Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hankalin Armad ya gushe, babu wanda ya sani ya mutu ko kuwa yana raye. --------- A dai-dai wannan lokaci acan doron ƙasa ta farko sarakuna goma mafi girma a duniya, wanda aka fi sani da ASHURA, ne suke jin wata sarewa mai alamar ƙugen yaƙi tana kaɗawa. Wannan sarewar nada ban mamaki tayadda duk wanda yaji ta kawai zaiji sarewa ne amma banda sarakuna goma na ASHURA. Su saƙo suke ji akan wani mutun da yayi ƙoƙarin ficewa daga kurkukunsu. Amma acewar wannan murya, idanuwan sarki Ururu Kuyurussa'ayi, idanuwanda suka yaki sarki Eyriyon Wibafos, sun halaka wannnan mutun har lahira . 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos Hausa ebooks - pdf,txt and doc www.hausaebooks.cf Download any kind of hausa ebooks hereMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 83: Dan Baiwa Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ____ Bayan gushewar hankalin Armad dukkan jikinsa saiya fara juyewa daga walƙiya yana komawa toka. Kafin ƙiftawar ido da bismilla Armad ya juye izuwa toka. Nan take wannan toka ta narke acikin wannan ruwa kafin daga bisani ayi watsi da ita ta dawo cikin wannan kurkuku. Idan da zaka ga yadda akai watsi da wannan toka zaka fuskanci cewa hatta ragowar tokar ba'a yadda ta fita daga wannan kurkuku ba. Lallai abinda ake faɗa na cewa indai ka shigo ka shigo kenan haka yake. Amma ba jimawa ƙarfin fasahar Armad ta ƙara warewa, wannan toka ta kama ci da walƙiya. Sannnan daga bisani ta juye izuwa surar Armad, kafin daga bisani ta juye izuwa Armad a kwance a sume yana aman jini. Haka Armad yaci gaba da kasancewa acikin wannan hali baisan inda kansa yake ba har tsahon kwana biyar. A kwana na biyar ɗinne wasu mutane sanye da kayan farar fatar raƙumi su biyu suka iso wajen. Dukkaninsu suna kan ingarmar dawakai, sannan kuma suna riƙe da takubba. Na damansu ne ya fara sakkowa inda ya zunguri Armad da ƙafa domin ya gano da rai ko ba rai. Kafin daga bisani ya ɗaɗɗaure shi a jikin dokinsa kafin su koma da Armad inda suka fito. Armad bai san yadda akai ba, kuma bai san kwana nawa yai ba, kawai dai ya farka ya tsinci kansa a cikin wata ƴar bukka shishi kaɗai. Yai shiru yana tunano abubuwan da suka faru dashi acikin bango, inda nan take wata tambaya ta faɗo masa. Shin ya fita daga kurkukun ko kuwa har yanzu yana ciki. Abu ɗaya daya sani shi ne idanda da matsala da lallai acikin ankwa zai ganshi, amma gashi nan a sake akan gado. A wannan lokaci yaji surutan mutane a waje saboda haka nan take ya gano cewa hanya ɗaya dazai samu amsar wannan tambaya shi ne ya fita waje ya tambayi ɗaya daga cikin mutanenda yaji suna magana a wajen tantin. Saboda haka ba tare da tunanin mai zai faru ba Armad ya buɗe ƙofa ya danna kai waje. Abin mamaki yana fitowa yaga babu ko mutun ɗaya dake gadinsa, suma masu wannan magana suna can gefe kuma kallo ɗaya sukai masa suka ɗauke kai suka ci gaba da hira. A kewaye da wajen duk irin wannan bukkoki ne sama da hamsin. Daga gaba garesu kuma akwai wannan ruwa da ake kira da bango, lamarinda yasa Armad