Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙasa ta uku har ya zuwa sanda suka haɗu dasu Zahra da kuma yadda ya ƙare a wannan waje. Sai dai kuma abu ɗaya; duk da haka bai gaya mata tsakaninsu da Masanin-ƙasa ba dangane da sunansa na gaskiya ba. Ya kula sosai wajen labarinsa, tayadda shidai bai ƙara yi ƙaryar sunansa ba, amma kuma bai gaya mata sunansa Wilbafos ba! Kawai yai shiru yabar wajen a haka. Ita ma kuma, tunda ta fuskanci baya son maganar, sai kawai ta share. Wani abu da Armad ya kula dashi shi ne, tunda farko daya ambaci sunan Tirifil-fakta fuskarta ta canja sosai, sai dai tunda batai magana ba shima bai ce mata komai ba, kawai ya ci gaba da zayyana labarinsa. Bayanda ya gama sai yai shiru inda ya kalli gabansa daidai wajen wannan hijabi. Ya dubi Núsí da niyyar ya tambaye ta me ake buƙata mutun yayi kafin ace ya wuce wannan waje, amma kafin yayi magana yaji muryarta tana cewa, ”Tirifilfakta……!!! ”Lallai kana da ƙarfin aniya…. amma shin kasan meka ɗaukowa kanka kuwa!” Tayi shiru gami da ajiyar zuciya tana kallon Armad cikin mamaki. Can bayan daƙiƙu ta ƙara numfasawa tace ”Bazan kashe maka gwiwa ba, amma abu ɗaya daya kamata ka fara sani akan wannan alamari shi ne; babu wani mahaluƙi, rayayye ko matacce, tun daga kan doron ƙasa ta farko harya zuwa doron ƙasa ta bakwai daya kai mai wannan suna yawan masu so su cimmasa. ”Wasu maƙiya wasu masoya. Babu wanda yasan daɗewar wannan suna a doron ƙasa babu kuma wanda yasan wanene ko kuma ya yake. Kai hikayoyi da dama ma sun rawaito cewa daɗewar sunan tamkar daɗewar ƙasashe bakwai ne. ”An rawaito a mas’alolin farkon lokaci, cewa shi shi kaɗai ne mutumin da Ma’abota Ururu suka taɓa saka kyauta ga duk wanda ya kamo ko kuma ya bayarda wani bayani daya kai aka kamashi. ”Kimanin shekaru ashrin da suka wuce Dul’ururu ya saka hannu kan dokar kyauta akansa. ”Kayi sani cewa a halin yanzu zaka iya cewa duk duniya babu wani mahaluƙi kai tsaye ko kuma ba kai tsaye ba, yana sane ko kuma baya sane, da baya neman mai wannan suna. ”Da dama su na nemansa ne saboda kyautar da za’a Bawa duk wanda ya kawo shi, ko kuma kawai ya bada wani bayani daya taimaka aka iya cimmasa. ”To, zata iya yiwuwa wasu su na da tsohuwar ƙiyayya, wasu kuma akasin haka, amma dai a zahirin gaskiya zaka iya cewa mutanen da suka san Tirifil-fakta ko kuma wani abu muhimmi akansa ƙalilan ne, domin har sunfi adadin jaki mai ƙaho yawa.” ”Shin yanzu ka fahimci wa kake nema?” Ta rufe jawabinta da tambaya. To a wannan lokaci bayan ta gama duk wannan jawabi Armad na tsaye yana kallonta, wanda a sannan ne ya bata amsar da bata taɓa tsammani ba. Inda yayi murmushi gami da cewa, ”ba matsala, kawai yana nuna ina da buƙatar na fi ƙarfin duk ragowar masu neman nasa ko?” Fuskarsa cike da murmushi ya ci gaba da cewa, ”ta yaya ake wuce matakin wannan jarabawa?” Ya tambaya ya na nufat gurin wannan hijabi cikin sauri da kwanciyar hankali tamkar wanda zai shiga cikin ɗakinsa. Sai dai kuma a wannan lokaci ne Núsí wadda tun amsar daya bata bakinta ke buɗe cike da mamaki, ta taso da sauri inda ba tare da cewa komai ba ta riƙo hannunsa da sauri a dai-dai lokacinda yake ƙoƙarin miƙa hannu cikin wannan waje. Ta janyoshi da ƙarfin tsiya inda har saida yayi tagataga gami da yowa baya kamar zai faɗi. Tun kafin Armad ya gama nutsuwa ya fara magana