Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suka farkar da Ururunsu za'a raba su izuwa mataki-mataki. Muje mu rakaki ki saka sunanki." Suwainah tana so taje ta saka sunanta to amma bata so tabar wajen ba tare da taga Armad ba. Domin kuwa tuntuni take ta zulumin ina Armad ya shiga. To amma babu yadda zatai, tunda babu wani uzuri da zata iya gayawa ƴan matan saboda haka suka rankaya tare izuwa cikin wannan gari. Wannan tsibiri dai waje ne na musamman wanda yake da tarihi na sama da shekaru dubu. Ya kasance akan iska a tsakanin doron ƙasa ta farko da kuma doron ƙasa ta biyu. Sunan wannan tsibiri Tsibirin Sido-Ururu. Akan tsibirin Sido-Ururu anan ƙabilar Ururu take bawa ma'abota Ururu horo akan yadda zasu farkar da Ururun dake idanunsu. Asali dai ana haifar ƴan ƙabilar Ururu ne da baƙaƙen idanuwa to amma wannan idanu na farko basa aiki da Izza. Duk wanda yake so ya farkar da Ururunsa izuwa matakin Izza saiya fara juyarda idanunsa izuwa fari fat kamar irinna waɗannan ƴammata. Irin wannan fararen idanu su ake kira da Sido-Ururu. Daga matakin Sido-Ururu akwai horo kala-kala da ake bayarwa kafin mutun ya ƙara juyarda idanunsa izuwa baƙaƙe. Duk wanda yabi wannan matakai ya zama ma'aboci Ururu. A ƙarƙashin ƙabilar Ururu mai mulkin doron-ƙasa ta farko akwai aƙalla manyan gidaje guda goma. Kowanne gida yana da matuƙar girman da shi kansa zaka iyai masa kallon ƙabila mai zaman kanta. Wannan gidaje guda goma sune kamar haka: 1)Gidan Kuyurussa'ayi Ururu: Ɗa ɗaya 2)Gidan Dumaƙisu Ururu: ƴaƴa ashirin. 3)Gidan Uznu Ururu: ƴaƴa sha takwas 4)Gidan Dul'Ururu Ururu: ƴaƴa tara. 5)Gidan Jushai Ururu: ƴaƴa talatin da uku. 6)Gidan Ƙilbaru Ururu: ƴaƴa sha tara. 7)Gidan Jidda Ururu: ƴaƴa bakwai 8)Gidan Nasára Ururu: Ƴaƴa huɗu 9)Gidan Shiysui Ururu: ƴaƴa shida 10)Gidan Fayziy Ururu: ƴaƴa sha ɗaya. Kowanne ɗaya daga cikin gidajen nan yana da jikoki barkatai, waɗanda sune wanda ake turowa wannan tsibiri domin samun horo su farkar da Ururunsu. Sauran ragowar ma'abota Ururu dake doron ƙasa ta farko idan suna buƙatar tayarda Ururunsu sai dai suyi shi a sauran wajaje da aka tanada a bisa doron ƙasa ta farko. A saboda haka Armad bai sani ba, amma a dai-dai lokacinda ruhinsa ya ɓalle ya bayyane akan wannan tsibiri inda yayi arba da Suwainah Ururu da Zeera Ururu jikokin gidan Ƙilbaru Ururu. Akwai jarabawowi da dama da ake gudanarwa kafin a zama Ma'aboci Ururu, kuma waɗannan ƴan mata, Suwainah da ƙanwarta, abinda ya kawo su wannan tsibiri kenan. Kwana ɗaya kafin baiyanar ruhin Armad a wannan tsibiri, ruhin mutanen nan uku dake muradin mallakar littafin, wanda Ikenga yayi musu haramiya ya kuma yi cilli dasu izuwa Tsibirin-Sido-Ururu suka bayyana. Suna bayyana mahaifinsu Suwainah wanda shima jikane a gidan Ƙilbaru Ururu ya ɗebe su ya nufi dasu wajen sarkin wannan tsibiri mai Shadi Ururu, wanda jikan gidan Fayziy Ururu ne. Babu wani ɓata lokaci, Shadi Ururu yana ganin ba suda Ururu yasa aka sare musu kai sannan aka binne