Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
toba alkhairi bane. Dan babu yadda za'ai a iya tunaninsu mutun yana cikin hayyacinsa ya ce zai nemo Tarifil Fakta acikin wata bakwai masu zuwa. Mutumin da duk duniya suka kasa nemowa. Dakyar Armad ya iya daina haƙi, sannan ya dube du cikin sauri ya fara jawabi, "Masanin Ƙasa Abul-Babara ya bani adadin wata bakwai na nemo Tarifil-faƙta. Yace ya gama haɗa maganin mahaifiya ta, amma idan nanda wata bakwai ban nemo shi ba, to nama haƙura da nemansa, domin kuwa alƙwarinmu dashi ya tashi." "Kai…." Cikin tsananin mamakin rashin sanin ya kamata na ma'abota duba dukkanin su ukun sukai ajiyar zuciya tare da riƙe baki. Domin sun san lallai aikin dake gaban Armad ya tashi daga mai-kama-da-mara-yiwuwa zuwa wanda-bazai-taɓa-yiwuwa ba. To amma ganin halin da Armad ke ciki na rikici da firgici, nann da nan Nusi ta fuskanci cewa kamata yayi sunkwantar masa da hankali, su kuma bashi buri maimakon su ƙara kashe masa gwiwa. "Indai haka ne to kai sani cewa mu ukun nan zamu taimaka maka da iyakacin ikon mu a cikin waɗannan wata bakwan. Abinda ya kamata ka sani shi ne. "Na farko dai babban mafitar ka ta nemo Tarifil-fakta a yanzu shi ne shiga cikin garinmuna ƙarƙashin ƙasa wanda na labarts maka a baya. Domin ina jin cewa indai muka iya shiga wannan gari, to kamar mun samo Tarifilfakta ne. "Amma kai sani cewa, hanya ɗaya da zamu iya shiga garuruwan ƙarƙashin ƙasa shi ne idan akai mana rijista acikin waɗanda zasu biga gasar Jinzidal. Ni zan nemo mana katin shiga na garin Maikironomada. Sannan kuma idan muka shiga sai fake da taka rawa acikin gasar mu silale muyi namu waje. "To amma Armad kai sani cewa lallai komin saurin da kake baxan bari ka shiga gasar Jinzidal ba, ba tare da na tabbatar da ƙarfin Izzar ka ba. Saboda haka maimakon wata biyu yanzu na maida shi sati ɗaya. Zamu jira anan, kai kuma zaka hau kwale-kwale. Akwai wani tsibiri idan ka miƙe wannan hanya," taɗan tsaya taja numfashi tare nuna masa hanyar da hannunta, "abinda kawai nake so shi ne ka ɗebo min ƙasar dake wannan tsibirin ka dawo nan cikin sati ɗaya." Ta ciro wani Ayrid daga jakarta, inda ta karanta wasu ɗalasimai ta juyarda shi izuwa ɗan ƙaramin kwale-kwale. Babu ko cewa ƙala, Armad ya hau wannan kwale-kwale ya zare takobinsa, tare da nufar hanyar tsibirin nan. Nusi tayi ajiyar zuciya tare da kallon su Iliyasis, waɗanda sun kasa cewa komai tunda suka ji zancen wata bakwan nan. Ta numfasa tace, "ko ya nemo Tarifil-Fakta ko ba ya nemo shi ba, duk ya ta'allaƙa da ƙaddararsa. Mudai namu shi ne mu taimakawa abokinmu mu kuma bashi kwarim gwiwa. Saboda kada wani acikin ku ya kuskura yace masa bazai yiwuwa ba. Ku kafa mana tanti, anan zamu jira shi sati ɗaya." Kwanaki uku bayan da Armad ya ɓace acikin hazon dake kewaye da wannan kogi daya haɗe tsakanin doron ƙasa ta uku da kuma dajin Ikwatora, Armad ne ke tafe yana ta tuƙa kwale-kwalen a hankali, domin ko gabansa baya iya gani saboda hazo da duhu. Domin tunda yai kwana biyu yana tafiya, ya daina ganin rana, kullum dare ne kuma kullum duhu ne. Sai dai kuma babban abinda ya bawa Armad mamaki shi ne, duk da kasance war wannan kogi