Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dake ɗaure da Uznu Ururu, rassan ta suka fara tamkewa suna ƙara girma da yawa. Kai kan kace meye wannan tuni kowanne reshe ɗaya ya koma dubu, sannan kuma dukkaninsu suka ɗaure Uznu tamau ko jikinsa ba'a gani. Haka na faruwa Nusi ta rame nan take, fuskarta ta fara tsufa, wani farin gashi guda ɗaya ya bayyana a goshinta. Babu abinda take sai haki, ko tsaiwa bata iyayi sai ta ɗan rankwafa. Lallai wannan fasaha ta janye ƙarfinta da yawa. Uznu Ururu kuwa na tsaye ɗaure cikin wannan bishiyar tsafi baya ko motsi. A dai-dai wannan lokaci ne sarki Deniz Iluru ya miƙe cikin firgici, idanunsa na karkarwa. Ya juya ya dubi jaruman da suka rako shi yana mai cewa, "Kuyi maza ku saka hijabi tsakanin ƴan kallo da filin can!" Ya nuna inda Ururu ke tsaye a ɗaure, "Waɗannan yaran sun jawo masifa. Yau duniya zata kara yin arba da abinda ake kira da Ururu." Yana magana yanayin fuskarsa na nuna girman halin da ake ciki, "Domin mutane da dama basu san mai ake cewa Ururu ba." Ai kuwa bai rufe bakinsa ba Uznu Ururu ya yaye hijabin dake rufe da idonsa, lamarinda yasa baƙaƙen idanun nasa suka bayyana a fili. Kallo ɗaya zakai musu kasan cewa duk abinda da ake gani bawai shi ne haƙiƙanin idanun Uznu ba, domin kuwa asalin idanun nasa na bayan hijabi. Wasu manyan abubuwane suka bayyana masu kama da wata da rana, baƙaƙe ne masu firgitarwa. Bayyanarsu keda wuya Uznu ya ƙifta idonsa sau ɗaya lamarinda yasa nan take wannan bishiyar tsafi da Nusi ta ɗaure shi da ita ta narke. Sannan a lokaci guda yai duba izuwa Nusi da Armad. Armad tuni dama yake ganin duhu tunda farko da sukai arba da Uznu, wanda hakan ne yasa ya kasa komai. Amma a wannan lokaci kawai ji yayi wannan manyan baƙaƙen abubuwa masu kama da rana da wata sun daki ruhinsa, sannan suka fara karya shekarun Izzarsa suna tarwatsa su. Nan take ya faɗi ƙasa sumamme. Ita kuwa Nusi kawai karkarwa take cikin tsoro da firgici. Domin kuwa tuni ta ƙarar da ƙarfinta a harin da tayi na farko, kuma bata taɓa tunanin ƙarfin Uznu yakai haka ba. Domin acikin wannan bishiyar tsafin data ɗaureshi da ita akwai sama da shekaru dubu na Izza. Tana cikin wannan tunani taji wani abu mai kama da nauyin dukkan duniya ya dake ta aciki, nan take ta jita anyi cilli da ita can sama ta fice daga cikin gaba ɗayan filin. Abu na ƙarshe da ta sani shi ne aman jini da take kafin ta sume. Amma duk da ta suma bata daina gudu a sama ba saboda wannan duka da Ururu yayi mata. Taci gaba da tafiya inda taje ta daki ƙarƙashin ƙasa sannan ta fice daga duniyar ƙarƙashin ƙasa izuwa wata duniya ta musamman. Lallai tasan rayuwarta na cikin hatsari a wannan lokaci domin kuwa dukkan ƙasusuwan jikinta sun ruguje kuma kayan cikinta sun farfashe. --Shi kuwa Armad kamar a mafarki, yaji hannu yana shiga rigarsa zai ɗauki littafin takobi, amma kuma sai yaji Littafin ya narke nan take sannan kuma yaji shi ya shige jikinsa baki ɗaya. A wannan lokaci Uznu Ururu ya kira ɗaya daga cikin Sadaukai biyar dake ƙasansa ya bashi umarnin ya ɗaukan masa Armad izuwa babbar shalkwatar Ururu dake doron ƙasa ta huɗu