Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙanƙarar izzarsa shekaru ɗari da sha bakwai ce. "Yaro kayi ganganci. Babu wanda ya isa ya kwana da rai bayan ya taɓa min Gashin-balbela." Kyaftin ɗin jirgin Gashin-balbela ya gayawa saurayin. Kafin ya juyo ga mutumin dake gefensa. "Kawo min kansa." Mutumin yai tsalle ya diro cikin Fataken-dare. Sannan ya zare takobi ya nufi saurayin da niyyar sare masa kai. A wannan lokaci ne Armad yai tsawa mai tsananin firgitarwa daga yake zaune. Abin mamaki Armad bai ɗaga muryarsa ba, amma babu wanda baiji tsawar ba har cikin ransa, musamman mutanen cikin Gashin-balbela. Nan take wannan sadauki daya tunkaro saurayin ya tsaya cak a inda yake, kafin gumi ya fara keto masa. A hankali ya ɗaga kansa cikin tsoro yai tsinkaye da ma'aboci wannan tsawa, lamarinda yasa ya fara karkarwa kamar wanda aka jefa tubalin ƙanƙanra acikinsa. Armad yakai ƙololuwar ɓacin rai, kuma tuni ya yanke shawarar nitsar da Gashin-balbela. Ya dubi wannan sadaukin dake ƙoƙarin kashe saurayin ya kirawo ɗaya daga cikin kalaman izzarsa, "Sanyin-babban-sihiri!" Nan take ƙanƙara ruwan toka ta haɗiye sadaukin. Armad ya nunashi da ɗanyatsansa, lamarinda yasa ƙanƙarar ta tamke shi tamau kamar zata fasa ƙasusuwansa. Kan kace meye wannan ya faɗi ƙasa sumamme. Armad ya dubi kyaftin ɗin Gashin-balbela ya ce, "idan kana so ka tsira da ranka, toka koma inda ka fito. Amma kayi sani cewa anan zaka bar wannan jirgin naka." **MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 92: Maikiro Inara Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Armad bai jira amsar ƴan-fashin dake cikin jirgin Gashin- balbela ba ya wuce izuwa wannan saurayi ya rusa akwatin ƙanƙarar daya rufe shi. Sannan ya juya izuwa jirgin dake gabansa. Kyaftin ɗin cikin jirgin, wanda ƴan daƙiƙu kaɗan da suka wuce shi ne ya bada umarnin a kashe wannan saurayi saboda ya taɓa masa jirgi, shi ne ya fara yin tsalle ya afka cikin ruwa. Kafin daga bisani sauran ƴan fashin su bishi. Lallai duk wanda ya rayu a wannan zamanin yasan menene sanyin-babban-sihiri, babu ko tantama akwai ratar izza mai yawan gaske tsakanin mutumin da yake iya sarrafa sanyin-babban-sihiri da wanda bai iya ba. Armad yai ajiyar zuciya sannan ya juya izuwa kyaftin Bisaiya, a lokacin ne ya gane cewa dukkan mutanen dake cikin jirgin kallonsa suke kamar wanda suka ga wani mala'ika. Kowa ƙoƙari yake yasan wane ne shi. Kasancewar Armad yana iya sarrafa sanyin-babban-sihiri hakan na nuna yakai aƙalla izza shekaru dubu ɗaya, wanda hakan ke nuna Armad ya futo daga ɗaya daga cikin manyan dauloli biyar na ƙasa bakwai. Domin kuwa bawai abu ne mai sauƙi ba ka samu wanda shekarun izzarsa suka kai dubu, saboda duk hanyoyin da ake iya samun izzar da takai dubu hanyoyi ne wanda zaiyi matuƙar wuya wanda baya cikin wannan dauloli ya samu. Koda isar Armad saiya tarar Bisaiya na kakarin mutuwa, inda yana ganinsa yayi masa manana jini na fita daga bakinsa. "K....kayimin abu ɗaya badan na... isa.. ba." Armad ya riƙe hannunsa cikin tausayi. Bai san mai Bisaiya zaice ba amma kawai ya kyaɗa kai. Bisaiya ya ɗaga ɗan-yatsansa da kyar yai nuni izuwa wannan jarumin saurayi ya ce, "Ka kularmin da ɗana." Armad najin haka ya zare ido cikin mamaki da al'ajabi. Tun farko dai bashi da masaniyar Bisaiya nada ɗa, sannan kuma shi kansa wahalhalun kansa sun masa yawa ballanta ace ya kula da wani. To amma a halinda Bisaiya ke ciki na gabda mutuwa babu yadda za'ai yace masa a'a. Daɗin daɗawa kafin Armad ya gama tunani yaji kakarin da Bisaiya ke yi ya ƙaru, kafin daga bisani ya faɗi matacce. Armad na ganin Bisaiya ya mutu ya canja shawara yai tsalle ya faɗa cikin ruwa yabi wannan ƴan fashi. