Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Jikinta ya ingantu matuƙa sama da na duk wata budurwa da Armad ya taɓa gani, ba shiri Armad ya fara kamuwa da surar wannan mace dake gefensa. Nostaljiya ta fuskanci hakan sabida haka kawai tayi murmushi ta kuma ja hannun Armad izuwa ƙarshen wannan kogo. Suna zuwa ƙarshe suka ga wata ƴar ƙaramar ƙofa. Suna shiga ƙofar suka tsinci kansu a wani ƙaton lambu mai bada yanayin ni'ima da annushuwa. Armad ya fahimci cewa ashe wannan kogo a tsakiyar lambu yake. A wannan lokaci ne Nostaljiya Sisiyu da Armad Wilbafos sukai tafiya a matsayin saurayi da budurwa a karo na farko a tarihi. Nostaljiya ce ta fara magana, "Bari na fara, nasan kana da tambayoyi da yawa, amma idan na gama wataƙila ba sai kace komai ba. "Kaga dai mahaifina Bihanzin ya daɗe yana neman hanyar da zai ruguza wannan Rukunai na Jinzidal guda biyu. Amma hakan ba abu ne mai yiwuwa ba indai baka da ƙarfin Izzar da zaka iya cin galaba akan sauran sarakunan Jinzidal biyar ba. Hakan ne ma yasa zaka ga ma'abota Izza wanda suke ƙin jinin cinikin bayin amma dole sai dai suyi biyayya saboda al'amarin na girman Izza ne da kuma girman runduna. Babu wanda ya isa ya fito shi shi kaɗai ya ce yau zaiyi fito na fito da dukkan manyan ma'abota Izzan dake kare cinikin bayi. Hatta mahaifina wanda ɗaya ne daga cikin sarakunan Jinzidal bashi da wannan ƙarfi. Kai hasalima bari kaji, na taɓa tambayar mahaifina akan irin ƙarfin Sarakunan Jinzidal yake cemin hatta daular Ururu da kanta baza ta iya yin fito na fito da dukkan sarakunan Jinzidal ba, koda kuwa zasu yi nasara to kuwa zasu rasa sama da rabin rundunarsu da mutanensu wanda kuma Ururu baza su yadda da hakan ba. Hakan nema yasa zaka ga Ururu na bawa wannan sarakuna na Jinzidal ƙima da mutunci sosai da sosai. "Mahaifina yayi bincike ya gano cewa idan ka ɗauke Tarifil-fakta wanda har yanzu ba'a san waye ba ko kuma a ina yake ba, akwai wani mutun ɗaya wanda ya taɓa yin faɗa da Ururu kuma yaci nasara. Wannan mutun kuwa shi ne Bayajidda, kuma shi ne wanda kaji muryarsa a cikin wannan gari dana ceto ka daga ciki. "To a binciken mahaifina ya gano cewa Bayajidda ya bar wani allon sihiri. Tun daga ranar da mahaifin nawa ya gano wannan allo yake ta bincike a kansa har zuwa wannan rana da muke magana. Wanda idan kai lissafi shekaru dubu ɗari da uku kenan, kaga shekaru tamanin da biyar kenan kafin a haifeni. "Mahaifna ya bani labarin yadda ya gano sirrin wannan allo amma a yanzu bamu da lokacin da zan baka wannan labari domin kuwa ba ƙaramin dogon labari bane. Amma dai kai sani cewa wannan allo shi ne dai wannan allo wanda muka baka kaji mana muryar Bayajidda aciki shekaru da suka gabata. Mahaifina ya gano cewa sirrin Izzar da yake buƙata ya rusa Jinzidal dashi yana cikin wannan allo, kuma kaida kaji wannan murya da kunnenka zaka fi kowa gane mai nake nufi da wannan Izza. Dalilin da yasa kaga mun neme ka domin kaji mana wannan murya ta dake cikin wannan allo shi ne babu wanda ya isa yaji wannan murya sai wanda yaji muryar Bayajidda a cikin wannan gari wanda kuma dani da ƴan uwana duk mun kasa, hasalima ni kaɗai nake