ta, ya faɗaɗa fara'arsa ya ce.
"Baby kin yi kyau sosai." A madadin ta ba shi amsa sai ta ce.
"Wato Hafiz ni ka so tozartawa ko? Saboda za ka dawo da matarka shi ne ba za ka sanar da ni ba. Na gode, ai yanzu amfanina ya ƙare tun da ta dawo." Zama Hafiz ya yi a gefenta ya ce.
"Haba Bilkisu, me ya sa za ki ce haka? Ina kasuwa mahaifinta ya kira ni, amma don Allah ki yi haƙurin rashin kiranki." Yana rufe baki sai kawai Bilkisu ta fashe da kuka, janyo ta jikinsa ya yi ya shiga lallashinta. Sai da ta tsagaita da hawayen sannan ya ce.
"Ina abincina?"
"Yana kicin." Ta ba shi amsa a daƙile.
Har ya miƙe zai fita ya waigo ya ce.
"Am dama tun da Amina ta dawo, a ɗakinta zan kwana yau."
"To mene ne na faɗa mini Abban Sayyid, ai duk abin da ka yi ka isa ne. Da za ka dawo da ita ka faɗa mini? Sai don za ka je ka kwana a wurinta za ka yi mini 'yar murya, duk abin da mutum dai ya yi Allah Yana kallo." Murmushi kawai Hafiz ya yi ya fita, don ya fahimci rikici Bilkisu take ji, idan ya ce zai tanka mata sai ta mayar da abin ya zama babba.
A ranar kwanan farinciki suka yi tsakanin Hafiz da Amina, duk wani tabon da take kallon Hafiz da shi ya goge. Kuma tun daga wannan lokacin Amina ta sauya taku, duk wani motsi da furucin Bilkisu tana ganewa. Don haka koda ta yi wani abin Amina ba ta nuna mata ta damu, wannan dalilin ne ya sa Amina ta cigaba da zaman aurenta cikin kwanciyar hankali. Sai laulayin cikin da yake danunta, shi ma a lokacin da ya shiga wata huɗu sai laulayi ya yi mata sauƙi sosai. Don babu abin da ba ta ci sai wanda ba a rasa ba, haka kuna ta ɓangaren ciwo zazzaɓin dare da yawan ciwon kan da take yi duk ta daina.
Ana cikin haka sai Bilkisu ta tsiri duk ranar da Hafiz yake ɗakinta, a ɓoye za ta aiki yaranta gidan wata ƙawarta Maman Siyama, da yake yaran Maman Siyama sun girmi su Sayyada sai su sayo mata Nama ko kifi a ɓoye. Sai ta yi girki da shi, ko kuma da safe ta sayo ƙwai tun da dare ta soya musu ita da yara. Haka wunin ranar Amina za ta yi ta cika tana batsewa, kuma sai abin ya haɗe mata ga saurin fushi irin na mai ciki ga kuma abin da Bilkisu take yi. A irin haka har faɗa suka taɓa yi da ita da Hafiz, ya yi mata rantsuwar duniya a kan ba shi yake saya wa Bilkisu ba ta ƙi yarda. Tun yana lallashinta har ya yi watsi da ita, sai watarana da ta jin sallamar yaro bayan ya shiga ɗakin Bilkisu har zai fita ta bi shi soro da sauri. Murmushi ta yi masa cikin bugar ciki ta ce.
"Ni kam kifin da kake sayo wa Maman Sayyada yana da arha kuwa? Naman da kifin wanne ya fi sauƙi ne?"
Yaron ya yi jim sannan ya ce. "Gaskiya kifin ya fi arha don Ummanmu ma shi take saya, amma na ga ita Maman su Sayyid ta fi son na sayo mata nama." Jinjijna kai ta yi ta ce.
"To je ka, na gode ka ji."
Ya amsa mata ya tafi.
Ɗaki ta koma tana nazari, sai kuwa ta ɗauko waya ta kira Hafiz sai da ta ji ya ɗauka sannan ta fita tsakar gida ta ce.
"Hello Habibi, ba na jinka ko network ne?" Bilkisu tana tsakar gida tana koyawa su Sayyada aikin makaranta, ta ji muryar Hafiz raɗau a kunnenta. Amina da ta tabbatar da Bilkisu ta ji, sai ta fakaici idonta ta katse kiran ta ce.