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya dawo dasu a ɗaure cikin igiya. Wannan saurayi na zaune a gefen Bisaiya yana hawaye. Sauran ma'aikatan cikin jirgin duk kuka suke, kana gani kasan sunji daɗin aiki da Bisaiya. Duniya budurwa wawa, yanzu kake da rai in anjima babu. Waye zai taɓa tsammanin Bisaiya wanda ke da cikakkiyar lafiya ƴan daƙiƙu da suka wuce zai faɗi matacce yanzu. Su kuwa sauran fasinjoji wanda ke kwance a sume sun fara farkawa, abu na farko da suke iskewa shi ne gawar Bisaiya. Nan take Armad yasa aka rataya igiya a wuyan dukkan ƴan-fashin goma sha bakwai. Sannan ya dubi wannan saurayi ya fara bayani. "Wanda ya kashe wani shima kasheshi za'ayi. Idan kana so ga igiya." Armad ya miƙawa saurayin igiyar dake hannunsa wadda ana janta zata ƙarasa rataye ƴan-fashin. Babu wani kokwanto wannan saurayi ya miƙe ya nufi inda Armad yake ya karɓi igiyar dake hannunsa. Idanuwan wannan ƴan-fashi suka zazzaro cikin tsoro, sun san cewa rayuwarsu na gab da ƙarewa. Wasu daga cikinsu suka fara roƙon yafiya wasu kuma suna jiƙa wandonsu. Wannan saurayi ya ja igiyar ya rataye su. Da dama daga cikin fadinjojin kasa kallo sukai suka koma ciki. Amma Armad da saurayin da ma'aikatan cikin jirgin na tsaye suna kallon har ƴan-fashin suka gama harɗe- harɗensu suka mutu. Armad ya jefa gawarwakinsu cikin ruwa sannan ya bada umarnin ayiwa Bisaiya wanka. Bayan Armad ya tambayi ɗaya daga ma'aikatan jirgin akan al'adun ƙabilar da Bisaiya ya fito daga ciki ta fannin binne mamaci saiya fuskaci cewa ƙonawa suke sannan su jefa acikin ruwa. Armad ya tambayi saurayin idan akwai abinda yake buƙata ko kuma wani canji da yake so ayi wajen binne mahaifinsa, saurayin ya amsa da a'a. Sun samu dukiya mai yawa acikin jirgin Gashin-balbe wanda hakan ke nuna ba ƙananan ƴan fashi bane aciki. Daga ƙarshe suka zaɓi suci gaba da tafiya acikin jirginsu domin girmamawa ga Bisaiya. Kwanaki uku akai ana jimami acikin jirgin Fataken-dare kafin Armad ya samu damar tara kowa ya fara yi musu bayani cikin tattausar murya mai cike da kwarjini. "Marigayi kyaftin Bisaiya shi ne wanda ya ceto ni daga cikin ruwa yayimin maganin ciwuka na a lokacinda bai sanni ba. A lokacin rayuwarsa ya kasance jarumi ne mara tsoro, domin kuwa baiji tsoron komai ba a lokacinda yake ceto ni. Lallai bazan taɓa mantawa da abinda yayimin ba. Kowa da lokacinsa, lokacin ɗan-uwanmu Bisaiya yayi babu wanda zai iya hanawa. Amma nayi muku alƙawari zan kare wannan jirgi daga nan har zuwa sanda zamu isa daular Sisiya." Armad ya ɗanyi shiru na ɗan lokaci kafin ya wuce izuwa ɗakinsa yana tunani akan wasiyyar da Bisaiya ya bar masa taya kular masa da ɗansa. Tsahon kwanakin nan uku bai cewa ɗan komai ba, domin bai san mai zaice ba. Bai san mai ake buƙata daga gareshi ba. A rana ta shida saurayin ya gabato