Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
"Eh koda na mutu! Baka da labarin akwai wasu Rauhanan aljanu goma da suka yaudari Hidaya a shekarar 1801BA kuma suka sha guba suka mutu kafin ta kama su. Amma Hidaya ta kira taron aljanu tasa aka tashe su sannan ta ƙare kashesu ta mummunar hanya. Kasan sunan da suke gayawa Hidaya a tsakanin aljanu?" Idan Armad yana jin irin waɗannan maganganun a game da Hidaya sai yaji kamar ba yayarsa ba daya sani. Yai murmushi ganin yadda fuskar Babara ta fara canjawa, "Indai kana tare dani kada kaji komai, bazan gaya mata ba. Amma wanne suna suke gaya mata?" Wata dariyar mugunta tazo gefen fuskar Armad, lallai ya samo lagon Babara tunda dai ya gano abinda yake jin tsoro. "Ka ƙyale wannan sunan, idan kun haɗu ta gaya maka da kanta." Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 65: kasa bakwai Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Haka dai Armad da Babara suka ci gaba da tafiya sannu a hankali har zuwa faɗuwar rana. Mafi yawancin hirar tasu Babara ne yake yiwa Armad tambayoyi akan abubuwan da suka faru dashi a yayin neman Tarifil fakta. A dai-dai wannan lokaci ne suka fara hangen ƙatoton bangon ruwan nan wanda akewa laƙabi da bangon arewa. Babara ya tsaya tare da neman waje ya zauna a ƙasan wata bishiya. "Nayi wa kakanka Zaikid alƙawari zan koya maka yadda zaka sarrafa idanuwanka ka taimaki mahaifiyarka, amma daga nan dani dakai zamu yi hannun riga. Saboda haka har zuwa wannan lokaci, Zaikid ya barmin amanarka a matsayin ɗalibi da malaminsa. Zanyi zaton ka bani irin girmamawar da kake bawa Zaikid a yayin da nake koyar dakai." Armad yayi murmushi. Dama dai shi Armad ba mutun ne mai raina manya ba, kuma koda Babara bai faɗa ba bashi da niyyar raina shi. Babara ya ƙara duban Armad, "Mai ka sani game da tsarin ƙasa bakwai? Ina so kayimin bayani dalla-dalla." Armad ya ɗanyi shiru yana kokwanton wacce alaƙa wannan tambaya take dashi akan abinda Babara zai koya masa, amma daga bisani ya yanke shawara yayi wa Babara biyayya kawai kada yace ya rainashi. "Ƙasashe bakwai sune kaɗai wajen da bil adama zai iya rayuwa aciki. Nasan waɗannan ƙasashe a jere suke ɗaya a saman ɗaya; daga doron ƙasa ta farko zuwa na bakwai. Nisan dake tsakanin wannan ƙasashe bazai misaltu ba, kuma haka ne yasa ƙasa ɗaya bata taɓa iya hangen wata ƙasar. Hasalima wata ƙasar baza ta taɓa sanin samuwar wata ƙasar ba idan banda kasancewar bangon ruwa wanda ya haɗe dukkanin wannan ƙasashe. Shi dai wannan bangon ruwa ya sakko ne tun daga doron ƙasa na farko har zuwa na bakwai, kuma tun a farkon lokaci yake tsaye a yadda yake bai daina zuba ba. Da dama daga cikin masana sunyi rubutu akan wannan ruwa da dalilin da yasa yake ta zuba amma yaƙi ƙarewa, sannan kuma wajen da yake zubar yaƙi cika da ruwa yayi ambaliya, amma har zuwa wannan lokaci amsar kawai da suka samo ita ce 'TSAFI'. Wato dai kowa ya yadda tsafi ne ke riƙe da wannan katafaren gangar ruwa wanda ake kira da BANGO." Armad yaja numfashi sannan shima ya nemi waje ya zauna a gefen Babara kafin