cikin mamaki, ”aargh.. Yaya?” Nan take ta rufeshi da masifa, ”kasha giya ne! hannuka yana taɓa wancan waje zaka ƙara shiga yanayin daka shiga ɗazu. ”Dama gashi bawai gama farfaɗowa kai ba. ”Kuma nidai bani da wani abu daya rage dazan iya ceto ka idan haka ta faru. ”Saboda haka ya kamata ka nutsu, mu zauna muyi tunani akan mai ya kamata muyi.” Har a lokacin da take magana Armad idonsa na kafe akan wannan waje. Shi dai waje ne wanda babu wani abu ban tsoro a tattare dashi ko kaɗan. Kai hasali ma babu komai face dai kawai tamkar wani layi ne aka sa aka raba tsandaurin ƙasar zuwa gida biyu; ɗaya, inda su Armad ke tsaye, ƙasar nada launin ruwa ƙasa kamar a ko’ina, sai kuma ɗan rairayi daya rufe ta, ɗaya kuma wanda ke gabansu shi ma fili ne kawai kamar na farkon, sai dai kawai ƙasar wajen launinta na musamman ne, imda take da launin ja mai gauraye da shuɗi. Wannan kala ta ja-da-shuɗi ta ɗau haske sosai, inda har kyalli take tana zubarda haske inda ya maida iskar dake yawo a saman ƙasar irin kalar. Aƙa’ida duk wani tsarar Armad daya kalli wannan waje ya kamata yaji nauyi yana tashi acikin zuciyarsa, kamar yadda ita ma Núsí take ji. Amma abinda bata sani ba shi ne Armad baya jin komai ko kaɗan daga kallon wannan waje, kuma hasalima ji harga ALLAH shi ji yake acikin ran nasa tamkar ɗakin nasa zai shiga. Bayan Armad ya gama kallon wannan waje, bai bata amsar duk maganganun da tai masa ba, sai kawai ya dubeta, gami yi mata murmushi, wanda ke ƙunshe da godiya na kula da take nuna masa. Amma gama murmushi keda wuya, shi kansa bai san mai yasa ba, kawai yaji tsananin soyayyar ya tashi ya shiga wannan wuri, tamkar wanda wani abu acikin wajen yake kiransa. Armad ya ƙara juyawa ya kalleta gami da cewa, ”bari na gwada, sau ɗaya kurum, idam baiba, saimu canja wata shawarar!” Tayi niyya, kuma harta buɗe baki domin gaya masa wani abun, duk don ta gaya masa cewa bazai yiwuba, amma ina kafin ma tayi wani abu tunu Arnad ya kwace ya nufi wannan guri gadan-gadan, tamkar wanda ake jansa. Nan take ta miƙe ta kuma bishi, amma kafin ta cimmasa tuni ya afka da ƙafafunsa biyu cikin wannan waje! Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 19: sa hannun sarki dul ururu Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos . . Saboda saurin da Nusi ta taso dashi, duk dan ta riƙo Armad cikin ƙoƙarinta na ta hanashi sanya ƙafa acikin wannan waje, tana ganin ya riga ya faɗa sai taci birki da ƙarfin tsiya domin kada ita ma ta faɗa ayi biyu babu. Amma ina, dama a lokacin bai wuce sauran kamu uku ba tsakaninsu da Armad ba, saboda haka duk da cijewar da tayi saida ta ita ma ta afka. Duk da cewar ba dukkan jikinta bane ya faɗa ba, amma ƙafarta ta dama tuni ta shiga wajen. Nan take ta rufe ido cikin takaici, babu abunda take tambayar kanta face, ”mai yasa…mai yasa… duk akan wannan yaro da bai ma san banbancin fari da baƙi ba, nake neman halaka kaina….” Wannan shi ne tunaninda yake ta juyawa a ranta, a lokacin da ta gano cewa ta rasa komai data daɗe tana tanadi, duk acikin ƙanƙanin lokaci, sannan kuma ga rayuwarta nan ma tana kusantar halaka. Amma wani abun mamaki ga ita kanta shi ne, gashi dai lallai ya kamata tayi baƙin ciki gameda yadda abubuwa suka juya mata, kuma babu wanda ya kamata ta zarga face Armad, amma ko kaɗan bata jin dana sani acikin zuciyarta. Hasalima