izuwa ɗakin Armad. "Suna na Maikiro Inàra." Saurayin ya ce, "Asalin mu ƴan daular Maikironomada ne amma dani da mahaifina mun zaɓi zama a daular Sisiya. Idan ka yadda zan bika na koyi al'amuran izza daga gareka na ɗan lokaci kafin mu rabu." Armad yaja dogon numfashi, sannan bayan ɗan tunani ya amince. Koyarda al'amuran abu ne mai tsada wanda sai anje manyan makarantu na manyan dauloli kafin a koya, amma idan kana da babban ma'aboci izza wanda zai koya maka ba saika je ba. Shi ma Armad kakansa shi ne ya koyar dashi. Koyawa wannan saurayi ba wani abu bane, kuma zaisa Armad ya biya bashin ceto shi da Bisaiya yayi. "Na amince zan koya maka al'amuran izza amma a halin yanzu ina kan hanyata ta zuwa daular Sisiya domin samawa mahaifiyata lafiya. Ban san yadda zata kaya ba, kuma abubuwa zasu iya rincaɓewa. Bazan iya gaya maka koni waye ba, amma ni mutun ne wanda keda kuɗi akansa. Bina zai zamo abu mai hatsari a gareka. Abu na ƙarshe idan zaka bini saidai ka haƙura da sana'arka ta tuƙa jirgi, domin kaga nidai ba'a ruwa nake yawo ba." Saurayin yai murmushin takaici tare da zubewa akan gwiwowinsa yana cewa, "Nasan haƙiƙanin kokai waye, Armad Wilbafos. Kuma a kowanne lokaci zan iya dawowa sana'ar tuƙa jirgi baƴan na gama koyon al'amuran izza. Koyon al'amuran izza shi ne abinda rayuwata ke buƙata a yanzu, babu wanda na zarga da mutuwar babana sai rashin ƙarfin izza ta. Indai zaka koyamin al'amuran izza zan bika ko'ina ne a duniya."MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 93: Samari Biyu Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Ragowar kwanakin da Armad yayi acikin wannan jirgi baiji daɗinsu ba sosai, domin kuwa kowa idan ya ganshi kaucewa yake tamkar yana tsoron kada ya ɓata masa. Tun yana damuwa harya daina, shi kuwa Maikiro Inára kullum a ƙofar ɗakin Armad ya dawo kwana, a cewarsa ɗalibi kullum yana tare da malaminsa. Babu yadda Armad baiyi ba amma Inára bai daina kwana anan ba. Hatta ma'aikatan jirgin duk abinda zasu yi sai sun nemi izini wajen Armad. A sati na huɗu suka iso daular Sisiya, ɗaya daga cikin manyan dauloli shida dake faɗin duniya a wannan zamani. Armad yayi farin ciki sosai da faruwar hakan domin koba komai ya ƙara kusantar matakin samawa mahaifiyarsa lafiya. Yana ji a ransa cewa wannan shi ne karo na ƙarshe da zai fita nemar mata lafiya domin kuwa a wannan lokaci zai samu abinda yake nema kuma bazai ƙara bari ta faɗa cikin rashin lafiya ba koda sama da ƙasa zata haɗe. Sannu a hankali jirgin Fataken-dare ya sauka a gaɓar doron-ƙasa na huɗu sashin arewa inda anan daular sisiya take. Gaɓar jirgin acike take da ƴan kasuwa da kuma iyalan fasinjojin da duka zo taryar su. Cikin ƙanƙanin lokaci fasinjoji kowa yai sallama da juna sannan suka godewa Armad kafin kowa ya kama gabansa. Tuni daman Inára ya sallami dukkan ma'aikatan jirgin ya biya su haƙƙinsu, saboda baya sa ran ƙara tafiya a kowanne lokaci kusa. Koda kowa ya ɓace aka bar Armad da Inára sai Inara ya nemi iznin zuwa ya bada ajiyar jirgin Fataken-dare har zuwa lokacinda zai dawo kan ciniki. Armad ya amince kuma ya bayyana masa wajenda zasu haɗu bayan ya gama. A lokacinda suka iso gaɓar rana na tsakiyar sama amma kafin Inara ya hattama komai sai da rana ta faɗi. A lokacin