Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Nusi ta kammala zancenta tare da miƙa hannu taja jan kyallen dake goshin Armad cikin tsokana, tana cewa, "wai kai tunda ba Miyurar ka cire wannan abun mana." "Hmmmm.." Armad yaja numfashi yana tunano mai zaice ya tsokani Nusi shima, "indai zaki iya cire ɗankwalinki to nima zan cire. Kin yarda?" "Me kace?" Nusi ta cije haƙora, kasancewar a ƙabilar su Nusi kowacce mace data haura shekaru sha takwas tana saka ɗan mayafi taɗan rufe gashinta. Kuma sukan ɗauki abun abun tsokana idan bakya yawo da wannan mayafi da ake kira da ɗankwali. "Zaka iya ƙara wani kyallen ma.... Ni ina ruwana..." Nusi ta haɗe rai tana hararar Armad. Lallai acikin wannan harara akwai abota wadda take ginuwa a hankali a hankali. Ko ina wannan abota zata kaimu, lokaci ne kaɗai zai gaya mana. Awa shida nayi aka buga ƙugen yaƙi..... Mazaje guda biyu da suka fito zagayen ƙarshe na wannan fafatawar suka bayyana a fagen daga. Sune waɗanda sukai nasara akan sama da mutun ɗari bakwai da suka fafata a wannan gasa. Kuma yanzu gashi sun haɗu da juna, lallai akwai karan-batta irin wanda ba'a ga irinta ba a baya. Waye zaiyi nasara? Waye zai je ƙas? Waye zai nunawa duniya ya isa? Waye zai mallaki dubunnan bayin da aka tara? ____ Armad na tsaye a gefe guda da takobinsa a rataye a kafaɗarsa, yana karantar Ikenga wanda ke gabansa a tsaye, idanunsa a rufe. Kuma abin mamakin shi ne anfi minti uku da kaɗa musu ƙugen yaƙi, amma babu wanda ya motsa acikinsu. Can daga bisani Ikenga ya buɗe ido ya kalli Armad, inda dubansa ya kafe akan jan kyallen dake ɗaure a goshin Armad, nan take kaifafan idanununsa, wanda ga dukkan alamu zasu iya gani har hanji, suka ƙurawa wajen ido cikin mamaki, kafin daga bisani ya buɗe baki ya fara magana cikin tsananin girman kai da taƙama da ƙarfin Izza, "a wannan rayuwar na tsani mutane da dama! "Amma daga cikin waɗanda nafi tsana akwai matsorata masu jin tsoron bayyana kosu su waye!! "Da farko nayi niyyar mutunta jarumtarka ta zuwa zagayen ƙarshe, na nuna maka fasaha ta mai suna 'Takun-Sarki', wanda hakan nema yasa tunda nayi takun farko ban matsa daga nan ba, da niyyar zan ɗauki taku na biyu na halaka ka dashi. Domin kaga idan ka mutu ta wannan hanyar zakai alfahari a lahira, saboda kana daga cikin kaɗan da suka mutu daga maɗaukakiyar fasahar 'Takun-sarki'. "Amma ina, ka ɓata min lokaci kawai! Lallai duk wanda ke tsoron bayyana cewa shi Magajin-wilbafos ne to bai cancanci Takun-sarki ba. Ko kana tunani dan babu Miyura a goshinka idanu na zasu kasa gane ka. Lallai inaga baka da masaniyar cewa wannan idanu nawa su na ganin hatta safa-da-marwar mutuwa a lokacin da take ɗaukar rayukan bil-adama." Yana gama faɗar haka bai jira komai ba, ya nufi kan Armad da takobinsa a hannun dama tsirara. Jikinsa na sassarfa irin ta mazajen aljanu. Yana isa ga Armad ya kai masa wawan sara da niyyar tsinke kansa, amma a wannan lokaci Armad ya farfaɗo daga cikin mamakin da yake na yadda akai Ikengan ya gano shi ne Magajin Wilbafos, ya kuma kare wannan sara da tasa takobin. Takubban biyu na haɗuwa Ikenga yayi amfani da tsananin kwarewa ta fasahar takobi ya zame takobinsa daga jikin ta Armad, ya