daga bisani yaci gaba da bayani, "Ada bansan mai yasa ake cewa wannan ruwa bango ba, amma lokaci na farko dana fara ganinsa shi ne shekarar dana zo wajenka. Bayanda na tafi na haɗu dasu Nostajiya naga yadda ake ganin wannan gangar ruwa ya shafe ko'ina sannan yana ambaliya a tsaye cikin ƙasaita tamkar tamkar wani bangon duniya wanda bazai taɓa faɗuwa ba. Nan take na gane dalilin da yasa ake ce masa Bango. A sannanne na gano cewa ashe akwai Bango ɗaya a ɓangaren gudu ɗaya kuma a arewa: wadanda ake kira da bangon kudu da bangon arewa. Waɗannan bangwaye guda biyu sune suka datsa kowacce doron-ƙasa acikin ƙasashen nan guda bakwai izuwa gida uku: ɓarin arewa, ɓarin kudu, da kuma ɓarin tsakiya wanda shi ake kira Ikwatora. "Kowanne ɓari duniya ce mai zaman kanta wanda take ƙunshe da mutane miliyoyi. A kowanne lokaci na shekara ɓarin kudu suna da sanyi sosai kuna a sau da dama har ƙanƙara ke zuba, amma ɓarin arewa zafi ne dasu kaf shekara. Kakana Zaikid ya gayamin ɓarin Ikwatora sune suke da sanyi da zafi: rabin shekara ai zafi rabi kuna ayi ƙanƙara. "Akwai hanyoyi biyu kacal da bil adama suke iya yin safara daga wata doron ƙasa zuwa wata. Hanya ta farko ita ake kira da Eycigan, hanya ta biyu kuma hanyar jiragen ruwa. Eycigan kalma ce ta yaren Aldurish wadda take nufin gida. Kuma haka abin yake, Eycigan tsarin gidaje ne guda goma sha huɗu wanda aka gina su a kowacce tasha na ɗaya daga cikin doron ƙasashen nan bakwai. Babu wanda yasan yadda aka gina su ko kuma yadda suke aiki, amma indai ka biya kuɗinka ka shiga ciki to zaka bayyana a inda kake so. Bayanda ka buɗe min wannan ƙofa na shiga a shekarun baya na gano cewa Eycigan tana kama da irin wannan ƙofofi na tsafi da ake yawo ta ciki. Nostaljiya ma ta buɗe min wata a ƴan kwanakin baya. "Hanya ta biyu ita ce amfani da jiragen ruwa ayi tafiya daga ƙasa zuwa akan Bango. Amma duk da cewa hanyar Eycigan nada matuƙar tsada mutane sunfi amfani da ita saboda sharrin ƴan fashin ruwa da Dordor masu cin naman mutane da kuma lokaci da ake ɗauka a jiragen." Armad yai shiru yana jira Babara ya jinjina masa, domin a ganinsa babu wani abu daya shafi fasalin ƙasa bakwai da bai faɗa ba, amma Babara yai masa irin kallon nan mai nuna ana so kaci gaba. Armad haɗe gira, yaya za'a ce da saura. Babara ya kyaɗa kai, "Eh... bayaninka yayi to amma baka faɗa min yadda ake safara daga wani ɓarin zuwa wani ba akan doron ƙasa ɗaya. Wato dai ina so naji yadda zaka iya ketawa daga ɓarin arewa zuwa ikwatora zuwa kuma ɓarin kudu duk akan doron ƙasa ɗaya? Kai sani cewa hatta gidajen Eycigan da ƙofofin daka ga muna buɗewa basa iya kai mutun daga wani shashi zuwa wani." Nan take Armad gwale ido cikin mamaki. Bai ma taɓa tsayawa yayi wa kansa wannan tamabaya ba. Duk a tunanin Armad tafiya daga doron wata ƙasa zuwa wata shi ne mai wahala, amma tafiya daga wani sashi zuwa wani ba zaiyi wahala ba. Armad ya gurgiza kai, "Ban sani ba gaskiya." Babara yayi murmushi, "To wannan shi ne dalilin da ya na tambaye ka bayani akan doron ƙasa bakwai, domin najin ko kasan irin