Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
take ya ɗago kai ya dubi AbulBabara inda ya buɗe baki ya ce, "Suna na Armad Dji....." Kan ya ƙarasa rufe baki, AbulBabara ya ɗaga masa hannu gami da ƙura masa kaifafan idanunsa, sannan ya tambayi Armad cikin ɓacin rai, "Armad Djinn ko Armad Wilbafos?" Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 2: Tarifil Fakta Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Tun daga yadda Abul'Babara yai tambayar kasan cewa akwai wani abu a ransa, wanda hakan yasa Armad ya fuskanci lallai ƙarya ba zata fitar dashi daga wannan tarko ba, saboda haka nan take ya amsa da cewa, "na biyun; Armad Wilbafos!" Tsahon lokaci idanun Abul Babara na kansa, kuma kallo ɗaya zakai masa kasan ransa a ɓace. Babu abinda zuciyar Armad keyi sai bugawa, saboda yasan ya riga yayi kuskure, kuma Abul Babara na da dukkan haƙƙin dazai ƙi duba babar tasa, kuma a ƙarshe Armad bazai iya yafewa kansa ba, idan ta rasu ta dalilin wannan. Saboda haka kan kace meye wannan gumi ya gama jiƙa masa riga. Sai dai kuma bisa mamaki abu na gaba daya biyo baya daga ɓangaren AbulBabara shi ne murmushi, inda kwatakwata baima koma takan wancan zance, tamkar ma bai faru ba, ya ɗora da cewa," yanzu saura sharaɗi na biyu. "Shi wannan sharaɗi ba tambaya bace irin na farko ba, umarni ne. "Ina so kayi tafiya aban ƙasa, ka nemo min wani mutum da akewa laƙabi da Tirifil-fakta!" "Indai ka nemo wannan mutun, ni kuma nai maka alƙawarin komai daren daɗewa zaka dawo ka sami mahaifiyarka, a warke, nayi mata magani!" Armad na gama jin wannan batu ya dubi Abul Babara cikin tsananin mamaki, gami da maimaita wannan suna 'Tirifil-fakta!!' Babban abinda ya jefa Armad cikin wannan mamaki shi ne, da daɗewa mahaifiyarsa tasha gaya masa cewa da ita da mutanenta su na neman wani mutun ne mai su na Tirifil-fakta. Kuma ta gaya masa cewa an haramta zancen wannan mutun akan doron ƙasa ta uku, shi yasa ba'a sanshi ba kwata-kwata a garin nasu ba, amma kamar yadda ta labarta masa cewa amsar da zata kai ga cimma wannan mutun, bata kan ita wannan ƙasa, saboda haka ta gaya masa wannan shi ne babban dalili daya zama wajibi akanta da tayi tafiya bisa doron ƙasa domin neman wannan mutun. Wata biyu da suka gabata, sukai maganar ƙarshe akan wannan mutun da mahaifiyar tasa, gab da zata fita wannan yaƙi. Inda ta gaya masa cewa su na gab da cimma burinsu, kuma mataki na ƙarshe ya ta'allaƙa ne kacokam da wannan yaƙi, saboda haka ya wajaba da taje ta bada gudummuwarta. Har kullum Armad ya daɗe yana so ta ringa tafiya dashi a duk lokacinda zatai irin waɗannan tafiye-tafiye, amma a kodayaushe sai tace masa sai ya ƙara girma, kuma saiya gama karatunsa. Yana daga cikin maganganun da Armad yafi tunawa na babar tasa, inda take gaya masa cewa, "kayi haƙuri bazan iya tafiya dakai ba, idan banyi nasara ba wajan nemo wannan mutun a wannan karan ba, to ya rage naka ka ɗora daga inda na tsaya." Irin wannan maganganu, dama sauransu, da Armad ya saba ji daga mahaifiyar tasa, dama kuma yadda yaga ta zuba dukkan ƙarfinta akan neman wannan mutum, shi ne ya sa Armad ya daɗe yana ji a ransa kamar dalilin rayuwarsa ma nada alaƙa da nemo wannan mutun, koma wane ne kuma