Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi ne, gab da kafin hankalinsa ya dusashe, ya kasance yana ta kai-komo da abubuwan sirrin da yaji daga wannan murya wadda take magana akan Rukunai guda biyu na Ururu. Sirrin da Armad ya tabbatar indai ya fita to lallai sai ya rikita dukkan duniyar ƙasa bakwai, tayadda zaman lafiya ma zai iya zuwa ƙarshe!! Da farkawarsa abinda ya fara yin arba dashi shi ne fili fetal gabas da yamma, gudu da arewa ko ina ya duba baya iya gano ƙarshensa. Babban abun mamaki da wannan waje shi ne babu alamun wata halitta a wajen ko kaɗan; kama daga kan namun daji zuwa tsirrai zuwa tsuntsaye, ko’ina ka duba ba komai a wajen kawai sai fili fetal da tsandaurin ƙasa. Sai dai kuma Armad bai shiga al’ajabin ganinsa a wajen ba, saboda ba wannan karonsa na farko ba da yayi amfani da irin wannan fasaha, kuma ya samu kansa acikin wannan yanayi ba. Kuma daya tambayi kakansa dake koyarda shi, sai ya ce masa sakamakon rashin kwarewa ne. Amma wannan bai hana Armad yin amfani da wannan fasaha ba, lokaci zuwa lokaci idan ya tsinci kansa a mawuyacin hali. Kuma kamar koda yaushe yakan farka a wani waje tafiyar wuni ko kwana ɗaya daga wajen da yayi amfani da ita. Iya hangensa baya iya ganin koda shuka guda ɗaya a wannan waje. Babu komai sai kurum tsandauri iyakacin hange. Armad ya samu kansa a kwance bayan farkawarsa, sannan kuma daga bisani bayanda hankalinsa ya fara dawowa kansa sai ya lura cewa kayan jikinsa ma ba nasa bane. Yana ganin haka yasan tabbas duk da alamun wajen baya nuna wani ɗan adam zai iya rayuwa a wajen, lallai bashi kaɗai bane a wajen ba. Saboda haka abu na farko daya fara faɗo masa a rai shi ne takobinsa, wadda a iya tunaninsa ita kaɗaice abinda yake gani ya tuno da mahaifiyarsa. Cikin sauri ya juya ɓarin kafaɗarsa ta hagu inda ya saƙale takobin tasa, amma babu ita babu alamarta. Nan take ya miƙe tsaye ya kuma fara dubu-dube. Amma idanun nasa basu gane masa komai ba, banda filin turɓaya kurum dake gabansa iya hangensa. A wannan lokaci ya juya bayansa, inda bisa mamaki yai arba da wani abu, wanda gaba ɗaya acikin wajen nan shi kaɗai abinda ya gani tun bayan farkawarsa. Wannan abu ba komai bane illa wani ƙaton allo mai rubutu a gabansa. Ba komai bane a jiki illa suna ye masu yawan gaske, kowanne da lamba a jikinsa da kuma shekara. Sunayen sunyi wa Armad wahala, saboda bai saba jin irinsu ba a ƙasa ta uku, duk da cewa abune mara wahala ka samesu acikin littattafan daya karanta, to amma anan ɗin ma ba son su yake ba. Saboda haka kawai sunayen da suke da lamba ɗaya a jikinsu su ya iya karanta uku daga ciki. Inda ɗaya yaga ansa Bihanzin Djinn shekarar 1833, ɗaya kuma ansa Ikenga O. Bayajidda shekarar 1852 sai kuma ɗayan ansa Deniz Bizáya shima shekarar 1852. Zaka iya cewa ganin shekarar 1852 shi ne abu mafi girman mamaki da Armad ya fuskanta tun bayan barin sa gida. Badan komai ba kuwa saidan cewa yasan kamata yayi ace wannan shekara da suke ciki ta zama 1851, wato shekarar da aka gama wancan yaƙi da mahaifiyarsa ta samu wannan ciwo a ciki. Kuma daga fitowarsa daga gida zuwa wannan lokaci kaf iyakacin lissafinsa ƴan kwanani ne kawai. Amma yanzu gashi yana ganin 1852, wanda hakan ke nuna tuni yayi shekara ɗaya da barin gida. MEKE FARUWA? Ya tambayi kansa. Amma idan da a haka abin ya tsaya masa da da sauƙi, to amma a lokacin ne idanunsa suka kai kan wani sunan wanda a jikinsa akasa