da niyyar aje a zaƙulo littafin daga jininsa. *** A dai-dai wannan lokaci da ake shirin ɗaukar Armad a tafi dashi fadar Ururu, Armad ya tsinci kansa a wani hali mai ban mamaki. Ya tsinci kansa a tsaye a wata duniya ta musamman. A gabansa a ɗaure cikin ankwa wata ƙatotuwar halitta ce wanda girmanta yakai zira'i dubu. Yana ganin wannan duniya abinda ya fara zuwar masa kai shi ne kodai mutuwa yayi ko kuma mafarki yake, saboda haka tun bayan samun kansa a wajen Armad ya mari kansa domin ya tabbatar shi ɗin ne ba wani ba. Inda ya tabbatar lallai shi ne a tsaye a wajen ba kuma mafarki yake ba. Dukkan duniyar launin fara ce fat, babu wata kala banda fari. Kuma shi Armad ɗin abu na ƙarshe daya ke iya tunawa shi ne ganin idon Uznu Ururu da yayi da kuma suma da yayi amma gashi a wannan waje. Armad ya ƙurawa wannan halitta ido kamar yadda ita ma take kallonsa. A ƙololuwar kanta akwai ƙahonhuna guda uku, sannan kuma idanunta koraye ne masu ratsin toka. Sannan kuma fatar ta fara ce fat babu ko kwayar gashi. Girman wannan halitta yakai yadda zaka iya cewa ƙaramin ɗan yatsanta shi ne dukkan girman jikin Armad. Bayan ɗan lokaci Armad ya numfasa ya dubi wannan halitta tare da cewa, "Kaiko waye kai, kuma mai yasa aka ɗaure ka, kuma sannan ina ne nan wajen?" Wannan halitta ta dubi Armad cikin ɓacin rai tare da ɗauke kai. Kallo ɗaya kacal zakai mata kasan cewa koma mece ce, kuma koma ya ake ciki bata farin cikin ganin Armad a wajen. ____ Ko wacce halitta ce wannan? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 50: Tsarin Ruhi Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Bayan wasu ƴan daƙiƙu na kallon-kallo tsakanin Armad da wannan halitta, sai halittar ta buɗe baki ta fara da cewa, "Idan da ka tsaya ka koyi al'amuran Izza a lokacin da Hidaya take koya maka da baka tsinci kanka a wannan hali na baƙin ciki da rasa yadda zakai ba." "Ehmmmm!" Armad ya ja numfashi tare da haɗe gira, "Nai maka tambaya baka bani amsa ba, waye kai?" Halittar ta ƙara buɗe baki cikin ɓacin rai, inda wani farin hayaƙi ya fito daga bakin, "Ni ne aljaninka JIDAIME! Baka ma san aljaninka ba, baka san koda ma'anar Izza ba, baka san tarihin Izza ba, baka san tsarin ruhinka ba, to tayaya zaka iya gwada kafaɗa da manyan ma'abota Izza." Armad bakinsa a buɗe yake ya kasa magana, babu abinda yake kai-komo acikin ransa sai abubuwan da wannan halitta ke faɗa. Da farko dai halittar tace ita aljaninsa. Ta kuma ce baisan ma'anar Izza ba, bai san tarihin Izza ba, sannan kuma bai san tsarin ruhinsa ba. Lallai Armad bai yadda da waɗannan abubuwa ba, hasalima yana ji cewa ai zancen banza ne ace baisan ma'anar Izza ba, ko kuma ace baisan tarihin Izza ba, tunda yayi karance-karance masu yawa akan al'amuran Izza tun yana yaro. Sai dai kuma abu na biyu da aljanin ya faɗa lallai Armad bai gane mai suke nufi ba. Na farko zancen cewa shi ne aljaninsa Jidaime, domin Armad bai taɓa ganin aljaninsa ba. Kullum abinda kawai yake gani shi ne ɗan taƙin dake tsakanin ruhinsa da aljanin nasa. Na biyu kuma Armad bai gane mai aljanin nasa yake nufi da baisan Tsarin-ruhinsa ba. Amma duk da