Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kace meye wannan wata ƴar ƙofa ta bayyana a jikin bangon. Cikin sauri wannan dattijuwa ta juyo ta dubi wannan budurwa tare da cewa, "gimbiya ta lokaci yayi, wannan ne gwaji na talatin da ɗaya, wanda kuma kamar yadda muka yanke shawara yanzu shi ne kwaji na ƙarshe, indai ba'a samu nasara a wannan karanba, to dole mu bi umarnin shugaba Bihanzin mu koma gida!" Kafin ta gama rufe bakinta tunu wannan budurwa wadda ba'a iya tantance launin kayan jikinta da kamanninta kwata-kwata, badan komai ba saboda tsananin haske mai kashe ido dake tashi daga jikinta, ta tashi tsaye gami da duban wannan dattijuwa tare da kyaɗa kai. Kafin daga bisani ta shige cikin wannan ƙofa. Tana shiga ƙofar ta ɓace ɓat, a lokacinda ita kuma wannan dattijuwa tai ajiyar zuciya tare da cewa, "sa'a tana tare dake gimbiya Nostalgiya Nára!" *** Bayan kwana huɗu da shigar wannnan budurwa cikin wannan ƙofa, a zaune a bakin wani kogi mai ɗauke da baƙin ruwa, ita ce. Inda take zaune cikin nutsuwa, ƙafafunta a tankwashe, kanta a kafe akan wannan ƙatoton kogi tana nazari, wannan ruwa wanda gaba ɗayansa baƙi ne, baƙi-ƙirin! Abin al'ajabi a kefenta kuma wani saurayi ne kwance a sume dukkan kayan jikinsa sunyi daga-daga, tayadda sama da rabin jikinsa a fili yake a bayyane. Fatarsa ta ƙoƙƙone, sannan kuma duk jikinsa ƙasa ce da kuma datti ko'ina ka kalla. Sannan kuma bisa mamaki akwai wani farin haske mai siffar miciji yana ta kewaya jikin wannan saurayi dake kwance a gefe bai san inda kansa yake ba. Sai dai kuma duk da wannan hali da wannan saurayi yake ciki, akwai wani jan kyalle a ɗaure a goshinsa, wanda babu alamun ƙonewa a tattare dashi ko kaɗan. Hasalima ko datti babu a jikinsa tamkar daga baya aka ɗaura masa shi. Idan ka lura da wannan saurayi sosai zaka ga ba wani bane illa Armad Wilbafos! A kwana a tashi Armad na kwance a sume a gefen wannan budurwa, har tsahon kwana uku, ita ma tana zaune tana nazarin wannan baƙin ruwa ko motsi batai ba tsahon wannan kwanaki. Sai a ƙarshen wannan rana ne, wannan budurwa ta ɗauke idonta daga kan wannan baƙin ruwa, ta kuma juyo ta kalli Armad da dara-daran kyawawan idanuwanta. Wannan budurwa ta kasance nada matuƙar kyawun gaske, tayadda a lokaci ɗaya zata sa duk wanda ya kalleta cikin zulumi da tunanin anya kuwa ya taɓa ganin mai kyanta akaf tsahon rayuwarsa da mafarke-mafarkensa da labaran daya taɓa karantawa. Da kuma kokwanto ko anya ma kuwa mutun yake gani! To kamar dai ƙirar jikinta tsayin fuskarta ya dace matuƙa da faɗinta, lamarinda ke bayarda fasalin tsananin cikar kyawun diri. Idanuwanta dara-dara ne, wanda farin cikinsu fari ne fat, kuma baƙin cikinsu baƙi ne wuluk. Sannan kuma ga hanci wanda tsahonsa ya dace da girman fuskar tata. Tana da yawan gira, wadda take a saice dai-dai da dai-dai a saman idanunta. Duk da cewa tsahon baƙin gashinta ya kai har gadon bayanta, amma wannan ba abu bane da Armad bai saba gani a ƙasar daya baro ba, amma babban abinda zai bashi mamaki dazai farka shi ne, wannan yadda wannan gashi yake kyalli yana sheƙi, tayadda idan ka ƙura masa ido zaka iya faɗawa wasu tunane-tunane basu dace ba. Tun kafin tai