shekarar 1853!! Kafin kace meye wannan tuni tunane-tunane sun cika ziciyarsa, kuma a lokaci guda sama da hakaicehakaice ɗari sun bayyana a ransa; ko kaza ko kaza. Amma duk ciki babu wanda ya bashi amsa mai ma’ana. Yana cikin wannan hali ne sai ya fara hangen wata inuwa daga nesa, inda nan take ya fara shirya zuciyarsa cikin shirin ko ta kwana. Ba’a daɗe ba halittar dake bada wannan inuwa ta bayyana, inda ya fara hango kanta. Wanda hakan yasa kaɗan daga cikin tashin hankalin da yake ciki ya ragu, badan komai sai dan cewa ya gani da idonsa cewa wannan mai ƙarasowa mutun ne kamarsa. Kuma a lokacin ya ƙara jin sanyi acikin ransa, saboda yasan cewa indai wani mutun zai iya rayuwa a wannan waje to fa shima yana da dama. Halittar mai ƙarasowa bata ɗauki lokaci ba ta iso gareshi, inda idanunsa suka gane masa mace budurwa mai kalar fata irin tasa sak wato ‘wankan tarwaɗa’. Tana da gashi mai tsayi da yawa wanda ta tattareshi ta ɗaure. Fuskarta na nuna alamun yarinta, tayadda Armad ya yanke shawarar baza ta wuce shekaru ashirin ba, wato dai baifi ace ta bashi shekaru huɗu ko uku ba kenan. Amma duk da ƙarancin shekarun da fuskarta ke nunawa idanunta su na ƙunshe da alamun kafiya da saiti, wanda ke nuni cewa duk abinda wannan mace ta saka a gaba saita cimmasa. Duk da cewa kyakkyawa ita ma ta gaske, amma Armad bashi iya bata lambar girma a kyau a wannan lokaci, badan komai ba sai dan cewa a zuciyarsa yana hangna mai suna Nostalgiya. Tana ƙarasowa ta tsaya kimanin taku biyar kafinsa, sannan kawai ta ɗan ƙura masa ido na ɗan lokaci, kafin daga bisani ta zira hannunta na dama acikin baƙin mayafin da take sanye dashi, inda ta fito da takobi sanye acikin kufe mai adon baƙi da yalo ta kuma jefawa Armad ita. Kallo ɗaya kacal Armad yayi wa takobin ya gane cewa kufensa ne kuma takobinsa ce. Ya miƙa hannu ya cafe, wanda a lokacin ne yaji hankalinsa ya kwanta kamar wanda aka bawa wata nutsuwa. A lokacin ne kuma ya ƙara lura cewa kayan jikin nasa shima baƙaƙe ne, kuma sunyi kama dana wannan budurwa dake gabansa. Nan take ya haɗa ɗaya da biyu ya gane duk abinda ke faruwa. Baiyi wata-wata ba ya sunkuyar da kai alamun girmamawa ya kuma ce mata, ”na gode sosai da kayan da kika bani da kuma kula dani da kikai tsahon wannan lokaci.” Armad ya ɗago kai ya kalle ta yaga babu alamun komai a fuskarta tamkar ma bata ji mai yace ba. Saboda haka kawai ya yanke shawara, ya juya da niyyar tafiya, to amma a wannan lokaci ne yaji tayi magana, ”Ya sunanka, kuma ya akai kazo nan wajen?” Muryar tata bata ɗauke da taushi ba kuma ta ɗauke da kaushi, tamkar kwata-kwata bata damu da amsar waɗannan tambayoyi da tayi ba. Armad ya ci birki, inda ya juya ya fuskance ta idonsa cike da son ya gane meke faruwa a wajen. Ya ɗanyi shiru yana kai-komo da abinda ya kamata ya faɗa, inda a lokacin ya gane cewa lallai bashi da wani zaɓi da yafi yayi mata bayanin kansa. Tunda ko ba komai, baya jin zuciyarsa na ɗarsa masa wata mugunta a tattare da wannan mace, sannan abisa mamaki yaji kurum zuciyarsa ta fara nutsuwa da ita, wato yana ji kamar ba cutar dashi tazo ba. Kuma mafi muhimmanci ma idan ya rabu da ita ya tafi a yaushe ne yake tunani a irin wannan waje zai ƙara ganin wani ɗan adam ɗin, sannan gashi yana jin yunwa da ƙishi. Nan take ya tako ya nufeta, bayanda ya kusa isa, sai ya tsaya kawai ya nemi waje ya zauna ya kuma ɗaga kai ya kalleta yana yi mata bishara data zauna ita