koma a ina yake. Saboda haka tun baikai haka ba ya ƙudure a zuciyarsa yana gama lodin littattafan da aka wajabta masa, zai ƙara himma wajen karɓar horo, domin shima ya fara taimaka mata cikin wannan aniya ta ta. Hakan nema yasa yana jin sunan wannan mutum a bakin AbulBabara ya cika da mamaki. Armad na cikin waɗannan tunane-tunane ne, ko yanke shawara baiyi ba, yaji muryar Babara ta katse shi, "Armad Wilbafos, kana ganin zaka iya?" To amma abinda Abul Babara bai sani ba shi ne, koma babu wannan sharaɗi nasa, Armad ya daɗe da ƙudure niyyar zuwa nemo wannan mutumi kawai yarjewar mahaifiyarsa yake jira. Saboda haka a wajen Armad, kamar faɗuwa ce tazo daidai da zama. To amma wani hanzari ba gudu ba, wanda ya hana Armad saurin amsawa shi ne, hankalinsa yaƙi kwanciya akan ya tafi ya bar mahaifiyarsa a wajen wannan mutum. Bai ɗauki lokaci ba ya yanke shawara, inda ya fara magana da cewa, "na yarda, amma bis sharaɗi guda ɗaya, kaka na shi ne zaiyi jinyar baba ta, kai kuma can zaka ringa zuwa kana duba ta, idan ka amince ni kuma nayi alƙawarin daga nan ko gida bazan koma ba, zan bazama neman wannan mutun, idan kuma baka amince ba to....'' Babara yai murmushi kawai baice komai ba, kafin daga bisani ya tafa hannunsa biyu, lamarinda yasa wata iska mai kama da guguwa ta tashi sama, wadda ta lafa bayan ƴan daƙiƙu. Bayan lafawar wannan iska, a dai-dai inda wannan guguwar tai tsiri saiga ƙofa ta bayyana aka gabansu a inda da ba komai. Ƙofar shuɗiya ce gaba ɗayan ta, mai matsakaicin faɗi. Saboda tsabagen shuɗinta bama kewayenta kaɗai ba, hatta gaba ɗaya muhallin da suke tsaye saida ya fara komawa shuɗi duk da kuwa akwai ragowar duhun dare a lokacin. Bata da girma sosai, kuma idan da zaka auna da ka fuskanci cewa tsayinta dai-dai yake dana Babara, domin ko Armad bazai iya wucewa ba saiya durƙusa. Nan take Abul Babara ya dubi Armad, sannan cikin sauri ya fara bayani, "bazan iya riƙe wannan ƙofa sama da daƙiƙa ɗari ba! "Idan ka shiga cikinta zaka fice daga cikin wannan ƙasa zuwa wata ƙasar ba tare da ka fuskanci matsalar caje ba, musamman saboda wannan yaƙi da bai daɗe da kammala ba. "Saboda haka ya zama wajibi kai sauri ka shiga idan har kanason tafiya! "Zancen kula da mahaifiyarka kuwa, kamar yadda ka buƙata a wajen kakan ka zatai jinyarta ba'a nan ba. "Sannan kuma zancen alƙawarin mu, yana nan; Idan ka nemo Tirifil-fakta nai mata magani, idan kuma baka nemo ba, to...." Tun kafin ya rufe baki, ƙofar ta fara yin dishi-dishi, alamun ɓacewa. Sai dai kuma shima Armad a lokacin ne ya fara tafiya da sauri domin shiga cikin ƙofar, wadda yana kusa zuwa ta buɗe. Amma har ya ɗaga ƙafa zai shiga, sai ya juyo da sauri, lamarinda yasa AbulBabara yin ajiyar zuciyar da buɗe baki da niyyar magana, amma kan ya ce wani abu ya fuskanci abinda Armad yake nufin yi. Wannan kuwa ba wani abu bane illa yin sallama da mahaifiyar sa, inda ya durkusa, idanu cike da tausayi. Bakinsa ne kawai yake motsi amma sauti baya fita, lamarinda yasa hatta Babara dake kusa dashi baiji mai yace ba. Can bayan kimanin daƙiƙa goma ya tashi tsaye, gami da miƙa hannu ya ciro takobin dake ɗaure a bayanta, ya rataya, sannan ya miƙe cikin sauri ya nufi cikin wannan shuɗiyar