Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bayani kaɗan akan darajar Ayrid. Shi dai Ayrid kamar yadda aka labarta a baya kwaya ce ƴar ƙarama kamar masara ko kuma dawa. Wasu su na zuwa manyan wasu ƙanana. Kowanne yana da launinsa na daban. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, akwai busasshen Ayrid, akwai kuma ɗanye. Dukkaninsu daga irin bishiya (zangarniya) ɗaya suke. Shi busasshe, shi ake sarrafawa izuwa sisi da kwandala domin kashewa. Akwai ma'aikatu na musamman dake shalkwatar Ururu wanda ke sarrafa irin wannan Ayrid. Shi kuwa ɗanyen Ayrid shi ne wanda keda mataki-mataki kamar yadda aka gani a baya. Kamar wanda Nusi tayi amfani dashi (mai keken doki). Akwai wasu da dama irinsa. Ana iya amfani dasu wajen ajiya na kayan abinci ga matafiya ko kuma kayan yaƙi. Akwai na magani, akwai na sihiri, akwai masu ƙara ƙarfin Izza. Kai dama dai sauransu. Kuma iya matakin Ayrid ɗin, iya darajar abubuwan da zai iya yi. Idan ka duba zaka ga sama da kaso casa'in da tara na al'umma iyakacin wanda suke iya mallaka, shi ne mai daraja ta uku, wanda dashi zaka ga suna tura saƙo komai nisan waje, kuma su karɓa. Sannan kuma su iya ajiye kayansu a yayin tafiya. Amma Ayrid masu daraja sama da uku amfaninsu bazai lisaafu ba anan, domin kuwa idan muka fara za'aci shafuka da dama anayi, saboda haka ku biyu mu a gaba zakuga irin al'ajabin dake ƙunshe cikin wannan ɗan iri da akewa laƙabi da Ayrid! Bayan kimanin mintuna sha biyar, alƙalin wasa ya bada umarnin su Armad su shiga cikin filin su uku. Inda bayan sun shiga suka tararda wannan abu da ake cewa Alkadar! Wannan dai ba wani abu bane illa wani mutun-mutumi da akai da jan dutse. Komai kamar na jikin mutun ne, amma a wajenda ya kamata ace fuska ce, sai ya zamana kamar gilas ne kawai, daya rufe kaf wajen. Aciki akwai hoton lambobi guda uku a jere, wanda ba wani abu bane illa sikelin wannan abu mai suna Alkadar. Kuma kamar yadda Nusi ta bayyanawa Armad cewa abinda kawai yake da buƙata yayi shi ne, yayi amfani da sak irin Izza da yai amfani da ita ya wuce mataki na farko, ya tattare ta ya kuma daki cikin wannan mutumi da ita. Ta kuma gaya masa cewa wannan sikeli ɗaya zuwa ɗari ne, kuma duk wanda ya fi kowa lamba shi ne zai wuce zagayen gaba! Saboda haka a lokacin Niyashi shi ne a gaba, Kiru na biyu, sannan kuma Armad na ƙarshe. Cikin sauri, fuska a murtuke, Niyashi ya isa kusa da wannan mutun-mutumi, inda ya ɗaga hannu ya daki cikin wannan mutun-mutumi. Hakan na faruwa lambobin dake fuskarsa suka fara bada haske, sannan suka fara motsi. Kan kace meye wannan tuni sun wuce hamsin... sittin..saba'in, inda suka fara rage sauri. Amma dukda haka saida suka kai tamanin da tara, sannan suka tsaya. Kan kace meye wannan shewa ta ɓarke, tuni har an fara taya ƴan Infiriya murna. Kasancewar dama abinda su Armad basu sani ba, shi ne, mafi girman makin da aka taɓa samu a gasar Jinzidal ƙarama shi ne casa'in da ɗaya, saboda haka samun tamanin da tara a wajen Niyashi lallai abin yabo ne. Ana cikin haka ne Kiru ya isa gaban Alkadar, inda ya ɗaga takobinsa da niyyar ya caki cikin Alkadar ɗin dashi, amma a wani salo mai ban mamaki