ma. Ta ɗau kimanin minti ɗaya kawai tana kallonsa, kafin daga bisani ta zauna ta zauna nesa dashi. Bayan ta zauna sai ta juya kai ta kalleshi tana kuma bashi alamar cewa ya fara jawabi. Abu na farko daya fara tambaya cikin mamaki shi ne, “kafin na gaya miki yadda nazo nan, da… ALLAH… ko zaki gayamin a wacce shekara muke yanzu haka???” Cikin mamaki ta dube shi gefe da gefe, sannan a hasale ta amsa masa da cewa, “kanka ya bugu ne? A ƙarshen shekarar 1853 mana muke!” Nan take Armad yai zumbur ya miƙe, baki a hangame, ido a kwale. Cikin ƙinƙina ya ce, “1853????? “Kin tabbata! Saboda ƴan watanni kaɗan da suka wuce na na baro gida, kuma ina da tabbas a shekarar 1851, shekarar da aka gama wancan yaƙin na fito!!!” Kallonsa kawai tai, tana ƙoƙarin tabbatar wa da kanta cewa ba’a cikin hayyacinsa yake ba, amma duk yadda tayi sai taga cewa idonsa yana nuna gaskiya yake faɗa. Saboda haka kawai tai shiru tana tunanin mai ya kamata tayi dashi. Tana cikin wannan tunani ne taji muryar Armad, wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye, “dan ALLAH ko zaki bani aron Ayrid guda ɗaya, ina son na tura saƙo gida!” Kallonsa kawai tayi, irin kallon mai nuna rashin yadda, sannan ta ɗauke kai. Yana ganin haka ya fuskanci yana da buƙatar yayi mata bayanin kansa dalla-dalla da kuma yadda yazo wannan waje indai yana buƙatar haɗin kai daga gareta. Saboda haka nan take ya kwashe dukkanin abinda ya faru dashi ya gaya mata. Sannan ya ƙara jaddada mata buƙatar Ayrid ɗin da yake. Bayan tsahon lokaci tana kallonsa, sai ta zira hannu cikin mayafinta ta ɗakko kwayar Ayrid guda ɗaya ta cilla masa. Nan take Armad ya fasa ɗan yatsansa guda na dama ya ɗisa jini akai, sannan ya miƙa hannu ya ɗan gitsiri wannan jan kyalle dake ɗaure akansa, kafin daga bisani ya haƙa ƙasa a wajen ya binne. Suna zaune babu wanda ya ce ƙala a cikinsu, shi Armad yana jiran amsa daga kakansa wanda dama shi yai niyyar yana nutsuwa ya iso ƙasa ta huɗu, ya turawa saƙo cewa yaje lafiya. Sannan kuma ya tambayi lafiyar mahaifiyarsa. Amma bayanda ya farka sai ya tsinci kansa a tare da waɗancan mutanen, kuma yanzu gashi ya faɗo nan wajen. Duk a tunaninsa baifi ƴan watanni ba, amma gashi ana ce masa shekara biyu ta wuce. Ita wannan budurwa tana nata tunane-tunanen. Ba jimawa ƙasar dake wajen ta fara motsi, inda kan kace meye wannan ƴar shuka ta bayyana, wadda a samanta kwayar Ayrid ce guda ɗaya. Armad ya miƙa hannu ya tsinka. Yana riƙewa a hannunsa, ta juye izuwa takarda. A jiki an rubuta; ; ; *** kai jika Armad! Ina ta turo maka saƙonni baka bada amsa, to amma tunda na jika yanzu nasan komai lafiya. Naji matakin daka ɗauka na neman Tirifil-fakta, kuma kai sani ina alfahari dakai. Da fatan acikin wannan shekaru biyu da suka wuce kana gabda nemoshi, inma baka riga ka nemoshi ba. Mahaifiyar ka ta fara samun sauƙi tuntuni, kuma idan bakai sauri ba idan ta tashi ban san mai zan gaya mata, taƙi biyoka ba! Kayi ka gama ka dawo, ina jira kazo naga ci gaban Izzar daka samu! Ka kula da ma’abota Ururu!! Sune suka sawa mahaifiyarka wannan cuta! Zanso idan na ƙara ganin saƙon ka naga ka cika wannan aiki!!! *** Armad na gama karanta wannan saƙo yai wata mummunar ajiyar zuciya, inda wani mugun gumi ya keto masa, bai san ya fara jin jiri ba, ba shiri ya nemi waje ya zauna. Tsahon lokaci baice komai ba, kawai kallon sama yake, yama rasa mai zaiyi tunani!! *** To fa! Armad yayi shekaru biyu, amma bai san a ina ba! Domin bama ya tuno wucewarsu ko kaɗan acikin ransa!! Mai kuke tunani ya faru ne?? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 14: Ikenga O Bayajidda Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . A A shekarar 1851 After Amri (A.A), a wani gari mai suna Jíha, dake kan doron ƙasa ta bakwai ɓangaren Arewa. Tsakiyar dare ne, kuma a wannan rana ma wuni akai ana azababben yaƙi tsakani ɓangaren Ururu da kuma ɓangaren ƴan adawa dake da shalkwatarsu a wannan gari. Babu abinda kake gani sai gawarwakin jama’a duk inda ka duba, dan kusan a wannan rana zaka iya cewa aka kawo ƙarshen wannan babban yaƙi. Wannan yaƙi dai shi ne wanda mahaifiyar Armad ta samu rauni ashi, kuma harma Armad yaci alwashin sai ya kawo mata mutumin data fita nema ta samu wannan ciwo har gida, komai rintsi komai wuya. To acikin wannan gari dai, duk inda ka kalla gawarwaki ne a kwance fululu, amma duk da haka idan ka samu ɓangaren da ba mutun a kwance, zaka ga cewa gaba ɗaya ƙasar wajen ta juye izuwa launin ja da baƙi, saboda yawan jinin daya kwarara a wannan rana. A ƙasa kaɗai al’ummar dake kwance a mace sun haura dubu ɗari, wani ba kai, wani ba ƙafa, wani kayan ciki a waje, wani a caccake da takubba, haka dai kowa ka kalla zaka ga akwai sanadin mutuwarsa. Babu abinda yake kewayawa a saman wannan gari sai hankakan mutuwa, wanda shi kansa saboda yawan jinin da aka zubar ya fara komawa canjawa daga fari izuwa launin ja. Acikin waɗannan gawarwaki, idan ka duba zaka gano cewa, mafi yawa daga ciki mata ne da ƙananan yara da tsafaffi, waɗanda kasan tabbas irin waɗanda ake bari a gida a fita yaƙi ne. Amma duk da haka babu ko ɗaya mai rai acikinsu! Can bayan wani lokaci wata gawa daga cikin waɗannan mutane, wadda idan ka kalle ta, to zaka iya lissafa mashi sama da biyar a jikinta a cake, amma a haka ta motsa ƴan daƙiƙu kaɗan da suka wuce. Lamarinda yasa hankakan mutuwar dake wajen tashi sama. A hankali a hankali, wannan gawa ta miƙe tsaye ta kuma tsaya akan sauran gawarwakin dake ƙasanta. Kallo ɗaya kacal zakai mata kasan cewa yaro ne wanda bazai haura shekara sha biyu zuwa sha uku ba. Amma wannan yaro sama da awa goma kenan tun bayan da aka cake masa waɗannan mashi ka a jikinsa, amma yake ta fafatawa a tsakanin mutuwa da rayuwa, yana rantsuwa da mahaliccin sarkin Bayajidda na farko, akan cewa lallai bazai mutu ba. Tuni hankalinsa baya jikinsa, kuma babu abinda ke zagaye a jikinsa banda jini ko’ina da ina, idanunsa sun canja izuwa jajaye kamar garwashi, kana ganinsa zaka tabbatar da cewa ya kamata ace shekaru da dama da suka wuce ya mutu, amma ina, rantsuwa kawai yake, yana ƙara rantsewa akan lallai bazai mutu ba a wannan rana ba. Yana haka jini ya ɗebe shi ya ƙara faɗuwa, amma ba jimawa ya tashi ya ci gaba da wannan rantsuwa. Sai da wannan yaro yai kwana goma acikin wannan hali, sannan ana sha ɗayan, yana gabda mutuwa, wani mutun ya bayyana, fuskarsa a rufe bubu abinda kake gani sai kwayar idanunsa guda biyu. Waɗanda kallo ɗaya kacal zakai musu kasan cewa baƙaƙe ne ƙirin, babu alamar wani fari ko kuma haske acikinsu. Hasalima, yana bayyana duk ilahirin hasken wajen ya fara dusashewa. Yana bayyana ya isa wajen wannan yaro, inda ya dube shi ya ce, “yaro, ka rantse ka kuma rantsewa akan baza ka mutu ba, kuma ka ƙi mutuwa.. “Shin mai yasa kake son kaci gaba da rayuwa, bayan duk wanda ka taɓa sani a duniya ya mutu, bayan