gawarwakinsu ba tare da kowa ya sani ba. Domin a wajen ma'abota Ururu indai ba kada Ururu to kai ba mutun bane. A wannan lokaci hatta su Suwainah basu san halinda ake ciki ba, sudai kawai mahaifinsu yace kada su faɗawa kowa labarin waɗannan mutane da suka tsinta, sannan kuma ya gaya musu idan sunga wasu su kira shi. Saboda haka Suwainah ta tura ƙanwarta Zeera domin ta nemo mahaifin nasu, amma bisa mamaki ruhin Armad ya ɓace ɓat babu shi babu alamunsa. 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 75: Miyura (2) Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ---------- Yara ma'abota Sido-Ururu guda dubu goma ne akan wannan tsibiri suna karɓar horo. Suwainah da Zeera biyu ne kacal daga cikin wannan adadi. Kowanne babu abinda yake so illa ya farkar da Ururun da tafi ta sauran ƴan uwansa girma. Abu ne sananne akwai Ururu mataki-mataki ɗai-ɗai har mataki bakwai. Mataki na bakwai shi ne mataki da yafi kowanne ɗaukaka da buwaya da girman Izza. Kaɗan ne daga cikin ma'abota Ururu tun daga farko duniya har izuwa wannan lokaci suka taɓa mallakar mataki na bakwai na Ururu. Hasalima mutun uku ne kacal. Ɗaya shi ne sarkin Ururu wanda ya ture Eyriyon Wilbafos daga kan kujera a lokacin juyin-mulkin Amri, sai kuma yarima mai jiran gado na Ururu wanda aka fi sani da Dúmaƙisu Kuyúrussa'ayi Ururu, sai mutun na ƙarshe wanda shi ne babban wazirin sarki Kuyurussa'ayi Ururu. Mataki na shida na Ururu shima abu ne mara yawa, kuma waɗanda aka sani dashi basu da yawa. Akwai sarakuna goma dake jagorantar gida je goma na Ururu wanda muka labarta a babi na baya, sarakunan da ake kira da ASHURA. Sannan bayansu akwai wasu ƴan tsirarin sadaukai wanda sukai shura a gidan Ururu. Mataki na biyar shi ne iyaka da aka sani, wanda duk wanda yaje shi ana ganin yakai ƙololuwar Izza a gidan Ururu. Mataki na huɗu dana uku dukkansu suna da ƙarfin izzarda zasu iya tarwatsa rundunar mutane da aljanu komai girmanta ba tare da wahala ba. Mataki na biyu akan yi musu laƙabi da Matasan-Ururu, wanda su ake bawa muƙamin kyaftin-kyaftin na runduna. Mataki na farko kuwa sune mayaƙan Ururu mafi ƙanƙanta. Amma a hakan kowanne ɗaya daga cikinsu idan har ya kware akan sarrafa Ururun sa shi kaɗai dai-dai yake da runduna guda. Abin mamaki ruhin Armad na laɓe akan wannan tsibiri yana kallon duk abinda ke faruwa tamkar mutun mai rai. Jiki ne kawai babu. Ba jimawa yana cikin wannan hali ya yanke shawarar abinda zaiyi. Saboda haka ya ci gaba da laɓewa yana nazarin wannan yara tsahon wata da watanni. Inda ALLAH ya taimaki wannan ruhi baya buƙatar ci ko sha, sannan kuma saboda rashin gangar jiki yana iya shigewa ta jikin kowanne abu. Hasalima a waɗannan watanni wannan ruhi na Armad ya gano cewa yana iya shiga jikin mutun ko dabba harma su gana da wannan mutun ba tare da kowa ya sani ba. A saboda hakan ɓuya ba abu bane mai wahala ba. A wata na goma wannan ruhi yabi wannan yarinya mai suna Suwainah cikin wani daji inda take keɓe wa tana koyon sarrafa