kuma kai masa wani saran da ita ta ƙasan hannunsa. Cikin tsananin zafin nama Armad yayi amfani da walƙiya mai ɗauke da ƙarfin shekara ɗaya ya ƙarawa kansa ƙarfi domin zamewa wannan sara. Yai tsalle izuwa gefe guda tare da mayarwa da Ikenga martanin sara mai ɗauke da shekarun Izza biyar. Lamarinda yasa dole Ikenga yayi amfani da Izzarsa sannan ya iya kaucewa ta hanyar yin tsalle ya koma baya. Armad ya bishi da kallo riƙe da takobinsa, inda shima ya kalleshi yana mai yamutse fuska. Lallai ɗan wannan bata kashi na ƴan daƙiƙu daya wakana tsakanin wannan ma'abota Izza biyu ya girgiza ƴan kallo domin kuwa babu abinda kake ji sai shewa da ife-ife. "Hmmmm...." Armad yaja numfashi cikin yarda dakai yana mai cewa, "shin kana ganin dan ka fita daga cikin Mairakana da Bizaya ya saka ka aciki shi ne ka isa. To ya kamata ka canja tunani, domin lallai sai nayi nasara a wannan fafatawa. Kuma wani abu guda ɗaya da baka sani ba, koda kasan ni ne Magajin Wilbafos ko baka sani ba, ko kana ganin mutuwa ko baka gani duk bai shafe ni ba. Domin lallai koda zan mutu saina fito daga kabari na nemo Tarifil-fakta nan da wata shida. Kai koda dukkaninku zaku haɗu na farkon ku dana ƙarshenku, baza ku iya hana ni nemar mata lafiya ba." "Hmm.." Ikenga yayi murmushi tare da tafa hannayensa biyu ya kuma kira sunan ɗalasimi acikin ransa, sannan ya ci gaba da cewa, "Da takobi kaɗai, ba tare da aljani ba, ba kuma tare da fasahar Takun-sarki ba zan halaka ka. A matsayinka na zuri'ar Wilbafos koba komai ka cancanci na nunawa duniya ƙarfin Izza ta akanka. Kayi sani cewa a irin wannan rana ta yau Wilbafos-na-uku ya rasu. Kuma kaima yau ita ce ranar da zaka isa magabatanka a lahira." Armad ya haɗe gira cikin mamaki domin bai taɓa jin wani Wilbafos-na-uku ba. Kuma ga dukkan alamu Ikenga ba ƙarya yake ba, sai dai kuma yasan koya tambaye shi bazai gaya masa wani abu ba. Saboda haka kawai ya share zancen, kawai abinda ke ransa shi ne ya zaici nasara akan Ikenga. "Bari muga har tsahon daƙiƙa nawa zaka iya zama akan zancenka naƙin yin amfani da aljaninka." Armad na faɗar haka ya zuƙo shekaru biyar na Izza a matsayin ƙawanyar walƙiya biyar, ya kuma aikawa da Ikenga su. Ikenga ya kaɗa takobinsa a sama, sannan yayi tsalle tare da kaiwa ɗaya daga cikin wannan walƙiya sara. Nan take takobin tasa ta ratsa cikin walƙiyar, kafin daga bisani ta tarwatsa ta ta ɓace acikin iska. Lamarinda ya jawo shewa mai ƙarfin gaske acikin ƴan kallo. Kowa yasan cewa ba ƙaramin ƙarfin fasahar takobi ake buƙata ba kafin mutun ya iya tarwatsa harin aljani da takobinsa, amma ga Ikenga akan iska ya tarwatsa ɗaya cikin kwanciyar hankali. Tun ma kafin shewar ƴan kallo ta mutu Ikenga ya ƙara ratsa walƙiya ta gaba, sannan ta gabanta. A haka a haka har saida ya gama da guda biyar ɗinnan hankalinsa a kwance. Sannan ya dira ƙasa yana kallon Armad. Nan Armad take Armad ya duba yaga yana da kimanin ragowar shekarun Izza arba'in, sabida haka nan take yasan maiya kamata yayi. Armad ya zuƙo shekaru goma nan take, sannna ya haɗa ƙatotuwar ƙawanyar walƙiya da ita. Ya ɗora ta a saman hannunsa na dama sannan yai ƙaraji ya afkawa Ikenga. Yana zuwa yakai masa duka da ita, inda shi kuma