"Yawwa dama na ce, don Allah idan za ka taho ka biya gidan Aunty Nana ka ba ta kuɗin naman kai ƙafa, don gobe farfesunsu nake so kuma ba na son na yi wahalar dafa su." Sai ta shige ɗaki ta ce.
"Eh network ɗin ya dawo, to shi kenan Hubby Allah Ya bar mini kai." Amina ta leƙa ta windo ta ga Bilkisu ta yi kasaƙe har da sakin ƙwafa.
Tun a daren ranar ta kira yayarta Aunty Nana ta tura mata kuɗi, ta ce da safe ta aika yara a sayo naman kai ta yi mata farfesu, idan ya so da rana idan Hafiz ba ya gida sai ta aiko a kawo mata.
Kamar yadda suka tsara Amina tana zauna a tsakar gida washegari da rana, tana sai ga Usaina 'yar yayarta ta yi sallama. Da yake budurwa ce, kuma Amina ta kitsa mata komai tana shiga cikin ɗan ɗaga murya ta ce.
"Aunty ga farfesun naman kan, wai Umma ta ce ga canjin dubu ɗaya da ɗari biyar na Yaya Hafiz." Amina ta karɓa ta buɗe, take ƙamshin ya mamaye gidan har ta ji yana shirin saka ta amai. Gani suka yi Bilkisu ta fito, Amina ta ɗan yamutsa fuska saboda dama can naman kai bai wani dame ta ba ta ce.
"To ku kunci ne?" Yarinyar ta girgiza kai, sai ta ɗauko wata ƙaramar roba ta ɗauki ƙafa ɗaya ta ɗora a kai da romo ta ce a miƙa wa Bilkisu. Tun Usaina ba ta rife baki daga sallamar da ta yi wa Bilkisu ba, ta buga mata tsawa da cewar ba ta ci. Dariya Amina ta yi a ranta, ta dubi Usaina ta ce.
"Ungo canjin nan nasa je ki kanti ki sayo mini multina guda biyu, don wannan naman kan ba lallai na iya cinye shi ba sai dai ki tafi da shi."
Babu jimawa Usaina ta sayowa Amina, sai da suka shiga ɗaki sannan Amina ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Maza ki mayarwa da Aunty naman kan nan, don wallahi daurewa kawai nake yi ji nake kamar zan yi amai." Dariya Usaina ta yi, ta yi saurin fita daga gidan ba tare da Bilkisu ta ganta ba.
Tun bayan zuwan Usaina Bilkisu ta cika fam tana jiran dawowar Hafiz, yana dawowa da daddare ko mashin ɗinsa bai gama ajiyewa ba fuuu Bilkisu ta je ta same shi a wurin ta ce.
"Wallahi ka ji tsoron Allah Hafiz, don kuwa Allah sai ya tuhume ka a kan rashin adalcin da kake yi."
Da mamaki ya dube ta ya ce. "Rashin adalcin me na yi miki?" Takaici ya sa Bilkisu ta fashe da kuka ta ce.
"Yanzu don zalinci har naman kai za ka sa a dafowa Amina ni yarana muna zaune ko oho? Wallahi Allah ba zai barka ba, idan kuwa kana zalintata ban yafe maka ba." Rai a ɓace Hafiz ya ce.
"Ni kike faɗa wa haka?"
"An faɗa maka, mugu azzalumi. Wallahi ban yafe maka ba Hafiz." Har ya ɗaga hannu kamar zai mare ta sai ya sauke, bayan ya gyara mashin ɗinsa ya ce.
"Amina! Amina!"
Da sauri Amina ta ƙaraso ta ce.
"Gani baby, ashe ka dawo."
"Me yake faruwa? Na ji Bilkisu tana zancan naman kai?" Hafiza ya tambaya. Amina ta wara hannu ta ce.
"Ranka shi daɗe itaa za ka tambaya, ba ita ta yi maka maganar naman ba."
A ƙufule Bilkisu ta ce. "Ni za ku mayar mahaukaciya ko 'yar iska? Na ji kina waya kina cewa Hafiz ya biya ya kai kuɗin a saya miki naman kai, har a kawo ki kawo mini ɗazu shi ne za ki raina mini hankali?"
Amina ta zaro ido tana tafa hannuwa haɗe da salati ta ce.