ƙofa da sauran ƙiris ta ɓace gaba ɗaya. Yana gabda shiga yaji murya a kunnuwansa tana ce masa, "ka kula da ma'abota Ururu!" Cikin sauri fuska cike da mamaki ya waiwaya dama da hagu sama da ƙasa amma baiga mai maganar ba, kuma ya tabbata ba maganar AbulBabara bace, sannan kuma baya tuna lokacin daya taɓa jin wannan magana a iya tsahon rayuwarsa. Nan take ya tamabayi kansa koma kawai kunnensa ne, amma kuma kalma ɗaya daya kasa cirewa daga zuciyarsa ita ce kalmar, "Ururu", lallai yasan yaji wannan kalma, duk da bai taɓa jinta ba, kuma bai san mai take nufi ba! Amma a lokacin ne Abul Babara yai masa tsawa gami da nuni da cewa ƙofar ta kusa rufewa, saboda hakan nema nan take Armad ya manta da wannan magana daya ji ya faɗa cikin ƙofar. Abu na farko da yai wa Armad sallama yana shiga cikin ƙofar shi ne tsananin duhu, amma ko kaɗan hakan baisa ya canja shawara ba, duk da kuwa yasan cewa Abul Babara ba abin yarda bane, amma kuma yasan bashi da wani zaɓi. Hakan ne yasa duk da haka zuciyarsa gaya masa take kawai ya ƙarasa, saboda haka baiko waiwayo ba, ya danna kai ciki, inda ƙofar ta rufe, kafin daga bisani ta ɓace gaba ɗaya. Koda rufewarta sai Armad yaji wani irin yanayi, kamar ana cillashi sama, nan take kansa ya fara juyawa, kuma kan kace meye wannan ganinsa ya zama dishi-dishi, inda jiri ya ɗebeshi ya faɗi ƙas. Bai san iyakacin tsahon lokacin da yai a cikin wannan yanayi ba kafin daga bisani ganinsa ya dawo dai-dai ba. Kawai abu daya ɗazai iya tunawa bayan ganinsa ya dawo dai-dai shi ne ganinsa da yayi a wani fili wanda babu komai a cikinsa sai wasu fararen bishiyu masu kama da na kuka wajan girma, saidai kuma sun banbanta ta yadda ko ganye ɗay babu a jikinsu, illa kawai wani abu mai kama da ƙaya. Armad ya duba gaba da baya amma babu wani mahaluƙi mutun ko aljan a wurin, kai ko gida babu, sai kurum shi kaɗai a tsaye kwallin kwal. Sai dai kuma bai daɗe acikin wannan yanayi ba ya fara jin takun ɗan adam yana gabato shi daga nesa, ɓangaren kudu maso gabas. *** Kalmar 'Izza' acikin wannan littafi tana ɗaukar ma'anar abu daban ne, da yadda aka saba amfani da ita a harshen hausa. Kamar yadda akai bayani cewa shekarun da mutane gama gari zasu iya yi a duniya da kuma wanda Sadaukai suke yi sun banbanta matuƙa acikin wannan labari. Misali; mafi yawancin mutane gama gari sukanyi shekaru sittin zuwa saba'in ne, amma shekarun da Sadauki zai iya yi sun ninninka haka, kuma irin wannan shekaru na musamman su ake kira da suna 'Izza!' A taƙaice dai wannan kalma tana ɗaukar ma'anar adadin shekarun da sadauki zai iya yi a duniya! Iyakacin yawan shekarun da Sadauki zai iya yi a duniya kan ya mutu, iyakacin yawan Izzarsa, kuma hakan kamar wani mizani ne na gwada ƙarfi da buwaya tsakanin sadaukai. *** Armad na tsaye cak, baiko motsa daga inda yake ba. Can bayan wasu daƙiƙu saiya fara hangar inuwar wani mutun tana dososhi, saboda haka nan take ya miƙa hannunsa kan takobinsa dake rataye a kafaɗarsa ta hagu. Daƙiƙa biyar, daƙiƙa goma, daƙiƙa sha biyar...'aaarrgh', mamaki ya fara shiga zuciyar Armad saboda yanzu daƙiƙa ashirin wannan inuwa ƙaruwa kawai take amma Armad baiga mai ita ba, lamarinda yasa ya fara tunanin cewa idan dai har