Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Bakar guguwa Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ___ A kowanne yanki na Ikwatora dake kowacce ɗaya daga cikin ƙasashe bakwai na duniya, akwai wani tsibiri wanda shi ne waje da ma'abota wannan yankin suke gani a matsayin tsarkakakken waje. Wannan tsibiri shi ake cewa Tsibirin-guguwa. A duk bayan kowacce shekara sittin wata guguwa mai ƙarfin gaske na tasowa daga Tsibiri. Wannan guguwa ita ake kira da Baƙar guguwa. Duk lokacin da aka fara ta akanyi watanni kamar biyar ana yinta, kuma anyi ittafaƙi wannan iska tana da ƙarfin da zata iya tarwatsa duwatsu da ƙarafa da al'amudai komai girmansu. Amma acikin wannan guguwa ake fitarda shugaban da zaiyi mulki a kowanne shashi na ikwatora a shekaru sittin masu zuwa. Hanyar kuwa mai sauƙi ce, duk wanda yake so ya tsaya takarar wannan kujera saiya fito ya kuma tsaya a tsakiyar wannan guguwa har tsahon wannan watanni biyar, indai aka kammala iskar duk wanda yai ragowa shi ne zai zama shugaba a wannan sashi na Ikwatora har tsahon wasu shekaru sittin masu zuwa. To amma mulki dai bashi kaɗai ne abinda ake muradi ba a shiga cikin wannan guguwa ba. Babban abinda ake muradi shi ne sadakar baiwa da ake acikin wannan iska. Babu wata irin baiwa a duniya ko kuma wani sihiri ko kuma wata fasaha wadda baza a iya tsinta ba acikin wannan iska ba. Sabida haka nema wasu sukan siyar da ransu su shiga duk da kuwa sunsan cewa ƙarfin Izzarsu bai kaiba, amma saboda kwaɗayin wannan baiwa da ake samu. To wannan dai shi ne kaɗan daga cikin Tarihin wannan sashi na Ikwatora inda a dai-dai wannan lokaci Nusi take kwance rai a hannun ALLAH tana jira Dordor mai kai biyu yayi layya da namanta. Sai dai kuma kash, lallai naman Nusi yafi ƙarfin wannan Dordor, domin kuwa a dai-dai wannan lokaci ne aka fara busa wata sarewa wadda duk wanda ya rayu a sashin Ikwatora yasanta. Sarewar da take nuni da cewa lokaci yayi. Wato shekaru sittin sun kewayo kenan. Ai kuwa wannan busa tana isa kunnen wannan Dordor yai tsalle gami da cilli da wuƙar dake hannunsa, sannan ya taka a guje. Bawai shi kaɗai bama, duk wani Dordor dake wajen babu abinda yake face gudu izuwa maɓoya. Tunda dama a wannan lokaci tuni lissafi ya cika, kuma a kowanne lokaci ana jira ne kawai aga baiyanar wannan guguwa. Hakan nema yasa a lokacinda Nusi ta bayyana ta iske manyan Dordor suna tsaye cirko-cirko a wannan waje. Ba jimawa da fara wannan busa sarkin dake mulki a wannan lokaci wanda ya kasance Dordor ne mai kai tara ya bayyana sanye cikin kayan yaƙi. Kowanne ɗaya daga cikin kayikansa tara yasha kwalliya ta kayan yaƙi. Lallai kana ganinsa kasan ya shirya saiya koma kan wannan mulki. Izzaraa kaɗai shekaru dubu bakwai da tamanin ce. Sannan kuma fatar jikinsa da komai na jikinsa Ja ne. Sai dai kuma amma bawai shi kaɗai bane, akwai sauran zaratan tsofaffin Dordor da mutane ma'abota Izza wanda suma suke neman wannan muƙami da kuma baiwa da za'a raba a cikin wannan baƙar guguwa. Babu wanda yake cikin filin nan wanda Izzarsa bata kai dubu biyar ba acikinsu, sannan kuma babu wanda baiyi shekaru samada da hamsin yana shirin wannan rana ba sai mutun ɗaya. Wato