haka Armad ya yanke shawara bari yabi wannan aljani a hankali koya ci ribar zancen, "Jidaime? Sunanka kenan. Da farko dai a sani na mutun baya iya ganin aljaninsa sai yakai shekaru ɗari bakwai da ɗoriya na Izza. To ta yaya nake iya ganinka bayan Izza ta bata kaiba? Na biyu kuma na yarda bansan tsarin ruhi na ba, kuma bansan tarihin Izza ba, saboda haka ka ganar dani. Amma duk da haka, kada ka manta baka amsa min tambayata ba: mai yasa kake a ɗaure idan kai aljani na ne, ko kuma dukkan aljanu irinka a ɗaure suke, sannan kuma nan a ina muke?" Aljani Jidaime najin hakan wani ɗan murmushi ya gilma ta gefen korayen idanunsa masu ratsin toka. Domin a ɗabi'ar aljanu suna so a basu girma, kuma a yarda ba'a sani ba sune suka sani. Saboda haka yana ji Armad ya yarda bai sani ba ya juyo izuwa gareshi tare da buɗe haƙoransa masu kama da farar kasa, "Bari na sanar dakai ilmi. "Kowanne bil-adama ana haifarsa da abinda ake kira da Tsarin-Ruhi. Duk wani Tsarin-Ruhi yana ƙunshe da abubuwa guda uku: Na farko aljani, na biyu takobi na uku Izza. "Kamar yadda ka riga ka sani kowanne mutun yana iya sarrafa fasahohi daban-daban kamar na Wuta ko Ruwa ko Ƙanƙara kwatankwacin aljaninsa. Kamar yadda ka sami fasahar walƙiya daga gare ni. To wannan gabatarwa ce kawai akan harkar tsakanin mutun da aljaninsa, kuma da dama manyan ma'abota Izza sun ƙarar da rayuwarsu gaba ɗaya akan gano wannan alaƙa amma basu gama ba. Lallai mutun kamar ka wanda baima taɓa ganin aljaninsa ba bashi da tacewa. "Takobi ita ce abu na biyu a ɓangaren Tsarin-Ruhi. Kuma anci sa'a bayanda ka rasa ƴar uwarka Hidaya ka farkarda fasahar takobinka, kuma yanzu kana iya amfani da fasahar takobi mataki na farko. Amma kayi sani cewa baka san komai ba a wannan fage. "Na uku a Tsarin-Ruhi shi ne Izza. Kamar yadda ka sani Izza wani tsarin shekaru ne na musamman tsakanin sadaukai ma'abota Izza, wanda yake basu damar ƙarin tsahon rayuwa. "To amma duk abubuwan nan guda uku daka ji baka san komai ba akansu. Hasalima kai baka iya amfani da kaso goma cikin ɗari na aljaninka domin ko kwance ni baka yiba. Sannan kuma har yanzu baka iya haƙiƙanin amfani da takobinka ba, daɗin daɗawa kuma Izzarka tayi kaɗan da yawa. Kai hasalima kai baka ma san matsayi na a tsakanin rundunar aljanu ba a matsayi ni aljaninka. Saboda haka baka san komai ba a duniyar Izza, idan kana so ka zamanto daga cikin manyan ma'abota Izza to kwance ni, ni kuma na koyar dakai abinda kake buƙata ka zama ma'aboci Izza. "Kuma ban manta da tambayoyinka guda biyu ba: na farko dai nan kana cikin duniyar aljanu ne, nine na janyo ka nan domin na gaji da ganinka a wulaƙance kana jawo min cin mutunci a tsakanin ƴan uwana sarakunan aljanu. Amma ka sani har yanzu jikinka yana hannun Uznu Ururu kuma bani da ikon kuɓutar dakai daga hannunsa, domin bazan iya shiga duniyar mutane ba. Wannan kawai ruhinka na janwo. "Na biyu kuma ina ɗaure ne saboda yayarka Hidaya ta ɗaure ni. Kada ma ka tambaye ni nima bansan mai yasa ba, amma wannan yaya taka ita kaɗai ce wadda aka haifa da ƙarfin ruhin da tun tana ƙarama take iya yin safa da marwa a tsakanin