inuwa tana da wannan tsayi, to mai ita fa, ya yake! To amma baima gama tunani ba yaga wani dattijo ya bayyana daga bayan wannan inuwa, rataye da takobin jan ƙarfe. Babban abin mamakin shi ne, duk da mugun tsayin wancan inuwa da Armad ya gani amma wannan mutun va wani mugun dogo bane, hasalima ƙafa huɗu da rabi ne, wato dai da kaɗan yafi Armad tsayi. Kuma sannan gashinan a zahiri wannan inuwa tasa ce! Kallo ɗaya Armad yai masa yaji zuciyarsa tana neman ficewa daga ƙirjinsa saboda tsananin bugawa, badan komai ba sai dan kasa iya karanta Izzar wannan mutun da yayi! Armad ya daɗe da koyar yadda ake iya karanta Izzar sadauki a gane nawa ce, kuma yana da cikakkiyar masaniyar cewa indai mutun bai ninninka Izzar ka ba, to zaka iya karanta Izzarsa. Sabida haka yana ganin ya kasa karanta Izzar wannan mutun ya gane hakan mai yake nufi. Armad na cikin wannan hali na mamaki yaji murya acikin kansa tana cewa, "idan kana so ka wuce wannan waje to lallai saika ci nasara akaina tukun!" Murya ce kawai, amma saboda ƙarfin Izzar dake ƙunshe acikinta saida Armad yaji tamkar an ɗora masa nauyin dukkan ƙauyensu akansa. Domin tuni ya fara haɗa gumi, data ci gaba da magana da lallai sai ya faɗi ƙas, saboda kurum nauyin da yaji tana ɗauke dashi. Wannan murya bata kowa bace illa wannan mutun dake tsaye a gaban Armad fuska babu alamun komai aciki tamkar wanda ke magana da dutse. Yaci gaba da cewa, "a duk tsahon ɗaruruwan shekarun danai a wannan duniya, kaine mafi ƙaranci Izza dana taɓa gani!" Wannan ba wani abin mamaki bane, saboda a wannan lokaci Izzar Armad hamsin ce kawai da ɗaya! Dattijon yaci gaba da cewa, "kayi sani cewa ƙa'idar wannan hanya ita ce, kodai ka samu nasara akaina ka wuce ko kuma ka rasa ranka anan, duk kai ya shafa! "Sai dai kuma, ka godewa ALLAH, shekara da shekaru na daɗe banga wani ɗan adam ba, sabida haka zanso muɗan daɗe muna fafatawa. Hakan nema yasa zanyi maka taimakon rage Izza ta zuwa ɗari kawai a wannan fafatawa da zamu yi." Jin wannan magana ƙara firgita Armad yai kawai, maimakon ya kwantar masa da hankali, badan komai ba saboda yana da cikakkiyar masaniyar irin nisan dake tsakanin Izzarsa wato hamsin da ɗaya da kuma Izzar mai mataki na ɗari. Musamman idan ya tuna irin wahalar da mutun yake sha, kafin ya haura daga casa'in da tara zuwa ɗari. Sannan kuma duk wannan ba wani abu bane idan aka kwakwanta da ainihin girman Izzar wannan mutun dake gabansa. Yana cikin wannan tunani ne ya ƙara jin muryar wannan dattijjo a kunnensa, "duk sanda ka shirya zaka iya farawa!" To amma da yake Armad mutun ne mai saurin lissafi musamman a yanayi na buƙata, nan take ya yanke shawarar mai ya kamata ya aiwatar. *** Aljanu kala-kala ne, akwai daga cikinsu masu aman wuta, akwai masu aman ƙanƙara, wasu kuma iska, wasu turɓaya wasu ƙarfe, wasu tsawa, wasu ruwa...... Kai duk wani abu da zaka iya tunani akwai aljanin da yake iya sarrafashi!!! To kamar dai yadda aka sani, kusan kowanne ɗan adam yana da aljaninsa; wasu ana haihuwarsu suke yin hannun riga da nasu aljanin, wasu kuma basa rabuwa da nasu, wasu suna bautar dasu, wasu kuma saidai aljanun su bautar dasu. To waɗanda daga cikin mutane suka samu damar bautar da irin waɗannan