Nusi kenan. Ba jimawa gari yai duhu, ko tafin hannu ba'a gani, sannan kuma daga bisani Baƙar guguwa ta fara sauka. Sadaukai suka fara fitowa da shirye-shiryensu da suka tanada. _______ Babu wanda yasan taƙamaimai maike faruwa acikin wannan baƙar guguwa, domin a duk bayan shekaru sittin mutun ɗaya ne kaɗai yake samun nasara, shi kuma tarihi yazo cewa indai ya bayyana abubuwan da suka faru aciki to duk wata baiwa daya samu zai nemeta ya rasa. Hakan yasa sai dai kawai ka samu shaɗi faɗi, amma taƙamaimai babu wanda yasan maike faruwa. To haka dai wannan iska taci gaba da wanzuwa tsahon lokaci, wata ɗai-ɗai har wata biyar. Sannan daga bisani ta fara lafawa. Inda alƙalan kowanne yanki suka fara fitowa domin suga wane ne sabon sarkinsu. Saida aka ɗauki wasu kwananki ukun cir, sannan komai ya lafa gari yai haske. Alƙalai suka gabato cikin filin da aka gudanar da wannan gasa. Amma bisa mamaki maimakon su tararda sarki sai suka tararda da sarauniya. Wata mace ce mai kyawun sura baƙar fata. Tsaye take riƙe da kambun nasara wanda duk wanda yaci nasara yake samu. Babu alamun ciwo ko rauni a tattare da ita. Kana ganinta kasan ta cika jaruma irin ta mutanen farko. Idanunta suna fitarda farin hasken mai ɗauke da Izza abar girmamawa. Abin aljabi wata ƴar ƙaramar tukunyar dinare ce a hannunta na dama, sannan kuma a hannunta na hagu wata ƴar ƙaramar bishiya ce mai yawan koren ganye. Amma da dama zasu fi yadda dani idan nace babban abin mamakin shi ne wannan sarauniya ba wata bace illa Nusi. Wannan alƙalai suna ganinta suka zube a ƙasa cikin gaisuwa da biyayya. To wannan dai shi ne abinda ya kasance da Nusi bayan rabuwarsu da abokinta Armad wilbafos. ____ A can cikin fadar Ururu kuwa yau ankai wata biyar kenan aljani Kalkuta da aljani Netti suna azabtar da Armad duk domin Littafin takobi, amma babu labari. Tuni hankalin Arnad ya gushe yafi sau ɗari yana dawowa. Amma a kowanne lokaci sai dai aljanun su ƙara ƙarfin azabar da suke yi masa. Tuni Armad yaci alwashin kashe wannan aljanu guda biyu da danginsu da kuma Uznu Ururu. Yayi kuma alƙawarin lallai bazai mutu ba saiya ɗau fansar abinda sukai masa. Idan kuwa a sakamakon tsare shi da sukai anan babarsa ta mutu, to lallai saiya kashe duk wani ma'aboci Ururu sannan zai huce. Ana cikin haka ne Armad yaga watarana wannan aljanu guda biyu sun shigo wannan ɗaki. Suna zuwa suka ɗaure shi, sannan suka rufe masa fuska suka fice dashi daga cikin wannan ɗaki sannan suka ɓace sukai yamma. ___ To ko ina suka tafi da Armad? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 54: Cinikin Bayi Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Aljani Kalkútu da aljani Netti na keta hazo suna tattauna al'amuran da suka shafi wannan yaro mai suna Armad da suke azabtarwa. Aljani Netti dai shi yake magana a wannan lokaci, "Babu abinda ba muyiwa wannan yaro ba amma littafin takobi yaƙi fitowa. Yau wata biyar kenan, indai abu sunansa azaba a duniya to munyi masa shi, amma babu labari. Ni ina ganin shawarar da shugaba Uznu ya bayar tayi dai-dai amma kai naga hankalinka bai kwanta ba." Kalkutu yai kyaran murya gami da kallon Armad wanda ke ɗaure a bayansa ya ce, "Eh.... Haka