Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mabiya a wannan kurkuku.
Bawai dan ina buƙatar su ba, domin kuwa kai kaɗai ne
abinda ya shigo dani wannan kurkuku, kuma a kowanne
lokaci naga dama zan iya fita cikin sauƙi. Alƙawarurruka
na guda huɗu suna nan, abinda kawai kake buƙatar kayi
shi ne ka durƙusa a ƙasa kayimin mubayi'a."
Armad yai shiru yana sauraron Ikenga, abubuwa da
dama sun ɗau hankalinsa acikin bayanan Ikenga. Akwai
yiwuwar ƙarya Ikenga yake akwai kuma yiwuwar gaskiya
ne. Bayan tsahon lokaci yana tunani sai yayi murmushi
sannan ya bawa Ikenga amsa a nutse.
"Manufarka mulki, manufa ta ceto wanda basu da ƙarfi
daga tafarkin cinikin bayi, lallai alƙiblarmu ba ɗaya bace.
Sannan kuma ina so ka sani koda alƙiblarmu ɗaya ce
kaine zakai mun mubayi'a ba nine zanyi maka ba. Kakana
Eyriyon wanda na gaji fasaharsa sarki ne na duniya baki
ɗaya. Ƙabila ta mulki dukkan duniya. Ina da ƙarfin
fasahar da jikina bazai taɓa halaka ba, bana buƙatar ci ko
sha. Ina da ɗalasimai wanda sun girmi lissafinka. Bama
kaiba Ikenga, babu wanda ya isa nayi
masa mubayi'a a wannan zamani. Kamar dai yadda na
gaya maka a farko, idan kana ji zaka iya hanani aiwatar da
manufa ta, to ka gwada.
Armad na rufe baki ya juya ya fice.
......
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 88: Sabuwar Fasaha
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Lallai akwai raini acikin abinda Ikenga yayi wa Armad,
domin duk wanda ya nemi kayi masa mubayi'a to lallai
yana nuna cewa yafi ka ƙarfin izza. Wannan shi ne abinda
yake ta kai-komo a zuciyar Armad tun bayanda suka rabu
da Ikenga.
Babban abinda yafi ɗaukewa Armad hankali shi ne yadda
Ikenga yake nuni da cewa yana iya shiga da fita ta cikin
Bango ba tare da matsala ba.
A halin yanzu Armad baida lokacin tsayawa yayi nazari
akan labaran da Ikenga ya bashi, ko gaskiya ko ƙarya.
Saboda haka ya yanke shawara zai ƙara gwada ficewa ta
cikin wannan bango. Idan ya wuce shikenan, idan kuma
bai wuce ba saiya koma izuwa Babara da mutanen
Lamarudu Wilbafos.
Amma Armad yana da cikakkiyar masaniyar cewa ƙara
shiga Bango ba tare da wani shiri ba lallai halaka ne,
saboda haka tuni Armad yai amfani da kwakwalwarsa ya
gano wata sabuwar fasaha. Hasalima akan hanyarsa yake
ta gwada wannan fasaha.
Wajenda Armad yake tafiya yayi nisa da Bango sannan
yana da ƙarancin ƙanƙara. Amma wata irin iska ce mai
ƙarfin gaske take kaɗawa. Babu gida gaba babu gida baya,
babu wani rai a wannan waje face Armad. Tuni Armad ya
alkinta kansa da kayan sanyi daga cikin zoben da
Nostaljiya ta bashi. Yana tafiya yana ƙara sauri, yasan dai-
dai inda zashi.
Lallai wannan kurkuku ta musamman ce, domin babu
wanda ake ƙullewa acikin ɗaki ko kuma a bayan kanta.
Fili ne kawai fetal iya ganinka. Kowa yana da damar yayi
yawo acikin ta, yayi gini ma idan yana so, ya haihu ya
rayu, yayi duk abinda yaga dama. Amma dai bazai fita
daga cikinta ba har abada. Wannan shi ne sharaɗin
wannan kurkuku. Tuni Armad ya samu taswirar wannan
kurkuku a hannun Sailári, wanda da ita ya gano dai-dai
wajenda yafi ko'ina sharri acikin kurkuku. Wajenda
mutanen cikin kurkukun basa ko ziyara.
Shi kuwa Armad wannan waje nan ya tunkara da niyyar
gwada sabuwar fasahar da yake ƙoƙarin amfani da ita
domin fita daga wannan kurkuku.
