Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
duk wata fasaha da suke da ita. Amma babban abin mamakin shi ne a ina wannan yaro ya samo wannan laya? Ta yaya ɗan ƙaramin yaro zai mallaki Farar-laya." Haka dai Ghalee ya ci gaba da bayyana alajabinsa a fili ƙarara da yadda akai Armad ya mallaiki Farar-laya. Domin dai ko ba'a faɗa ba ansan ya riga yaci nasara akan Amuru, wanda tuni ya faɗi ƙasa ko motsi baya iya yi. Domin bawai kaɗai ɗaure aljanu wannan Farar-laya take yiba, hatta ma'aboci aljanin sai yaji muguwar kasalar da bazai iya komai ba. Babu daɗewa abinda ya faru ya girgiza kowa a wajen, kuma tuni mahangar da dama daga cikin ƴan kallon akan Armad ta canja nan take. Kusan sama da kaso arba'in sun fara yi masa kyakkyawan zato. Likitoci suka garzayo cikin filin-dagar suka ɗauki Armad, domin abin mamaki shi ne, Armad shi ne yayi nasara amma kuma shi yake ta aman jini. Saboda ko ciwo ɗaya babu a jikin Han Amuru in banda kasancewar dai ko tashi bazai iya yi ba saboda aikin wannan Farar-laya. Inda dai ALLAH ya taimaki Armad shi ne akwai wata fafatawar kafin ayi wasan ƙarshe. Saboda haka yana da lokacin da zai huta ya ɗan farfaɗo. ____ Ba daɗewa aka buga wani ƙugen yaƙin, dake sanarda cewa lokaci yayi da za'a fafata tsakanin Deniz Bizaya ɗan sarki Deniz Iluru mai masaukin baƙi, da kuma Ikenga O. Bayajidda wanda shi ne sanadiyyar rabewar ruhin Armad gida biyu da kuma ɓacewar Miyurar sa! A can gefe ɗaya kuma Armad ya fito matakin ƙarshe na wannan gasa! Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos Alƙalin wasa Ghalee ya kira wasa na gaba. Deniz Bizáya ɗan sarki Deniz Iluru ya fito kan filin wasa tare da abokin karawarsa wato Ikenga O Bayajidda. Kai daga ganin tsaiwar waɗannan jarumai biyu kasan sun banbanta da sauran. Sa'ilin nan kuma tsayuwa ce wadda ake gani a jikin jaruman farko waɗanda ƙafafunsu suka ginu a fagen daga. Fuskokinsu babu tsana ko kallon raini a game da junansu, lamarinda ke nuna cewa kowa acikinsu ya yarda da matsayin Izzar abokin fafatawarsa, amma fa kana ganin idanunsu zaka ga kafiya, irin ta ƙololuwa. Irin wadda lallai idan mutun ya sa abu a gaba, to saiya cimmasa. Tunda farko dai babban dalilin da yasa Ikenga ya riga kowa zuwa shi ne goron gayyata da Deniz Bizáya ya aika masa na cewa yana jiransa yazo su motsa jini kafin a fara gasar! Haka kuma akai, Ikenga yazo, shi kuma Bizáya yasa aka buɗe masa ƙofa tun ma kafin lokacin fara gasar yayi. Kwanansu goma sha uku su na fafatawa a gaban waɗannan giwaye, lamarinda yasa daga ƙarshe suka haƙura aka tashi kunnen doki, dan kowa ya kasa samun nasara. Kuma a ƙarshen wannan doguwar fafatawa da sukai, kowa acikinsu ya tafi da abu guda ɗaya acikin ransa; cewa indai yana so ya zamo na ɗaya a wannan gasa to saiya ƙara ƙarfin Izzarsa fiye da ɗan'uwansa domin inba haka ba kuwa, sai dai koda sun haɗu a zagayen ƙarshe, a ƙarayin kunnen doki. Dan haka kyautar ma sai dai a raba musu. Wanda kuma wannan abu ne da babu wanda acikinsu ya yarda dashi. Hakan nema yasa kowa acikinsu yayi amfani da ragowar kwanakin wajen ƙara samun horo. Kuma yanzu gashinan sun haɗu tunma kan aje zagayen ƙarshen. Deniz Bizáya ne ya fara magana