haɗarin da zaka shiga nan bada dadewa ba." "Hatsarin dazan shiga kuma?" Armad ya kasa yin shiru. Babara yayi kamar baiji tambayar Armad ba yaci gaba da maganarsa, "Ketawa ta cikin Bango wani babban abu ne wanda hatta manyan ma'abota Izza suke jin tsoro. Kai sani cewa Bangon arewa dana kudu suna da girma sama da yadda kake zato ko tsammani, kuma acikin su akwai sharrika wanda kaɗan ne daga cikin biladama suka taɓa gani ko ji. Ina daga cikin wanda suka yadda cewa duniyar dake cikin Bango ita ce waje mafi hatsari a duniya. Dani dakai zamuyi tafiya acikin wannan waje, kuma aciki zan koya maka yadda zaka sarrafa idanuwanka. Kai sani cewa sau ɗaya kacal na taɓa iya keta rabin wannan waje. Lallai dani dakai duk zamu iya halaka, amma na riga nayi wa kakanka alƙawari zan koya maka yadda zaka sarrafa idanuwa ka, kuma lallai mu ƴan ƙabilar Bayajidda bama saɓa alƙawarinmu." _______ 1) Na ɗan samu free time, so zaku ga post ya ƙaru amma fa ba cewa nayi zai ɗore ba. Saboda kada kuga daga baya mun koma yadda muke yi da. 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu akan http://hausaebooks.cf Ko kuma shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 67: Bango Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ____ Armad ya yamutse fuska domin tuni ya fara gajiya da aikin da Babara ya bashi sama da sa'a uku da suka wuce. Tun bayan da Armad ya amince zai fara koyon yadda zai sarrafa idanuwansa a wajen Babara sai Babara ya fito da wani ƙaton dutse daga aljihunsa ya sa Armad ya ɗora hannunsa na dama akai. Fuskar dutsen a shafe take, kuma launinsa fari ne fat. Yana da faɗin da mutun uku zasu iya ɗora tafin hannunsu saboda haka ba matsalar Armad bace wajen da zai ɗora hannunsa, matsalarsa ita ce hannunsa ya ƙage saboda daɗewa, sannan kuma ga wani koren haske da yake ta walwali daga fuskar dutsen yana haske masa ido. Armad yana ji tamkar wannan dutsen yana zuƙar wani abu a jikinsa wanda baisan meye ba. Hasalima Babara yayi bacci tun sa'a ɗaya data wuce, amma kafin yai bacci saida ya jaddadawa Armad kashedin kada ya sake ya ɗauke hannunsa daga kan dutsen har sai dutsen ya daina haske. Babban abin haushin kuma baima gayawa Armad amfanin dutsen ba. Armad na gabda kwalawa Babara kira ya tashe shi ya gaya masa ya gaji sai wannan dutse ya daina wannan walwalin haske da yake. Armad yai ajiyar zuciya sannan ya cire hannunsa. Yana niyyar tashin Babara sai idonsa yakai ga wasu ƙananun rubutu akan dutsen, wanda ba daban sunansa daya gani a farkon rubutun ba da ba wani abu bane. Amma kalmar farko a jerin rubutun sunan sa ne. A dai-dai wannan lokaci ne yaji muryar Babara a kunnensa, "Miƙo muga Tsarin-runinka." "Tsarin-ruhi?" Armad ya ɗaga gira cikin mamaki. Yasan meye Tsarin-ruhi amma bai taɓa ganin wannan dutse ba. Akan dutsen an rubuta:: Suna: Armad Ƙabila: Wilbafos Aljani: ?? Izza: Shekaru 1000 Fasaha: Kabanshisu, Wasu-wasi, Hisabi, Ƙawanya-walƙiya, Sanyin-babban-sihiri, Ɗorawa, Wilbafosiyan-siwod-dans, Al'yaya. Babara yayi murmushi gami da girgiza kai, "Lallai ka koyi abubuwa da dama