ne, amma kana ganin siyar dashi a matsayin bawa shi ne zaisa Littafin- takobi ya fito. Kada ka manta da irin azabar da muka gana masa. Ai ina ganin azabar da mukai masa tafi azabar siyarwa a matsayin bawa." Netti ya gurgiza kai tare da cewa, "Eh da wannan dan wannan, amma koma dai mene ne yadda aka umarce mu haka zamu yi. Zamu je mu siyar dashi a matsayin bawa ga ɗaya daga cikin sarakunan Jinzidal ɗinnan. Sannan kuma zamu ci gaba saka ido a kansa har illa mashaALLAH, har sai sanda Littafin ya fito. Wataƙila idan yaji azabar bauta Littafin ya bayyana." Haka dai suka ci gaba da tattauna yadda suke shirin siyarda Armad a matsayin bawa. ____ Ranar sha tara ga watan goma na kowacce shekara, ita ce ranar da aka tana da domin yin gagarumin taron da za'a gabatar da dukkan bayin da aka samo ta hanyar gasar Jinzidal. Duk wani mai iko yazo ya siyi abinda yake so. To kamar dai yadda aka sani sarakunan Jinzidal guda biyar sune suke gudanar da wannan ciniki, kuma sukan rarraba wajen gudanarda wannan gasa a kowacce shekara a tsakaninsu. Idan wannan shekara a ƙasar wannan sarkin akai, wata shekarar sai aje ƙasar wani sarkin. To a wannan shekara a ƙasar sarki Rafiya ake wannan taro. Sarki Rafiya ɗaya ne daga cikin sarakuna biyar na Jinzidal, kuma yana da iko akan miliyoyin mutane da kuma ɗaruruwan ƙasashe. Wajen da aka tanada domin yin cinikin bayin dai wani ƙatoton ɗakin taro ne mai hawa-hawa har guda uku. A hawa na farko akwai mutane gama gari na zaune, a hawa na biyu kuma ƙananun sarakuna ne, a hawa na uku kuwa anan sarakunan Jinzidal da muƙarrabansu suke. Daga gaban filin akwai dandamali mai ɗan tudu. Akansa akwai wani ɗan akwati da akayi da gilashi. Ba sai ma ka tamabaƴa ba, kana gani kasan acikin akwatin gilashin ake saka wannan bayi domin gabatar dasu ga maiso. Taro yayi taro kuma babu wanda bai hallara ba, saboda haka ba jimawa aka fara shigo da bayi kala-kala ana gabatar dasu acikin wannan gilashi ga mai buƙata. Mai gabatarwar wani ɗan dogon mutun ne mai yawan ƙasumba. Muryarsa tuni ta dusashe, koda yake dai dama ba zaƙi ne da ita ba. Bayan an gabatarda sama da bayi ashirin saiga wani saurayi nan an fito dashi. Yana tafiya dakyar cikin ankoki na baƙin ƙarfe. Duk jikinsa jini ne, sannan kuma rigarsa ta yayyage. Aka shiga da wannan saurayi cikin wajen nan, sannan alƙalin ya saka masa kuɗi kimanin kuɗin Ayrid dubu sittin kacal. Wannan saurayi ba wani bane illa Armad Wilbafos. Ga dukkan alamu aljani Netti da aljani Kalkutu saida suka saka wasu ɗalasimai a jikin Armad tayadda babu wanda zai iya gane shi. Domin lallai da mamaki ace jaruminda yai suna a gasar Jinzidal ta wannan shekara amma duk taron dubunnan jama'un nan dake wajen cinikin bayin babu wanda ya gane Armad. Sai dai kuma wani abin Alajabi ana shirin siyarda Armad ga wani attajirin birni kawai sai aka ji murya daga cikin wajen hawa na uku, wato wajen da sarakunan Jinzidal ke zaune. Wannan murya ba wata bace illa muryar gimbiya Nostalgiya. To koma dai ya ake ciki idanun Nostalgiya sun gano wannan saurayi, kuma ga dukkan alamu babu yadda za'ai aƙi siyar mata dashi. Ana jin muryar daga inda take duk wani mai so yai jayayya akan