"Aunty sharri za ki yi mini? Ni na ce Baby zai tura kuɗin naman kai?" Sai kawai Amina ta rushe da kuka.
Ummou Asalam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA SHA ƊAYA
KU ZO KU SAYI MUSULMAN KAYANMU💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Assalamu Alaikum
Ina manyan mata yan gayu masu ji da kwalisa ...
Ina masoyan jakankuna da mayafai da kuma sarƙoƙi?
Ummee's Collection ta tanadar muku su kala kala acikin farashi mai sauki, lallai ku hanzarta kada a barku a baya.
Domin mallakar naku sai ku tuntube mu anan
What'sapp or call :- 08082350419
A ɗan rikice Hafiz ya riƙo Amina ya ce.
"Haba Maman baby mene ne abin kuka kuma daga tambaya? Kin san fa na ce miki ba na son duk wani abu da zai dinga ɓata miki rai."
Amina ta sake ƙaƙalo hawaye ya cigaba da zuba shaa, ta kwantar da kanta a jikin ƙirjinsa har tana sauke ajiyar zuciyar kamar wacce ta ci kuka ta more. Hakan ya sake damun Hafiz, a ɗan faɗace ya dubi Bilkisu ya ce.
"Yanzu don Allah me kika yi haka Bilkisu? Ƙiri-ƙiri kin ɗaga wa yarinya hankali tana fama da kanta." Ran Bilkisu ya ƙara ɓaci, cikin kumfar baki ta ce.
"Ni za ku yi wa makirci, munafuka ba ɗazu aka kawo miki ba har da ragowar canjinsa da kika sa aka sayo miki multina." A zafafe Hafiz ya nuna ta ya ce.
"Kada ki sake ce mata munafuka, ban bari ta raina ki ba don haka son zuciyarki ba zai sa na bari ki wulaƙanta mini mata ba." Amina kamar tana jira ta sake fashewa da kuka ta ce.
"Ka ji wani sharrin da za ta yi mini ko? Wai na sha multina Baby don Allah tun da na samu cikin nan ba sau ɗaya na sha ba? Ita ma ba amai ta saka ni ba." Hafiz ya gyaɗa mata kai sannan ya ce.
"Bilkisu ba na son tashin hankali, kin san dai babu yadda za a yi na sayo abu a ɓoye na ba ta ban ba ku ba. Ki sama mini lafiya, kada ki sake ki sakawa matata hawan jini ki bar ni da wahala. Yarinyar nan ba huruminki take shiga ba, don haka ki kama kanki." Daga haka ya yi gaba yana riƙe da Amina har ya kai ta ɗaki.
Bilkisu ta kusa minti biyu a tsaye tana hawaye, sai da ta gaji don kanta sannan ta wuce ɗaki ta zauna ta rafka tagumi. Nazari ta yi sosai, lokaci ɗaya ta miƙe tsaye zumbur tana kai kawo a ɗaki.
"Wato yarinyar nan ni za ta yi wa bariki kenan?"
Bilkisu ta furta cike da jinjina kai, ta koma ta zauna sannan ta sake cewa.
"Ai kuwa kin yi da 'yar halak, idan kuwa haka ne yanzu muka fara wannan wasan." Ta ƙarasa furucinta tana sakin murmushi.
Duk da Bilkisu ta gano makirci Amina ta yi mata, haka ta cigaba da cika tana batsewa. Da yake Hafiz shi ma a ƙule yake da ita, sai ya yi watsi da ita. Har sai da ta gaji don kanta sannan ta sauko.
Tun daga wannan ranar Bilkisu sai ta ja baya da ƙulla makircin da take yi wa Amina, koda ta yi idan Aminan ita ma ta rama sai ta watsar da shi. Haka suka cigaba da tafiya har aka shiga watan azumi a lokacin cikin Amina ya shiga wata shida. Rimi-rimi suka ɗauki azumi kamar zamansu ya yi lafiya, sai da aka kai azumi na tara sannan Bilkisu ta kira Maman Siyama ta tura mata kuɗi. Da yake duk Azumi Yaya Salisu yana yi musu rabon kuɗi da atamfofi, don haka a ranar ta kira ta suka gama tsara duk yadda za su ita da Maman Siyama. Washegari sai da Hafiz ya tafi kasuwa, sannan wani ɗan matashi ya yi sallama a soron gidan. Bilkisu tana ji ta yi shiru kamar mai bacci, Amina ce ta amsa masa haɗe da tambayar waye. Daga can ɓangaren matashin ya ce.
