Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shaƙa yana da yawa, dan bai tashi ba saida rana ta kusa zuwa tsakiya a samaniya. Yana farkawa abinda ya fara Arba dashi sune wasu kuyangi guda uku dukkansu wankan tarwaɗa, suna jera masa kayan abinci. Yana tashi suka zube a ƙasa gami da cewa, ''barka da asuba, shugaba Armad, da fatan ka tashi lafiya.'' Cikin tsananin zafin nama Armad ya wartsake gami da kyaran murya da kuma ajiyar zuciya, ya ce, ''shugaba!!?? ''Waye kuma shugaba?'' ya tambaya cikin mamaki. Nan take suka ɗago kai cikin ladabi suna niyar amsa masa, amma a wannan lokacin ne waɗannan samari guda biyu da Armad ya gani suka nemi izinin shigowa ɗakin. Bayan sun shigo sun gaisa, sun kuma nunnunawa Armad sauran sassan gidan da kuma duk abinda yake sai suma suka fice. Amma har suka tafi babu wanda ya bawa Armad amsar tambayarsa da yayi. Saboda haka kawai sai ya ƙara shiga cikin shubuha akan wai taƙamaimai maike faruwa. Bayan ya gama kimtsawa saiya fito ƴar harabar ɗakin da ya kwana aciki domin ya hangi gari. yana tsaye iskar dake kaɗawa na dukan jikinsa, jan ƙyallen daya ɗaure kansa yana kaɗawa, nan take baisan mai yasa ba sai kawai yaji ya fara tunanin gida da mahaifiyarsa. Nan fa ya nutsa acikin tunaninsa kan kace meye wannan tuni tsananin begen gida yasa rabin sa'a ta wuce ba tare da ya sani ba. Yana cikin wannan hali ne yaji magana a bayansa, ''Armad, ka kwana ƙalau!'' Yana waiwayawa yayi arba da Nusi tana masa murnushi. Ƙarasowarta keda wuya ta tafa hannu, waɗannan kuyangi guda biyu suka bayyana da kujeru guda biyu, wanda suka saka musu domin su zauna. Bayan sun zauna, sai ta dube gami da yin murmushi kana tace, ''ya kaji iskar garin namu, da daɗi ko kuwa?'' Armad murmushi kawai yayi gami da godiya ta karamcin da take nuna masa. Sun ɗan ɗauki lokaci a haka suna maganganu na yau da kullum, kafin daga bisani ta numfasa ta fara bayani, ''Kasan kowanne ɗan adam da yadda aka rubuta masa rayuwa. ''Misali, lokacin dana fara tunanin gayyatarka ka biyo ni wannan gari, abinda ke raina shi ne, na samar maka muhalli mai kyau da kuma duk wasu abubuwa da kake buƙata, sannan kuma na nemar maka babbar makarantar koyon Izza ta wannan gari. ''Amma kaga saboda abu ɗaya daya faru, wanda ban taɓa kawowa ba, hakan ba zata yiwu ba.'' Tana faɗar haka ta ɗan ɗaga kujerarta gami da saita ta ta fuskance shi, ta yadda take kalonsa ido cikin ido. Kallo ɗaya zakai mata kasan cewa a wannan lokaci babu alamun wasa acikin zuciyarta, kuma duk abinda zata faɗa zata faɗe shi ne tamkar tana rantsuwa da abin imaninta. ''Armad kayi sani cewa wancan tsari dana gaya maka shi ne na farko acikin guda uku! ''Amma tunda yanzu bazai yiwuba abinda zaisa mu zaɓi tsari na gaba, duk ya ta'allaƙa da sakamakon daka fito mana dashi idan ka shiga Non-toch-teka. ''Kayi sani cewa a wannan gari, babu wani zancen ƙabila ko kuma ƙungiya, abinda kawai yake nuna matsayinka shi ne, acikin manyan matakan Izza, a ina kake. Ta ja dogon nunfashi, sannan taci gaba da cewa, "a yau ina ganin ka cancanci na gaya maka sirrin mu, sirrin duk wani ɗan ƙabilar Djinn, wanda kuma shi ne manufar duk wani ɗan wannan ƙabilar! "Kai sani cewa, mutanen da suka san abinda