ji take tamkar tayi wani babban abu mai matuƙar muhimmanci a gareta, tamkar sauke wajibi daga cikin wajibai. Saboda irin wannan tunani da take, kawai saita rufe idanunta cikin ɗimuwa a wani yanayi na bankwana da duniya. Ƙafarta tata tana shiga cikin wata iska mai tsananin ƙarfin gaske ta finciko dukkan jikinta daga inda yake izuwa cikin wannan waje. Nan take ta buɗe ido, sanda taji ta a sama tana lilo tana nufar ƙasa, ƙiris ta faɗo. Abu ne sananne cewa acikin waje da suke kira da Hijabi, tsananin hawa-hawa ne, kuma yana mafi ƙarfi akan ƙasar wajen. Saboda haka ta fara ƙoƙarin yin wata dabarar, domin kada ta taɓa ƙasa, amma ina kafin tayi wani abu tuni baifi saura kamu biyu ba a tsakaninsu da ƙasa ba. Idanunta a rufe tana jira ta fuskanci irin wannan uƙuba data riga ta sani aduk lokacinda tayi arba da wannan guri, kwatsam kawai sai jitayi komai ya tsaya tsak aduniya babu abinda ke motsi. Kai a yadda taji ma, hatta zuciyarta saida ta tsaya da bugawa na taƙi ɗaya kafin ta ci gaba. Nan take ta buɗe ido gami da duba izuwa muhallinta domin ganin mai yake faruwa. Nan kuwa idanunta sukai arba da Armad wanda ke riƙe da ita akan iska. Bata san lokacinda tsananin mamaki ya kamata ba, a sanda ta juya ta kuma tabbatar da cewa ƙafafun Armad ɗin a tsaye suke cak akan wannan waje babu kuma ko alamun girgiza a tattare dashi. Kai hasalima babu wani alamun yana kan wani waje na musamman ko kuma mai sharri. Armad yayi murmushi mai ɗan ɗauke da yarinta ta dai-dai shekarunsa, inda baice komai ba, bai kuma tsaya ba, nan take ya ci gaba da tafiyarsa a wannan waje. Duk inda Armad ya taka saiya ƙara yin tsananin ja sosai, tayadda har sai kore-koren dake gauraye da launin jan ya ɓace ɓat, amma hakan ko kaɗan baya ko alamun cutar dashi, hasalima tamkar sauri yake ƙara masa. Tuni mamakin daya haɗiye Núsí ya rikiɗe ya koma firgici, inda idanunta suka fara karkarwa saboda firgici. Ba komai bane ya jawo haka ba illa abinda take tunani acikin ranta, ”mai ke faruwa, hatta sinadarin Negrinkin cikin wannan waje ma baya masa komai, maimakon su rinƙa tureshi, shi kuma yana ƙoƙari akan su karɓeshi, amma wannnan yaro tamkar nemansa suke, tamkar sune suke buƙatarsa bashi bane yake buƙatarsu ba…. “Wai haƙiƙanin wane ne wannan yaro, kuma maike faruwa…kuma dai na tabbatar ba mafarki nake ba!!!” To abinda bata sani ba shi ne Armad yana shiga wajen, yaji wannan mutun-mutumi da suka haɗa ido dashi a baya ya ƙara motsawa, inda wani abu ya faru cikin tsananin sauri, wanda lallai da Armad ɗin ya ƙifta ido sau ɗaya kacal to da lallai bazai gani ba. Abinda kuwa ya faru shi ne; Armad na sanya ƙafa cikin wannan guri yaji tamkar ya faɗa cikin garwashi. Tsananin raɗaɗi ya gauraye jikinsa, tayadda kafin yayi wani abu tuni ƙafafunsa sun kasa ɗaukarsa kuma sun fara neman durƙushewa. To amma a wannan lokaci ne wannan mutunmutumi ya motsa cikin tsananin sauri tayadda inka ƙifta ido sai ɗaya kaɗai bazaka lura da faruwar abin ba. Amma wannan motsawa da yayi ita ce tasa iskar dake kewaye dashi ta motsa, inda wata ƴar ƙaramar guguwa ta kaɗa inda kafin kace meye wannan tuni ta gauraye wajen. Armad bazai taɓa iya bayanin maiya faru ba, ko kuma taya ya abinda ya faru ya faru ba, amma zai iya rantsewa cewa acikin wannan iska data giftashi wadda ta fita daga jikin wannan mutun-mutumi, akwai