"Aike ne daga wurin mai gidan." Hijabinta ta ɗauka ta zura, sannan ta ƙarasa ta ce.
"Kawo."
Janye kayan ya yi ya ce.
"Ai ya ce ba ke za a ba wa ba." Mamaki ne ya kama Amina, saboda ta san sautari idan Hafiz ya yi aike duk wacce ta fita za ta iya karɓa. A daidai lokacin Bilkisu ta ƙarasa tana ɗan murza fuska kamar mai bacci ta ce.
"Au wai dama kai ya aiko? Yanzu na ji kiransa a waya ina bacci."
Ɗan matashin ya ce.
"Eh, ga shi wannan cewa ya yi na amfanin gida ne." Sai ya miƙa mata wata ƙaramar baƙar leda. Ya janyo wani ɗan ƙatan buhu, mai ɗauke da doya dankali har da kayan shayin su gwangwanayen madara. Da gayya Bilkisu ta ce.
"To ai ya ce saƙon biyu ne, akwai na Babanmu." Matashin ya ce, "Eh ga shi nan, ya ce kun yi maganar zuwanki gida shan ruwa." Murmushi Bilkisu ta yi ta ce.
"Kai yanzu Abban Sayyid duk shekara ba ya gajiya, to ɗan shigar mini da shi ciki don ya yi mini nauyi." Matashin kafin ya ɗauki buhun ya ce, "Yawwa ya ce ki duba drower kayansa, a cikin kuɗin da yake ba ki ajiya ki ɗauki dubu biyar ki ba wa Baba ya sa yi takalmi." Bilkisu ta wani narke kamar za ta yi kuka ta ce.
"Har ban san me zan ce ba. Kai bari na kira shi a waya, maza shigar mini da kayan ciki." Wayar da ke hannunta ta latsa layin Hafiz, sai da ta tabbatar da Amina ta ji maganar Hafiz bayan ya ɗauka. Sai ta yi cikin gida tana faɗin.
"Hello Aljannata."
Katse wayar ta yi ta saka ta a aeroplane mood sannan ta cigaba da cewa.
"Habibi ban san me zan ce maka ba, thanks you so much Zauji. Allah Ya bar mini kai har cikin aljanna."
Tana gama faɗa ta sakarwa wayar kiss, sannan ta ajiye ta faɗa banɗaki ta yi wanka.
Amina ta fi minti biyar a tsaye tana jin zuciyarta tana zafi, musamman da ta tuna yadda suka yi da shi a ranar da za a kai na azumi na takwas. Da ta ce ya ba ta kuɗi ta saya wa iyayenta kayan shan ruwa, ya ce mata ba shi da kuɗi. Hawaye ne ya zubo mata, don haka jiki a saɓule cike da tsangwamar kanta ta wuce ɗaki. Bilkisu ta saki murmushin ƙeta ta ce.
"Kika ce ba kya ji yarinya, baƙinciki ma yanzu kika fara sha."
A gurguje Bilkisu ta gama shiri tana fitowa, wani yaro ya shigo da sallama ya ce.
"Wai nan ne gidansu Maman Sayyid?"
Bilkisu ta saci kallon Amina da ke kwance a tsakar gida tana shan iska ta ce.
"Eh nan ne, ya aka yi?"
Yaron ya ce. "Wani mai adaidaita sahu a ƙofar gida ya ce a faɗa miki, wai mai ɗan sahun da Baban Sayyid ya turo zai kai ki unguwa ne."
Amina tana zaune sai da ta tashi zaune, zuciyarta ta ji tana zafi. A hankali ta furta.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un."
Bilkisu ta saki murmushi ta ce.
"Ka ce masa tana zuwa." Tana faɗar haka ta yafa mayafinta, ta kinkimi buhun har ta je tsakiyar gida ta ce.
"Auntyn yara ni zan wuce, ina jin ma ba sai kin yi abinci da yawa ba. Saboda har Abban Sayyid a gidanmu zai sha ruwa." Amina da baƙinciki ya gama cika ta ko amsawa ba ta yi ba. Bilkisu tana fita hawaye ya fara zubo mata, takurewa ta yi a gefe ta ci kukanta mai isarta. Sai zuwa can yamma ta ga kiran wayar Hafiz ya shigo mata, kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta taushi zuciyarta ta ɗauka don ta ji me zai ce mata. Sallama ya yi mata bayan ta amsa ya tambayi ƙarfin jikinta don ya ji muryarta ba kamar yadda ya fita ya bar ta ba.