a wajen Zaikid da kuma a yayin tafiyarka ta neman Tarifil-fakta. Idan na fahimci abinda wannan dutse yake faɗa, kakanka Zaikid shi ne wanda ya farkar da aljaninka da kuma Izzarka, wanda shi ne mataki na farko da kowanne sadauki ma'aboci Izza yake fara takawa. Sannan kuma daga nan ya fara koya maka yadda zaka sarrafa fasahar walƙiya. "Daga bisani ya koyar dakai hare-hare wanda suke amfani da fasahar ka ta walƙiya da kuma takobi. Ɗaya daga cikin irin wannan hare-hare shi ne harinka na Wasu-wasi. Sai dai matsalar wannan hari na wasu-wasi baka iya aiwatar dashi akan mutun indai Izzarka bata fi tasa ba. "Zaikid ya koyar dakai wasu daga cikin manyan ɗalasimai irinsu Kabanshisu, wanda shima sau ɗaya kacal zaka iya amfani dashi a shekara. "Sannan kuma ya koya maka Wilbafosiyan-siwod-dans wanda baka kware akai ba, kuma duk sanda kai amfani dashi sai hankalinka ya gushe. Hasalima ka gayamin lokaci na ƙarshe dakai amfani dashi ka rasa shekaru biyu na rayuwarka ba tare da kasan yadda akai ba. "Sannan kuma bayan ka sami Takobin Wilbafos daga Hidaya ka fara koyar fasahar Ɗorawa wadda take baka dama ka wanzarda Nauyi akan abokin gabarka ka hanashi motsi. Sai dai ita ma wannan fasaha tana zuƙe shekarunka na rayuwa wanda haka ne yasa mahaifiyarka ta hanaka amfani da ita. "Kafin ka rasa Miyurarka kana iya amfani da ita ka ƙarawa kanka Izza a lokacin da kake buƙata. Sannan kuma Miyurar taka ta baka matsayin Magajin-wilbafos. "Ka kuma samu matsayin Al'yaya a ƙofar garin Maikironomada, sannan kuma a gasar Non-toch-teka ka samo Littafin-takobi. "Ina ganin wannan sune dukkanin abubuwan da kake dasu a yanzu idan akwai abinda na rage kai magana." Armad yai shiru kafin daga bisani ya girgiza kai, "A'a, komai ka faɗa." Babara ya kyaɗa kai tare da miƙewa, "Lokaci yayi da zamu shiga Bango, mu fara abinda ya kawo mu." Nan take su biyu suka nufi hanya izuwa wannan katafaren bangon ruwa wanda yake ta kwaranya tamkar bazai taɓa tsayawa ba. Lallai wannan bangon ruwa yana da ban al'ajabi, musamman duba ga yadda jirage suke hawa kansa su tsaya cak suyi tafiya ba tare sun faɗi ba. Armad ya daɗe yana mamakin yadda za'ace jirgi yana tafiya akan Bangon, ga dukkan alamu yau zai ganewa idonsa dalili. Suna isowa dai-dai gaɓar inda ƙasa ta yanke Armad yaga tamkar ansa takobi an datsa ƙasar gida biyu tayadda Bangon ruwan yayi katanga a gaba kaɗan da inda ƙasar ta ƙare. Armad ya leƙa tsakanin ruwan da inda ƙasar ta yanke, inda wani ƙasaitaccen duhu yayi masa sallama. Babara ya ɗakko Ayrid mai mataki na biyar daga aljihunsa inda ya juyar dashi izuwa ɗan ƙaramin kwale- kwale. Ba jimawa Babara ya jada baya yai tsalle ya tsallake ramin dake tsakanin Bangon da doron ƙasar da suke kai. Abin mamaki yana dira akan ruwan ya tsaya cak da ƙafarsa. Armad yayi tunani Babara zai faɗa ƙasa cikin ramin ko kuma ya nutse amma sai gashi ya tsaya cak akan ruwan tamkar wanda ke kan doron ƙasa. Hankali kwance Babara ya ajiye kwale-kwalen ya shiga ciki sannan ya ɗagowa Armad hannu da niyyar ya taho. Hankalin Armad bai yadda da