zan gaya maka a yanzu, basu da yawa a duk faɗin duniya. Saboda haka abinda zaka ji, ka tabbata lallai baza ka taɓa gayawa wani mahaluƙi ba a ban ƙasa. "Asalinmu mu ƴan ƙabilar Djinn, mun fito ne daga ɗaya daga cikin garuruwan ƙarƙashin ƙasa, wanda ake cewa Shaníza. "Mun kasance daga cikin mafiya girman ƙabilu a duk faɗin duniyar ƙasa bakwai, harma muna gogayya da ma'abota Ururu! "Babu inda ba'asan sunanmu ba, kuma babu inda ƙarfin mulkin mu baije ba! Kwatsam watarana, sai waɗansu mutane suka bayyana a shashin Ikwatora, wato inda aka fi sani da 'Danja zon!' "Du du du, adadinsu ɗari ne kacal, duk da wasu suna cewa ɗari da ɗaya ne, wasu kuma da biyu. Amma su kaɗai sai suka addabi dukkan wani mahaluƙi, a doron ƙasa cikin kwanaki bakwai kacal! "Hatta ma'abota Ururu, babu yadda suka iya dasu, sai kawai komawa da baya da sukai, suka shata musu iyaka da doron ƙasa ta biyu da kuma ta farko. Amma haka suka rabu dasu. "Kuma babban abin al'ajabin shi ne, babu wanda yasan komai akansu, illa abu ɗaya kacal, wato aniyarsu, wadda aka ce wai suna kan hanyar su ne ta Tafiyar Alwashi! "Ba jimawa, sai jama'a suka fara ce musu, MatafiyanAlwashi. "To ana cikin wannan rikici kwatsam, sai aka nemi waɗannan mutane aka rasa, ko sama ko ƙasa. Har tsahon kwana uku, babu su babu labarinsu. "Kwatsam a rana ta ukun, sai suka suka bayyana a ƙofar garinmu Shaníza. "Kafin mu farga sun shige cikin garin, inda suka ƙullo ƙofar ta ciki. Tun daga wannan rana ta litinin, shekarar 683 Bayan Amri (A.A), babu wani mahaluƙi daya ƙara shiga ko kuma fita daga wannan gari, har yau ɗinnan da nake maka wannan zance." Tai shiru, gami da duban Armad, kafin daga bisani taci gaba da cewa, "nasan mai kake tunani! "Cewa duk tsahon shekarun nan, idan babu wanda ya ƙara shiga ko kuma fita daga cikin garin, to ta ina muka fito! "Lallai kam wannan abin tambaya ne, domin kuwa kaɗai daga cikin iyayen mu da kakannin mu wanda suka fito daga cikin garin, kafin shigar waɗannan mutane, su su kaɗai ne suke yawo aban ƙasa yanzu. "Kuma sune suka hayayyafa, har aka samemu. To amma da yake gaba ki ɗayan yawansu, baifi cikin cokali ba, har yanzu bamu fi a irga mu ba. "Kuma dukkanin a inda muke, muna gane kanmu, sannan kuma ba muda wani buri, banda muga cewa watarana mun koma cikin garinmu, mun fitar da waɗannan mutane, kuma mun tseratarda miliyoyin mutanen mu dake ciki. "Sai kuma wata tambayar da zaka iya ƙarayi, cewa idan dai har al'amarin waɗannan mutane ya baza duniya, to ya akai yanzu babu wanda ya sani, bayan dududu ba'afi shekara dubu ɗaya da ɗari biyar da wucewa ba. "Lallai wannan tambaya ce mai kyau, kuma amsar ta faru ne shekaru biyu bayan shigar waɗannan mutane cikin garin mu; "Kwatsam sai aka wayi gari Sarki Dul'Ururu, sarki bisa doron ƙasa ta biyu, ya haɗo runduna ta ma'abota Ururu, irin wadda ba'a taɓa gani ba, ya kuma bayyana a bakin wannan gari namu. "Babu wanda yasan mai ya faru, illa cewa anyi sama da kwana ɗari ana kwabza yaƙi, amma daga ƙarshe, katangar garin nan bata faɗi ba, kuma shi ɗin, bai samu damar shiga garin ba. Haka ya juya ya koma izuwa ƙasarsa! "Muma iyayenmu da kakannin mu, sunyu iya ƙokarinsu domin suga sun shiga cikin garin, amma ina. Duk