aljanu, sune wanda zaka ga suna iya amfani da irin waɗancan abubuwa kamar su wuta, ƙanƙara, iska, tsawa, ƙarfe, ruwa, turɓaya,...kai dadai sauransu! Kuma suna hakan ne ta hanyar arar ƙarfin waɗannan aljanu nasu! To badan komai ba saboda horo da Armad ya samu daga wajen kakansa, shima ya samu ya bautar da nasa aljanin, wanda kuma wannan aljani nasa 'tsawa' yake iya sarrafawa! Lamarinda yasa shima Armad ya zamanto yana iya sarrafa tsawa a duk sanda yaso!! *** Nan take Armad ya zare takobinsa, lamarinda yasa tsawa da walƙiya ta fara rawa akan takobin tana fitarda wani sauti. Abin mamaki a wannan lokaci sai shima wannan dattijo ya zare takobinsa, inda bisa mamaki wata irin wuta ta fara tashi daga jikin takobin, lamarinda yake nunawa a fili cewa shima wannan dattijo ya bautarda aljaninsa, kuma aljanin nasa wuta take sarrafawa!!! Ba tare da tsayawa ɓata lokaci, Armad yayi wo kan wannan dattijo gadan-gadan da niyyar aiwatar da shawarar daya yanke. Babu abinda ke tashi daga jikin takobinsa illa walƙiya da alamun tsawa, acikin udanunsa babu tsoro ko kaɗan. Jan kyallen dake ɗaure a gaban goshinsa kawai kaɗawa yake akan iska. Hannayensa a buɗe; na dama a dunƙule na hagu kuma rike da takobinsa. Duk inda ya wuce sai kaga ita kanta iskar wajen ta fara tarwatsewa acikin wannan walƙiya. Daga nesa idan ka hangi Armad cikin farar riga, baƙin wando, riƙe da takobi mai walƙiya, saika rantse wani ɗan saƙon mutuwa ne. MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 3: wasi wasi part 1 Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Idan mai karatu bai mantaba, a Babi na biyu mun tsaya a inda Armad Wilbafos ya zare takobinsa, wadda tsawa da walƙiya suke rawa akan farin ƙarfenta, ya kuma yiwo kan wannan mutun mai matakin Izza ɗari, wanda ya bayyana acikin wannan duniya, ya kuma bayyanawa Armad cewa indai yana so ya wuce, to sai yaci galaba akansa. To daga nan zamu ci gaba! *** A shekarar dubu ɗaya da ɗari takwas da arba'in da bakwai 1847 bayan Amri, akan doron ƙasa ta uku ɓangaren arewa. Acikin wani fili mai matsakaicin girma, wanda ya kasance a kewaye da busassun itatuwan bishiyar giginya, wasu mutane guda biyu, saurayi da dattijo suna tsaye suna fuskantar juna a wani salo mai kama dana malami da ɗalibi. Wannan saurayi na sanye da farar ƴar shara mara girma sosai kuma iya ƙugu, sannan yana sanye da baƙin wando zuwa tsakiyar ƙaurinsa, idan ka kalli fuskarsa zaka ga jan ƙyalle a ɗaure a gaban goshinsa, wanda iska take ta kaɗawa. Duk da cewa akwai ragowar duhun dare a lokacin, amma idan ka lura sosai zaka gano cewa wannan saurayi ba wani bane illa Armad Wilbafos! Wannan dattijo kuma dake tsaye a gabansa ba wani bane illa kakansa wanda akewa laƙabi da farfesa-Zaikid. Kallo ɗaya zakai kasan cewa horo ake bawa Armad. Wannan dattijo ya buɗe baki gami kyaran murya yana mai cewa, "abun alfahari ne ga sauran al'umma su zamanto sunkai matakin bautar da aljanunsu domin su ringa amfani da fasahar su, amma kai a wajenka ba wani kayan gabas bane! "Saboda kai ɗan zuriyar Wilbafos ne, kuma tsarin rayuwarka ya banbanta da sauran, saboda haka kada ka saki jiki wai dan ka haura wancan mataki! "Yanzu abu na gaba dake gabanka shi ne kwarewa