Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haka ya yiwo kan Ikenga ta ɓangaren dama. A gabansa kuwa tuni wannan sara ya haɗu da wannan ƙanƙara da wuta da walƙiya. Haɗuwar tasu keda wuya gaba ki ɗayan abubuwan nan guda uku suka tarwatse suka ɓace, tamkar ba'a taɓa yinsu ba. Sannan saran yaci gaba da tafiya yayi kan wannan mutun-mutumi gadangadan. Amma suma basu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da aikowa da wannan sara saƙon bala'i. A haka suka samu suka tsayar dashi kafin ya isa gare su. Ai kuwa saran na tsayawa duk su ukun sukai kan Armad suka hanashi ƙarasawa kan Ikenga wanda ke tsaye a gefe na ganin maike faruwa. Suka saka Armad a tsakiya, sannan suka fara aika masa da saƙon ruwan zafi, walƙiya da dusar ƙanƙara. Suna niyyar halaka shi ta kowanne ɓangare. Amma ina, Armad a tafe ya kwana. Domin kuwa a dai-dai wannan lokaci ne ya fusata ya juya takobinsa da karfin tsiya, sannan ya kaiwa waɗannan mutun-mutumi uku sara, inda ya tsinke musu kai nan take. Wata iska mai zafi ta fice daga jikin takobin tasa sannan ta daki jikin mutun-mutumin suka juye izuwa toka. Cikin ƙiftawar ido Armad ya bayyana a gaban Ikenga ya kuma kai masa wawan sara. A dai-dai wannan lokaci babu wata kalma da zaka iya yin bayanin Armas da ita illa kace yayi kama da matashin bajimin aljani ɗan fari. Babu alamun tausayi ko yafiya a tattare da idanunsa, lallai a kowanne lokaci Ikenga zai iya ziyartar lahira. Sai dai ana cikin haka ne Ikenga yaga babu sarki sai ALLAH yai zafin nama ya tafa hannayensa tare da kiran ɗalasimin Takun-sarki, "Shaibal-shísu." Acikin wani yanayi na ban al'ajabi gaba ki ɗaya lokaci ya tsaya cak, ya kuma bawa Ikenga damar yin taku bakwai da ƙafafunsa kafin saran Armad ya cimmasa. Yana ajiye ƙafa a takun ƙarshe wani duhu irin na farkon ketowar alfijir ya bayyana ya maye gurbin hasken da da ke cikin filin kallon. Hatta ƴan kallon dake cikin filin basu samu damar ganin abinda ke faruwa ba a dai-dai wannan lokaci. Bayan kimanin daƙiƙa biyar wannan duhun ya sarara, sannan haske ya dawo. Ai kuwa sukai arba da Ikenga sanye da wata rigar tsafi ruwan dinare, sannan kuma riƙe da wata takobi mai kyalli ita ma ruwan Dinare. Armad kuwa na can gefe a tsaye shima riƙe da takobinsa ruwan ɗorawa. Babu alamun ciwo ko rauni ko gajiya a jikin kowannensu, amma ga dukkan alamu iskar dake kaɗawa a tsakaninsu ta canja, kuma lallai yanzu ne za'ai faɗan ƙarshe. Kana gani kasan kowa acikinsu yai rantsuwa daya faɗi ƙasa a wannan wasa a gaban idon duniya kwara ya mutu. "Fasahar Ɗorawa ko?" Ikenga ya kalli takobin Armad cikin nazari sannan yaci gaba da cewa, "lallai babbar fasaha ce. Kuma idan da ba dani ka haɗu ba, to da lallai zaka iya yin nasara akan kowa. Amma kayi sani cewa ƙarfin dake cikin ruhi da jini na ya wuce gaban lisaafin ka, kuma yanzu zan nuna maka dukkan ƙarfina. Zan nuna maka fasahar takobi dana sakawa suna Lokacin Alfijir. Ina mai baka shawara idan har kana da wani shiri a ɓoye, to ka fito dashi." Yana rufe bakinsa yai kan Armad cikin zafin nama tare da kaɗa wannan takobi ruwan dinare dake hannunsa. Ai kuwa nan take wani duhu