wata murya ta fara magana acikin kunnensa, wadda kuma shi kaɗai ke iya jinta, duk da kuwa ba'a hankali take maganar ba!! Nan take hannunsa ya tsaya cak a sama, abinda yasa ƴan kallon buɗe baki. Wannan murya cike da wata irin Izza mai ban mamaki ta ci gaba da raɗa masa, ''kada kayi amfani da sama da kaso tamanin na Izzarka!'' Wannan murya na gama faɗa ta ɗauke, inda takobin Kiru ta ci gaba da tafiya daga inda ta tsaya. Ta kuma ƙarasa ta daki cikin Alkadar ɗin, lamarinda yasa wata ƙara tayi sama sannan lambobin suka motsa kuma basu tsaya ba har saida suka je sittin!! Shiru kamar mutuwa ta gifta, haka mutane suka kwalalo masa ido yayinda ya juyo kansa a sunkuye cikin ƴan tawagarsa. Kai hatta alƙalin bai iya cewa komai ba har Armad ya tashi ya isa gaban Alkadar ɗin! Domin babu wanda zaiyi tunanin ɗan Behanzin guda zai tsaya a sittin kawai. Armad na isa yasa hannu ya zare takobinsa dake rataye a kafaɗarsa ta hagu, wato takobin mahaifiyar tasa wadda tun a farkon fitowarsa daga gida yake tare da ita. Ya kuma ɗagata sama, inda iya ƙarfinsa ya sari Alkadar ɗin a ciki! Wanda hakan na faruwa lambobin nan suka fara motsawa cikin sauri. Basu fara rage gudu ba, har saida suka kai sittin da biyar, inda suka fara juyawa a hankali a hankali har suka isa tamanin da takwas dai-dai!!! Inda suka tsaya cak! Armad ya tsaya kurum yana kallon waɗannan lambobi, kamar wanda bai yadda da abinda yake gani ba. "Lamba ta bata kai ta Niyashi da ɗaya ba kenan?" cikin mamaki Armad ya girgiza kai. Domin ya fuskanci mai hakan yake nufi. Wato dai dashi da Kiru sun fita kenan, shi kuma Niyashi yayi nasara. ____ To ko waye yayi wa kiru magana ta kunnensa? Ko mai zai faru bayanda Armad baiyi nasara ba? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 33: Bayyanar Ururu Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos . Armad saida ya ware dukkan ƙarfin dake dantsensa sannan ya afkawa wannan Alkadar da sara. Amma bisa mamaki gashi akan idonsa yana gani cewa ƙarfin wannan fasaha bata kai ƙarfin fasahar da Niyashi ma'abocin mashi yayi amfani da ita ba! Koda yake Armad kusan yayi tunanin hakan zai iya faruwa, tunda dukkanin waɗannan samari da yake karawa dasu yara ne waɗanda suke karɓar kulawa ta musamman daga manyam ƙabilu. Wanda ma zaka iya cewa acikin ƙabilunsu anai musu kallon waɗanda zasu jagoranci ƙabilun ne a gobe. Saboda haka Armad yayi tunani cewa lallai dukkaninsu baza suyi amfani da ƙananun fasahohi ba ko kaɗan, kuma su ɗin ba ababen da Armad zaiyi wasa da su bane! Musamman duba ga cewa ya rasa Miyurarsa. Kuma hakan ya ƙara tabbata acikin ransa, a lokacin da yaga makin da Niyashi ya samu. Kamar yadda ta gaya masa, amfanin Alkadar ɗin shi ne, a tantance tsakanin waɗanda suka samu maki ɗaya, wane ne Izzar da yayi amfani da ita tafi ƙarfi. Hakan zai iya kawo adalci, domin tunanin cewa wani lokacin Izzar ka zata fi ƙarfi, amma ka gamu da abokan gabar da zasu fi na ɗan uwanka. Saboda haka shi Alkadar abu ne da zai banbance tsakanin dukkan Izzan da akai amfani dasu domin fitarda wanda yake gwani na gaskiya acikin wanda suka sami maki iri ɗaya. Saboda duk waɗannan abubuwa, duk da tunanin dake