iya shiga garin amma nima ɗin ban taɓa jin komai ba. Ranar dana fara ganinka kwance cikin jini acikin wannan gari nasan cewa ƙaddararka da tamu ta riga ta haɗu a wannan duniya kuma babu wanda zai iya rabata domin kuwa kai kaɗai zaka iya jiyo mana sirrin wannan allo wanda shi kaɗai muke buƙata mu cimma burinmu. "Da farko da na ganka acikin garin nan jikinka yana ci da wuta kawai na ceto kane sabida ina so kazo ka fassara mana wannan allo. Amma daga baya dana karanta tunaninka naga kana so ka taimaki mahaifiyarka ne sai naji tausayin ka ya kamani. Nakan so duk wanda naga yana son ya taimaki iyayensa. "Amma a lokaci na farko dana taɓa jikinka sai naji tamkar na taɓa ganinka a wani zamani mai tsaho daya gabata, harma inajin cewa dani da kai mun taɓa soyayya wadda aka rubuta a tarihi. Da nayi zaton ni kaɗai nake jin hakan idan na taɓa jikin naka, amma sai na gano cewa kaima kana jin irin abinda nake ji. Bansan yadda abubuwan suka ci gaba da faruwa ba a cikin zuciya ta ba, amma tun daga wannan rana na kasa daina tunaninka. Na tambayi mahaifina ko irin hakan zai iya faruwa a gaske, amma yace min bai taɓa samun labari ba a tarihi. Saboda haka sai naci gaba da bincike. "Haka na ci gaba da bincike amma har ila yau ban samu komai ba. "Amma daga baya nayi alƙawarin zan taimakeka ka samarwa mahifiyarka lafiya koda kuwa zan rasa raina. "Kayi sani cewa yanzu naga ka farkar da Izza mai ƙarfi acikin jininka, amma kana da buƙatar lokaci kaje ka sami horo ka gane yadda zaka sarrafa ta. Kuma idan ka ɗakko faɗa da Ururu yanzu baza ka sami wannan damar lokaci ba. Saboda haka nema na hanaka aiwatar da abinda kaso ka aiwatar a baya a wajen cinikin bayin can. Ni kuwa kaga ina da mahaifina dazai kare ni. Kuma kaima kasan saƙon da muka karɓa daga wannan allo, wanda kuma sauran ƙiris mu kammala haɗa wannan Izza. Zarar kuwa muka gama to babu wani Sarkin Jinzidal da zamu ji tsoro. "Armad.... " Nostaljiya taja hannunsa suka tsaya a gaban wata bishiyar giginya sannan ta matsa kusa da jikinsa tana murmushi, "Ina sonka Armad. Karɓi wannan," Ta kama hannun Armad ta saka masa wani zobe a jiki, "Ba lalle mu ƙara haɗuwa ba a wannan duniyar. Amma wannan zoben zaisa ka ringa tunawa akwai wata data taɓa sonka wai ita Nostaljiya. Ba jimawa mahaifina zaizo nan, kuma bazan so ku haɗu ba. Sabida haka ka shiga wannan ƙofa zata maida kai ƙasa ta uku. Nayi bincike na gano akwai wani sharri a tattare da wannan ɗan duba Babara, kaje kaga halin da mahaifiyar ka take ciki kafin ka ci gaba da neman wani Tarifil fakta wanda babu wanda yasan taƙamaimai inda yake. Idan kana so kaje kayi horo a shashin Ikwatora to akwai ruhi na a jikin wannan zoben zai nuna maka hanya. Akwai ajiyar abinci da abinci da shekarun Izza ɗari biyar aciki da mahaifiya ta barmin a lokacin da zata mutu. Idan kana so zaka iya amfani dasu." Ga dukkan alamu Noltajiya bata so taji amsar da Armad zai bata a yayin ta buɗe wata ƙofa ta tsafi ta tura Armad ciki ta rufe. Armad yana shiga ya waiwayo da niyyar yayi mata magana amma sai kawai yaji wani ƙarfin Izza na musamman yana zuƙe shi ciki kuma bashi da damar magana. Abu na ƙarshe