ya iske Armad a ɗaya daga cikin gidajen-kwana na wannan gaɓa. Armad na zaune yana tattara bayanai akan wannan daula ta sisiya. Dama abinda yazo yi kenan. Inara na bayyana Armad ya tashi suka kama hanya. Armad ya dubi Inara ya ce, "Da fatan ka gama komai?" Inara ya gyaɗa kai. "Eh, na gama ya shugaba na. Na samu wanda zai ajiye min jirgin Fataken-dare har zuwa sanda zan dawo." "To yayi kyau." Armad ya ce, "daga binciken da nayi na gano cewa wannan daula nada adadin mutane miliyan ɗari biyar zuwa ɗar shida. Wannan mutane sun rarrabu a tsakanin garuruwa ashirin da tara da babban birni guda ɗaya wanda ake kira da Jékis. "Kowanne ɗaya daga cikin wannan garuruwa ashirin da tara nada sarki amma dukkan wannan sarakai suna ƙarƙashin babban sarkin dake mulki a babban birnin tarayya na Jékis. Wanda ba wani bane illa Bihanzin mai dauwamammen sara. Daga nan zuwa can tafiyar wata da watanni ce, amma ina da sihirtaccen doki mai suna Ubbaru wanda zai taƙaice mana wannan tafiya." Armad na zuwa nan a zancensa ya hanhanga ya tabbatar babu wanda ke kallo sannan ya sha kwanar wani layi mai duhu ya buɗe ƙofar zobensa ya ɗakko Ubbaru. Inara na cikin mamakin wannan zobe na Armad yaji muryar Armad na masa bayani. "Saboda tsananin gudun wannan doki jama'a basa ganinsa a yayinda yake tafiya. Ina ganin ba matsala muyi amfani dashi mu isa babban birnin." Armad da Inára suka hau dokin sannan suka ɗau hanya. Da tsakar dare suka isa babban birnin Jekis, wanda hakan ke nuna Ubbaru ya taƙaice tafiyar wata da watanni acikin awanni. Babban abinda ya bawa Inara mamaki shi ne yadda shi yake iya ganin mutane da garuruwan da suke wucewa amma mutane basa ganinsu. Kuma duk wannan azabar gudu iska bata damunsu. Lallai Ubbaru doki ne mai yawan sihiri. Inara ya dubi Armad ya ce, "A yanzu sun rufe ƙofa sai dai mu jira zuwa asuba." Armad ya amince suka sami gindin wata bishiya suka fake har zuwa safiya. Abin mamaki har yanzu ƴaƴan itacen da Nostaljiya ta bar masa suna nan basu lalace ba, saboda haka Armad ya fito dasu suka ci sukai hani'an. Da safe suka nufi ƙofar wannan babban-birni mai suna Jekis. Duk da sammakonsu saida suka tararda layin mutane a bakin ƙofar wanda a tafe suka kwana. Wani tafkeken bango ne iya ganinka ya kewaye garin. Duk wanda zai wuce saiya nuna shedar ɗan-ƙasa ta sisiya da kuma harajin ayrid hamsin ko ɗari idan baka da sheda. A wannan lokaci Armad ya tuno bashi da ko sisi duk da akwai naira miliyan ɗaya da rabi a kansa. Koda Inara ya fuskanci halinda Armad ke ciki saiya fito da ayrid ɗari da hamsin ya riƙe a hannunsa. Kallonsa kawai Armad yayi tare da yin murmushin godiya. Sannu a hankali layi ya fara raguwa, saura mutun sha uku a gabansu. A wannan lokaci ne Armad ya hango wasu samari guda biyu a gabansa. Tsakaninsa dasu mutun goma ne kawai. Ɗaya daga ciki yana da ƙiba, ɗaya kuma siriri ne kuma yana ɗauke da takobi. Dukkansu sun saka hirami sun nannaɗe fuskarsu amma Armad yana ji lallai ya sansu amma babu dama ya sauka daga layi ya isa gare su. Saboda haka saiya rufe ido ya gane yanayin-izzarsu. Bayan wannan samari sun wuce layi ya iso kan su Armad. Masu gadi ashirin ne a bakin ƙofar. Rabi riƙe da makamai rabi kuma suna ƙirga kuɗi. Dukkansu sanye da kaya yalaye masu ratsin