duk wanda zai taimake ka ya mutu?” A wannan lokaci tuni muryar wannan yaro ta dashe kuma bata fita ko kaɗan, amma a haka ya dubi wannan mutum ya buɗe baki ya faɗi wata kalma guda ɗaya cikin firgici, “U….ururu??” Ya tambayi kansa ne, domin akan idonsa yaga baƙaƙen idanuwa guda biyu a jikin fuskar wannan mutun, kuma yasan cewa ƴan ƙabilar Ururu su kaɗai suke da irinsu. To amma babban abinda ya firgita shi, shi ne, Ururun dai sune suka jagoranci wannan yaƙi dayai sanadiyyar halin daya tsinci kansa aciki. Hasalima su suka sa, yana ɗan gawurtaccen sarki, amma ya dawo wanda bashi da kowa acikin dare ɗaya. To amma yanzu ga wani mai baƙaƙen idanuwan nan ya bayyana a gabansa! Sautin muryarsa bai fito ba sosai, amma tsananin fushi da tsana dake ƙunshe acikin wannan kalma guda ɗaya ta ‘Ururu’ daya furta, sai daya jawo gaba ɗayan ilahirin wajen ya ƙara duhu, gami da cika da tsananin yanayi irin na Fansa da Tsana. Haka dai bayan wani lokaci, wannan ma’aboci baƙaƙen idanuwa ya ɗanyi wani murmushi wanda komai iya karanta fuskarka, baza ka iya gane ma’anarsa ba, sannan ya miƙa hannunsa yai nuni izuwa wannan yaro, wanda hakan yasa yaron tashi akan iska ya taho wajenda yake tsaye, inda ya tsaya a gabansa riƙe akan iska idanunsa suna kallon waɗannan baƙaƙen idanuwa ciki da ciki. An ɗauki lokaci a haka, kafin daga bisani a wani al’amari mai cike da al’ajabi, ya juya ya fara tafiya izuwa gabas, wannan yaro kuma ya biyo bayansa ɗaure akan iska. Sunan wannan yaro Ikenga O. Bayajidda! *** Acikin wannan sihirtaccen fili kuwa, bayan tsahon lokaci, Armad da wannan budurwa na zaune, kana kallonsu zaka fuskanci dukkansu sun nutsa acikin tunani; shi Armad na tunani akan wannan shekaru har sama da biyu daya bayyana cewa sun wuce ba tare da yasan ya akai yayi su ba, kamar wani a mafarki. Ita kuma tana ta tunani akan dukkan labarinsa daya gaya mata, musamman ma tayadda ya ce mata ya shigo wannan waje, wanda a iya saninta babu wani mahaluƙi daya isa ya shigo inba da yardar ƙabilar da ake kira da Maikironomada ba. To haka dai suka wanzu tsahon kusan rabin sa’a, kafin daga bisani ta dubi Armad gami da cewa, “wato dai kana gayamin kaima a zahirin gaskiya baka ma san tayadda ka shigo wajen nan ba? “Kawai kayi amfani da wata fasaha ce, kuma kamar yadda kace, ka buɗe ido ka ganka anan! “Sannan kuma kana gayamin cewa kwata-kwata baka da masaniya akan shekaru biyun da suka wuce? Wannan budurwa ta ɗaga ido ta kalleshi babu alamun canjin yanayi kwata-kwata a tattare da ita. Sai dai duk da haka zaka iya gane cewa acikin zuciyarta abinda ke kaikomo bai wuce zantuttukan da Armad ya gaya mata, shin gaskiya ko ƙarya yake faɗa! Bayan wasu ƴan daƙiƙu kawai sai ta ɗauke kai daga Armad gami da yin ajiyar zuciya, inda ta fara da cewa, ”wannan ƙasar da kake kai tana daga cikin yankin sihirtattun ƙasashe uku dake ƙarƙashin mulkin ƙabilar Maikironomada. ”Kuma waje ne wanda a iya sani na an killace shi ne saboda jarabawa ta musamman ga jaruman da suke takarar zama zaɓaɓɓun babban birnin Maiki na duniyar Maikironomada. ”Ban san taya akai ka shigo wannan waje ba, saboda hanya ɗaya kaɗai da ake shigowa shi ne ta ƙofar sihiri guda ɗaya kacal dake garin Arewar Maikironomada.” Tayi ɗan shiru tana karantar Armad da ido da kuma yanayin yadda taga fuskarsa ta canja. Bai ɗauke ta dogon lokaci ba ta fahimci cewa Armad ɗin bashi da wata masaniya bisa abubuwa da dama data