"Amina idan azumin nan yana ba ki wahala don Allah ki ajiye shi ki huta, ai Allah Ya ga halin da kike ciki daga baya sai ki rama. Saboda duk na ji muryarki wani iri, ko akwai abin da yake damunki?" Hafiz ya faɗa cike da kulawa, takaicin tambayarsa ta ji. Tana ganin kamar ma ya raina mata hankali ne, murya babu walwala ta ce.
"Ba komai."
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce.
"Dama kira na yi na faɗa miki, zan sha ruwa a gidansu Bilkisu, kin san mahaifinta duk shekara yana gayyarar surukai da 'yaransa shan ruwa a gidansa."
"Hmmmm!" Kawai Amina ta ce, saboda tana buɗe baki za ta iya faɗa masa maganar marar daɗi.
"Amina ko ba kya ji ne, cajin wayata zai mutu."
Hafiz ya furta a gaggauce. A daƙile Amina ta ce.
"Na ji."
A sanyaye Hafiz ya ce.
"Wallahi tun safe mantawa na yi ban sanar da ke ba. Amma ba daɗewa za mu yi ba, kuma su Sayyada suna nan za su ɗebe miki kewa."
"Sai an jima aiki nake." Amina ta furta tana kashe wayar gabaɗaya. Hawaye ne ya zubo mata, cike da takaici ta ce.
"Hmmm namiji munafiki, duk wani makirci namiji ya iya ƙulla shi. Wai ni zai mayar 'yar iska, saboda ya raina mini hankali."
GIDAN ALHAJI UMAR
Hajiya Karima suna zuwa harabar gidan motar Baba malam tana fakawa a ciki, da sauri ya fito daga cikin motar rai a ɓace ya ƙarasa wurinta ya ce.
"Karimatu, abin da Mamana ta kira ni a waya ta sanar da ni haka ne?" Mommy ta goge ƙwallar idonta ta ce.
"Haka ne yaya."
Baba malam yayan Daddy ne, shi ne babba a cikinsu. Sun ɗauke shi tamkar mahaifinsu, don haka suke shakkarsa. Cikin ɓacin rai ya ce.
"Ina Umarun yake?"
Da hannu Mommy ta nuna masa cikin gidan, tun ba ta sauke hannu ƙasa ba ya wuce ciki yana ƙwala masa kira.
"Kai Umaru! Umaru kana ina?"
Daddy hannunsa riƙe da Shukura ya fito ta ce.
"Ga ni."
Tass! Baba malam ya ɗauke shi da mari har sai da hannunsa ya rabu da na Shukura, a tsorace ta ja da baya ganin abin da ya faru. Cikin fusata Baba malam ya nuna shi ya ce.
"Ashe ba ka da hankali ban sani ba, ko ka fara shaye-shaye ne? Wato Umaru mu za ka tozarta ka wulaƙanta? Kana cikin hankalinta za ka saki Karima?" Ran Daddy ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, a fusace ya dube shi ya ce.
"Shi kenan ba ni da hurumun zartar da hukunci a kan iyalina? Yaya kai wa yake dakatar da kai a kan naka iyalin?" Baki sake Baba malam yake bin Daddy ya kallo, cikin mamaki ya ce.
"Umaru ni kake faɗawa haka?"
"Haifata ka yi da ba zan faɗa maka ba Yaya? Kowa fa ya ji da wutar gabansa. Karima matata ce kuma na sake ta, kawai shi ne har za ka zo ka gaban 'ya'yana ka kunyata ni ka mare ni." Wannan karon ba yayansa ba, hatta su Mommy tsoro lamarin Daddy ya ba su. Saboda sun san ko tari mahaifinsu ba ya yi, idan Baba malam yana yi masa faɗa.
"Baby wai duk a kan wannan matar ake wannan abin, ai dama ni na jima da fahimtar danginka ba sa ƙaunata. Kuma tun da haka ne, ni ba zan iya cigaba da zama da kai ba..."