da cewa, "inaga babu buƙatar mu ɓata lokaci a wannan faɗan, dani dakai kowa yasan kowa! Kar tasan kar! "Kuma jan faɗa a tsakaninmu a wannan mataki, ba abu ne mai amfani gare mu ba. Domin zamu iya gajiya ko kuma mu jiwa juna rauni, kuma ba lalle a bada hutu mai yawa a tsakanin wannan zagaye dana gaba ba. "Shin mai zai hana muyi wani abu a gaban kowa!" Yana zuwa nan a zancensa ya rufe idanunsa, bayan kimanin daƙiƙa biyar ya buɗe; yana buɗewa baƙar kwayar idonsa ta ɓangaren dama ta ɓace gaba ɗaya, kuma a wajenta na da babu komai sai hoton wani zane guda ɗaya mai kama da ƙatuwar ƙusa irin wadda ake ginin gidajen aljanu da ita! Wanda idan ka ɗaga idonka, ka kalli goshinsa dai dai wajenda ya kamata ace Miyura ce, zakai arba da sak irin wannan hoton ƙusa na cikin idonsa, sai dai kawai ya fishi girma. To idan da a haka abin ya tsaya, to da da sauƙi, amma buɗe idanun Bizaya keda wuya gaba ki ɗayan ilahirin cikin wajen filin ya fara girgiza kamar zai kife. Can bayan kamar daƙiƙa goma sai komai ya tsaya cak, amma kuma kowa ya samu kansa cikin sakin baki dan mamakin abinda suke gani tsaye cak a bayan Bizaya. Ba komai bane illa wata ƙatotuwar ƙusa mai malafa ta jan dinare. Tsaye take cak tamkar bata taɓa faɗuwa ba tunda aka shimfiɗa duniya, tamkar kuma baza ta taɓa faɗuwa ba koda duniyar ta ƙare. Saboda girman ƙusar idan ka ɗaga kai baka iya gano ƙarshenta, sai dai kawai ka hangi malafar ƙusar kawai ta nutse a cikin gajimare. Ƙasanta kuwa wanda a fiƙe yake, kuma a tsaye a bayan Bizaya, yana cake akan iska. Kai ta kowanne ɓangare, kuma komai duban mai duba bazai iya gane cewa wannan ƙusa ba'a zahirin gaske take ba. Indai ba zuwa kai ka taɓa ba, sai dai amma idan ka taɓa zaka fuskanci cewa wannan ƙusa hoto ne bawai a zahiri take ba. Ana cikin haka ne wannan ƙusa a gaban mutane, ta fara rabewa gida biyu! Kan kace meye wannan ta rabe zuwa gida biyu, wanda kuma kowanne rabi ya rabe zuwa gida biyu, inda kowacce ta ƙara rabewa, kai cikin ƙiftawar ido tuni wannan ƙusa ta rabe zuwa gida takwas. Hakan na faruwa ta daina rabuwa, amma kuma ɓariɓarin nata, wanda da kowanne wani ɓangare ne kawai na jikin ƙusar farko, suka fara mulmulewa su na haɗewa, kan kace meye wannan kowacce acikinsu ta zama ƙusa akan kanta. Kuma duk manya, wanda duk da basu kama ƙafar ta farkon ba, amma kowacce tafi zira'i ƙafa sittin! Duk wanda ya taɓa ziyartar daular Denizawa yasan sunan wannan hoton ƙusa daya bayyana a bayan Bizaya, wanda shi suke kira 'Márakána'. Bizaya yai wani murmushi mai cike da yadda dakai, gami da ci gaba da cewa, "zan saka dukkan ƙarfin Izza ta acikin wannan Marakana da kake gani, zan kuma sa su kewaye ka. "Abu ɗaya kacal kawai nake so kayi, ka iya fita daga cikinsu acikin daƙiƙa sittin! "Indai har kai haka, to ni Deniz Bizáya na yarda kayi nasara akaina! "Idan kuma ka kasa, to nima kayarda nayi nasara!" Cikin ƙasa da daƙiƙa ashirin duk wanda ke wajen yaji wannan gasa da Bizaya ya sakawa Ikenga, duk da kuwa ba da ƙarfi ya faɗa ba, amma ya faɗa yadda alƙali Gali zai iya ji, wanda daka ganshi a fili kasan Bizaya yake goyon baya. Ai kuwa yana ji ya fara yayatawa, tayadda kowa saida yaji meke faruwa, a wani