Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙirga adadin waɗannan jar azurfar data haɗa wannan ankwa, to da zaka ga cewa guda casa'in da tara ne dai-dai. Kowacce acikin wannan azurfa tana ɗauke da ƙarfin shekara ɗaya na Izza. Wato dai a taƙaice dukkan ƙarfin Niyashi na Izza yana tattare a jikin wannan azurfa. Yarima Niyashi ya ƙara tafa hannayensa, lamarinda ya janyo wannan ankwa ta jar azurfa ta rikiɗe izuwa mashi kwaya ɗai-ɗai har casa'in da tara. Kowanne mashi idan ka duba zaka ga irin na hannun Niyashi ne. Ba tare da ƙara ɓata lokaci ba, Niyashi ya tafa hannayensa a karo na uku, tare da kiran sunan ɗalasimi, "Láyukúr-mazayà!" Ya na rufe bakinsa goma daga cikin wannan masu suka fara ci wuta, tare da afkawa kan Armad suna masu burin halaka shi. Lallai waɗannan masu guda goma masu ɗauke da ƙarfin Izzar shekaru goma zasu iya bada komai domin su zubar da jinin Armad. Duk inda suka ratsa sai kaji ƙarar iska da ƙuwa na tashi, tamkar ita kanta iskar tsoronsu take. Armad na ganin haka ya ƙara yin duba izuwa wannan ɗan taƙi dake tsakaninsa da aljaninsa, nan da nan ya zuƙo walƙiya guda goma. Wannan walƙiya na bayyana ta kewaye jikinsa tana haske, kafin daga bisani ta rikiɗe izuwa ƙawanyar walƙiya ɗai-ɗai har guda goma. Armad ya kira ɗalasiminsa, "Hushúsul-baijuru." Yana rufe baki waɗannan ƙawanyu na walƙiya sukai kan wannan masu guda goma. Suna haɗuwa wata ƙara mai rikitarwa ta tashi sama, haɗe da wani haske mai kashe ido. Kan kace meye wannan filin fafatawar ya fara girgiza yana neman tarwatsewa. Alƙalin wasa kuwa saida ya durƙusa domin kare idanunsa daga tartsatsin wutar dake tashi. Tamkar ƴan kallo dake nesa saida firgici ya cika zuciyarsu suka fara rirriƙe kujerunsu domin tsoron kada girgiɗin da ƙasar filin wasan keyi tayi cilli dasu. Bayan kimanin daƙiƙu goma wannan sauti mai kama da girgizar ƙasa ya lafa. Amma maimakon aga Armad da Niyashi a tsaye suna hutawa, dukkaninsu sai suka ƙara ci gaba aikawa juna hare-hare. Armad na ƙoƙarin tarwatsa Niyashi da ƙawanyar walƙiyarsa, shi kuma Niyashi yana ƙoƙarin soke Armad da Jan mashinsa. Babu abinda kake ji sai ƙara mai kama da yaƙin duniya. Kan kace meye wannan tuni anyi musayar sama da hari hamsin a tsakaninsu. Sai dai kuma fa a wannan lokaci ne gizo ya fara saƙar. Domin kuwa kamar yadda ƙa'idar ƙasa-bakwai ta kasance tun iyaye da kakanni, iyakacin izzarka iyakacin shagalinka; idan kana da Izza hamsin to ƙawanyar walƙiya hamsin kaɗai zaka iya zuƙa daga aljaninka. Hakana idan kana da ɗari kawai ɗari zaka iya amfani dasu. Har sai ka jira kimanin awanni tukunna, bayan ƙarfin ruhinka ya dawo, wanda kuma baza ka samu hakan ba idan ana tsaka da faɗa. Wato dai a taƙaice a wannna lokaci ne adadin walƙiyar da Armad zai iya amfani da ita tazo ƙarshe. A yayinda shi kuwa Niyashi yana nan akan ganiyar ƙarfinsa. A wannan lokaci Armad ya miƙa hannunsa domin kwance ɗaurin dake gaban goshinsa, sai dai kuma a lokacin ne kwatsam alamarin daya faru da Miyurarsa ya faɗo masa. Shaf ya manta. Tunda farko Armad yayi lissafi da cewa faɗan fito-na-fito zai kai masa, tunda zai iya amfani da tambarin Miyurar ya ƙarawa kansa ƙarfi da yawan Izza. To abinka da abinda tunda