da kuwa acikin su, akwai wazirin sarkin mu, wanda yasan duk wasu ɓarauniyoyin hanyoyi da ake shiga. "Kai daga ƙarshe dai haka suka haƙura. "To amma abin bai tsaya anan ba, kwatsam bayan ƴan watanni, ba sai aka ji, sanarwa daga Dul'Ururu ba, cewa duk wani ɗan asalun garin nan, ya zama mai laifi, sabida haka da an ganmu a kama mu. "Sannan kuma acikin sanarwar, aka haramta ƙara ambatar sunan Tafiyar Alwashi, Matafiyan Alwashi, kai dama duk wani abu daya shafesu. Duk wanda ya karya dokar hukuncin kisa. "A haka aka ringa kashe mutanen mu, har takai saida muka daina amfanu da sunan mu kwata-kwata. Kuma a haka dukkan wannan labari ya mutu. Labarin dani da ragowar mutanenmu , baza mu taɓa mantawa ba. "Amma kai sani cewa bamu haƙura ba, kuma haka ta ƙarƙashin ƙasa mukai ta bin diddigin dalilin da yasa Ururu suka shiga al'amarin. "Bayan sama da shekaru dubu muna bincike, muka gano cewa, Ururu sun sami tabbashi daga wata majiya da bamu sani ba, cewa waɗannan mutane suna da alaƙa da Tirifil-fakta, kuma wannan shi ne dalilin da yasa suka shiga faɗan. Harma kuma suke son a rufe zancen! "Toh, Armad Wilbafos, wannan shi ne labari ne! Da fatan zaka riƙe shi har iya ƙarshen numfashin ka." Armad yaja dogon numfashi, gami da yin ajiyar zuciya, yana kallonta cikin mamakin wannan labari nata. Musamman duba ga cewa, a karon farko, ya sami wani abu mai alaƙa da abin da yake nema, wato Tirifil-fakta! Tunda fari, bai san mai yasa ba, amma tunda dadewa idan ya kalleta abinda yake ji acikin ransa ba komai bane ba illa ƴan uwan taka, saboda haka daya ga irin kallon da take masa, sai kawai zuciyarsa ta cika da tunanin mai yasa take gaya masa duk wannan sirrikan, shim bata tunanin ya fallasata? ''Kuma wani abu da kake da buƙatar ka sani da wuri shi ne," taci gaba da bayani, kamar bata fuskanci kallon da yake mata ba, "wannan haske da kaga ya tashi sama kuma daga baya ya fara tattarewa a wajen ƙofar gari, idan ya gama haɗuwa kaf, shima sifar mutun zai bayar, wanda kuma ba kowa zai zamo ba face kai!! ''A halin yanzu duk da binciken da jama'a keyi zaiyi musu wuya su gano ka, amma daga lokacinda aka ce wancan mutun-mutumi ya gama bayyana, kallo ɗaya kacal ya isa kowa ya gane ka indai ya taɓa ganinka. ''Mafi tsayin lokaci da yazo a tarihi wanda wannan mutun-mutumi da ake cewa Al'yaya, ya ɗauka kafin ya gama haɗewa shi ne wata uku! ''Mafi ƙanƙanta kuma kwana tara! Ta ɗanyi shiru kamar tana tunani, kafin daga bisani ta girgiza kai, sannan ta ci gaba da cewa, ''ya wajaba akan ka kayi azama ka maida hankali a Non-toch-teka da zaka shiga nan da ƴan kwanaki masu zuwa, domin idan son samu ne kafin mutun-mutuminka ya gama haɗuwa yadda mutane zasu iya ganeka ya zamanto ka fice daga cikin garin nan. ''Domin babbar matsalar ka a yanzu bawai masu farautarka a matsayin Magajin Wuobafos bace, babbar matsalarka ita ce mahaifin gimbiya ZAHRA Sisiyu(Nostalgi ya) daka labarta min kun haɗu a baya, wato Sarki BIHANZIN wanda akafi sani da Shugaba Bihanzin mai DAUWAMAMMEN SARA!!! "Babban sarki mai kula da harkar cinikin bayi a wannan doron ƙasa, mutun na farko daya fara mallakar Alyaya mai takobi a garin khan. A dukkan tarihin duniya ba'a taɓa samun wanda ya