abinda ke faruwa ba, amma babu yadda zaiyi haka yai tsalle izuwa cikin kwale- kwalen nan. Yana dira aciki kwale-kwalen ya ɗanyi ƙasa alamun mutun ya shiga ciki, amma dai suna nan a tsaye cak ba suyi gaba ba kuma basu nutse ba. Babara ƴa dubi fuskar Armad wadda ke cike da mamaki yai murmushi, sannan kamar yasan mai Armad yake tunani ya fara yi masa bayani, "Kai sani cewa Bango tamkar doron ƙasa yake, kuma daga sanda kahau kansa babu zancen ace zaka faɗa ƙasa domin kuwa tamkar kana kan wata doron ƙasar ne. Da sannu zaka gane mai nake nufi. To amma yanzu cikin bangon zamu shiga, saboda haka....." Babara ya zaro sandarsa ta Izza daga inda ya ɗaure ta a bayansa ya daki kan ruwan dai-dai ƙasan kwale-kwalensu. Abu kamar almara saiga ruwan nan ya fara darewa kwale-kwalen nasu kuma yana shigewa ciki. Armad ya miƙa hannu ya maƙale cikin kwale-kwalen domin yana jin tamkar zai faɗa cikin ruwan a kowanne lokaci, amma hakan bai faru. Ba jimawa Armad ya tsinci kansu acikin tsakiyar wannan bangon kewaye da ruwa amma ruwa baya taɓa su. Yana jin wani sanyi yana ratsa jikinsa tamkar wanda aka saka masa tubalin ƙanƙara acikin cikinsa. Gashin jikinsa ya miƙe zuciyarsa ta fara tunane-tunane. Ana samun matsala wannan ruwa zai haɗiye su, kuma lallai sai sun halaka. Babara dai yaga halinda Armad yake ciki amma kawai murmushi yayi baice komai ba. Bayan kimanin daƙiƙa ɗari suna tafiya sai kwale-kwalen ya fara gudu, lamarinda yasa Armad yin sauri ya zauna ya riƙe kefensa ƙam ya kuma rufe idonsa. Kwatsam ana cikin haka sai jiyayi tamkar sun faɗa cikin wani ƙaton rami, lamarinda yasa ba shiri ya buɗe idonsa. Ai kuwa yai arba da kwale-kwalensu yana faɗowa ƙasa. Ya waiwaya bayansa yaga wannan Bango da kuma wannan ƴar ƙofa da suka shigo ta ciki. Nan take ya gane cewa lallai kodai cikin tsakiyar wannan Bangon ruwa suka shigo ko kuma bayansa. Bayan sun shafe sama da daƙiƙa hamsin suna faɗowa Armad ya tafa hannunsa ya kirawo duk wata fasaha da yake da ita domin kare kansa, domin yasan koma ina zasu faɗo to lallai yana da nisan gaske kuma jikinsu zai iya tarwatsewa. Banda kuma cewa bai masan mai zasu tarar ba. 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 68: Tarihin nusi Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos *Yanzu zamu ɗan ajiye Armad a gefe mu leƙa muga halinda Nusi da Ikenga da kuma Miyurar Armad suke ciki* ------- Garin Khan Shekarar 1835 Bayan Amri ** Acikin babbar kasuwar dake wannan gari wata yarinya ce kimanin ƴar shekaru shida sanye da baƙaƙen kaya wanda kana ganinsu kasan sunji jiki. Tana tafiya da kyar tana iya ƙoƙarinta wajen kaucewa mutane. Tana da duhun fata sannan fuskarta nada tsayi madaidaici. Idanunta na cike da yarinta amma kuma haɗe da rashin tsoro. Tasan cewa bata da kowa a dai-dai wannan lokaci, kuma hanya ɗaya da zata rayu shi ne idan tayi juriya da jarumta ta tsaya da ƙafafunta. Domin kuwa wannan gari ba garin su bane, kuma lallai tayi nesa da gida. Abu ɗaya kacal da wannan yarinya take iya tunowa a game da iyayenta shi ne rabuwarsu ta ƙarshe, da kuma