irin na alfijir ya fito daga jikin ƙarfen takobin ya kuma yiwo kan Armad. Duk inda wannan duhu ya gifta sai kaga wajen ya tsufa nan take kuma ya murmushe tamkar wanda yayi shekara dubu a ajiye. Kan kace meye wannan tuni filin da suke fafatawa akai ya tashi daga sabo mai kyalkyali ya koma izuwa tsoho tamkar wanda akai shekara dubu da sarrafa shi. Armad na ganin haka ya ja da baya da sauri ya tafa hannayensa ya sa tsinin takobinsa ya caki hannunsa, sannan ya shafa jinin akan takobin. Kafin wannan sara na Ikenga ya ƙaraso tauraruwa ɗaya dake saman takobin Armad ta fara ƙoƙarin rabewa izuwa biyu. Amma ina, kan ta ƙarasa rabewa wannan sara ya iso, inda ya daki jikin takobin Armad da ƙarfin tsiya sannan ya ɓace. Yana ɓacewa Armad ya kalli hannunsa yaga yayi furfura ya tsofe ya yamushe tamkar wanda yayi shekara dubu a raye. Cikin ɓacin rai ya maida takobin hannun dama, inda lokacin tauraruwar ta koma biyu. Dukkan wani ƙarfi dake jikin Armad da takobinsa ya koma izuwa biyu. Nan take wani tsananin nauyi mai ban tsoro ya fara fita daga jikin Armad yana yiwo wa kan Ikenga. Kan kace meye wannan wajen da suke tsaye ya fara lotsawa cikin ƙasa, tamkar wanda aka dunƙule nauyin dala da kwauron dutse aka ɗora masa. Ikenga yaji ƙafafuwansa sun fara ƙara suna neman karyewa saboda wannan nauyi. Amma a lokacin ya ƙara kaɗa takobinsa ruwan dinare, lamarinda yasa wannan nauyi ya tsofe nan take, tamkar yayi shekara dubu. Lallai ba nauyi ba koma mene ne zai ƙare idan yayi shekara dubu. Ana cikin haka ana kallon kallo aka ji muryar Ikenga, "Hmmm.... wato kana da takobin da take sarrafa nauyi. Ta ƙarashi ko kuma ta rage shi. Lallai kaima ma'aboci Izza ne, amma duk da haka baza ka iya tsayawa a gaban fasaha ta Lokacin alfijir ba. Takobi ta ta duhun alfijir tana sarrafa lokaci. Kuma duk abinda na sara da ita a lokacin take yake tsufa na shekara ɗari. Ko yaro ne anan take zai tsofe tamkar yayi shekara ɗari. Lallai saina mulki duniya da fasaha ta takun sarki. Kayi sani cewa indai na sare ka koda sau ɗaya ne, kuma komai ƙanƙantar saran sai ka tsufa na kimanin shekara ɗari nan take." Yana rufe baki yai kan Armad da takobinsa gadan-gadan, shima Armad kawai fusata yaƙara yi ya kuma yiwowa kansa. Duk inda Armad ya gifta sai wajen ya nutse a ƙarƙashin ƙasa tamkar an haƙeshi da kimanin ƙafa ɗari. Shi kuma Ikenga duk inda yayi sai kaga wajen ya tsufa. Suna haɗuwa suka kaure da azababben yaƙi, ƙura ta turnuƙe, iska ta tsofe, haske ya ɗauke. Ƴan kallon basa jin komai sai ƙarar takubba. Cikin daƙiƙa ashirin kawai su biyun sun isarwa da juna sara sama da hamsin. Duk sanda saran Ikenga ya yiwo kan Armad, Armad zaiyi amfani da nauyi ya danne shi izuwa ƙas ya hanashi zuwa wajensa. Shi kuma Ikenga kawai tsofantar da saran Armad yake kafin ya isa gareshi. Haka wannan yaƙi yaci gaba tsahon kimanin mintuna bakwai, kafin daga bisani a daina jin komai. Kowa acikin ƴan kallo yayi tsit acikin filin wasan. Jira kawai ake aga ƙurar ta lafa domin aga maike bayan wannan ƙura. Bayan minti ɗaya ƙurar ta lafa, akai arba da Ikenga da Armad a kwance cikin jinin shane-shane, babu wanda yake iya