da yake kai za'a iya yin ittafaƙi akan cewa yana daga cikin wajen mafi hatsari a dukkanin duniyoyin ƙasa, amma bisa tsananin mamaki babu ko Dordor ɗaya da yai arba dashi. Hasalima babu wata halitta mai hatsari daya gani, kai a rana ta uku ma yana cikin tafiy kawai idanunsa suka kai ƙasan kwalekwalensa bayanda yaji motsi, ai kuwa yana dubawa yaga manya-manyan kifaye suna gudu a cikin ruwan nan a ƙoƙarinsu na gukewa daga inda Armad yake tsoro. Nan take Armad yasan cewa akwai wani hatsari dake faruwa, Amma ko kaɗan hakan baisa yaja baya ba, ko kuma ya tsaya ba. Kai tsaye, cikin dakiya da rashin tsoro ya ƙara numfasawa cikin wannan duhuwa da hazo. A rana ta huɗu da yamma yana tafiya ya fara hangen wannan tsibiri da Nusi ta kwatanta masa. Ai kuwa nan take ya ƙara azama ya nufi wannan waje gadan-gadan. ALLAH sarki, rashin sani yafi dare duhu, akan wannan tsibiri waɗansu mutane ne guda huɗu. Dukkan tsibirin babu gida gaba babu gida baya. Babu wata halitta mai rai, face rugurguzazzun gida je da duwar-watsu. Lallai kana gani zaka fahimci cewa shekaru aru-aru anyi babbar alƙarya akan wannan ruwa, amma a yanzu sai dai tarihi. Iskar dake tashi daga wannan tsibiri duk da a tsakiyar ruwa yake, amma tana da tsananin zafi, sannan kuma tana ɗauke da tsananin tsoro da firgici acikinta. Babu komai sai duhu da kaɗaici da alamun mutuwa da alhini acikin wannan waje. Amma bisa mamaki waɗannan mutane huɗu, maza uku mace ɗaya suna tsaye a tsakiyar wannan waje. Su su kaɗai ne halitta mai rai duk faɗin wajen. Dukkanin gashin jikinsu fari ne fat alamun tsufa da daɗewa a duniya. Amma hakan ko kaɗan baya nuna alamun gajiya wa a tattare dasu. Hasalima kowanne ɗaya daga cikinsu zai iya yaƙar daula guda shi kaɗai kuma yai nasara ba tare da ko kwarazane a jinkinsa ba. Babban cikinsu mai sanye da rawani wanda ya rufe fuskarsa, yana fitar da kamala mai ƙarfin gaske. Wadda ita kaɗai zata iya zubar da ƙananun ma'abota Izza ƙasa a sume. Hasalima Izzarsa shekaru dubu ɗaya ce da ɗari biyu da sha uku (1213 years). Mai biye masa yana da Izza shekaru ɗari tara da arbain da ɗaya. Macen nada ɗari baƙwai da sha uku sai kuma ƙara munsu mai ɗari biyar da huɗu. A wani na salo na wata irin murya mai saka tsoro a cikin iskar dake kaɗawa, mai biye wa babban yai magana, "Ya shugaba na, yau shekaru sama da ɗari bakwai muna neman wannan littafin-takobin, amma yau gashi ya bayyana a garemu. Lallai jiranmu yazo ƙarshe. Ina so ka bani iko na zo maka da wannan littafi cikin ƙiftawar ido." Tsahon lokaci wannan nasu baice komai ba, hasalima ko kallon sa baiyi ba. Sai bayan kimanin daƙiƙa sittin wannan mace ta cire mayafin data rufe fuskarta ta kuma rusuna a gaban shugaban nasu tace, "ya shugaba na, ni kuma ina ganin mu bari yaron mai suna Armad ya iso, tunda shi ne kaɗai wanda littafin ya amince ya bayyana a gareshi bayan duk waɗannan shekarun. Idan ya iso saimu kashe shi cikin kwanciyar hankali, mu kuma yi amfani da ruhinsa wajen sarrafa littafin." Babban abinda mamaki da wannan mace data bada wannan shawara ita ce, kamarsu ɗaya sak da Nusi babu wani abu daya raba su, kama daga kalar fatar har komai da komai. Kai kamar har tafi