murmushi akwai alamun dimful dake bayyane akan madaidaicin kuncinta. Idan ka haɗa cikakken kyawun diri da ƙololuwar kyawun fuska da wannan budurwa ke dashi, sannan kuma ga yanayin yarinta dake tashi daga ilahirin jikinta, sai kaga cewa lallai samun wadda takai ta kyau abu ne da zaiyi matuƙar wahalar gaske koda tsakanin mafi kyawun fararen aljanu da mutane farko. Kai lallai babu wata tantama idan kace kasancewar wannan budurwa a wajen da take yayi matuƙar ƙarawa wajen kyau, tamkar kyawun surar ta yana shafar shi kansa muhallin da take musamman duba ga irin hasken da jikinta yake bayarwa yana ƙarawa bakin wannan kogi ƙawa. Bayan ta juya ga Armad ta ɗaga hannunta na dama, inda ta ɗorashi a ƙirjinsa. Abin mamaki hakan na faruwa nan take gaba ki ɗayan ciwukan dake jikin Armad suka fara warkewa. Kan kace meye wannan tuni sun gama haɗewa, jikinsa ya koma kamar ba'a taɓa jin rauni ba akansa. Sai dai kuma abin mamaki a lokacin gaba ɗaya hasken dake jikin wannan budurwa a lokaci guda ya zuƙe ya ragu sosai, tayadda kallo ɗaya zakai mata kasan cewa warkar da ciwukan Armad da tayi Armad yana da farashi mai tsauri. *** Tana ɗauke hannunta ta fara haki tana nishi irin wanda ya dace da ma'abota ƙololuwar kyawun sura da ruhi, na ɗan tsahon lokaci, kafin daga bisani ta dawo hayyacinta, inda ta fiddo da wata takarda daga cikin rigarta, ta kuma sakawa Armad acikin ragowar fatattakakkun kayansa. Haka na faruwa ta miƙe, inda tayiwa wannan baƙin ruwa kallon ƙarshe, sannan ta juya tabar Armad a kwance a inda yake. Kuma kan kace meye wannan, wannan kyakkyawar sura ta ɓace daga wannan waje. To a ƙarshen wannan ranar ne shima ya farka a wani yanayi na kasala. Abinda ya fara bashi mamaki shi ne ya tabbatar da cewa acikin wannan gari ya faɗi ya suma, bayan yaji wannan murya, amma kuma yanzu gashi nan a kwance a gefen wani kogi. Sannan kuma ga kayansa nan a ƙoƙƙone, alamun tabbas wuta ce ta ƙona su, amma kuma shi babu ko rauni ɗaya a jikinsa. Yana ganin haka abu na farko daya fara faɗo masa shi ne wannan takarda wadda yasan cewa ita ce manuniyar hanya a wajensa, indai yana so ya fita daga cikin wannan duniya lafiya. Saboda haka cikin sauri ya miƙa hannunsa cikin aljihun wandonsa duk da yasan ba'anan ya saka ta ba, to amma kamar yadda ya gani shishi kaɗai ne aljihun daya rage a jikinsa. Sai dai kuma bisa mamaki sai yaji takarda aciki. Yana fito da ita mamaki ya ƙara kamashi, bayanda ya fara ganin canje-canje a jikinta, lamarinda ya tabbatar masa cewa ba wancan takardar bace. Domin a ƙasan wannan takardar hadda rubutu, ansa 'Gimbiya Nostalgiya Nára' an kuma saka hannu daga can ƙasa. Abubuwan da duk babu su a wancan takarda da Armad ya sani. Cikin mamaki ya fara tunanin me ya faru bayan ya suma, amma ina duk yadda yai ƙoƙari baya iya tuna no komai. Sai dai kawai abu ɗaya da yake iya hasashe shi ne cewa, lallai cetarsa akai daga cikin wancan gari daya suma aciki, kuma ga dukkan alamu waɗanda suka ceto shi sun san muhimmancin wancan takarda. Wanda hakan yasa da suka ga tasa ta ƙone suka canja masa wata. "To amma su wane ne suka cece ni?" Wannan ita ce tambayar da yake ta yiwa kansa kuma bashi da amsa illa abu ɗaya, wato