baƙi a hannunsu. Inara ya miƙa kuɗin dake hannunsa tare da katinsa na ɗan ƙasa yana cewa, "ga nawa ayrid hamsin, gana malami na ayrid ɗari domin bashi da shedar ɗan ƙasa." Mai gadin yayi wa Armad wani kallo mai tsayi kamar wanda ke kallon mai laifin kisa. Sannan daga bisani ya ce, "daga wacce daula kake?" Armad ya amsa da cewa, "daular Hán ta doron ƙasa na uku." Mai gadin ya ƙara matsawa kusa kamar wanda ke kokwanton kamannin Armad. A jikinsa yana ji cewa lallai Armad mai laifi ne. Nan take ya buɗe wani ƙaton littafi a gefensa mai ɗauke da hotunan mutane masu laifi wanda aka sa kuɗi akansu. Duk da Armad yasan kamanninsa a canje suke sai da zuciyarsa ta buga da yaga mutumin ya buɗo shafin da hotonsa ke ciki. Mai gadin ya tsaya tare da ƙara tambayar Armad, "Yama kace sunanka?" Armad ya amsa da cewa, "Han Djinn." Mai gadin yaja dogon numfashi tare da buɗe baki zai ƙara wata maganar amma sai Inara ya zira hannu a aljihu ya miƙa masa ƙarin Ayrid ɗari. Lamarinda yasa yai murmushi tare da buɗe musu ƙofa. Cikin sauri Armad yabi bayan wannan samari biyu daya hanga a gabansa. Suna shiga kuwa manyan gine-ginen birnin sukai musa sallama. Amma duk da haka ya iya jiyo yanayin-izzar wannan samari guda biyu a ɗan gaba da inda suke. Nan take ya umarci Inára daya jirashi anan, sannan yayi amfani sabuwar fasaharsa ta Kaban'shisu ya ɓace daga inda yake ya bayyana a bayan wannan samari biyu. Yana bayyana ya kalli samarin sama da ƙasa. Nan take sai farin ciki ya cika zuciyar sa. Cikin dariya da annushuwa ya kira sunansu. "Iliyasis... Cokali... Ina Nusi?" Iliƴasis ya juyo cikin zafin nama ya ɗora takobinsa a wuyan Armad yana cewa, "Waye kai? Kuma a ina ka sanmu? Idan baka bani amsa ba yanzu zan tsinke maka kai." ** Yi comment da cikakken sunan jarumi/jaruma acikin wannan littafiMAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 94: Tsumin Izza Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** Wata biyu kafin fitar Armad daga kurkuku. ** A can daular Infiriya, babban birnin Rafiya inda sarki Rafiyan Kaltume ke mulki, Cokali da Iliyasis ne suka shigo domin neman bayanin ƴar'uwarsu Nusi a wajen yarima Niyashi. Tafiya suke cikin yadda dakai da rashin tsoro suna tunkarar babbar fadar ƙasar inda sarki Rafiyan Kaltume ke mulki. Idan mai karatu bai manta ba yarima Niyashi shi ne wanda baya tsufa. Kuma shi ne wanda ya taimaki Nusi dasu Cokali tun suna ƴan shekara shida. Saboda haka ba abin mamaki bane da Iliyasis da Cokali suka yanke shawarar su fara neman Nusi daga wajensa. Koda bai san inda take ba zai iya taimaka musu da kwatance. Iliyasis ya tsayar da wani saurayi mai jan gashi dogo ya tambaye shi, "da ALLAH mu baƙin yarima Niyashi ne. Ko kasan inda zamu iya samunsa?" Koda jin tambayar sai saurayin ya haɗe rai cikin fushi ya ce, "yarima Niyashi? Amma banda ku baƙi ne saina sare muku kai. Faɗar sunan yarima mai jiran gado gatsal babban laifi ne idan baku sani ba." Iliyasis najin haka yai murmushi tare da sanyaya murya yana cewa, "afuwa. kamar yadda ka faɗa mu baƙi ne. Amma maiya kamata mu ce masa?" Saurayin yai shiru yana hucewa kafin daga bisani ya amsa da cewa, "shi dai wanda kuke nema shi ne alfaharin mutanen wannan daula. Kuma muna girmama shi da sunan 'Nazára' wanda