wani ‘umarni’, irin umarnin da babu wata halitta mai rai ko mara rai data isa ta saɓashi. Armad baisan haƙiƙanin meke cikin wannan umarni ba, amma lallai zai iya rantsewa cewa an bada wannan umarni. Wanda kuma faruwar hakan keda wuya yaji duk abinda yake ji a jikinsa ya kau, babu ko alamun ciwo ko zafi. Kuma hakan na gama faruwa hankalinsa ya dawo jikinsa inda yaga Núsí tana ƙoƙarin faɗuwa, shi kuma yayi sauri wajan tallafo ta. Su na tafiya tana riƙe a hannun nasa, inda shi kuma yake nufar ɗaya ɓangaren domin fita daga wajen. Kuma koda yaga irin yanayi na mamaki da firgici data shiga, sai kawai ya fara mata bayanin dukkanin abinda ya faru, daga sanda ya taka ƙafarsa har ya zuwa wannan lokacin. To dama dukkanin wajan da zasu wuce ɗin wanda ake kira da Hijabin, baifi taku ashirin ba, saboda haka a daidai kusan lokacin da suke niyyar ficewa ya hattama zayyana mata abinda ya faru. Haka dai suka ƙarasa takunsu na ashirin da ɗaya wanda ya ƙarasa fitar dasu daga wannan waje gaba ɗaya. Inda ya ajiye ta gami da kyara musu waje dominsu zauna. Ƙasar dake bayan wannan waje tana da banbanci da wadda suka baro; tayadda duk inda ka duba zaka ga alamun rayuwa. Kamarsu tsirrrai da namun daji, kuma gaba kaɗan garesu daji ne katafare. Núsí ta ɓoye mamakin ta kuma ta haɗiye tambayoyinta game da Armad, domin a ɗan iya lokacinda suka yi dashi da kuma abubuwan daya gaya mata, ta fahimci cewa lallai akwai abubuwa na ban al’ajabi a tattare da wannan yaro. Kuma babban abin mamakin shi ne, shi kansa ga dukkan alamu bashi da masaniya akan wannan abubuwa. Saboda haka taji a ranta bata san ta matsa masa da tambaya. Amma wani abu guda ɗaya wanda dole ne shi da ita su warware shi ne, a wanne matsayi suke a yanzu. Nanfa ta buɗe baki, fuskarta cike da murmushi mai alamun godiya tace, ”nagode Armad, daka wutar dani wannan jarabawa, domin kuwa ban taɓa tsammanin wucewa da wuri haka ba. ”Amma wani hanzari ba gudu ba, naji labarinka kuma naji aniyarka ta neman Tarifil-fakta. ”Sannan kuma na gaya maka kaɗan daga cikin irin hatsarinda wannan aniya taka ke ciki. Amma daga alamun daka nuna min naga baka da niyyar canja ra’ayi. ”To amma naga lallai bakai kama da wawa ba, saboda haka nasan daga ɗan abinda na gaya maka da kuma wanda ka sani, ya isheka ka gane cewa a yadda kake ɗinnan babu abinda zaka iya. A taƙaice dai ina ganin baka da ƘARFIN DA ZAKA IYA NEMO SHI A YANZU!” Data zo nan a zancenta, sai ta ɗan tsaya, saboda ganin da tayi ya ɗago kai yana kallonta. Duk da ba tayi mamaki ba sosai, kuma bata daɗe ba ta ci gaba da bayani ba, amma abinda bata sani ba shi ne, dalilin da yasa ya ɗago kai shi ne, ta taɓa dai-dai inda yake masa ƙaiƙayi. ”Kamar yadda kaji a labari na ina daga cikin manyan ɗalibai a mazhabar Maikironomada, saboda haka idan kana so zan iya zuwa dakai na samar maka wajen fara horo!” To daya ke faɗuwa ce tazo dai-dai da zama, Armad bai tsaya ɓata lokaci ba ya amince ɗa wannan shawara. Inda suka zauna a wannan waje tsahon kwanaki biyu suna hutawa. Suka kafa ɗan ƙaramin tanti, inda suka zauna aciki. Duk da cewa bata kulashi sosai, amma hakan baisa ya rage bata labarai ba wanda mafiya yawansu na doron ƙasa ta uku ne, da kuma yi mata tambayoyi akan yaya ƙasar Maikironomada take, kuma yaya irin horonsu yake. A rana ta uku suka ɗaura siddi akan wata alfadara