al'amuran Izza. Suwainah na tsaye a tsakankanin bishiyu masu kama dana darɓejiya sai dai sun fisu tsayi da kauri, sannan kuma rassansu suna da kaifi da tsini tamkar masu. Kana ganin idanun Suwainah kasan tana da kafiya irin ta ma'bota Ururu. A waɗannan watanni da ruhin Armad yayi yana nazarin waɗannan yara ya gano cewa Suwainah irin mutanan nance da zasu iya aikata koma meye akan su sami ƙarfin Izza. Kuma wannan shi ne dalilin da yasa ruhin Armad ya zaɓe ta. Idanun Suwainah suna nan a farare fat sanfurin Sido- Ururu, amma takobin ta tuni ta juye izuwa baƙa-ƙirin samfurin Ururu. Lallai Suwainah tayi rantsuwa saita zamanto ɗaya daga cikin matasan Ururu da ake kwatance dasu. Musamman duba ga yadda sama da shekaru ɗari biyar babu wanda aka samu ya fito daga gidansu wanda ƙarfin Ururunsa yakai mataki na biyar. Wanda hakan yasa ake ganin gidan nasu ya fara rushewa. Amma Suwainah tayi rantsuwa lallai saita ɗago da wancan martaba a matsayinta na ɗaya daga cikin ƴan gidan. Hannunta a miƙe, tana riƙe da doguwar takobin. Idanunta a rufe tana fuskantar yamma. Saboda yadda ta tsaya a ƙame tare da miƙe ƙafa ɗaya da kuma ɗage ɗayar ƙafar, lallai zaka ce mutun-mutumi ne wanda bai taɓa motsi ba. Ruhi da Izza na Ururu na kewaye da jikinta. Hatta wannan bishiyu idan ka lura zaka ga suna tsoron suyi wani abu da zai dame ta. Acikin wannan hali Suwee ta ci gaba da tsayuwa tana nazari da lazimin al'amuran Izza dake cikin idanunta har saida asubahi ta gabato. Sannan ta buɗe idanunta, inda wani baƙi mai ɗauke da Izzar gidan Ururu ya bayyana a idanun nata tsahon daƙiƙa biyar kafin daga bisani ya ɗauke idon ya koma fari. Suwainah ta nufi gindin bishiyar dake kusa da ita inda ta ajiye kayanta, ta ɗauki robar ruwa tasha. Sannan daga bisani ta juyo ta fara wasa da takobin dake hannunta. Kai kace wannan takobi bata da nauyin komai, domin kuwa yadda take sarrafa ta tana juyata tamkar kawai takobin wani ƙari ne na hannunta. Haka dai taci gaba da rawa da wannan takobi har saida rana ta ɗaga, sannan ta fara shirin komawa cikin ƴan- uwanta domin karɓar horon safe. A dai-dai wannan lokaci ne ruhin Armad ya bayyana a gabanta, cikin tsananin zafin nama, Suwainah ta kawo sara da takobin dake hannunta. Amma ruhin Armad ko motsi baiyi ba. Ya bari takobin ta ƙaraso, sannan ta sari wuyansa, amma bisa mamaki sai takobin ta shige ta cikin wuyan tamkar babu kamai a wajen. Ruhin yayi murmushi tare da girgiza kai yana mai cewa, "takobinki baza ta iyayin aiki akaina ba." Suwainah ta ja da baya tare da fara kiran ɗalasimai. Amma a dai-dai wannan lokaci ne ruhin Armad ya ɓace daga inda yake sannan ya shige jikinta. Yana shiga taji tamkar zatai atishawa amma bata zo ba. Ta tsaya tana tunanin mai zatai amma a lokacin ne taji muryar ruhin yana mata magana. "Dani dake zamu iya taimakon juna. Ki taimake ni na taimake ki." Suwainah ta haɗe rai tana cewa, "Mai zaka iya taimako na dashi? Na gane ka, ba kaine wanda kuka zo tare da waɗannan mutane ba