sunan 'Gimbiya Nostalgiya Nára', wanda ya gani a jikin takardar. Sunan da bashi da masaniyar ko na waye!!! Armad bashi da masaniyar cewa ga wadda ta ceto shi, sannan kuma a wannan lokacin za'a iya cewa kusan duk su biyun basu da masaniyar cewa wannan shi ne abu na farko da zai haɗa tsakaninsu a wani irin tarihi da baza a taɓa mantawa dashi ba!!! *** Sai dai kuma ba jimawa Armad ya yanke shawarar lokaci yayi da ya kamata ya fita daga cikin wannan duniya izuwa doron ƙasa ta huɗu. Inda ya yanke shawarar zai fara neman Tirifil-fakta daga nan. Saboda haka nan take ya ajiye tunanin gimbiya Nostalgiya Nára a gefe ya kuma dubi takardar dake hannunsa inda ya fara karanto wasu ɗalasimai daga ciki. Yana gama ambatarsu, ba daɗewa ya fara hango wani ɗan ƙaramin kwale-kwale yana isowa inda yake. Yana zuwa baiyi wata-wata va ya ɗare akai, sannan ya ƙara karanta wasu ɗalasiman ƙamarinda yasa wannan jirgi ya fara tafiya izuwa gabas masi kudu akan wannan baƙin kogi!! Armad ya fuskanci gaban kwale-kwalen nan, yana ta miƙa ido ko zai hango gaba, amma ina. Har gari ya waye, rana taje tsakiya bai ga komai ba. Lamarinda yasa ya yanke shawarar ya ɗan rintsa kaɗan kafin ya isa, inda ya nemi waje ya kwanta, hannunsa akan takobinsa. A lokaci daya tashi baiga rana a sama ba, hasalima yana kallon gabas yaga alamun ɗagowar rana, lamarinda yasa yasan lallai safiya ce, abinda ke nuna cewa ya kwana ya kuma wayi gari yana bacci. Yayi mamakin yadda yai bacci da yawa haka, lamarinda yasa ya fara ƙoƙarin tuno lokaci na ƙarshe daya kwanta yai bacci haka, ya kuma tuno cewa ai tun sanda aka ƙwanƙwasa masa ƙofa aka ce ga mahaifiyarsa ta dawo daga yaƙi amma bata san inda kanta yake ba. "Hmmmm!!" Ajiyar zuciya kawai yai, ya kuma ƙara ji a ransa cewa lallai yana so yai sauri ya nemo wannan mutun mai suna Tirifil-fakta, koya koma gida yaga mahaifiyarsa. Amma yana cikin wannan tunani ne yaga wani abun; wannan kuwa ba komai bane, illa sararin samaniyar wannan waje. A iya saninsa, a kullum idan rana ta fito, akwai rana ɗaya wadda take tasowa daga gabas ta faɗi a yamma, sannan sai kuma ɗayar wadda bata motsawa tana tsaye a tsakiyar sama cak. To amma banda a wannan waje, inda duk yadda ya duba guda ɗaya tak yake iya gani, wadda ke tasowa daga gabas. Bai san mai ya janwo hakan ba, amman babban abinda yake gabansa shi ne yaushe zai isa bakin gaɓa. A zuciyar sa tun daga sanda ya taka ƙafa ya shiga wannan ƙofa da Abul-Babara ya buɗe masa, yake ta tunanin dame zai fara wannan alƙadari nasa na neman TF, idan ya isa doron ƙasa ta huɗu. Armad nata tafiya acikin wannan jirgi, babu abinda ke ransa sai son ya isa bakin gaɓa. A rana ta biyar yana cikin tafiya yunwa ta tayar masa, inda ya rasa yadda zaiyi, kawai saiya rufe ido ya fara rera wakar da mahaifiyarsa take masa sanda bai kai shekara goma ba, idan tana so yai bacci. Ai kuwa haka akai, ba jimawa bacci ya ƙara ɗauke shi, yana kwance yana bacci, kwatsam girgizar jirgin da yake ciki tasa ya farka. Yana buɗe ido, yayi arba da abinda ya daɗe yana jira, wato bakin gaɓa. Sai dai kuma ba a yadda yai tsammani ba. Domin kuwa abinda ya hango daga nesa shi ne bango ruwa, wanda kallo ɗaya kawai