yanayi na tabbatar da cewa Ikenga bazai iya cewa a'a ba! Abin mamakin shi ne, kana kallon Ikenga kasan kai komo yake da zuciyarsa, akan ko ya yarda ko a'a. Wanda a gaskiya, kowa zaiyi mamakin hakan, musamman duba ga yanayin tsananin buwayar ƙarfi da kowa yasan Ikenga da shi, shi-shi kaɗaine a iyakacin tarihi tsahon lokaci wanda aka taɓa samu ya fafata da Yarima Deniz Bizaya acikin filin horonsa kuma baije ƙas ba. Amma ganin cewa yana kokwanton amsawa Bizaya wannan abu, sai ya fara bawa mutane mamaki, kuma kan kace meye wannan tuni ƙus-ƙus ya fara tashi akan cewa ko dama Ikengan da ake faɗa da labaran faɗansa da Deniz duk ba gaskiya ne. Amma acikin wajen manyan baƙi kuwa, tun ɗazu da wannan ƙusa ta jan dinare ta bayyana, a karon fari Asifu yayi wa Sarki Deniz Iluru magana, "lallai Deniz Iluru zanso naga yadda Bizaya zai taso. "Wataƙila ma yazo ya fika!!" Maganar da wasa ya faɗe ta, amma acikin idanunsa idan ka kula zaka ga nufaƙa a can ƙasa, kuma da yake shima Deniz ba na yau bane, tuni ya gane hakan, inda kawai ya bashi ɗan ƙaramin murmushi mai ƙunshe bayanai kalakala. Amma abinda mutane basu sani ba shi ne duk wanda bai taɓa shiga cikin Marakana ba, to bazai taɓa sanin maike faruwa aciki ba. A faɗansu na kwanaki da suka wuce, Bizaya ya samu damar saka Ikenga acikin Marakana, lamarinda saida yasha matuƙar wahala aciki kafin ya iya fitowa. Amma kuma yanzu ga abinda Bizaya ya zo dashi. Tunda jimawa Ikenga ya rantse da mahaliccin Bayajiddan farko, wadda ita ce mafi girman rantsuwarsa, cewa saiya zo na ɗaya a wannan gasa. Wanda wannan wani mataki ne na farko acikin tsaretsaren daya shirya zaibi wajen ɗaukar fansar abinda ya faru da ƙasarsa da danginsa! To amma kuma ko ma a wanne yanayi ake ciki, yana daga cikin halayen Ikenga shi ne, baya son abinda zai ɓata masa suna ko kaɗan. Saboda haka yana kallon dariyar dake kan fuskar Bizaya, ya kuma ji abubuwan da ƴan kallo ke faɗa, da kuma yadda alƙali Gali yake ta ƙara zuzuta maganar, cikin isa ya amsa cewa ya yarda. Lamarinda yasa wajen yai tsit, ana jira aga mai zai faru a gaba. MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 41: Shaibal shisu Takun Sarki Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos . Deniz Bizaya dariya kawai yayi, gami da ƙara taku ɗaya gaba, lamarinda yasa waɗannan ƙososhi guda takwas dake bayansa ɓacewa ɓat daga inda suke a sama kansa. Kafin daga bisani su bayyana a gaban Ikenga, inda suka kewaye shi, kuma suka ci gaba da matsawa suna rufe shi, har saida ya zamo ba'a iya ganin ko da rigar Ikenga, sun rufeshi ruf. A dai-dai wannan lokaci ne Bizaya yayi wata ƴar ƙaramar dariya gami da cewa, "daƙiƙar ka ta farko ta fara, Ikenga! "Saura daƙiƙa hamsin da tara!" ƴan kallo najin wannan batu suka fara shewa su na ihu su na kiran sunan Bizaya. Acikin zuciyar Deniz Bizaya yana da cikakkiyar amannar cewa indai mutun Izzarsa bata haura shekaru dubu ba, to lallai bazai iya fita daga cikin wannan kurkuru ta ƙusar tsafi ba. Kuma yasan Izzar Ikenga bata haura shekara ɗari ba, saboda haka yana da nutsuwa acikin ransa cewa tabbas yayi nasara. Idan kuma Ikenga ya iya fita daga ciki to lallai abinda mahaifinsa sarki