki. Bihanzin dai ya kasance mutun ne wanda kana kallonsa zaka san yayi matuƙar daɗewa a duniya. Idan kana kallonsa zaka ga tamkar shekarun ƙarni-ƙarni ne ke wucewa ta ruhinsa. Idanunsa a kafe suke kuma suna bada wani haske mai ɗauke da firgici da saka jimami. Fuskarsa nada tsayi da faɗi kamar dukkan jikinsa, sannan kuma cike take da farin gemu. Gashin kansa ma fari ne dogo mai tsayin gaske wanda har bayansa yake taɓawa. Hatta shi kansa gashin girar Bihanzin a lanƙwashe yake zubin takobinsa. Rigar dake jikinsa doguwar ƴar shara ce wadda ta bashi damar saƙale takobinsa a sauƙaƙe. Armad na ganin takobin nan yaji hankalinsa ya ɗugunzuma, tsigar jikinsa na tashi. Yanayin-izzar dake kewaye da takobin iri ɗaya ne sak dana Hankakan-mutuwan da Armad ya gani. Nan take Armad ya miƙa hannunsa kan takobinsa ba tare da ya sani ba. Tuni Armad ya manta da inda yake, babu abinda yake tunawa sai labarin da mahaifiyarsa ta gaya masa akan waccan ƙabila wadda aka manta da sunanta. Ƙabilar da tarihi ya nuna cewa saida ƙabilar Wilbafos da ƙabilar Ururu suka haɗa hannu da ƙarfe sannan suka ga bayanta. "Kada ka damu da takobi na. Ita wannan takobin tawa babu wanda take yadda dashi idanba ƴaƴa na ba." Muryar Bihanzin ce ta farfaɗo da Armad daga tunanin daya shiga. Amma duk da haka bai ɗauke idonsa daga kan takobin ba. Takobin dai bata da faɗi da yawa amma tafi tsayin zira'i uku. Lallai ba daban Bihanzi basamude bane da bazai iya ɗaukanta ba. Abin mamakin shi ne takobin har wani huci take tana kallon Armad tamkar tana jin mai ake cewa. Koda Bihanzin yaga Armad bai daina kallon takobin ba sai yaja rigarsa ya rufe ta yana cewa, "sunan wannan takobi tawa Bankái. Indai ka biya ta Bankái haka zatai ta tsokanarka har sai ta jaka izuwa faɗa." Mamaki ya ƙara rufe Armad yadda yaji Bihanzin yana maganar takobinsa yana bata suna kamar wata mai rai. Nan take Armad ya tuna yadda yayarsa Hidaya take yiwa takobinta magana. A sau da dama Armad yana yaro yakanyi tunanin ko Hidaya tsokanarsa kawai take amma takan ce masa takobin ta tana da ruhi nata na kanta kuma tana ji idan akai mata magana. Armad yai murmushi na girmamawa sannan ya ce, "barka da warhaka. Ina fatan ban ɓata maka ƙa'idarka ba dana shigo fadarka ba tare da izini ba." Bihanzin yai gyara murya haɗe da girgiza kai, lamarinda yasa muryar tayi kama da ana goga busasshen ƙashi a jikin bango. Dama dai muryar Bihanzin kaushi ne da ita, amma gyaran muryar da yayi shi ne yasa abin ya ƙara fitowa fili. A wannan lokaci Armad yayi ƙoƙarin jin yanayin-izzar Bihanzin amma bisa mamaki baiji komai ba sai wani sanyi mai ratsa ƙashi wanda ya banbanta da sanyin-babban-sihiri kuma ya banbanta da sanyin hunturu ko na ƙanƙara. Wannan sanyin da Armad yake ji yafi dana tsohon kabari. Nan take Armad ya daina ƙoƙarin jin yanayin-izzar Bihanzin amma duk da haka saida yaji ya fara rawar ɗari. Muryar Bihanzin ce ta ƙara farfaɗo dashi. "Kada ka damu, Magajin Wilbafos, tunda har ka shigo ba tare an kama ka ba ai gayyato ka akai." Armad ya zare ido cikin mamakin wannan magana, domin hakan na nuna Bihanzin na sane da shigowarsa. Nan take Armad ya buɗe baki zai tambayi Bihanzin amma sai Bihanzin ya riga shi magana. "Nakan ji yanayin-izzar abokan gaba tsahon tafiyar shekara guda tun ina ɗan shekara bakwai. A lokacin da na cika shekara takwas ina iya banbance mutane na gane ko su waye ta hanyar yanayin-izzarsu koda nisansu da inda nake yakai tafiyar shekara guda. Kaga bazai zama abin mamaki ba dan naji shigowar ka daula ta a lokacin da ka sauka daga jirgin Fataken-dare." Armad ya zare ido cikin tsananin al'ajabin ƙarfin izzar wannan halitta dake gabansa. Lallai ba'a zama sarkin Jinzidal a banza. Koda yake dama wannan shi ne karo na farko da Armad yai arba da ɗaya daga cikinsu. Idan dai har Bihanzin zaiji yanayin-izzar mutun kimanin nisan tafiyar shekara guda kuma ya gane waye, lallai babu wanda ya isa ya shigo wannan daula ba tare da saninsa ba. Kuma lallai ba abin mamaki bane dan Bihanzin yasan Armad shi ne Magajin Wilbafos. Kai tsaye Armad ya bugi ƙirji ya tambayi Bihanzin. "Mai kake buƙata daga gareni daka bari na shigo?" Chapter 99 & 100 MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 