ya gano cewa lallai akwai matuƙar yiwuwar haƙarsa bai cimma ruwa ba. Ajikin bangon akwai wani baƙin ƙarfe wanda yai sama sosai tayadda ba'a iya gano ƙarshensa. Akwai mutane a wajen amma basu da yawa, kuma abin mamaki ba ruwan kowa da kowa, kowa harkarsa kawai yake. Can dai Armad ya kasa daurewa ya tare wani mutun sanye da jallabiya ya tambayeshi, "Malan da ALLAH ina ne nan?" Mutumin ya kada baki ya ce, "baka ma san inda kake ba. Kaine wanda aka ce yayi ƙoƙarin shiga ta cikin bango kai tsaye ko?" Mutumin na faɗar haka ya wuce gaba ba tare da amsawa Armad tambayarsa ba. Armad ya haɗe rai yana niyyar finciko mutumin baya sai yaji murya a gefensa. "Kana shalkwatar ƴan-daban ƊAN- BAIWA." Armad ya juyo da kansa ɓangaren inda yaji muryar inda yai arba da wani saurayi kalar larabawan yamma mai yawan dogon gashi mai launin ja da fari. "Shalkwatar ƴan-daban ƊAN-BAIWA? Wane ne ɗan-baiwa kuma?" Saurayin ya ja dogon farin gashin dake kansa tare da yin murmushi yana cewa, "kamar yadda ka sani wannan kurkuku an rabata tsakanin ɓangarori guda uku. Shekara ɗaya baya, ɓangare ɗaya basa ƙoƙarin guduwa daga wannan kurkuku, amma dama can ɓangarori biyu sun daɗe suna ƙoƙarin guduwa. Amma a yanzu hatta wannnan ɓangare ƙoƙarin guduwa suke. Wanda hakan ya jawo sauye-sauye da dama acikin wannann kurkuku. Da dama ana ganin wannan canji yana faruwa ne saboda bayyanar wannan mutun da ake kira da ƊAN-BAIWA, duk da babu tabbashi akan wannan maganganu amma lallai a yanzu sama da kaso sittin na wannan kurkuku suna biyayya ga wannan mutun mai suna ɗan-baiwa. Babu wanda yasan daga inda yake ko kuma tayaya ya shigo wannan kurkuku amma bisa mamaki tuni jama'a suka naɗashi a matsayin sarkinsu. Suna na Indimi Iyyka Citta Sailari Abati. Ni ne na ceto ka daga inda ka suma." Wannan mutun ya kammala bayaninsa da miƙawa Armad hannu su gaisa. Abubuwa da dama Armad bai fahimta ba saboda haka yai shiru yana tunanin mai zaice masa. Baima kula da dogon sunan wannan saurayi ba. Koda saurayin yaga haka sai yai tunanin ko Armad bai yadda dashi ba ne, saboda haka ya ce, "Kada da damu, dani da abokina muka ceto ka. Kuma a wannan waje babu wanda ya damu dakai, sai dai kawai kai sani cewa muna zaune Tsarin dake jikin bangon nan ya fara haske irin wanda ke nuna cewa wani yayi ƙoƙarin guduwa. Hakan ne yasa akai ƙungiya ta mutun bibiyu domin su kewaya su gano inda abin ya faru. Ta haka ne dani da wanda aka haɗani muka gano ka." Armad ya numfasa ya ce, "nagode. Amma ina da tambayoyi da yawa. Da farko dai wanne sunanka acikin sunayen daka gayamin?" Saurayin yai murmushi tare da cewa, "suna na Indimi Iyyka Citta Sailari Abati. Kada ka damu a hankali zaka riƙe su. Da dama sukan ɗau lokaci." Armad yaja numfashi mai tsayi kafin ya girgiza kai. "To amma menene manufar wannan shugaba naku mai suna Ɗan-baiwa? Sannan kuma shin zan iya tafiya idan ina so?" Wannan saurayi mai dogon suna ya ce, "Eh zaka iya tafiya mana, amma idan har kana so kaga Ɗan-baiwa to ka tsaya domin kuwa yau zai biyo ta wannan waje." Armad ya tsaya yana tunani kafin daga