Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bakwai, sannan yana sanye da wata baƙar hula da aka sarrafa da fatar aljanu zalla. Abin mamaki ɗauke a kafaɗun wannan aljani hankakan mutuwa ne baƙaƙe har guda biyu. Yana bayyana ya faɗi yai gaisuwa ga Bihanzin yana cewa, "Ya shugaba na. Mai kake buƙata?" Bihanzin ya amsa da cewa, "mahaifiyar wannan yaro na fama da cutar izza, ina so ka bata shekarun izza daga ɗaya zuwa dubu ashirin. Iyakacin yadda zai ishe ta ta warke." Aljanin ya ware samudawan hannayensa guda biyu yana cewa, "An gama ya shugabana." Nan take wani jan haske mai ɗaukar ido ya fara taruwa a hannayen wannan aljani kafin daga bisani ya karkatar da hasken izuwa gare ta. Hasken na taɓa ta jikinta ta fara girgiza kamar mai farfaɗiya. Armad yai wuf zai riƙe ta amma Bihanzin ya riƙe shi yana cewa, "Kada ka damu, shekarun Izza ne ke shiga jikinta." Haka Armad ya haƙura yana kallon mahaifyarsa wannan jan hasken na shiga jikinta tsahon lokaci. Saida akai sa'a guda acikin wannan hali sannan hasken ya ɗauke, aljanin ya dubi Bihanzin ya ce, "An gama ya shugaba na. Na bata shekarun izza dubu goma sha huɗu da dari biyu da sha uku, kuma a lissafi na zata farka nan da wata tara." Cikin sauri Armad ya durƙusa a gefenta yana share mata gumi. Yana cikin haka kawai sai yaga a karo na farko acikin shekaru uku mahaifiyarsa tayi motsi. Cikin murna yai ihu yana niyyar yin tsalle yai shewa kawai sai yaga ta buɗe ido. Ta kalli Armad, Armad ya kalleta. Nan take hawaye ya fara zuba daga idanunsa. Ta buɗe baki zatai magana amma kafin tayi magana saita ƙara komawa ta suma. Amma duk da haka murnar Armad bata ragu ba. Yana cikin haka yaji muryar Bihanzin a kunnensa. "idan ka daɗe da yawa acikin wannan waje komawa duniyar daka fito zaiyi maka wahala." Armad najin haka ya maida mahaifyarsa cikin zoben sannan cikin murna da annushuwa irin wadda ba'a taɓa ganinsa aciki ba ya biyo bayan Bihanzin suka nufo waje. Koda suka dawo cikin wannan ɗaki sai suka tarar da Nostaljiya na tsaye tana jiransu. Tana ganin murnar dake fuskar Armad ta fashe da murmushi, lallai tasan an samu abinda ake nema. Koda Bihanzin yaga haka saiya dubi Armad ya ce, "Ni zan barku anan. Ka tuna da abinda na gaya maka. Ka zama CIKAKKEN MUTUN." Babi na 100: Shawarar Armad ** Armad da Nostaljiya suka nufi hanya izuwa ɗakin da aka saukeshi. Akan hanyarsu kowa yayi shiru bai ce komai ba. Nostaljiya tana jira Armad ya gaya mata abinda suka tattauna da mahaifinta amma Armad yayi shiru. Ita kuma bata tambaya ba. Koda isarsu ƙofar ɗakin sai Armad ya shige ɗakin ba tare da yace uffan ba sannan ya turo ƙofa. Nostaljiya ta buɗe baki zatai magana amma ta fasa. Cikin ɓacin rai ta juya ta tafi. Har ta kusa ƙulewa ta juyo ta dubi kuyangar dake ƙofar ɗakin ta ce, "Ku bashi duk abinda yake buƙata, idan ya nemi ku nuna masa hanyar fita daga fada ku nuna masa." Tana rufe baki ta juya ta tafi. Armad ya faɗa kan gado yana jinta harta ƙule. Yai shiru yana tunanin maganarda Bihanzin ya gaya masa. Abu ne mai sauƙi tunda mahaifiƴarsa ta sami sauƙi ya fice daga wannan daula kada ya ƙara waiwayarta. Yaje can wani waje ya tsara sabuwar rayuwarsa cikin kwanciyar hankali. To amma Armad