motsi acikinsu. Lallai duk su biyun sunkai ƙarshe wajen ƙarar da ƙarfin jikinsu. Kai hatta ɗan yatsa basa iya motaswa. Amma duk da haka basu daina yiwa juna kallin tsana da azabar yaƙi ba. Kansu na tsaye suna kallon juna, kuma da da yadda zasu yi da tuni sun ƙara tashi sun afkawa juna. Ana cikin haka alƙali ya rasa wa zai bawa nasara, kawai sai Armad yaga wani dattijo mai yawan farin gashi bayyana akan Ikenga ya dafa shi. Haka na faruwa dukkan Izzar Ikenga ta dawo tamkar yanzu aka fara faɗan. Yana ji Ikenga ya ce, "Bayajidda, karfa wani ya ganka." Sannan kuma yana ji dattijon da aka kira da Bayajidda ya amsa, "Ai ko Uznu Ururu dake cikin can bai isa ya ganni ba. Saboda dalili guda biyu, na farko dai ƙarfin Izzarsa bai kai ya ganni ba, sannan kuma koda ƙarfinsa yakai babu wanda zai iya gani na sai jinin Bayajidda." Armad ya buɗe baki zai gayawa alƙali da ƴan kallon cewa Ikenga zaiyi fasha, amma hatta bakinsa ma yaƙi motsawa saboda tsananin gajiya da ƙarewar ƙarfin Izzarsa baki ɗaya. Kai hatta idonsa ma ya kasa ƙiftawa. Tunani kaɗai yake iya yi acikin ransa, 'wai mai wannan tsohon yake nufi da babu wanda zai iya ganinsa sai jinin Bayajidda, gashi ina ganinsa. Kuma yana nufi Uznu Ururu ma bai kai ƙarfinsa ba. Koma dai meye lallai bazan yadda ba, wannan ai fasha ce!' ___ Nauyin dake fita daga takobin Armad shi ake kira da GRAVITY da English. Amma nayi ta bincike ban samu fassararsa da hausa ba, saboda haka nayi fani da kalmar NAUYI. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 47: Hidaya Wilbafos Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Armad na ganin wannan ruhi mai girman Izza daya bayyana ya taimaki Ikenga babu abinda ya faɗo masa acikin rai sai ƴar uwarsa mai suna Hidáya Wilbafos. ___ 1847 Bayan Amri Kaɗan daga cikin tarihin Armad da ƴar uwarsa. "Armad wallahi zan dake ka! Wai baza ka maida hankali ba!" Wata budurwa mai matuƙar kama da Armad tayi masa tsawa a yayinda suke tsaye a filin horo. A wannan shekara ta 1847 Armad yana ɗan shekara takwas, kuma tun a wannan lokaci aka fara koyar dashi al'amuran Izza. Wannan budurwa na tsaye sanye cikin jar alkyabba irin ta mutanen farko. Kimanin shekarunta zai kai ashirin da biyar koma fiye da hakan. A rataye da kafaɗarta ta dama akwai doguwar takobi mai zanen taurari ruwan ɗorawa. Budurwar doguwa ce wadda a ƙalla zata yi zira'i uku a tsaye. Kamanninta akwai kamala da nutsuwa da jarumta aciki, lallai akwai ƙarfin Izza a tattare da ita. Sunan wannan budurwa Hidaya Wilbafos. Kuma yayar Armad ce ta jini duk da kuwa ratar shekarun da ke tsakaninsu. Armad na sanye cikin farar ƴar shara ɗaure da jan kyalle a goshinsa. Daga ganin yadda yake ɓata rai kasan dole tayi masa, amma lallai da zata kyaleshi da bazai yi wannan horo ba. "Shikenan, idan baza ka dage ka koyi al'muran Izza ba to ba ruwa na da kai. Idan bana nan wa zai kare ka? "Ehmmm..." Hidaya ta ja dogon numfashi tare da girgiza kai. "gaka da tsokana amma baka san dagewa ka koyi al'muran Izza, sai muga idan bana nan wazai ringa hana yaran da kake tsokana suyi maka duka. Zo mu tafi gida, kuma gobe ma sai mun dawo ka ci gaba. Ai