Ba jimawa Armad ya bayyana a tsakiyar bishiyu dogaye
masu kama dana tsamiya. Abu na farko daya fara yi masa
sallama shi ne kukan Dordor da aljanu. Koda jin haka sai
Armad yai murmushi tare da cusa kai cikin duhuwar
dajin dake gabansa. Ai kuwa yana shiga wata ƙatuwar
damisa wadda tafi girman duk wata damisa daya taɓa
gani ko ji ta bayyana a gabansa. Babu alamun jira ko
haƙuri a tattare da ita a yayinda ta afko masa da saurin
gaske tana dalalar da yawu.
Armad ya rufe idonsa domin banbance wacce irin
damisa ce. Kasancewar duk jinsin dabbar da suke iya
amfani da izza an ware su, kuma su ake kira da ALJANUN-
DABBOBI, misali idan wannnan damisa tana iya amfani
da izza sai ace mata aljanar-damisa. Aljanun dabbobi
suna da matuƙar banbanci da sauran dabbobin dawa
wanda basu da izza a wajen sauri da tsananin ƙarfi da
rashin imani. Kuma da yawansu abincinsu shi ne naman
mutane. Wannan aljanun-dabbobi su ne dalilin da yasa
jama'ar wannan kurkuku suke gujewa wannan daji.
Armad na rufe ido yaji yanayin-izza a tattare da wannan
ƙatuwar damisa, lamarinda yasa ya tabbatar cewa
aljanar-damisa ce. Amma bisa mamaki duk da wannan
damisa tana gab da cimmasa Armad bai motsa daga inda
yake ba, kuma bai maida jikinsa walƙiya ba.
Suna yin arba da wannan damisa ya buɗe baki ya kira
ɗalasimin KABAN'SHÍSU. Lamarinda yasa ya ɓace daga
inda yake ya bayyana a bayan wannan damisa. Yana
ɓacewa yaji wannan damisa taci birki tana laluben inda
yake. A dai-dai wannan lokaci Armad yaji shekarun
Izzarsa dubu sun girgiza, nan take ya fara ganin dishi-
dishi yana jin jiri. Yaji wani tari mai ƙarfi ya taso masa,
kafin yai wani abu ya fara tari yana aman jini. Wannan
damisa najin tarinsa ta juyo izuwa gareshi da mugun
nufi.
Armad dai yasan maiya taka, domin tunda yake bai taɓa
karya dokar da kakansa Zaikid ya ɗora masa ba akan
ɗalasimin Kaban'shísu, wato bai taɓa yin amfani dashi
sama da sau biyu a shekara ba. Amma a wannan lokaci
yayi amfani dashi sau biyu a wata ɗaya.
Armad na cikin wannan hali wannan damisa ta ƙara
cimmasa, amma ya rufe ido ya ƙara kiran ɗalasimin
Kaban'shísu. Inda ya ƙara ɓacewa ya bayyana a bayan
wannan damisa. Nan take jini ya fara fita daga idanunsa
da kunnuwansa. Armad yai wata ƙara saboda tsananin
zafin da yake ji, tamkar ana jera garwashi akan fatarsa.
Amma wannan damisa ta ƙara yiwowa kansa, inda yai
ƙaraji tare da ƙara kiran wani ɗalasimin a karo na uku.
Nan take yaji mutuwa ta fara yi masa sallama, ba shiri ya
juye izuwa gundarin walƙiya. Amma duk da haka saida ya
faɗi ƙasa sumamme.
Wannan damisa ta faɗa kansa da niyyar tsinke masa kai,
amma koda hasken walƙiyarsa ya dake ta saita jada baya.
Bayan tsananin ɓacin ran rasa abincinta ta ɗanyi turje-
turje da gurnani kala-kala kafin ta bar wajen.
Armad yaci gaba da zama a wannan halin tsahon kwanaki
shida, inda bayan ya farka ya tsinci kansa a kewaye da
aljanun-zakuna farare masu jajayen idanuwa.
Koda tashinsa saiya fuskanci jiransa kawai suke ya juye
izuwa mutun su cinye namansa. Tunda baza su iya
cinyeshi a haka ba to bari su jira.
Armad yai murmushin izza tare da juyewa izuwa mutun.
Wannan aljanun-zakuna guda uku suka nufo shi gadan-
gadan. Armad ya ƙara kiran ɗalasimin Kaban'shísu ya
bayyana a nesa dasu kimanin taku goma. Yana bayyana
ya ƙarajin irin raɗaɗi da tashin hankalin da yaji a baya. Su
kuwa wannan zakuna suka ƙara yiwowa kansa. Armad ya
ƙara kiran ɗalasimin ya ƙara ɓacewa ya bayyana ƙafa
goma gaba da inda yake. Wannan zakuna suka ƙara
fusata suka tisa shi.