ran Armad ya daure bai ƙara ko kuma canja Izzar tasa ba, amma kuma bisa takaici gashi makinsa bai kai ba. Abu na farko daya fara zuwa ransa shi ne, irin imanin da Nusi tayi cewa shi zai ci, amma gashi ya faɗi. Saboda haka da wace fuska zai kalle ta ma!! Shi ne kawai tambayar da yakewa zuciyarsa. Acikin wannan waje na manyan baƙi kuwa, tun kusan sanda Uznu ya gayawa sarki Deniz abinda ke tafe dashi, sarkin ya shiga wani yanayi, bai kuma ƙara cewa komai ba sai a wannan lokaci, inda ya motsa domin bada umarnin a kaɗa wasa domin zuwa zagaye na gaba. Sai dai kuma a wannan lokaci ne, mutumin dake zaune a gefensa, wato Uznu'Ururu, wanda tunda yazo bai buɗe idanunsa ba, kai kace dama can a haka aka yisu, ba'a taɓa buɗe suba. Amma a wannan lokaci ya buɗe idanun nasa!! Yana buɗewa sarki Deniz duk da ba kallonsa yake ba, yaji wani gumi ya keto masa, gami da rawar ɗari. Nan take ya gane maike faruwa!!! Saboda haka ya fasa abinda yake niyyar yi na bada umarnin a fara zagaye na gaba. Kawai ya tsaya cak, a inda yake. Duk da cewa sarki Deniz shi ya tsayar da kansa yana sane, amma al'amarin ba haka yake ba, ga ragowar sauran duk mutanen dake wajen, idan ka ɗauke Asifu, wanda shi ma ya nutsu, kuma kamar wata ibada ya daina motsi kwatakwata gami da kallon gabansa kamar yadda Deniz Iluru yayi! Amma kama daga kan wanda suke hira da Asifu, zuwa kan dukkanin ragowar mutanen da ke cikin wajen manyan baƙin, zuwa kan waɗannan samari guda shida da masu kula dasu, harda su Armad da Nusi. Zuwa ga dukkanin ƴan kallon dake wajen da dukkanin waɗanda ke bibiyar abubuwan dake faruwa acikin wannan fili saida suka shiga cikin wani yanayi mai ban mamaki. Abinda kuwa ya faru shi ne, kowa daga cikinsu ya tsaya cak a dai-dai inda yake, kuma acikin abinda yake yi. Misali idan ka kalli Armad zaka ganshi a tsaye a gaban Alkadar ɗin, kuma yana ƙoƙarin juyawa, amma daga ganin cikin idanunsa kasan akwai wani dalili da yasa baya son juyawa. Idan kuma ka kalli Nusi zaka ganta a tsaye cak, hannunta yana rufe da fuskarta kamar wadda ke ɓoye wani abu. Wani daga gefenta kuwa magana yake mata a kunnenta na dama. Haka dai kowa ka kalla zaka ganshi a ƙame cak baya ko motsi. Dukkanin abubuwan dake faruwa, ba wani abu bane ya jawo su ba, illa buɗe wasu idanu guda biyu rak. Idan da waɗannan mutanen na cikin hankalinsu da sun lura da cewa wajen da suke kwatsam ba dalili ya fara yin duhu. Duk da kuwa ba yamma bace, ba kuma dare bane! Rana ce tsaka, sannan kuma ga futulu ko'ina a wajen! Tamkar kawai wani abu ne yake zuƙe dukkanin hasken wajen baki ɗaya. Sai dai kash! Da ace wani daga cikin mutanen nan dake wajen yana cikin wajen manyan baƙin nan, kuma hankalinsa na jikinsa kamar Deniz Iluru da Asifu, da yaga cewa haka abin yake! Wato waɗansu idanu ne guda biyu, dukkanin cikinsu gaba ɗaya baƙi ne kurum. Baƙi-ƙirin, babu zancen wani farin ido, babu komai sai baƙi. Irin baƙin nan da idan ka kalla zakaji tamkar ana jan ka ciki saboda tsabagen duhu. To idan da iyakacin abubuwan da suke faruwa kenan to da da sauƙi, amma ina! Idan ka kalli waɗannan idanu zaka ga cewa a zahiri dukkanin hasken wannan waje cikinsu yake