yasa takobinsa ya kare. Sai dai kuma shima Ikenga yasan babu yadda za'ai ya iya kare shekaru goma na Izza a haɗe, da takobi kawai. Koda kuwa ya iya karewa, zata iya fancala ta gefe ta ƙona shi. Saboda haka nan take ya ɗaga hannunsa sama ya kira ɗalasimi, inda wata takobin ta ƙara bayyana akan ɗayan hannunsa. Nan take ya kawo wa Armad sara da ita. Dama Armad yayi tunanin haka zata iya faruwa, saboda haka ya shirya mata. Takobin na fitowa wata ƙawanyar wuta mai ɗauke da shekaru sha biyar na Izza ta bayyana ta tare ta. Sannan kuma a lokaci guda wata ƙawanyar mai ɗauke da wasu shekaru sha biyar ɗin ta ƙara bayyana ta yiyo kan Ikenga ta baya. Da farko Ikenga ya kasa riƙe ƙawanya mai ɗauke da shekaru goma, a dalilin hakan ya kira wata takobin, amma kuma Armad ya shiryawa hakan, inda shima ya ƙara aika masa wata ƙawanyar mai shekaru sha biyar har guda biyu; ɗaya ta gaba ɗaya ta baya. Lallai Armad ya kware a harkar sarrafa aljaninsa yadda yake so. Kuma ga dukkan alamu kullun ƙara kwarewa yake. ___ Shin taya Ikenga zai iya kaucewa halaka daga girman Izzar dake tunkararsa ta gaba ta baya? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 44: Aljani Gal-Iyyu Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos "Hmmm...." Ikenga ya ja dogon numfashi tare da girgiza kai, "eh lallai ka cancanci kaga aljani na, na janye abinda na faɗa a baya. Amma kayi sani cewa duk abinda ya faru dakai, kada ka zargi kowa ka zargi kanka." Yana rufe baki ya tafa hannayensa biyu tare da faɗar wasu ɗalasimai ƙasa-ƙasa, kana daga bisani ya kira sunan aljaninsa, "Gal-iyyu!" Faɗar hakan keda wuya wannan filin wasa ya fara girgiza yana neman rugurgujewa. Waɗannan manya-manyan ƙawanyu na walƙiya ɗauke da shekarun Izza dake tunkaro shi suka fara girgiza kafin daga bisani su tsaya cak tamkar ansa wani bango an tare su. Sai dai idan ka lura zaka ga cewa bawai haka kurum waɗannan ƙawanyu suka tsaya ba. Wani baƙin abu ne mai kama da hadari yayi musu hijabi tsakaninsu da Ikenga. A zagaye da wannan baƙin abu akwai wani jan layi daya kewaye dukkaninsa. A tsaye wannan baƙin abun da kaɗan ya haura Ikenga, amma a kwance yana da faɗin daya kewaye shi ya kuma kare shi daga sharrin wannan walƙiya dake neman halaka shi. Wata irin Izza mai saka firgici na tashi daga jikin wannan abu. Kallo ɗaya kacal zakai ka tabbatar da cewa akwai ƙarfin maɗaukakin aljani a jikin wannan abu mai kama da hadari. Kai idan ma ka nutsu ka ƙara matsawa kusa zaka iya jin ƙarfin Izzar baƙin Rauhanin aljani na tashi daga ciki. Babu abinda kake ji sai ajiyar zuciya da ƙara kwale ido daga ƴan kallo, domin ga dukkan alamu har yanzu babu wanda ya gano haƙiƙanin me wannan aljani na Ikenga mai Gal-iyyu yake sarrafawa. Wasu ƴan kallo daga ɓangaren kusurwar arewa suka fara bada hasashe kan mai suke tunani akan wannan aljani. Ɗaya daga cikinsu ya ce, "ina ganin aljanin duhu ne, ko?" Ɗayan kuma ya girgiza kai, "a'a, ni ina ganin aljanin hadari ne." "A'a anya kuwa, ka taɓa ganin hadari da yakai baƙin wannan? Lallai ni inaga ba hadari bane.. Ko kuma wataƙila ma aljanin ƙasa ne ko kuma na......" Sai dai kafin ya rufe bakinsa ya haɗiye ragowar maganarsa domin abinda ya gani na