duniyar aljanu da mutane ta shiga inda take so. Lallai ƙarfin Izzarta abun tsoro ne har a tsakanin manyan aljanu. Ta haka ne ma ta shammace ni ta yaudare ni ta ɗaure ni." Koda aljani Jidaime ya faɗi jimlarsa ta ƙarshe sai ya canja fuska izuwa kalar fuskar wanda budurwarsa ta yaudare shi, tare da jan irin numfashin nan na dana sani, sannan yaci gaba da cewa, "Saboda haka zaɓin ka ne, kodai ka kwance ni ka koyi al'amuran Izza ko kuma ka bari Uznu Ururu ya kashe ka, kaga babu zancen samarwa mahaifiyarka lafiya. "Duk biyun zaɓinka ne!" Aljani Jidaime na zuwa nan a zancensa ya kautar dakai ya rufe ido ya fara kyankyaɗi." ___ Ina godiya ga dukkan waɗanda sukai min addu'a ta Komawata makaranta ngd, sai gobe zamu cigaba Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos Anan muka kawo karshen fita na daya Wanda muka tsakuro maku littafin magajin wilbafos daga part 1 zuwa part 50 in Allah ya yarda zamu cigaba, Daga http://hausaebooks.cf MAGAJIN WILBAFOS Fita na biyu 2 Marubucin littafin Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 51: Umarnin Ururu Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ___ SHEKARU DA SUKA GABATA (ALAƘA TSAKANIN HIDAYA DA ALJANI JIDAIME) ___ Hidaya ta ɓata rai tana duban aljani Jidaime wanda ke tsaye yana lilo akan iska, "Kasan mai yasa Ururu suka fi kowacce ƙabila ƙarfi a wannan zamani, ba komai bane saboda su basu dogara da aljanu ba. Saboda haka babu wata farar-laya da zata iya aiki a kansu. Sun dogare ne kachokam da ƙarfin Izzar dake cikin baƙaƙen idanuwansu. Haka nake so Armad shima ya dogara da ƙarfin jininsa na Wilbafos. Bana son ya dogare dakai a matsayinka na aljaninsa, domin hakan bazai kaishi ko'ina ba." Aljanin najin haka ya murtuke fuska, "Kina nufin kin raina ƙarfina ne. Kuma kema ai kina amfani da aljaninki, danme yasa kike so ki hana shi amfani da nasa." Hidaya ta ɗanyi murmushi sannan ta amsa da cewa ,"Bawai ina cewa ban yadda da ƙarfin ka bane, Jidaime. Kawai dai nasan akwai ƙarfin Izza irin wadda ni kaina ban san iyakacin ta ba acikin ruhin ƙani na, saboda haka ina so yayi amfani da ita maimakon ya dogara da ƙarfin aljaninsa. Saboda haka kayi haƙuri zan ɗaure ka ta yadda babu yadda Armad zai iya amfani da haƙiƙanin ƙarfinka. Kuma ina mai yi maka gargaɗi na ƙarsge da kada wani tsautsayi yasa ka ƙara haɗa kanka da aljani na domin yin hakan zai jawo maka hukunci. Aljani na bai taɓa biyayya ga Ururu ba kuma Ururu basu isa su baahi umarni ba. Kai kasan mai nake nufi." Tana rufe baki Aljani Jidaime ya fara jada baya yana neman guduwa, amma ina tuni Hidaya ta saukarda al'amudan Farar-laya akansa. Tun daga wannan rana yake a ɗaure, kuma basu samu wata damar ganawa da Armad ba sai a wannan lokaci. Hasalima Armad baisan cewa aljaninsa a matsayi ɗaya suke dana Ikenga ba. Kuma bawai kaɗai Walƙiya aljanin nasa yake sarrafawa ba. Kai a taƙaice ma wannan walƙiya ba daga aljanin nasa take fitowa ba. Tana fitowa ne daga ainahin cikin ƙarfin ruhin Armad wanda aka haifeshi dashi. Irin ƙarfin da yayarsa Hidaya take so yayi amfani dashi. _____ Acikin filin Jinzidal kuwa, har wannan sadauki