da suka kama a ranar farko, kuma suka nufi gabas ta cikin wannnan daji dake gabansu. Duk da cewa sun ɗauki sama da sati ɗaya suna tafiya acikin wannan daji, amma babu wani abu muhimmi daya faru a yayin tafiyarsu. A kwana na tara suka iso wani ɗan ƙauye mai yawan bukkoki. Duk da akwai ƙofar gari amma babu wani caje da ake kafin shiga wannan ƙauye, kuma babu wata doka ta musamman. Saboda haka basu sha wata wahala ba suka shiga kuma kai tsaye Núsí ta jasu wani ɗan waje da aka gina da rumbu. Daga saman ƙofar shigar an rubuta, ‘wajan shan furar matafiya’. Har sun kusa zuwa sai ta buɗe baki ta ce, ”shekaru uku da suka wuce kafin na fara wannan jarabawa, anan nasha fura da zan wuce. ”Musha fura anan, kafin mu nemi wajan kwana a wannan gari saboda…….” Dai-dai sanda tazo nan a zancenta tana gabda shiga ƙofar wannan waje, amma saita tsaya cak ta kuma yi sauri ta juya. Ba komai bane ya jawo haka ba face Armad wanda ya tsaya cak, fuskarsa a kafe akan bangon wannan wuri na ɓangaren kudu. Kana ganinsa kasan acikin firgici yake, jikinsa kaf karkarwa yake amma kuma wani babban abin mamaki shi ne idanunsa a rufe suke ruf. Kuma ƙarara ƙoƙari yake tayi ya buɗe su harda hannayensa biyu amma ya kasa. Bata tsaya ɓata lokaci ba ko kaɗan, ta juyo ta kuma nufoshi da sauri, sannan kuma a lokaci guda, idanunta suka bi dai-dai fuskar ta Armad take kafe a jikin bangon. Ba komai ta gani ba, illa takardar da kusan kowa a wannan doron ƙasa ta huɗu ya sani. Wadda kuwa ita ce takardar da Sarki Dul’Ururu ya saka hannu akai. Wadda ita ce ke ƙunshe da Kyaututtukan da za’a bawa duk wanda ya kawo ko kuma ya bada wani bayani daya taimaka aka kama Tarifil-Fakta. Sannan kuma da wasu hanyoyi da za’a iya ganeshi. Sai kuma sa hannun sarki bisa doron ƙasa ta biyu, wato Dul’Ururu, wanda ke jaddada ingancin wannan takarda! Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 20: magajin wilbafos Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Minti ɗaya da daƙiƙa ashirin kafin rufewar idon Armad. Tafiya yake yana dube-dube hagu da dama, badan komai ba sai dan irin kyawun muhalli da yaga wannan ƙauye nada shi. Duk da cewa wannan ƙauye bashi da girma, amma duk inda ka duba akan hanyoyinsu sunyi shuka ta korayen tsirrai masu sanyaya ido. Sannan kuma ga filawowi masu launi daban-daban ko ina ka kalla. Armad bai san mai yasa ba, amma yana shiga wannan ƙauye yaji hankalinsa yayi matuƙar kwanciya tamkar tsumma a randa. Wani farin ciki da baisan daga ina yake ba ya fara lulluɓeshi. To yana cikin wannan hali ne idanunsa suka kai ga kan wata ƴar takarda mai launin ja, kuma tana da matsakaicin faɗi. Acikin wannan takarda akwai ɓangarori guda uku; na farko yana magana kamar hakaTarifil-fakta mutun ne mai tsananin hatsari ga zaman lafiyar al'umma. Saboda haka maɗaukakiyar masarauta take tabbatarwa da jama'a su kwantar da hankulansu domin zatai duk wata mai yiwuwa wajen ganin cewa an kama shi. Ɓangare na biyu kuma yana magana ne akan kyaututtukan da aka tanada ga duk wanda ya kawoshi ko kuma ya samarda jawabi daya taimaka aka cimmasa, kamar hakaDuk wanda ya kamoshi ko kuma ya bayarda wani bayani daya taimaka aka cimmasa, to yana da waɗannan kyatuttuka; 1-Za'a ɗaga darajarsa data ƙabilarsa zuwa doron ƙasa ta farko! 