"Ke rufa mana baki." Baba Malam ya katse kalaman Shukura, cikin ɓacin rai Daddy ya ce.
"Yaya ina ba ka girmanka fa, amma wallahi kada ka sake yi wa matata tsawa. Haka kawai a dake ta a hana ta kuka, yarinyar nan sun zalince ta don kawai an ga ba ta da hatsaniya ne?"
Jinjina kai Baba malam ya yi ya ce.
"Ba laifinka ba ne Umaru, ke Karima ku wuce mu je can gidana."
Daddy cikin halin ko inkuka ya ce.
"Oho gara ku je, ba za ka birge ni ba sai ta gama idda ka aure ta." Daga Mommy har Baba Malam waigowa suka yi suna kallomsa, su Ruƙayya da ƙannenta ban da kuka babu abin da suke yi. Motar Baba malam suka shiga, rai a ɓace ya tuƙa su suka fice daga gidan zuciyarsa tana ƙuna.
Suna zuwa gida ya sanarwa da matansa abin da ya faru, gabaɗaya jikinsu ne ya yi sanyi. Kuma nan take suka fahimci ba yin kan Daddy ba ne, don haka ya kira Mommy har ɗakinsa don ya ji takamaiman abin da ya faru.
Sai da Mommy ta share hawayenta, sannan ta zayyane masa irin zaman doya da manjan da suke yi tsakaninta da Alhaji tun bayan tarewar Shukura. Shiru ya yi yana nazari sannan ya ce.
"Karimatu sai dai mu taya Umaru da addu'a, kuma zan saka masallatai da malamai su taya mu da yi masa addu'a. Domin tun furucinsa na farko da ya yi mini ɗazu na fahimci ba ya cikin hayyacinsa, ke shaida ce. Tun da kika da shi bai taɓa yi mini musu ba, ban taɓa faɗar magana shi da ragowar 'yan'uwanmu sun yi mini musu ba. Amma babu komai, In Shaa Allahu babu abin da ya fi ƙarfin Ubangiji. Yanzu za ku cigaba da zama a nan keda yara." Hajiya Karima ta numfasa ta ce.
"Na gode sosai Yaya da karamcin da ka nuna mini, amma ka yi haƙuri na yake hukuncin zan koma gida."
Girgiza kai ya yi ya ce.
"Karima ashe har kawo wannan lokacin ba mu zama ɗaya ba kenan? To ai ko ba Umaru ba ne mijinki, ni me riƙe ki ne da yaranki idan kika duba zumuncin da ke tsakanin iyayenmu. Idan har na isa da ke, ban ba ki damar komawa gida ba. Kuma duk abin da kike buƙata ko yara, ki same ni kai tsaye ki tambaye ni." Godiya sosai Hajiya ta yi masa tana kuka, da suka gama magana sai ya ga ta jim kamar akwai abin da yake damunta. Cikin kulawa ya ce.
"Ko akwai wani abu ne Karima?"
"Yaya dama maganar Haidar ne, ina tsoron kada ya sa jami'an tsaro su azabtar da shi. Sai kuma maganar auren yarinyar nan da ya ce ba zai ɗaura mata aure ba."
Mommy ta furta cikin damuwa.
Murmushi ya yi ya ce, "Ki kwantar da hankalinki Karima, yanzu haka daga nan wurinsa zan tafi." Sai ya dafe kansa cikin damuwa ya ce.
"Sai dai ban san wanne station aka kai shi ba."
Mommy ta ɗan yi nazari ta ce, "Ina tunanin na Sharaɗa ne, saboda na ji ya kira DPO abokinsa."
"D.P.O Ayagi kenan?"
Baba malam ya tambaya. Gyaɗa masa kai Mommy ta yi.
Baba Malam ya ce, "Ai ta zo gidan sauƙi, Indai Ayagi ne yayansa aminina ne zan yi masa magana In Shaa Allah."
Sai ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Maganar auren Mamana kuwa kada wannan ya dame ki, da Umaru da babu Umaru za mu yi mata aure ta tare a ɗakin mijinta. Tun da muke ba a taɓa yin abin kunya a danginmu ba, don haka Umaru bai isa ya zubar mana da kima a wurin dangin saurayinta ba. Ki sa a ranki kamar an yi bikinta an gama idan muna da rai da lafiya." Cikin girmamawa Mommy ta ce.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 35