A haka a haka saida Armad ya kira ɗalasimin Kaban'shísu
sau biyar sannan ya faɗi ƙasa sumamme. Wannan zakuna
sukai iyayinsu su halaka shi amma tuni ya juye izuwa
walƙiya haka suka haƙura.
Bayan kwanaki ya ƙara farkawa ya ƙara maimaita irin sak
abinda yayi. Sannan ya ƙara maimaitawa. Ba jimawa
Armad ya kai tsahon kimanin wata uku a wannan daji
yana gwada amfani da wannan ɗalasimi. Bayan ya samu
nutsuwa ya koyi abinda ya kawo shi saiya juya izuwa
Bango domin jarraba wannan fasaha.
Ita dai wannan sabuwar fasaha ta samo asali ne daga
ilmin Armad na ɗalasimin Kaban'shisu da kuma ƙarfin
fasaharsa ta walƙiya. Da ita zai iya tafiya cikin tsananin
sauri daga wani waje zuwa wani tayadda za'a ga kamar
ɓacewa yai. Tun a sanda ya shiga Bango a karo na farko
ya gano cewa shi kansa ɗalasimin Kaban'shísu bawai
ɓatarda mutun yake ba, yana saka mutun yai tafiya cikin
tsananin sauri tayadda za'a ga kamar ɓacewa yayi. To
idan kuwa haka ne, idan ɗalasimi guda ɗaya ya wutar
dashi rabin hanya an watsoshi waje, to idan yayi amfani
da ɗalasimi goma a lokaci ɗaya zai iya wucewa.
Daɗin daɗawa wannan sabuwar fasaha ta Armad zata
bashi damar cin galaba akan abokan fafatawarsa cikin
sauƙi. Domin kuwa komin sharrin daya tunkaro shi zai
iya ɓacewa ya dauje masa. Sannan zai iya bayyana a
bayan abokin fafatawarsa ya aiwatar da harinsa ba tare
da an ankara ba.
Armad yayi niyyar sakawa wannan fasaha sabon suna
amma daga ƙarshe ya yanke shawarar yaci gaba da
kiranta da Kaban'shìsu.
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 89: Hannun Aradu
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Armad na tafe yana goge takobinsa, rabonsa da amfani
da takobi an kwana biyu. Kai hatta harin ƙawanyar-walƙiy
a an daɗe rabonda yayi amfani dashi. A iya tunaninsa tun
bayan fafatawarsa a gasar Jinzidal. A halin yanzu
hannunsa ƙaiƙayi yake, saboda haka maimakon ya
kewaya ya zagaye wannan daji sai ya yanka ta tsakiyarsa.
Ai kuwa ko taku goma bai yiba Dordor uku masu kai ɗai-
ɗai da wasu aljanun-shirwa guda biyar suka tunkaro shi.
Dordor suna kawo masa hari ta ƙasa, shirwa na kawo
masa hari ta sama. Armad yai murmushi tare da dunƙule
hannunsa na dama. Sannan ya juyarda dashi izuwa
walƙiya ya daki iska dashi yana cewa, "HANNUN-ARADU."
Haka na faruwa wata farar walƙiya mai layin kore-kore ta
fara ɓulɓula daga hannunsa tare da afkawa wannan
shirwowi da Dordor. Wannan shi ne karo na farko da
Armad yayi amfani da wannan fasaha mai suna Hannun-
aradu, wadda ta banbanta matuƙa da ƴar walƙiƴar daya
saba amfani da ita ada. Idan ka kalli dunƙulen hannunsa
na dama zaka ga ya juye izuwa walƙiya sannan kuma
walƙiya tana ɓulɓula daga cikinsa tamkar ana ambaliyar
ruwa. Duk abinda wannan walƙiya ta taɓa saita narkar.
Babu wani abu dake tsaye a gabanta face Armad
Wilbafos. Bayan daƙiƙa bakwai Armad ya saki hannunsa
ya ɗauke walƙiyar sannan yai duba izuwa abinda ya
aikata.
Dukkan abubuwan dake gabansa sun ƙone ƙurmus, babu
shirwa babu Dordor babu koda bishiyu da suka rage.