da Armad ya gani shi ne kwalla guda ɗaya daga kowanne idon Nostalgiya na fitowa. Sannan kuma daga bayanta yaga wani mutun ya bayyana wanda ganinsa ma kaɗai yasa Armad yaji ruhinsa yana neman fashewa ya tarwatse. Ba komai ya jawo hakan ba illa Izzar wannan mutumi. Armad baya jira a gaya masa cewa wannan mutun shi ne Bihanzin mai dauwamammen sara kuma lallai ransa a ɓace yake matuƙa. Armad yaso a ransa ya fito ya tsaya a gaban wannan mutumi duk wani abu da zaiyi wa Nostaljiya yayi masa, idan ma kashe shi zaiyi yayi, amma dai kada ya sake ya taɓa Nostajiya, amma ina kafin yayi wani motsi wannan ƙofa ta ɓace dashi. ____ Sunan Nostaljiya zaku ga ya canja da ina saka mata Nostalgiya, sorry mistake ne saboda da english ina rubuta shi da Nostalgia so saina manta cewa saina juya 'G' ta koma 'J' Tirifil fakta ma zai koma Tarifil-Fakta (shima Triple Factor yake da english) Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 58: Sabuwar Izza Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Bayanda Armad ya shiga wannan ƙofa sai yaji wata irin Izza mai ƙarfin gaske ta zuƙe shi ciki. Idanun sa suka rufe saboda ƙarfin iskar da yaji. Ba jimawa Armad ya buɗe idanunsa inda ya tsinci kansa a fili fetal babu kowa sai shi kaɗai. Ya duba hagu da dama amma babu wani mahaluƙi sai ƙasaitaccen daji da manyan bishiyu. Armad yai ajiyar zuciya inda ya nemi waje ya zauna ya fara tunano abubuwan da suka faru dashi. Domin kuwa abubuwan sun faru da sauri ta yadda har izuwa wannan lokaci bai samu damar zama ya hakaito suba. Ya tuno da watannin da yayi yana shan azaba a hannun wannan aljanu guda biyu. Ya tuno da yadda ya rantse saiya ɗauki fansa akansu amma sai gashi acikin daƙiƙa kaɗan Nostaljiya ta gama dasu. Ya tuno da maganar data gaya masa akan sarkin duba Babara dama sauran maganganu da dama data faɗa akan wannan allo da Bayajidda ya bari dama sauran sirrika data gaya masa. Ya tuno da kalmar data gaya masa cewa tana son sa. A dai-dai wannan lokaci Armad ya tsaya yai duba izuwa wannan zobe data bashi. Yana murza zoben, zoben yana walƙiya tamkar ita mai zoben. Armad ya kula cewa da wani irin dinare na musamman akayi wannan zobe tayadda jikinsa har wani ƙanshi yake irin na musamman. Armad yaro ne amma duk da haka bazai rasa sanin ma'anar kalmar so ba, kuma lallai yasan cewa abu ne mai matuƙar wahala mace ta fara gaya maka hakan, amma gashi Nostajiya ta ajiye kunya ta kuma gaya masa. Lallai ya amince acikin ransa cewa Nostaljiya da gaske mai ƙaunarsa ce da gaskiya. Amma babban abinda ya ɗaga masa hankali shi ne maganar data faɗa cewa ba lallai su ƙara haɗuwa ba. Abin ya tsaya masa a rai kuma ya kasa mantawa. Amma koma dai menene Armad ya yanke shawara cewa da kansa zai nemi Nostaljiya a duk lokacin daya samarwa mahaifiyarsa lafiya. *N.....nusi?