faruwa a wannan filin daga. "Kaiiiiii.... Ai kuwa aljanin hadari!!!" Yai ajiyar zuciya tare da kallon abokin hasashen nasa. "Duba kaga yadda yake zuƙe walƙiyar dake kewaye da dashi. Aljanin hadari shi kaɗai ke iya zuƙe walƙiya a iya sani na." Ai kuwa abinda ke faruwa kenan. A kewaye da Ikenga wannan abu ya fara rage shekarun dake ɗauke acikin wannan ƙawanyu na walƙiya. A gaban idon kowa na suka fara rage yawa tamkar wasa. Nan take Armad yai tsalle izuwa baya tare da haɗe fuska, acikin ransa yasan lallai akwai matsala. Domin shima kamar sauran ƴan kallon ya gano cewa wannan aljani na hadari ne. Domin yana da cikakkiyar masaniyar shi kaɗai ne zai iya zuƙe walƙiyar sa haka. Ikenga ya ɗaga hannunsa na dama yana nuni da Armad, "Kayi sani cewa tun daga lokacin da aka hallicemu aka rubuta nayi nasara akan ka. Kai koda ma ba haka aka rubuta ba, lallai yanzu al'amari zai canja. Koba komai zaka yi alfahari idan kaje lahira kana daga cikin waɗanda suka mutu ta hannuna. Domin lallai abin alfahari ne a gareka, ace ka mutu a hannun sarkin ƙabilar Bayajidda." Armad ya ja numfashi gami da murmushi, "kayi dai ka gama surutun ka. Ni dai nasan lallai bazan bari naje ƙas ba a wannan fafatawa. Ko da aljani ko babu!" Ikenga najin wannan magana ya ƙara tafa hannayensa, lamarinda yasa wannan baƙin hadari ya ƙarasa zuƙe dukkanin walƙiyar dake kewaye dashi. Sannan nan take ya aikawa da Armad wannan hadari da niyyar ya halaka shi dashi. Armad yai tsalle ya kaucewa hadarin ta hanyar yin gefe. Amma tunma kafin yaje ƙas wannan dunƙulen hadari yayiwo kwana ya ƙara tunkaro shi da ƙarfin tsiya. Saboda ƙarfin gudunsa har wata iska ce ke tashi tana bada gunji tamkar ana ƙuga ruwan sama. Armad yai sauri ya baje a ƙas inda wannan hadari ya wuce ta saman kansa da kaɗan. Lallai bada ban yayi dabarar yin sauri ya kwanta ba da tuni wannan hadari ya dunƙule shi. Duk da cewa hadari ne kawai amma tsananin ruɗani da ƙarfin Izza dake tashi daga jikinsa yana da matuƙar tsoratarwa, lamarinda yasa Armad ya san lallai bai kamata ya bari wannan hadari ya riske shi ba. Haka dai suka ci gaba da kai komo; Armad yana ta zillewa hadari, shi kuma Ikenga yana ƙarawa wannan hadari ƙarfi da gudu. Amma duk da haka Ikenga bai samu damar riskar Armad. Armad na tsalle yana lissafi acikin ransa, "saura daƙika ashirin da ɗaya." Dama dai duk guje-gujen da Armad yake so yake aljaninsa ya tara masa wata walƙiyar. Kuma yasan dai-dai lokacin da zai ɗauka kafin hakan ta faru, saboda haka ya yanke shawarar yaci gaba da guje-guje zuwa sanda zai iya sarrafa wata walƙiyar. Amma a ɓangaren Ikenga kuwa, koda ganin babu yadda zaiyi ya iya kama Armad da hadarinsa saiya canja taku. Nan take ya tafa hannayensa ya kuma ƙara kiran wani ɗalasimin, "Samá'u!" Yana rufe baki wannan baƙin hadari dake bin Armad ya tsaya cak. Sannan daga bisani ya fara yin sama. A hankali a hankali har saida yakai kimanin ƙafa ashirin sannan ya tsaya. Yana tsayawa kuma ya fara buɗewa yana ƙara girma. Cikin abinda bai wuce daƙiƙa uku ba wannan hadari ya gama karaɗe saman wannan filin gasa. Armad ya buɗe baki yana kallon abin mamaki. Hadari ne baƙi-ƙirin ya rufe saman wajen baki ɗaya. Babu abinda kake