wadda ke tsakanin yan biyu ma, idan dai banda cewa kana zuwa bakin wancan ruwa zaka ga Nusi dasu Cokali a inda Armad ya barsu ba, toda sai kace ita ce ma. Wannan littafi da waɗannan mutane suke nema idan mai karatu bai manta ba, shi ne wanda aka labarta acikin 'Gabatarwar' wannan littafi. Wanda hatta ma'abota Ururu suke nema, amma sun rasa. Yanzu gashi su waɗannan mutanen sun gano cewa wannan littafi da Armad ya samo acikin Non-toc-Teka, shi ne dai wannan littafin da suke nema. Kuma gashi nan yana tafe zuwa inda suke bayan shekaru sama da ɗari bakwai da sukai suna nema. *** Deniziyya Kuronikil (Jinzidal), suna ne da akewa wata gasa laƙabi dashi. Gasa ce wadda kamar yadda aka labarta a baya wajibi ce, kuma babu wata ƙasa ko kuma wani sarki daya isa yaƙi shiga. Kowanne sarki daga kan doron kowacce ƙasa zai kawo wani adadi na bayi, waɗanda za'a saka a matsayin kyauta ga duk ƙasar da tayi nasara a gasar. Akan tara sama da bayi dubu ɗari waɗanda za'a rabasu tsakanin wanda sukai nasara na ɗaya dana biyu da kuma na uku. Ta haka waɗannan ƙasashe su zasu juya akalar cinikin bayi a wannan shekara. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 27: Tsibirin Kadaici Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Armad na tafe a hankali a hankali, babu abinda yake sosa masa rai sai labarin watanni bakwan da suka rage masa kafin wa'adin da sarkin duba Abul Babara ya bashi ya cika. Lallai yasan cewa duk abinda zaiyi daga wannan lokaci saiya zamo a ƙaiyade da lokaci. Da yammaci liƙis yakai bakin gaɓa, inda ya sauko hannunsa na hagu bisa kan takobinsa, sannan na dama kuma yana ƙoƙarin ɗaure jirgin a iyaka. Bayanda daya gama ɗaure jirgin saiya ɗago ya kuma yi duba izuwa cikin wannan tsibiri dake gabansa. Babu komai akai face ƴan gidaje ɗai-ɗai ɗai-ɗai ƙirar mutan da. Wanda tun daga nesa baka da buƙatar ace maka maka babu wata halitta aciki. Domin kuwa banda yana data rufe ko'ina babu komai sai shiru da kaɗaici dake tashi daga kaf ilahirin gida jen. Ga dukkan alamu ko namun dawa basu iya sakewa akan wannan tsibiri. Duk yadda akai yana daga cikin tsibiran da akayi wa mummunan sammu irin na mutanen farko. Har izuwa wannan lokaci Armad bai daina mamakin dalilin da yasa har ya zuwa wannan lokavi bai gamu da Dordor ba. Domin a iyakacin lissafinsa ya ƙididdiga cewa ya kamata zuwa wannan lokaci ace tskobinsa tasha jinin sama da Dordor arba'in zuwa sama. Nan take ya tabbatarwa da kansa cewa lallai akwai wani abu akan wannan tsibiri wanda hatta su Nusi basu sani ba. Saboda haka nan take ya zare baƙar takobinsa, tare da karanta ɗalasimai kamar haka, "Ƙaban'shisu!" Nan take walƙiya da tsawa ta fara haɗowa a jikin ƙarfen wannan takobi, inda nan take dukkan ilahirin ta ya cika da wannan walƙiya. Kafin daga bisani ilahirin jikin Armad shima ya ɗau haske yana bada walƙiya tamkar ɗan saƙon mutuwa. Hasken jikin walƙiyar Armad ya fara haskake dukkan ilahirin wannan tsibiri, lamarin da yasa ya fara hangen alamun wasu mutane daga wata ƴar duhuwa da bata da nisa daga inda yake. Babu shiri yayi linƙaya acikin girman ɗalasiminsa na 'Ƙaban'shísu', ya kuma ɓace daga inda yake, sannan ya bayyana gaban