kaishi ƙarfin saran takobi ba. Kuma indai yace saiya halaka mutun tofa lallai ƙarshensa yazo. "Saboda wani dalili da ba'a sani ba, duk wanda ya taɓa mallakar mutun-mutumin daka samu a ƙofar wannan gari, saida Bihanzin ya hallaka shi. Kayi sani cewa a halin yanzu, a dukkan doron ƙasa bakwai, babu wani mahaluƙi da baya tsoron kaifin taƙobin shugaba Bihanzin. Hasalima akwai dalili na musamman da yasa ake kiranta da suna DAUWAMAMMEN SARA. "Kai sani cewa bani da ƙarfin da zan iya kareka daga takobin Bihanzin kuma lallai kaima baza ka iya tsayawa a gaban Dauwamammen sara ba. Domin kuwa ina so na labarta maka cewa da DAUWAMAMMEN SARA aka kashe Magajin wilbafos na uku." Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 24: Dauwamammen Sara Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Acikin wannan haraba Armad na zaune suna tattaunawa da Nusi inda take zayyana masa dukkan shirinta da kuma sharrin da yake tunkaro shi. Bayan ta ƙara kurɓar lemon dake gabanta ta kuma tambayi Armad mai yasa baya shan nasa, amma maimakon ya bata amsa, wata kalma ɗaya ce kawai ta fito daga bakinsa, ''Bihanzin!'' Nusi ta girgiza kai, sannan tayi murmushi wanda kana gani kasan akwai firgici acikinsa, gami da cewa, ''Zanso matuƙa nace maka baka cikin wani sharri to amma abin bahaka yake ba. Domin kuwa kasan cewa......." Armad ne ya ɗaga mata hannu tare da girgiza kai alamun hankalinsa har yanzu a kwance yake, "Kada kiji tsoro! Lallai bazan daina numfashi ba saina cika burin mahaifiyata na nemo Tarifil Fakta. "Amma ni yanzu ma babban abin da nake so naji shi ne cinikin bayinnan. Shin menene asalin cinikin bayin nan kuma mai yasa babu wanda zai buɗe baki a ɗuk cikin sarakunan duniyar ƙasa bakwai ya ce adaina. Domin ni a gani na zalunci ne kawai da ƙara ƙarawa mai ƙarfi ƙarfi da kuma danne mara ƙarfi. Amma ke meye ra'ayinki akai?" Ga dukkan alamu wannan al'amari na cinikin bayi da ake yana matuƙar ciwa Armad tuwo a kwarya, kuma ya daɗe yana damunsa. Nusi ta girgiza kai tare da mummunar ajiyar zuciya, sannan a wani yanayi mai ban tsoro gumi ya fara keto mata tamkar wadda aka kunnawa wuta. Ta tashi daga kan kujerarta sannan cikin sauri da tuntuɓe ta nufi bakin ƙatuwar tagar dake ɗakin da suke ciki. Tana isa ta leƙa ta fara dube-dube zuciyarta tana dukan uku uku. Koda ta tabbatar babu kowa a wajen tagar saita rufota cikin sauri, sannan saita ƙara juyowa tana gudu ta isa bakin ƙofar ɗakin tana zuwa ta leƙa sannan kuma ta rufeta. Lamarinda yasa nan take ɗakin ya rufe dunɗum da duhu. Armad bakinsa a buɗe mamaki ya cika zuciyarsa akan meke faruwa, kuma meye dalilin da yasa kawai tana zaune a nutse kwatsam ta rikice. Mamaki yasa ko magana ya kasa. Wata ƴar fitilar aci bal-bal ce a hannun Nusi wadda ta iya haskaka ɗan iyakacin tsakiyar ɗakin kaɗai inda suke zaune. To sai a lokacin da Nusi ta zauna sannan Armad ya samu ya iya yin magana, "wai meke faruwa ne? Lafiya?" Nusi ta ja kujerarta inda ta matsa kusa dashi sannan ta fara magana ƙasa-ƙasa, "kana so ka faɗi abinda za'a hallaka dukkan miliyoyin alummar ƙasar nan ne. Baka da masaniyar cewa iska zata iya ɗaukan maganarka ta kaita kunnen ma'abota Ururu. "Baka da masaniyar cewa wasu daga cikin