yasan cewa tun daga ranar da yayi rantsuwa zai tarwatsa cinikin bayi rayuwarsa baza ta ƙara kasancewa cikin kwanciyar hankali ba. Irin wannan rayuwa wadda za'ai aure a haihu a sami ƴaƴa biyar ko goma, sannan a zauna cikin kwanciyar rai har a tsufa a mutu ba tasa bace. Dama dai tuntuni abinda yasa Armad bai maida hankali ba akan shirinsa na tarwatsa cinikin bayi shi ne halinda mahaifiyarsa ke ciki. Amma ga dukkan alamu wannan ya kau. A yanzu ne lokaci mafi dacewa daya kamata ya fara aiwatar da shirinsa. Auren Nostaljiya lallai zai ɗaukaka martabarsa a idon duniya kuma zai saka rundunar sarki Bihanzin ta zama kamar tasa. Daɗin daɗawa daga abinda Nostaljiya ta gaya masa a wancan lokaci da suka haɗu, akwai rigima tsakanin sarakunan Jinzidal tayadda kowannensu zaiso yaga bayan ɗan'uwansa. Duk da cewa manufar Bihanzin ta yaƙi da sauran sarakunan Jinzidal ba lalle bane ta zama ɗaya data Armad ba, amma dukkaninsu suna da abokan gaba iri ɗaya. Matsala ɗaya ita ce; shin Bihanzin akan kansa yana so ya tarwatsa cinikin bayi ko kuma kawai yana so ya tarwatsa sarakunan Jinzidal ne? Domin zata iya yiwuwa Bihanzin yana goyon bayan cinikin bayi amma yana rigima da sarakunan Jinzidal. Armad na zuwa nan a tunaninsa ya yanke shawara, Idan har Bihanzin ya amince ce zai taimake shi ya rusa gasar Jinzidal to shima zai taimaka masa ya karya sarakunan Jinzidal. Bayan Armad ya cimma wannan matsaya saiya fito da Maikiro Inara daga cikin zobensa. Har izuwa wannan lokaci Inara bai farfaɗo ba, amma ga dukkan alamu ruwa kawai yake buƙata. Ai kuwa Armad yana yayyafa masa ruwa ya farka, inda Armad ya kwashe dukkanin labarin daya afku bayan ya suma ya gaya masa. Inara ya taya Armad murnar samun lafiyar mahaifƴarsa sannan yayi masa fatan alkhairi. --------- Armad da Inara suka kwana acikin wannan ɗaki, washe gari da safe Armad ya kaisu wannan tafki sukai wanka sannan suka ci suka sha. Bayan sun dawo ɗaki Armad ya fara jira ko zaiga Nostaljiya amma shiru har yamma ta kawo kai rana ta faɗi ba labari. Da magariba Armad ya tura ɗaya daga kuyangin dake kawo musu abinci ta kira masa Nostaljiya amma bisa mamaki hakan bata samu, Nostaljiya ta amsa amma bata zo ba. Haka ya gaji da jira har dare yayi gari ya waye. Washe gari Armad ya ƙara tura wata kuyangar, Noltaljiya tace taji amma har dare yayi bata zo. Nan take Armad ya fara shiga damuwa saboda yasan haƙiƙanin dalilin da yasa Nostaljiya bata amsa kiransa ba. Washe gari Armad ya yanke shawara ya taka yaje wajenta da kansa. Koda ya fito bakin ƙofa saiya tarar da ɗalibinsa Inara na tsaye yana gadin ƙofar. Murmushi kawai Armad yayi ya bashi umarnin yazo ya rakashi. Armad ya dubi ɗaya daga cikin kuyangin dake wajen ya ce, "Muje ki rakamu wajen gimbiya." Amma wannan kuyanga ta kada baki ta ce, "Ai ba'a shiga wannan ɓangare daga mu kuyanginta sai ita kanta, gimbiya." Maganar bata yiwa Armad daɗi ba, ya tsaya yana ta tunani kafin daga bisani ya juya ya koma ɗaki. Har ya isa bakin ƙofa sai wata dabara ta faɗo masa, yaci birki ya tsaya tare da juyowa izuwa wannan kuyanga ya ce, "muje naga wajen saboda tsaro." Kuyangar fara ce mai tsaho sanye da farar doguwar riga. Tana jin abinda Armad ya ce ta zare ido tana