ko kana so ko baka so saika zama ma'aboci Izza." Hidaya ta juya zata tafi amma Armad ya tsaya yaƙi binta, fuskarsa cike da shagwaɓa irin ta ƙananun yara. "Ka taho mana...." Hidaya ta waiwayo tai masa magana. "Ni.....ni fa ƙafa ta ciwo take!" Armad ya haɗe fuska kamar zai fashe da kuka. "Hmmm....." Hidáya taja numfashi gami da gyaɗa kai. Domin tuni ta gano abinda Armad yake nufi. Sau da dama idan suka fita tare yakan ce bazai iya tafiya ba saita goyashi shi a bayanta. Kuma a wannan lokacin ma abinda yake nufi kenan. "Indai baka dage ba ai daina ɗaukan ka zanyi." Cikin sanyin zuciya da tausayi irin na ƴan uwa ta juyo izuwa Armad. Inda ta durƙusa ta goya shi sannan suka kama hanya. Ba jimawa suka fara fita daga cikin duhun manyan bishiyun goriba da suka kewaye wajen. Hidaya ta numfasa tare da ci gaba da nunawa Armad muhimmancin ya dage da horonsa. Ga dukkan alamu baza ta haƙura ba indai Armad bai maida hankali yayi ba. "Kaga ina so na koya maka duk wasu fasahohi na sarrafa aljanu da suka shafi zuri'ar gidan wilbafos kafin lokaci ya ƙure. Amma kaƙi maida hankali, towai mai kake so ka zama ne, gayamin naji?" Armad na kwance a bayanta cikin shagaɓa irin wadda yayar tasa ita kaɗai yake yiwa, ya fara da cewa, "kinsan me yaya, ni dai abinda nake so a rayuwa shi ne zaman lafiya ya wanzu. Ko wa ya zamanto acikin kwanciyar hankali. Idan na girma na zama kamar ke nayi aure, idan na kara girma saina haifi ƴaƴa guda uku duk masu kama dake, sannan idan na tsufa saina mutu akan gado na akan cinyarki tare da mama da Abba da ƴaƴa na duk sun kewaye gadon da zan mutu. Shikenan inna mutu sai kuyi kuka sannan kuma ku ringa tunani na...." Koda yazo nan a zancensa sai yai shiru tamkar wani abu ya gilma acikin ransa, inda cikin tsoro irin na yara ya ɗaga kai ya dubu yayar tasa Hidaya. Idanunsa a wangale ya ce, "Ai zaki ringa tunani inna mutu ko Yaya?" Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta juyo da kanta ta ƙura masa ido tana mai mamakin wannan abu daya faɗa. Badan komai ba sai dan cewa ita ma kanta shekaru da dama da suka wuce burinta kenan. Tamkar ƙanin nata Armad ya shiga ranta ya gani, duk da kuwa cewa bata taɓa gayawa wani mahaluƙi wannan buri nata na yarinta ba har zuwa wannan lokaci. Saboda haka sai kawai tayi murmushi tare da cewa, "eeh, zan tuna ka." Amma ga dukkan alamu wannan magana kaɗai ta faranta wa Armad rai, inda ya ƙara maƙalewa a bayanta tamkar yana tsoron wani abu zaizo ya raba su da ita. Murmushi kawai tayi taci gaba da tafiya tana yin tunanetunanen ya zatayi ta kare wannan ƙani nata wanda baya son koyon al'amuran Izza ko kaɗan. Tana cikin tunani ne taji muryar sa yana cewa, "ehmmm... Kinsan me? Mu ɗaura alkawari cewa duk wanda ya riga mutuwa ɗayan zai ringa tuna shi." Tun kafin ya rufe bakinsa ya ziro ɗan ƙaramin ɗan yatsansa ta gefen kunneta da niyyar su ɗaura. Babu abinda tayi face ajiyar zuciya sannan kuma ta kama hannun nasa da niyyar ta yarda. Kamar zaiyi shiru, amma abu na gaba daya faɗa shi ne, "to indai da gaske kin yarda toki ɗakko min ɗaya daga cikin filawar dake wancan lambun." Armad yai nuni da wani katafaren