yai masa yasan cewa lallai wannan yana kama da bangon duniya. To amma ba wannan ne abinda ya firgita shi ba, illa wani ƙatoton waje mai kama da wawakeken rami dake tsakanin wannan bangon da kuma wannan baƙin ruwa da jirginsa yake kai, wanda lallai idan da za'a auna zai kai kimanin faɗin taku dubu da ɗoriya. Kuma daga yanayin tafiyar jirgin, ya fuskanci cewa bashi da niyyar tsayawa ko kaɗan, hasalima yana ƙara kusanto wannan rami yana ƙara sauri, tamkar dama aikinsa ya jefa Armad cikin wannan rami. A lokacin da Armad ya farka tuni wanki hula ya kaishi dare, saboda baifi saura taku biyar ba tsakaninsa da wannan rami ba, amma a wannan lokaci saura taku uku kacal. Tuni Armad yake ta tunanin wacce hanya zaibi ya tsayarda wannan jirgi, amma ina babu wata hanya mai ɓullewa data zo kansa. Duk tunanin da yayi sai yaga bamai ɓullewa bane, saboda babu wani abu mai kama da alamun Armad zai iya riƙewa ko kuma ɗanewa wanda zai iya sawa wannan kwale-kwale ya ƙi faɗawa wannan rami. Yana cikin wannan tunani ne, ba shiri wannan jirgi nasa yaje bakin wannan rami, inda bisa mamaki kawai ya tsaya cak, sannan kuma kafin Armad ya ƙarasa ajiye ajiyar zuciyar da yayi tuni wannan kwale-kwale ya ɗaga shi sama, inda cikin sauri ya cilla Armad cikin wannan wawakeken rami, shi kuma ya juya ya koma inda ya fito!!! Copyright © 2017 A M IBRAHIM . All rights reserved Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 8: Sirrin da zai rikita Duniya Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Abu ɗaya da Armad yake iya tunawa a lokacin da yake tsaka da faɗawa cikin wannan wawakeken rami shi ne riƙe takobinsa da yayi, ya ɗaure ta a jikinsa. Amma bayan wannan, gaba ɗaya hankalinsa dusashewa yayi, kafin daga bisani ya sume gaba ɗaya. To koma dai mai ya faru bayan wannan, wanda bazai iya tunawa ba, to yana ganin bai halaka shi ba tunda a dai-dai wannan lokaci ya tsinci kansa a kwance a kan tantagaryar ƙasa da kuma ragowar numfashi a jikinsa, ga kuma waɗansu abubuwa daya kasa tantancewa a tsaye a kansa... "Hmmmm...." Cikin firgici Armad yai ajiyar zuciya, acikin ransa bayanda kwatsam abin ya faɗo masa a rai cewa ko mutuwa yayi. A hankali a hankali, ganinsa yana ƙara dawowa, waɗannan halittun dake bisa kansa su na ƙara bayyanuwa, sai ya gano cewa ashe mutane ne! Ba daɗewa ya gano cewa ashe maza ne guda biyu da mace ɗaya. wadda ke tsaye a bayansu. Mamaki ya cika zuciyar Armad kuma hankalinsa ya ɗan kwanta, lokacin da yaga macen dake cikinsu ta cillo masa bututun ruwa. Amma kafin ma ta ƙaraso wajensa ɗaya daga cikinsu wanda ke tsaye a daman Armad yasa ƙafa ya doke bututun, yana mai cewa, ''meye amfanin shayar dashi!'' Babu wanda ya ce uffan acikinsu akan wannan abu daya afku, kuma akan idon Armad wannan mutun ya gabato gareshi da farar ankwa ya ɗaureshi gaba da baya. Sannan suka ɗaureshi shi akan wani doki ƙarami samfurin ak-wali, sannan suka hau nasu dawakan suka nufi gabas. Lokaci bayan lokaci Armad zai farka ya ji basu daina sukuwar da suke ba kafin ya ƙara komawa. Bai san tsahon lokacin da sukai su na tafiya ba, abu na gaba daya gani shi ne, farkawa acikin wani ɗan tanti ɗaure acikin ankwa. Bayan ya nuts, abinda