cinikin Armad ya fasa. Lallai babu wanda zai iya jada sarakunan Jinzidal koshi wane ne. Armad na cikin wannan gilashi yana rantsuwa da dukkan abinda ya taɓa isa ai rantsuwa dashi cewa lallai tunda aka saka shi acikin wannan gilashi to kuwa sai yaga bayan Jinzidal. Kuma lallai ya maida shi dalilin rayuwarsa cewa sai ya kawo ƙarshen ranar da za'a ringa saka mutane acikin keji kamar wasu kaji ana siyar dasu. Armad dama can ya tsani harkar cinikin bayi, to amma bai taɓa sanin haka waɗanda ake siyarwa a matsayin bayi suke ji ba sai a wannan lokacin. Ai kuwa nan take Armad yai rantsuwa ya ƙara rantsewa cewa sai yaga bayan dukkan sarakunan Jinzidal da dukkan Ururu waɗanda suka kafa harkar cinikin bayi. Sai yaga ranar da zai kawo ƙarshen komai. Sai ya hana dukkan cinikin bayi kafin ya daina numfashi. A wannan lokaci Armad yaji jinin jikinsa ya fara balbalin wuta yana soyuwa saboda baƙin cikin rashin ƙarfin Izzarsa. Domin babu wanda Armad yafi zarga a abubuwan dake faruwa dashi irin kansa. Armad yana zargin kansa da rashin ƙarfin Izza, da rashin tsayawa ya koyi abubuwa a lokacinda yayarsa taso ta koya masa. Amma yanzu komai yazo ƙarshe. Yana da ragowar wata ɗaya daya rage masa ya nemo Tarifil-fakta sannan kuma ya fara shirye-shiryen ruguza dukkan sarakunan Jinzidal da Ururu. A taƙaice dai a wannan rana ta sha tara ga watan goma na shekarar 1853 bayan Amri Armad yai alƙawarin yin faɗa da dukkan duniya ya kawo sabon tsari wanda bai yadda da cinikin bayi ba. Ai kuwa abin alajabi, tamkar wani sirri acikin jinin Armad dama jira yake Armad ɗin yayi wannan rantsuwa, sai nan take ya fara juyawa. Armad yaji idanunsa suna zafi tamkar ana tsire su. Gashin jikinsa tamkar anan tsitstsige geshi saboda zafi. Bada ban bashi da ƙarfin yin ihu bama da tuni ya kwalla ƙara. Nan take ya fara zubarda gumi ta ko'ina. Idan ka ganshi fassarar kawai da zakai ita ce yana tsoron mai zaije ya tarar a wajen waɗanda suka siyeshi. Sai dai kuma abinda shi Armad da dukkan ƴan kallo basu sani ba shi ne a wannan lokaci ƙarfin da Armad ya gada na zuri'ar Wilbafos a jininsa yake farkawa. ____ Ƙarfin Izzar jarumin jarumai Armad Wilbafos zai bayyana a babi na gaba, ko wacce irin Izza ce? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 55: Sabon Farin wata Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos _____ *** Idan ka/kin manta abubuwan da suka faru a babi na takwas zuwa na sha biyu to ya kamata ku duba, domin kuwa abubuwan zasu fara dawowa yanzu. *** Wata ne daren sha bakwai a sararin samaniya, hasken wannan wata ya cika ko'ina a sararin samaniya da sauran ƙasashen duniyar ƙasa bakwai. Kwatsam sai aka wayi gari hasken wannan wata ya fara dusashewa yana duhu. Idanun duk wani abu mai rai ya koma sama da kallo. Ba jimawa dukkan hasken wannan wata ya ɗauke ɗif tamkar an ɗauke wuta. Da dama mutane sun fara tunanin zazzaɓin wata ke faruwa kuma tuni an fara shiga zulumi, malaman addinai da dama suma sun fara nasu aikin. Kwatsam sai aka ga wannan wata ya dawo ya fara yin haske, sai dai kuma hasken nasa ba irin hasken da aka saba gani bane. Wannan hasken ruwan ƙasa ne mai launin toka. Ba jimawa mutane gama-gari suka