* A dai-dai wannan lokaci ne Armad ya tuno cewa tun bayan lokacin da hankalinsa ya gushe a tsakiyar fafatawarsu da Ikenga da Uznu Ururu bai ƙara ganin Nusi ba. Hankalinsa yai matuƙar tashi domin kuwa yasan cewa shi tazo taimako a yayin wannan gasa. Saboda haka koma mai ya same ta shi ne sila. Hankalinsa ya ƙara tashi yayin da ya tuno cewa ba wannan ne karo na farko ba da Nusi tai ƙoƙarin sadaukar da kanta ta taimake shi ba. Nan take Armad ya miƙe. A wannan lokaci yasan lallai zama bai same shi ba. Abu na farko da Armad ya fara yi shi ne duba taskar Izzarsa domin ganin sabuwar Izzar daya samu. Idanunsa suka gane masa abubuwa guda uku: shekaru dubu ɗaya, wani ɗan ƙaramin allo, sannan kuma da wani mutun- mutumi mai kama da Armad amma sai dai idanunsa ruwan ƙasa ne masu launin toka. Armad ya zauna ya lankwashe ƙafafunsa domin tayarda wannan abubuwa dake cikin ruhinsa. Ya karanta ɗalasiman da ake buƙata a ransa sannan ya kira wannan Izza ta shekaru dubu. Nan take yaji wannan Izza ta shiga jikinsa da wani irin ƙarfi wanda bai taɓa jinsa ba. Armad ya riga yasan cewa duk da cewa yawan shekarun Izza nada muhimmanci amma bayan yawa akwai inganci. Wato tayadda zaka samu cewa wani yana da shekaru wanda basu kai naka yawa ba amma kuma yafi ka ƙarfin Izza. A wannan lokaci Armad yana ji a jikansa cewa hatta ƙasa baza ta iya ɗaukansa. Wannan shekaru dubu na Izza suka shiga jikinsa suka haɗe da ruhinsa. Ya zama su suma suka zama shi. Armad yaji gashin jikinsa ya fara zafi, zuciƴarsa ta fara bugawa da ƙarfi kamar zata fito. Kafin yai wani abu wata kumfa mai zafi ta fara fita daga fatarsa tamkar ana wanke wata cuta daga jikinsa. Kayan jikinsa suka jiƙe sharkaf da datti da wannan kumfa mai haɗe da gumi. Haka ya kasance a wannan hali tsahon sa'a ɗaya kafin daga bisani wannan kumfa ta daina fita. Armad ya miƙe tsaye ya kalli jikinsa yaga hatta yanayin fasalin sa ya canja. Fatarsa kaɗai tana bada wani alamun ƙarfin Izza wanda shi kaɗai zai iya tarwatsa abokan gaba. A wannan lokaci ya gane cewa wannan kumfa shekarun Izzarsa ne guda hamsin da ɗaya aka tarwatsa su aka watso su waje domin baza su iya haɗa kafaɗa da wannan sabuwar Izza ta gidan Wilbafos. Shi kansa yasan cewa yana jin wani irin ƙarfi wanda bai taɓa tsammanin ɗan adam zai iya jinsa ba a rayuwarsa. Yai duba izuwa wannan mutun-mutumi dake cikin ruhinsa ya kira shi da ƙarfin Izzarsa. Nan take wannan mutun-mutumi ya taho ya shige jikin Armad. Haka na faruwa idanun Armad suka juye izuwa ruwan ƙasa masu alamun toka. Wannan idanu na bayyana Armad yaji ƙarfin Izzarsa na walƙiya ya dawo jikinsa duk da kuwa babu aljani a jikinsa. Armad yai kira ga wannan allo inda shima ya gabato a gabansa. Ya karanta ɗalasiman dake kan wannan allo a nutse. Yana gamawa yaga takobinsa ta Wilbafos ta bayyana, amma a kanta maimakon taurari biyar yanzu sun koma bakwai. Sannan kuma ƙarfin Nauyi dake cikin wannan takobin ya wuce hatta shi kansa yadda Armad zai iya misaltawa. Murmushi irin na Izza kawai yayi sannan ya juya ya nufi hanya da niyyar samun kogi domin ya wanke jikinsa ya kuma nufi doron ƙasa ta uku. A dai-dai wannan lokaci Armad ya gane cewa ai Babara bai ma isa ya sashi aiki ba. Ya kuma yanke shawara zai koma izuwa Babara ya tursasa masa yayi wa mahaifiyarsa magani dole ko yana so ko baya so. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 59 & 60: Ubbaru Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ______ Armad ya gama wanka, amma babbar matsalarsa kayan sawa. Rigar dake jikinsa har yanzu a yayyage take. Lallai bai kamata mutun mai ƙarfin Izza irinsa ya ringa yawo da ita ba. Yana zaune a gefen ƙoramar da yai wanka yana lissafin hanyar da zaibi ya gane a wane doron ƙasa yake sai hankalinsa yakai ga zoben dake hannunsa. Armad yai duba izuwa zoben, wanda ba wani bane illa wanda Nostaljiya ta bashi. Yana ayyanawa a ransa yaya zaiyi amfani da wannan zobe sai ƙofa ta bayyana a saman zoben ta kuma fara girma a hankali a hankali har saida takai yadda Armad zai iya shiga cikinta. Armad baya iya hango komai aciki sai haske saboda haka ya fara tunanin ya shiga ko karya shiga. Daga ƙarshe dai ya yanke shawarar cewa Nostaljiya baza tayi abinda zata cuceshi ba, saboda haka ya miƙe ya shiga cikin wannan ƙofa. Yana shiga ƙofar ta rufe. Armad ya tsinci kansa a wata duniya ta musamman. Komai acikin wannan duniƴar kyalkyali yake da haske. Ga wasu ƙofofi nan guda biyu a gabansa. A saman ɗaya ansa Armad a saman ɗaya kuma ansa Nostaljiya. Kowacce daga cikin ƙofofin a buɗe take amma bisa mamaki Armad baya iya hango abinda ke ciki. Idan yai duba izuwa ciki babu abinda yake hangowa sai haske. Armad ya yanke shawara ya shiga ƙofar da aka sa sunansa a jiki. Inda ya tafi gadan-gadan ya tura ƙofar ta ƙarasa buɗewa sannan ya faɗa ciki. Yana shiga ya tsinci kansa a wani ɗaki mai cike da kantoci sama da goma. Kowacce kanta na ɗauke da kaya na musamman a kanta. Kanta ta farko da Armad ya fara gani itace ta kayan sawa. Riguna irin na alfarma wanda za'a iya sawa a gari kuma za'a iya fita filin daga dasu kala-kala. Ƙanshi ne kawai ke tashi daga wannan kaya wanda Armad bai taɓa ganin mai kyansu ba. A ɗaya ɓangare kuma akwai takubba, masu, kulke dama sauran kayan yaƙi na musamman. Sannan kuma a wani ɓangaren kuma ga kwalabe na magani kala-kala. A wani ɓangaren kuma ga kayan ci da sha na marmari irin na musamman. Wani abu guda ɗaya daya bawa Armad mamaki shi ne wani ingarman doki wanda tsayinsa yakai zira'i da dama. Yana tsaye a ɗaure baya ko motsi, ba kuma alamun abinci ko abin sha a tattare dashi. Lallai kana ganinsa abinda zaizo kanka shi ne wannan dokin na aljanu ne. Koda ganin wannan kaya da wannan doki na musamman babu abinda yazo zuciyar Armad sai cewa Nostaljiya ta daɗe tana so ta taimakeshi ta bashi wannan zobe, domin lallai wannan shiri bana dare ɗaya bane. Armad yai ajiyar zuciya, shidai baya tunano lokacin da yayi tunanin Nostaljiya tun bayan sanda suka rabu a shekarun baya amma ga dukkan alamu abin ba haka yake ba a wajenta. Kuma lallai irin wannan halacci da tayi ya shiga zuciyar Armad. Abinda kawai zai hanashi komawa gareta shi ne lashin lafiyar mahaifiyarsa da kuma Nusi. Domin tuni Armad ya yanke shawara saiya koma daular denizawa domin gano inda Nusi take. Armad ya zaɓa daga cikin kayayyakin ya kuma canja kaya, ya kuma ɗebi kayan itace domin ya cika cikinsa. Sannan ya nufi wannan doki. Koda isarsa sai dokin ya durƙusa ba tare da gardama ba, inda Armad ya hau kansa a nutse. Hakan na faruwa Armad yaji tamkar yana jin mai wannan doki yake tunani kuma tamkar zai iya magana da dokin. Armad baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen tambayar dokin sunansa. Abin mamaki wannan doki ya amsawa Armad ba tare da ya buɗe bakinsa ba. Wato dai a taƙaice da zuciya sukai magana da ubangidansa, Armad. "Suna na Ubbaru." Armad yaji muryar dokin tamkar haniniyar ingarman doki. Da farko saida yaja da baya cikin tsoro amma ba jimawa ya ware. Sannan ya umarci dokin daya nufi ƙofa dashi. Abu kamar wasa dokin ya miƙe ya nufi bakin ƙofa ya fito yana sassarfa. Inda ya tsaya a bakin ƙofar da aka saka sunan Nostaljiya akai amma zuciyar Armad ta gaya masa bai kamata ya shiga wannan ɗaki ba domin kuwa ba sunansa bane akai. Saboda haka Armad ya umarci Ubbaru daya juya ya fita daga duniyar wannan zobe. Armad na bayyana a wajen wannan ƙofa dake saman zoben, ƙofar ta ɓace baki ɗaya. Daga Armad sai wannan ƙorama, sai kuma jaka mai cike da tuffa da inubi dake hannunsa. Rigar jikinsa doguwa ce ƴar shara ce irin ta mutanda wadda jarumai ke so domin basu dama da take wajen watayawa su sarrafa takobi. Kalarta shuɗiya ce. Sannan kamar yadda ya saba a baya Armad ya samo maɗaurin kai ya kuma ɗaurashi a kansa dai-dai inda yake sawa a baya ya rufe tambarin Miyurarsa. Sai kuma Ubbaru wanda fari ne fat mai yawan faɗin kafaɗu da dogayen ƙafafuwa. Armad ya ɗakko tuffa ɗaya da inubi ya cilla a bakinsa sannan ya nufi hanya. Bashi da niyyar tsaya har sai sanda yaga gari, a nan kuma zai tsaya ya tambayi a wacce doron ƙasa yake. Sannan ya kara bazama bazai yada zango a ko'ina ba sai doron ƙasa ta uku. Ubbaru yai haniniya, sannan ya miƙa dogayen fararen ƙafafunsa gaba ya nufi hanya yana matsanancin gudu. Armad ya kula cewa gaba ɗaya gefensa da duniyar dake kewaye dashi ta ɗauke saboda tsananin gudun da Ubbaru yake. Babban abin mamakin shi ne ko kaɗan iska bata damun Armad duk da wannan gudu, sannan kuma yana iya hango abinda ke can gabansa kafin ya tunkaro shi. Armad bashi da wata hanyar dazai iya hakaita iyakacin gudun da Ubbaru yake, amma lallai yasan al'amari ne babba. Kimanin sa'a biyar bayan fara wannan tafiya Armad ya keta a ƙalla dazuka hamsin. Amma babu abinda ya kawo masa tsaiko domin duk namun dawar dake wajen tamkar ma basa iya ganin Ubbaru. To a wannan lokaci ne Armad hango wani ɗan ƙaramin gida dake can gabansa a tsakiyar daji. Armad ya sanarda Ubbaru ya tsaya idan yaje wannan gida. Ai kuwa ba jimawa Ubbaru ya isa gidan inda ya tsaya cak tamkar matacce babu ko tirjiya. Yana tsayawa Armad yaji muryar mutane acikin wannan gida. Wani murmushi yazo masa domin kuwa yasan cewa zai samu labari akan a wacce doron ƙasa yake. __________________________________ Armad ya tura ƙofar wannan gida wadda dama a buɗe take ya kuma shiga ciki. Abu na farko daya fara gani shi ne jerin tebura da mutane zaune akai wasu suna shan barasa wasu suna cin abinci. Sannan daga can gefe kuma ga wani ɗan tsoho mai yawan sanƙo yana ɗago masa hannu yana tambayarsa, "Mai kake so ɗan yaro, abinci ko barasa?" Nan take Armad ya gane cewa wannan waje irin gidajen nan ne na ci da sha na matafiya da ake gina su a hanya. Kuma ya tuno cewa da dama daga cikin waɗannan gidaje basu da nisa da gari. Armad ya dubi