faɗa. Ta sunkuyar dakai gami da ajiyar zuciya, sa’annan kuma a lokaci na farko tun bayan haɗuwarsu da Armad fuskarta ta ɗan nuna alamun ɗan tausayi, wanda bai ɗauki sama da daƙiƙa ɗaya ba ya ɓace. Sannan ta ce, ”toh! koma dai meye ka gane cewa yanzu tunda kariga ka shigo nan abu ne mai wahalar gaske ka tsira, kasancewar nima ka ganni anan shekara ta uku kenan ina ƙoƙarin cin wannan jarabawa na fita daga wannan waje, amma abin ya ci tura!” Bayan wasu ƴan daƙiƙu kawai sai ta ɗauke kai daga Armad gami da yin ajiyar zuciya, inda ta fara da cewa, ”wannan ƙasar da kake kai tana daga cikin yankin sihirtattun ƙasashe uku dake ƙarƙashin mulkin Maikironomada. ”Kuma waje ne wanda a iya sani na an killace shi ne saboda jarabawa ta musamman ga jaruman da suke takarar zama zaɓaɓɓun babban birnin Maiki na duniyar Maikironomada. ”Ban san taya akai ka shigo wannan waje ba, saboda hanya ɗaya kaɗai da ake iya shigowa shi ne ta ƙofar sihiri guda ɗaya kacal dake garin Arewar Maikironomada.” Tayi ɗan shiru tana karantar Armad da ido da kuma yanayin yadda taga fuskarsa ta canja. Bai ɗauke ta dogon lokaci ba ta fahimci cewa Armad ɗin bashi da wata masaniya bisa abubuwa da dama data faɗa. Ta sunkuyar dakai gami da ajiyar zuciya, sa’annan kuma a lokaci na farko tun bayan haɗuwarsu da Armad fuskarta ta ɗan nuna alamun ɗan tausayi, wanda bai ɗauki sama da daƙiƙa ɗaya ba ya ɓace. Sannan ta ce, ”toh! koma dai meye ka gane cewa yanzu tunda kariga ka shigo nan, ka shigo kenan, kasancewar nima ka ganni anan shekara ta uku kenan ina ƙoƙarin cin wannan jarabawa na fita daga wannan waje amma abin ya ci tura!” *** To fa! Ana dara ga dare yayi, Armad ya shiga inda ba fita!!! Sannan kuma munga kaɗan daga cikin yaƙin daya janyo mahaifiyar Armad ta samu rauni, a shekarar 1851(After Amri), har ya ɗauƙi alwashin cika mata burinta na kawo mata abinda take nema har gida. To amma waye wannan yaro, kuma waye wannan mai baƙaƙen idanu daya ceto shi, kuma saboda me, bayan cewar dasu sukai yaƙin. shekarar 1851 After Amri (A.A), Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 15: Sanyin Babban Sihiri Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . . A can wannan daji kuwa duwatsu ne iyakacin hangen ɗan-adam, inda daga cikinsu mutane sanye da kayan yaƙi suke ta ƙara ɓulɓulowa su na nufo wajan da su Zahra suke tsaye cirko-cirko tun bayan jin wannan murya. Kafin kace meye wannan mutane da dama sun kewaye su ta kowanne ɓari. Ana cikin haka wasu manya-manyan mutane waɗanda su kaɗai ne fuskarsu bata naɗɗaɗe da rawani suka fito fili daga bayan wasu jajayen duwatsu. Su na fitowa, kai tsaye suka fara kusantar inda su Hasanu suke tsaye. Dukkaninsu manya-manyan halittu ne tayadda in baka kula ba sosai ba, sai kace samudawa ne. Na tsakiyar tasu ya ɗan ɗara ragowar tsayi yana sanye kuma da jan rawani wanda kamar kamar rawanin sauran mutanen dake kewaye da wajan ba, bai rufe masa fuska ba. Yana ɗauke da wani ƙatoton farin gatari. Idan kuma ka duba zakaga cewa duk da duhun wajen bai hana idanunsa walƙiya ba, wanda idan ka ƙura ido zaka fahimci cewa acikin idon nasa akwai waɗansu abubuwa guda biyu acikin kowanne ido. Idan ka ƙara ƙura ido zaka fahimci cewa waɗannan abubuwa ba komai ba ne ba illa hoto na taurari waɗanda suka maye gurbin baƙin kowanne idonsa, biyu a kowanne ɓangare wanda ya bashi taurari guda huɗu kenan idan aka tara. Su kuma mutun biyun dake gefensa