Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙarfin Izza a doron ƙasa ta huɗu, idan son samu ne kada ka taɓa yin faɗa dashi!" Yana gama faɗar haka ya juyawa Armad baya ya fara tafiya, a lokacin ne shi kuma Armad ya buɗe baki da niyyar tambayarsa mai ya kamata yayi, sai dai kafin yai magana yaji gaba ɗayan kansa ya fara juyawa, inda daga bisani ƙasar da yake tsaye akanta yaji ta fara narkewa tana komawa kamar ruwa. "Aaarrrghh" muryar Armad kenan bayan da yaji kwatsam ya rufta ƙasa. Wanda a lokacin ya tsinci kansa a wani yanayi mai kamada mutun yana faɗawa wawakeken rami mara ƙarshe, sai dai abinda Armad yake fuskanta a lokacin yama fi haka. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 5: Koriyar Duniya Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . A babi na hudu mun tsaya a inda Armad ya tsinci kansa yana faɗawa cikin rami ba tare da shiri ba, yanzu zamu ci gaba. *** Hankalin Armad tuni ya gushe, a lokacinda yake cikin halin ruftawa wannan waje, zuciyarsa cike da jimamin ina zai faɗa, kuma a wanne hali zai faɗa. Abu na gaba da Armad ya gani bayan hankalinsa ya dawo jikinsa shi ne tsintar kansa da yayi a wata duniya ta musamman. Tun kafin idanunsa su ƙarasa buɗewa wani haske wanda gaba ɗayansa kore ne babu ko garwaye, ya fara yi masa sallama ta hanyar haske masa ido. Kafin daga bisani ya ƙarasa buɗe idanunsa ya kuma ga zahirin wannan duniya daya tsinci kansa aciki. Bayan buɗe idon nasa ne ya kuma ɗaga kansa sama, inda ya fahimci cewa dukkan abinda ke wannan wajen kore ne shar. Kama daga kan sararin samaniyar wannan duniya har zuwa kan tantagargar doron ƙasar. Ba shiri ya durƙusa gami da dantsi ƙasar dake kusa dashi domin ya ƙara ganewa idonsa launinta. Wani abu daya ƙara bashi mamaki shi ke babu wani alamun rauni a jikinsa, duk da kuwa cewar bai san yadda akai yazo wajen ba, amma kuma abu na ƙarshe da yake tunawa shi ne faɗawa cikin wannan rami wanda a iya lissafinsa, a tayi masa da kyau ya sha da karaya biyu zuwa biyar. Yana tsaye cikin mamaki da talazzuzin yanayin daya samu kansa a wannan duniya sai kawai jin alamun motsi yai a samansa. Ai kuwa yana ɗaga kai yai arba da wani ƙatoton shaho kore shar, wanda yakai kimanin ƙafa uku a kwance, yana ƙoƙarin kawo masa wata muguwar wafta da niyyar tsinke masa kai. Bakin shahon yana da tsayi da tsini matuƙa, sannan kuma ga kyalli da sheƙi da yake yi. Daga can ƙarshen bakin kuma akwai wani koren abu mai kama da yawu da yake ɗisa daga cikin bakin shahon. Wani abun mamaki shi ne, wannan koren abu, babu abinda yake sai tiriri, tamkar daga cikin wuta yake futowa!! Ba shiri Armad yai sauri ya sunkuya ƙasa, lamarinda yasa ya kubuta da ɗan taƙi kaɗan daga tsinin bakin wannan shaho. Sai dai kuma kafin Armad ya ƙarasa ɗagowa tuni wannan shaho ya juyo a fusace, tamkar wanda aka hana abincin daya halatta a gareshi ko kuma wanda aka hana haƙƙinsa, ya kuma ƙara nufo Armad ta baya. Kan kace meye wannan tuni yayi ƙasa-ƙasa ya kuma ɗaura azamar ƙara kawowa Armad wata suka mai cike da mugun nufi irin wanda shi kaɗai zai iya karayar da rundunar abokin gaba hamsin da ɗoriya. Ba shiri Armad ya wartsake daga halin da yake ciki, gami da