2-Za kuma a bashi mafificin muƙami a wannan ƙabila kowacce ce! 3-Za'a ƙarfafa ruhinsa dana zuriyarsa da ɗaya daga cikin huɗu na Izzan dake Maɗaukakiyar masarauta! Ɓangare na uku kuma yana bayani ne akan alamonin yadda za'a gane shi; Yana da tambarin Miyura a goshinsa madauwami, wanda baya taɓa ɓacewa. A kewaye da wannan tambarin akwai hoton wata guda uku; ɗaya daren tara, na biyun daren sha takwas sai kuma na ƙarshe daren ashirin da bakwai! Waɗannan watannin guda uku su na motsawa tamkar masu rai, inda suke kewaye wannan Miyura! Ga hoton wannan Miyura! Sai kuma daga ƙasa aka bayarda hoton Miyurar da ake magana akai! Ɓangare na ƙarshe kuma yana ƙunshe da sa hannu na sarki bisa doron ƙasa ta biyu, wato Dul'Ururu. A gabansa kuma kaɗan akwai alamun fuska, wadda ba abinda ake gani acikinta face ɓaƙaƙen idanuwa guda biyu. Waɗanda idan ka kula sosai zaka ga wasu lokutan idan wani yazo yana karanta wannan takarda suna motsawa su kalleshi. Sai dai kuma ba kowa ba, domin wani ko mai duban da zaiyi ba zasu taɓa nuna alamun motsi ba, tamkar ma babu wanda ke wajan. Sai kuma wani lokaci da idanun suke motsi shi ne, idan wani yazo yai magana a gabansu cewa yana da bayani akan Tirifil-fakta, to su na motsawa su kuma kalli cikin idanun mutun. Kuma kamar yadda kowa ya sani, a gaban waɗannan idanu baka da buƙatar ka mayarda bayaninka zuwa kalmomi, domin kallo ɗaya kacal suke da buƙatar suyi maka su zaƙulo wannan bayani daga cikin kwakwalka ba tare ma ka sani ba. Abu na ƙarshe a jikin wannan takarda shi ne tambari mai ɗauke zanen ƙasa bakwai wanda a samansa yake da hoton fada. Wannan ba wani tambari ba ne, illa na maɗaukakiyar masarauta. To ko mai yasa idanun Armad suka rufe ruf, kuma duk da ya sa hannu amma ya kasa buɗe su. Abinda ya faru shi ne, Armad na zuwa ƙarshen wannan takarda bayan ya gama karanta jawaban saman, kuma tuni ya ƙara fahimtar abinda Núsí ta gaya masa akan girman al'amarin daya ɗauko da kuma kaɗan daga cikin wane ne Tarifil-fakta. Sai idanunsa suka nufi kan ɓangare na ƙarshe a jikin wannan takarda, wanda ke ƙunshe da alamun wannan fuska da kuma waɗannan baƙaƙen idanu guda biyu. Amma a wannan lokaci ne, ya ji kawai idanunsa da kansu sun fara rufewa da kansu, kuma kafin yayi wani abu yaji suna ƙoƙarin rufewa su kaɗai. Nan take ya fara ƙoƙarin rufe su, amma ina. A wannan lokaci ne yaji tamkar wata Izza mara iyaka ta taso daga jikin wannan mutun-mutumi dake cikin tambarin Miyura dake goshinsa,ta ƙarawa idanun nasa sauri, inda cikin ƙiftawar ido suka rufe ruf. Sannan kuma wannan Izza ta kewaye su, gami da tabbatar da cewa sun zauna a rufe. Armad bai yadda da abinda ke faruwa ba, saboda haka nan take ya fara ƙoƙarin buɗe idon nasa. Amma ina ko motsi basuyi ba. Sai dai kuma amma a wannan lokaci ne iskar dake kewaye da wannan baƙaƙen idanu a jikin wannan takarda ta kaɗa. Wanda nan take duk da cewa idanun Armad a rufe suke ya fara jin wata irin Izza wadda tunda yake a rayuwarsa bai taɓa jin irinta ba ko da a mafarki kuwa, ta fara tashi daga wannan idanu. Kuma inda idanunsa a buɗe suke da yaga abinda Núsí take gani baki a buɗe a wannan lokaci. Domin kuwa wannan idanu sun fara fitarda wani baƙi hayaƙi, wanda kafin kace meye wannan ya cika wannnan waje ta yadda da kyar kake ganin waye a gabanka. Kafin kace meye wannan kusan dukkanin mutanen wannan ƙauye sun firfito daga gidajensu cikin firgici, kasancewar sun