idanunsu kamar na kowa ne, amma kuma a goshinsu akwai tambari na Miyura, na ɓangaren daman yana da taurari uku irin na cikin idanun na tsakiyar, su na motsi su na kewaya wannan Miyura dake goshinsa. Na ɓangaren hagun kuma yana da taurari guda biyu, shima kuma su na kewaya Miyurar dake goshinsa. Babban nasu mai taurarin a ido ya fara magana, ”Hasanu, a bayyane yake a fili babu yadda zaku iya fita daga wannan waje inba mu muka barku. ”Da farko da muka gano mutun uku kacal na tafiya da Ayrid mai babban mataki, munyi niyyar kawai mu kashesu mu kwace. ”To amma bayanda na gano kaine aciki, sai na canja shawara cewa idan kuka bamu wannan Ayrid, da kuma duk abinda kuka mallaka, to zan barka ka wuce da ranka. ”Duk da kuwa mataimaka na guda biyu basu goyin bayan hakan ba, amma badan komai saboda tuna baya, naga ya kamata kai kaɗai dai na bari ka wuce da ranka.” Ya ƙarasa maganarsa yana mai waiwayowa yana kallon mutun biyun dake bayansa furkarsa cike da dariyar ƙeta. Fuskar Hasanu cike da fushi ya dubi wannan jibgegen mutum ya fara magana cikin izgili, ”hmmm Ƙiliƙ, ai ban san ka mallaki taurari huɗu ba, dana nemeka nayi maka murna.” *** Ƙarin bayanin akan kalmar Ótaki Kalmar Miyura daga yaren Alderiya take, kuma tana nufin tambari a gaban goshi, kamar Irin wanda Armad yake dashi. To akwai wani abu dake faruwa a wannan zamani wanda yake da ban al’ajabi kwarai da gaske. Wannan kuwa ba wani abu bane illa haihuwar kowanne mutun da ake da tambarin Miyura a goshinsu. Kowacce ƙabila tana da irin tambarinta, wanda kuma su kaɗai suke dashi. Harma ana amfani dashi wajen gane asalin ƴan kowacce ƙabila a yayin haihuwa. Sai dai abinda ke faruwa shi ne, kwana bakwai daidai da dai-dai bayan haihuwa, babu ragi babu ƙari, wannan tambarin yake goge wa da kansa, tamkar ba’a taɓa yinsa ba. Sannan kuma bazai ƙara dawowa goshin mutun ba, har sai mutun yakai wani babban matsayi na Izza da ake cewa ‘Ótaki’ wanda yake nuni da Izza mai mataki na Shekaru ɗari biyar, sannan tambarin zai ringa bayyana a gaban goshinsa, kaɗai lokacin da zaiyi amfani da Izzar data kai ɗari biyar! Kaɗan daga cikin dalilan da yasa Armad yake ɗaura jan kyalle a gaban goshinsa shi ne, domin ya rufe tambarin Miyurar dake goshin nasa. Na farko dai, duk wanda ya gani zai iya gane cewa Armad ɗan ƙabilar Wilbafos ne, (idan baku manta ba, wannan mai tsaron ƙofar, Han’Diyuza, mai aljanin wuta, yana ganin Miyurar Armad yake cewa daga ƙabilar Wilbafos yake!). Ƙabilar Wilbafos dai sunan ta ma ba’a san faɗa. Saboda ƙabila ce da suka taɓa fito na fito da Ururu, wanda a dalilin haka babu wanda yake son yai alaƙa dasu, saboda tsoron Ururu da ake ji. Kai hasalima, har kyauta mutun zai iya samu idan ya kama Armad ya miƙawa Ururu, a matsayin wanda ya fito daga zuri’ar Wilbafos. Sannan kuma na biyu, kamar yadda na faɗa, ana haifar mutun tambarin yake ɗaukewa, to amma bisa ƙololuwar mamaki irin wanda ba’a taɓa gani ba, tunda aka haifi Armad Miyurar sa bata taɓa ɓacewa ba. Ana jira aga bayan kwana bakwai ta ɗauke, amma taƙi, har akai shekara, har aka kai shekaru goma, har izuwa wannan rana, bata taɓa ɓacewa ba, koda sau ɗaya!!! Saboda hakan nema, tun kafin magana ta fara yaɗuwa, mahaifiyarsa ta samu jan kyalle ta rufe masa goshinsa tun yana jariri, wanda kuma dashi ya taso, kuma har a wannan lokaci yake ɗaurashi domin rufe Miyurar. Saboda abu ne wanda zai iya rikita duniya baki ɗaya, idan