mabiya ɗarigar Ururu zasu iya jinka kuma su isarda da labarin abinda ka faɗa. "Baka da masaniyar cewa Shísu Ururu yana kan wannan doron ƙasa. Lallai kada ka ƙara faɗar wata mummunar magana akan harkar cinikin bayi. Idan dai baso kake a wayi an shafe garin Khan daga ban ƙasa." Tunda ta fara magana bata shaƙi numfashi ba, saboda haka tana zuwa nan a zancenta dole ta tsaya ta fara haki tana ƙoƙarin kama iska. Amma duk da haka bata dawo hayyacinta ba sai bayan sama da daƙiƙa ashirin. "Armad Wilbafos bawai kai ba, a'a sauran mutane zaka duba. Domin kuwa Ururu babu ruwansu da yara ko mata ko tsofaffi. Saboda hakaina roƙonka, indai zaka faɗi wata magana akan ɓatanci ga harkar cinikin bayi toka bari harsai kakai matakin Izzar da zaka iya kare mutane daga tsananin ƙarfin mulkin da mayaƙan azaba na Ururu keda shi." Idanunta kafe akansa, babu abimda take so taji inba amince warsa ba. "Amma kinsan wani abin mamaki, sak irin wannan magana da kika gayamin ita kakana Zaikid ya gayamin." Maimakon ya bata amsa saiya canja akalar zancen. " 'kada ka yaƙi cinikin bayi idan baka da ƙarfin da zaka iya kare mutanen ka daga abinda zai biyo baya.' haka yake gayamin a duk lokacin da zancen cinikin bayi ya tashi." Armad yai shiru yana kallon ƙasa, a yayinda ita kuma Nusi take kallonsa. Lallai ya daɗe al'amarin cinikin bayi yana ci masa tuwo a kwarya. To amma ga dukkan alamu babu abinda zai iya a wannan lokaci. "A shekara ta ɗari bayan saukar da mutane zuwa ƙasashe shida na ƙasa, su kuma Ururu suka gaje ƙasa ta farko, wato shekaru dubu ɗaya kenan da ɗari huɗu. Kaka na ya labarta min cewa harkar cinikin bayi ita ce Rukuni na farko da Ururu suka fara wanzarwa a dukkan doron ƙasa shidanan." Nan take Armad ya shiga bada labarin dukkan abinda ya sani akan harkar cinikin bayi tun daga asalinta, da zummar ko zaiji wani abu da bai sani ba daga Nusi. Hasken fitilar aci bal-bal yana tashi inda yake haskake jan kyallen dake ɗaure a gaban goshinsa yana kaɗawa akan iska. "Farko da Ururu suka bayyana suma suna cikin waɗanda suke shiga cikin gasar cinikin bayin. A wannan lokaci ta fara ne da wata gasa mai suna Jinzi, wadda acikinta kowacce ƙabila babba da ƙarama zasu kawo wani adadi na bayi a ƙarshen kowacce shekara, waɗanda za'a fafata akansu duk wanda yaci nasara daga ƙarshe, to shi za'a bawa kyautar dukkanin waɗannan bayi da kowacce ƙabila suka tara. "Saboda haka wannan ƙabila da taci nasara su zasu juya akalar kasuwar bayi a wannan shekara. "A haka wannan gasa ta Jinzi ta fara kafin daga bisani a maida sunanta Jinzidal bayanda Ururu suka koma doron ƙasa ta farko. "A tsahon sama da shekaru dubu da akai ana yin wannan gasa ta cinikin bayi, Ururu suna daga ƙasa ta farko suna zuba ido suga ko wani zai kawo mata tangarɗa. Wanda kuma da dama sun aikata hakan amma a yanzu babu zuri'arsu a ban ƙasa. Ururu sun riga sun gabatar dasu izuwa lahira. "Akwai manya-manyan sarakuna guda biyar wanda su suka fi kowa muƙami acikin wannan gasa. Waɗannan kuwa sune Sarki Hanibal na ƙasa ta uku da sarki Maikiro Abbas na ƙasar Maikironomada da sarki Deniz Ururu wanda ya zaɓi ya zauna a ƙasashen ƙasa shekaru dubu da suka wuce lokacin da zuriarsa ta ma'abota Ururu zasu