hakan ke nufin mai ceto. Sannan kuma kamar yadda ake yiwa ƴaƴan babbar masarautar wannan daular shima ana saka masa kalmar 'Rafiyan' a farkon sunansa. Saboda haka daga yau ku riƙe sunansa 'Rafiyan Nazára' ɗan sarki Rafiyan Kaltume." Koda saurayin yazo nan a zancensa sai yai shiru yana kallon su Iliyasis domin ya tabbarar sun fahimce shi kafin daga bisani ya ci gaba da cewa, "Idan kuka miƙe wannan hanya tsahon tafiyar wuni ɗaya zaku tarar da ɗakin bauta na sarki Rafiya wanda ke daura da fada. Anan zaku tadda shi yana karɓar Tsumin-Izza." Saurayin na gama magana yayi nasa waje ba tare da sanin ko sun fahimce shi ba. Cokali yana niyyar finciko shi Iliƴasis ya ɗaga hannu. Haka suka ji gaba da tafiya suna tambayar sunan Rafiyan Nazára har saida rana ta faɗi. A lokacin da suka iso wani ƙaton shinge kewaye da sadaukai ma'aibota izza aƙalla dubu. Dukkaninsu sun durƙusa ƙasa sanye da fararen kaya tamkar suna bauta. A can tsakiyarsu wani saurayi ne zaune yake kallon sama. Abin mamaki ƙanƙarar Sanyin- babban-sihiri ce ke zuba a dai-dai kewayen wannan saurayi. Ba jimawa Iliƴasis ya gane saurayin ba wani bane illa Yarima Niyashi. Duk yadda akai wani babban sihirn ake haɗawa. Cikin zafin nama suka je suka samo fararen kaya tare da matsawa kusa da ɗaya daga cikin sadaukan dake wajen domin samo bayanai. Sunan abinda ke faruwa dai Tsumin-izza, kuma yawanci ana yiwa duk wani yarima mai jiran gado na kowacce daula domin su sami izza maɗaukakiya. Mutun zai zauna ya karɓi shekarun izza daga asusun izza na daularsu. Wato shekarun izza da kowacce daula ke tarawa ta hanyar fasahar kwangila. Ƙa'idar shi ne duk kwana ɗaya mutun zai karɓi shekarun izza dubu ɗaya, kuma mutun zai ci gaba da karɓa har zuwa sanda ƙarfinsa zai ƙare. Sai dai a ƙa'idar ba ci ba sha har a gama. A wannan rana kwanan Yarima Niyashi bakwai yana zaune yana karɓar wannan tsumi daga asusun izza na daularsa. A kwana a tashi saida yarima Niyashi ya kwashe kwanaki tara acikin wannan yanayi. Lamarinda ya bashi izza shekara ɗai-ɗai har dubu tara. Hatta manƴan sadaukai uku da ake ji dasu a dukkan faɗin daular izzarsu bata wuce shekaru dubu shida ba. Amma ga yarima Niyashi wanda dama yana da sirrin rashin tsufa a jininsa ya samu shekaru dubu tara. Lallai a wannan rana an ƙara haifar wani babban ma'aboci izzar wanda ya kamata a saka sunansa acikin manyan gobe. Saida akai ƙasaitaccen biki tare da gayyato kowanne sarki daga cikin sarakuna talatin da ɗaya dake daular Infiriya domin a taya yarima Niyashi da sarki Rafiyan Kaltume murna. Bayan komai ya lafa Iliyasis da Cokali suka samu damar ganin Niyashi. Labarin ɓatan Nusi bai masa daɗi ba kwata-kwata amma daga ƙarshe shawarar daya basu kawai shi ne su nemi Armad. Duk inda take zai sani. Sunyi mamakin yadda Niyashi ya riƙe sunan Armad to amma bawai sakawa Armad kuɗi da akai bane kaɗai yasa kowa ya sanshi ba. Babban abin shi ne yadda gimbiya Nostaljiya wadda ake ganin tafi duk wata yarinya kyau a duniya take kareshi a gaban kotu. Zuwa wannan lokaci kowa ya san cewa Nostaljiya ita ce ta ceci Armad a wajen cinikin bayi daya gabata, amma saboda matsayin baban ta a idon duniya ake so a rufe a ɗorawa Armad laifi. Abin mamakin shi ne har yanzu Nostaljiya taƙi bada shedar Armad