wannan duhuwa. Ai kuwa idon Armad bai masa ƙarya ba, domin kuwa kamar yadda ya gani haka yake. Mutane ne guda huɗu a tsaye a wajen. Dukkansu da ransu da lafiyarsu, amma kuma babban abin mamakin shi ne, babu wanda acikinsu yake kalli Armad. Tamkar basu ganshi ko kuma basu masan wani yana tsaye a wajen ba. Duk da kuwa haske da zafin Aradu dake tashi daga jinkinsa da kuma na takobinsa. Armad ya dube su tare da haɗe gira, "kamar yadda babu ruwanku dani, nima haka babu ruwana daku." Yana gama magana ya juya zai tafi. A zuciyar Armad yayi tunani cewa yadda basu kula shi ba, yana nuna tamkar basu damu dashi bane. Sai dai kuma amma kash, abin ba haka yake ba, domin kuwa yana juyawa yaji maganar wata mace daga cikinsu, wanda yake shi baima kula akwai wata mace acikinsu ba. "Waya ce maka ba ruwanmu dakai," macen na rufe baki Armad ya juyo da niyyar ganin kowa ce ce ke magana, ai kuwa nan take ya buɗe baki tare da kwale ido. "Nusi??" Armad ya lura cewa wannan mace data gama magana kamarsu ɗaya sak da Nusi daya baro a bakin gaɓa. "Me kikeyi a nan?" Armad ya ƙara tambaya. "Ba ita bace," ta bashi amsa a nutse, "abinda kawai muke nema a wajen ka shi ne littafin daka samo acikin Nontoc-teka." Armad ya yatsine fuska cikin fushi, "damme yasa zan baku littafina!" Wannan mace mai kama da Nusi ta ƙara girgiza sannan tace, "idan da munso yaudararka toda munyi shigar ƴar uwarka Nusi mun kuma ɓata tsakanin ku ts hanyar yin amfani da sunanta mu kwaci wannan littafi. To amma shugaban mu yace mu bika a hankali. Saboda haka ina so ka ƙara tunani kafin ka ƙara bamu amsa. Domin kuwa wannan itace dama ta ƙarshe dazan baka." Tana gama magana ta zare takobinta tare da tsayawa a gaba Armad. Armad ya lura cewa tana sane take ƙara futo da ƙarfin Izza ta domin ya karanta ya gane matsayinta a fagen Izza. Idon Armad sukai tsinkaye da abubuwa kamar haka; Izza : 713 Negrinki : Duniya ta biyu Aljani : Aljanin Iska Fasahar takobi : Mataki na Shida Har ya zuwa wannan lokaci babu wanda yai motsi acikin waɗannan mutane uku dake tare da wannan ma'abociyar Izza dake kama da Nusi. Lallai Armad yasan cewa akwai babban aiki a gabansa kafin ya tserewa waɗannan mutane. Domin kuwa yasan cewa a doke lallai bazai iya ja da dukkaninsu ba. Gashi har ila yau ko gwada ƙarfin wannan littafin takobin baiyi ba, ballanta yasan ko akwai wata fasaha aciki da zata iya taimaka masa. To amma wani babban abin mamaki shi ne yana jin cewa bazai taɓa iya bayarda wannan littafi ba. Ko mai zai faru. Saboda haka saiya fara ƙoƙarin ɓullo da wata sabuwar hanyar, "mai yasa kuke san wannan littafi." Armad ya tambaye ta a nutse. Nan take fuskar ta ta fara canjawa, inda a fusace ta bashi amsa, "wannan bai shafe kaba. Zaka bayar ko baza ka bayar ba." Armad yana cikin tunanin mai zai aiwatar kawai yaji hucin takobinta yana iso shi. Inda nan take ya miƙa tasa ya tare. Sai dai amma banbancin Izzar da yawa, nan take ta danne Armad izuwa ƙasa bisa gwiwowinsa. Badan takobin tasa ma tasha tsimi ba, to da lallai tuni ta tarwatse. Armad na ƙoƙarin kare kamsa daga wannan sara nata, amma ina, tuni cikin zafin nama ta zira hannu cikin rigarsa. Inda kafin yai wani