fara shiga tashin hankali ana raɗe-raɗen cewa masifa ce zata sauka. Amma tsofaffin ma'abota Izza wanda suka ga jiya suka ga yau sun san sarai maike faruwa. A daular sarkin Jinzidal sarki Bihanzin mai dauwamammen ciwo wani tsohon mutun ne ya farka daga cikin wani akwatin gawa, yana buɗe idonsa wata Izza wadda girmanta ya haura shekaru dubu goma ya cika wannan ɗakin. Wannan mutun dukkan jikinsa a bushe yake, fatar jikinsa tayi ɓawo-ɓawo, bashi da maraba da gawa. Amma duk da haka sai gashi ya buɗe bakinsa yana magana, "Jinin gidan Wilbafos ya bayyana." Yana gama magana ya koma ya rufe idonsa ya ci gaba da bacci. Wannan magana daya faɗa babu inda ta isa sai kunnen sarki Bihanzin mai dauwamammen sara. Haka dai irin wannan mutun mai kama da gawa ya ƙara tashi a daular Denizawa dake ƙarƙashin ƙasa ya kuma ƙara faɗar irin abinda na farkon ya faɗa. A can wani sashi kuwa na duniya dake kan wani siririn tsibiri, wani mutun ne riƙe da AL'ƘURANI mai girma a hannunsa. Idanun wannan mutun daɗe a rufe kuma babu wamda zai iya kwatanta shekarunsa a duniya. Yana buɗe idanunsa saiga irin hasken wannan wata aciki. Murmushi kawai yayi irin na mutanen Sannan ya ƙara rufe idanunsa. Haka ire-iren wannan abubuwan al'ajabi suka ci gaba da faruwa a dukkan dauloli na faɗin duniya. Wannan sabon hasken farin wata kuwa ruwan ƙasa ko ajikinsa, haka ya ci gaba da ƙaruwa yana game duniya. A tsakiyar wannan ɗakin cinikin bayi kuwa wani saurayi ne acikin gilashin da ake tallan bayin nan dashi. Saurayin ya miƙe ya tsaya a tsaye yana kallon dukkan mutanen dake wajen. Duk wanda ya ganshi zai iya tunanin tsoron siyarwa ne yake damunsa. Amma ba jimawa dukkan hasken wannan farin wata mai ruwan ƙasa da ratsin toka ya fara raguwa a dukkan sassa na duniya yana curewa a waje ɗaya. Kan kace meye wannan dukkan hasken ya gama curewa a waje ɗaya sannan ya fara sakkowa ƙasa a hankali a hankali har saida yazo dai-dai idon wannan yaro dake cikin wannan gilashi, sannan dukkaninsa ya shige cikin idon wannan saurayi. Wannan saurayi dai ba wani bane illa Armad Wilbafos. Nan da nan idanunsa suka fara haske suna bada launin hasken wannan wata wato ruwan ƙasa mai ratsin toka. Komai da yake faruwa a idon kowa ya faru, saboda haka a dai-dai wannan lokaci wannan mutumi dake bada rahoton akan bayin da aka saka acikin gilashin ya fara karkarwa yana matsawa baya. Armad ya kalli wannan ankoki dake jikinsa, nan take dukkan ankokin suka zube ƙasa, sannan dukkanin ciwukan jikinsa suka warke nan take. Sannan ya ɗaga idonsa ya kalli jikin wannan gilashi, ai kuwa hasken nan ruwan ƙasa na dukan gilas ɗin ya tarwatse. Armad ya bayyana a waje kamar wani ɗan ƙaramin bajimin aljani. Inda ya haska idonsa akan dukkan mutanen dake cikin wannan waje, nan take da dama daga cikinsu suka fara jin karkarwa suna rawar ɗari tamkar wanda akace mutuwa ce tsaye ke kallonsu. Koda yake a wannan lokaci Armad bashi banbanci da mutuwar kanta. Idanunsa kawai haske suke suna fitarda tsananin azabar yaƙi da ƙarfin Izza. Armad ya miƙa hannunsa sama, nan take wata taga ta buɗe akam iska inda ya miƙa hannu ya zaro takobinsa ta Wilbafos. Abin mamaki sai ga taurari guda biyar a saman