ƴan watannin baya. Dama sarki yana nemanka." Ruhin Armad yai kyaran murya sannan yaci gaba da magana tamkar baiji mai take cewa ba. "Zan iya baki ƙarfin Izzar da kike buƙata ki farkar da Ururu mafi girma a tarihi. Idan baki yadda ba tsaya na gwada miki." Ruhin Armad dai daya ɓalle yazo wannan tsibiri shi ne ruhin dake cikin Miyurar dake goshinsa. Hasali idan mai karatu bai mantaba wannan Miyura tana iya ƙarawa Armad Izza, kuma tunda Armad ya rasa ta ya daina samun wannan ƙarin Izza. A dai-dai wannan lokaci, tun kafin Suwainah ta amince, taji ruhinta ya girgiza, sannan izzarta ta fara juyawa. 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 76: Alƙawarin Urúrú da Wilbafos Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ---------- A dai-dai wannan lokaci, idanun Suwainah suka kaɗa sukai baƙi-ƙirin, ta fara ƙoƙarin fitarda da ruhin Armad daga jikinta. Amma ana cikin haka taji izzarta ta fara girgiza tana juyawa. Jikinta ya fara ɗaukan zafi, kafin daga bisani taji wani tsananin ƙarfi irin wanda bata taɓa jinsa ba. Nan take taji a ranta cewa indai za'a zo yin jarabawar rantsar da Ururu a wannan hali sai tayi nasara. Tana cikin haka taji muryar ruhin Armad na cewa, "zan iya baki izza sama da haka. Amma kiyi min alƙawarin zaki yimin abu ɗaya." Suwainah ta ɗanyi shiru na ɗan taƙi kafin ta yanke shawara. "Mai kake so?" Ruhi ya kada baki ya ce, "Fasahar sarrafa lokaci ta ƙabilar Ururu." Suwainah tai murmushi tare da cewa, "Babu wanda ya isa ya mallaki wannan fasaha idan ba manya goma na Ururu ba wato Ashura. Kuma mai kake so kayi da ita?" "Abinda zanyi da ita ni ya shafa. Kamar ƴadda abinda zaki yi Ururun ki ke ya shafa. Kuma nasan kowanne ɗaya daga cikin gidaje goma na Ururu suna da wannan fasaha guda ɗaya a rubuce a ajiye. Idan kina son Izza to ki samo min wannan fasaha." Bayan tsahon lokaci tana tunani ta kada baki tace, "Ba zanyi alƙawari ba har sai naga girman izzar da zaka bani. Zuwa ƙarshen shekarar nan za'ayi jarabawar rantsar da Ururu a doron-ƙasa ta farko. In har ka taimake ni na samu matakin Ururu na biyar zuwa sama to nayi alƙawarin samo maka wannan fasaha." Ruhi ya kada baki ya ce, "Na amince." Idan mai karatu bai manta ba, Uznu Ururu yayi amfani da irin wannan fasaha ya canja sakamakon Jinzidal wanda hakan ya bawa Armad damar wuce matakin Alkadar. Da irin wannan fasaha abu ne mai matuƙar sauƙi ruhin Armad ya koma jikin Armad ya kuma haɗe da gangar jikinsa. Amma a duk faɗin duniya ƙabilar Ururu su kaɗai keda wannan fasaha. Hasalima hatta acikin Ururu, manyan nan guda goma wanda ake kira da ASHURA su kaɗai keda iko su mallaki wannan fasaha. Ruhin Armad yana da tunani nasa daban dana Armad, sannan kuma abin mamaki kowanne yana zaman kansa ne a matsayi ruhi guda bawai rabin ruhi ba. A taƙaice madai abin ya saɓawa al'ada baki ɗaya. Domin kuwa tunda ake rayuwa a duniyar ƙasa bakwai ba'a taɓa samun wanda ruhinsa ya rabe gida biyu ba sannan kuma ya rayu, to amma wani sirri wanda har