bisani yai ajiyar zuciya. Babban abin shi ne duk wata tambaya da Armad yayi wa saurayin bao amsa masa ita ba kai tsaye. Hasalima har yanzu bai masan taƙamaimai meke faruwa ba. Daɗin daɗawa jikimsa bai gama warewa ba. Yana cikin tunani yaji muryar wannan saurayi a kunnensa yana cewa, "zo kaga zanensa kafin ya ƙaraso." Saurayin yaja Armad izuwa wata kwana. Suna isa wasu mutane ne guda shida suke ta kallon wani ƙaton zane dake kafe a jikin bango. Suna matsawa kusa sai Armad ya fara jin abinda suke cewa. "Shi ne Ɗan-baiwa. Yadda ka ganshi a jikin hoton nan haka yake a gaske. Kana ganinsa kasan jarumi wanda zai iya canja duniya." Koda Armad yaji wannan kalamai sai ya ƙara azama domin yaje ya ga wannan ɗai-baiwa da idonsa. Amma yana isa ya tararda hoton wanda ya sani kamar tafin hannunsa ajikin wannan zane. Wannan dai ba wani bane illa Ikenga O Bayajidda. Koda ganin wannan zane sai Armad yaja da baya cikin tsananin mamaki da ɗimuwa. Ya dubi wannan saurayi mai dogon suna ya ce, "Wannan ne ɗan-baiwan?" Saurayin ya kyaɗa kai, "Eh shi ne. Kasan shi ne?" ** . 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos Hausa ebooks - pdf,txt and doc www.hausaebooks.cf Download any kind of hausa ebooks here MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 85: Kabilar Nara Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ____ Koda Armad yaga wannan zane na Ikenga sai zuciyar ta yamutsa, ya rasa abinda ke masa daɗi. Abin mamakin shi ne fafatarwarsu da Ikenga a shekarar data gabata ita ce take ta dawo masa. Yana cikin haka yaji muryar wannan saurayi a gefensa. "Kasan ɗan-baiwa ne?" Nan take Armad yai sauri ya farfaɗo daga zurfin tunanin daya shiga. "Eh... a'a! Na dai taɓa gamuwa dashi a wajen kurkukun nan." Koda jin wannan amsa sai saurayin ya haɗe gira cikin mamaki, kafin daga bisani ya numfasa ya tambayi Armad. "Ya akai kuka haɗu? Ko kaima mabiyinsa ne a wajen wannan. kurkuku?" Cikin sauri Armad ya amsa da cewa, "a'a, ni ban san ma yana da mabiya ba ballantana na zama ɗaya daga cikinsu. Shi kuwa meye manufarsa ta haɗa mabiya? Yaƙi yake shiryawa ko kuma me?" Wannan saurayi yai murmushi, "Eh.. lallai wannan ita ce tambayarda kowa yake tayi a tsahon shekara ɗayannan da ɗai-baiwa ya shigo wannan kurkuku. Sai dai kuma babu wanda yake da amsarta sai shi kansa da kuma manyan kwamandojinsa guda biyar dake haɗa masa jama'a. Kamar dai yadda na gaya maka ana saka ran ɗan- baiwa zaizo nan yau, kuma koda baizo yau ba lallai acikin satin nan zai bayyana domin yiwa mabiyansa bayani akan manufofinsa." Koda jin wannan jawabi sai Armad ya yanke shawarar lallai ya kamata yaji wannan manufofi na Ikenga. Domin kuwa duk da Armad baisan Ikenga sosai ba amma fafatawar da sukai tasa yana ji a ransa cewa akwai wani sirrin Izza a tattare dashi. Sannan kuma babban abinda ya tsayawa Armad a rai shi ne maiya kawo Ikenga wannan kurkuku, domin kuwa a lissafi shekarar Ikenga ɗaya cir da zuwa wannan kurkuku. Wanda hakan ke nuna cewa Ikenga yazo kurkukun lokaci kaɗan bayan gama fafatarwarsa dashi a gasar Jinzidal. Lallai da