takobin. Armad yai murmushin girma bayan da yaga adadin taurarin dake kan takobin kuma ya tuna wanda suke kai a lokacin da yayi faɗa Ikenga. Lallai Armad ya samu gagarumin canji a jikinsa wanda keda ban al'ajabi. Tun daga kan hawa na farko har zuwa na uku kowa yayi shiru ba'a cewa komai. Ana haka kawai sai aka ga Armad ya ɗaga takobinsa ya nufi kan waɗannan bayin da aka riga aka siyar. Ko ba'a tambaya ba kasan nufin Armad ya kwance su ya kuma ƴantar dasu a gaban dukkan duniya. Wanda zarar Armad ya aiwatar da wannan abu, to dai-dai yake da fito na fito da dukkan ƙabilar Ururu da kuma Sarakunan Jinzidal biyar. Kuma lallai a wannan lokaci zaka ga ma'abota baƙaƙen ido sun fara sauka daga ƙasa ta farko domin kama Armad. Lallai hatta sarakunan manyan gidajen Ururu goma sai sun sauka idan Armad ya aikata wannan abu. Domin wannan shi ake kira da fito na fito da Ururu. Sai dai kuma amma a wannan lokaci ne kwatsam gimbiya Nostalgia ta bayyana a gaban Armad tana mai murmushi. Babi shiri Armad ya tsaya, kuma duk da ɓacin ran da yake ciki zuciyarsa bata fasa tunano masa wannan kyakkyawar gimbiya ba da suka haɗu a shekarun baya ba. Gimbiyar da ta ceto rayuwarsa sau adadi da dama tun bai ma fuskanci yadda yanayin duniya ke gudana ba. Armad yana tuno sanda ta hanashi faɗawa rami da kuma hawayenta guda ɗaya daya faɗa idonsa. Sannan kuma lallai Armad yana sane da wannan sirri daya jiyo musu acikin wannan allon tsafi, sirrin dazai rikita duniya baki ɗaya. Armad bai manta da fasahar Izza ta musamman, wadda ake iya duba cikin kwakwalwar mutun aga mai yake tunani ba wadda wannan gimbiya mai suna Zahra wadda akewa laƙabi da Nostaljiya take da ita ba. "N.....nostaljiya? Mai kike anan, babu ruwanki da tsakani na da wannan mutane da suke so su ringa bautar da bil adama. Idan kuma kika shiga tsakani na dasu, to lallai zan manta da duk wani abu daya taɓa faruwa a tsakaninmu na yaƙe ki, sannan kuma...." Armad yana magana amma dole ya tsaya cak, badan komai ba sai dan saboda kwalla daya gani acikin idanun Nostaljiya bayan da tayi arba da kayan jikinsa a yayyage, kuma duk sunyi faca-faca da jini. Armad ya buɗe baƙi zai ci gaba da magana, amma a wannan lokaci yaji hayaniyar ƴan kallon dake wajen suna cewa, "Kai.... Wai wannan yaron ba shi ne Armad Djinn ba daya fafata a gasar Jinzidal ba? Lallai shi ne, ya akai da bamu gane shi ba? Wai ya akai ma za'a siyar dashi a matsayin bawa? Mai yake faruwa?" To ga dukkan alamu an cire dukkan hijabin dake hana wannan mutane gane Armad, kuma lallai a wannan lokaci kowa ya gane wanene Armad. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 56 & 57: Nostojiya nara Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ____ _______ Nan take Nostalgiya ta juya ta kalli waɗannan ƴan kallo da suka zo wannan cinikin bayi, ai kuwa daga cikin girman Izzar ta sai ga SANYIN BABBAN SIHIRI nan ya fara sauka acikin wannan waje a yanayinsa na ƙanƙara ruwan toka. A wannan lokaci ya fara bin jikin dukkan mutanen dake wajen, kuma duk wanda ka kalla babu abinda zaka gani sai ƙanƙara ruwan toka nannaɗe a jikinsa. Nostalgiya tai ƙaraji na ɓacin rai, ta ɗaga takobinta sama takai sara kan