gani face shi. To amma idan da shikenan al'amarin toda da sauƙi, amma a dai-dai wannan lokaci ne wannan hadarin ya fara rugigi, sannan tsawa ta karaɗe ilahirin wajen. Nan take aka fara tsuga ruwa kamar da bakin kwarya. Ikenga ya ɗaga hannunsa yai nuni ga Armad, lamarinda yasa dukkan wannan ruwa dake saukowa ya tunkari inda Armad yake da wani gudu irin na walƙiya. Kafin ma Armad ya motsa tuni wannan ruwa ya zagaye shi ya jiƙa shi sharkaf. "Kana da masaniyar cewa daga hadari akan samu ruwa." Ikenga ya fara magana cikin girman kai, tamkar babu wani ma'abocin Izza daya kaishi a ban ƙasa. Sai dai duk wannan abu bai tsorata Armad ba, domin kuwa a dai-dai wannan lokaci da yake tunanin zaiji wani canji kamar zafi ko kuma wani abu a yayinda ruwan ya taɓa shi baiji komai ba. Saboda haka ya ɗaga tafin hannunsa yana nazarin wannan ruwa daya jiƙa shi. A daidai wannan lokaci ne Armad yaji motsi a saman kansa. Amma kafin ya ɗaga kai wata ƙatotuwar ƙawanyar walƙiya mai ɗauke da ƙarfin Izza na shekaru ɗari ta fito daga cikin wannan hadari ta tunkaro shi. Kafin yayi koda tunanin kaucewa ta cimmasa. Inda nan take ta daki ruhinsa ta zagaye jikinsa tana neman tarwatsi shi. To da yake koda kana da aljanin walƙiya indai wannan walƙiya ba daga aljaninka ta fito ba saita yi aiki a kanka. Saboda haka nan take rauni ya cika jikin Armad. Da kyar ya iya zuƙo ƙawanyar walƙiyar da bata fi ta shekarun Izza biyu ba ya kare kansa. Abinda shi kaɗai ne yasa jikinsa bai tarwatse ba. A dai-dai lokacin ne ya ƙara jin muryar Ikenga, "shin kasan cewa daga cikin hadari akan samu walƙiya?" Wata dariyar mugunta ta cika fuskar Ikenga a yayinda ya ƙara ɗaga hannunsa ya ƙara kiran sunan wani ɗalasimin, "Sainówi!" Yana rufe baki dukkan ruwan dake kewaye da Armad ya juye nan take izuwa farar ƙanƙara. Cikin ƙiftawar ido da bismillah wannan ƙanƙara ta kewaye Armad ta rufe shi ɗaki ɗaya. Kai daga nesa idan ka hango Armad kace wani gunki ne da aka sarrafa da farar ƙanƙara. Ga baki ɗaya jikinsa ya ƙanƙare baki ɗaya, kai ko fatar jikinsa ba'a gani. Ikenga ya gabato inda ƙanƙararren Armad yake a tsaye yana taku ɗai-ɗai na ƙasaita, "Shin kasan daga cikin hadari akanyi ruwan ƙanƙara. Lallai ni Ikenga saina mulki duniya, kuma zan fara ta halaka ka, na kuma nunawa duniya ƙarfin Izza ta da ƙarfin aljani na Gal-iyyu, aljanin Hadari!" A wannan lokaci ne wata iska mai cike da tsoro da firgici ta tashi daga cikin ƴan kallon. Lallai a wannan da dama daga cikinsu suka san an fara gasar Jinzidal. ___ Kowa ya gayyato mana friends dinsa wanda suke son littafin yaƙi zuwa wannan page. Na fuskanci da dama basu da labarin Magajin Wilbafos. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 45: Dorawa Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos SHEKARA ƊAYA KAFIN ARMAD YA FITO NEMO WA MAHAIFIYARSA MAGANI. "Armad daga yau ya kamata kwata-kwata ka daina amfani da wannan fasahar takobin." Mahaifiyar Armad ce zaune a kusa dashi take lallashinsa a cikin ɗaki. Ga dukkan alamu dare ne kuma Armad bai jima da dawowa daga karɓar horo daga kakansa ba, domin ko kayan jikinsa bai cire ba. "Kaga duk amfanin da zakai da takobi zaka iya amfani da aljaninka na walƙiya