ƴanzu ba'a san menene ya saka Armad ya zamo mutun na farko da ya iya rayuwa duk da kuwa ruhinsa ya rabe gida biyu. Wani abun mamakin shi ne yadda kowanne acikin ruhin guda biyu keda tunani nasa na musamman. Misali, ruhi mai ɗauke da Miyura yana da wasu ilmummuka wanda ke ƙunshe acikin Miyura wanda shi Armad baima san dasu ba. Musamman tunda dama Armad bai gama kwarewa wajen sarrafa Miyurar ba. Ta haka nema ruhin yake da masaniyar wannan fasaha ta Ururu da kuma yadda zaiyi amfani da ita wajen komawa jikin ɗan'uwansa. To a wannan rana ruhin Armad da Suwainah Ururu suka ɗaura alƙawari zasu taimaki juna domin cimma burinsu. Duk da kuwa ruhin Armad baisan cewa burin Suwainah guda ɗaya ne kacal a duniya, wanda shi ne ta ƙarar da dukkan ƴan ƙabilar Wilbafos da Bayajidda da suka rage. Sannan kuma ita ma Suwainah Ururu bata da masaniyar cewa wanda zai taimake ta burinsa ya ruguza gidan Ururu da Rukunan su ba guda biyu na Amri da Jinzidal. Suwainah da ruhin Armad haka suka ci gaba da kasancewa a wannan hali tsahon wannan shekara. Ruhin yana ƙara mata ƙarfin Izza, ita kuma tana ƙara dagewa wajen samun horo domin cimma burinta. ---------- A can duniyar ƙasashen-ƙasa kuwa, Armad ne tare da sarkin duba Babara ke ketawa ta cikin Bangon arewa domin zuwa wajenda za'a fara horar da Armad. Bayan kimanin daƙiƙa ɗari suna tafiya sai kwale-kwalen ya fara gudu, lamarinda yasa Armad yin sauri ya zauna ya riƙe kefensa ƙam, ya kuma rufe idonsa. Kwatsam ana cikin haka sai jiyayi tamkar sun faɗa cikin wani ƙaton rami, lamarinda yasa ba shiri ya buɗe idonsa. Ai kuwa yai arba da kwale-kwalensu yana faɗowa ƙasa. Ya waiwaya bayansa yaga wannan Bango da kuma wannan ƴar ƙofa da suka shigo ta ciki. Nan take ya gane cewa lallai kodai cikin tsakiyar wannan Bangon ruwa suka shigo ko kuma bayansa. Bayan sun shafe sama da daƙiƙa hamsin suna faɗowa Armad ya tafa hannunsa ya kirawo duk wata fasaha da yake da ita domin kare kansa, domin yasan koma ina zasu faɗo to lallai yana da nisan gaske kuma jikinsu zai iya tarwatsewa. Banda kuma cewa bai masan mai zasu tarar ba. Iska mai ƙarfin gaske ta cikawa Armad ido da hanci. Amma ana cikin haka ya fuskanci cewa Babara ko a jikinsa. Hasalima nishaɗi yake yana murmushi ganin halinda Armad ke ciki. Babara ya tafa hannayensa ya fito da wata ƴar tasa mai launin ja. Acikin ta akwai wani ruwa mai ɗauke da ɗalasimai na musamman. Kafin Armad ya farga, Babara ya watsa masa wannan ruwa. Ai kuwa ruwan na taɓa jikinsa yaji tamkar an zare masa rai, nan take Armad ya sume. Armad bai tashi farfaɗowa ba sai bayan kwanaki uku. Yana farkawa ƴa tsinci kansa acikin wani ɗan tanti mai duhu-duhu. Abu na farko da Armad ya fara fuskanta shi ne wani tsananin sanyi mai ratsa ƙashi, tamkar an sashi a tsakiyar tekun ƙanƙara. Ana haka ya miƙa kansa ya kalli wajen tantin ta wata ƴar taga, inda ya fuskanci cewa ƙanƙarar ce kuwa ke zuba da gaske. A sashin arewa doron-ƙasa ta uku, akanyi sanyi amma bai taɓa kaiwa inda ƙanƙara