shigewa, tamkar dai wani abu ne acikin idon wanda yake zuƙe hasken. Ko kuma shi kansa hasken ne da kansa yake ji cewa bai kamace shiba ya kasance a waje ɗaya da waɗannan idanuwa guda biyu a waje ɗaya ba, wato yana ji cewa yayi rashin kyautawa! Kafin kace meye wannan komai dake wannan waje ya koma duhu, duhu dun ɗum! Amma abin mamakin a dai-dai lokacin kuma kowa ya dawo hayyacinsa, kowa ya ci gaba da abinda da yake yi, tamkar wani abu bai faru ba. Amma a wannan lokaci ne kowa ya kula da duhun dake wajen, wanda da ba haka yake ba! Kafin kace meye wannan idanun kowa sun koma kan abu guda ɗaya rak dake da ragowar haske a wajen. Wannan abu ba komai bane ba illa wannan Alkadar dake gaban Armad, saboda haka kan kace meye wannan hankalin kowa ya dawo kansa. Wani abin mamakin shi ne, akan idon kowa lambar da da take kan tamanin da takwas ta juya ta dawo tamanin da tara, wato dai-dai da Niyashi. Hakan na faruwa waɗannan idanu wanda idan ka kula zaka ga ba na kowa bane illa, Uznu'Ururu suka rufe ruf. Wanda tamkar an kawo wuta dukkanin wannan duhun ya ɗauke ɗif, wajen ya dawo kamar yadda yake a da. Kuma komai ya ci gaba da yadda yake. Tamkar babu abinda ya faru. Amma banda abu ɗaya; wannan kuwa shi ne makin Armad, wanda ya ƙaru da ɗaya. Kuma babban abin mamakin shi ne, abinda kowa kawai yake iya tunawa shi ne Armad ya samu maki ɗaya da Niyashi. Hasalima idan ka matsa kusa da jama'a, zaka ji maganar abinda zai faru a gaba kawai suke; wanda kowa ya riga ya sani, cewa fafatawa ce gaba da gaba taakanin Armad da Niyashi, wanda yaci nasara kuma shi ne zaije kewaye na gaba! Babu wani abu da zai iya yin bayanin haƙiƙanin abinda ya afku, wanda yasa dukkanin mutanen dake wajen duk da sun gani da idanunsu cewa makin nan ƙaruwa yayi da baya, amma kowa acikinsu, hatta Armad ɗin abinda ke ransa shi ne ya sami maki iri ɗaya da Niyashi, kuma bisa ƙa'idar gasar kamar yadda Nusi ta gaya masa abu na gaba shi ne su biyu su kece raini! Saboda haka abinda ke ransa kenan kawai. Wato dai a taƙaice kowa ya manta duk abinda ya faru. Amma kuma wata tambaya da Deniz Iluru yayiwa Uznu'Ururu ita ce ta nuna cewa shi ɗin lallai yasan mai ke faruwa a wajen ba kamar sauran mutanen wajen ba, ''Uznu, mai yasa ka taimake shi?'' Uznu Ururu ya amsa masa da cewa, ''Wancan yaron mai suna Armad ya nada abinda nake buƙata, amma ina so na tabbatar kafin nayi wani abu. Kuma lallai indai ya fita daga gasar a wannan mataki, tabbatarwar zata yi wuya.! ''Saboda haka ina son naga fafatawarsa, domin na tabbatar da abinda nake tunani! Shi kuwa Asifu na gefe sun ci gaba da tattaunawa akan Izza da wannan Badenize, wanda yai matuƙar nutsuwa, kai a sunkuye yana sauraron wani bayani daga Asifu, ''Deniz Kalhari, girma da faɗin al'amuran Izza sun wuce yadda kake faɗa! ''kasan kuwa hatta kwakwalwa tana riƙe abubuwan da suke faruwa na yau da gobe, a mataki-mataki ne kuwa. ''Wanda kuma gaba ɗayan waɗannan matakai sun ta'allaƙa da Izza ne! ''Misali, zaka iya raba abubuwa zuwa gida uku; na farko abinda kwakwalwarka zata iya riƙewa, wanda kamar kace Izzar ka zata iya kusantar wannan abu ne harta iya riƙeshi acikin kwakwalwarka. ''Na biyu abinda