mai muƙamin kyaftin ya ɗauki Armad a sume da niyyar tafiya dashi sai Uznu Ururu ya dakatar dashi. Uznu na tafiya taku ɗai-ɗai ya iso ga jikin Armad ya kuma saka hannunsa akan zuciyar Armad. Haka na faruwa wani haske ya fara fita daga jikin hannunsa yana shiga jikin Armad. ____ Acikin duniyar aljanun nan kuwa Armad yana tsaye yana tunani wacce shawara ya kamata ya yanke kawai sai yaga duniyar ta fara cika da wani baƙin haske. Lamarinda yasa shi ajiyar zuciya. Amma tun kafin ya gama gane maike faruwa yaga fuskar aljaninsa Jidaime ta canja. "Armad ko ka kwance ni yanzu ko kuma baza ka iya ƙara amfani da fasahar walƙiya ba." Aljanin ya faɗa cikin sauri da alamun tsoro. Idanun Armad suka cika da mamaki a lokacin da yaga canjin yanayin da aljanin ya samu kansa aciki. Nan take ya buɗe baki ya tambayi aljanin, "Mai yake faruwa?" "Uznu Ururu ne yake neman ƙara ƙarfin ankwar dake ɗaure dani. Ban san tayaya ba, amma da ƙarfin baƙaƙen idanun sa yana iya gani har cikin ruhinka. Wato dai a taƙaice yana ganinmu a halin yanzu. Kana da ƙasa da daƙiƙa biyar ka yanke shawara akan abinda zakai." Aljanin na rufe baki ya fara karkarwa lamarinda ya ƙara ruɗa Armad, domin har a wannan lokaci ya kasa yanke shawara. Abu ɗaya dai da Armad ya sani shi ne ba dukkan maganganun da aljanin ya faɗa zai yadda dasu ba, yasan cewa lallai ba'a raba aljanu da ƴan ƙarairayi nan da can. Amma a halin da yake ciki bashi da wani zaɓi face ya bawa wannan aljani dama yaga kozai iya kuɓutar dashi daga halin da yake ciki. Saboda haka Armad yayi tsalle izuwa wannan aljani, ya kuma ja ankwar da ƙarfin tsiya. Abun mamaki bai taɓa tsammani ba, amma kawai sai yaga ankwar tana murmushewa tana sakar wannan aljani. Wanda a iya lissafinsa cire ankwar zai ɗau lokaci kuma yana buƙatar makami kafin ya faru. Amma koda Armad ya tuna cewa ai ankwar ta tsafi ce, sai kuma ya gane yadda abin yake. Aljani Jidaime yai ƙaraji tare da miƙe hannayensa sama bayanda yaji shi a sake. Ranar daya daɗe yana jira tazo. Amma kafin ya fara komai yana buƙata ya kashe Uznu Ururu dake waje, wanda idan baiyi saurin yin hakan ba wannan baƙin hayaƙi zai iya ƙara ɗaure shi ya maida shi gidan jiya. Nan take ya finciko ruhin Armad daga wannan duniya ya dawo dashi izuwa jikinsa a wannan fili. Shi kuma ya bayyana a gaban Uznu Ururu yana mai riƙe da farin al'amudin aljanu a hannunsa na dama. Koda bayyanarsa sai dukkanin kyaftin guda biyar ɗinnan dake biye da Uznu sukai tsalle suka dira a gabansa domin su kare shi. Amma suna dira aljani Jidaime ya kawo wata muguwar wafta da al'amudinsa inda ya share su baki ɗayansu a lokaci guda. Sannan kuma yayi kan Uznu gadan-gadan. Lallai ƙarfin aljanu da bil-adama da banbanci. Nan da nan fuskar Uznu ta canja, yanayin firgici ya bayyana akanta. Amma a wannan lokaci ne ya ciji ɗanyatsansa na dama, inda jini ya fara ɗisa. Uznu baiyi wata-wata ba wajen saka wannan jini acikin idanunsa baƙaƙe guda biyu. Ai kuwa haka na faruwa wani baƙin haske ya fara ɓulɓula daga ciki, sannan Uznu ya fara magana, "Ina mai umartarka da ƙarfin Ururu dake jini na, da ƙarfin Ururu dake bisa ƙasa