motsi tuni ta ƙara nuna masa banbancin dake tsakanin Izza shekaru ɗari bakwai da ɗoriya da kuma wadda bata kai shekaru ɗari ba. Inda wannan littafi ya bayyana a hannunta. Armad yai iya ƙoƙarinsa ya riƙo shi amma ina babu abinda yake sai ƙara nisa dashi, yayinda ita kuma tai tsalle take komawa baya. Kafin Armad yayi wani abu tuni dukkanin su ukun dake bayan wannan mace sukai tsalle tare da matsowa kusa da ita. Sannan kuma a wani salo na samarda ƙawanyar tsafi, dukkaninsu huɗun suka kewaye wannan littafi a yayinda macen ta sashi a tsakiya. Kafin daga bisani su fara karanta wasu a wani harshe wanda Armad bai gane ba. Dukkan abubuwan sun ɗauki lokaci wajen bayani amma a zahiri basu wuce daƙiƙa ɗaya ba. Sai dai Armad na niyyar kai musu farmaki ya kwace littafin, kawai sai ya ƙara ganin wani hasken ya bayyana daga sama. Inda kafin ma Armad ya gama zare takobinsa, tuni wani saurayi ya bayyana daga cikin wannan haske, inda kai tsaye ya caka farar takobin dake hannunsa a tsakiyar waɗannan mutane huɗu. Kuma kan wani acikinsu yayi wani abu tuni takobin tasa ta haɗu da jikin wannan littafi dake tsakiyarsu. Nan take wani baƙin haske mai kama da duhun dare ya gauraye dukkan wajen. Inda kai tsaye ya sumar da Armad cikin abinda bai wuce daƙiƙa ba. Babu abinda Armad ya ƙara tunawa illa farkawa da yayi bayan tsahon lokaci yai arba dashi kwance acikin taɓo sannan kuma daga can gefe kuma ga littafinsa nan. Sai dai kuma babu kowa a wajen sai shi kaɗai. Har Armad ya fara tunane-tunane kawai sai ya tuna cewa koma ina suka tafi bai shafe shi ba, tunda ga littafinsa basu tafi dashi ba, abinda kawai ya rage masa shi ne ya ɓace daga wajen. Sai dai kuma yana cikin saurin da yake ne, kwatsam kan ya kai ga littafin ya gano cewa a gaban goshinsa babu wannan jan kyalle da kullum ke tare dashi. Babu shiri ya tafi da gudu izuwa gefen ruwan nan domin duba wanne irin hali Miyurar sa ke ciki. Shin tana haske ko bata yi. Amma isarsa keda wuya kwatsam ya gano cewa ai babu komai a goshinsa. Miyurarsa bata nan, ta ɓace ɓat. Babu ita babu alamunta. Nan da nan fa ya fara haki, harma yana tunanin anya kuwa shi ne. Babu abinda yake sai dubawa da yake yana ƙara dubawa. Amma ina babu Miyura babu labarinta! *** Wani abu daya faru awa ɗaya kafin isowar Aemad wannan tsibiri; Waɗannan mutane guda huɗu dake so su kwace wa Armad littafin takobinsa suna tsaye suna jiransa. Kowa aciki yana kawo shawarae yadda za'a gama da Armad kai tsaye a kashe shi sannan a kwace littafin. Amma bayan kowa ya gama, sai shugaban nasu ya numfasa ya ce, "lallai kamar yadda kuka ce kashe shi mu kwaci littafin ba abu ne mai wahala ba. To amma kun manta da cewa acikin wannan littafi akwai ƙarfin Izza wanda zai iya jiya lokaci ya kuma canja zamani? Saboda haka lallai bazan yarda ɗaukan wani hatsari na faɗa ba, inda litrafin yana hannunsa. Dukkaninku kunsan mai zai faru idan jikin takobin wani ya taɓa wannan littafi. Saboda haka mafi kyawun hanya shi ne mu lallaɓa shi mu karɓi littafin sannan saimu kashe shi. *** Sai dai kash, abinda basu sani ba shi ne, a dai-dai wannan lokaci wani jarumi ma'aboci Izza yana kan wannan tsibiri. Wanda shi kuma babu