Babu komai sai ƙarfin izzar Armad wilbafos. Wannan daji
ya ƙone ƙurmus tamkar ba'a yishi ba. Daga inda Armad
ke tsaye yana hango Bango.
Armad yai murmushi tare da tunkararsa. Tuni dai ya
gano wata hanya da zaiyi amfani da ita domin ƙirƙiro
sabuwar fasahar takobi amma ba sauri yake ba zata iya
jira. Saboda haka ya tunkari wannan Bango gadan-gadan.
Yana isa ya juye izuwa walƙiya sannan ya kira ɗalasimin
Kaban'shísu.
Armad ya tsinci kansa a tsakiyar wannan ruwa mai kauri
wanda ke narka jikin ɗan adam. Yana bayyana ya ƙara
ido biyu da wannan baƙaƙen idanuwa na Ururu. Amma
tuni Armad ya shirya musu, kafin wani abu ya faru tuni
ya ƙara kiran wani ɗalasimin, ya ɓace daga inda yake ya
bayyana a gaba da inda yake. Wannan idanu suka ƙara
bayyana suna neman haɗiye amna Armad ya ƙara
ɓacewa da taimakon sabuwar fasaharsa ta Kaban'shisu.
A haka saida Armad yayi amfani wannan ɗalasimi sau
goma, a kowanne lokaci yana ƙara kusantar ƙofa amma
wannan idanu suna ƙara cimmasa. Armad yasan
iyakacinsa ɗalasimi goma, kuma indai ya wuce haka to a
take zai fara aman jini ya sume. Amma babu yadda zaiyi,
baiyi tunanin ɗalasimi goma baza su isa ba. Saboda haka
ya rufe ido ya ƙara kiran wannan ɗalasimi a karo na
goma sha ɗaya. Abun mamakin shi ne duk da yana
walƙiya amma hakan bai hanashi aman jini ba da jin zafi
da radaɗin wannan ɗalasimi ba.
Gabda Armad zai sume ya ga wani haske ya rufe masa
ido, bashi da tabbas mene ne amma yana fatan hasken
fita daga kurkukun ne.
**
A can doron ƙasa na farko kuwa wannan sarewa dake
gadin wannan kurkuku ce ke ƙara bada labarin wani mai
ƙoƙarin ficewa daga cikin kurkuku. Amma a wannan
karan ya samu damar fita, sannan kuma abin mamaki
irin ruhi ɗaya ne sak da wancan mutun da yayi ƙoƙarin
fita a watan baya.
Nan take wannan sarewa ta bada umarnin ayi maza-maza
a kamo wannan mutun sannan a gane mene ne alaƙarsa
da wancan mutun da yayi ƙoƙarin guduwa a watan baya.
Shin duk mutun ɗaya ne bai mutu ba ko kuma wani ne
mai irin ruhinsa.
Gidan Uznu Ururu shi ne gidan da aka ɗorawa alhakin
kamo wannan fursuna.
**
Al'ada ce sananniya kwararrun matuƙa jirgin ruwa sukan
sakawa jiragensu sunaye. Wani suna kawai na sha'awa ne
wani kuma yakan dace da tsarin jirgin. A dai-dai wannan
lokaci wani madaidaicin jirgin ruwa ne ke tafiya akan
Bangon arewa ya nufi doron ƙasa ta huɗu, daular Sisiya.
Sunan wannan jirgi Fataken-dare. Yakan ɗauki jama'a
aƙalla ɗari biyu da hamsin zuwa ɗari uku, kuma shaidar
safararsa tana tsakanin doron ƙasa ta uku data huɗu.
Duk da kasancewar yawan ƙofofin Eycigan da ake tafiya
ta cikinsu amma duk da haka masu sana'ar jirage basu
rasa abinci ba, indai ka yiwa jirgin ka shaidar kariya ta
hukumar tafiye-tafiye ta sarakunan jinzidal to zaka samu
fasinja. Rashin yin shedar na nuna kana daga ɓata gari ku
kuma ɓarayin ruwa.
Jirgin Fataken-dare na tafiya sannu a hankali iska na
kaɗashi izuwa hanyarsa. Fasinjojin wannan jirgi na
harkokin gabansu cikin kwanciyar hankali, sun san nan
da wata ɗaya mai zuwa zasu isa garuruwansu a daular
Sisiya.
Shi kuwa kyaftin ɗin wannan jirgi sunansa Bisaiya Sisiyu.