shi ne mai laifi. Niyashi ya dubi su Iliyasis ya ce, "sarki Bihanzin baya son yaƙi ya ɓarke tsakaninsa da sauran sarakunan Jinzidal saboda haka yau kwana uku kenan ya bada auren Nostaljiya ga yarima mai jiran gado na daular Denizawa wato Deniz Bizáya. Nan bada jimawa ba za'a saka ranar bikin. Ina tunanin duk inda Armad yake zai bayyana a daular Sisiya kafin wannan biki. Indai kuna so ku gamu dashi can zaku tafi." Koda jin haka sai Iliyasis ya kalli Cokali cikin jimami. Indai har da gaske ne maganar auren Nostaljiya da Deniz Bizaya lallai akwai yiwuwar Armad yaje daular Sisiya. To amma akwai matsaloli da dama da zasu iya afkuwa. Bayan sun ƙara ƴan kwanaki a daular Infiriya ƙarƙashin kulawar yarima Niyashi sai sukai azama suka nufi daular Sisiya. A lokocin da suka fito labarin auren bai baza duniya ba domin kuwa suma a bakin Niyashi suka ji, amma kafin su isa babban birnin Sisiya wato Jekis labari ya baza ko'ina. Kowa yasan gimbiya Zahra wadda akafi sani da Nostaljiya Nára zata auri yarima mai jiran gado na daular Denizawa wato Deniz Bizáya. A wani mataki na hana afkuwar yaƙin da zaiyi asarar miliyoyin rayuka. To ta haka Iliyasis da Cokali suka iso daular Sisiya, kuma gashi ƙaddara tasa suna shigowa sun haɗu da Armad kafin su isa cikin gari. **MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 95: Hankakan Mutuwa Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ** ** Tun kafin Iliyasis ya janye takobinsa Cokali yai tsalle ya rungume Armad cikin murna. Saida Armad yai da gaske sannan ya kwaci kansa. Cokali ne ya fara magana. "Armad! Ashe da gaske nan zaka taho. Amma mai yasa kake tambayarmu ina Nusi bayan tare muka barku? Kar dai kace kaima bakwa tare." Nan take wannan tambayoyi suka jefa Armad cikin tunani. Ga dukkan alamu bama saiya tambaya ba, suma su Cokali basu san inda Nusi take ba. To amma abin mamakin shi ne yadda su Cokali suka san zaizo daular Sisiya. Armad ya dube su ya ce, "kuma nemanta kuke yi kenan? Rabo na da ita tun shekarar data wuce a gasar cinikin bayi ta Jinzidal. Amma yaya akai kuka san zanzo nan?" Nan take jikinsu Iliyasis yai sanyi. Suna tunanin samun Nusi a wajen Armad amma shima bai san inda take ba. Kuma yanzu dole sai sun bayyanawa Armad tsakaninsu da yarima Niyashi da kuma yadda akai suka gano zaizo wannan gari. Iliyasis ya dubi Armad ya ce, "Mu ƙarasa mu samu mafaka kafin muyi magana." Armad ya kyaɗa kai sannan dashi da Maikiro Inara suka bi bayan su Cokali izuwa cikin gari. Suna tafe suna kalle-kallen wannan ƙasaitaccen birni na Jekis wanda ke ɗauke da manya-manyan gine-gine masu samfuri kala-kala. Amma Cokali baiyi shiru ba, saida ya taɓo labarin faɗan Armad da yarima Niyashi da kuma yadda Armad yai nasara, domin labarin tuni ya baza ko'ina. Armad dai baice komai ba murmushi kawai yake. Ba jimawa suka iso harabar wani ƙaton gidan-kwana a farfajiyar wata kasuwa. Har yanzu dai Armad bashi da ko sisi saboda haka Inara ne ya biya masa kuɗin ɗaki kafin daga bisani duk su huɗun su hallara a ɗaki ɗaya domin tattauna matsalolinsu. Iliyasis yayiwa Armad inkiya daya tura Inara waje dan su tattauna cikin sirri amma nan take Inara ya buɗe baki ya dubi Iliyasis ya ce, "indai daga daular Maikironomada kuke kunsan ɗalibi baya barin