wannan ɗan tsoho yana mai cewa, "Ruwa kawai nake so." Tsohon ya kyaɗa kai sannan ya nunawa Armad wajen zama. Ba jimawa aka gabatowa da Armad abinda ya buƙata. Wata yarinya sanye da doguwar riga samfurin al'adar doron ƙasa ta uku. Armad na ganin haka yai mata murmushi sannan bayan ta ajiye ruwan ya tambayeta, "Ina ne nan?" Yarinyar tana da ƙaton wawulo daga saman dasashinta saboda haka data yiwa Armad murmushi saida ya ɗan buɗe ido cikin mamaki. Yarinyar ta fahimci haka saboda haka ta ɗan rufe bakinta cikin kunya tana mai cewa, "Doron ƙasa ta uku kusa da ƙauyen garin Jari" "Ehmmm...." Armad yaja numfashi cikin mamaki. Duk da baiyi yawo da yawa yana yaro ba amma yasan cewa wannan ƙauye data faɗa yana kusa da ƙauyensu, nisan baifi tafiyar ƴan kwanaki bace. Nan take wani gagarumin farin ciki ya cika zuciyarsa domin ko ba komai yau zaiga mahaifiyarsa. "Yauwa nagode. Nawa ne kuɗin ruwan." Yarinyar ta kyaɗa kai, "A'a ba saika biya ba. Ruwa ai kyauta ne." Armad na niyyar yin magana ya ga an dako ƙofar wannan gida ta ɓalle, sannan kuma yaji muryar wani bajimin gardi daga ƙofar, "Kai wannan ko dokin wane ne ya zama nawa! Idan kuma maishi nada ƙarfi yazo kwata." Gardin nada shekaru casa'in na Izza sannan kuma a bayansa akwai girɗa-girɗan mutane wanda duk sunma fishi girma. Suna tsaye akan Ubbaru suna jira Idan ba wanda yai magana su kwance shi su tafi. Dukkan waje yai tsit kamar mutuwa ta gifta, amma Armad murmushi kawai yayi sannan ya miƙe ya nufi gurin wannan ƴan fashi. Baiyi ko taku biyar ba yaji an riƙe hannunsa ana jawo shi baya. Yana waiwayawa yaga wannan yarinya mai wawulo a bakinta. Yarinyar tana girgiza masa kai alamun kada ya takale. Tana mai nuna masa wawulon bakinta alamun dai wannan ƴan fashin sune suka cire mata haƙoran nata. Armad na ganin haka tausayin yarinyar ya kamashi domin kuwa yana da tabbashin cewa wannan tsohon ba babanta bane. Domin kuwa an saba ganin yara irinta ƴan shekara goma zuwa ƙasa suna yawo a irin wannan gidaje neman aiki. Badan komai ba saidan cewa an siyarda iyayensu a cinikin bayi na Jinzidal. Wasu da dama daga nan suke lalacewa wasu kuma su shiga duniya. Irin wannan yara na daga cikin babban dalilin da yasa Armad ya tsani gasar ta Jinzidal. "Yaya sunanki?" Armad ya durƙusa ya tambaye ta. Yarinyar ta amsa a tsorace, "Aisha." Sannan tai ƙasa da muryarta sosai cikin tsoro ta gayawa Armad wata magana wanda shi kadai yaji. Armad naji ya miƙe ya nufi kan waɗannan ƴan fashi. Babban cikinsu mai Izza casa'in ya dunƙule hannunsa saiga ƙawanyar wuta ta bayyana akai. Baya ganin Izzar Armad amma yasan cewa Armad yana da Izza saboda haka ya fara shiri tun kafin Armad yazo. Na bayansa ma suka fara dariyar tsokana suna zare takubbansu. Kana ganinsu kasan sun raina Armad kuma suna tunanin baifi suyi masa ɗauka ɗaya ba. Amma dukkanin hakan ya canja a lokacin da Armad ya bayyana a gabansu. Yana ajiye ƙafarsa sanyin babban sihiri ya bayyana ya rufe waɗannan ƴan fashi. Idanunsu a kwale cikin tsananin mamaki suka ƙanƙare a tsaye a inda suke. Waye zaiyi tunanin samun ma'aboci izzar da zai iya amfani da sanyin babban sihiri a wannna