sake. Akwai wani abu dake faruwa a ƙasa. "Sailári, shin kana ganin nima zan iya shiga naji wannnan manufa ta Ikenga?" Wannan saurayi najin wannan tambaya ya fashe da dariya yana cewa, "Sailári? Wato a duk sunaye na guda biyar biyar shi ka riƙe. To ba komai, hakan ma yayi. Amma dole na gaya maka cewa Sailari suna ne da kishiyar babata ta saka min, saboda haka mahaifiyata bata faɗarsa. Kai sani cewa ina da wata ƙanwa mai suna Ranâ-Ƙísa-Hurura-Inshala-Yaƙa-Dása. Ita wannan ƙanwa tawa indai tayi laifi babarmu ta dake ta to ranar baza ta faɗi kowanne suna ba sai Sailári, wai itama ta rama saboda tasan maman mu bata so." Saurayin ya ƙara yin dariya yana tuno da, kafin daga bisani ya amsawa Armad tambayarsa. "Eh zaka iya zuwa mana. Mabiyan ɗan-baiwa suna da yawa, babu wanda ma zai gane kai baƙo ne." Armad ya kyaɗa kai ya ce, "to indai haka ne kuwa zanje. Amma mai yasa dakai da ƙanwarka kuke da sunaye har guda biyar? Inzan iya tunowa sunanka Indimi-Iyka-Sai lari-Citta-Abati." Saurayin ya amsa da cewa, "A kabila ta duk yaron da aka haifa yakan samu sunaye daga ɗaya zuwa ɗari. Dalili kuwa shi ne haƙƙin saka suna yana kan duk wanda suke zaune gida ɗaya da wannnan yaro da aka haifa. Misali a gidanmu mu biyar ne sanda aka haifeni. Babata ta saka min Indimi, babana ya saka min Abati, kakata ta saka min Iyka, Kishiyar babata ta saka min Sailari, sannan sai kuma yar aikinmu ta saka min Citta. Shi yasa ƙanwata kuma sunanta ya zama guda shida saboda nima na ƙaru sanda aka haifeta." Saurayin na zuwa nan ya ja Armad izuwa tantinsa yana cewa. "Muje mu shirya kafin ɗai-baiwa yazo." Sai dai suna cikin tafiya ya fashe da dariya kamar wanda ya tuno wani abu. Armad yai niyyar tambayar mai yasa yake dariya amma ya fasa. Can dai Sailari ya kada baki ya ce, "na tuno wani aboki da aka haifa a gidan yawa. Sunayensa guda saba'in da bakwai ne. A lokacinda muka shiga makaranta akan ɗauki rabin awa ana kiran sunayensa idan akazo kiran suna." A zuciyar Armad ya ce lallai akwai al'ada kala-kala a duniya. Idan kaji wata ma saika riƙe baki. Suna shiga Sailari ya jefowa Armad ɓarin gurasa yana cewa, "satinka ɗaya baka ci abinci ba amma jikinka bai nuna yana jin yunwa ba, lafiya kake kuwa?" Armad najin haka ya zare ido tare da kallon gurasar. Lallai kuma haka ne. Abin mamakin shi ne saida ma akai magana sannan ya tuna, domin kuwa da daida kwayar zarra baya jin yunwa ko ƙishirwa. Lallai ba lafiya ba. Amma ba daɗewa Armad ya tuna da cewa ashe fa dukkan jikinsa ya juye izuwa walƙiya, saboda haka baya buƙatar yaci abinci dan yunwa sai dai kawai dan marmari. Amma a haƙiƙa wannan ba abu bane da zai iya gayawa kowa kai tsaye ba. Domin wannan sifa ce ta manyan sarakunan aljanun, kuma zaiyi wahala a yadda cewa ba aljani bane shi indai aka ji. Saboda haka yai murmushi kawai tare da jefa gurasar a bakinsa amma bai bawa Sailari amsarsa ba. Shima Sailarin bai damu ba kawai yaci gaba da hirarsa. A wannan rana saida Armad yasan kusan komai akan ƙabilar Nára, wadda ita ce ƙabilar su Sailari. Amma Ikenga baizo ba, washe gari ma haka, har