akan wannan tafarki naka na 'Aradu, tsawa da kuma walƙiya'. "Kai sani cewa na kira ka wannan waje ne a wannan rana saboda abu ɗaya kawai; domin na fara koyar dakai waɗansu manyan fasahai guda biyu! "Ɗaya daga ciki zaka iya koya a yanzu, amma amfani da ita sai sanda Izzarka takai mataki na ɗari, ta biyun kuma ita ce wadda zaka iya amfani da ita nan take!" Yana zuwa nan a zancansa wata iska mai ɗauke da sanyin asuba ta busa, lamarinda yasa babbar rigar dake jikinsa ruwan ƙasa, ta kaɗa sama wanda hakan ya bayyanar da wata doguwar takobi sanye acikin kufe rataye acikin babbar rigar tasa. Farfesa Zaikid ya ƙara ɗaga kai ya dubi Armad gami da tambayar sa, "mai kake gani a tunaninka tsakanin iska da tsawa wacce tafi wata gudu?" Armad najin wannan tambaya ya cika da mamaki, domin shi a iya saninsa babu abinda yakai iska sauri, saboda baya ganin akwai wani abin tambaya ma akai, saboda haka nan take ya bada amsa da cewa, "farfesa, iska tafi sauri ni a gani na." (Yawanci indai suna wajen horo, Armad yafi so ya kira kakan nasa da farfesa.) Farfesa Zaikid najin haka yai murmushi, gami da cewa, "amsarka ba dai-dai take ba! "Indai zance kake na sauri, tsawa tafi. Kuma sannan tafi daɗin sarrafawa ga bil'adama dama aljanu. "Kai a tunaninka, daƙiƙa nawa tsawa take ɗauka ta iso tun daga sararin samaniya zuwa doron ƙasa! Bai kai ko rabin daƙiƙa ba!" Armad najin haka ya cika da mamaki, inda daga bisani kawai ya gyaɗa kai, amma duk da haka fuskarsa cike take da kokwanto. Lamarinda yasa kakan nasa ya dubeshi yai murmushi, gami da cewa, "a yanzu ba lalle kai amanna ba, amma a hankali zaka fuskanci abinda nake nufi. "Nasan cewa kasan wata fasaha ta saran takobi, wadda masu amfani da aljanun da suke sarrafa iska suke amfani da ita, wadda sukewa laƙabi da 'gayawa jini na wuce'?" Armad ya ce, "eh nasani farfesa, ita ce wadda take amfani da tsananin sauri wajen saran mutun tayadda har sai ta wuce sannan jini yake fitowa. Hakan nema yasa baka taɓa ganin jini a jikin takobin kwararrun da suke amfani da aljanu masu sarrafa iska." Bayani akan ire-iren fasahai abu ne wanda kakan nasa ya daɗe da koya masa, shi yasa Armad baisha wahalar bada wannan amsa ba. Kakan naji ya kyaɗa kai alamun amincewa da abinda Armad ya faɗa, sannan kuma ya ɗora da cewa, "Armad kasan cewa akwai fasahar saran takobi wadda tasha gaban 'gayawa jini na wuce'?" Armad najin haka ya gwale ido cikin al'ajabi da mamaki, "farfesa wadda tasha gaban 'gayawa jini na wuce' fa! "Zaiyiwu kuma?" Mamaki ya bayyana ƙarara a fuskar Armad. Murmushi kawai farfesa Zaikid yayi, gami da zira hannu cikin rigarsa ya fito da wannan takobin, sannan ba tare da ɓata lokaci ba yaja daga ya fara horar da jikansa Armad akan waɗannan fasahai(fasahohi) guda biyu! *** Acikin wannan duniya kuwa da Armad ya tsinci kansa, a dai-dai wannan lokaci yana riƙe da takobi tsirara yayi kan wannan mutun da niyyar afka masa, sai dai kuma a daidai lokaci ne, shima wannan mutun ya ɗaga tasa takobin sama, wadda tuni ƙarfen takobin wanda na jan ƙarfe ne ya kama da wuta tamkar wanda ake sawa ziga-zigi. Kallo ɗaya zakai masa kasan cewa babu alamun zai ragawa Armad ko kaɗan acikin wannan fafatawa. Kan Armad ya ƙaraso