Deniz Iluru ya labarta masa akan tsakanin Ikenga da ƙabilar Ururu gaskiya ne. Daga waje babu abinda ake gani sai rumfar waɗannan samudawan ƙusoshi. Acikin wannan ƙusoshi kuwa, Ikenga ne ya tsinci kansa acikin wani ɗaki, wanda yake a kewaye da katangu iyakacin ganinsa. Kowacce katanga anyi tane da irin wannan jan dinare na wannan ƙusoshi. Kuma idan da zaka lissafa, zaka ga a kewaye da wannan ɗaki adadin waɗannan katangu guda dubu takwas ne daidai da dai-dai! Kowacce idan ka ɗaga kai baka gano ƙarshenta! Kuma babu komai a wajen sai duhu! Sannna shi kuma gashi acikin ɗaki a ƙulle sannan kuma a sarƙafe da ankoki, waɗanda suma da zai lissafa su da yaga cewa guda dubu takwas ne dai-dai. Ikenga ya taɓa shigowa irin wajen sak, sai dai a wancan lokacin ankokin daya tarar guda dubu huɗu ne kawai, sannan suma katangun dubu huɗu ne kawai. Kuma yasan cewa idan yana so ya fita daga wajen saiya sare gaba ɗayan waɗannan katangu, waɗanda tsananin taurinsu bazai misaltu ba! Amma abin mamakin shi ne, tuni daƙiƙa talatin da uku sun wuce, amma Ikenga na kwance ko motsi baiyi ba! Idanunsa a buɗe, babu abinda yake sai kallon cikin duhun ɗakin nan, zuciyarsa na tunani. "Hmmm... yayi kyau da ban nuna masa dukkan fasata a karawarmu dashi a baya ba! Yayi kyau da ban nuna masa fasahar TAKUN-SARKI ba!" Ikeng ya ci gaba da magana a nutse tamkar babu wani lokaci dake jiransa, cikin ƙasaita tamkar duk duniya shi kaɗai ne sarki, "Lallai dana nuna masa bazai taɓa yarda da wannan gangancin gasar daya saka min ba. Domin kuwa lallai yayi kuskure. Kash... amma koma na nuna masa koma ban nuna masa ba, babu abinda zai canja. "Gaskiyar kawai ita ce indai baka kai matakin Izza shekara dubu ɗaya ba, to fa lallai baza ka iya tsayawa a gabana ba kai maganar Izza ba. Ballantana ma kace zaka fafata dani." To ko mai wannan saurayi mai suna Ikenga ya taka da yake wannan cika-baki haka. Bari dai muga gudun ruwansa.... Ikenga ya kira wani ɗalasimi, "Shaibal-shísu!" Wanda idan da mutun yana jin yaren Aldurish to da zai gane cewa fassarar wannan ɗalasimi yana nufin TAKUN-SARKI. Yana rufe bakinsa, takobin dake bayansa a saƙale ta fara haske, inda ɗakin ya fito fili ya bayyana cewa shima anyi shi ne da jan dinare iri ɗaya da sauran. Wannan takobi ta fara motsi da kanta, inda ta fice daga cikin ankokin nan tamkar basa wajen. Tana fitowa ta sari ankokin dake hannunsa na dama, inda nan take suka zube ƙas. Ya ɗaga hannunsa izuwa cikin bakinsa, ya cizi babban ɗan yatsansa, inda jini ya fara ɗiga. Nan take ya kai hannun goshinsa, inda ya fara zana wani tambari mai kama da Miyura da jinin. Yana gamawa a dai-dai wajen wata Miyura ta musamman ta bayyana. Babu komai acikinta sai wasu zanen idanu guda uku, kowanne a kusurwa daban, haɗe da wani jan layi a tsakaninsu! Wannan Miyura na bayyana yai wata dariya, sannan kai tsaye ya miƙe, ya kuma miƙa hannu ya damƙi takobinsa dake kan iska! Ya ja dogon numfashi, ya ɗaga ƙafarsa ta dama yai taku ɗaya da ita. A dai-dai lokacin da yai wannan taku, dukkanin waɗannan ankoki dake ɗaure ajikin sa suka juye suka koma takubba. Idan ka hango daga nesa, babu abinda zaka gani face wani waje mai ban tsoro, wanda