lambu kimanin taku dubu daga inda suke tsaye. Babu abinda kake gani daga nesa sai baƙin duhuwar wannan daji da wasu manya-manyan baƙaƙen bishiyu waɗanda lallai koda basu yi shekaru dubu a raye ba to kaɗan ne babu. Tsayin kowacce bishiya yakai zira'i maitan da ɗoriya. Kai lallai har sai hular mai kallo ta faɗi ƙasa saboda ɗaga kai amma bai gano ƙarshen wasu daga cikin bishiyun ba. Lambun daban yake da wanda su Armad ke ciki, kuma an kewaye shi sannna kuma ansa shedar sarki Hanibal Sarkin ƙasa ta uku akai. Sarki Hanibal shi ne sarki mai mulkin doron ƙasa ta uku, sannna kuma yana ɗaya daga cikin sarakunan Jinzidal biyar. Koda jin wannan magana sai Hidaya ta canja fuska, "Armad ka fasan cewa duk abinda ke cikin can wajen na Hanibal ne kuma ya hana shiga." "Eh na sani, amma fa ta sama zamu bi kawai mu ɗauki guda ɗaya ai ba wanda zai sani fa. Kinji Yaya, kinji... Kinji daga wannan fa shikenan." Tai murmushi tare da ajiƴar zuciya, "To muje amma karka taɓa komai kaji." Armad ya kyaɗa kai. A dai-dai wannan lokacin Hidaya ta tafa hannayenta ta kuma kira wani ɗalasimi a zuci, sannan tai tsalle ta tashi sama tamkar tsuntsu mai fuka-fuki. Abu ne sananne cewa duk wanda ya haura shekaru dubu na Izza to zai iya tashi yayi tafiya a sama ba tare da matsala ba. Kuma hasalima Armad bawai filawar ce ta dame shi ba, sai dai kawai yana so ƴar uwar tasa ta tashi sama dashi, saboda yasan lallai indai zasu shiga dajin to saisun tashi saman. Ai kuwa suna tashi sama Armad ya ƙara saƙale hannunsa ta ƙirjinta tamau, sannan ya saki ɗayan akan iska yana ihun farin ciki. Duniya tayi masa daɗi domin a wannan lokaci babu abinda yake so face tashi sama a bayan yayar tasa. "Wuuuuuu...." Tun daga nesa zaka iya jiwo ihun Armad a saman. "Dama nasan abinda kake so kenan. Ka riƙe ni dai sosai karka faɗo." Tana cikin magana suka dira acikin tsakiyar wannan daji. Inda ta ajiye Armad ta kuma juya tana hangen imda filawar take. "To ka tsaya anan, ga wata can bari na ɗauko maka." Nan take ta ƙara tashi sama ta nufi wani surƙuƙi a ɓangaren arewa. Bayan daƙiƙa ashirin ta dawo da wata filawa yaluwa mai kyawun gaske. Amma tana sauka a gaban Armad taga hannunsa na ɗisa da jini. "Waye ya ji maka ciwo?" Shi ne kawai abinda ta tambaya. Tun kafin Armad ya bata amsa siffarta ta canja baki ɗaya. Wani yalon haske ya fara fita daga jikin takobin dake rataye a kafaɗarta. Wata baƙar wuta ta fara ci acikin idanunta. Nan take iskar wajen ma ta canja ta ƙara nauyi, sannan kuma wani sauti ya fara tashi daga cikin wannan daji. Lallai inda akwai mai fassara maganar tsirrai da yaji cewa haƙuri waɗannan bishiƴoyi ke bawa Hidaya. Amma ina, tuni ta toshe kunnenta tsahon lokaci. Kai hatta alkyabbar dake jikinta ta canja launi izuwa baƙa, lallai a wannan lokaci Hidaya tayi kama da siffar mutuwa kanta. Amma a wannan lokaci shi kamsa Armad karkarwa yake yana matsawa baya ganin yadda yayar tasa ta canja kama. Yana ji tamkar wutar dake cikin idanunta zata soya naman jikinsa nan take. Bai san lokacinda bakinsa da kansa ya fara magana ba ba tare da ya bashi umarni ba. "Wancan ƙayar dake jikin wancan bishiyar