miƙa hannu ya kuma zare takobinsa. Wata muguwar ƙara ce ta tashi, irin wadda ke tashi idan ƙarfe ya haɗu da ƙarfe, a lokacinda tsinin bakin wannan shaho ya haɗu da kaifin takobin Armad. Wani abun mamaki daya firgita Armad shi ne bayan haɗuwar takobinsa da bakin wannan shaho, kawai sai allankatafur suka ƙi rabuwa da juna tamkar ansa wani abu an ɗaure su a tare; a dai-dai lokacin Armad fincikar takobinsa kawai yake amma ina, ko motsi bata yi. Shi kuwa wannan shaho ya caka bakinsa akai shima baya ko motsi. Lamarinda ya ƙara bawa Armad mamaki. Abu na gaba da Armad yai shi ne dunƙule hannunsa na dama, inda ya dubi wuyan wannan shaho, cikin zafin nama ya kai masa wani mugun duka ya kuma ci sa'a ya sameshi. Amma bisa mamaki shahon ko gezau baiyi ba da niyyar kaucewa hannun na Armad, haka ya barshi yaje ya haɗu da wuyan nasa, lamarinda yasa wata ƙara ta tashi sama mai kama da ana dukan dutse. Idanunsa cike da mamaki Armad ya janye hannunsa cikin mamaki da ɗimuwa, hannunsa yana karkarwa kamar ba'a jikinsa yake ba. Ba komai bane ya jawo haka ba illa abinda Armad yaji bayanda ya daki wuyan wannan shaho. Wanda duk da cewa gashi a ido wuya ne mai ɗauke da nama da jini, amma a zahiri taurinsa yafi na jan dutse. To amma da ace lamuran da Armad yake fuskanta anan suka tsaya, toda da sauƙi matuƙa, to amma a dai-dai wannan lokaci ne hannunsa dake riƙe da takobinsa ya fara fuskantar wani abu. Wannan kuwa ba wani abu bane illa ji da yayi takobinsa ta fara rage nauyi, lamarinda yasa ya ƙurawa takobin tasa ido domin tabbatarda ko abinda yake ji a hannunsa gaskiya ne! Sai dai kuma amma a lokacin ne akan idonsa ya fara ganin takobin tasa ta fara rage tsayi da faɗi. Duk da wannan abubuwa da suke faruwa, mamakin Armad bai kai ƙololuwa ba, saida idonsa yakai kan wannan shaho ya kuma ganshi acikin halin limshe ido, bakinsa a kafe ajikin ƙarfen takobin. Nan take Armad ya lissafa abubuwan dasuke faruwa ya kuma gano cewa lallai wannan shaho mayarda takobinsa abinci yai kurum, abinda ke faruwa kuwa shi ne shahon yana zuƙe ƙarfen takobin ta Armad ne kawai ta wata hanya da Armad bai taɓa jinta koda a karance-karancen littattafan tarihi da yaƙi da yai a iyakacin tsahon rayuwarsa. Mamaki da ɗimuwa su ne abubuwan da suka cika masa zuciya a wannan lokaci. Sai dai kuma a lokacin ne ya fuskanci cewa wannan ba lokacin ya tsaya yana mamaki bane, kasancewar wani mummunan ƙaraji da yaji mai tsoratarwa ta bayansa, wanda yasa nan take Armad ya juya izuwa ɓangaren da yaji wannan ƙaraji. Sannan kuma a lokaci guda wani abu ne yake faruwa wanda Armad bai sani ba, wannan kuwa ba wani abu bane illa haske da wannan takarda da wannan dattijo mai suna HanDiyúza ya bashi, take tayi acikin aljihun wandonsa! Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 6: Kuskuren armad Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Armad na tsaye yana cikin yanayin tunanin maiya kamata yayi har tsahon kimanin daƙiƙu biyu zuwa uku. Kafin daga bisani ya ƙara jin irin wannan ƙaraji da yaji a baya, lamarinda yasa ba shiri ya waiwaya ɓangaren da ihun ya taso. Inda idanuwansa sukai arba da wani ƙatoton miciji kore, wanda a tsaye kaɗai yakai tsayin Armad wato taku huɗu, a kwance kuwa yakai kamu sittin da ɗoriya. Idanun micijin suma koraye ne kaf, kuma a buɗe suke tar-tar, domin tun daga nesa Armad ya hangesu suna bada sheƙin kore. Sai dai kuma wani babban abin mamaki shi ne kana ganin wannan miciji zaka fuskanci cewa ba'a cikin hayyacinsa yake ba, domin gumi kawai yake sannan yana cikin halin gudu mai tsanani tamkar wanda yaga mutuwa ido da ido. Armad na tsaye baima gama karantar abinda ke faruwa ya ƙara hango wata koriyar ƙura ta turnuƙe a can bayan wannan miciji, kafin kuma daga bisani ya fuskanci cewa ashe wata tawagar korayen namun dawa ce, irinsu su zaki da damisa da kuma manya-manyan kuraye, dukkaninsu koraye, sai dai kuma bisa mamaki dukkaninsu suma gudun suke kamar ransu zai fita. Yana cikin haka sai kawai yaji wannan wannan shaho dake manne a jikin takobinsa ya fara karkarwa kamar wanda ke cikin farfaɗiya. Ba shiri Armad ya juyo da niyyar ganin meke faruwa, inda yai arba da wannan shaho acikin wani yanayi na firgici kamar irin wanda yaga wancan miciji na ciki. Ba shiri Armad yaga wannan shaho ya fizge bakinsa daga jikin takobin, inda cikin tsananin sauri da zafin nama ya fara kaɗa manyan fuka-fukansa, tare da kuma yin sama da juyawa ya doshi gabas. Nan take Armad ya tabbatarwa da kansa cewa lallai akwai wani abin tsoratarwa da yake saka waɗannan manyan halittu wannan gudu. Saboda haka nan take shima Armad, a irin girman rashin tsoronsa, ya yanke shawarar maiya kamata yai. Wanda ba komai bane illa ya tsaya yaga abinda yasa suke gudun kafin shima yasan maiya kamata yayi. Ko cikakkun daƙiƙu bakwai ba'ai ba, wannan halittu dake ta gudun fanfalaƙi suka zo suka wuce inda Armad yake tsaye, ko kallonsa babu wanda yai acikin su, lamarinda ya ƙara bashi mamaki sosai. Domin a sannan ne ya tabbatar lallai ko menene yasa waɗannan namun dawa gudu, ba ƙaramin abin firgici da tashin hankali bane, kuma koma menene ba abu bane da Armad ya kamata yai gangancin tara ba, saboda nan take Armad ya fara tunanin yanke sabuwar shawarar shima ya kamata ya ranta a na kare, in yaso daga baya yaga mene ne! Har Armad ya juya zai bi bayan waɗannan halittu, kawai sai yaji ƙarar gudun ruwa, lamarinda yasa ala dole ya juyo da niyyar ganin mai ya kawo ruwa wajen. Tun kafin ya ƙarasa juyawa idanunsa suka fara karkarwa, fuskarsa cike da mamaki, gashin jikinsa ya mimmiƙe, sannan kuma a lokaci guda gumi ya fara keto masa. Duk ba wani abu bane ya janyo haka ba illa abinda idanun Armad suka gane masa da kuma abinda zuciyarsa take ɗarsa masa. Wannan abu ba wani abu bane illa wata ƙatotuwar igiyar ruwa wadda girmanta yafi gaban misali, sannan kuma launinta baƙi ne, baƙi ƙirin. Kuma wannan shi ne karon fari da Armad yaga wani abu ba kore ba, tun bayan shigowarsa wannan koriyar duniya. Armad ne tsaye cak, kamar an riƙe masa agara, ya kasa ko motsi. Babu abinda yake mamaki sai launin wannan ruwa. Kasancewar tunda yake bai taɓa gani ruwa mai launin baƙi, baƙi-ƙirin irin wannan ba! Sannan kuma wani abin mamaki ruwan ya tokare sararin samaniya, ta inda baka iya gano ƙarshensa duk yadda ka ɗaga kai. Nan take Armad ya juya cikin tsananin sauri da niyyar da fara