ya fara lura dashi shi ne, kwatakwata jikinsa babu alamun ciwo ko kaɗan, lamarinda ya bashi mamaki sosai, saboda sanda ya fara buɗe idonsa bayan faɗowarsa daga wannan waje, baya ko iya motsa jikinsa saboda ciwo. Yana ɗaga ido yai arba da waɗannan mutane ne uku da suka ɗakko shi, zaune akan kujerun alfarma da akaiwa ado da jan dinare, inda ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Yana kwance, baya iya motsa komai a jikinsa face idanunsa, wanda yayi amfani dasu wajen ƙurawa suturar dake jikin wannan mutane kallo. Dukkaninsu a sanye suke da kayan yaƙi, wanda kallo ɗaya ya isa mutun yasan cewa masu tsadar gaske ne, kuma na sarauta. Mafi tsayi acikinsu namiji ne, yana tsaye bisa saitin kan Armad, sai kuma mai biye masa, wanda ke tsaye a gwiɓinsa, sai kuma macen, Babban cikinsu magidanci ne wanda tabbas zaifi shekaru talatin. Yana da ƙira cikakkiya abar dacewa da sadaukai. Domin tun daga inda Armad yake yana iya hangen murɗaɗɗen zubin jikinsa. Da kafaɗunsa masu faɗin gaske duk da cewa bashi da tsayi sosai. Fuskarsa tana da ɗan tsayi, amma saboda faɗin ta ba sosai mutun zai iya kula da tsayin ba. Babu gashi da yawa a fuskar tasa, face wani ɗan gemu mara tsayi sosai. Sai kuma mai biye masa, wanda a karon farko da Armad ya kalleshi ya yanke shawarar cewa ƙanin wancan zabgegen ne. Badan komai ba saboda kama da suke da juna, duk da kuwa cewa babban ya fishi girma sosai da sosai, amma kana ganinsu zaka ga kama. Dukkanin su, su na sanye da ƴar shara ta jan alharini, wadda akaiwa ado da zinare daga wuya zuwa ƙasa. A wannan lokaci ne kuma idanunsa suka kai ga macen dake gefensu. Yana ɗora idonsa akanta ya ce, "kai!!!" Cikin mamaki ya ƙara wara idanuwansa saboda wani abu dake faruwa a dai-dai wannan lokacin. Ba komai bane yake faruwa illa kasancewar Armad acikin waniyanayi da yake ji a ransa cewa lallai ya taɓa ganin wannan budurwa, sai dai kuma a lokaci guda hankalinsa na tambayarsa a ina! Bakinsa a buɗe, mamaki kawai yake akan abinda ke faruwa, sannan kuma yana ƙara tambayar kansa akan wace ce taƙamaimai wannan budurwar! Duk da ƙarancin shekaru na Armad amma bai daɗe yana kallonta ba, ya tabbatarwa da kansa cewa lallai bai taɓa gani ko jin halitta mai kyawunta ba, kai koda a zane ko kuma a labarai da tarihin fararen aljanu! Tuni Armad ya ƙurawa wannan budurwa, wadda bata fi sa'ar sa ba ido, bama tare da ya sani ba. Badan komai ba saboda kwatsam yaji a ransa cewa lallai akwai yiwuwar idan ya fiya kallon fatar jikin wannan budurwa, zai iya samun damar ganin wucewar jini da idonsa, kamar yadda ya ji ya faru a 'Hikayar Lasína Naitingel', macen da aka ce ba'a taɓa haifar wata data kaita haske ba! Sai dai amma Armad bai samu damar cimma burinsa na ganin hakan ba, domin a dai-dai lokacin ne ya fuskanci cewa ashe a ɗaure yake tamau acikin ankoki!!! Ba shiri ya dawo hayyacinsa, tare da canja fuska gami da cewa, "wai su waye ku, kuma me nayi muku da zaku ɗaure ni acikin ankoki haka!" Bai ƙarasa rufe baki ba, saurayin dake ɓangaren dama ya dubeshi a fusace gami da cewa, "mu zamuyi maka tambaya, bakai zakai mana ba. "Saboda haka abu na farko daya kamata ka sani shi ne, muna so kayi mana wani