babu komai acikinsa face takubba marasa adadi na jan dinare. To idan da shikenan, lallai da da sauƙi, amma Ikenga na ƙarasa dire ƙafarsa daga wannan taku na farko, waɗannan takubba suka ɓace ɓat, suna bayyana kowacce na cake a jikin wannan katangu guda dubu takwas da suka zagaye wannan ɗaki. Abu na gaba kuma daya faru shi ne, fashewa da wannan katangu sukai dukkaninsu a lokaci guda, lamarinda ya bada ƙara mai kashe kunne, da kuma ƙura wadda ta tashi sama, kuma tasa baka ganin komai. Tana lafawa babu wannan ɗaki da waɗannan katangu ko sama ko ƙasa, kaf sun ɓace ɓat! A dai-dai wannan lokaci daƙiƙa ta hamsin da ɗaya tayi! Sai dai kuma da yake na wajen wannan duniya basa ganin abinda ke faruwa, basu ga komai ba sai a daƙiƙa ta hamsin da shida inda suka ga waɗannan ƙososhi dake zagaye da Ikenga sun tarwatse ɗaya bayan ɗaya, har gaba ɗayansu suka ƙare. A tsaye, idanunsa a rufe, Ikenga ne riƙe da takobinsa tsirara a hannun hagu. Baiyi magana ba, kuma bashi da niyyar cewa komai, daga ganin yadda ya tsaya! Kai dukkan kamannin sa ma sun canja. Lallai a wannan lokaci idan da zaka kwatanta Ikenga, to zaka ce yafi kama da jan jarumin zaki irin na mutanen farko. Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne, Bizaya ya tafa hannu gami da cewa, "ahhhh...ka samu nasara!" Fuskar Bizaya babu damuwa aciki. Yana tafa hannu ya fara matsowa kusa da Ikenga, ko kaɗan a fuskarsa babu alamun baƙin cikin rashin zuwa zagaye na karshe, lamarin da hatta Gali saida yayi mamaki. Amma ina kowa idonsa na kansa, babban abinda ya ƙara jan hankalin kowa shi ne yadda suka ga Bizaya na dosar Ikenga, saboda su ga mai zaiyi yayinda yaje kusa da Ikenga. Amma bisa mamaki babu abinda ya faru, yana zuwa ya ƙarasa kunnen Ikenga yai masa magana acikin raɗa, "dama nayi tunanin akwai abinda kake ɓoyewa a fafatawarmu dakai a baya!Amma.... kana tunanin kai kaɗai ne mai shiri a ɓoye? Hmmm... Bari dai kawai da sannu wataran zamu ƙarasa wannan faɗan!" Yana gama faɗin haka yai tsalle ya fice daga cikin wajen, mutane kuwa suka bishi da kallo, cikin rashin gane mai ke faruwa, amma ina taku kaɗan yai suka nemeshi suka rasa. Tuni wajan ya rikice da ƙananan maganganu, akan abubuwan dake faruwa. Kowa dai ya gani da idonsa Ikenga shi ne yaci wancan gasa data gabata, amma abin mamakin shi ne, yadda Bizaya bai damu ba kwata-kwata, hasalima wasu tuni sun fara raɗe-raɗen yana sane ya bari aka cinye shi. Toh! Koma dai meye gaskiyar al'amarin bari mu koma kimanin kwana ɗaya kafin fara wannan gasa. ____ KWANA ƊAYA KAFIN A FARA JINZIDAL. A cikin ƙatoton ɗakin-karatu dake cikin tsakiyar fadar daular Denizawa, sarki Deniz Iluru ne sanye da ƴar shara yana yiwa ɗansa Deniz Bizaya karatun ƙarshe akan gasar da zata gudana a washe garin ranar. Sarkin ya kasance masoyin tarihi ne matuƙa, domin zaiyi wuya a samu wanda ya kaishi son tarihi da bincikarsa. Hakan nema yasa aka gina masa ƙaton ɗakin-karatun da babu irinsa a ƙasa-bakwai, domin kawai ya ringa tara al'amuran tarihi aciki. "Bizaya kana ji ko," sarkin yaci gaba da yiwa ɗan nasa bayani, "wannan yaro Ikenga da ka gayyato kuka fafata dashi, na gano acikin tarihi cewa abunda muka daɗe muna nema