aka haifeka yana tare dakai, lallai koda Armad ba yaro bane ɗan shekara sha shida ba, zai iya mantawa. Kuma dole sai a hankali zai saba da rashin Miyurar. Nan da nan Armad yayi tsalle baya cikin firgici da tunanin maiya kamata yayi, sannan kuma ta yaya ne zai iya cin galaba akan Niyashi wanda yana da kusan ragowar masu guda arba'in a ƙasa. A ɓangare guda kuwa, koda Niyashi ya gano halin da Armad ke ciki sai yayi wata dariyar mugunta. Tare da cewa, "dama na gaya maka, da sannu zaka gane kuskurenka!" Yana rufe baki ya aikawa da Armad dukkanin ragowar masun dake kewayawa a saman kansa. Kai daka gani kasan so yake ya tsire Armad duk a huta. Domin yana ji acikin ransa cewa lallai bazai samu kwanciyar hankali ba idan bai halaka Armad ba a wannan lokaci. Domin kuwa Armad ya gaya masa maganganun da babu wanda ya taɓa gaya masa. Dukkanin ƴan kallo da alƙalin wasa sun riga sun gama hango Armad a lahira. Domin dai dama sunan Armad baya daga cikin waɗannan sunaye guda shida da ake ta kallo kafin a fara gasar. Sunayen da ake tunanin zasu samu nasara. Shi kuwa Niyashi yana ciki. Sai dai kuma wasu daga cikin ƴan kallon sun soma ɗan sawa Armad kyakkyawan zaton zaiyi abin kirki. Musamman yadda suka ga yana wasa da walƙiya cikin kwanciyar hankali. Amma a wannan lokaci tuni suka cire rai kuma suka ɗebewa Armad haso daga dukkan tsira. Kai a taƙaice dai shi kansa Armad yana cikin yanayi na kokwanton ko zai rayu. Musamman sanda yaga ratar dake tsakanin ƙirjinsa da waɗannan masu sama da arba'in baifi taku ɗaya ba. ____ To ko tayaya kuke ganin Armad zai kuɓuta?? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 37: Motsin littafin Takobi Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos . A dai-dai wannan lokaci ne da Armad Wilbafos yake cikin halin ƙaƙa ni kayi, dogayen jajayen masu sama da arba'in masu cike da Izza suna gab da tsire shi. Sannan kuma gashi dukkan Walƙiyar da aljaninsa zai iya bashi ta ƙare, a wannan lokaci na tsanani da matsi, kwatsam sai yaji wani ɗan motsi acikin aljihunsa na ciki. Kafin yayi wani tunani akan wannan motsi da yaji kawai sai yaji wani mummunan raɗaɗi mai zafin gaske a dai-dai wajen da yaji wannan motsi. Kan kace meye wannan raɗaɗin ya juye izuwa raɗaɗin garwashi. Nan take Armad yaji wajen yana soyuwa. Da kyar ya iya tunano cewa a dai-dai wannan wajen da yake jin wannan raɗaɗi wannan littafin-takobin ya ajiye a wajan. Nan take ya fara ƙoƙarin yin cilli da littafin. Amma kafin yayi wani abu yaji wata irin Izza irin ta mutanen farko ta shiga jikinsa. Bai san lokacin da yayi wani ihu ba saboda zafin da yake damunsa. Kan kace meye wannan Armad yaga ɗan taƙin dake ɗauke da walƙiyarsa ya cika da walƙiya. Bai san daga ina wannan walƙiya take ba, abu dai guda ɗaya daya sani shi ne lallai wannan walƙiya ba irin tasa bace ta da. Domin akwai wani sirri na ƙarfin Izza aciki, wanda Armad bazai iya ganewa ba. Armad ya zuƙo wannan walƙiya daga ruhinsa inda ya fuskanci cewa walƙiyar bata da yawa sosai, kuma zata iya samar da Ƙawanyar walƙiya guda ɗaya ne kawai. Sai dai kuma a jikin wannan walƙiya akwai wasu layika jajaye guda uku suna kewayata. Kai daka gani kasan cewa wannan walƙiya ta