mutane suka ji wannan labari. Domin kamar a wannan zamani namu ne ace an samu Jaki mai ƙaho ko kuma mutun mai tashi sama ko kuma ace an tsinci raƙumi acikin kuratandu!! *** Ga dukkan alamu ɗan wannan abu da Hasanu ya faɗa yayi matuƙar ɓatawa Ƙilik rai, kamar wanda yake tuna wani abu a baya tsakaninsa da Hasanu, nan take yai gunji gami da dariyar mugunta yana cewa, ”Yau dai girman kanka lallai yazo ƙarshe.” Ya nuna jaruman dake bayansa da hannu yana cewa, ”Ina da janar mai taurari uku, ina da mai taurari biyu, sannan kuma ina da sadaukai dubu biyar waɗanda kawai kalmata suke jira su afka muku ba tare da wani tsoro ba. ”Ka gayamin mai kake taƙama dashi, waye zai iya tseratar dakai yau daga hannuna. ”Kai na canja shawara ta ma, yaune ranar shan numfashinka na ƙarshe, Hasanu.” yai gunji mai razanarwa, lamarinda yasa wata iska mai ƙarfi kaɗawa. Wadda ita kaɗai zata iya karayar da zuciyar abokin karawarsa. Nan take ya ɗaga hannu sama, ya kuma bada umarnin su afaka musu, lamarinda yasa gabaki ɗayan waɗannan mutane dubu biyar, da kuma su ukun suka afkawa su Hasanu. To amma a dai-dai wannan lokaci ne Hasanu ya umarci Kiru da Zahra dasu koma dai-dai bayansa su tsaya, yana mai cewa, ”ku lura sosai, ku zira ido, kuga dukkan abinda zanyi, domin ba lallai ba ne ba, ku ƙara samun dama a rayuwarku ba daza kuga irin abinda zai faru yanzu ba!” A wannan lokaci da wannan babban nasu ya ɗaga hannunsa sama, dukkansu sukai kukan kura inda suka afkawa mutun uku kacal, wato Hasanu da Kiru da kuma Zahra. Hasanun wanda tuni ya umarci ƙannan nasa guda biyu dasu koma bayansa, ya ɗaga ƙafarsa ta dama inda yayi taku ɗaya gaba. Taku ne guda ɗaya kacal, amma a dalilinsa abubuwan da suka faru suna da yawa ta yadda duk wanda ya samu damar ganin abubuwan da suka faru kuma ya tsira da ransa to lallai harya mutu bazai manta da abinda ya gani ba. A ƙunshe acikin wannan takun, taurari ɗai-ɗai ɗaiɗai har guda biyar suka bayyana acikin idanun Hasanu, uku a dama, biyu a hagu inda suka maye gurbin baƙin dake cikin idon nasa. Acikin takun wata iska mai tsananin ƙarfin gaske ta fara fita daga jikinsa. Kan kace meye wannan tuni wannan iska ta game duk wani abu dake wannan kewayen dutsen. Acikin wannan takun waɗansu mutun-mutumi guda biyu waɗanda gabaki ɗaya jikinsu anyi shi ne da wanna iska suka bayyana. Ɗaya a damansa ɗaya kuma a hagunsa. Bayyanarsu keda wuya wani yanayi mai ɗauke da sanyin gaske, tamkar a tsakiyar hunturu, ya cika wajen baki ɗaya, tamkar ƙankara zata fara sauka. Fara kaɗawar wannan iska keda wuya dukkan waɗannan mayaƙa dubu biyar dake doso su Hasanu suka tsaya cak a inda suke. Cikin wani al’amari mai kama da almara kawai wannan iska ta daki jikin waɗannan Jarumai dubu biyar, lamarinda yasa akan idon kowa, wani abu mai kama da ƙanƙara ya fara fitowa daga jikin fatarsu. Sai dai kawai banbancin wannan abu da ƙanƙara shi ne launinsa ruwan toka ne, maimakon fari da aka san ƙanƙara dashi. Amma kuma duk da haka tsananin sanyi ne irin mai ratsa ruhin nan yake shigarsu, wanda tuni yasa suka faɗi ƙasa sumammu. Duk wanda ya rayu a wannan zamani, yasan sunan wannan iska mai ɗauke da ƙanƙara ruwan toka, wadda ita ake cewa, Sanyin babban sihiri!! Wanda kuma idan mutun yakai matsayin Ótaki yake mallaka. Babu waɗanda suka rage illa waɗannan manya nasu su uku wanda ke gabda isa kusa dasu Hasanu. Babu shiri suka ci birki cikin tsananin zafin

Chapter 8 of 33