takobin dattijon ta gama tashi sama, inda nan take, ta dai-dai ɓangaren da Armad yake nufowa wannan mutun ya ɗaga takobin ya sari iska da ita. A dai-dai lokacin da saran takobin tasa ya sauka babu wani canji daya faru ko kaɗan, kai kace ma babu abinda ya afku, amma daƙiƙu biyu kacal bayan ya sauke takobin tasa ƙasa gaba ki ɗayan ilahirin iskar dake kewayen wajen ta fara ɗaukar wani azababben zafi irin na musamman. A kimanin daƙiƙa ta huɗu bayan saran iskar da wannan mutun yai, wannan iska takai ƙololuwar ɗaukan zafi, lamarinda saida yasa Armad Wilbafos cin birki daga afkawa wannan mutun, badan komai ba saboda duk wani taku daya ƙara a wajen kusantar wannan dattijo, ji yake zafin wannan iska yana ƙara ninninkawa tamkar wanda aka sa acikin wuta. Sai dai kuma da ace a iya nan wannan ibtila'i da yake fuskanta ya tsaya toda da sauƙi, amma ina! A kimanin daƙiƙa ta shida bayan saran iskar, gabaki ɗayan ilahirin iskar dake tsakanin Armad da wannan mutun ta kama da wuta, wadda ta fara ci tamkar wadda ake zubawa fetir. Kan kace meye wannan tuni wanan wuta ta fara dunƙulewa a waje ɗaya. Inda a kimanin daƙiƙa ta goma bayan wannan saran iska, wannan wuta ta ƙarasa dunƙulewa zuwa wani ƙatoton dunƙulen wuta murje akan iska, inda ta bada wata sifa mai kama da ƙatoton al'amudin wuta irin wanda mutanen farko suke azaba dashi! Baki a buɗe cike da mamaki, Armad ya ƙurawa wannan dunƙule ido, amma kafin ya samu damar yin wani abu tuni wannan dunƙule ya fara motsi, inda kan kace meye wannan ya fara mirginawa yana nufoshi da gudun gaske. A dai-dai kimanin daƙiƙa ta goma sha ɗaya bayan saran wannan iska, wannan wuta ta ƙaraso dai-dai wajen da Armad yake tsaye riƙe da takobinsa tana neman haɗiye shi. Nan take zuciyar Armad ta fara bugawa tana bayyana masa alamun tsananin firgici, lamarinda yasa yaji a jikinsa cewa lallai indai ya bari wannan wuta ta taɓa shi, tofa lallai kwanansa ya ƙare a ban ƙasa. A dai-dai lokacin da wannan wuta ta fara taɓa jikin Armad a lokacin ne ya buɗe baki ya kira ɗaya daga cikin ɗalasiman da ya koya a wajen kakansa farfesa Zaikid, wanda ake cewa "ƘABAN'SHISU!" Yana furta wannan ɗalasimi ya ɓace ɓata daga inda yake, inda ya bayyana a can gefe cikin yanayi na galabaita. Ita kuma wannan wutar taci gaba da tafiya cikin sauri, inda taje ta haɗu da ɗaya daga cikin manya-manyan bishiyun nan masu kama dana kuka. Suna haɗuwa nan take wannan bishiya ta juye izuwa toka, kuma duk da cewa girman wutar ita ma ya ragu, amma bai ƙare ba domin saida taci gaba da tafiya ta ƙara samun wata bishiyar irinta, wadda itama ta koma toka. A haka a haka saida nan take bishiya biyar suka dagargaje izuwa toka, kafin wannan wuta ta ƙare. Armad wanda yasha dakyar yana gefe yana kallon abinda ke faruwa, ajiyar zuciya kawai yai ya kuma tabbatar da cewa, kiran wannan ɗalasimi da yayi ita ce shawarar data dace a wannan lokaci duk da kuwa hatsarin dake tattare da ɗalasimin. Armad yana da cikakkiyar masaniyar sau ɗaya kacal zai iya amfani da wannan ɗalasimi mai suna, 'ƙaban'shísu' a shekara. Shi dai wannan ɗalasimi, kakan nasa ne ya koya masa shi saboda tsaro, domin yayi amfani dashi a irin yanayi mai matuƙar hatsari domin ya kuɓucewa halaka. Domin