kayi. Amma dai amfani da takobi haka ba tare da kasa walƙiya ba ina ganin a daina. Duk amfani ɗaya kana ƙara rage kwanakin da zakai a duniya. Kana kuma ƙara kusantar mutuwarka. Lallai bazan yafewa kaina ba idan wani abu ya same ka. Saboda haka ka daina kawai. Walƙiya ta ishe ka duk abinda zakai. Kuma hatta yayar taka Hidaya data bar maka takobin nasan da tasan haka zata faru da bata bar maka ba." "To mama naji. Na daina fa!" Armad ya faɗa cikin jimami da tuno wahalar da yasha kafin ya koyi wannan fasahar takobin amma gashi ala dole ya daina amfani da ita. Shekaru kimanin biyar kafin wannan rana ya gaji wannan takobi daga yayarsa mai suna Hidaya. Kuma tun daga wannan rana ya kwallafa ransa akan amfani da ita duk da cutar da jikinsa da take. Yakan ce takobin ita kaɗaice abarda tafi tuno masa da yayar tasa. Ita dai yayar Armad wato Hidaya ita ta sawa wannan takobi sunan ƊORAWA. Da dama mutane sukan yi tunani kodan saboda launin yalo na takobin shi yasa tasa mata sunan, amma ba haka bane. Dalilin ta shi ne ƙaninta Armad yakan bata sautu ta taho masa da ɗorawa a duk lokacin da zata tafi wata ƙasar. Armad dai masoyin ɗorawa ne, kuma tun yana yaro ya kwallafa a ransa cewa kan ya mutu saiya sha ɗorawar kowacce ƙasa dake duniya, tun daga kan doron ƙasa ta farko har zuwa ta bakwai. ___ A dai-dai wannan lokaci Armad ya ji sanyin wannan ƙanƙara yana neman lalata masa jiki. Saboda tsananin sanyi yana ji tamkar ana soya fatarsa. Hatta ganinsa ya fara komawa dishi-dishi, kuma tuni ya daina jin muryar Ikenga saboda ƙanƙarar data kewaye shi. Armad yana da cikakkiyar masaniyar cewa da Miyurarsa tana nan zai iya amfani da fasaharsa ta Wasu-wasi ya tarwatsa wannan ƙanƙara ya kuma saukarwa da Ikenga sara kafin ya farga. To amma yanzu babu. Kuma lallai idan ya ci gaba da zama a cikin wannan ƙanƙara to lallai ya faɗi wannan gasa, kuma Ikenga yayi nasara. Lamarinda ke nuni da cewa hanya ɗaya tak da yake da ita a wannan lokaci ta nemo Tarifil-fakta ta ɓace. Wanda kuma lallai abu ne da bazai amince ba, tunda baifi saura wata shida ne ya rage masa ya nemo wannan mutun ba. Nan take ya yanke shawara, "Idan ana zancen taimakawa iyaye a lokacin da suke cikin buƙata, idan ana zancen nemawa mahaifiya lafiya, to ai rasa shekaru ɗaya ko biyu koma goma na tsahon rayuwa ba matsala bane. Wanda zaiyi shekara hamsin ai zai iya haƙuri da arba'in!" A wannan lokaci Armad ya kira ɗalasimin da aka hanashi amfani dashi a rayuwarsa. Ɗalasimin da yake buɗe ƙofar amfani da takobin tarihi mai suna Ɗorawa. Takobin ita kanta Hidaya gada tayi daga mahaifinsu Wilbafos. Wannan ɗalasimi dai anyi amfani dashi ne wajen sihirce wannan takobi acikin wani shinge na tsafi. Wanda babu wanda ya isa yaje ko mutun ko aljan. Kuma wannan ɗalasimi an haɗa shi ne da ruhin Armad da kuma jinin zuciyarsa, saboda haka nema sunan wannan ɗalasimi, "Armad-Wilbafos!" Ai kuwa Armad na cewa, "Armad-Wilbafos!" Wata walƙiya mai ruwan ɗorawa ta fara ɓulɓula daga jikinsa. Nan take wannan ƙaton akwatin ƙankara dake kewaye da Armad ya fara narkewa. Ikenga ya juyo cikin mamaki, amma kafin ya ƙarasa juyowa tuni dukkan ƙanƙarar tasa ta narke. Abinda kawai ya tarar shi ne walƙiya