ce." Ya nuna wata bishiyar ƙaya a kusa dashi yana karkarwa. "Wato har akwai wanda ya isa ya jiwa ƙanina ciwo ina wajen! Lallai yau ba Hanibal ba, koda wannan dajin na sarkin Ururu ne a bisa doron ƙasa ta farko saina rusa ku." Tanan rufe baki ta zare takobinta, inda nan take wasu taurari guda uku suka bayyana a kewaye da takobin. Ai tunma kafin ta juya takobin dukkanin wannan lambu ya kama da wuta. Wanda idan da zaka kula zaka ga irin wutar dake ci acikin idonta ce. A dai-dai wannan lokaci Armad ya sume a wajen. Babu abinda yake iya tunowa sai tashi dayayi washe gari ya ganshi akan gadonsa Hidaya na gefensa tana shafa kansa. To a wannan shekara ne da kakan Armad mai suna Zaikid da yayar tasa Hidaya suka tafi wani aiki wanda Armad yayi-yayi amma suka ƙi bayyana masa ina zasu. Daga ƙarshe ya haƙura. Bayan wata biyu da wannan tafiya tasu, dattijo Zaikid ya dawo shi kaɗai. Babu Hidaya amma akwai takobin ta mai taurari ruwan ɗorawa a hannunsa. Armad ya taho da gudu yana tambaya ina take, amma kakan nasa baice komai ba sai kawai takobin daya miƙa masa. Armad na karɓa ya fashe da kuka ganin alamun jini a jiki. Tun daga wannan lamari Armad ya ɗau takobi ya kuma shiga koyon horo da alamuran Izza. ____ To ko ina Hidaya Wilbafos? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 48: Uznu Ururu 1 Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin WilbafosRundunar mayaƙan sarki Ururu, sarki bisa doron ƙasa ta farko, sun rabu ne izuwa kaso kimanin biyu, kaso na farko masu kare Rukunin gasar Jinzidal, kaso na biyu kuma masu kula da doron ƙasa ta farko da babbar fadar sarki Ururu. Idan muka ɗauki runduna mai kare rukunin Jinzidal zamu ga a can ƙololuwar sama akwai manyan kwamandoji biyar, a ƙasansu kuma akwai muƙamin kyaftin-kyaftin guda biyar-biyar, wanda kowannensu nada iko akan miliyoyi mayaƙa dake ƙarƙashinsa. Kowanne kwamanda acikin biyar ɗinnan nada Kyaftin guda biyar a ƙasansa. Kowanne kyaftin kuwa nada a ƙalla girman Izza da yakai shekaru dubu da ɗoriya, kuma kowannensu mutun ne shahararre a fagen Izza a ƙasa bakwai. Su kuwa kwamandojin nan guda biyar kowannensu nada a ƙalla girman Izzar da takai shekaru ɗai-ɗai har dubu biyar da ɗoriya. Sannan kuma a ƙalla sai ya mallaki Ururu. Wato dai sai yana da baƙaƙen idanu. Kowannensu anyi ittifaƙi yana da ƙarfin da zai iya juya daula duk girmanta izuwa toka cikin ƴan daƙiƙu. Aikin wannan mayaƙa shi ne kawai kula da rukunin Jinzidal. Da tabbatar da cewa lallai kowa yana biyayya akansa. Uznu Ururu ɗaya ne daga cikin wannan kwamandoji biyar na mayaƙan Ururu. ____ A wannan lokaci Armad ya tattaro dukkan ƙarfinsa, inda ya miƙa hannu ya daki Littafin-takobin dake cikin rigarsa. A iya saninsa wannan littafi daya samu a sakamakon rasa Miyurarsa ya taka rawa ta musamman a faɗansa na baya, amma baisan mai yasa a wannan hali da yake buƙatar taimako yaƙi yi masa komai ba. Hakan nema yasa ya yanke shawarar ya zungureshi yaji ko zai iya tashinsa. Ai kuwa hannunsa na taɓa littafin, littafin ya fara ɗaukan zafi yana bada koren haske. Tun daga nesa zaka iya hango wannan haske. Shima Ikenga wanda ya daɗe da