musamman ce. Armad bashi da lokacin tsayawa yayi tunani sosai akan abubuwan dake faruwa saboda haka kawai kai tsaye ya aikawa Niyashi da wannan ƙawanyar walƙiya. Dukkanin abubuwan dake faruwa sun ɗau lokaci wajen bayani amma a zahiri sun faru ne cikin abinda bai wuce daƙiƙa biyu ba. Wata ƙara ce mai kama da girgizar ƙasa ta tashi sama, sannan kuma wani haske ya lulluɓe ko'ina babu abinda ake gani face rugugin tsagewar filin wasan da Armad da Niyashi ke kai. Kan kace meye wannan komai ya tarwatse inda bayan da abubuwa suka lafa aka ga Armad ya bayyana daga cikin wannan rugugi yana mai riƙe da takobinsa a hannun hagu cikin ƙasaita. Bisa mamaki shi kuwa yarima Niyashi na kwance a sume. Ko madai mai ya faru tsakanin ƙawanyar walƙiyar Armad guda ɗaya da kuma masun Niyashi sama da arba'in babu wanda ya gani. Saboda haka kowa idanunsa akan Armad suke a kafe, suna fatan ko zai yi musu bayani akan abinda ke faruwa. Amma ina, abinda basu sani ba shi ne shi kansa Armad bai san maike faruwa ba. Domin kawai abinda ya gani shi ne dukkanin waɗannan masu guda arba'in da ɗoriya ɓacewa ɓat sukai a lokacin da suka haɗu da walƙiyar nan guda ɗaya daya tura, tamkar ma basu taɓa faruwa ba. Sannna kuma walƙiyar taje ta daki Niyashi inda ta sumar dashi nan take. Abu ɗaya da Armad ya sani shi ne wannan Littafin-Takobi dake ɓoye acikin rigarsa lallai yana da muhimmancin gaske. Nan take aka buga ƙugen nasara, kuma aka bawa Armad nasara. Inda shi kuma Niyashi likitoci suka tafi dashi. Sai dai kuma wani abu ya faru a dai-dai lokacin da Armad yaji motsin wannan littafin-takobi acikin rigarsa. Wannan abu kuwa babu wanda ya sani illa mutumin da abin ya faru dashi wato Uznu Ururu. Acikin rigar wannan ma'aboci Ururu wani ɗan ƙaramin allon tsafi yayi girgiza tare da fitarda wani baƙin haske kalar Idanun ubangidansa wato Uznu Ururu. Nan take wani ɗan murmushi na farin ciki ya bayyana akan fuskar Uznu Ururu. Domin yasan abinda yake nema ya samu. Wannan allon tsafi ba wani abu bane illa abinda yake amfani dashi wajen neman littafin-takobi. Matsafansa a ƙasa ta farko sun labarta masa cewa indai littafin takobin ya bayyana to wannan allo zai sanar dashi. Yanzu kuma gashi abinda ya daɗe yana nema sama da shekaru dubu ɗaya da ɗari biyar ya samu. Nan da nan ya juyo da hankalinsa gaba ɗaya kan Armad tunda daman abinda ya kawo shi wannan waje kenan. ____ A can bayan fili kuwa Armad ne ya isa wajensu Nusi, "Ahhhhh..." Nusi tayi ajiyar zuciya tare da riƙe Armad tana cewa, "hankali na har ya tashi, ga dukkan alamu bama saina damu dakai ba! Kai wataƙila dama ban rakoka ba ko!" Nusi ce a gefe da sauran mutanen da suka rako su daga garin Khan, suke ta yabawa Armad saboda jarumtar daya nuna a karawarsa da yarima Niyashi. "Hmmmm....kayi ƙarfi da yawa acikin ɗan ƙanƙanin lokaci, ina alfahari da kai!" Inji Nusi, acikin zuciyarta babu abinda take tunani sai wannan walƙiya ta ƙarshe da taga Armad yayi amfani da ita. Lallai tasan akwai wani abu a ƙasa. Amma dai kawai tayi shiru a lokacin domin bata so ta faɗi wani abu dazai ɗaukewa Armad hankali daga faɗan gaba daya rage masa. "Yaya Armad, da ALLAH zan zamo ɗalibinka, ko na samu na ɗan koyi abu ɗaya