domin samun damar rayuwa akan doron ƙasa yana da alaƙa da shi. Ko kuma nace yana da alaƙa da abinda ya faru shekaru dubu biyu da suka wuce tsakanin kakanninsa da ƙabilar Ururu. "Labari ne mai tsayi, amma zan gaya maka kaɗan daga ciki. Abinda kawai nake so dakai shi ne ka gano mana cewa shin wannan Ikenga da gaske shi ɗinne wanda yake da wannan sirri ko kuwa. Indai ka gano haka to yama fi ace kai nasara. Domin lallai zan baka kyautar da baka taɓa zato." Koda jin kalmar ƙarshe dake magana akan kyauta sai tasa Bizaya ya daina ɓata rai. Domin yasan lallai kyautar mahaifin nasa aba ce maɗaukakiya. Da fari baiji daɗin maganar ba, domin yana so ya samu nasara a wannan gasa ya nuna kansa a duniya. Amma da yaji zancen kyautar baban nasa nan da nan ya amince. Yazo dai a tarihi cewa asali dole ce tasa daular Denizawa suka koma ƙarƙashin ƙasa saboda wani yaƙi daya afku shekaru aru-aru da suka wuce. Kuma sirrin dalilin wannan yaƙi babu wanda ya sani inba sarki Deniz Iluru ba. Shima saida ya zama sarki ya sani, saboda haka hatta Deniz Bizaya bai sani ba. A ƙa'idar daular Denizawa sai ka zama sarki zaka san wannan sirri. Amma abu ɗaya da duk manyan wannan ƙabila suka sani shi ne su na da buƙatar su dawo rayuwa a saman ƙasa koma ta halin ƙaƙa. "Saurara kaji kaɗan daga cikin tarihi." Deniz Iluru ya fara labartawa ɗansa kaɗan daga cikin tarihin duniya. ___ Hasashen waɗanda suka ce Ikenga zaiyi nasara ya dace da gaskiya. Armad Wilbafos yana gaisheku! Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 42: Takun Sarki part 2 Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos .TARIHIN ƘASA BAKWAI. Shekara ta 352 Kafin Amri. Sarki Deniz Iluru ya zaro wani ƙaton littafi daga cikin wata kantar littattafai dake gefensa. Kai daka ganin yadda shekaru sukai sheda akan takardun wannan littafi kasan yayi shekaru aru-aru a duniya. Sarkin yai duba izuwa ɗansa dake durƙushe a gabansa, kana ya fara karanto tarihi daga wannan littafi. ____ Kimanin shekaru dubu biyu da suka wuce, a wata ƙabila da akewa laƙabi da Jidda, anyi wani zamani na wani sarki mai suna Báya Azába. Asali shima sunan mutun na farko daya kafa ƙabilar aka sakamasa, wato dai bashi ne Azába na farkon da ƴan ƙabilar ke rantsuwa dashi ba. Wani tarihi babba a game da wannan sarki, wanda baza a taɓa mantawa dashi ba shi ne abinda ya faru a wannan shekara ta 352 Kafin Amri. Kuma wannan al'amari shi yasa aka sakawa wannan sarki suna Báya. Hasalima shi ne asalin dalilin da yasa aka canja sunan wannan ƙabila daga Jidda ta koma Baya+Jidda, wato Bayajidda. An rawaito cewa a lokacin da aka haifi wannan sarki, a dai-dai lokacinda ya faɗo duniya bai faɗi ƙasa ba, kuma bai faɗo a kwance ba; hasalima da ƙafafunsa ya dira ƙasa, inda akan idon kowa yai taku ɗaya, biyu, har zuwa taku bakwai yana fuskantar gabas, sannan ya faɗi! A lokacin waɗanda suka halacci wannan haihuwa suka rankaya zuwa ga sarki baban wannan yaro, suka labarta masa. Amma bai yarda dasu ba, hasalima sawa yai a daina zancen, wai acewarsa baya son a ringa yiwa ɗansa kallon wani mai aljanu ko kuma wani mai rauhanai. Haka wannan magana ta mutu a bisa umarnin sarki. Amma kuma wani abin mamaki shi