shi wannan ɗalasimi idan mutun ya kware ashi, yana da damar ɗauke mutun daga duk inda yake ya kaishi wani wajen daban, ta haka kenan mutun zai iya guduwa daga hatsari komai girmansa, kuma Armad yana da yaƙinin cewa ko daga cikin wannan waje yake son tafiya, wannan ɗalasimi zai iya ɗauke shi. Sai dai kuma shi Armad ɗin yana da cikakkiyar masaniyar sharaɗin da ake buƙata kafin hakan ya faru, wanda shi ne sai kasan wajen da kake so kaje sosai da sosai acikin ranka, wanda kuma zaka aiyana a yayinda kake ambatar ɗalasimin. To matsalar ita ce duk inda Armad ya sani a wannan lokaci doron ƙasa ta uku ne, wanda kuma shi bashi da niyyar komawa can. Hasalima tunda jimawa yayi rantsuwa acikin ransa cewa komai wuya komai daɗi, komai duhu komai tsanani komai wahala saiya nemo wannan mutun da ake cewa Tirifil-fakta, koma wane ne, kuma koma a ina yake!! Armad na cikin wannan yanayi ne, wannan dattijo ya ƙara ɗaga takobinsa wadda har a lokacin bata daina ci da wuta ba, ya kuma kara sarar iska da ita. Armad yayi tunanin cewa dama zai iya ƙara turo masa da wannan irin harin na farko, kuma tuni ya ƙudure a ransa abinda zai aiwatar idan hakan ta faru. Amma kuma bisa mamaki wannan takobi na dukan iska, maimakon dunƙulen wuta irin na baya, kawai sai wata koriyar wuta ta fara fita daga tsinin takobin, lamarinda yasa fuskar Armad ta ƙara canjawa. Ba'a haura daƙiƙa biyar ba wannan wuta ta gama ficewa gaba ɗaya, a lokacinda wannan mutun wanda har a lakacin idanunsa suna kafe akan Armad. A wani yanayi mai nuna cewa bazai ɗauke su daga kan Armad ɗinba har yaga ya daina numfashi. A kimanin daƙiƙa ta uku bayan ficewar wutar, wani zazzafan gumi ya fara ɗisa daga jikin jan kyallen dake ɗaure a gaban goshin Armad. Ba komai bane ya janyo haka ba illa ganin da yayi wutar ta fara lankwashewa tana buɗewa. Abu kamar wasa akan idonsa, cikin daƙiƙu uku masu zuwa wannan koriyar wuta ta canja siffa zuwa zagaye, inda ta bada fasalin ƙawanya. Da farko girman ƙawanyar baifi kimanin taku ɗaya ba, amma kan kace meye wannan ta fara buɗewa tana ƙara girma, cikin kowacce daƙiƙa tana ƙara buɗewa da kimanin girman taku uku, sannan kuma Armad ya lura cewa ta fara motsi tana kusanto shi a lokaci guda. Duk da cewa ba sauri take sosai, amma firgicin da zuciyarsa take gaya masa a lokacin, sun ninninka wanda ya ji ɗazu a lokacinda yai arba da wannan wutar ta farko. To da ace ma a iya haka abin ya tsaya, toda da sauƙi. Amma ina, a dai-dai wannan lokaci ne ya fuskanci cewa duk inda wannan ƙawanyar ta gifta akwai wani abu mai kama da toka da yake murmushewa ta bayanta. Saboda haka nan take wasu tunane-tunane akan abinda yake gani suka kwaranyo masa a zuciya. Kusan zaka iya cewa yasan abinda yake faruwa, amma yaƙi yadda saboda tuni gumi ya gama jiƙa masa riga, badan komai ba sai dan cewa, yasan lallai in abinda yake tunani ne, to al'amari yakai ƙololuwar lalacewa. Saboda haka nan take ya durƙusa cikin zafin nama, ya ɗebi ƙasa a tafin sa, sannan cikin sauri ya miƙe ya watsata cikin wannan ƙawanyar koriyar wuta da take gabato shi. Wannan ƙasa ta tafi cikin sauri, tana zuwa ta shige cikin wannan ƙawanya, kuma ta fice ta baya. Amma bisa mamaki bawai

Chapter 2 of 33