mai ruwan ɗorawa na kewaye da jikin Armad. Sannan kuma a gaban Armad akwai wani dogon haske shima ruwan ɗorawa, wanda ya bada siffar takobi mai tsayin gaske. Kafin Ikenga ya gama tunani ko takobi ce ko ba takobi bace tuni dukkan yalon hasken ya ɗauke kuma wata doguwar takobi mai launin ɗorawa ta bayyana a gaban Armad. Tsayinta ya haura tsayin Armad da kamu uku da rabi, amma kuma siririya ce bata fi rabin tafin hannu ba. Dukkan jikin ta ruwan ɗorawa ne. Amma babban abun mamakin shi ne wata tauraruwa ruwan ɗorawa guda ɗaya data tsaya a saman wannan takobi ta kuma ƙi ɓacewa. Girman wannan tauraruwa baifi kamu ɗaya ba, amma tana fitarda wata irin Izza mai ban mamaki. Irin Izzar da baza ta misaltu ba, sai dai kurum wanda yake cikin wannan fili kuma yaji ta a jikinsa shi ne kawai zai iya fassara ta. Amma dai akwai kalma ɗaya da zata yi kama da wannan Izza wato MUTUWA. Lallai wannan Izza na kama da irin ƙanshin mutuwa wanda mutumin dazai mutu shi kaɗai ke ji. Bayyanar wannan takobi keda wuya da dama daga cikin manyan baƙin da ke tare da Uznu Ururu da sarki Deniz suka miƙe tsaye suna buɗe baki. Kai hatta Uznu Ururu saida ya haɗe fuska cikin mamaki. Ga dukkan alamu waɗannan mutane sun san wannan takobi. Ko kuma dai a ƙalla sun taɓa ganinta. 'Takobin Wilbafos!' Wannan shi ne kawai abinda Uznu Ururu ya ce acikin ransa. Abinda ya nuna cewa yasan takobin sosai, kuma har sunanta ya sani. A wannan lokaci ya zira hannunsa a aljihu ya fiddo da wannan allon tsafi, ai kuwa sai ganshi yana haske. Abin mamaki yadda allon yake haske da aka fito da Littafintakobi haka yanzu ma yake haske. Kana ganin fuskar Uznu Ururu kasan ya gama yanke shawara cewa lallai Littafin-takobi yana tare da Armad. Duk da wannan abubuwa dake faruwa ko a jikin Armad, miƙa hannu kawai yayi kan takobinsa ya kuma ɗaga ta sama, sannan cikin kwarewa da sabawa ana yi ya juya ta a sama ya kuma yiwo kan Ikenga. Nan take Ikenga yai nuni da ɗan yatsansa sama, lamarinda yasa wannan hadari dake sama ya fara rugugi kafin daga bisani a fara ruwan manya-manyan al'amudan ƙanƙara guda uku. Ya ƙara tafa hannayensa waɗannan al'amudai suka juye izuwa mutun-mutumi. Kowanne ɗaya daga wannan mutun-mutum ya juye izuwa siffar mutun sak irin Ikenga, harda kayan jikinsa. Ikenga ya ƙara tafa hannu, waɗannan mutun-mutumi suka buɗe bakunansu a tare. Abu na gaba daya faru shi ne wata ƙuwa da sauti masu rikita zuƙata da suka fara tashi daga bakin wannan mutun-mutumi uku. Ba komai ya jawo wannan ƙara ba illa wata dusar ƙanƙara mai tiriri dake fita daga bakin mutun-mutumi na farko, da kuma aradu mai ɗauke da jar walƙiya dake fita daga bakin mutun-mutumi na biyu, da kuma ruwan zafi dake fita daga bakin mutun-mutumi na uku. Dukkaninsu kan Armad suka yi gadan-gadan suna neman halaka shi. A wannan lokaci Armad ya juya doguwar takobin dake hannunsa. Wannan tauraro dake samanta ya kaɗa a sama. Sannan Armad ya aika wawan sara izuwa Ikenga. Nisan dake tsakaninsu ya fi taku biyar kuma babu yadda za'ai takobin takai inda Ikenga yake, kai ko inda wannan walƙiya da ruwa da dusar ƙanƙara suke ma baza ta taje ba. Amma bisa mamaki sai kawai wata walƙiya ruwan ɗorawa ta fice daga jikin