saida akai kwana uku. Magana ta tabbata cewa mutumin daya haɗa kan fursunonin wannnan kurkuku suke masa biyayya acikin shekara daya kacal, wanda akafi sani da ɗan-baiwa zaizo wannan yankin na ƴan-daban warure, kuma anan zai bayyana manufofinsa. Saboda haka kullum wajen ƙara cika yake da mutane. Kullum Armad zai kewaye ya nuya yana gwada fasahohinsa domin ƙara kwarewa, sannan kuma yana nazarin Bango domin ganin hanyar guduwa. Amma hakan bai hana Sailari yin hira dashi ba ta sama da awa biyar a kowacce rana. A rana ta biyar Armad ya haƙura da ganin Ikenga yana niyyar tafiya sai kwatsam ƴan shela suka fara yin shelar cewa ɗan-baiwa ya bayyana. Nan take fursunonin nan suka fara ambaliya suna tururuwa izuwa ga ɗan-baiwa. Armad na tsaye daga gefe tare da Sailari suna kallon. Sai a lokacin Armad ya gane lallai akwai mutane da yawa a wajen. Ba jimawa saiga Ikenga nan ya bayyana sanye da jajayen kaya samfurin alkyabba, rataye da takobinsa. Abin mamaki sai Armad yaga duk da cewa ga kama nan amma kamar Ikenga ya ƙara girma da faɗi sosai da sosai. Ba jimawa ya gane cewa ƙarfin Izza ne kawai ba wani abu ba. Koda gano haka sai Armad ya rufe idonsa domin jin yanayin-izzar Ikenga. Amma bisa mamaki babu komai, tamkar Ikenga baida wata izza. Ya tuno da abinda Babara ya gaya masa na yadda wasu manyan ma'abota izza suke ɓoye yanayin-izzarsu domin kada kowa yasan halin da suke ciki. Armad na cikin tunane-tunanensa yaji hayaniya, Ikenga ya bayyana. . 2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama ta samu. Wepsite din Hausaebooks wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku barka da zuwa. Yi hanzari ku ziyacemu A shafin mu na facebook akan www.facebook.com/hausaebooks Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos Hausa ebooks - pdf,txt and doc www.hausaebooks.cf Download any kind of hausa ebooks hereMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 86: Ikenga da Armad Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Mutane sun jejjeru iyakacin ganinka a gaban dakalin da Ikenga ke tsaye shi da tawagarsa. Kuma saboda da ragowar hasken rana kowa na ganin kowa tar-tar. Babu murmushi ko ɓacin rai a fuskar Ikenga saɓanin mabiyansa wanda keta murna da shewa. Koda bayyanar Ikenga sai wannan taron jama'a suka ƙara ruɗewa da shewa. Babu abinda kake ji sai sunan ɗan- baiwa. A dai-dai bayan Ikenga wani tsoho ne a tsaye, wanda ba wani bane illa wannan mutun mai suna Kána dake tare da Ikenga. A bayan Kána wasu sadaukai ne sanye da kayan yaƙi daban-daban susu biyar. Dukkaninsu ba'a ganin fuskokinsu. Armad najin yanayin-izzarsu ya gane cewa babu wanda acikinsu bai haye izza dubu ba. Amma ko a jikinsa. Abinda kawai ya dami Armad shi ne yaji manufar Ikenga ya bar wajen. Ana jira Ikenga ya fara jawabi kawai saiya juya ya koma inda ya fito. Lamarinda yasa nan take wajen yai tsit, kowa ya fara kalle-kalle yana tunanin maike faruwa. Ana cikin haka shima Kána tare da mutun biyar ɗin dake bayansa suka bi bayan Ikenga. Koda ganin haka sai Armad yai tsaki gami da juyawa izuwa tantinsa domin