alƙawarin da mahaifin ta yayi mata na cewa bazai huta ba saiya kaita gida wajen mahaifiyarta. Sai dai kuma kash, wannan yarinya tasan cewa a matsayin ta na ƴar ƙabilar Djinn komawa gida a wajenta abu ne mai wahala. Domin kuwa garinsu mai suna Shaniza an ƙulle ƙofofinsa sama da shekaru ɗari da suka gabata, sannan kuma an katange bangwayensa daga dukkan halittu, mutun ko aljan ko dordor. Amma abin mamaki wannan yarinya tana jin yaƙini zata koma gida watarana. Kuma lallai baza ta mutu ba sai taga mahaifiyarta wadda ke cikin garin Shaniza. Sunan wannan yarinya Nusi, Nusi Djinn. Wata biyar kenan da babanta ya barta a hannun abokinsa domin ya kula da ita a yayinda shi kuma ya tafi domin gamuwa da wata tawaga, amma ƙaddara ta ratsa, sai gawarsa aka dawo da ita. Koda abokin baban nata ya tabbata a yanzu babu wani abu da zai samu saiya kore ta daga gidansa, lamarinda yasa watanta uku kenan cir tana rayuwa akan titi. Abincin da zata ci ma wahala yake mata. Sauƙi ɗaya kacal da take samu shi ne abokanta guda biyu wato Iliyasis da Cokali, wanda suma yara ne sa'anninta wanda suke bin titi a sakamakon siyar da iyayensu da akai a cinikin bayi na wannan shekara. Nusi na tafe kanta na nazarin mutanen dake gefenta. Daga ganin yadda take ɓoye fuska kasan akwai wanda take gujewa. Ba jimawa tasha wata kwana inda babu mutane da yawa. Tana shan kwanar ta fara gudu inda ta ƙara shan wata kwanar dai-dai gefen wata bola inda babu mutane da yawa. Da yake magariba ce kuma duhu ƴaɗan fara yi da kyar ta iya hango wasu yara dake laɓe a bayan wani ƙaton kwanon zuba shara dake gaba da ita. Nan da nan ta isa wajen yaren, inda suka ƙura mata ido cikin tsammani suna jira suji mai zata ce. Ita kuwa Nusi sai ta canja fuska zuwa kalar tausayi, lamarinda yasa nan take jikin waɗannan yara yayi sanyi. Koda taga haka saita fashe da dariya tana cewa, "Wululu... Tsokanarku nake na samo..." Wannan yara dai ba wasu bane illa Iliyasis da Cokali. Dukkaninsu suna yara, Cokali irin yaran nan me masu ƙiba da kumburarriyar fuska mai ɗauke da kalar tsoro, amma Iliyasis siriri ne mai tsayi kuma yafi Nusi haske sai dai kuma shima Cokali ya fishi haske. Nusi ta zira hannu acikin tsohuwar rigarta ta futo da ƴar jaka mai ƙunshe da kuɗaɗen Ayrid. Suna ganin haka sukai tsalle suka rungume Nusi cikin farin ciki, haƙarsu ta cimma ruwa. Nusi ta zira hannu a cikin jakar ta lissafa Ayrid ɗai-ɗai har guda ashirin ta miƙawa Iliyasis. Sannan ta ƙara miƙawa na Cokali Ayrid ashirin. Sannan itama ta ɗebi ashirin. Amma duk da haka jakar na nan cike da Ayrid ko rabi basu ɗiba ba. "Ƴar uwa mai za'ai da ragowar?" Suka tambaye ta cikin mamaki. "Mayar masa zanyi. Dama aikin da mukai masa na wata biyu akan kuɗi Ayrid ashirin-ashirin ne. Tunda yaƙi biyanmu ba laife bane idan muka kwaci kuɗinmu, amma bai kamata mu ɗebi sama da haka ba." Daga ganin fuskar Iliyasis da Cokali basu yadda da wannan mataki ba, amma tunda ita ta ɗakko kuɗin babu yadda zasu yi. Iliyasis ya buɗe baki ya ce, "To ta yaya zaki mayar masa? Kinsan za'a iya kama ki fa tunda yanzu