abinda yake buƙata face ya hallaka waɗannan mutane huɗu dake neman yiwa Armad kwace. Saboda wani tsohon tarihi dake tsakaninsu. Wannan jarumi ba wani bane illa Ikenga O Bayajidda. Wanda kuma ya ci gaba da jira ya fakaitansu har sai da yaga sanda suka shagala suna so suka wasu ɗalasimai su sawa littafin takobin layar zana. Shi kuma ya fito ya caki littafin da takobinsa. Yanzu gashi dukkanin su biyar ɗin har dashi sun ɓace ɓat. Babu su babu alamarsu. Sannan kuma babban abinda ya shafi Armad shi ne sum ɓace masa da Miyura. Duk da har a wannan lokaci bai san taƙamaimai maiya faru ba!! Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 29: Jinzidal Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Armad na cikin wannan hali su Nusi suka bayyana akan wannan tsibiri. Inda suka samu labarin dukkan abinda ke faruwa dalla-dalla daga Armad. Ganin cewa hankalin Armad ya tashi, babu wanda ya nuna masa cewa rasa wannan Miyura tasa da yayi abu ne mai kyau ba. Domin su suna ganin cewa hakan zai sa masu neman hallaka shi su ragu. Sai dai shi kuma kwata-kwata baya jin tsoron masu neman nasa ko kaɗan. Ita kuwa Nusi ta shiga cikin zulumi tunda taji ance anga mai kama da ita sak. To a haka dai suka lallashi Armad ya fara gudanar da horon sa wanda yazo yi tunda fari. Wato fafatawa da waɗannan halittu masu suna Dordor. A wannan lokaci da Armad ke fafatawa a tsakanin waɗannan halittu da akewa laƙabi da Dordor, a can waɗansu wajaje sauran ma'abota Izza ne da dama suma ƙoƙari suke suga suma sun nuna kansu a duniya a wannan gasa da za'ai ta Jinzidal ƙarama (Wadda akafi sani da Deniziyya kuronikil). Wasu daga ciki, kamar su Ikenga O. Bayajidda, wanda idan mai karatu bai manta ba, a lokaci na ƙarshe da aka ganshi, yana kan hanyarsa ta zuwa garin Denizawa domin shiga wannan gasa ta Deniziyya Kuronikil, duk da kuwa akwai ragowar watanni kusan biyu kafin zuwan gasar. To ko mai yasa mai yasa shi tafiya da wurin?? Amsar dai tana cikin wani daji mai yawan giwaye. Wannan daji ba a ko'ina yake ba, illa acikin daular Denizawa ta ƙarƙashin ƙasa. Kuma ɗaya daga cikin dazuka na musamman da aka warewa babban ɗan sarki Deniz Iluru, wato Deniz Bizáya, domin motsa jiki. Kusan zaka iya cewa duk wata dabba mai rai data rage acikin wannan daji tsahon lokaci ta daɗe da zama abincin waɗannan giwaye. Ko kuma dai tuni sun shige ƙarƙashin ƙasa sun ɓoye kansu, ko kuma waɗanda suke da sa'a sun shiga rububi sun guje daga dajin da kyar. Waɗannan giwaye lallai na musamman ne, domin kuwa duk da cewa girman jikinsu ya ɗara na da yawa daga cikin giwaye, jikin nasu bai hanasu yin tsalle mai tsayin gaske ba. Misali a wannan lokaci, saboda abinda ke faruwa a ƙasan wannan daji tsakanin waɗansu mutum biyu, dukkanin giwayen nan sun yi tsalle sun haye can saman waɗansu bishiyu masu kama dana dabinon farko. Babu abinda suke sai hangen abinda dake faruwa, cikin tsananin burin ɗaya daga cikin waɗannan mutane ya faɗi matacce su sami abincin buɗa baki. Koda yake sukan ci wata dabbar idan sun samu, amma a ƙa'idarsu an gina jikinsu ne kawai domin yin buɗa baki da naman ɗan adam. Saboda haka nema wajen ya zama abin so ga Deniz Bizaya, domin