koma ƙasa ta farko. Sai kuma Sarki Rafiya wanda akewa laƙabi da mai Izza dubu ɗari, sai kuma Sarki Bihanzin Mai dauwamammen sara. Nasan cewa waɗannan sarakuna biyar su su suke da iko akan duk wata Izza dake doron ƙasashen nan shida na ƙasa. "Kuma nasan cewa duk wanda ya taɓa cinikin bayi waɗannan Sarakuna sune zasu fara gamawa dashi kafin ma URURU SU SAUKA. To amma duk da haka bana cire ran watan watarana zan hana bautar da bil'adama da ake. Bari dai kawai yanzu ta rashin lafiyar mahaifiyata nake. Zuciyar tana dukan uku-uku ta kalli idanun Armad ta kuma tabbatar da cewa lallai abinda yake faɗa har cikin ransa yake, kuma babu wasa aciki. Babu yadda ta iya, haka tai ajiyar zuciya bayan dogon lokaci tana kallonsa. Kafin daga bisani ta girgiza kai gami da cewa; ''Muhimmin abindai anan shi ne, babu ruwanka da harkar cinikin bayi a yanzu, zaka shiga cikin fasahar Nontoch-teka, idan ka fito kuma zamu duba muga hanyar da tafi kamata ka nemo Tarifil fakta ko ka koma izuwa mahaifiyarka. ''Sabida haka a yanzu babu abinda zan iya akai sai dai kawai ka jira zuwa nan da kwana shida.'' Armad ya ɗago kai cikin murmushi, amma baice komai ba, inda yabarta taci gaba da jawabi, ''ni yanzu kamar yadda na gaya maka ina da buƙatar na shiga cikin kogon Asúlu, domin fuskantar wankin Izza saboda haye matakin jarabawar can da nayi za'a ƙaramin matsayi. ''A iyakacin lissafina bazan fi kwana biyar ba, komai daɗewa, Zuwa yamma zan shiga, amma a yanzu zanje na shirshirya, kuma da ana zuwa rakiya, to da ka rakani, amma ba'ayi, daga ni sai waɗanda na zaɓa daga cikin majalisa. ''Saboda haka muyi sallama kawai. Sai ka huta kuma na haɗaka da aminaina guda biyu Iliyásis da Cokali su nuna maka gari.'' Faɗar haka keda wuya kamar ta tuno wani abin dariya, sai ta fashe da dariya, gami da cewa, ''su na da kirki da kuma saurin sabo, nima tare muka shigo nan, amma bayan wani lokaci ALLAH yasa na wuce su matsayi. Ka kwantar da hankalinka a game dasu. ''Iliyásis baya magana sosai, amma yana da tunani mai ƙarfin gaske. Ka lura da duk abinda zaiyi zaka koyi abubuwa da dama. ''Shi kuma Cokali.....'' tuni dariya ta ƙara kwace mata daga faɗar sunan kawai. Da kyar ta ƙarasa da cewa, ''yana da ban dariya, amma duk da haka jarumi ne! Washe gari acikin garin Khan akan wata hanya data wuce ta cikin wasu gida je, waɗansu mutane uku ne suke tafiya. Dukkansu babu alamun baƙin ciki a tattare da zuƙatansu, sai dai ɗaya daga cikinsu wanda duk yaɗan fisu haske da kuma siranta fuskarsa acike take da fara'a sannan kuma bakinsa motsi kawai yake yana jawabi. Bayan wani lokaci ya buɗe baki yace, ''ni suna na Cokali!'' Sannan kuma ya nuna ɗayan dake ɗaya ɓangaren, ya ce, ''wannan kuma shi ne, Iliyásis.'' Yayinda yake maganar idanunsa nakan kan saurayin da ke tsakiyarsu, wanda ya kasance mai matsakaicin jiki da kyakkyawar fuska. Fatarsa wankan tarwaɗa ce, sannan kuma saboda tsayinsa kai kace ya haura shekaru ashirin da haiwuwa. Idanunsa nada haske sosai, kuma idan baka kula ba sosai sai kace har haske suke fitarwa. Yana da ɗan ƙaramin saje daya ƙara inganta kamalarsa, sannan kuma idan ka haɗa da rigar dake jikinsa wadda ta kasance ƴar shara, ta yadda cikakken dantsensa