mamaki. Abinda bata gane ba shi ne mai Armad yake nufi da 'saboda tsaro'. To amma ba muhallinta bane a matsayinta na kuyanga ta tsaya tana yiwa Armad tambaya, saboda haka ta shige gaba ta fara tafiya, su Armad suka bi bayanta. Abin mamaki sai Armad yaga sun ɓulle ta wata ƙofa wadda ta shigar dasu wani ƙaton fili. Duk kewayen da Armad yayi na kwana biyu bai san da wannan filin ba. Haka suka ci gaba da bin kuyangar har suka ƙarar da wannan fili suka nufi ɓangaren arewa, sannan daga bisani suka iso wata farfajiya mai yawan bishiyun dabino. Wannan bishiyun dabino sun kekkewaye wannan sashi ta yadda ba'a iya gano cikinsa sosai. Suna ƙara matsowa sai Armad ya fuskanci cewa wannan ɓangare an raba shi ne izuwa gida uku manya-manya. Abin mamaki shi ne hatta katangar da aka kewaye wannan waje da zinare aka yaɓe ta. Komai kawai walwali yake. Nan take Armad ya fara tunani yana mamakin irin dukiyar dake cikin wannan fada. Suna isowa gindin wannan bishiyu sai wannan kuyanga ta tsaya tana nuni da ginin dake tsakiyar gine-ginen guda uku. "Wancan ne na tsakiyar. Na ɓangaren dama kuma na ƴarima Kiru ne, na ɓangaren hagu kuma na yarima Hasanu me. Amma daga nan babu wanda yake da damar haurawa sai su ƴaƴan sarkin uku." Tuni Armad ya gama lissafa yadda zai biyo dare ya haura wannan katanga sai kawai wani haske mai kashe ido ya haske masa ido. A zuciyar Armad ya gane wannan haske amma yana ji a ransa wataƙila kawai dai idonsa ne. Amma ba jimawa wanda ke ɗauke da hasken ya bayyana daga bayan wannan bishiyun dabino. Lallai Armad yayi gaskiya, domin kuwa ba idonsa bane. Wannan haske hasken Farar-takobi ce, wato takobin yarima Kiru Sisiyu ɗan sarki Bihanzin wanda suka fafata da Armad shekaru da dama da suka gabata. Kiru ya fashe da dariya tun kafin ya iso. "Ko baka zo nema na ba zan neme ka. Domin kuwa bamu idar da fafatawarmu dakai ba a wancan zamani. Da sannu zaka gane ƙarfin Farar-takobi na." A zahiri Armad ba wajen Kiru yazo ba, amma babu yadda zaiyi. Wannan fafatawa kamar anyi ta ne an gama. Armad ya fara magana yana leƙen saman benen ko zai hango Nostaljiya, "K....kiru, lallai naji daɗin ganinka, domin kuwa ina neman wanda zan wasa takobi na dashi." ...... Allah cikin ikonsa a yau mun riski posting na Dari 100 wanda ya kusan kai mu wajen watanni Hudu, A lokacin da Dr Abdullahi ya fara post na littafin nan sai da yayi shekaru Biyu 2 kafin ya kawo chapter 100, , In bazan manta ba tun a shekarar 2016 Dr ya fara rubuta littafin Magajin Wilbafos wanda har yanzu yana kan aikin rubutawa bai idar ba . Cikin watanni mu gashi mun kada chapter 100 har mun kusan mu riski Dr, ......... Toh jama'a zan dan Huta na Sati Daya kafin na cigaba da kawo maku littafin, amma kafin nan in baku manta ba lokacin da muka idar da chapter 1-50 mun hada su gaba daya a matsayin document inda na saka su a wepsite dina, Haka wannan karon ma zamu hada tun daga chapter 51-100 a waje guda cikin manhajar document mu sake shi a wepsite namu na Ebook . Ebook din zai fito daga nan zuwa JIBI sai a ankare --------- Na barku lafiya its Shuraih Usman Inkiya 99% MAGAJIN WILBAFOS Fita na biyu 2 Marubucin littafin Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 33 of 33