abu guda ɗaya, idan kayi shi, zamu sake ka ka tafi, idan kuma baka yishi ba to...!" Saurayin na zuwa nan a zancensa sai ya ja numfashi tare da kallon doguwar takobinsa yana kuma yiwa Armad inkiya da ita. Mamaki ne kawai ya cika zuciyar Armad, ya kuma rasa mai zaice, lamarinda yasa nan take ransa ya ɓaci. Amma koda ya duba ya ganshi ɗaure acikin ankoki sannan kuma ga takobinsa can a ajiye a gabansu, sai yasan babu abinda zai iya a wannan lokaci, banda sauraronsu yaji mai suke tafe dashi. Ba tare da ɓata lokaci ba, ɗaya namijin ya taso daga inda yake, ya gabato gaban Armad a hankali. Inda yana zuwa ya zaro wani ɗan allo daga cikin ƙasaitacciyar alkyabbarsa ya nunawa Armad. Sannan kuma a lokaci guda da ɗanyatsansa na dama ya nunawa Armad wasu rubuce-rubuce a gaban allon wanda aka yisu tayadda suka kewaye izuwa fasalin ƙawanya, gami da cewa, "abinda kawai muke buƙata da kai shi ne ka ɗisa jininka acikin wannan ƙawanya." Muryarsa a nutse take, tamkar babu wani tashin hankali aciki ko kuma damuwa aciki, amma kana kallon idanunsa zaka ga wani abu mai kama da buri, wanda zai tabbatar maka da cewa ko ma mai suke nema a game da Armad, lallai babban abu ne. Wannan allo ya kasance yana da matsakaicin girma, kuma fari ne mai ɗan duhu. Sinadarinsa kuwa yana kama da sinadarin haƙorin bakin ɗan adam. Sheƙi kawai yake da ɗaukar ido duk da rana bata haska shi ba. A tsaye baifi kamu biyu ba, sannan bashi da kauri kwatakwata. Ƙurawa wannan rubutu ido kawai Armad yayi tsahon lokaci yana nazari, kafin daga bisani ya gane anyi shi ne da tsohon yaren Aldurish! Yaren da kusan zaka iya cewa an manta dashi kwata-kwata a wannan lokaci. Saboda sama da shekara dubu aka maye gurbinsa da sabon yaren Aldurish, wanda akewa laƙabi da AldurishAmri saboda alaƙarsa da Amri. Kuma kusan kowa ya iya Aldurish-Amri, amma samun mutun ɗaya daya iya Aldurish-tsoho, dai-dai yake da samun raƙumi acikin kuratandu. Armad na ganin wannan yare yasan cewa lallai waɗannan mutane dake gabansa kodai ƴaƴan manyan sarakuna ko kuma sun fito daga cikin manya-manyan ƙungiyoyi, domin a iya tunaninsa indai ba haka ba to babu yadda za'ai su samu wata alaƙa da wannan yare. Armad ya iya wannan yare sosai da sosai, duk da cewar sai da ya ɗauki lokaci mai tsahon gaske yana koyonsa a wajen mahaifiyarsa. Saboda haka yana gani wannan rubutu, ya karance shi. Ya kuma ƙara tabbatar da cewa abinda suke nema lallai babban abu ne. Saboda haka sai ya fara tunanin mafita. Badan komai ba, sai dan cewa daga cikin ƴan dabarun daya ilmantu dasu a iyakacin ƴan shekarunsa, yasan cewa abu ne mai sauƙi bayan yayi musu abinda suke so, su halaka shi. Ƙurawa wannan rubutu ido kawai Armad yayi tsahon lokaci yana nazari, kafin daga bisani ya gane anyi shi ne da tsohon yaren Aldurish! Yaren da kusan zaka iya cewa an manta dashi kwata-kwata a wannan lokaci. Saboda sama da shekara dubu aka maye gurbinsa da sabon yaren Aldurish, wanda akewa laƙabi da AldurishAmri saboda alaƙarsa da Amri. Kuma kusan kowa ya iya Aldurish-Amri, amma samun mutun ɗaya daya iya Aldurish-tsoho, dai-dai yake da samun raƙumi acikin kuratandu. Armad na ganin wannan yare yasan cewa lallai waɗannan mutane