baza ka iya riƙewa ba, wanda wannan kuma shi yake nuna cewa Izzarka baza ta iya kusantar wannan abu ba, wanda kuma idan tayi to tarwatsewa zatai, shi yasa kawai saita haƙura, tayadda kai kuma bazaka iya taɓa tuna wannan abin ba, har sai sanda Izzarka takai wannan mataki!! ''Sai kuma mataki na ƙarshe wanda ke tsakatsakiya, wato zaka tunowa amma rabi da rabi!!'' Asifu yai shiru kamar wanda yake tunani, sai daga ƙarshe ya ɗago kai ya ƙara duban Deniz Kalhari, ya ce, ''Deniz, kasan a wanne mataki kake idan aka kwatanta ka da wancan mutumin dake zaune idonsa a rufe?'' Cikin sauri Deniz Kalhari ya miƙa ido ya hangi Uznu'Ururu, sannan ya dawo da kansa izuwa Asifu, gami da cewa, ''nasan yafi ni ƙarfin Izza, amma dole ma a mataki na farko nake dashi. ''Domin a irin ƙarfin Izza ta, dole komai ƙarfinsa bazai yimin nisan da zan shiga kashi na uku dashi ba, idan aka dubi wannan labari naka. Wato dai ina nufin duk abinda Izzarsa zatai, to inada ƙarfin Izzar da kwakwalwata zata iya riƙewa!!'' "Hmmm!!!" Asifu yaja wani kwauron numfashi. "Hakane!" Wannan kawai shi ne abinda Asifu ya bashi amsa dashi gami da murmushi, sannan ya bayyana masa cewa tattaunawar su akan Izza tazo ƙarshe a wannan lokaci, sai dai ko wataranar. Domin yana so ya kalli ragowar wasannin da zasu kasance! Haka Asifu yace, amma a zahiri abu ɗaya ne kawai a ransa. Yana tunanin cewa wannan Badenize mai suna Deniz Kalhari bai masan matsayinsa ba a harkar Izza. Saboda haka babu amfanin yaci gaba da bayani akan Izza dashi. Sannan kuma ya maida idanunsa izuwa cikin filin da ake shirye-shiryen fafatawa tsakanin Armad da Niyashi. Idan ka lura sosai zaka idanunsa na kan Armad Wilbafos!!! Babu abinda yake kewayawa acikin ransa sai tunanin mai yasa Uznu Ururu ya taimaki wannan yaro. Sannan kuma menene tsakaninsu. Lallai zaiso yaji tsakaninsu da kuma dalilin da yasa Ururu yake taimakon wani mahaluƙi wanda ba Ururu ba Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 34: Karan Battar Armad da Niyashi Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos . Note : wannan chapter tayi Kadan sosai, nayi niyyar kada nasa. Na bari saina Karasa ta. Amma bisa ganin cewa tadan bada ma'ana a hakan, da kuma cewa karashen chapter zai iya daukan Dan lokaci. ____ Acikin wannan filin gasa kuwa, tuni aka kammala duk wasu shirye-shirye da ake buƙata domin fafatawa tsakanin Armad da Niyashi, a wani salo na tantance tsakanin aya da tsakuwa. A kuma ga wanne acikin su zai isa zagaye na kusa dana ƙarshe. Dukkanin ƴan kallo, tuni suka fara murna da nishaɗin ganin mai zai faru, da kuma wa zaiyi nasara. Kusan kowa, sama da mutun dubu ɗari zaka iya cewa idonsu akansu yake, a dai-dai wannan lokaci da alƙalin wasa ya bada umarnin a fara. Armad na ɓarin arewa, rataye da takobinsa, Shi kuma Niyashi na tsaye a ɓarin kudu, mashinsa na maƙale acikin wani abu mai kama da aljihu da aka ɗinka masa na musamman domin ajiye mashin. Gashi dai an busa ƙaho, kuma an basu dama su fara fafatawa, amma har zuwa tsahon daƙiƙa talatin babu wanda ya motsa acikinsu, kuma babu wanda yace uffan! Can daga bisani Niyashi yai ajiyar zuciya a wani yanayi mai kama da