na tabbatar yasan kuɗinsa baya nan, kina mayarwa zai gane ke kika ɗauka." Nusi ta kyaɗa kai, "Eh haka ne, amma dai duk da haka sai an mayar masa. Wataƙila amma sai gobe. Yanzu muje mu ci abinci mu siyi kayan sawa mu kuma nemi wajen kwana. Wataƙila zamu samu ko ɗaki ɗaya ne da kuɗinmu." Su ukun suka juya suka nufi hanya domin suje su ci abinci. Da wannan kuɗi nasu suka samu suka siyi abinci kuma suka kama wajen kwana. Sun kwana cikin farin ciki a wannan rana, ko ba komai sun kwana acikin ɗaki sannan kuma cikinsu a cike da abinci. ------ Washe gari bayan isha duhu ya fara yi, ƙasaitaccen ɗan kasuwarnan mai suna Ɗan-darbejiya yana tafe zai koma gida bayan rufe shaguna. A kewaye dashi akwai zaratan samari uku majiya ƙarfi waɗanda aikinsu kawai su kare shi. Fuskar Ɗan-darbejiya na rufe da ƙasumba da gemu amma hakan bai hana baƙin cikin dake lulluɓe da ita bayyana ba. Kuma zaka fuskanci lallai Ɗan-darbejiya yana da dalilin yin baƙin cikin idan ka lura cewa jiyan nan yayi asarar dukkan ribar da ya samu ta gaba ɗaya watan. Babban abinda yake ciwa Ɗan-darbejiya tuwo a kwarya shi ne bai masan yadda akai kuɗin suka ɓace ba. A iya tunaninsa bai taɓa yarda ko da Ayrid ɗaya ba a tsahon rayuwarsa. Hasalima saboda san kuɗi na Ɗan-darbejiya yana da shaguna sama da goma amma yana tafiya yana kallon hanya ko zaiga wani ya yadda kuɗinsa ya tsinta. A cewar Ɗan-darbejiya duk wanda ya yarda kuɗi baya so ne. Abu ne sananne duk wanda yayi wa Ɗan-darbejiya aiki to da wuya kuɗinsa su fito, hakan nema yasa duk ƴan kwadagon kasuwar suke gujewa yin harka dashi. Kuma dalilin da yasa Ɗan-darbejiya yake saka yara ƙananu aiki domin kada ya biya kuɗi da yawa. Kwanakin baya ya saka Nusi da Iliyasis da Cokali aiki. Kuma daga bisani ya hanasu kuɗin. Su Nusi sukai jele har suka gaji suka daina zuwa. Amma kwanaki huɗu bayan sun ɗauke ƙafa Ɗan-darbejiya ya wayi gari aljihunsa da yake saka kuɗaɗensa ya yage kuma kuɗinsa sun faɗi a tsakiyar kasuwar. Ɗan-darbejiya yai rigimarsa ya gaji, amma babu wanda zai kama a tsakiyar kasuwa. Hasalima da dama suna tunanin Ɗan-darbejiya haɗa labarin kawai yayi domin kada ya biya bashin da ake binsa. To abinka da yarinta, tunanin yara ƴan shekara shida zuwa takwas bashi da ƙarfi. Kawai Ɗan-darbejiya yana tafiya yana saƙe-saƙe a ransa saiga ƴar sakarsa da yake ajiye kuɗi ta yiwo tsalle daga sama ta faɗi a gabansa. Ai kuwa tunma kafin yayi magana ƙarti biyun dake kewaye dashi suka rankaya a guje zuwa wajen da wannan jaka ta taso. Su Nusi dai sune suka cilla wannan jaka da danƙo, kuma suna cilla ta suka rankaya a guje suka sha kwana. Amma suna cikin gudu saiga ɗaya daga cikin ƙartin ya bayyana a gabansu, lamarinda yasa suka juya da gudu, amma suna juyawa suka iske ɗaya ƙaton tsaye a bayansu an saka su a tsakiya. Ƙaton gardin dake gabansu yai dariya gami da kyaɗa, "Hahaha.... Nusi, Iliyasis, Cokali, dama na gayawa oga kune kuka saci kuɗin nan yaƙi yadda." Na bayan yai wata dariyar mugunta tare da cewa, "Hukunci sata kisa." *** 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 