gudun-tsira da rai, inda ya ɗaga ƙafarsa ta dama gami da yin tsalle da niyyar fara gudu. To amma rashin sani yafi dare duhu, juyawarsa keda wuya sai kawai bisa mamaki yaji wani abu mai santsi yana ƙoƙarin haɗiye shi, abu na gaba sai kawai yaga ganinsa ya fara yin dishi-dishi, kafin daga bisani ya fara jinsa akan iska wani mugun jiri yana ɗaukansa, inda ba zato ba tsammani sai kawai tsintar kansa yayi a sume. Bayan adadin wani lokaci da Armad bai iya tantancewa ba, sai kawai farkawa yayi ya kuma tsinci kansa acikin wani ɗaki. Ya na buɗe ido jikinsa ya fara bashi cewa lallai akwai wani kuskure daya aikata, duk da kuwa cewa bashi cikakkiyar masaniyar menene, amma yana da yaƙinin cewa lallai yayi kuskure a wani waje! To babban abinda Armad bai sani ba shi ne, duk wani abu da zakai a wannan duniya yana da sakamako, kama daga kan motsi, numfashi, magana da dai sauransu. Kuma shi ne babban amfanin wannan takarda mai ƙunshe da bayanai da ɗalasimai da wancan mutun mai suna HanDiyúza ya bashi. Daga inda da Armad yake tsaye acikin wannan koriyar duniya zuwa cikin wannan ɗaki tafiya ce ta sama da shekara goma akan ingarman doki, wadda gabaki ɗaya Armad yayi ta ba tare da ya sani ba. Sai dai babban abin tambayar shi ne, a ina ya bayyana, kuma ina ne cikin wannan ɗaki. Ɗaki ne mara girma sosai, kuma samansa a buɗe yake hanhai, sannan yana da bangwaye guda huɗu; gabas da yamma, kudu da arewa. Babban abin mamakin shi ne, kowanne bango launinsa daban ne; bangon arewa shuɗi ne na kudu kuma kore ne sai kuma na gabas da yamma waɗanda farare ne. Babu ƙofa ko taga acikin wannan ɗaki. A tsakiyar ɗakin akwai wata ƴar ƙaramar shirwa ta zinare. Wannan shirwa ta kasance an gina ta akan wani gadan aba'i wanda sai mutum yabi takansa sannan zai iya kaiwa gareta. Bayan tsahon lokaci Armad na tsaye yana mamakin bayyanarsa a wannan waje, sai kawai ya yanke shawara ya gwada zuwa wajen wannan shirwa ya duba ko zai tadda wani abu. Yana isa matattakalar gadon aba'in nan ya tsaya, ya fara dube-dube yana tunanin maiya kamata yayi, amma bisa mamaki kan ya yanke wata shawara yaga bakin wannan shirwa ya fara buɗewa da kansa ba tare ya taɓa komai ba. Kan kace meye wannan ya buɗe hanhai. Wanda sai a dai-dai lokacin ne Armad ya kula da hasken da takardar dake aljihunsa take yi. Inda nan take ya zira hannu ya fito da ita. Nan take ya fara karantawa, tunda daman karatu da rubutu a wajensa ba matsala ba ne, musamman yanayin yadda mahaifiyarsa ta matsa masa tun yana yaro akan karance-karancen abubuwa da dama, wanda har a wannan lokaci Armad bai san amfanin da dama daga cikinsu ba, ko kaɗan. Ba komai ake bayani acikin wannan takarda ba sai umarni da ƙaidojin yadda za'a fita daga cikin wannan duniya, wanda ganin hakan ne yasa Armad ya fara fuskantar abinda ya faru dashi a baya acikin wancan koriyar duniya daya bayyana. Sai dai kuma Armad bashi da lokacin tsayawa tunani a lokacin. Nan take cikin sauri ya karanta wasu ɗalasimai daga cikin takardar sannan ya tofa acikin bakin shirwar nan data buɗe. Sannan ba tare da ɓata lokaci ba ya dawo tsakiyar wannan ɗaki, wato kusan daidai inda ya fara bayana a karan fari kenan. Daga nan ya dubi