ta farko daka tsaya a inda kake." Abin mamaki yana rufe baki wani irin ƙarfin izza marar misaltuwa mai cike da buwayar Ururu ya fara ambaliya acikin filin. Kan kace meye wannan aljani Jidaime ya tsaya a inda yake cak ya kasa motsi. Sannan kuma Izzar Uznu ta fara hawa tana ambaliyar har saida takai Shekaru dubu huɗu da ɗari tara da casa'in da tara. Uznu ya cafi takobinsa yayi kan aljani Jidaime. Tun kafin ya ƙarasa akaji muryar aljanin na cewa, "Idan ka kashe ni kasan ƙabila ta baza suyi shiru ba. Kuma babban sarki Ururu Kuyurussa'ayi yayi mana katanga daku..." Yana magana yana karkarwa, kuma ganin cewa Uznu baya saurarensa kawai sauri yake ƙarawa yasa tsaya ya kasa ƙarasa abinda yake faɗa tare da fara karkarwa. Uznu na ƙarasowa yasa takobinsa ruwan toka ya tsarge aljani Jidaime gida biyu. Aljanin yai wata ƙara mai firgitarwa, inda daga bisa ya fara narkewa izuwa toka yana murmushewa. "Da kasan da tsakanin da akai mana da baka tunkare ni ba. Ko ba komai ina da hujja idan aka je gaban babban sarki Ururu Kuyurussa'ayi." Uznu na magana yana goge takobinsa. Sannan nan take ya ɗau Armad ya ɓace daga wannan filin gasa. ___ A can gefe guda kuwa sarki Deniz Iluru da dakarunsa suna tsaye suna kare duk wani hari da yayo kan ƴan kallo a lokacin da ake wannan fafatwa tsakanin Uznu da su Armad. Duk da kuwa cewa tunda Uznu ya buɗe idonsa dukkan ƴan kallon suka sume, amma bayan da aka gama komai hankali ya dawo jikinsu saida hukumar yaƙin garin tayi amfani da rahoton ƙarya na cewa girgizar ƙasa ce tasa aka tsayar da gasar wannan shekara. Amma ta ƙarƙashin ƙasa sarki Deniz Iluru ya rubuta ƙara izuwa fadar Ururu dake ƙasa ta biyu mai kula harkokin Jinzidal akan su hukunta Uznu Ururu saboda cikas ɗin daya kawo a gasar Jinzidal ɗin. Cewa kuma suna fata ai musu adalci. To haka dai aka kawo ƙarshen wannan gasa ta Jinzidal ta wannan shekara. ____ To ALLAH ya kawo mu ƙarshen Jinzidal. Yanzu zamu shiga wani sabon sashi na wannan littafi. Duk mai tambaya ko kuma wani abu da bai gane ba a babika 50 da suka wuce ya rubuto a comment. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 52: Dordor mai waka Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Doron ƙasa na huɗu Shalkwatar Mayaƙan Ururu ____ Sahu-sahu ne na mutane ɗai-ɗai har sahu ɗari, kowanne ɗaya daga cikin wannan sahu yana ɗauke da mutane guda ɗari. A taƙaice dai mutanen dake cikin wannan sahu su dubu goma ne. Dukkaninsu na sanye da baƙaƙen kaya. Babu mai ko magana acikinsu. Kai ko tari babu maiyi. Dukkanin wannan mutane ba kowa suke jira ba illa kwamanda Uznu Ururu. Uznu Ururu dai yaje ƙaro ilmi a jami'a mafi girma a duniya dake bisa doron ƙasa ta farko. Jami'ar da ake kira da Namibiya da yaren Aldurish na Ururu. Saboda daɗewar da yayi nema baya nan suka shirya masa wannan gagarumar tarya. Amma bisa mamaki Uznu yana bayyana kawai tsayawa yayi kimanin daƙiƙa ɗaya, inda ya kyaɗa musu kai alamun jinjina sannan yai ɓangaren inda ofishinsa yake. Koda yake baza a iya kiran wajen na Iznu Ururu da ofishi ba kaɗai, tunda iya girman wajen kaɗai yakai wani ɗan ƙaramin gari. Sannan kuma ga