ko biyu!" wani daga cikin ƴan rakiyar dake tare dasu Armad ya fara kamun ƙafa. "Nima haka....Nima haka...." Toh haka dai bayan kammala faɗa tsakanin Armad da Niyashi, ire-iren waɗannan maganganu suke ta kewayawa a tsakanin dukkanin mutanen dake wajen. Ana cikin wannan hayaniya kuwa tuni alƙalin wasa Gali, ya fito da wasu ganyayyaki na musamman guda huɗu. Dukkaninsu jajaye ne, inda yana fitowa dasu kaf ilahirin wajen yai tsit. Kasancewar kowa yasan waɗannan ganyayyaki bana komai bane illa na fitarda tsakani na wasannin gaba, wato dai dawa-dawa za'a kara. Kowa abinda ke ransa shi ne, wanne faɗa ne zaifi ƙayatarwa. Shin tsakanin Armad da Ikenga ne ko kuma tsakanin Bizaya da Han-Amuru wanda mutane da dama a wajen suke bayansa. Domin wani abin mamaki shi ne, idan ka cire Bizaya, zaka ga babu kusan wanda waɗannan ƴan kallo ke goyar baya kamarsa, duk da kuwa masu goyon bayan Armad sun ɗan ƙaru bayanda yaci nasara akan Niyashi. Alƙali Gali ya ɗauko alƙalami, wanda a jikinsa aka rubuta Deniziyya Kuronikil, ya miƙa hannu yabi kan dukkanin waɗannan ganyayyaki huɗu ya rubuta sunan ɗaya daga cikin mutun huɗun nan da suka fito. Sannan yana gamawa ya haɗesu waje ɗaya, kuma a gaban idon filin nan wanda tuni yayi tsit an zuba ido, alƙali Gali ya jefa waɗannan ganyayyaki huɗu sama. Nan take suka luluƙa sama kimanin taku huɗu, sannan suka fara sakkowa. Idon kowa akai, kawai so ake aga waɗanne guda biyu ne zasu fara dira ƙasa, wanda hakan shi zai nuna waɗanne ne zasu haɗu da juna. Wato dai a taƙaice, ganye biyun da suka riga zuwa ƙas, sunan dake kai, sune zasu kara da juna, kuma su zasu fara. Sannan kuma ragowar biyu da suka rage a sama su biyo baya. Wannan ita ce hanyarda suke bi a wannan gasa wajen zaɓar waɗanda zasu kara da juna. Kuma hanyace da kowa yake ganin tayi, saboda waɗannan ganyayyaki an tsinko sune daga bishiya ta musamman wanda kowa ya santa. Bishiya ce wadda babban abinda kowa ya sani akanta shi ne, tun daga sanda ta fara ganye har ƙarshen rayuwarta, a kodayaushe ganyayyakin ta iri ɗaya ne sak. Sunan wannan bishiya Safá, su kuma ganyayyakinta ana kiransu da Safáha. Har zuwa sanda waɗannan ganyayyaki huɗu suka zo kusan tsakiya a tare suke tafiya, amma a wannan lokaci ne iska ta kaɗa, inda biyu daga cikin ganyen suka wuce sauran. Kuma kan kace meye wannan tuni sun kusa isa ƙasa. Suna dira suna ɗaya ya bayyana kuma sunan Han-Amuru ne a jiki. Ɗayan kuma a juye yake. To dama a dai-dai lokacin da Gali zai jefa waɗannan ganyayyaki waɗansu mutane sanye da fararen kaya su biyu, sun matso gefe sun tsaya. Dukkansu fuskokinsu a rufe suke, kuma su na tsaye cak kamar baza su taɓa motsawa ba. Amma a dai-dai lokacin da waɗannan ganyayyaki biyu suka dira a ƙas, waɗannan mutun biyu suka ɓace daga inda suke tsaye suka kuma bayyana a a dai-dai kan waɗannan ganyayyaki inda suka ɗauke su cikin sauri, tun kafin ragowar biyun su sauka. A gaban idon kowa kuma suka buɗe ɗayan, inda kowa yayi arba da sunan Armad Djinn akai. Nan take wajen ya ruɗe da shewa, kowa yana tattauna yadda rabon ya kasance, da dama dai yai musu, amma kaɗan daga ciki ba haka suka so ba. Armad na tsaye a kusa da Nusi tana ja masa kunne akan ya kula