tausayawa Armad, ya ce, ''naga kaima kana daga cikin ƙalilan da a zagaye na farko baka kashe kowa ba, saboda haka zan baka dama ɗaya ka fita daga cikin filin nan. Domin kuwa hakan ne kaɗai zaisa ka tsira da ranka. Na baka daƙiƙa biyar. Bayan ya gama magana sai kawai yai shiru yana kallon Armad. Idanunsa cike da mamakin ko mai yasa Armad bazai yi amfani da wannan dama ba, ya fice daga cikin wajen. Kasancewar a dukkanin tunaninsa shi ne, Armad bazai taɓa iya jure koda ɗaya tak daga cikin azabar hare-haren jan mashin saba. Amma ganin Armad yai masa shiru, kuma bashi da niyyar fita daga filin, yasa ransa ya ɓaci. Nan take ya ce, "bana son masu girman kai, saboda haka kada ka zargi kowa sai kanka akan abinda zai biyo bayan girman kanka." Yana ambata haka ya tafa hannayensa guda biyu inda ya kira sunan ɗalasimin da yake so yai amfani dashi, ''Sayanósis!!" Koda wannan ɗalasimi ya fita daga bakin Niyashi sai ya dunƙule hannunsa na dama ya fara dukan iskar dake gabansa. A duka na uku ne wata iska mai zafin gaske tamkar wuta, ta kaɗa a dukkanin ilahirin wannan fili. Wannan iska tayi kan Armad ganga-ganga tamkar zata haɗiye shi. Ya ɗaga hannunsa ya ɗan kare fuskarsa, amma ina, wannan iska ta fara ƙoƙarin kaishi ƙas. Wani mummunan jiri ya fara ɗibansa yana neman kaishi ƙas. Yai taga-taga ya nufi ƙasa, amma a lokacin ne ya dage ya dasa takobinsa a ƙasa tayadda gwiwowinsa basu je ƙas ba. Can daga nesa ya ci gaba da jin Niyashi yana bayani cikin girman kai da yadda da kai, "kamar yadda kaji, wannan ɗalasimi sunansa Sayanósis, kuma na ƙabila ta ne kaɗai a duk faɗin duniya. "Muna amfani da faɗan hannu da akewa laƙabi da 'fiƙar zaki' wajen canja iskar da mutun ke shaƙa! "Mu tsame kason da jiki ke buƙata, tayadda inma ka shaƙi iskar baza tayi amfani a jikinka ba. "Ta haka idan babu iskar da jikinka ke buƙata acikin jininka, fatar jikinka zata fara canjawa izuwa koriya ko kuma baƙa, kafin daga bisani ka fara jin jiri, kafin ka suma." Yana faɗar haka ya juya da niyyar tafiya, yana cewa, "ban san iyakacin lokacinda zaka iya jurewa ba kafin ka faɗi. Amma an riga an kammala wannan faɗan, sai dai ka tara a gaba!!!" Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos Tsakanin kowanne mutun da aljaninsa akwai wata ƴar rata wadda bata wuce taƙi uku ba. Bayan an haifi kowanne mutun kafin ya girman baya iya ganin aljaninsa sai dai kawai wannan ɗan taƙin dake tsakani. Acikin wannan ɗan taƙin ake ganin fasahar da aljaninka ke da ita. Yawanci ana fara gani daga shekara biyar zuwa sama. Sannan kuma bayan mutun ya girma ya mallaki hankalin kansa, sai kuma ayi ƙoƙarin haɗa shi da wannan aljani nasa a wani salo mai kama da bautarda wannan aljani. Tayadda wannan mutun zai iya sarrafa sirrin wannan aljanin. Wato dai idan aljanin mai sarrafa wuta ne, shima zai zamo yana iya sarrafa wutar. Armad tun yana yaro ɗan shekara sha uku, ya fara iya ganin wannan ɗan taƙi dake tsakanin ruhinsa da aljaninsa. Kuma yakanga wajen acike da walƙiya da tsawa da aradu, tamkar ana maka tsawa daga sama. Yana ɗan shekara tara, kakansa da babarsa da Shugaban makarantar da yake koyon harkar Izza aciki, suka haɗa ƙarfi da