zata zuba ba. Saboda haka nan take Armad ya fara karkarwa, domin kuwa wannan shi ne karo na farko daya taɓa fuskantar irin wannan sanyi. Ba shiri ya fara tunanin a ina yake. Bayanda ya duba ya tabbatar jikinsa ba ciwo saiya miƙe ya futo waje. Wata iska mai ɗauke bushin farar ƙanƙara ta daki fuskarsa. Yai duba izuwa ƙafarsa ta hagu yaga inda ya taka ya nutse acikin ƙanƙara. Dukkan wajen yayi duhu tamkar lokacin isha saboda tsananin ruri da rugugin iska da ƙanƙara dake kaɗawa. Yayi haka zai juya ya koma tantin sai yaji an dafa kafaɗarsa. Inda ya jiyo amma baiga kowa ba. Nan take Armad ya zare takobinsa ta Wilbafos sannan kuma ya ɗaga hannunsa na hagu inda wata ƙatuwar ƙawanyar aradu ta bayyana. Wannan aradu ta haske wajen amma duk da haka Armad baiga kowa ba. Can yaji an ƙara taɓa shi, amma ta ɓangaren dama. Nan take yakai wawan sara wajen, amma kamar yadda yai tsammani bai samu komai ba. Armad na shirin ƙara kai wani saran yaji muryar Babara a kunnensa. "Baza ka iya gani na ba, saboda da idon ka kaɗai kake gani. Cikakkun ma'abota Izza suna gani kuma suna ji koda sun makance kuma sun kurumce. Lallai idan kana so ka rayu a wannan kurkuku na tsahon kwana ɗaya to lallai saika fara gani izzarka bada idonka ba. Kuma wannan shi ne mataki na farko na horonka." Armad yaji duk bayanin da Babara yayi, kuma dama Armad baiyi tsammanin zai samu horo ta sauƙi ba. Amma abu ɗaya ne bai gane. "Sarkin duba kurkukun gaske ko kuma salon-magana kake?" Babara yai murmushi tare da girgiza kai yana cewa, "lallai ba salon-magana nake gaya maka ba. Wannan ita ce kurkuku mafi girma da tsaro a duk faɗin duniyar ƙasa bakwai. Yau sama da shekaru dubu da ɗari biyar kenan da gina ta, amma tunda aka halicce ta ba'a taɓa samun wani ya fita daga cikinta taba ko sau ɗaya. Duk wanda ya shigo, ya shigo kenan har abada. Koda gawarsa baza ta fita ba." 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 77: Mubayi'a ta farko Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ------------ "Kurkuku?!" Armad ya faɗa cikin ɓacin rai. Yana niyyar ƙarewa Babara tanadi sai wani abu ya faɗo masa. Nan take ya ce, "idan a kurkuku nake to ai kaima a kurkuku kake kenan?" Babara yai murmushi inda dattijon takarsa ta ƙara bayyana. "Lallai kayi gaskiya. Idan kana kurkuku to nima ina kurkuku. Ko a baya dana gaya maka cewa na taɓa keta rabin wannan Bango a zahiri bawai Bangon na keta ba. Mu kanyi amfani da manya-manyan hatimai wanda ƙungiyar duba ta duniya ta samar domin kawo yara wannan duniya ta bango domin muyi musu horo. Amma a zahiri hatimin yana canja taswirar waje tare da mutanen dake kai, a saboda haka bawai cikin nan muke kawo suba. A taƙaice dai ni kaina wannan shi ne zuwa na wannan waje na farko." Koda Armad yaji haka saiya haɗe gira yana mamaki. Nan take zare ido gami da tambayar Babara. "Idan baka taɓa zuwa ba to tayaya kake niyyar fita daga wannan waje?" Babara najin tambayar ya sunkui da kansa ta yadda Armad bazai iya karanta halinda