shirye-shirye na musamman na al'amura da suka shafi Izza da ake gudanarwa a wajen. Kusan zaka iya cewa duk wani sinadari da za'a iya samu a ƙasa bakwai akwai a wannan ɓangare na Uznu Ururu, kasancewar shi ɗin yawanci kayansa daga doron ƙasa ta farko yake tahowa dasu. Amma dukkanin wannan abubuwa basu suka dami Uznu ba, a yayin da cikin sauri ya shige wani ƙaton ɗaki na bincike-bincike inda yana shiga ya turo ƙofa ya rufe, tunda dama babu kowa acikin ɗakin. Sannan ya zaro wani ɗan irin Ayrid na musamman daga aljihunsa ya karanta wasu ɗalasimai, wanda nan take wannan Ayrid ya fara ƙara girma yana girma har saida ya kai girman ƴar ƙaramar ƙofa, inda nan take wannan irin Ayrid yai aman Armad ta cikin wannan ƙofa. Uznu ya fizgi Armad ya kwantar dashi akan wani ƙaton taburi na aiki. Sannan kuma ya fara karanta wasu ɗalasimai wanda suka saka wani farin haske ya fara cika ɗakin. Nan take wasu Rauhanan aljanu guda biyu, ɗaya mai ƙaho ɗaya mara ƙaho, suka bayyana, suna bayyana suka zube a gaban Uznu, kana gani kasan alaƙar dake tsakaninsu bata wuce ta bawa da ubangidansa ba. Uznu ya amsa sannan ya fito da wasu fararen takardu daga aljihunsa guda biyu ya miƙa musu. Sannan ya fara jawabi da cewa, "Kunga wannan shi ne karo na biyu da muka shigo da Littafin takobi wannan ɗaki acikin shekaru ɗari da suka wuce, saboda haka haka ina fata zamu kiyaye duk abubuwanda suka sa a wancan lokaci bamuyi nasara ba." Ya kalli aljanin mai ƙaho daga cikin guda biyun yace, "Kalkutu kasan mai zakai." Sannan ya juya izuwa mara ƙahon, "Kaima Netti kasan meye aikinka." Uznu ya ci gaba da bayani a yayinda wannan aljanu biyu suka nutsu suna saurare, "A bisa bincike na na gano cewa Littafin-takobi yana da rai yana kuma da hankali nasa na kansa. Kawai dai ba irin yadda mutane da aljanu suke ba. Kuma ta hakan nema na gano cewa indai akwai ma'aboci Ururu a waje to Littafin-takobi bazai taɓa baƴyana kansa ba. Kuma hakan ba abin mamaki bane tunda shi wanda ya samarda Littafin takobin ɗan adawar gidan mune na Ururu. "Saboda haka a lokacin da za'ai wannan aiki dole ne ya zamanto bana kusa da wannan yaro, in ba haka ba wannan Littafi bazai taɓa bayyana kansa ba. "Sannan kuma a wani binciken da muka gudanar a jami'ar Nimibiya mun gano cewa wannan Littafin ya zaɓi ƴan zuri'ar Wilbafos har a karo biyar daga cikin karo bakwai da ya taɓa zaɓar wani. Kuma shima wannan yaron daya zaba ɗan zuri'ar wilbafos ɗinne. Amma babban abinda zaku riƙe ku kiyaye shi ne, Littafin-takobi yana bayyana ya taimaki waɗanda ya zaɓa. Saboda haka hanya ɗaya da zamu tabbatar ya bayyana shi ne mu tabbatar da cewa mun azabtar da wannan yaro ta kowacce hanya ƙololuwar azabatarwa tayadda Littafin zai fito da kansa ya taimakeshi. Da zarar ya fito kunsan abinda zaku yi na gaba, saboda haka ku fara aiki. "Zan shiga shalkwata na fara shirye-shiryen sarrafa wannan Littafi tayadda kuna zaƙulo shi kawai aiki zamu fara akansa. A tafiya ta zuwa doron ƙasa ta farko na samu dama na tattautana da Babban ɗan sarki Kuyurussa'ayi, yarima mai jiran gado Níwajítu Dúmaƙísu Kuyurussa'ayi. Kuma ya bada koyon bayansa