san cewa indai wannan idanu suka fara fitar da hayaƙi to yana nuna cewa kenan akwai sanarwa ta musamman daga maɗaukakiyar masarauta. Tuni wannan baƙaƙen idanu suka fara sheƙi, suna ƙara baƙi. Kafin kace meye wannan tuni wannan ƙauye ya fara duhu duk kuwa da cewa rana ce tsaka. Tamkar baƙaƙen idanuwan suna zuƙe haske gaba ɗayan ƙauyen ne! Bayan kimanin daƙiƙa talatin, sai kawai suka ga wannan hayaƙi ya fara tattaruwa yana dunƙulewa a waje ɗaya. Kafin kace waye wannan ya haɗe a waje ɗaya ya dunƙule, inda nan take ya fara juyawa da ƙarfin gaske, ta yadda idan ka fiya ƙura masa ido kaima sai kaji kanka ya fara juyawa. Cikin daƙiƙa bakwai wannan hayaƙi ya rikiɗe ya koma siffar ƙararrawa. Baƙar ƙatuwar ƙararrawa, wadda idan ka ɗaga kai, sai kaga tamkar ta rufe dukkanin sararin samaniya. A dai-dai wannan lokaci tuni Núsí ta isa kan Armad wanda tuni abinda ke faruwa a cikin kwakwalwar sa yasa yama daina ƙoƙari buɗe idon nasa, ya tsaya kawai jikinsa yana karkarwa. Dukkanin abubuwan dake faruwa, idanun Armad a rufe suke, saboda haka bai san da dama daga abubuwan dake faruwa ba. Sai dai kuma shima acikin ruhinsa yana ganin abinda babu wanda yake gani saishi. Acikin kwakwalwar tasa yana ganin wata duniya ce ta musamman, inda yake tsaye kamar matacce, wannan hayaƙi dake tashi daga wannan baƙaƙen idanu guda biyu yazo ya fara ƙoƙarin buɗe idon nasa ta ƙarfin tsiya, tamkar wanda rayuwarsa da samuwar sa ya wanzu akan wani abu dake cikin idanun na Armad. To amma kuma a wannan lokaci ne wannan mutunmutumi da hotonsa ya bayyana acikin kwakwalwar Armad wanda ke ƙoƙarin hanashi buɗe idon nasa ya ɗaga hannunsa inda wata doguwar takobi, wadda takai tsayinsa ta bayyana aciki. Wanda kuma nan take yayi kan wannan hayaƙi da sara. To sai dai kuma a dai-dai lokacin ne wannan baƙin hayaƙi ya juye izuwa halitta mai kai tara. A jikin kowanne kai akwai baƙaƙen idanu guda biyu, wanda hakan ya sa baƙaƙen idanu guda gima sha takwas suka bayyana. Armad dai na tsaye acikin wannan duniya kamar ɗan kallo, mahaukacin azababben yaƙi ya kaure. Dukkaninsu daga ita wannan halittar, har shi mutunmutumin babu wanda hotonsa ya fita sosai yadda Armad zai gane kamanni sosai, amma duk da haka yana jin irin ƙarfin tsananin tsana da azabar yaƙi ta har abada dake tsakanin sifofin guda biyu. A waje kuma acikin duniyar mutane, Núsí tana tsaye tana ta ƙoƙarin farkar da Armad, amma ina, baya ko alamun jinta, kuma har wannan lokaci idanunsa a rufe suke. Nusi na tsaye inda a dai-dai lokacinda wannan ƙararrawa ta gama haɗuwa ta ɗaga kai sama, kuma ta samu cewa bisa mamaki ƙararrawar tana dai-dai samanta. A saboda haka nema dukkan mutanen wannan ƙauye da suka firfito, idan suka ɗaga kansu sama suka kalli wannan ƙararrawa sai kuma su saukar da kai kuma su dubi su Armad domin ganin mai ke faruwa. Wanda kuma, abinka da ƙauye kowa yasan kowa, saboda haka nan take maganganu suka fara tashi ana nunosu ana cewa baƙi ne suka shigo. Wannan abu dake faruwa bai ɗau hankalin mafi yawa daga cikin jama'ar ƙauyen ba, domin da dama har a lokacin kansu yana kan wannan ƙararrawa kuma su na jira su ji wane bayani ne zai sauka daga maɗaukakiyar masarauta a wannan lokaci. To kowa dai yana tsaye yayi kasake, wasu kuma hankalinsu nakan Armad wanda suke tunanin mai yasa ya rufe idonsa. Wasu ma tuni sun fara tunanin