yin shiri ya kama gabansa. Saboda haushi ko Sailari bai yiwa magana ba. Amma bisa mamaki a lokacin ne yaji muryar Ikenga a kunnensa. "Idan kana so kaji manufata to ka rufe idanunka kayi tafiya kimanin taku hamsin a jikin bango kana fuskantar gabas kana kiran ɗalasimin 'Shaibal'shísu' zaka bayyana a fada ta." Koda jin wannan batu sai Armad ya haɗe gira yana mamakin yadda Ikenga ya iya shiga kansa yayi magana ba tare da ya bashi izini ba. Amma kawai ya share yai kamar baiji ba. Inda ya nufi tantinsa ya haɗe kayansa ya buɗe ƙofar zobensa na sihiri ya saka su aciki. Abu ɗaya ya rage kafin ya bar wannan waje, shi ne sallama da Sailari. A wajen tantin jama'a ne barkatai suke ta tattaunawa akan dalilin da yasa ɗan-baiwa baice komai ba, amma bisa mamaki babu wanda ya juyawa ɗan-baiwa baya duk da haka. Hasalima wasu da dama daga cikinsu suna ganin abinda yayi ya dace da girman izzarsa. Armad na fitowa ya fara laluben Sailari acikin tantinsa, amma babu shi babu labarinsa. Saboda haka ya nufo cikin taron jama'ar nan inda ya barshi. Duk da ruɗani da yawan jama'ar dake wajen ba jimawa sukai ido huɗu da Sailari a tsaye yana jimamin rashin jin muryar Ikenga. Armad ya jashi wajen mutane ya ce, "kai yanzu Sailari baka damu da abinda Ikenga... ɗan-baiwa yayi ba?" Koda jin wannan magana sai Sailari yai murmushi ya ce, "ai wannan ba wani abu bane. Mutun biyar ɗin da ka gani a bayansa sune manya-manyan ma'abota Izza acikin wannan kurkuku kafin bayyanar ɗan-baiwa. Mutane kamar mu basu isa suje kusa dasu ba ballantana su gansu. Ai ganin ɗan baiwa kaɗai da mukai falala ce." Koda jin wannan magana sai Armad ya fara gane yanayin yadda ake rayuwa a wannan kurkuku; mai ƙarfi kamar wani abin bauta ne. Sannan kuma Armad ya tabbatar cewa Sailari zai iya dagewa saiya bishi idan yaji cewa zai tattauna da Ikenga. To amma Armad bai san yanayin yadda zata kaya ba. Ƙazamin faɗa zai iya rincaɓewa tsakaninsa da Ikenga saboda haka bazai iya tafiya dashi ba. Nan take Armad ya fasa gaya masa inda zaije. "Au haka abin yake... Ai ban sani ba. Bari naje na dawo ai kana nan ko?" Sailari ya kyaɗa kai, yana niyyar tambayar Armad mai yasa yake kiran ɗan-baiwa da Ikenga amma ya fuskanci sauri Armad yake saboda haka ya fasa. Haka Armad ya bi ta tsakankanin wannan taron jama'a ya ratse can nesa izuwa shiyar da Bangon yake. Yana isa ya nufi gabas tare da fara lissafa adadin takun da yake. Babu wani tsoro ko kuma tunanin mai zai faru da yake. Yana jin cewa Ikenga bai isa ya cutar dashi ba a yanayin ƙarfin izzarsa. Ba jimawa Armad ya cika adadin wannan taku da Ikenga ya bashi, inda ya buɗe idonsa ya tsinci kansa a wata ƴar ƙaramar farfajiya kewaye da rafi. Komai dake wajen dai- dai yake idan ka ɗauke launin ruwan dake cikin wannan rafi. Ja ne jajawur, hasalima da dama zasu yadda idan aka ce jini ne ba ruwa ba. Armad na bayyana ya iske Ikenga shi kaɗai a zaune kan kujera ta ƙasaita. A gaba dashi akwai wata kujerar wadda ba kowa akai, sannan a tsakiyarsu akwai ɗan teburi ɗauke da abin sha irin na mutanan farko. Ikenga yai wa Armad