sosai da HanAmuru, kuma kada ganin cewa daga kan doron ƙasa ɗaya suke yasa yayi wasa, kawai sai yaji alamun ana kallonsa ta baya, inda na take ya juya ɓangaren. Yana juyawa yai arba da idanun Han'Amuru, wanda kallonsu kaɗai zai iya sawa kaji tamkar an jefa ka acikin wuta, saboda wutar da take ci aciki. In ba'a manta ba aljanin Han Amuru na wuta ne. Kana gani kasan kallo ne mai cike da so da marmarin yaƙi, haɗe kuma da turawa Armad saƙon cewa a shirye yake. Shima Armad baiyi ƙasa a gwiwa ba, wajen mayar masa da irin wannan kallon dake gaya masa shima a shiryen yake. ____ To fa, Wuta da Walƙiya sun haɗu, wa kuke tunanin zaici nasara? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 38: Badalar Wuta Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos . "Zo kaji!" Nusi ta ja Armad da sauri suka bar cikin mutane izuwa wani ɗan shinge dake wajen filin-wasan. "Wannan yaron mai suna Han Amuru na sanshi a shekarun baya da suka wuce a lokacin da mukai ƙoƙarin shiga garin ƙarƙashin ƙasa na Shadniza dana labarta maka a baya. Lallai yana da hatsarin-gaske sama dana gobarar daji, dole ka kiyaye." "Ehmmm......" Armad ya kyaɗa kai tare da ajiyar zuciya. "Kada ki damu kanki sosai, ni nasan zanyi nasara domin sama da ƙasa zata haɗu bazan mutu ba saina tabbatar mahaifiyata ta samu lafiya. Akwai fasahar Wasu-wasi da nake da ita wanda har yanzu banyi amfani da ita ba. Akwai ɗalasimin Kaban'shisu shima." Armad yana magana cikin taushi musamman ganin yanayin tausayi da so acikin idanun Nusi. "Da gaske fa...... Ki dena damuwa da yawa." Armad ya matsa kusa da Nusi tare da ƙara jaddada mata abinda ke zuciyarsa bayanda yaga alamun rashin amincewa a idonta. Nusi ta girgiza kai, "Ban san mai yasa ba amma jikina yana bani kamar akwai wani hatsari dake tafe. Lallai hankali na bazai kwanta ba sai naga mun bar wajen nan lafiya." Nusi ta matsa kusa da Armad domin kare shi daga wasu mutane dake wucewa wanda suka fara nuna Armad suna cewa, "shi ne Armad Djinn, shi ne yai nasara ɗazu akan yarima Niyashi." Nusi ta ƙara jan Armad suka bi bayan wasu shaguna dake kewaye da filin domin ɓuya daga idanun jama'a. "Ungo wannan Layar." Nusi ta fito da wata Farar-Laya ɗaure da wani zare mai launin roɗi-roɗi daga cikin rigarta ta kuma miƙawa Armad. "Nasan kasan amfanin ta." Idanun Armad suka cika da mamaki, shin wai abinda yake gani dai-dai ne ko kuma mafarki yake. Domin kuwa idan dai Layar da yake tunani ce to lallai ya tsinci dami a kala. "N......nusi... Ya akai kika samu Farar-Laya....." "Sh...sh.... ka daina faɗa da ƙarfi mana kosai kasa wasu sunji." Nusi tayi sauri ta rufe masa baki. Sannan taci gaba da bayani bayan ya karɓi Layar. Ga dukkan alamu wannan Laya aba ce ta musamman. To ko meye amfaninta. "Zaka iya amfani da wannan Farar-Laya amma ka sani ba mai ƙarfi bace, saboda haka sau ɗaya kacal za'a iya amfani da ita. Ungo wannan safar kasa a hannunka, domin kaima baza ka iya taɓa ta ba." Ta ƙara miƙa masa wata ƴar safa ruwan ƙasa. Har a wannan lokaci daya miƙa hannu ya karɓi safar idanunsa cike suke da mamaki. Domin yana da cikakkiyar masaniyar cewa ba ƙaramin abu mai wahala bane ga mutun ya mallaki wannan Farar-laya ba koda kuwa