ai makaho ne, amma daga bisani daga bisani suka ƙara ƙura masa ido suka ga kwata-kwata baiyi kama da makahon ba. Sannan kuma akwai wasu jijiyoyi a zagayen idanun nasa dake ƙara kumbura wanda ke nuna alamun cewa idanun nasa da ƙarfi aka rufesu, wato bashi ya rufe su ba. Ana cikin wannan hali ne, ƙararrawar nan tai ƙara sau ɗaya, wanda hakan yasa duk mutanenda ke wajen suka zube akan gwiwowinsu. Hatta Núsí sai da ta zube ba tare da ta sani ba, tamkar wadda bata da iko da jikinta. To amma wani abu wanda yasa dukkanin mutanen wajen suka maida hankalinsu kan Armad cikin mamaki, shi ne ko kaɗan Armad bai durƙusa ba. Hasalima hatta Nusi da taga mutane nata kallonsa, saida ta fara ƙoƙari fizgarsa dan shima ya durƙusa amma ina, tamkar wanda take jan bishiyar kuka. Wannan ƙararrawa ta ƙara kaɗawa ta biyu, inda wata murya mai ɗauke da wata irin irin Izza wadda ke tursasawa kunne sauraro kuma ta tursasawa kwakwalwa fahimta ta fara jawabi, ''sanarwa zuwa ga dukkan ma'abota dukkan ma'abota ƙasashen ƙasa. ''Wani Magajin Wilbafos ɗin ya sake bayyana. ''Yana da tambarin Miyura mai tsarin dauwama a goshinsa. ''Mai irin wannan tsari'' Wannan murya na furta haka, sai hoton wannan Miyura da take nufi ya bayyana acikin ruhin dukkan wani mutun da yaje sauraron wannan magana. ''Wannan wata dama ce ga dukkan wani mai so ya cimma Tarifil-fakta, ku kamashi kuyi amfani da jininsa.'' Tana faɗar haka sai tayi shiru, sannan bayan ƴan daƙiƙu ta ƙara kaɗawa inda dukkanin al'ummar dake wajen hankalinsu ya dawo jikinsu. Nan take suka mimmiƙe, idanunsu cike da mamakin abinda suka ji. ''Magajin Wilbafos........ ''Magajin Wilbafos.... maike faruwa... ''Wane ne wannan...ai koma wane ne dai an kamashi an gama." Nan take mutanen wannan gari suka fara tattaunawa a tsakakninsu. A can gefe wasu dattijai guda uku suka numfasa tare da fara fara jawabi, ''Yanzu bayanin shi ne wane ne zai fara cimmasa...domin kuwa duk wanda ya kama wannan magajin Wilbafos ɗin, lallai ya samu wata dama musamman ta kama Tirifil-fakta. ''To amma kuke tunanin shi wannan magajin bashi da ƙarfin Izza, domin kuwa na tabbata indai tarihin da yazo a littattafai akan zuriyar Wilbafos haka ne, to fa lallai jarumin gaske ne kaɗai zai iya zama magajin wannan gida. ''A'a, ai ni ina gani cewa komai ƙarfinsa, to fa lallai kamar an kamashi ne an gama, domin ko waye shi babu tayadda za iya da dukkanin miliyoyin al'ummar jaruman dake son kama Tirifil-fakta, dan ni idan ni ne shima, kawai zan miƙa kaina ne kawai.'' To waɗannan dai sune kalamanda al'ummar wannan ƙauye suka fara tattauna hankulansu na dawowa jikinsu. Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne wannan ƙararrawa bayanda ta baje, ta ƙara komawa wannan hayaƙi, shi kuma ya dunƙule waje ɗaya inda ya rikiɗe izuwa siffar wani hannu mai girman gaske, wanda ke a rufe da baƙin gashi. Wannan hannu yana bayyana ya nufo Armad da saurin gaske a buɗe, tamkar wanda ke ƙoƙarin ƙwaƙule masa ido. Kafin wani yayi wani abu tuni wannan hannu ya isa gabda idanun Armad, kuma yana gabda taɓa su. Amma a dai-dai wannan lokaci ne wata iska ta bayyana ta daki wannan hannu, inda yayi sama izuwa goshinsa. Kafin kace meye wannan yayi sama inda ƙarfin wucewar tasa ta cire jan kyalle da Armad yake amfani dashi wajen ɗaure goshinsa. Nan take tambarin

Chapter 10 of 33