ya fito sosai, ga kuma doguwar takobin dake rataye a kafaɗarsa, da kuma jan kyallen daya ɗaure kansa wanda ya saje da farin wandon dake jikinsa da kuma farar rigarsa, sai kaga lallai yana fitar da kamalar jarumai a tattare dashi. Wannan saurayi dake tsakiyarsu ba wani bane ba illa Armad Wilbafos, wanda kwanakin baya kaɗan a wani ɗan ƙauye aka laƙaba masa Magajin-Wilbafos. Sunan da ya rasa murna zaiyi saboda shi ko kuma baƙin ciki. Kafin Cokali ya ɗauke idonsa daga kan Armad sai ya tambayeshi, ''idan nace maka ɗana ba matsala?'' Idanunsa babu ko alamun wasa aciki, hasalima cike suke da soyayar ɗa da uba, a lokacin da yake tambayar. Tunda suka haɗu acikin gidan da aka sauki Armad, bayanda suka ƙara zuwa wajensa, ya ƙare musu kallo, kuma Armad ya tabbatar cewa acikinsu ukun Cokali ne ƙarami. Sannan kuma ɗaya daga cikin su Iliyásis da Nusi ya zama babba. Amma to ita kanta Nusi baza tafi ashirin ba. Sabida haka daya ji wannan tambaya, sai kawai ya fashe da dariya, kuma ya tuna da abinda ta gaya masa akan cewa Cokali ɗan cafta ne kawai. To amma yana niyyar amsawa masa tambayar da yayi sai kawai idanunsa yakai kan wani zabgegen rami daya gifta ta inda zasu wuce an ɗan kewaye shi da ƙarafa. Yana kallon cikinsa yaji wata irin Izza mai tsananin gaske, wadda tasa yaji tamkar idanunsa zasu fashe daga kallonta kurum. Babu abinda yake iya tunawa daya gani acikin ramin face baƙi da duhu da kuma wani tiriri mai alamun mutuwa da kanta. Amma dai abinda ya tabbatar shi ne lallai yana da matuƙar zurfin gaske, hasalima idan akace bashi da ƙarshe baza ai musu ba. Nan take ya ɗaga ido inda ya ƙara hango irin wannan rami a gabansu, saboda haka cikin zafin nama ya juya domin tambayarsu meke faruwa a wajen, domin lallai yaji gashin jikinsa ya tashi, ruhinsa ya fara zafi, kuma tambarin Miyurar dake goshinsa ya fara haske da kansa ba tare da ya taɓa shi ba. Amma kafin yace wani abu yaji maganarsu; ''Ba'a kallon cikin waɗannan rami ka, lallai ka kiyaye, saboda har halaka zaka iya yi idan kalli cikin manya daga ciki. Kaga har can nesa duk sune. Danma an kewaye manyan ciki da bangon sihiri. Suma waɗannan ɗin da a kewaye suke, amma a hankali a hankali suka cinye bangwayen da aka kewaye su dashi. ''Ramika ne da Bihanzi yayi da takobinsa wato Dauwamammen Sara. ''Shekaru da dama da suka wuce, a lokacinda ya fara shigowa wannan gari kuma ya zama Al'yaya. ''Da dama daga cikin ƴan majalisun wannan gari a wannan lokaci basu yarda ba, saboda sun san cewa idan suka barshi ya girma zasu iya rasa muƙaminsu. ''Saboda haka a ɓoye suka saka a hallaka shi kwanaki kaɗan bayan shigowarsa! ''A sakamakon haka suka fafata, kuma a ƙarshe ba komai ya faru ba illa waɗannan rami ka da kake gani. ''Ya dai bayyana cewa duk waɗanda Bihanzin ya jiwa ciwo a wannan rana basu ƙara kwana da yawa ba suka mutu. ''Ba dan komai ba sai cewa duk ciwon da yayi da takobinsa, to fa bazai taɓa warkewa ba har abada!! ''Kai bama jikin mutun ba, hatta ƙasa, ko kuma duk wani abu mara rai, domin duk waɗannan ramika da kake gani sakamakon saran takobin Bihanzin ne daya sari ƙasa a lokacin. ''Bayan tafiyar shugaban babu yadda sabon shugaban majalisa baiyi ba domin rufe waɗannan ramika ba, amma ina, ga sunan har yanzu kuma har abada, an rasa yadda za'ai dasu, sai dai kawai a kewaye waɗanda za'a iya. Yau shekaru arba'in da biyu kenan!!! "Musamman mutane suke yiwo tattaki suzo suga wannan ciwo da aka jiwa ƙasa, da dama shiɗewa suke saboda irin girman Izzar dake cikinsa. "Wanda daga haka aka koma ambatonsa da, Bihanzin mai Dauwamammen Sara!" Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 25: Fasahar Marubutan Farko Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Acikin garin Khan haka a kwana a tashi kwana uku suka wuce. Armad yana ta tunanin irin abubuwan daya gani a lokutan da suke zazzaga gari dasu Cokali, kuma babban abinda ya kasa cirewa a ransa shi ne sunan Bihanzin mai dauwamammen ciwo! To da yake dama yana zaune ne acikin ɗaki a wannan lokaci, kawai saiya tashi ya ɗauki alƙalami ya zaro ɗaya daga cikin ganyayyakin da aka kawo masa ko zaiyi rubuta, ya rubuta sunan Bihanzin da manyan baƙi da yaren Alderiya(Aldurish). Haka ya kwana yana tunane-tunane, bayanda gari ya waye, ya gama kintsawa kenan saiga Iliyásis ya bayyana a gabansa da labarin maza-maza ya kamata su isa wajen Non-toch-teka, domin jiya da daddare saƙo ya iso daga sarki cewa an rage kwana uku akan yadda aka tsara za'a buɗe wajen, saboda wani dalili da ba'a bayyana ba. A azalzale haka Armad ya ƙarasa shiri suka fice tare da Iliyásis. Har a lokacin da suka fita rana bata ɗaga ba, kuma iskar alfijir tana nan tana kaɗawa, tana kaɗa maɗaurin kan Armad da kuma sajensa, yanayin da ya ƙara masa kyau matuƙa. Basu ɗauki lokaci ba suka iso wajen da zasu. Tun daga nesa Armad ya hango wani katafaren gini, wanda iyakacin hangenka, dama da hauni, sama da ƙasa duk shi ne, kuma baka iya ganin ƙarshensa. Iliyásis ya nuna masa da hannu cewa acikin wancan ginin abinda muke nema yake. Suna isa wajen, akwai mutane ƴan tsiraru waɗanda da dama kallo ɗaya kawai sukai musu suka ɗauke kai, saboda basu sansu ba sannan kuma tuni labari ya gama bazuwa cikin garin cewa yau za'a fara shiga Non-tochteka, saboda haka ba abin mamaki bane ba kowa ma ya bayyana a wajen. Amma daga lokacinda suka fara jan hankalin saura shi ne, daga sanda suka zarce harya zuwa ɗaya daga ƙofa goma dake gaban ginin. Sannan kuma nan take Iliyásis ya miƙa wata takarda inda mai gadin ya karɓa kuma ya buga mata sheda, sannan ya buɗe musu ƙofa suka wuce. Tun daga wannan lokaci ƙus-ƙus ya fara tashi, su na cewa, ''kaɗai mai iya shiga a wannan lokaci sai dai mai shedar majalisar! ''To su waye waɗancan mutun biyu?'' Haka dai suka ci gaba ƙus-ƙus a tsakaninsu a yayinda jama'a suke ta ƙara zuwa. Su na shiga ciki, mamaki ya ƙara cika zuciyar Armad, saboda abinda ya gani, yayi matuƙar saɓawa abinda yai tsammani. Domin shi a tunaninsa wani ginin ko kuma dai wani abun zai ƙara gani, amma bisa mamaki bai ga komai ba. wato dai a taƙaice babu komai sai fili fetal. Sannan kuma kamar inda Armad ya gani a lokacin da yake saukowa daga doron ƙasa ta uku, shi ma wannan waje komai launinsa iri ɗaya ne. Hatta ƙasar wajen da samaniya. Sai dai a wannan lokaci maimakon shuɗaye kamar na wancan lokaci, waɗannan farare ne! Duniyar komai fari fat kamar farin kitse. Babu kowa saisu

Chapter 12 of 33