iska. Ai kuwa saiga wasu aljanu nan guda biyu sun bayyana suna ƙoƙarin kare wannan sara mai ɗauke da Izzar sanyin babban sihiri. Abu ne sananne idan ka ɗauke Farar-laya babu abinda aljanu ke tsoro irin Sanyin babban sihiri. Nostalgiya tasan haka kuma ga dukkan alamu tayi niyyar halaka wannan aljanu ne baki ɗaya. Inda tayi tsalle sama ta dira akan ruwan cikin wannan aljanu da ƙafafunta ma'abota Izza. Yau waye ya isa ya jada ƴar gidan Bihanzin mai Dauwamammen Sara. A wani irin yanayi mai kama da hauka da tsananin ɓacin rai Nostaljiya ta hau saran wannan aljanu baji ba gani. Jinin aljanun yayi sama, kan kace meye wannan yayi faca- faca da ko'ina. Ko dama ɗaya bata bawa wannan aljanu ba na kare kansu ba kafin ta aikasu lahira. Ta juyo da idanunta ga wannan bayi da aka riga aka siyar, idanunta na sauka akansu nan take duk ankokin dake ɗaure dasu suka zube a ƙas. Armad na gefe yana kallon tsananan ɓacin rai wanda har yaso yaɗan ɗara nasa. Abu na gaba daya ji shi ne hannun Nostaljiya ta jashi sun tashi sama inda suka fice daga cikin wannan waje suka tashi sama. A can cikin wajen hawa na uku kuwa manyan jarumai ne masu wakiltar sarakunan Jinzidal. Daga ɓangaren dama jaruman sarki Rafiya ne guda uku. Dukkaninsu Izzarsu ta haura shekaru ɗubu biyar. Kai ɗaya daga cikinsu ma shi ne wanda muka gani a wannan Jinzidal wadda Armad ya taka rawar gani, wato Asifu wanda akewa laƙabi da Ruwan Bala'i. Asifun ne ya fara magana yana cewa, "Wannan yarinya bata da hankali. Bansan maike faruwa ba, amma ga dukkan alamu sa'a tana tare damu domin kuwa akwai alamun soyayya a idanun wannan yarinya, kuma wannan soyayyar dake idonta ta rufe mata ido ta aikata abinda zai taimake mu mu ruguza daular babanta baki ɗaya. Saboda haka baza mu bita ba, kuma baza muyi mata komai ba anan. Mu barta ta gudu dashi wannan yaron. Kaga da haka zamu samu damar cin galaba akan tsohon ɗan adawar mu wato babanta Bihanzin. Tunda kunga duk laifin daya faru anan kawai saimu ɗora shi akan babanta kuma rubuta a rubuce mu aikewa da Ururu." Asifu na zuwa nan a zancensa yai dariya mai cike da farin cikin, sannan ya ƙara yin ƙasa-ƙasa da muryarsa domin kada sauran mutanen dake wajen suji, "Ban taɓa tunani babbar dama kamar wannan zata samu ba a garemu. Lallai wannan babban labari ne muyi maza mu tashi mu gabatar dashi izuwa sarki Rafiya." Sauran manyan ma'abota Izzar guda biyu dake tare dashi suka girgiza kai alamun amincewa. _______ Babu inda gimbiya Nostalgiya ta sauke Armad sai cikin wani sihirtaccen kogo. Wannan kogo dai waje ne na musamman wanda ke cikin daular babanta sarki Bihanzin, kuma babu wanda yasan dashi inba ita. A sau da dama idan tana so ta nutsu ta tuno babarta wadda ta mutu wannan kogo take zuwa tayi kwana da kwanaki tana hutawa tana kewar mahaifiyar tata. Acikin kogon dai akwai ƙorama mai bada sanyi mai ciƙe da ni'ima da annushuwa. Ga kujeru da shimfiɗu na alfarma, ga kuma kayan ci da sha duk na sarakuna wanda Armad ma bai taɓa yin tsinkaye da suba. Tana ajiye Armad ta ɗakko wata sabuwar rigarta ta wadda akaiwa ado da dinare ta fara goggoge masa datti da jinin dake jikinsa. Har a wannan lokaci ta kasa ɗago kai ta dubi Armad