Asalinsa ɗan daular Sisiya ne kuma tunda ya taso yake yin
sana'ar kwandasta a irin wannan jirage, yanzu gashi a ɗan
shakara talatin ya mallaki nasa jirgin. Duk da bashi da izza
amma yana da ma'abota izza guda shida dake aikin tsaro
a jirginsa. Kuma ko a wannan lokaci mutun biyu daga
cikinsu na tare dashi.
Bisaiya ya dubi ɗaya daga cikin ma'aikatan ya ce, "idan
iska ta bamu dama nanda kwanaki ashirin zamu isa. Shi
yasa dole saina ɗauki ma'abocin aljanin iska aiki."
Mutumin sanye da fararen kaya ya gyaɗa kai yana cewa,
"gaskiya ne, kyaftin Bisaiya. Amma duk da haka ina
tunanin zamu isa a yadda muka tsara."
Bisaiya baice komai ba, kawai yaci gaba da kallon gangar
ruwan dake gabansu. Yana sane da cewa ƙaro wani
ma'aikacin dole zai jawo ya kori ɗaya daga cikin
ma'aikatansa shida dan bazai iya biyansu ba, amma dole
yana buƙatar wanda zai ringa ɗaure masa 'iska' a yayin
tafiyarsu.
Yana cikin wannan tunani ne sai ya hango wani abu
kwance a gaban jirginsu. Abun yana ta iyo yana sama da
ƙasa kamar ƙirgin itace. Da farko Bisaiya bai ɗauki wani
abu ba saida yaga abin yana motsi kamar ɗan adam. Nan
take ya haska fitilar jirgin saitin abun domin ya
tabbatarwa da idonsa. Ai kuwa wani saurayi ne kwance a
sume ba kaya a jikinsa.
Abu na farko daya fara zuwa ran Bisaiya shi ne wannan
ɗaya ce daga cikin dabarun ƴan fashin ruwa. Domin ka
tsaya ceto suyi maka fashi.
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 90: Sa'a ko Kaddara
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
"Ɗakko shi." kyaftin Bisaiya ya umarci ma'aikacin dake
gefensa daya ɗakko gangar jikin wannan saurayi dake
yawo akan ruwa.
Ba jimawa aka shiga da wannan saurayi cikin ɗakin duba
marasa lafiya na jirgin tare da kirawo wani siririn mutun
sanye da fararen kaya ya dubashi. Idan kayi duba izuwa
wannan saurayi zaka ga ba wani bane illa Armad
Wilbafos.
Shi kansa kyaftin Bisaiya bai san mai yasa ya ceto shi ba,
duk da kuwa yana tunanin ƴan fashi. Amma koda yaga
Armad sai ya zare ido cikin mamaki tare da fara tunanin
mai ya kamata yayi.
Abin mamaki duk da Armad na numfashi amma sun kasa
farkar dashi.
"Ransa yana hannun ALLAH. Amma tashinsa zaiyi
wahala." Likitan ya bayyana wa kyaftin Bisaiya bayan yayi
iya yinsa ya kasa.
A kwana a tashi saida Armad yai sati ɗaya cir a sume kafin
ya farka. Bayan ya buɗe ido ya fara ganin dishi-dishi kafin
daga bisani ya warware ya fara jin surutan fasinjojin
jirgin suna tattauna rayuwa.
Armad ya daddagira ya sakko daga kan gadon inda ya
nufi bakin ƙofa. Jikinsa na nan yadda yake babu gajiya ko
tsami. Yana isa ya buɗe ƙofar, hasken rana ya haske masa
ido lamarinda yasa ya kare da hannunsa. Iska mai ɗumi
ta daki fuskarsa lamarinda ya gano lallai ya rabida
wancan sanyi da ƙanƙara na cikin kurkuku.
"Kunga ya farka... "
"Ashe zai rayu.."
"Yana da ƙarfin ruhi..."
"Kai yaushe rabon da naga wanda yai sati a sume kuma
ya rayu.."
"Ko maiya sameshi?"
Haka dai Armad ya fara tsintar maganganu fasinjojin
daga nesa. Ga dukkan alamu kowa ya san da zuwansa.
Armad ya gano cewa ɗakin cin abinci ya buɗe bayanda ya
fuskanci cewa jama'ar na zaune a zagaye da tebura na
abinci.
"Koma ka kwanta karka faɗi.." Likitan jirgin ya tallafi
Armad ta gefe. Abinda bai sani ba shi ne Armad tar yake
jinsa kamar ya rungumi zaki. Juyewar jikinsa izuwa
walƙiya yana bashi damar shanye gajiya da ciwo cikin
ƙanƙanin lokaci.