mara ƙarfi. Nan danan ya ƙara sanin cewa lallai akwai manyan ma'abota da suka tsayawa Nusi. Musamman daya tuno labarin data gaya masa na cewa suna da ƙungiya mai ƙarfin gaske da suke ƙoƙarin buɗe garin ƙarƙashin ƙasa na Shadeniza. A dai-dai lokacin da yazo nan a tunaninsa ne suka jiyo ƙarar ƙararrawa alamun lokaci yayi daza aci gaba da fafatawa. Nan da nan suka rankayo izuwa cikin filin. Lokaci kaɗan bayan kaɗawar ƙararrawar aka buga ƙugen yaƙi, inda Armad da Han'amuru suka fito filin daga, babu abinda kake ji sai shewar ƴan kallo wasu suna goyon bayan Armad wasu Hanamuru, amma kana gani zaka san na Hanamuru sunfi yawa. Gabda zai hau kan filin dagar Armad ya ƙara shafa aljihunsa domin jin halin da Littafin-takobi yake ciki. Shi kansa baisan dalilin da yasa bai gayawa Nusi labarin wannan littafi ba duk da kuwa yasan ya kamata ya gaya mata. Sai dai abu guda ɗaya da yake ta sukar Armad a rai shi ne, baisan dalilin da yasa Littafin-takobin ya taimake shi a yayin faɗansa da Yarima Niyashi ba. Saboda haka bashi da tabbas zai ƙara samun irin wannan taimako daga wannan littafi, kuma lallai bai kamata ya ta'allaƙa dashi ba. Saboda haka ma baya son ya gaya mata hankalinta ya ƙara tashi. Kuma tunda ma'aboci aljanin wuta Han Amuru ya fishi girman Izza lallai yana da buƙata ya fito da wata hanya da zai samu nasara cikin gaggawa. Saboda haka ya fara tunanin mafita, 'Ina da Saran takobi mai suna Wasu-wasi, sannan kuma ina da adadin ƙawanyar walƙiya guda hamsin da ɗaya. Mafi muhimmanci kuma ga Farar-laya dana samu daga Nusi.' Armad ya ci gaba da tunane-tunanen hanyar dazai samu nasara ba tare da neman taimako daga littafin ba. Saboda shima yana ji a jikinsa cewa akwai wani sharri maɗaukaki a tattare da wannan Littafi. Suna dira acikin filin, Han Amuru ya ƙara ja da baya, ya kuma ƙara nisan dake tsakaninsa da Armad inda cikin sauri ya tafa hannayensa biyu gami da cewa, "Badalar wuta!!" Yana faɗar haka, wata wuta ta bayyana a gefensa. Wadda tana bayyana ta fara ƙara yawa tana zagaye shi, kan kace meye wannan tuni wannan Badalar wuta ta rufe Han Amuru har zuwa kafaɗaunsa, inda ta tsaya. Amma kuma tana tsayawa sai wata irinta ta fara kewaye ta inda ita ma tayi ta ringa ƙaruwa har takai tsayin kamar wancan. Tana gamawa wata ta fara... haka-haka har saida aka samu ƙawanyar wuta zagaye shida a kewaye da Han Amuru. Wannan badaloli su na gunji suna fitar da baƙin hayaƙi da tiriri suna kare Han Amuru tamkar sarki acikin bangon Badalar garinsa. Lallai ko kakai ƙanƙantar kiyashi baka isa ka cimma Han Amuru ba a yadda yake. Han Amuru ya miƙa hannunsa gaba, inda ya nuna Armad, wanda ke tsaye har a lokacin bai motsa ba. Yana nuna Armad, cikin ƙiftawar ido da bismilla, biyar daga cikin waɗannan ƙawanyar badala ta wuta, suka ɓace daga inda suke, suna ƙara bayyana sui gasu zagaye da Armad. Haka na faruwa Hanamuru ya kyalla ido ya hango Armad a tsakiyar wutannan, kowa na gani yai wata wawar dariya gami da cewa, "Armad....Djinn ko? Naga faɗanka da Niyashi kuma ina mai tabbatar maka da cewa lallai sai nayi nasara akanka. Ni zan ƙone ka ƙurmus acikin Badala ta ta wuta! Kai sani cewa ni idan ina filin daga babu ruwana da yaro