nuni daya zauna akan wannan kujera, sannan ya miƙa masa abin sha. Armad kai tsaye ya zauna ya kurɓi wannan abin sha wanda bai taɓa ganinsa ba sannan ya dubi Ikenga da wani kallo mai cike da tambayoyi. Koda ganin haka sai Ikenga yai murmushi tare da cewa, "kana da tambayoyi da dama amma kayi sani na kira ka nan ne domin na baka dama wadda baza ka ƙara samun irinta ba. Saboda haka tambayoyinka sai dai su jira. "Zan fara kai tsaye. Ina so a matsayinka na Magajin Wilbafos kayimin mubaya'a. Ni kuma zan arzutaka da abubuwa guda huɗu." Koda Armad yaji wannnan magana saiya fashe da dariya yana cewa, "ni zanyi maka mubayi'a ko kai zakai min?" Amma bisa mamaki sai Ikenga yaci gaba da bayani tamkar baiji me Armad ya faɗa ba. "Abubuwa huɗu dazan arzutaka dasu sune; na farko zan gaya maka inda ɓarin ruhinka yake, na biyu zan gaya maka labarin mahaifinka, na uku zan baka ɗalasimin dazai fitar dakai daga wannan kurkuku, sannan na huɗu zan kare ka daga wani babban sharri dazai faru dakai acikin wannan shekarar mai zuwa." . ____ Rashin Response naku akan wannan littafi yasa na daina kawo maku shi gaba daya,,,,,, Izan har bakwa response to zamu runga daukan lokaci kafin muyi post MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 87: Alkiblar Armad Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Koda Armad ya ga lallai Ikenga da gaske yake saiya canja fuska tare da kyara zama. Ya dubi Ikenga ya ce, "Idan zan iya tunowa lokaci na farko da na ganka akan wani tsibiri ne ana rigimar Littafin-takobi. Kuma a wannan rana ta dalilinka na rasa Miyura ta tare da ɓarin ruhi na. "Lokaci na biyu dana gamu dakai ƴar uwata Nusi ta gano hanyarda zan samo Tarifil-fakta na ceto mahaifiyata amma bisa sharadin sai nayi nasara a gasar Jinzidal. Kai ne sanadiyyar rashin samun nasara ta da kuma faɗawa hannun Uznu Ururu da nayi, sannan kuma da rasa ƴar uwata Nusi wadda har yanzu ban san inda take ba. "To yanzu gashi mun kara gamuwa dakai a lokaci na uku. Sai dai kuma a wannan lokaci kazo da wani sabon salo na buƙatar mubayi'a. Kai sani cewa ban damu da me kake ciki ba, ban damu me kake ƙullawa ba, ban damu da yadda ka shigo wannan kurkuku ba, ban damu da ko kana da hanyar fita ba ko baka da ita ba, ban damu da mai yasa kake haɗa mabiya acikin wannan kurkuku ba, ban damu wani hasashenka na wani sharri dazai faru dani ba, ba damu ko kasan inda ruhi na yake ba. Amma abu guda ɗaya dazan gaya maka, ni Armad Wilbafos saina kawarda Jinzidal a ban ƙasa kuma saina samowa mahaifiyata lafiya koda sama da ƙasa zasu haɗu. Idan kana tunanin kana da karfin izzarda zaka iya hanani to ka gwada. Wannan shi ne kashedi na farko kuma na ƙarshe da zan baka." Koda Armad yazo nan a zancensa saiya ɗauki wannan kofi ya ƙara kora abinsha. Sannan yaja kujerarsa baya ya miƙe da niyyar tafiya. Amma a wannan lokaci Ikenga shima ya canja fuska ya kuma fara bawa Armad jawabi. "Ni Ikenga O Bayajidda saina mallaki wannan duniya koda kuwa mutane da aljanu da Ururu zasu haɗa kai su yaƙe ni. Domin tun a ranar da aka haifeni tauraruwa ta take bada hasken