Armad ya dubi likitan ya ce, "Ehmm... Nagode amma naji
sauƙi. A ina nake?"
Likitan ya amsa da cewa, "kana cikin jirgin Fataken-dare,
muna hanyar zuwa doron ƙasa ta huɗu daular Sisiya."
Armad najin wannan jawabi yai murmushi tare da cewa,
"Sa'a ko ƙaddara?"
Likitan bai gane mai Armad ya ce ba saboda haka ya
tambaya, "Sa'a ko ƙaddara? Mai kake nufi?"
Armad ya amsa da cewa, "Ba komai. Kawai dai nima
hanyar Sisiya nayi, ban sani ba ko zaku taimaka ku isar
dani domin bani da ko sisi tare dani amma idan muka isa
akwai wacca zata ranta min na biya ku."
Koda jin wannan batu sai Bisaiya ya taso a fusace, "Da
kuɗinka nake buƙata da ban ceto ka ba. Kai dai kawai ka
samu sauƙi kurum."
Armad na ganin Bisaiya ya gane shi ne kyaftin din wannan
jirgi. Saboda haka yai shiru yana kai-komo da karamcin
da Bisaiya yake nuna masa a zuciyarsa kafin ya kyaɗa kai
cikin murmushi yana godiya. "Nagode."
"Zo ga abinci." Bisaiya ya kira Armad izuwa teburinsa.
Tuwo da nama haɗe da kifi soyayye sune cike a kwanon
da aka turowa Armad. Cikin annushuwa ya fara danna
tuwon nan yana korawa da sanyayyar fura samfurin
daular Sisiya. Kowa idonsa na kansa amma ko a jikinsa.
Kan kace meye wannan tuni ya gama da kwanukan dake
gabansa.
"Bari a ƙaro ma, lallai yunwa kake ji." Bisaiya yai odar
wasu kwanukan. Armad baice a'a ba, koba komai baya so
mutanen wannan jirgi su fara yi masa kallon aljani wanda
baya buƙatar abinci.
Bayan ya ci ya sha sai Bisaiya ya kaishi wani ɗaki domin
ya huta. "Ga ɗakinka kafin mu ƙarasa. A lissafi na nanda
sati biyu zuwa uku zamu isa."
Armad yai godiya, har ya doshi ɗakin saiya waiwayo ya
dubi Bisaiya yana cewa, "baza ka tambaye ni daga ina na
fito ba. Baka tsoron ɓarayin ruwa ko kuma na jawo muku
wata matsalar?"
Bisaiya yai murmushi, "Tuni nasan ko kai waye, Armad
Wilbafos. Amma ka kwantar da hankalin ka babu wanda
ya gane ka acikin fasinjoji na."
Nan take Armad yaja da baya ido a zare yana cewa, "mai
kake nufi? Ya akai kasan suna na?"
Bisaiya ya kada baki ya ce, "Kada ka manta hotunan ka
sun baza ko'ina. Kuma duk wanda ke karanta jarida yasan
fuskarka. Saboda haka nasa likita na yaɗan kyara maka
hanci da baki da ido." Yana magana ya nunawa Armad
mudubi.
Abu na farko da Armad ya gani shi ne hancinsa ya loma
ciki sannan ya gajarce kamar na biri. Idanunsa sun futo
waje sun zama manya-manyan kamar na masu maƙoƙo.
Sannan bakinsa ya ƙara faɗi kamar an yaga. Kalmar farko
data zo bakimsa zagi ne amma ya fasa, "Kut... wa yasa ku
mai dani haka?"
Bisaiya ya dubi Armad babu alamun wasa a fuskarsa,
"Idan ban maida kai haka ba ya zanyi da fasinjoji na idan
suka gano akwai Ayrid miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar
acikin jirgin?"
Armad yai zumbur ya buɗe baki kamar wanda wani abu
ya faɗo masa, "Idan haka ne to mai yasa kai baka miƙa ni
ba? Ko kana jira ka isa gaɓa ne ka miƙa ni?"
Bisaiya ya amsa da cewa, "ba zance maka ka yarda dani
ba, amma nayi maka alƙawarin baza ka samu matsala
daga jirgi na ba. Shekarar mahaifina bakwai a kurkuku
yanzu, saboda an saka kuɗi akansa akan abinda bai kai ya
kawo ba. Kaima ina da yaƙinin ba wani abu ka aikata ba
aka dora wannan kudi akanka. Kawai dai ana so a wanke
gimbiya Nostaljiya ne a ɗora maka laifi saboda kai baka
da galihu. Idan baka yadda dani ba zaka iya sauka a
kowanne lokaci." Yana rufe baki ya juya ya bar Armad a
tsaye a wajen.