ko babba, duk hukunci ɗaya nake musu. Saboda haka kada ma kayi tunanin cewa dan kana da Izza ƴar ƙarama wadda bata fi rabin tawa ba zan ɗaga maka ƙafa." Gunji da tiriri da wannan wutar ke bayarwa tuni ya fara ƙoƙarin haɗiye Armad. Armad ya ɗaga ido yaga shekarun Izza ɗai-ɗai har goma sha bakwai ajikin kowacce ɗaya daga cikin wannan badalar wuta guda biyar dake neman haɗiye shi. Lallai yasan indai ya bari ɗaya daga cikinsu ta taɓa shi to fa lallai ƙarshensa yazo. Nan take ya zira wannan safa da Nusi ta bashi sannan ya tuno da ɗaya daga cikin ɗalasiman daya koya a wajen kakansa wato 'Kaban'shisu'. Ba shiri Armad yayi amfani da ƙarfin Izza na kimanin shekara goma ya tayarda wannan ɗalasimi. Lamarinda ya bashi damar kuɓucewa wannan badalar wuta abar ruruwa. Inda ta daki wajen da Armad ya bari kuma nan take ta maida shi toka. Armad ya bayyana acan gefe yana mai duba izuwa wannan waje daya bari tare da tuno cewa da bai bar wajen ba, toda tuni ya zama toka shima. Sai dai yana cikin tunani ne wata badalar ta ƙara yiwowa kansa da niyar haɗiye. Amma ina, Armad ya ƙara kuɓucewa. Lamarinda ya bawa Han Amuru haushi yai wani ƙaraji tare da saka badalolin wutar guda shida su haɗe izuwa babbar badala guda ɗaya. Wadda nan take ita kuma ta kewaye dukkan filin dagar inda tasa Armad da shi Niyashi a tsakiya. Sannan kuma ta fara matsewa tana haɗewa izuwa tsakiya. Wato dai a taƙaice Armad bashi da wajen guduwa indai ba tashi sama zaiyi ba. Wataƙila da yana da Miyurarsa, da zai iya tashi saman kamar yadda yayi a faɗansa damai tsaron hanya Han Diyuza, amma yanzu babu. Gashi a tsakiyar wutar badala tare da ma'aboci aljanin wuta wanda babu alamun imani a tattare dashi ko kaɗan. ____ To ko taya Armad zai kuɓuta daga wannan badalar wuta? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 39: Farar Laya Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos . Duk taƙi ɗaya da wannan wuta ta ƙara kusantar Armad sai yaji raɗaɗinta ya ƙaru. Tamkar ana soya naman jikinsa. Lallai bada ban jarumin gaske bane da tuni ya kwalla ƙara. Amma duk da wannan hali daya ke ciki wani abu ɗaya ya ɗauke masa hankali. Wannan abu kuwa shi ne kasancewar wancan badala ta wuta data nemi halaka shi, ya sha dakyar ta hanyar ɓacewa daga inda yake, ya kamata ace shekarun Izzar dake jikinta sun ragu daga sha bakwai zuwa ƙasa. Amma bisa mamaki tana nan dai-dai a yadda take; ɗauke da shekaru goma sha bakwai na Izza. Lallai Armad yasan akwai matsala idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka. Domin kuwa idan Izzar mutun bata raguwa idan yayi amfani da ita, to tayaya Armad zai iya cin galaba akansa. Hayaƙi da turiri ya fara neman sawa hankalin Armad ya gushe, amma Armad yasan cewa lallai indai ya bari ya suma a wajen to ƙarshensa yazo. Saboda haka ya cije ya daure ya tsaya da ƙafafunsa, ya kuma fuskanci inda Amuru yake tsaya yana kallonsa cikin isa da ƙasaita. A dai-dai wannan lokaci ne Armad ya yanke shawarar mai zaiyi. Nan take ya zira hannunsa mai safar cikin aljihunsa. Inda ya janyo wannan Farar-laya da Nusi ta bashi. Sannan kuma a lokaci guda yayi duba izuwa ruhinsa, inda ya janyo ƙawanyar walƙiya na ƙarfin Izzarsa daya rage na shekaru