ƙarfe domin haɗa shi da wannan aljani nasa. Akai sa'a aljanin ya amince, kuma Armad ya mallake shi. Tun daga wannan rana Armad ya fara sarrafa tsawa da walƙiya tamkar shima walƙiyar ce. Idan ka hangi Armad walƙiya tana rawa a jikinsa da hannunsa kai kace ɗan aiken mutuwa ne. Lallai mallakar ƙarfin aljanu da sarrafa fasaharsu abu ne wanda yake ƙara daraja da ƙarfi na ma'aboci Izza. Kuma abu ne wanda yake sawa sauran mutane su tsorace shi. Abinda kawai Armad yake buƙata shi ne yayi duba izuwa wannan ɗan taƙi dake tsakaninsa da aljaninsa, ya kuma ɗebo walƙiyar dake wajen wadda aljanin nasa ya tara masa. Sannan ya aiwatar da fasaharsa. Armad yakan yi amfani da walƙiyar sa wajen ƙarawa kansa gudu kamar yadda aka gani a harinsa mai suna 'WASU-WASI', ko kuma yayi amfani da ita kanta walƙiyar domin kaiwa abokin gabarsa harin Aradu. ____ Armad najin duk abinda Niyashi yake faɗa, kuma hasalima duk waɗannan bayanai ALLAH ya taimakeshi ba sababbi bane a wajensa! Ba dan komai ba, sai dan cewa daga cikin littattafan daya koya yana yaro akwai mai suna "jiki da Izza" na dafta Hauwas al-kamaini. Wanda babu abinda babu acikin abubuwan da ya faɗa, kai harma da ƙari. Sai dai kuma Armad ba komai yake iya tunowa ba. Amma dai cikin sa'a ya iya tuno abinda zai iya cetarsa daga cikin wannan hali da yake. Armad ya dage yai ƙaraji gami da buɗe idanunsa, inda yai taga ya dawo ya tsaya cak da ƙafarsa gami da kafa ido yana kallon Niyashi, wanda ya juyo cikin sauri, fuska cike da mamaki. "Eehhhh...." shi ne kawai abinda ya fito daga bakin Niyashi, sannan ya ƙurawa Armad ido yana kallonsa ciki da bai, kamar wanda ke ƙoƙarin karanta wani abu acikin jikin Armad. Can bayan wasu ƴan daƙiƙu yayi wani murmushi mai cike da mugunta, gami da cewa, "lallai yaro ba laifi! "Watohar zaka iya amfani da Izzar dake jikinka, kana rage yawan iskar da jikinka ke amfani da ita, tayadda duk da baka shaƙar dai-dai adadin iskar da jikin naka ke buƙata, zaka iya jurewa tsahon wani lokaci." Ya girgiza kai gami da cewa, "ban taɓa tunanin kamar kai zai samu irin wannan ilmi ba, wanda ko a ƙabila ta abu ne daba kowa ya sani ba. "Amma duk da haka ina sane cewa wannan hanyace kawai da zata ƙara maka lokaci, amma a hankali cikin awanni masu zuwa baza ka iya jurewa ba." Ya ƙara girgiza kai yana yatsine fuska. "Sai dai kash, bani da wannan lokaci. Saboda hakan bazan iya jiranka ba." Yana faɗar haka ya ja baya gami da canja tsayuwa. Lamarinda yasa shima Armad wanda ya riga ya dawo daidai, ya canja tsayuwarsa. Daga can gefe kuma, wannan alƙalin wasa yana kan wajen gabatarwarsa babu abinda yake sai zuzuta abinda ke faruwa tsakanin Armad da Niyashi. Amma yana ganin dukkaninsu sun canja tsayuwa ya saki baki gami da cewa, "ga dukkan alamu kowa acikinsu ya maida hankali, bari mu zuba ido, shin yarima Niyashi daga Infiriya ne zai samu nasara, ko kuma wannan saurayi da ba'a san ko wanene ba, mai suna Armad Djinn daga Maikironomada." Kafin ma ya ƙarasa rufe baki Niyashi ya nufi Armad da sassarfa. Idan ka lura da hannunsa na dama zaka ga cewa wani baƙin haske ne ya bayyana kuma ya keta zagaye hannun. Yana isa ga Armad wanda har yanzu