gefen malaminsa a kowanne lokaci har sai sanda malamin ya yaye shi. Saboda haka ina cikin wannan ɗaki, amma nayi muku alƙawarin duk abinda zaku faɗa baza ajishi a bakina ba koda bayan raina." Cokali ya kalli Iliyasis tsahon ƴan daƙiƙu kafin su kyaɗa kai alamun amincewa. Iliyasis ne ya kwashe dukkan tarihin dake tsakaninsu da yarima Niyashi ya gayawa Armad sannan kuma ya gaya masa yadda suka san zaizo wannan gari da kuma labarin auren Nostaljiya. Armad yai shiru yana tunani tsahon lokaci. Dukkan abubuwan dake afkuwa harda yaƙin dake neman ɓarkewa tsakanin sarakunan Jinzidal ta dalilinsa ne. Amma babban abinda yafi damunsa shi ne zancen wannan aure da kuma ɓatan ƴar uwarsa Nusi. Wani irin ɓacin rai mai zafi wanda Armad bai taɓa jin irinsa ba ya taso masa a ƙirji a lokacin daya hango Nostaljiya a ɗakin yarima Deniz Bizaya. Tun bayan sanda Nostaljiya ta bayyana masa tana sonsa Armad bai taɓa tsayawa yayi wani dogon tunani akan maganar ba, kuma ko a jikinsa. Amma a halin yanzu da yaji zatai aure hankalinsa yayi mummunan tashi. Da farko yayi tunanin saboda baya so ayi mata auren dole ne amma ba jimawa ya gano cewa lallai shima akwai ƙaunar Nostaljiya acikin ransa. Cokali ya dubi Armad cikin al'ajabi ya ce, "idanun ka sunyi ja ja wur. Da gaske kana son ta." Armad yai shiru baice komai ba. Iliyasis ya dubi Armad ya ce, "Idan zaka bi shawara ta ka haƙura. Wannan auren shi kaɗai ne zai kare afkuwar yaƙi da asarar miliyoyin rayuka. Idan ka hana wannan aure lallai yaƙi saiya afku. Ina ganin kawai kazo mu juya ba tare da kun haɗu da ita ba." Armad ya ja dogon numfashi sannan ya ce, "idan da ɗaurin auren ne ya kawo ni da nabi shawararka, amma nemawa mahaifiyata lafiya ne ya kawo ni wannan daula. Kuma lallai sai naga Nostaljiya na nemi taimakon ta. Zarar mahaifiyata ta samu lafiya sai mu tafi." A wannan lokaci Armad ya kwashe duk abinda ya faru dashi bayan rabuwarsa dasu Iliƴasis ya gaya musu. Sannan ya nemi iznin su jirashi ya je yaga Nostaljiya kafin ya fito su bazama neman Nusi tare. Daga ƙarshe Armad ya dubi Inara ya ce, "kaima ka jirani anan naje na dawo." Nan take Inara ya sunkui da kai cikin alhini yana cewa, "ya shugabana kayi haƙuri amma lallai bazan iya barin gefenka ba har izuwa lokacin da zaka sallame ni a matsayin ɗalibi." Dama Armad yayi tunanin Inara zaice haka saboda haka kawai murmushi ya kyaɗa kai. Da safe bayan sun karya Armad da Inara suka nufi hanyar fadar birnin Jekis da niyyar ganin gimbiya Nostaljiya Nára. Ba jimawa suka tsinci kansu a wata siririyar hanya da zata kaisu izuwa fadar. Armad ya dubi Inara ya ce, "ka farkar da fasaharka?" Inara ya girgiza kai. "A'a." Armad yai murmushi tare da cewa, "nayi tunanin haka tunda daman baka da yawan shekarun izza. Amma ba matsala ba ce. Kamar yadda ka sani zaka iya kwarewa akan harkar fasahar aljanu, ko kuma akan takobi ko kuma akan ɗalasimai. Naga kana iya amfani da takobi da kuma fasahar aljanin wuta. Kai sani cewa wannan bazai isa ba. Indai kana so ka kware akan harkar izza saika haɗa da ɗalasimai sannan kuma daga baya bayan ka farkar da fasaharka sai ka zaɓi hanya guda ɗaya. Ina da malami mai suna Babara wanda ya kware akan harkar ɗalasimai. Zarar muka gamu dashi zansa ya farkar da

Chapter 31 of 33