lokaci-lokaci yakan yazo ya fafata da waɗannan giwaye. Amma a duk tsahon lokacinsu dashi, basu taɓa ganinsa yana fafatawa da gaske ba irin satin daya wuce. Saboda haka nema kaf giwayen nan suka haye bishiyu suna fatan waɗannan samari biyu su hallaka kansu, su kuma su sakko su samu na buɗa baki. Idan ka kallo cikin dajin daga sama, babu abinda zaka iya hange face mutun biyu a tsaye. Ɗaya yana riƙe da fafalo-mai-lanƙwasa launin ja. Irin jan nan mai abin mamaki ta yadda zaka kasa gane cewa kalarsa ce a haka, ko kuma jinin abokin gabarsa ne yasa ya zama haka. Wannan saurayi ba wani bane, illa Deniz Bizáya! A ɗaya ɓangaren kuma wani saurayi ne, wanda shima daga saman bishiyun waɗannan giwayen babu abinda suke iya gani sai doguwar takobinsa dake ta kyalli tana ɗaukar ido. Wannan takobi duk da cewa saurayin dogo ne, zaka iya hangen cewa ta fishi tsayi. Wannan saurayi ba wani bane illa Ikenga O. Bayajidda! Kayansu tuni sun daɗe da komawa kalar ƙasa, saboda azabar fafatawa, kai da gani kasan an kai kwanaki da dama ana wannan bata kashi. Sannan kuma abu na ƙarshe da giwayen nan suke iya hange daga saman, wanda kusan shi kaɗai ne abinda yake ɗan faranta musu rai shi ne, haki da kowannensu keyi. Kana gani kasan waɗannan samari biyu sun gaji. Saboda haka nema waɗannan giwaye suke gani ko su na da rabo. *** A can daular Infiriya kuwa, wani saurayi ne zaune shi kaɗai yana ta kuka. Wannan saurayi yana kan kogin ƙasa ta huɗu wanda ya haɗe da Bangon arewa, acikin kwale-kwale. A gefensa kuma akwai wata gawa wadda idan kai mata duba na tsanaki zakaga cewa suna kama sosai da wannan gawa. Babu abinda ke fita daga cikin jajayen idanun wannan saurayi, sai kwalla kawai. Kana kallonsa bama ka buƙatar a gaya maka cewa wannan mutun dake kwance acikin kwale-kwalen mai suna Firius Firesa, makusancinsa ne. A rataye a bayan wannan saurayi, wani mashi ne wanda ke ɗauke da wasu rubuce-rubuce irin na da. Kuma idan ka kusanci mashin sosai, sai kaji kamar daga daga cikinsa magana ce ke tashi. Wadda kuma kamar ita ma kukan take! Wani babban abin mamaki, duk da fuskar saurayin nan a sunkuye take, sai dai ɗigar hawaye kawai da ake gani, amma ko motsi bayayi, amma a wannan waje da yake akwai Dordor sama da hamsin waɗanda bawai ganinsa ne basu yi ba, a'a tun ɗazu suke nufarsa da mugun nufi, amma suna kusan ƙarasawa sai kaga sun koma da baya. Hasalima ƴan mintuna da suka wuce, wani Dordor mai kai biyar ruwan ƙasa ya nufoshi, amma shima haka ya juya kamar sauran. Kayan jikin wannan saurayi na sarauta, amma daga gaba duk sun jiƙe da hawaye. Wannan saurayin ba wani ba ne illa Yarima Niyashi, daga daular Infiriya, garin Shífa. Bayan kimanin rabin sa'a, tuni a wannan lokaci adadin Dordor ɗin da suka kewaye shi, ya haura ɗari. Amma a wannan lokaci ne ya ɗago kansa a hankali, ya kalli sama, gami da yin ƙuwa mai ƙarfin gaske. Wannan ƙuwwa na tashi, wani abin mamaki ya faru; tamkar da wasa wani haske ya tashi daga jikin mashin nan nasa, wanda yana fitowa wannan ruwa ya fara girgiza kamar wasu abubuwa zasu fito daga ciki. Bayan ƴan daƙiƙu, ruwan ya fara ambaliya, amma bisa mamaki kwata-kwata bai haɗa da kewayen wannan