fuskarsa ke ciki ba. Lokaci ya fara tafiya, gari na ƙara duhi, sanyin dusar ƙanƙara na keta ruhin Armad yana sashi rawar ɗari. Can daga bisani Babara ya zube akan gwiwowinsa, kansa na kallon ƙasa cikin miƙa wuya. Abu na farko da Armad yayi tunani shi ne sanyi ne ya yiwa Babara yawa, ko kuma wataƙila ciwon ciki yake. Amma kafin Armad ya kaiwa Babara ɗauki yaga Babara ya zare doguwar wuƙa daga aljihunsa, ya yanki tafin hannunsa, inda jini ya fara kwaranya. Sannan yayi amfani da hannunsa mai jini ya cake sandar tsafinsa a ƙas. Armad ya rasa mai zaiyi tunani sai kawai yaji muryar Babara a kunnensa. "Ni Babara Bayajidda nayi mubayi'a ga sarkin mutane da aljanu Armad Wilbafos na uku." Idan ba daban tsananin imani da kafiya da Armad yaji a muryar Babara da lallai zai ɗauka wasa yake. Amma duk da hakan Armad bai gane abinda ke faruwa ba, nan take ya buɗe baki ya ce, "wai maike faruwa ne? Lallai kana sani ina jin kunya, kuma idan wannan ɗaya ce daga cikin dabarunka na horo bai bada ma'ana ba." Babara ya ja ɗan ƙaramin numfashi tare da ƙara sunkui da kansa yana cewa, "lallai wannan ba wata dabara bace. Ni Babara na bar muƙami na sarkin duba na dawo gefenka domin ganin cewa ka zama sarki wilbafos na uku. Ina fatan zaka karɓi mubayi'a ta." Armad yai farat ya ce, "to saboda me? Ni bance ina son na zama sarki wilbafos na uku ba. Sannan kuma ni ban masan abinda hakan ke nufi ba." Babara ya amsa a nutse, tamkar dama yayi tunanin Armad zaice hakan. "Zama sarki Wilbafos na uku ba abu ne da zaka iya zaɓa ba koda kana so. Abu ne da mutane su zasu gani su naɗa ka, kamar yadda yanzu nai amanna acikin raina cewa ka cancanci wannan muƙami. Kamar yadda na labarta maka a baya sarki Wilbafos na farko wato Aldaima Wilbafos da Wilbafos na biyu wato Eyriyon Wilbafos sune mutane na farko da suka taɓa yin yaƙi domin rusa rukunan Jinzidal da Amri. Kaima yaƙin da kake da rukunin Jinzidal yasa kabi sahunsu. Sannan kuma daɗin daɗawa kaima ɗan ƙabilar Wilbafos ne. Na daɗe ina ƙin jinin siyarda marasa ƙarfi da ake a ban ƙasa a matsayin bayi dasa hannun manyan sarakunan duniya, amma ƙungiyar duba suka nuna min basa son shiga rigima da sarakunan Jinzidal dana Ururu domin a cewarsu babu wata nasara da zata futo daga ciki. A saboda haka na zaɓi na bi sahunka domin ganin an daina wannan kaba'ira ta siyarda mutane a matsayin bayi." "Hmmmm...." Armad yaja dogon numfashi Babara na durƙushe a gabansa yama rasa mai zaice. Can bayan tsahon lokaci ya ce, "to amma idan na fuskance ka kana da wani dalili na musamman da yasa kake ganin zan iya aiwatar da wannan abu. Domin dai baza ka ajiye babban muƙamin ka na sarkin duba ba kawai ka dawo ɓangare na ba tare da wannan ba. Zanso naji mene ne." Babara ya fara da murmushi wanda daga bisani ya juye izuwa dariya sannan bayan ɗan lokaci ya tsagaita tare da cewa, "lallai kamar yadda ake haifar duk wani ɗan ƙabilar Wilbafos ko Bayajidda ko Ururu ko kuma ƴaƴan sarkunan Jinzidal da Izza ta musamman