99: Armad da Bihanzin part 2 Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos "Hmm... " Bihanzin yaja dogon numfashi sannan yaci gaba da bayani. "Wilbafos kai kake neman wani abu a waje na ba ni nake nema a wajenka ba. Zaka sauƙaƙa mana wannan tattaunawa idan ka gayamin hakikanin mai ya kawo ka daula ta." Armad ya sunkui dakai yana tuno asalin abinda ya kawoshi wannan daula. Koma meye a bayan samarwa mahaifiyarsa lafiya yake kuma lallai abinda kawai ya kawo shi kenan. "Nazo neman shekarun izza domin yiwa mahaifiyata wadda take fama da cutar izza magani." Bihanzin ya danyi shiru kafin daga bisani ya ce, "Naji labarin cewa abinda ya fito dakai daga gida kenan shekaru uku da suka wuce. Indai wannan ne kaɗai buƙatarka to babu matsala, a yanzu zan warkarda mahaifiyarka. Koba komai bai wuce biyan bashi ba, domin har yanzu bamu biyaka fassarar dakai mana ba a waccan shekara." Armad ya zare ido tare da miƙewa tsaye cikin murna yana cewa, "da gaske kake? Lallai idan ka samarwa mahaifyata lafiya bani da yadda zanyi na iya sakamaka. Nagode." Bihanzin ya ɗaga hannu yana dakatar da Armad alamun bai gama magana ba. "Nasan akwai soyayya tsakanin ka da ƴata Nostaljiya, kuma bazan ce maka ka haƙura ba indai kana sonta, amma akwai abu guda ɗaya da nake so ka sani." Koda Bihanzin yazo nan a zancensa sai ya dubi Armad a nutse domin ya tabbatar yana tare dashi sannan yaci gaba. "Shi CIKAKKEN MUTUN shi ne wanda yake ɗaukan alhakin abu idan yasan shi ya jawo shi. Nostaljiya ta ɗau alhakin abinda ta aikata a wajen cinikin bayi kuma taƙi yadda a ɗora maka laifi. Idan za'a wanke ta a idon duniya to sai dai ta yadda ta auri Deniz Bizaya wanda a zahiri ba shi take so ba. To amma idan bata aure shi ba, hukumar Jinzidal zata yanke mata hukunci. Hatta ni kaina a matsayi na na babanta bazan iya kare ta daga sauran sarakunan Jinzidal ba, kuma idan na hana ayi mata hukunci, yaƙi ne zai afku. Idan kace kana sonta, shin zaka iya zama cikakken mutun ka ɗauki alhakin komai a kafaɗunka ka kare ta, kuma ka shiga yaƙi saboda ita? Idan dai har zaka iya wannan to ka cancanci ƴata, amma idan baza ka iya ba to ka manta kawai. Biyo ni." Bihanzin ya miƙe ya nufi ɗaya daga cikin ƙofofin dake kewaye da wannan ɗaki, Armad na biye dashi. Bihanzin na tunkarar ƙofar ta buɗe, Armad ya tsinci kansa a wani ƙaton fili mai yawan rairayi. Abin mamaki iskar dake kaɗawa acikin wajen ta banbanta data cikin dakin daya baro, tamkar wata duniya ta daban suka shiga. Take saboda sanyi Armad ya tuna da cewa yana da kayan sanyi a ajiye acikin zobensa. Amma kafin ya fito dasu sai kwatsam yaji yanayin ya fara canjawa, rairayin ya fara ɗaukan zafi kamar ana kunna masa wuta. Kafin kace meye wannan gumi ya fara gudu a fuskar Armad. Suka ci gaba da tafiya Bihanzin bai ce masa komai shi kuma bai tambaya ba. Amma abu kamar wasa taku bakwai bayan an fara zafin kawai sai ruwa ya ɓarke kamar da bakin kwarya. Armad ya tsaya ido a zare yana mamaki. Lallai akwai abin al'ajabi a tattare da wannan waje. Kuma tashin hankalin shi ne bai san inda Bihanzin yake ƙoƙarin kaishi ba. Yana cikin tunane-tunane yaji murya Bihanzin, "A cikin wannan waje duk bayan minti ɗaya yanayi yake canjawa. Kaga maimakon zafi da sanyi da damina da rani kowanne yazo a shekara sau ɗaya, kowannensu a wannan waje yana zuwa a kowacce rana sau dubu uku da ɗari shida. Acikin wannan waje nake ajiye wani kaso daga cikin shekarun izza ta na kwangila ta. Ban san shekara nawa mahaifiyarka take buƙata ba amma nayi maka alƙawarin bata shekarun izza dubu goma zuwa ashrin. Fito da ita ka ajiye ta anan." Bihanzin ya nunawa Armad tsakiyar yashi inda ruwa ya ɗan taru. Da farko Armad ya fara mamakin yadda akai Bihanzin yasan mahaifiyarsa na cikin zoben dake hannunsa amma kuma ya tuna komai ma zai iya faruwa indai ana maganar sarki Bihanzin sabida haka babu wani abin mamaki. Nan take Armad ya futo da mahaifiyarsa sanye cikin fararen kaya kamar tana bacci. Amma yaƙi yadda ya ajiƴe ta a ƙasa har saida Bihanzin ya tafa hannunsa wani gado ya bayyana. Bayan wasu ɗalasimai da Bihanzin ya kira a zuci sai kawai wani ƙatoton shaiɗanin aljani ya bayyana. A tsakiyar kan aljanin akwai ƙahunhuna guda

Chapter 32 of 33