sarauta. Bari na baka kaɗan daga cikin tarihi. "Kafin zuwan Ururu, kafin zuwan Wilbafos, kafin zuwan Bayajidda, akwai taurari a sararin samaniya. Wannan taurari su suke tsara tafiyar lokaci da zamani a yadda aka sanshi. Bayan juyin mulki da Ururu sukaiwa ƙaɓilarka sai wannan taurari suka dusashe. A shekarar da aka haifeni wannan taurari suka ƙara bayyanar da haskensu, kuma tun daga wannan rana alƙalami ya riga ya bushe cewa sai na mallaki duniya. "Tun ina yaro nake iya karanta tafiyar taurari na gano abinda zai faru na gaibu dama wanda ya riga ya faru. Ina ɗan shekara bakwai na fara amfani da taurari ina sarrafa lokaci, wanda ta haka ne takobi na take iya tsofantar da duk abinda na sara ta hanyar zuƙe shekarun dake jikin wannan abu. Babu wanda yasan tayadda na rayu bayan yaƙin daya halaka gari na amma da wannan fasaha na kuɓuta daga hannun Ururu a wannan yaƙi. "Gamuwa dakai da nayi a lokaci na farko kawai kaciɓis ne da kuma ƙaddara, amma kafin lokacin ban taɓa sanin dakai ba a duniya. A gamuwa ta dakai ta biyu na gano cewa ajikin ka akwai wani sirri na musamman, amma kuma akwai inuwar mutuwa dake tattare da ruhinka. Wanda indai ka shallake ta to lallai zaka zamanto magajin wilbafos da ba'a taɓa gani ba. Nayi niyyar kashe ka a faɗan da mukai a Jinzidal dan kada ka kawomin cikas, amma na canja shawara. "Nayi tunanin idan ka durƙusa a ƙasa kayimin mubayi'a dani dakai zamu iya kawarda da daular Ururu da kuma sarakunan Jinzidal mu kawo tamu daular. Saboda haka a wannan lokaci na ɗora ɗalasimai masu aiki da tafiyar taurari acikin wannna filin daga da muka fafata tayadda koda wani abu ya faru zan iya ceto ranka. "Bayanda Uznu ya bayyana aniyarsa a fili ta halaka ka saina ƙara ƙarfin wannan ɗalasimi, amma sai bayan na ɓace sai taurari suka bayyana min cewa Uznu neman littafin-takobi yake bawai taƙamaimai kai yake so ya halaka ba. Saboda haka sai na juyo izuwa wannan fili da niyyar na canja fasalin wannan ɗalasimi, amma duk da nayi amfani da hasken taurari na ɓoye kaina saida idanun Uznu Ururu suka ganni, lamarinda yasa matsala ta faru a yayinda nake canja yanayin wannan ɗalasimi. Daga nan ni kaina ban san maiya faru ba, amma Uznu yayi amfani da wannan ɗalasimi da nasa domin kare ka ya cillo ƴar uwarka izuwa wannan kurkuku. "Bayan komai ya lafa na ƙara yin bincike akanka na gano cewa ruhinka ya rabe gida biyu, sannan kuma na gano cewa zaka bayyana acikin wannan kurkuku duk da cewa lokacin da zaka zo bai bayyana a gareni ba. Saboda haka na yanke shawara wannan kurkuku ita ce waje mafi dacewa da kayimin mubayi'a sannan kuma mu fara shirin yadda zamu mulki duniya. "A saboda haka ne nazo wannan kurkuku tun waccan shekara na jira ka amma baka zo ba sai yanzu. Acikin shekarar data wuce na gano cewa shi kansa Uznu yayi kuskure, maimakon ya jefo Nusi zuwa wannan kurkuku sai ta zarce izuwa sashin Ikwatora. Ban san mai take ciki ba amma lallai bata cikin matsala kuma tauraruwarta tana bada haske na lafiya. "Nayi amfani da wannan dama ta kasancewa a wannan kurkuku na fara haɗa kan

Chapter 29 of 33