tashi tsaye yaga wannan haske, kuma nan take ya zare takobinsa ya yiwo kan Armad da niyyar hanashi koma mai yake son aiwatarwa. Domin zuwa wannan lokaci Ikenga yasan Armad ba kanwar lasa bane, saboda haka bashi da wata hanya face yai sauri ya ƙarasa Armad kan ƴayi wani abu. A ɓangaren Armad kuwa wannan haske yasa yana jin zafi tamkar ana soya shi a raye. Amma duk da haka ya daure ya cije, kasancewar yasan a ƙarshen wannan haske babbar Izza na nan tafe. Kuma da sannu zai ci galaba akan Ikenga zarar wannan Izza ta bayyana a gareshi. Shekaru 10,20,......... A dai-dai lokacin da Izzar Armad ta fara yin sama a wannan lokaci Ikenga ya ƙaraso kansa. Yana zuwa ya ɗaga takobinsa sama ya kuma nufi wuyan Armad da niyyar sare masa kai baki ɗaya. ___ A dai-dai wannan lokaci da Ikenga ya ɗaga takobinsa Uznu Ururu ne ya canja fuska ya kuma haɗe tare da yanke shawara nan take. Acikin ransa yana mai cewa, 'Idan na bari ya kashe wannan yaro Armad to lallai Littafin-takobi ƙara ɓacewa zaiyi. Kuma ba lalle na ƙara ganinsa ba sai bayan wasu ɗaruruwan shekarun.' Yana gama wannan tunanin acikin ransa ya ɓace daga kan kujerarsa dake cikin wajen manyan baƙi. Yana ƙara bayyana sai gashi a tsakanin Armad da Ikenga. Nusi na ganin haka ta zare takobin ta, ta caki hannunta na dama, sannan ta shafa jini akan takobin. Wani sanannen farin haske wanda ke fita a duk lokacin da mutun yake ƙona ruhinsa domin ya samu ƙarin ƙarfin Izza ya fara tashi daga jikinta. Nan take Izzarta ta juye izuwa shekaru ɗari uku da saba'in da huɗu. Ta bace daga inda take ta bayyana a gaban Armad. Kana ganinta kasan tayi shirin ko a mutu. A dai-dai lokacin ne shima Armad Izzarsa takai ɗari da uku. Lamarinda ya bashi damar miƙewa cikin kwanciyar hankali ya kuma ɗauki takobinsa ya ja da baya tare da Nusi yana mai kallon wannan baƙon mutun daya bayyana. Shima dai Ikenga yana ganin dirar Uznu Ururu yai tsalle zuwa baya. Ya kuma ƙurawa wannan ma'aboci Ururu ido. Tunda Uznu ya dira a filin idanunsa a rufe suke kuma babu wanda yai motsi. Amma a wannan lokaci ya buɗe baki ya fara magana cikin wani sauti mai tsananin tsufa da firgici, "Suna na Uznu Ururu. Gasar Jinzidal ta wannan shekara tazo ƙarshe, kuma ina mai sanar daku cewa kowa zai iya tafiya amma banda wannan." Yai nuni da ɗan yatsansa izuwa Armad. Tun kafin ya rufe bakinsa Nusi ta fara magana, "Armad gudu...kada ka tsaya kuma kada ka waiwayo. Zan riƙe shi anan tsahon lokacin da zaka iya guduwa." Armad ya tsaya baki a buɗe cike da mamaki yana ƙoƙarin gane maike faruwa. Amma kan yace komai Ikenga ya tafa hannayensa ya kuma ɓace daga filin. Ga dukkan alamu Ikenga yasan wane ne Uznu Ururu. Armad na nufin tambayar Nusi maike faruwa ya ƙara jin muryar Ururu, "Indai aka rubutawa bawa adadin kwanaki, lallai bazai iya shallakewa ba. Tunda dai halakarku tazo a wannan rana lallai babu wanda ya isa ya hana hakan a ban ƙasa." Tun kafin Armad ya gama gane abinda yace, Uznu Ururu ya buɗe idanunsa a hankalinsa. Faruwar hakan keda wuya Armad yaga dukkan duniya ta koma baƙa-ƙirin, tamkar wanda aka rufewa ido ko kuma wanda aka saka acikin surƙuƙin baƙar