ne, sai ya sawa yaron suna Báya, ma'ana bakwai kenan da yaran wannan gari da ake kira da Wilburish. A kwana a tashi saida wannan yaro mai suna Baya ya girma ya zama hamshaƙin sadauki, ya kuma ɗaga martabar ƙabilar zuwa ƙololuwa aduniya, hasalima ance har gogayya ya yi da mutane irinsu Haruta Ururu da Maruta Ururu, dama irinsu Tarifil-fakta da kansa, da dai sauransu! Ana nan ana nan, watarana ya auri ɗaya daga cikin ƴaƴan manya-manyan ƙabilar Ururu. Wadda ake kira Dáya Ururu. Lallai kowa zaiyi mamaki ace ƴan wata ƙabila sun samu auren maɗaukaka ƴan ƙabilar Ururu. Wanda abu ne da ba'a taɓa yi ba a tarihi hasalima sarki ɓisa doron ƙasa ta farko, wato Sarki Ururu da kansa ya haramta yin hakan. A cewarsa za'a lalata masa jini idan aka sirka shi da wani. Amma a wannan lokaci shida kansa ya amince da wannan aure. Kowa daga cikin manyan sarakuna sunyi mamaki sosai, hasalima da dana daga cikinsu sun nemi aure daga Ururu tun iyayensu da kakanninsu sama da shekaru dubu amma an hana su. Yau gashi an bawa wannan yaro mai suna Baya ɗan gidan sarki Azába. Saboda haka hankalin duniya ya tashi, duniya ta girgiza. Babu yadda ba'ai ba a hana wannan biki ba, amma saida ya afku. A ranar wannan biki duk wani wanda ya isa a duniya saida yaje domin ganewa kansa wannan al'amarin mamaki. Dáya Ururu sanye da baƙaƙen idanuwan ta da kuma farar fata mai walƙiya samfurin jarirai irin wadda bata taɓa ganin ƙura ba. Ta fito sanye baƙar rigar ta kalar idanunta. Lallai ko acikin Ururu, Dáya na daga cikin kyawawa ababen misali. Labaranta na daga cikin waɗanda ake labartawa acikin littattafan mata kyawawa a wannan zamani. Bayan biki, babban sarki Ururu yasa aka bawa Baya Azaba sarauta kuma aka naɗashi sarki daga cikin daulolin dake ban ƙasa ta farko. Bayan shekaru uku, Daya Ururu ta haifi ƴan biyu; ɗaya yaro santalele ɗaya kuma mace, ALLAH yasa yana wajen, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka karɓi haihuwarsa, wata ƴar tsohuwa mai yawan farin gashi ita ma na wajen, duk da ta tsufa da yawa a lokacin. Yaron farko daya fito, babu wani abu na musamman daya faru, amma na biyun yana fitowa ya tsaya cak da ƙafarsa kuma ya fara tafiya, bai tsaya ba saida yayi taku ɗai-ɗai har bakwai. Wannan sarki na ganin haka, abubuwan da aka gaya masa a lokacin haihuwarsa suka fara dawo masa. Tun daga lokacin ya sawa wannan ɗa nasa ido, har ya girma, kuma cikin mamaki shima yaron ya girma ya zama shahararre kamar babansa. Kuma a lokacin wannan ɗa nasa ne aka canja sunan ƙabilar ya koma Báya-Jidda, daga asalinta na Jidda. Wato ya ƙara sunan kakansa wato Báya a farkon sunan ƙabilar. A haka a haka aka ringa samun ire-iren waɗannan mutane acikin ƙabilar Jidda (Bayajidda), wanda dukkaninsu suke zama shahararru, kuma a ƙarshe su suke zama katangar ƙabilar a zamaninsu. Ana nan ana nan, abin ya fara yawaita har kusan kowa a ƙabilar yasan da zancen, duk da basu bari maganar ta fita waje ba, amma duk da haka sai suka sawa abin suna 'HAIHUWAR-SARKI', wanda daga nan aka samu sunan 'TAKUN-SARKI!' Kwatsam sai wani abu ya faru wanda har a wannan rana da Armad zasu kara da Ikenga ba'asan maiya jawoshi ba. Wani haske ya ringa tashi daga