ƙauye? Armad ya dubi babban cikin nasu sannnan juya izuwa Aisha ya tambayeta, "Wannan ne?" Ta kyaɗa kai cikin tsoro. Abu na gaba da aka gani shi ne haƙoran wannan ɗan fashi a ƙas Armad ya zubar dasu. Armad ya fara magana cikin ƙarfin Izza, "Daga yau wannan waje yana ƙarƙashin kariya ta. Duk wanda ya taba shi, to ni ya taba." Sannan Armad yayi wa Aisha murmushi kafin ya hau kan dokinsa ya ɓace daga wannan waje ya nufi wajen sarkin duba Babara. _____________________________ Babu jimawa Ubbaru yakai cikin wannan daji da Armad ya haɗu da Babara shekaru da suka gabata. A wannan waje ne Armad yai bankwana da mahaifiyarsa ya fita nemo mata magani shekaru da dama da suka wuce. A wannan waje ne sarkin duba Babara yai masa alƙawarin indai ya nemo Tarifil fakta to zaiyi maganin cutar dake damun mahaifiyarsa. A wannan waje ne Armad ya fita daga ƙasarsa ta haihuwa zuwa duniya yana da Izza hamsin da ɗaya amma yanzu gashi ya dawo da dubu. Shin mai Babara ya taka? Ta yaya zasu ƙarke? Domin Armad yazo ne yayi wa Babara dole! Dole ya bawa mahaifiyarsa magani. Ko yaƙi ko yaso! Yaya wannan al'amari zai kasance? ____ Kuyi hakuri da jinkiri, kunsan wani lokaci abubuwa zasu taso babu yadda za'ai. A Babi na gaba zamu zo karshen littafin magajin Wilbafos na daya. Saboda haka duk wanda ya canki yadda tsakanin Armad da Babara zai kasance to shi zamu nada MAGAJIN WILBAFOS na shekarar 2018. Sannan kuma ni marubucin MAGAJIN WILBAFOS zan bashi kyautar babban kyauta , , Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos Kada ku manta banine na rubuta littafin ba hakanan ba ni bane na typing ba, Ni dai kawai na posting makune don ganin yadda littafin yake da matukar nishadi, Bayanai na , ____ suna : Shuraih Usman ____ Matakin izza: 99% ____ Nambar waya: 08170707521 Kowa ya rubuto nashi yayin bayar da amsarsa akan wanga tambaya na sama MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 61 & 62: Abul babara Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ______ Armad yai duba izuwa kwazazzabon rafin dake gabansa mai yawan duwatsu. Komai na nan dai-dai tamkar yadda ya rabu dashi a shekarun baya. Yana tuna dai-dai lokacin da ya ɗakko mahaifiyarsa yazo wannan waje yana neman sarkin duba Babara. Yau gashi shekaru da dama sun shuɗe kamar ba'ai ba. Armad ya sauka daga kan Ubbaru ya mai dashi Cikin zoben sihirinsa sannan ya ci gaba da nufar cikin wannan duwatsu yana tunkarar inda yake tunanin zai samu Babara. A wancan lokaci ya tuna cewa ya samu Babara a cikin ƴar bukka wadda ke cikin wannan daji to amma shekaru sunja, bashi da tabbas zai kara samun Babara acikin irin wannan yanayi daya barshi. Bai jima da fara tafiya ba yaji motsin halitta a bayansa, inda ya labe sannan yakai hannunsa kan takobinsa. Ba jimawa ya gane motsin na takun sahu ne, kuma ɓangarensa yake yiwowa. Armad ya laɓe a bayan wani ƙaton dutse domin ya ga waye ke tafe. Ai kuwa ba jimawa yaga wata budurwa sanye da farar riga doguwa irin ta ma'aikatan asibiti ta bayyana. A hannunta akwai ɗan tulu na ruwa, yanayin ta na nuna alamun sauri. Armad ya haɗe gira cikin mamaki. Bai taɓa tunanin ganin mace

Chapter 23 of 33