________
Shuraih 99%
.
Ai tunda aka ce za'abani Gimbiya Zahra (Nostolgiya Nara) na kidime kuma zan jajirce matuka wajen sambado maku da littafin nan har karshe,
Sai ku jirani zuwa MAKO mai zuwa ta yiwu ma ku jini Gobe, amma fa sai na ga Respond naku akan wayannan MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 91: Gashin Belbela
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Kwanan Armad shida acikin wannan jirgi yana ta kai-
komo da abubuwan dake ransa. Abu na farko gaskiyar
mutanen cikin wannan jirgi, zai iya amince musu ko
kuwa. Abu na gaba mai zaije ya tarar a daular Sisiya.
Tunda Armad yake bai taɓa saka ƙafa a babban birnin
ɗaya daga cikin garuruwan sarakunan Jinzidal ba, saboda
haka bai masan mai zai tarar ba. Yaya yanayin garin yake?
Shin wacce irin karɓa Nostaljiya zata yi masa? Abu ɗaya
da yake da tabbas dashi shi ne mahaifin Nostaljiya
Bihanzin mai dauwamammen sara bazaiyi murna da
ganinsa ba. Ko a gamuwarsa ta farko kuma ta ƙarshe
guduwa yayi dan kada su haɗu.
Duk da Armad bai ga laifin Bihanzin wajen ƙoƙarin kare
ƴarsa ba amma yana jimamin haɗuwa dashi.
Musamman duba da cewa wannan shi ne karo na farko
da zai gamu da Sarkin Jinzidal.
Sannu a hankali Armad yaci gaba da gudanar da ragowar
kwanakinsa acikin wannan ɗaki da Bisaiya ya bashi.
Lokuta kaɗan yake fita yaga hasken rana saboda baya so
wani acikin jirgin ya gane shi. A rana ta bakwai yana
kwance akan gado yana tunanin yadda rayuwarsa take
kasancewa sai kurum ya fara jin hayaniya daga waje.
Da farko Armad yayi tunanin fasinjojin ne ke caca kamar
yadda suka saba, amma ba jimawa ya gane cewa
hayaniyar tafi ta haka.
Bayan ya ɗauki daƙiƙa ashirin yana nazarin hayaniyar
saiya fuskanci ƙaraji ne kawai da ƙuwwa. Nan take
Armad ya yasan faɗa ake. Kodai ƴan fashi sun kawo
musu hari ko kuma faɗa ya kaure tsakanin fasinjojin
jirgin. Koma dai wanne ne bai shafi Armad ba. Koda ƴan
fashi ne, kowanne jirgi yana da dabarun kare kansa daga
irin haka. Rufe idonsa kawai yayi, yaci gaba da nazarin
yadda zaiyi ya gamu da Nostaljiya zarar ya isa daular
Sisiya.
Abu kamar wasa sai Armad yaji ihun ya fara raguwa,
lamarinda yasa yayi tunanin cewa anci galaba akan ƴan
fashin. Amma kuma wata zuciyar ta gaya masa cewa
lokacin yayi ƙaranci ace har an gama da ƴan fashin.
"Hmmm..." Armad yaja dogon numfashi tare da girgiza
kai. Bai san mai yasa ba amma hankalinsa yaƙi kwanciya,
saboda haka ya rufe idonsa ya fara laluben yanayin-izzar
ma'aikatan jirgin. Nan take ya miƙe zumbur ya nufi ƙofar
ɗakinsa. Yana buɗewa wani koren hayaƙi mai ratsin yalo
yai masa sallama. A ƙasan hayaƙin mutane ne fululu a
kwance sun sume.
Armad na ganin haka ya gane maike faruwa. Wannan
hayaƙi guba ne kuma shi ne dalilin suman mutanen cikin
jirgin. Koma waye ya feso wannan hayaƙi ba abokin
Armad bane.
Armad ya riƙe numfashinsa tare da tsayawa, tsaiwa irin ta
ma'abota izza, sannan kai tsaye ya afka cikin hayaƙin.
Bayan kimanin taku uku sai ya tsaya ya buɗe bakinsa ya
huro iska waje. Amma maimakon iska sai feshin walƙiya
ya fara ambaliya daga bakinsa. Kan kace meye wannan
tuni feshin mai ɗauke da walƙiya ya kawar da wannan
hayaƙi.