jirgi ba. Acikin wannan hargitsi wata murya mai cike da tsananin ɓacin rai da fushi, kai kace so take ta hallaka duniya baki ɗaya ta fito daga bakin wannan saurayi, ''ɗan uwa Firius, kayi ɓangaren ka, yanzu saura nawa! ''Nayi maka alƙawarin ɗaukar fansarka da kuma samun nasara!!!'' A wani salo mai ban mamaki wannan murya ta ringa ƙaruwa tana bazuwa ta cikin iska da wannan ruwan da kuma ƙasa. Kafin wani lokaci da dama daga cikin waɗanda aka yarda suji wannan magana suka jita, a ko'ina suke kuwa a faɗin ƙasa bakwai. *** Haka dai waɗannan samari dama wasunsu waɗanda zasu fafata a gasar Jinzidal ɗinnan mai zuwa suke ta shiri baji ba gani. A kan doron ƙasa ta huɗu kuwa, a shashin arewa, acikin wani daji mai ban al'ajabi Mutane ne sama da dubu a tsattsaye, wasu na kallo wasu, wasu na tattaunawa cikin raha, kamar suna murnar haɗuwar tasu. Babban abin mamakin wannan dajin shi ne, gashi dai kallo ɗaya tak, zakaiwa wajen kasan cewa daji ne mai shekaru da dama a duniya, domin iskar dake tashi daga wajen ma zaka ji daɗewa ta shekaru acikinta. Amma bisa mamaki babu wani abu daga cikin gimshiƙan kayayyakin daji a wajen; misali bishiyu, namun dawa, da dai sauransu! Babu bishiya ko ɗaya tak a wajen, kuma babu alamun koda dabbar dawa guda a wajen. Hasalima idan baka shiga wajen ba, ko kuma kawai ka hangeshi daga nesa, cewa zakai kurum fili ne, amma kana zuwa wajen jinin jikinka zai baka cewa acikin ƙasurgumin daji kake. Bawai anan abin mamakin ya ƙare ba, idan kuwa da haka ne to da da sauƙi, amma idan ka ɗauke kewayen da waɗannan mutane ke tsaye, to zaka fuskanci cewa kusan ko'ina acikin dajin manyan ramika ne kawai. Iya ganinka, duk inda ka hanga waɗannan ramika ne kurum. Sannan kuma waɗannan ramika kaf ɗinsu idan ka leƙa baka ganin ƙarshensu, hasalima abinda yazo a tarihi shi ne, da damansu basu da ƙarshe. Abin al'ajabi na gaba shi ne, abu ne sananne dama daular Denizawa a ƙarƙashin ƙasa take, kuma ta cikin waɗannan ramika ake zuwa can ɗin. Idan sun yarda kenan!!! Kuma suma ta ciki suke fitowa suyi mu'amala da sauran mutanen duniya. Wanda wannan shi ne ɗaya daga cikin babban abinda yasa da dama suke tsoron takalar Denizawa da faɗa, saboda baka da tayadda zaka iya cimmusu. Domin abu ne bayyananne duk wanda ya shiga ramin nan bai taɓa fitowa da rai ba. Babban dalili kuma shi ne, waɗannan rami ka bawai daular Denizawa kaɗai suka je ba, a'a dama sauran wurare da suka daɗe da ɓacewa a tarihi, waɗanda saboda tsananin haɗarinsu, tuni ma aka gogesu a tarihi. Waɗanda suma duk a ƙarƙashin ƙasa suke. Kuma babban abinda ke jiran duk wanda ya faɗa wannan waje shi ne ɗaya daga cikin waɗannan wajaje, idan dai har ba Denizawa ne suka buɗe buɗe masa tasu hanyar ba. Kai akwai wata hikaya ma data daɗe tana yawo a bakin mutane, cewa ɗaya daga cikin waɗannan duniyoyi da aka goge na karƙashin ƙasa, akwai wajenda mutuwa da kanta ke gadi. To koma dai ba gaskiya bane, kowa yasan babu wanda ya taɓa shiga ya fito, saboda haka babu wanda yake so ya kwada. Shi ne yasa kowa ka gani a wajen yake kaffa-kaffa, duk da kuwa baƙin Denizawa ne, kusan duk waɗanda ka gani a wajen. Mutane ne kawai da suka zo

Chapter 14 of 33