duniya. Babu abinda yake gani sai duhu da kuma wasu ɗugonguna kamar na tawada manya guda biyu a gabansa. Lallai bada ban zafi da nauyi da yake ji a jikinsa ba da tuni ya yarda da cewa mafarki kawai yake. Wata Izza mai ruɗarwa da rikitarwa ta fara shiga cikin jikinsa. Babu shiri ya fara ji tamkar ana soke shi da baƙaƙen wuƙaƙe ta ko'ina. Tamkar dukkan duniya so take ya mutu, tamkar saiya mutu sannan za'a samu sauƙi. Lallai babu makawa Armad bai taɓa jin ƙarfin Izza mai rushe ruhi irin wannan ba. Kai ko ta cikin wannan littafi bata kaita ba. Lokaci ɗaya kaɗai da Armad ya taɓa jin irin wannan Izza shi ne sanda yake tare da yayarsa Hidaya acikin wannan daji. 'Wato wannan Izza ita ce Ururu!' Wannan shi ne kawai abinda yace acikin ransa kafin yaji numfashinsa ya fara ɗaukewa. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 49: Uznu Ururu 2 Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos A cikin filin nan kuwa tuni ƴan kallo da kowa da kowa suka ƙame cak, babu mai motsi kuma babu wanda yasan inda kansa yake ballantana susan mai ake ciki. Amma bisa mamaki wannan abu da Armad ke gani baiyi aiki akan Nusi ba. Domin kuwa bawai motsi ƙaɗai take yi ba, tuni ta zare takobinta ta yo kan Uznu Urúrú da niyyar ta sare kansa. Tana ƙarasowa, ta ɗaga takobin ta ta da niyyar saransa, amma Uznu Ururu ko motsi baiyi ba har saida takobin ta kusa taɓa jikinsa da kimanin ɗan taƙi, inda a wannan lokaci ya ƙifta idonsa sau ɗaya kawai. Haka na faruwa wani baƙin haske mai tsananin duhu tamkar na kabari ya fice daga cikin idonsa. Wannan haske na fitowa ya juye izuwa siffar baƙin miciji mai kimanin tsayi zira'i hamsin. Wanda nan take ya fasa kai ya buɗe baki ya haɗiye wannan takobi tata. Ai kuwa haka na faruwa takobin ta fara murmushewa tana juyawa izuwa toka. Kan kace meye wannan, wannan miciji ya fara tunkarar jikin Nusi yana nema ya haɗiye ta. Nusi tayi tsalle ta koma baya. Amma Nusi na dira a ƙasa wannan miciji ya juye izuwa ƙatoton al'amudi na baƙin ƙarfe ya kuma yi kanta. Nusi ta zare wani allon tsafi ta kuma fara karanto ɗalasimai wanda suka sa wasu manyan ƙarafa na jan ƙarfe suka bayyana a tsakanin ta da wannan al'amudi. Tun kafin ma al'amudin ya ƙaraso Nusi tayi tsalle cikin fasaha da kwarewa izuwa gefe inda ta ƙara kiran sunan wani ɗalasimin. Wanda nan take ya saka wani tsiro ya fara bayyana a gefen Uznu Ururu, kuma kafin Uznu yayi wani abu tuni wannan tsiro ya zama bishiya ya kuma ɗaure shi a cikin jajayen rassansa. Nusi ta tafa hannu wata ƴar ƙaramar tukunya ta koren dutse ta bayyana a hannunta. Nan take ta fara daka wani sinadari acikin tukunyar a dai-dai lokacin da wata ƴar ƙaramar wuta ta kama a ƙasan tukunyar ta kuma fara soya abinda ke cikin ƙaramar tukunyar. Nan take wani sauti da wani irin ƙanshi mai kama dana ƙasan tekun maliya ya fara ɓulɓula yana mamaye ko'ina. Ba jimawa wani koren ruwa mai danƙo ya bayyana acikin tukunyar, sannan Nusi bata jira komai ba ta watsawa Ururu wannan ruwan tsafi. Dukkanin abubuwan nan sun ɗau lokaci wajen bayani amma a zahiri baifi daƙiƙa biyu zuwa uku suka ɗauka ba. Ruwan na taɓa bishiyar

Chapter 20 of 33