kudu, inda kai tsaye yayi taku biyar, idonsa a buɗe, kafin daga bisani ya rufe ido ya ƙara wasu taku biyar ɗin. Sannan ya tsaya cak yana duban wannan bango, kamar wanda ke tsammanin wani abu ya afku. Yana tsaye a haka ba jimawa sai wannan bango ya fara ƙara kamar ana buɗe ƙofa, kuma kafin a jima, gaba ɗayan bangon ya fara girigiza, inda daga bisani ya karkace ɓari ɗaya ya bada hanya kamar an buɗe ƙofa. Yana ganin haka, ya ɗanyi tunani kaɗan, kafin daga bisani ya faɗa cikin ƙofar. Shigarsa keda wuya wani haske ya kashe masa ido tsahon daƙiƙu, inda bayan ya washe ya tsinci kansa a wani fili na daban. Babu alamun rayuwa a wajen ko ɗaya, ko'ina ka kalla babu abinda yake tashi sai yanayin kaɗaici. Daga can nesa ɓangaren gabas akwai wasu manyamanyan tsaunuka guda biyu, wanda baya iya hango ƙarshensu daga inda yake. A tsakiyarsu kuma abin mamaki wani ƙasaitaccen gari ne, amma babban abin mamakin shi ne tun daga inda yake yana iya hangen yana ta rufe garin ruf, tayadda daga yawan yanar kaɗai zaka iya ƙiyasta cewa anyi shekara sama da dubu babu wanda ya shiga wannan gari. Bisa mamaki sai Armad yaji tsananin son ya shiga cikin wannan garin duk da bai san mai yasa ba, kuma yana da cikakkiyar masaniyar cewa kafin yai wani abu akwai abinda ya kamata ya karanta acikin wannan takarda. Amma kuma duk da haka yana ji tamkar rayuwarsa ta ta'allaƙa da shiga cikin wannan gari. Saboda haka bai san lokacin da ya ɗaga ƙafa da niyyar isa gun waɗannan tsaunika ba, da niyyar ya ɗan leƙa ciki kawai yaga meye aciki. Haka kuwa akai, cikin rashin tsoro, Armad ya nufi ƙofar garin, inda yana zuwa yasa hannunsa ya fara cire ƙoƙarin cire yanar data lulluɓe ƙofar. Haka kuwa akai, ba jimawa ya gama cire ta, lamarinda yasa ƙofar garin ta bayyana a sarari yadda yake iya ganinta. Sai dai kuma wani abu daya bawa Armad mamaki shi ne, ba kamar yadda yayi tunani ba da fari, ƙofar garin a buɗe take maimakon a rufe. Domin yana ɗan tura ta kaɗan ta tafi ta fara biɗe kanta hanhai. Lamarinda saida yasa Armad ya ɗan jada baya kaɗan, kafin daga bisani ya yanke shawara ya kuma shiga cikin wannan gari. Shigarsa keda wuya, takunsa na farko ya tsaya cak a inda yake,abu na gaba kuwa daya gani saida yasa nan take duk da ɗimbin rashin tsoro na Armad saida jikinsa ya fara karkarwa. Kuma kan kace meye wannan tuni ya fara ƙoƙarin jada baya cikin sauri da niyyar ficewa daga cikin garin kasancewar tuni ya daɗe da yin nadamar saka ƙafa aciki, da kuma tabbatar da cewa yayi kuskure! Sai dai kuma amma ina a dai-dai wannan lokaci ne yaji ƙasar wajen da yake tsaye ta haɗiye shi zuwa idan sahu. Ala dole haka ya tsaya cak a inda yake, bashi da ko niyyar juyawa baya, ya kuma ƙurawa abinda ke gabansa ido, abisa dole. Ba komai Armad yake gani ba illa wasu mutane manyamanya mutane samfurin adawa. Kowannensu cikin kayan yaƙi irin na al'ummar farko, sannan kuma a jere suke a layi; kowanne layi yakai mutun casa'in zuwa ɗari, sannan kuma akwai layika kusan guda goma a jere. Babban abin tsoron daya firgita Armad shi ne babu alamun canji na tsufa ko kuma gajiya ko kaɗan a jikin waɗannan mutane, wato dai kamar fitowarsu kenan zasu fita yaƙi, kawai motsi ne da basa