saman wannan ƙabila har tsahon kwana uku. Wanda daga baya ya ɗauke. Tun daga wannan al'amari aka daina samun waɗannan ƴan baiwa. Aka wayi gari an daina samun irin waɗannan yara kwata-kwata a wannan ƙabila. Har saida akai sama da shekaru dubunnai. Wanda hakan ya jawo cima baya wajen ƙarfi da Izzar ita ƙabilar a tsakanin tsaranta. Harma daga ƙarshe Ururu suka cire su daga layin sirakansa. Zamanin daya zo daga baya har saida aka manta da wannan al'amari na Takun-Sarki a ban ƙasa. ___ Koda sarkin yazo nan a zancensa saiya rufe littafin, ya kuma matso kusa da ɗan nasa yana cewa, "Inada labari cewa shekaru goma sha an haifi wani yaro, wanda yazo da wannan baiwa ta ban al'ajabi da ake cewa Takun-sarki. "Kuma an sakawa wannan yaro suna Ikenga! Abinda ban sani ba shi ne ko wannan yaro Ikenga shi ne dai wancan Ikengan da aka haifa da wannan baiwa. Saboda haka nake so ka gano min a yayin faɗanka dashi." Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin sarki Deniz Iluru da ɗansa Bizaya kwana ɗaya kafin a fara wannan gasa. ___ To kunji tarihin Ikenga wanda acikin jininsa akwai sirri na shekara sama da dubu biyu, sirrin da har zaisa Ururu da kansu su haɗa zuri'a da zuri'arsa. Lallai akwai tarihi mai yawa a tattare da Ikenga. Shin meye haƙiƙanin tsakanin Ururu da ƙabilar Ikenga. Shin mai yasa sarki Deniz Iluru yake so ya gano tarihin Ikenga. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 43: Karan batta Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos A wannan lokaci, alƙali Gali, cikin ɓacin rai ya sanar cewa Ikenga ne yaje zagaye na ƙarshe, inda zasu kara da Armad. Da dama dai abin bai musu daɗi ba, musamman tunda yawancin su Denizawa ne, kuma su na so suga nasu yaje zagayen ƙarshe. Amma tunda babu yadda zasuyi, kuma musamman bayanda suka ga shi kansa Bizaya bai damu ba, sai kawai suka ajiye abin a gefe, kuma suka fara zancen zagayen ƙarshe, wanda shi ya kamata ace yafi kowanne ƙayatarwa. A wannan lokaci ne, alƙali Gali ya sanar da cewa abisa doka, indai babu mai mummunan ciwo acikin waɗanda zasu buga wasan ƙarshe, to cikin awa shida masu zuwa za'a fara wasan ƙarshe. Da aka tambayi Ikenga ko yana da wani rauni da yake neman a ɗaga lokaci, sai yace shi bazai bar cikin filin bama. Yana nan a inda yake tsaye, lamarinda ya ƙara ɗaga ƙimarsa a tsakanin ƴan kallon nan. Shi ma Armad da aka tambayeshi, amincewa yayi da lokacin awanni shidan. Kamar ƙifta ido awa shida ta doso kai! Acikin wannan awa shida Nusi ta gabatowa Armad da wani labari mai daɗi. "Armad." "Na'am yaya Nusi, na shirya fa, ki daina damuwa sosai, kinji." Armad ya amsa mata cikin tsokana, a zatonsa maganar data saba zatai masa. Amma baisan wani abu ne daban ba. "Kasan mai zance maka ne a'a! Kuma nace maka ka daina cemin yaya." Nusi ta canja fuska haɗe da ɗan murmushi. Ga dukkan alamu su biyun sun fara sabawa sosai. "Indai kaci nasara a wannan fafatawar to lallai muna da damar zuwa garin Shadeniz. Domin kuwa munyi magana da ƴan uwana da muke so mu buɗe garin tare. "Kai koda bamu samu damar buɗe ƙofar garin ba, lallai zan samo maka labari akan Tarifil-fakta. Kai dai kawai ka dage kayi nasara, kaji!"

Chapter 18 of 33