A wannan lokaci Armad ya gane ashe wani ƙaton jirgin
ruwa ne ɓoye cikin duhu a gaban jirginsu. Girman jirgin
yasa jirgin su Armad ya zama kama wani ɗan kwale-
kwale. Daga inda Armad ke tsaye yana hangen sunan
jirgin ansa GASHIN-BALBELA da manyan baƙi.
Armad ya dawo da hankalinsa kan mutanen da ke cikin
jirginsa. Da yawansu wannan hayaƙi yasa sun sume,
amma wasu na tsattsaye. Ga dukkan alamu hayaƙin bacci
kawai yake sawa kuma rayuwarsu bata cikin hatsari. Har
Armad zaiyi ajiyar zuciya ya godewa ALLAH saiya hango
Bisaiya kwance cikin jini riƙe da ƙirjinsa. Ƙarshen kibiya
ya leƙo ta gaban ƙirjinsa. Dukkan ma'aikatan tsaron su
shida na kewaye dashi suna ƙoƙarin taimakonsa.
Armad na shirin ƙarasawa ya bada nasa agajin yaji murya
daga cikin Gashin-balbela.
"Ku bamu dukkan kayayyakin ku da makaman ku idan
kuna so ku tsira da ranku."
Kyaftin ɗin jirgin shi ne yai wannan kashedin, amma a
bayansa akwai ma'abota izza guda goma sha bakwai.
Babu ko tantama jirgin ɓarayi ne domin ko fasinja ɗaya
babu acikinsa.
Armad ya dubi ma'aikatan jirginsa guda shida yaga
dukkaninsu sun cika da tsoro, babu ko alamun kwarin
gwiwa a tattare dasu. Ya juya izuwa ragowar fasinjojin da
bacci bai ɗaukesu ba yaga tuni wasu daga cikinsu sun
fara tattaro ragowar kayayyakinsu da niyyar miƙawa
wannan ƴan fashi.
Ana haka Armad ya lura da wani jarumin saurayi tsaye
akan Bisaiya riƙe da takobi, idonsa babu ko alamar tsoro.
Cikin ƙiftawar ido Armad zai iya ƙarar da wannan ƴan
fashi amma mutanen jirginsa zasu gane waye shi, wanda
kuma hakan zai jawo masa matsaloli da dama a yayin
tafiyarsa. Daɗin daɗawa wannan ƴan fashi basu cancanci
ya kashe su ba indai ba wani suka taɓa ba, sannan kuma
fasinjojin jirginsa sun yadda da sharaɗin ƴan fashin.
Wasunsu tuni sun fara haɗo kayansu. Armad ya yanke
shawara maimakon yaƙar wannan ƴan fashi kamata yayi
ya fara ƙoƙarin ceto rayuwar kyaftin Bisaiya. Saboda
haka ya nufi inda yake.
Yana isa ya fuskanci cewa wannan kibiya a kusa da
zuciyar Bisaiya ta cake, lallai ana taɓa ta zai rasa ransa.
Duk ƴadda akai hayaniyar farko daya ji ƴan fashin ne
suka fara yi musu sallama da kibbau kafin su aiko
wannan hayaƙi maisa bacci.
Kala-kalar tunane-tunane suka fara yawo a zuciyar
Armad. Akwai tausayi na mutumin daya taimakeshi,
akwai kuma haushi na wannan ƴan fashi.
Ana haka Armad yaji wannan saurayi dake riƙe da takobi
yayi ƙaraji ya afkawa Gashin-balbela. Wuta ce mai
ruruwa tayi tsiri ta tsinin takobinsa ta daki akalar Gashin-
balbela. Nan take wajen da wutar ta daka ya tsage, jirgin
ya fara ƙara zai fashe. Ana cikin haka ɗaya daga cikin
jaruman dake cikin Gashin-balbela ya tafa hannunsa, ya
samarda wata ƙanƙara wadda ta ɗinke wajen daya tsage.
Sadaukin ya ƙara tafa hannunsa ya samarda ƙatoton
mutun-mutumin ƙanƙara wanda ya aikawa saurayin da
saurin gaske. Kafin saurayin yai wani abu ƙanƙanra tayi
masa akwati. Armad ya lalubi izzar wannan saurayi yaji
hamsin da ɗaya ce kamar tasa a lokacin daya fita daga
gida. Shi kuwa ma'aboci

Please Login or Register in order to submit comment