saboda hawaye da tausayin dake idanunta. Armad ɗin shima ya kasa cewa komai, abu ɗaya dai daya sani shi ne abinda ta aikata a wajen cinikin bayin can lallai saiya jawo wa babanta babbar matsala. Saboda haka bai san mai zai fara ce mata ba. Tunda dai saboda shi take duk wannan abun, kuma koma mai ya same ta shi ne zai zamo shila. Amma abu guda ɗaya daya kasa ganewa shi ne mai yasa take wannan abubuwa. Wai anya kuwa tana cikin hankalinta kuwa? Sai dai kuma Armad ya tuna ba wannan ne lokaci na farko ba data fara sadaukar da rayuwarta ba domin ta ceto shi. Yana tunano lokacinda zai faɗa wannan rami kuma wannan dordor ya so ya halaka ta, amma taƙi sakarsa. Can bayan wani lokaci Armad ya riƙe hannunta ya tsayar da ita, sannan ya ɗago da kanta domin yaga maike faruwa acikin idanunta. Amma bisa mamaki sai kurum Armad ya ƙara arba da irin sak abinda ya taɓa ji a shekarun baya, wato yaji tamkar ya santa a wani zamani mai tsaho daya gabata. Nan da nan ya cika ta yana haki. Yau dai koma mai ake ciki sai yaji amsar dukkan tambayar daya daɗe yana so yayi mata. Nostalgiya taja dogon numfashi sannan ta goge fuskarta da hankici. Ta miƙe daga inda take tana murmushi sannan ta fara da cewa, "Ka taɓa gani na babu hijabi?" Tambaya ce amma ga dukkan alamu ba amsa take nema a wajen Armad ba, domin kuwa tasan cewa bai taɓa ba. Shima Armad ɗin yasan haka, kuma nan take ya fara ƙinƙina a lokacinda yaga kamar tana nufin cire rigar dake jikinta. Muryarsa na rawa yana cewa, "Ehm.... Tsaya.....tsaya..... Ba saikin cire komai ba, na taɓa....." Kawai Armad yaji Nostaljiya tasa hannu ta doke shi aka. Nan da nan ya haɗe gira, "Laifin me kuma nayi miki harda duka?" Nostalgiya ta ɓata rai matuƙa tana mai cewa, "Mai ka ɗauke ni, a gaban naka zan cire kaya. Kawai kai mana shiru kaga mai ake yi mana, a'a!" Bayan data gama magana saita durƙusa a gabansa tana mai murmushi tana lallashinsa, "Kayi haƙuri na dake, ba zafi ko?" Armad yana rasa mai zaice, tambayar kansa kawai yake, towai mai take nufi ne? Waishin mai ake ciki nema? Ai kuwa ba jimawa Armad yaga dukkan wannan kogo ya cika da wani irin haske mai matuƙar ƙayatarwa. Da farko Armad yayi tunanin wata fitilar aka kunna, amma a lokacin ne Nostaljiya ta kashe fitilar dake ɗakin amma hasken kawai ƙara ƙaruwa yake. Ba jimawa Armad ya gano cewa wannan haske daga jikinta yake fitowa. Fatar ta gaba ki ɗaya ta juye izuwa wani abin kyalkyali da walƙiya mai tsananin kyawu. Armad ya fara tunowa da labarai daya karanta na tatsuniya akan wata wadda ake kira da Lasina Naitingele wadda aka ce tafi kowa kyau a duniya. Nan take Armad ya gano cewa wadda take gabansa lallai ta ma fita kyau. Idanun Nostaljiya na kaɗawa da tsananin ƙauna da tausayin Armad. Nan da nan Armad yaji jikinsa ya mutu murus. Dama Nostaljiya tama ɗan fishi tsaho saboda haka koda ta jashi ya tashi ya tsaya a gefenta ya kuma kalli dattin dake jikinsa sai yai matuƙar raina kansa. Lallai Armad ya tabbatar babu wata mai kyawun wannan yarinya a duniya. Fuskarta madaidaiciya ce kuma Armad bazai iya siffanta ta taba sai dai kawai yasan cewa wannan fuska ta ƙunshi duk wani abu da kyau zai iya bayarwa.

Chapter 22 of 33