bai motsa daga inda yake ba, ya ƙara sauri inda cikin ƙiftawar ido ya kaiwa Armad Sara da hannunsa mai zagaye da wannan baƙin haske ta gefen Armad na hagun. Yana mai kiran sunan wani ɗalasimi, "Kulo-han-Difómiti!" Sai dai amma a dai-dai wannan lokacin ne Armad ya ɗaga hannunsa sama, inda wani haske ya fara bayyana yana kewaye hannun. Nan take wannan hasken ya juye izuwa walƙiya mai kama da kama da Aradu. Wannan walƙiya ta rikiɗe izuwa dauƙule-dunƙule har guda uku. Dukkanin dunƙule ukun juyawa kawai suke akan hannun saman hannun Armad. Su na ƙaraji suna ƙuwa irin wadda kake ji yayinda ake ruwan sama. Kai kace zasu ci babu. Armad ya cillo ɗaya daga cikin wannan dunƙulallun walƙiya uku wadda ta taho tana gunji, ta kuma daki baƙin hasken dake zagaye hannun Niyashi. Wata ƙara mai kashe kunne ta tashi. Dukkanin ƴan kallon dake wajen saida suka rufe kunnensu. Kai harda ma idanunsu, domin kuwa hasken daya tashi saida ya kashe wa kowa ido. Ƙarfin daya tashi daga wannan walƙiya yai cilli da Niyashi gefe. Tamkar an cicciɓeshi sama an watsar. Toda yake shima ba ƙaramin ma'aboci Izza bane, tun kafin ya je ƙasa yasa jan mashinsa ya tare. Inda ya cake shi akan filin wasan, lamarinda ya bashi damar miƙewa ba tare da yaje ƙasa ba. Yai wata katantawa a wani salo na nuna kwarewa, sannan ya kuma ƙara fuskantar Armad yana mai nuna shi da mashinsa. Kai da kaga Niyashi zaka san cewa lallai duk wani wasa ya kau daga idonsa. Kuma lallai yanzu ne za'a fara fafatawar da gaske.A gefe guda kuwa shima Armad tasa takobin ya zare a hannunsa na hagu. Sannan a hannunsa na dama kuma yana riƙe da balabalan walƙiya guda. Waɗanda suke ta kewaya hannun nasa a wani salo mai ban tsoro. MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 36: karan battar Armad da niyashi part 3 Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos . . "Ehmm..." Armad yai ajiyar numfashi gami da haɗe rai, sannan yaci gaba da cewa, "bani da lokacin dazan tsaya ina wasa dakai anan. Watanni kaɗan ne suka rage min nayi abinda duk duniya ta kasa, saboda haka ina baka shawara daka haƙura, ka fitar da kanka daga wannan gasa." Tun kafin Armad ya rufe bakinsa wani abu yazo wuyan Niyashi ya tsaya saboda tsananin baƙin ciki dake dukan ransa. Lallai babu wanda ya taɓa gaya masa baƙaƙen maganganu irin waɗannan. A matsayinsa na ɗan sarki, jikan sarki. Sannan kuma babban abin takaicin ma shi ne, wanda ke gaya masa wannan baƙaƙen maganganu na raini Izzarsa bata fi hamsin ba. Bayan shi Niyashi yana da kusan ɗari. "Da sannu zaka gane kuskurenka!" Wannan shi ne kawai abinda ya fito daga bakin yarima Niyashi yayinda idanuwansa suka kaɗa sukai ja. Baƙin ciki ya cika ruhinsa, sannan kuma yaji babu abinda zaisa ya ƙara yin dariya a ban ƙasa idan bai turmuza hancin Armad a ƙas ba. Nan take yai ƙaraji da ƙuwa, tare da tafa hannayensa a wani salo na kiran ƙarfin dake cikin Izzarsa. Nan da nan wata ankwa mai launin ja, wadda akayi ta da zallar azurfa irin ta mutanen farko ta bayyana a saman kansa tana lilo akan iska. Wannan doguwar ankwa ta lanƙwashe izuwa ƙawanya ta kuma kewaye kan Niyashi. Idan da zaka matsa kusa ka kuma

Chapter 16 of 33