arba'in. Daga nesa idan ka hango Armad abin zai baka mamaki; zaka ga yaro saurayi wankan-tarwaɗa sanye cikin fararen kaya. A kewaye dashi akwai ƙawanya ta walƙiya ɗai-ɗai ɗai-ɗai har guda arba'in da ɗoriya su na kewaya shi. Lallai da dama daga cikin ƴan kallon baza su taɓa mantawa da wannan yaro mai suna Armad. Cikin sauri ya tunkari Han Amuru yana sassarfa. Sai dai kuma wannan badala dake ta kusanto su tamkar ta gane mai Armad yake niyyar yi, saboda haka tayi kansa cikin tsananin sauri. Lamarinda yasa ta cimmasa cikin ƙiftawar ido da bismilla. Tana zuwa ta daki wannan ƙawanyar walƙiya data kewaye Armad. Inda wata ƙara mai ruɗarwa ta tashi. Nan take faɗa ya kaure tsakanin wannan badalar wuta da kuma ƙawanyar walƙiyar Armad. Wuta tana ƙoƙarin haɗiye walƙiya, walƙiya kuma tana ƙoƙarin ƙona wuta. Lallai wannan faɗa ne na musamman, wanda dukkanin ƴan kallo hankalin ya koma kai. Sai dai kuma abinda basu sani ba shi ne a bayan wannan walƙiya Armad ne keta aman jini yana tafiya da kyar, saboda duk sanda wannan wuta ta daki walƙiyarsa sai yaji rauni a jikinsa. Badan komai ba saboda banbancin Izzar dake tsakaninsu. Lallai akwai banbanci maɗaukaki tsakanin mai Izza ɗari da mai hamsin. Wanda idan banda ƙarfin ruhi da dagiya irin ta Armad da tuni yaje ƙas. Armad ya ci gaba da tafiya yana aman jini, burinsa kawai ya isa ga Amuru. Koda yaje dab dashi sai Amuru yayi masa wani kallo mai cike da mamaki tare da cewa, "kana ta sauri ka iso gareni, shin kana tunanin dan kazo nan zaka iya yin wani abu ne? Bari dai na nuna maka banbancin ƙarfin Izzar dake tsakanin mu." Nan take Amuru ya dunƙule hannunsa, lamarinda yasa nan take dukkan wutar dake wajen ta cure izuwa tafkeken dunƙule guda ɗaya kewaye a hannunsa. Kafin Armad ya farga tuni Han Amuru ya kawo masa duka da wannan hannu nasa mai haɗe da wuta. Ko kokwanto babu Armad yasan indai ya bari wannan hannu ya taɓa shi, tofa lalle ko tokarsa baza a gani ba. Saboda haka nan take ya haɗe dukkan sauran ragowar shekarun Izzarsa izuwa wata ƴar ƙawanya ta walƙiya. Wadda yasa ta kewaye wannan Farar-laya dake hannunsa, sannan ya cillawa Amuru ita. Saboda yadda layar take kewaye da walƙiya, Amuru baiga layar ba, saboda haka yai tsaki tare da cewa, "shin kana tunani ƴar wannan walƙiyar daka cillo zata iyai min wani abu ne? Ka farka in ma mafarki kake, domin kuwa......" Han Amuru ya haɗiye ragowar kalominsa tare da rufe bakinsa yayinda wannan Laya ta taɓa jikinsa. Sannan kuma kafin ya ankara zaren dake jikinta ya rataye a wuyansa. Cikin abinda bai wuce ƙiftawar ido ba dukkan wutar dake kewaye da Amuru ta ɗauke tamkar ba'a taɓa yinta ba. Wani zafi mai haɗe da kasala ya cika jikinsa, inda hatta ƙafarsa yaji baza ta iya ɗaukansa ba. Ya nufi ƙasa gadangadan tamkar wanda aka zarewa rai. A dai-dai wannan lokaci da kowa ke mamakin abinda ke faruwa aka jiyo muryar alƙalin wasa wato Ghalee, "F.....farar-laya! Lallai babu kokwanto acikin abinda ke faruwa. Wannan yaro mai suna Armad Djinn yayi amfani da Farar-laya ya ɗaure aljanin Han Amuru. Kowa yasan ƙarfin wannan Laya da akewa laƙabi da Farar-laya wajen ɗaure dukkan wani aljani da kuma hana ma'abota su amfani da

Chapter 17 of 33