dake gabansa kodai ƴaƴan manyan sarakuna ko kuma sun fito daga cikin manya-manyan ƙungiyoyi, domin a iya tunaninsa indai ba haka ba to babu yadda za'ai su samu wata alaƙa da wannan yare. Armad ya iya wannan yare sosai da sosai, duk da cewar sai da ya ɗauki lokaci mai tsahon gaske yana koyonsa a wajen mahaifiyarsa. Saboda haka yana gani wannan rubutu, ya karance shi. Ya kuma ƙara tabbatar da cewa abinda suke nema lallai babban abu ne. Saboda haka sai ya fara tunanin mafita. Badan komai ba, sai dan cewa daga cikin ƴan dabarun daya ilmantu dasu a iyakacin ƴan shekarunsa, yasan cewa abu ne mai sauƙi bayan yayi musu abinda suke so, su halaka shi. Amma kuma bayan ɗan lokaci kaɗan, yana kallonsu suna kallonsa. Gashi acikin ankwa, gashi shi kaɗai su uku, sai kawai ya yanke shawara duk abinda zai aiwatar zai ta'allaƙa ne da mai ya faru a gaba bayan ya ɗisa jinin nasa. Badan komai ba, saboda baiga wata hanya dazai ƙi saka jinin nasa kuma su ƙyaleshi ba. Kuma idan suka samu matsala tun daga ɗisa jinin, ya tabbatar da cewa yiwuwar kuɓutarsa a gaba ta ƙara raguwa. Saboda haka ya yanke shawara ya nuna musu ya amince zai aikata hakan. Lamarinda yasa wannan saurayi daya taso ya zare farar doguwar takobinsa tare da nunawa Armad kakkaifan tsininta, yana mai cewa, "ina kake so na fasa?" Babu alamun tausayi ko kaɗan a tattare dashi, sai dai kuma shima Armad babu tsoro a tattare dashi. Domin tuni yayi masa nuni da tafin hannunsa na dama. Haka kuwa akai ba jimawa jinin Armad ya ɗisa akan wannan allo acikin wannan ƙawanya. Hakan na faruwa ragiwar mutun biyun dake zaune, suma suka taso suka tsaya akan Armad, inda macen tai wani ɗan ƙaramin murmushi wanda bai ƙunshi alamun komai, tare da cewa, "Nan bada jimawa, sak irin muryar da kaji acikin wancan gari zatai magana daga cikin wannan allo. "Abinda kawai muke so shi ne ka gaya mana abinda tace!!" Duk da ƙarancin shekaru irin na Armad, amma a dai-dai wannan lokaci abu ɗaya ne kawai yake ta kai-komo a zuciyar sa, wanda shi ne kawai yanayin yadda maganar wannan budurwa take shafar hatta iskar dake ilahirin wajen; kasancewar Armad zai iya rantsewa indai ba mafarki yake ba, to lallai yaga iskar cikin wannan tanti tana ƙara kyau. Bai gushe ba yana cikin wannan hali ba, har sai da yaga takobin ɗaya daga cikin samarin nan biyu a wuyansa tukun. To sai a wannan lokaci ne ya fara tuno abinda yaji ta faɗa na game da wancan murya. Sannan kuma ya fara mamakin yadda akai ta san al'amarin shigarsa wancan gari. Sai dai kuma tunda dama Armad ya kasance mutun ne mai saurin gane abubuwa, ba jimawa ya biɗe baki cikin mamaki yana kallon wannan budurwa tare da cewa, "Gimbiya Nostalgiya Nára?" Tsahon daƙiƙu bata ce masa komai ba, kafin daga bisani ta kalli Armad ido cikin ido sannan a yanayi daya kamace ta ce, "to kaga na cece ka a baya, to kaima yanzu ya kamata indai kaji wannan murya kada ka ɓoye mana domin tana da muhimmanci a garemu." Armad shima baice komai ba sama da daƙiƙa sittin tamkar ma bazai ƙara magana ba, kafin can daga bisani ya ja dogon numfashi ya fara bayani da godiya, "na gode Gimbiya, lallai kin ceci raina a baya, kuma nima yanzu zan saka miki da alkhairi! "Ina