69: Tarihin nusi 2 Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ------ Dukkanin wannan ƙarti biyu dake kewaye dasu Nusi Izzarsu akan shekaru casa'in da tara take. Na gaban ya taka a hankali ya isa gaban su Nusi, a yayinda su kuma suke ta janyewa suna ƙara takurewa a tsakiya cikin tsoro. Gaba zaki baya damisa. Yana isa saitin Nusi ya zaro wuƙa samfurin zabira, sannan ya finciko Nusi yana cewa, "A fuskarka zan rubuta miki ɓarauniya, kinga daga yau koda oga yaji tausayinku ya ce kada a kasheku nayi miki sheda." Babu abinda Nusi take sai karkarwa fuska cike da tsoro, amma wannan sadauki ko a jikinsa, babu ko alamun wasa ko tausayi a tattare dashi. Kana ganin yadda ya ɗaga wuƙar kasan lallai bashi da niyyar tsayawa. Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne komai dake wannan waje ya tsaya cak tamkar wanda aka tsayar da lokaci. Wannan sadaukai biyu dake neman halaka su Nusi suka ƙame ƙam, idan ka kalli wannan sadauki mai wuƙa a hannunsa zaka ganshi tsaye da wuƙa riƙe akan iska tamkar hoto. Na bayan shima ya ƙame a dai-dai inda yake. Da Nusi da Iliyasis da Cokali duk ba wanda yasan inda kansa yake. Ana cikin haka wannan sadaukai biyu tare da shugabansu, Ɗan-darbejiya, suka fara aman jini baƙi-ƙirin. Kan kace meye wannan tuni sun isa lahira. Duk abinda ke faruwa su Nusi basu san me ake ciki ba. Kuma abu na gaba da suka gani shi ne bayyanarsu acikin wani katafaren gida mai yawan bishiyu da sanyin ni'ima. Kuyangi da sauran bayi suna ta kai-komo acikin hidima. Idan da Armad yana nan da kallo ɗaya kacal zai yiwa wannan gida ya gane cewa wannan shi ne gidan da suka zauna da Nusi watannin baya. Su kuwa su Nusi da Iliyasis da Cokali tuni sun farfaɗo kuma suna zaune acikin ɗaki mafi alfarma acikin wannan gida. Kewaye dasu abinci ne irin wanda basu taɓa gani ba. Abin ka da yarinta kuma ga yunwa, babu wani tunani haka suka afkawa wannan abinci. Bayan da suka kammala saiga wata farar kuyanga nan tayi sallama a garesu. Kunyangar na shigowa su Nusi sukai tsalle suka jada baya cikin tsoro. Amma kuyangar kawai murmushi tayi, sannan kuma ta tambayesu ko suna buƙatar ƙari. Nan take duk su ukun suka ƙurawa wannan kuyanga ido cikin tsananin mamaki. "Ƙari??" Cokali ne ya fara yin magana, "a ƙaro, wallahi ban ƙoshi ba. Rabona da abinci tun ina yaro...." Wannan kuyanga tayi iya ƙoƙarinta amma ta kasa riƙe dariyar dake wuyanta. Koda ganin wannan kuyanga tayi dariya, sai itama Nusi tayi murmushi. Lallai ga dukkan alamu ba gidan yankan kai suke ba. Nan take wannan kuyanga ta tafa hannu, inda wasu kuyangin guda uku suka fara safarar kwanuka izuwa wannan ɗaki. Ba jimawa Nusi da Cokali da Iliyasis suka ƙara afkawa waɗannan kwanuka. Lallai baza kaga laifin su Nusi ba a wannan hali, domin kuwa da yunwa ta kashe ka kwanda daɗi ya kasheka. Ko manya sun san haka. Sannan kuma basu da tabbashin daga wannan rana zasu ƙara samun irin wannan abinci. Wataƙila ma shikenan haihata-haihata. Wannan kuyangar ta ɗanyi kyaran murya, lamarinda ya ja hankalin su Nusi suka ɗaga kai

Chapter 25 of 33