ɗari bisa ɗari akan abinda muke niyyar yi da wannan Littafi. Saboda haka lallai sai mun tabbata munyi nasara a wannan karan." Bayan Uznu ya tabbatar da cewa aljani kalkutu da Netti sun fuskanci halinda ake ciki sai ya fita ya barsu domin su fara aiki akan Armad. ________ A can wani sashin duniya dake ɓangaren Ikwatora na doron ƙasa ta shida kuwa wata mace ce kwatsam ta bayyana cikin jini kuma a sume. Lallai kana ganinta zaka san gab take da mutuwa, kuma lallai idan ba'ai wani abu akanta ba, to babu makawa mutuwa zatai. A tsakiyar inda wannan mace ta bayyana kamar wata daula ce ta Dordor launi-launi. Domin kuwa duk inda ka duba su zaka gani. Babu gida gaba babu gida baya a wannan daji da take, babu kuma abinda kake ji sai kukan tsuntsaye da maganganun jinsin halittar nan da ake kira da Dordor. To kamar masifar da wannan mata take ciki bata isa ba, sai kurum wasu daga cikin Dordor dake wajen suka hange ta. Ai kuwa nan take manyansu suka fara isa wajen. Amma bisa mamaki kowanne Dordor idan yazo ya shanshana wannan mace sai kawai yai tsaki ya juya kai ya tafi. Kuma dukkanin waɗannan dordor da suke zuwa kanta suna da kai sama da biyar. Kuma kowannensu fatar jikinsa nada launi na daban. Babu kuma wanda keda Izza ƙasa da ɗari biyar acikinsu. Lallai koda wannan mace na cikin hayyacinta bata ishe su kallo ba. To abu ne dai sananne a duniya cewa Dordor mai kai biyar zuwa sama shi ake cewa Babban Dordor, sannan kuma babban Dordor baya cin naman halittar da Izzarta bata kai ɗari biyar ba. Saboda haka dai ga dukkan alamu wannan mace ta taki sa'a. Sai dai kuma ana haka bayan waɗannan manyan Dordor masu kayika da yawa sun bar kanta sai ga wani Dordor nan mai kai biyu ya gabato, yana tafiya a hankali kana ganinsa kasan a yunwace yake. Tun daga nesa ya hangi wannan mace ya kuma fara murmushi da kansa na dama, sannan kuma yana dariya da waƙa da kansa na ɓangaren hagu. *Abinci ya samu Yau yau abinci ya samu Abinci har da kalace Abinci ya samu Abinci ya samu* Haka dai wannan aljani ya wanzu yana gudu-gudu sauri- sauri yana waƙa har ya isa inda wannan mace ke kwance. Abune sananne ansan cewa jinsin fararen Dordor sha'irai ne ma'abota waƙa, kuma sukan rera waƙa musamman a lokacin da suka samu abinci. Hakan nema yasa waƙa taƙi ƙarewa a bakin wannan Farin Dordor wanda kaf komai a jikinsa fari ne fat tun daga gashin kansa har zuwa fatar tafin ƙafarsa. Dordon ya miƙa farin hannunsa wanda yafi farar-ƙasa fari ya juyo da fuskar wannan mace. Sannan ya zaro wata ƴar ƙaramar wuƙa daga aljihunsa da niyyar ya fara yankar naman wannan mace yana kaiwa bakinsa-na- waƙa. Amma kafin ya fara komai ya ɗaga hannu ya fara da addu'a, "Godiya ga ubangijin daya jefowa da farin Dordor naman bil-adama. Muna fata gobe ma a bamu! Ameen!" Wannan Dordor ya shafa wannan addu'a sannan yai azama wajen fara yankan naman jikin wannan mace. Idan ka kalli fuskar wannan mace zaka ga ba wata bace illa Nusi ƙawar Armad wilbafos, wadda kwamanda Uznu Ururu yai cilli da ita aka nemeta aka rasa tsahon lokaci. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 53:

Chapter 21 of 33