yi. Domin idan badan wata kakkaurar yana data rufesu ba to da babu ta yadda Armad zai iya gane cewa wannan mutane sunyi shekaru aru-aru a tsaye basu motsa ba. Sannan kuma babban abin mamakin shi ne dukkansu idanunsu a buɗe yake, kuma acike da tsananin tsana da baƙin ciki. Sun kasance acikin yanayi na ɗaga kai suna kallon sama kamar wanda suke kallon abokin gaba a kan ƙasar dake samansu. Irin tsananin faɗuwar gaban da Armad yake fuskanta idan ya kalli waɗannan mutane irin wadda bai taɓa ji bace. Sai dai kuma duk wannan ba shi ne abinda ya razana Armad ba, kuma yasa yake ƙoƙarin ficewa daga cikin duniyar ba. Wannan abu kuwa ba wani abu bane illa wata murya da Armad yake ji a kunnensa, wadda tafi kama da muryar manya-manyan sarakunan aljanu ma'abota Izza maɗaukakiya, irin Izzar nan wadda ita kaɗai zata sa kaji dole saika durƙusa akan gwiwowinka ka kai gaisuwa idan kai arba da ita. Abinda kuwa da wannnan murya take cewa shi ne; "NI BAYAJIDDA ƊAN ALMA'ATA ƊAN DJINN ƊAN ODUDUWA ƊAN IKENGA DA HÁRÚNU ƊAN MASARAYÚLÚ, INA MAI RANTSUWA DA MAHALICCIN SARKI WILBERIYA, BAZAN TAƁA DENA YAƘAR KUBA, KU MA'ABOTA BAƘAƘEN IDANUWA (URÚRU). "KODA KUNYI AMFANI DA WANNNAN LA'ANANNIYAR IZZAR DA KUKA GADA ACIKIN WAƊANNAN BAƘAƘEN IDANUWA NAKU, KUN HANANI TAKA DORON ƘASA, TO NI KUMA ZAN YAƘE KU A TSAYE A INDA NAKE. "IDAN MA KUMA KUKA YI AMFANI DA WANNAN TSINANNIYAR IZZA DAKE CIKIN BAƘAƘEN IDANUWAN KU, KU KA HANANI MOTSI, TO NI KUMA ZANYI AMFANI DA BAKI NA NA YAƘE KU. "KAI KODA KUNYI AMFANI DA WANNNAN KORARRIYAR IZZAR DAKE CIKIN BAƘAƘEN IDANUWAN KU, KUN HANANI MAGANA, TO NI KUMA ZANYI AMFANI DA ZUCIYA TA NACI GABA DA YAƘARKU. "KAI KODA KUNYI AMFANI DA BAƘAƘEN IDANUWAN KU, KUN KASHE RUHI NA, BAZAN DAINA YAƘARKU BA, BAYAN NA MUTU!!!" Bayanda muryar tazo nan a zancenta saita ɗanyu shiru, kafin daga ƙarshe ta rufe da jimla guda ɗaya! "URURUUUUUU, DUK MASIFAR DA AL'UMMA KE CIKI KU NE SANADI!!!" A dai-dai lokacin da Armad ya gama jin waɗannan maganganu wanda yake jinsu suna tasowa daga can cikin garin nan, tuni ya faɗi ƙasa akan gwiwowinsa, jini ne kawai yake feshi daga idanunsa da bakinsa da hancinsa. Hankalinsa kuwa tuni ya gushe. Sai dai kuma abu na ƙarshe da Armad yai tunani a ransa kafin ya ƙarasa suma shi ne, "wannan ba wani abu bane illa kawai muryar wannan mutun mai suna BAYAJIDDA, wadda take neman halaka ni, kawai saboda na saurare ta! "To mai zai faru idan da shi wannan mutumin na ainihin ne ya tsaya a gabana!!" Armad ya ciji yatsa gami da girgiza kai, sannna ya rufe da cewa; "Lallai bani da ƙarfin Izza, lallai ya kamata na ƙara zage dantse, dan idan ba haka ba babu inda zanje acikin duniyar da mutane irinsu BAYAJIDDA suka rayu!!!" Waɗannan sune kalaman da Armad yake ta faɗa acikin zuciyarsa a yayinda ya suma a bakin ƙofar wannnan gari mai ban al'ajabi!!! Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 7: Gimbiya Nostoljiya Nara Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . A babi na shida mun tsaya a inda Armad ya faɗi a sume cikin wannan gari, bayan jin wannan murya. Yanzu zamu ɗora; *** Babban abinda Armad bai sani ba shi ne, wannan murya da yaji ta kasance kullum saita maimaita sak irin abinda yaji tana faɗa sau casa'in da tara. Bata taɓa fashin yin hakan ba, sannan kuma babu wani mahaluƙi daya taɓa shiga cikin wannan garin tun bayan da muryar ta fara maganar, sama da shekaru dubu kenan, sai Armad. A dai-dai wannan lokaci, Armad yana kwance a sume baisan inda kansa yake ba, sannan kuma bashi da masaniyar cewa duk sanda wannan murya ta gama maganarta, gaba ki ɗayan iskar wannan gari kamawa take da wuta, badan komai ba sai dan tsananin ƙarfin Izzar dake ƙunshe cikin muryar. Kuma hatta a wannan lokaci, abinda ya afku kenan; ɗaukewar muryar keda wuya, gabaki ɗayan ilahirin iskar dake cikin garin ta fara ɗaukan zafi. Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne wasu tafkatafkan jajayen kunami masu kafafu Irin na mutane, wanda a tsaye sunkai girman ƙananun giwaye, suka bayyana a dai-dai inda Armad yake. Kana ganinsu zaka tabbatar da cewa a matuƙar fusace suke, saboda yanayin yadda suke kallon Armad, wanda ke kwance a sume baima san abinda ke faruwa ba. Waɗannan kunami guda biyu ba wasu bane illa masu tsaron wannan gari. Kasancewar a dai-dai lokacin da Armad ya shigo garin suka ji shigowarsa, to amma saboda wasu dalilai basu bayyana ba saida ya suma. A wannan lokaci ne suka rikiɗe izuwa siffar mutane sanye da tufafi irin na can-can mutan da, launin ja da rotsi-rotsi, sannan kuma da irin hular nan mai lankwasa da tsoffin da suke sawa. Na hannun daman ya dubi na hagun tsahon ƴan daƙiƙu, kafin daga bisani ya fara magana a nutse da cewa, "zuri'ar Wilbafos ne, kuma ko badan komai ba, saboda alaƙar dake tsakanin shugaba Amraikugyu da Wilbafos-na-shida, bai kamata mu halaka shi ba." Yana zuwa nan a zancensa yai shiru tare da ci gaba da duban ɗan'uwan nasa, kamar yana jira yaji mai zaice. Shi kuwa babu abinda yai illa sunkuyawa, ya kuma dangwali jinin dake malale a gaban farar rigar Armad. Wanda ya ƙura masa ido tsahon daƙiƙa kusan talatin kamar wanda yake karanta wani haɗaɗɗen littafin da baya son ɗauke ido. Can daga bisani ya ɗago kai ya dubi wannan ɗan'uwa nasa da yai magana da fari tare da cewa, "abinda ka faɗa gaskiya ne, to amma kuma bai kamace mu ba, mu tseratar dashi." Yana gama faɗar haka ya miƙe, inda dukkaninsu suka kyaɗa kai alamun amincewa, kafin daga bisani su ɓace ɓat, babu su babu alamunsu. Sai dai kuma a dai-dai wannan lokacin tuni wuta ta fara tashi acikin wannan gari. Kuma duk wani abu da zaka iya gani wutar nan bata barinsa. Ba jimawa kayan jikin Armad suka fara ci da wuta, kan kace meye wannan tuni fatar jikinsa ma ta fara kamawa. Ana cikin haka sai kawai wannan takarda dake cikin aljihun Armad ta bada wata ƴar ƙaramar ƙara, mai kama da an fasa tulu. Inda ita ma ta fara cida wuta, kuma kan kace meye wannan tuni ta ƙone. Armad na kwance a sume, sannan kuma ga jikinsa ya fara cida wuta, sannan kuma ga takardar da ke ƙunshe da ɗalasiman da zasu fitar dashi daga cikin wannan duniya su kaishi zuwa doron ƙasa ta huɗu inda yake sa ran fara neman Tirifil-fakta, ta ƙone. Lallai da idonsa biyu da ana tamabayarsa zai yadda da cewa yana cikin mafi munin halin da zai iya samun kansa a ciki a wannan lokaci!!! *** Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne da Armad ke kwance a sume, a can wani ɓangare na duniya, wani ƙatoton lambu ne, wanda idan ka ƙiyasta girmansa sai kaga shi kaɗai yakai kimani girman wasu ƙauyukan. Wasu irin dogayen bishiyu ne na ƙasaita da isa da alfarma, masu fala-falan ganyayyaki, yawanci masu launin kore, yalo da ja suka kewaye dukkan wannan lambu. Daga cikinsa kuma ƙananun bishiyu ne a jejjere a layi-layi sahu-sahu. Babu komai akan waɗannan bishiyu banda ƴaƴan itatuwa kala-kala masu yawan gaske, waɗanda tsabagen yawansu da dama daga cikinsu ma idon bil'adama bai taɓa gani ba. Sannan kuma a tsakankanin waɗannan bishiyu dake jere akwai wasu ƙoramu suna kwaranya, masu ɗauke da wani tataccen ruwa garai-garai, wanda saboda kyawunsa, kai kace ba daga duniyar nan yake ba. Dukkanin waɗannan abubuwa sune suka sa tun daga nisan sama da tafiyar kwana ɗaya da wuni mutun zai iya fara jin ƙanshi mai sanyaya rai, na tashi daga cikin wannan lambu. Sai dai kuma a zahirin gaskiya duk wannan bashi ne abinda yasa wannan lambu ya zama na musamman ba. Abun kuwa da yasa hakan ba wani abu bane illa wani ɗan ƙaramin gida dake a tsakiyar wannan lambu, wanda yake ta bada wani irin haske mai tsananin ƙawa da kyawun tsari, wanda bazai taɓa misaltuwa dai-dai da dai-dai ba. Kuma wani babban abin mamakin shi ne babu alamun wata fitila wadda za'a ce ita ke bada wannan haske, a'a sai dai kawai hasken na ɓullowa ne daga cikin wannan gidan. Acikin wannna gida kuwa akwai wani ɗaki wanda shima a tsakiyar gidan yake. Kuma abin mamaki dukkan wannan haske da wannan gida yake bayarwa asalinsa daga wannan ɗaki yake fitowa. A dai-dai wannan lokaci wasu mutun biyu ne a tsakiyar wannan ɗaki akan wani gadon alfarma da aka yiwa ado da fatar fararen aljanu. Waɗannan mutun biyu ba wasu bane illa wata budurwa da kuma wata dattijuwa wanda ba daban kayan dake jikinsu sun banbanta suba, da idan ka kalle su ta baya sai saika ce ma ƴa da uwa ne, saboda dukkanin jikinsu haske yake. Amma ina, kallo ɗaya kacal zakai ka tabbatar da cewa lallai ratar dake tsakaninsu irin wadda ke tsakanin sarauniya da kuyangarta ce. Domin kuwa bisa ƙololuwar mamaki, duk wannan haske dake tashi wanda ya mamaye mutanen biyu da kuma gidan baki ɗaya, sannan kuma har yake fita waje yana haskaka wannan lambu baki ɗayansa, daga jikin wannan budurwa yake tashi. Tun daga baya idan ka dubi wannan budurwa zaka ji wani tsananin gwarjini irin na manyan sarakunan farko na tashi daga jikinta, wanda shi kaɗai zai iya saka maka tsananin firgici da tunanin wace ce wannan budurwa. Amma kuma wani ƙarin abin mamakin shi ne hatta wannan dattijuwar dake kama da kuyangar wannan budurwa, Izzar ta takai mataki na ɗari uku da arba'in da biyu, wanda hakan zai ƙara nuna ma girma da falalar wannan budurwar. A dai-dai wannan lokaci wannan dattijuwa ta kyaɗa kai alamun amincewa. Kai daka gani kasan cewa basu daɗe da gama tattauna wani abu mai matuƙar muhimmanci ba. Sannan kuma ta tashi daga inda take ta nufi jikin bangon ɗakin da wannan budurwa take fuskanta, inda ta tsaya ta kira sunan wani ɗalasimi, "Hai-há-ka!" Faɗar wannan ɗalasimi keda wuya kawai sai wannan bango ya fara haske, inda kan

Chapter 4 of 33