kaima kana da taka ta musamman. Amma bazan ɓoye maka ba, lallai abu ɗaya tak da yasa nayi mubayi'a shi ne manufarka ta cimma Jinzidal. "Kada ka manta akwai wani yaro wanda aka haifa da baiwa irin taka kuma ɗan ƙabila ta. Nasan ka gamu dashi. Ana ce masa Ikenga O. Bayajidda. Lallai Ikenga yana da ƙarfin da zan iya yi masa mubayi'a to amma manufarsa ba irin tawa bace. Hasalima Ikenga tuni ya farkar da fasahar gidan mu ta Byajidda wato Takun-sarki, wadda Izza ce wadda ke matakin Ururu. Amma a halin yanzu kai baka farkar da fasahar gidanku ta Wilbafos ba ballantana asan wacce irin fasaha zaka samu. "Sanin irin fasahar da zaka samu shi ne zai nuna ko zaka iya karawa da Ururu da sarakunan Jinzidal. A taƙaice dai ina gaya maka ni Babara na ajiye muƙamina na sarkin duba a duniya nayi maka mubayi'a ba tare da sanin wacce irin fasaha zaka samu ba. Kuma na biyo ka cikin wannan kurkuku ba tare da sanin irin fasahar da zaka samu ba. Kai sani cewa irin fasahar daka samu ita ce zata nuna ko zamu iya fita daga wannan waje ko kuma anan rayuwarmu zata zo ƙarshe." Armad yai shiru yana sauraren Babara. Babara ya gayawa Armad cewa fasahar sa ta Ɗorawa da Wilbafosiyan-si wod-dans da Al-yaya duk ba nasa bane na aro ne. Da farko Armad bai yadda ba, amma daga bisani Babara ya labarta masa cewa kowanne kabila suma da tarin fasahohinsu. Amma kadan daga cikin yan kabilar suna iya farkarda fasaha ta musamman wadda zata zama tasu. Hakan bawai yana nufin wasu baza suyi amfani da ita ba. Sai dai kawai duk wanda zaiyi amfani da ita to kamar da aro zaiyi, kuma bazai taba kaiwa asalin karfin masu ita ba. Ya gaya masa fasahar Dorawa ta Hidaya ce ta ara masa, sannan kuma fasahar Wilbafosiyan-siwod-dans ta kakanka ce Zaikid. Hatta fasahar Al-yaya wadda bai taba amfani da ita ba ta aro ce, asalin ta daga gidan Maikironomada ta fito. A saboda haka Armad yana da bukata ya farkarda fasaharsa ta musamman tasa shi kadai. *** ******* Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 78: Yanayin Izza Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos --------- Armad ya numfasa tare da duban Babara cikin mamaki ya ce, "To amma duk da haka baka bayyana min dalilin da yasa ka zaɓi wannan kurkuku a matsayin wajen da zamu yi horo ba." Babara yai murmushi yana cewa, "sannu a hankali zaka ga dalili, ya shugaba na." Armad najin kalmar 'ya shugaba na' ya haɗe rai. A ganinsa irin kalmomin nan ne da yakan ji aljanu na faɗawa iyayen gidansu acikin littattafan yaƙi. Amma haka dole Armad Wilbafos ya karɓi mubayi'ar sarkin duba Babara, duk da cewa bai san haƙiƙanin mai hakan ke nufi ba. Washe gari suka cire tanti tare da nausawa cikin dusar ƙanƙara suka nufi gabas. Suna ƙara nausawa waje na ƙara duhu, ba daɗewa Armad ya gano cewa tsananin duhu ne yasa baya iya hango abinda ke gabansu. Babara ya dubi Armad ya ce, "A ganinka taya ya mutun ɗan adam yake iya yaƙar aljanu? Kasan dai ba'a ganin aljanu indai basu suka bayyana maka kansu

Chapter 27 of 33