takobin a matsayin saran da Armad yayi, ta kuma tunkari waɗannan abubuwa uku dake gabato shi. Wato dai a taƙaice saran da Armad yayi ya fice daga jikin takobin tamkar abu mai rai, ya kuma tunkari Ikenga. Irin wannan fasahar takobi aba ce maɗaukakiya a wannan zamani, kuma ita akewa laƙabi da fasahar takobi mai tafiya. Wasu kuma sukan kira ta Fasahar takobi mai Tafiya. A dai-dai wannan lokaci ƴan kallo suka fara firgita da al'amuran da suke gani. Lallai basu yi kama dana masu shekarun Izza ƙasa da dubu ba. Babu abida kake ji sai, "Kunga Armad yana iya amfani da fasahar takobi mai tafiya!" Wasu kuma su na cewa, "Kunga aljanin Ikenga SARKI RAUHANI ne." To ko mai ake nufi da aljani SARKI RAUHANI? To aljanu gama gari dai su ake rabawa izuwa ƙabilar baƙi, fari da kuma ja. Aljanu maɗaukaka kuma ana raba su ne Izuwa ƙabilar Rauhani, Muridi, Shaiɗani da kuma Ifiritu. To ko acikin waɗannan ɗin ma akwai maɗaukaka na sahun farko, wanda ake musu laƙabi na musamman. Misali asalin sunan aljanin Ikenga shi ne IYYU, amma saboda kasancewarsa maɗaukaki na sahun farko shi yasa ake ce masa GAL-IYYU. Wato dai 'GAL' ɗin da aka ƙara wata lambar girma ce. Babban banbanci tsakanin waɗannan aljanu shi ne ƙarfi da kuma yawan sihirin da zasu iya sarrafawa. Misali aljani gama-gari ɗan ƙabilar Fari, ko Baƙi, ko kuma Ja, baya taɓa mallakar fasaha sama da ɗaya; dole sai dai ko ya zama aljanin wuta, ko na ruwa ko na walƙiya ko na ƙanƙara ko kuma dai wani abu amma dai abu guda ɗaya kurum. To shima jinsin Rauhani da Muridi da Ifiritu da Shaiɗani abu ɗaya kurum suke iya mallaka, sai dai banbancin shi ne su basu da ƙa'ida. Misali aljanin Wuta ɗan ƙabilar Fari ko Baƙi ko Ja yana da adadin wutar da zai iya sarrafawa a kowanne lokaci, kuma indai ta ƙare saiya jira ta taru. Amma wutar aljanin wuta na ƙabilar Rauhani ko Muridi ko Ifiritu ko Shaiɗani bashi da ƙa'ida, wato zai iyai ta samarda wuta har abada. A kowanne lokaci idan kai duba acikin ɗan taƙin dake tsakanin ruhin irin waɗannan aljanu da masu su zaka ga wuta bata ƙarewa. To sai kuma aljani maɗaukakin Rauhani, wanda shima fasaharsa bata ƙarewa kamar duk wani Rauhani, sannan kuma yakan mallaki fasaha sama da ɗaya. Yawanci biyu. Amma ƙasa da kaso ɗaya acikin ɗari sukan samarda fasaha sama da ɗaya kamar aljanin Ikenga kenan. Irin wannan aljanu su ake kira da SARKI, sai a ƙara kalmar sarkin a farkon sunansu. Wato dai a taƙaice shi ne abinda ƴan kallon can suke nufi da cewa aljanin Ikenga SARKI RAUHANI ne. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 46: Nauyi da Lokaci Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos •Suna : Armad •Ƙabila : Wilbafos •Aljani : Ji-daime •Fasaha : Farar Walƙiya •Fasaha ta musamman : Miyura •Fasahar takobi : Ɗorawa •Izza : shekara 51 ____ •Suna : Ikenga •Ƙabila : Bayajidda •Aljani : Gal-iyyu •Fasaha : Jar walƙiya, ruwa, ƙanƙara •Fasaha ta musamman : Takun-sarki (shaibal-shísu) •Fasahar Takobi : Lokacin alfijir •Izza : Shekara 100 *** "Hmmm...." Armad baiko tsaya kallon saran takobin daya aikawa wannan ƙanƙara da ruwa da walƙiya ba, domin yasan lallai saran sa na takobi mai tafiya ba sa'an waɗannan mutun-mutumi bane. Saboda

Chapter 19 of 33