mai tabbatar muku da cewa koda kun kwance bazan je ko'ina har sai wannan murya tayi magana! Wannan shi ne aƙƙawari na a gareki gimbiya!" Armad bai sani ba, amma tuni ya fara kallon wannan mace a matsayi na musamman!! Suna jin haka suka kalli juna, sannan bayan sun ja gefe, sun kuma gama yin ƙus-ƙus, sai suka dawo suka kwance Armad. Ba jimawa tuni har Armad ya fara jansu da hira, musamman ma gimbiya Nostalgiya, inda yake tambayarta tayi masa bayanin yadda akai ta same shi acikin wannan gari da kuma yadda ta ceto shi ta kaishi bakin wannan ruwa da kuma yadda har tasan takardarsa ta ƙone kuma ta canja masa wata. Sai dai kuma kash, duk tambayoyinsa babu wadda ta samu amsa. Domin kuwa ga dukkan alamu daga kan gimbiyar har samarin guda biyu basu da saurin sabo, ba kamar shi Armad ɗinba; wanda yake da saurin sabo da kuma son raha. Amma dai duk da haka daga ƙarshe saida yaji cewa dukkansu ƴan uwa ne, kuma babban sunan sa Hasanu Sísiyu Nára, ƙaramin kuma Kíru Sísiyu Nára, sai kuma ita gimbiyar wadda tace masa sunanta na asali Zahra Sísiyu, amma saboda wasu dalilai kowa yanzu Nostalgiya Nára Sísiyu yake kiranta. Duk da a lokacin Armad ya lura da cewa ƴan uwan nata biyu basu ji daɗin wannan sirri data gaya masa ba!! Amma kawai dai suka ɗauke, duk da daga baya saida babban ya gaya masa cewa wannan sunan nata kada ya gayawa kowa, domin ba'a faɗa yanzu! Armad baice komai ba kawai ya amsa da "eh!" Haka Armad yai ta ƙoƙarin jansu da hira amma bai samu nasara sosai ba, duk da kuwa kusan ya gama ɗebe labarinsa kaf ya gaya musu in banda sunan sa na gaskiya dabai faɗa ba; inda ya ce sunansa Armad Djinn! Suna cikin haka kwatsam sai ji sukai Armad yai shiru yana cikin magana! Lamarinda ya tabbatar musu da cewa wannan allo dake hannunsa ya fara maganar. Nan take suka tattaso daga inda suke, suka tsaya akansa. Inda a lokacin tuni hankalinsa ya fara gushewa, baima san inda kansa yake ba. Sai dai kuma ba kamar a cikin wancan gari ba, a wannan lokaci cikin abinda bai wuce daƙiƙa ɗari biyu ba ya farfaɗo! Inda bayan ya farka ya dawo hayyacinsa ya ɗaga kai ya kalle su, fuskarsa cike tsananin mamaki da firgici, saboda yaji abinda bai taɓa zato ba bai kuma taɓa tsammani ba. Amma kafin ya fara magana, bisa ƙarin mamakinsa kawai sai yaga duk su biyun sun juya sun kalli gimbiyar. Inda ita kuma ta kyaɗa musu. A dai-dai lokacin da Armad yaji kamar wani abu ya shiga cikin kansa ya karanta wannan murya da yaji sannan kuma ya fice. Duk su biyun suna ganin haka sukai wata dariya mai cike da murna da annushuwa da nuna cikar buri. Kafin daga bisani babban nasu ya dube su cikin murna tare da cewa, "ta wacce hanya kuke ganin yafi kamata mu kashe wannan yaro, mu ƙarasa aikinmu!!" Magana ce mai kama da tambaya, amma kana gani kasan ba amsar kowa yake nema ba, illa tasa. Domin kuwa kawai Armad yake kallo yana murmushi. A dai-dai wannan lokaci Armad ƙoƙari yake ya gane meke faruwa, saboda acikin ƴan daƙiƙun da suka wuce, lallai yaji gilmawar wani abu a kwakwalwarsa, amma yaƙi amincewa ya yadda da cewa kwakwalwarsa suka duba, sai dai kuma cewa lallai yasan cewa hakan ne ya faru daga abinda yaji babban nasu ya faɗa,

Chapter 5 of 33