akasinta. Sannan ka san Ubangiji ne ya ba ka Ɗan Bishir, a lokacin da ba ka yi tsammani ba. Don haka kenan ko a yau Allah Ya yi niyyar ɗauke abinsa zai iya. To me zai sa ka kashe kanka a banza da wofi, ko ka janyo wa kanka ciwo ya kwantar da kai. Lokacin da na zo likitoci sun tabbatar mini ko a asibitin nan ka yi suma ya fi bakwai, don Allah ka kwantar da hankalinka. Yanzu ina son daga nan zan wuce na je na samu Bala Wanzan, da shi Idi Naira na ji yadda aka haihu a ragaya. Idan na ji ta bakinsu sai mu wuce asibiti ɗungurungum a yi haihuwa da hanji, amma babu yadda za a yi a dinga faɗar cuta da fatar baki ba tare da an tabbatar ba."
Da sauri Baba Sale ya riƙo hannunsa ya furta. "Yaya zan bi ka, gara a yi komai a kan idona."
Baba Ibrahim ya sake haɗai rai ya ce, "Idan ka san za ka yi mini hayaniya ko ka je kana sume-sume gara ka yi zamanka a nan."
Cikin sauri Baba Sale ya girgiza kai, Baba Ibrahim ya yi wa lokitocin bayani sannan ya biya su kuɗin ruwa da alluran da ake yi masa; suka wuce Police station.
Bayan sun gaisa Baba Ibrahim ya gabatar da kansa sannan ya ɗora da cewa.
"Yallaɓai zuwa na yi domin na ji kan zancen abin da ya faru, idan da yuwuwar zuwa asibiti a yanzu sai mu wuce gabaɗaya."
Sergent ɗin da ke tsaye ya buɗe wani file ya zaro takarda ya ce, "Alhaji wani mutum mai suna Malam Shehu mai doya shi ya kawo ƙarar Bala wanzan, yana tuhumarsa da cin zarafinsa bayan ya je ƙofar gidansa. Sannan laifin da Bala ya yi har da zagin ɗaya daga cikin ma'aikatanmu, abin da kuma ya sake dagula case ɗin zargin cutar HIV da ake yi wa Alhaji Idi Naira. Yanzu haka shi ma Idi ya kawo Malam Shehu wurinmu, a kan zargin yana ɓa ta masa suna da wannan cutar." Ajiyar zuciya Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu za mu iya ganin Bala Wanzan ɗin?"
"Gaskiya sai dai zuwa gobe idan Allah Ya kai mu." Ɗansandan ya furta.
Babu yadda suka iya haka suka wuce gida, sai dai kaso talatin a cikin ɗari na damuwar Baba Sale ta ragu, saboda ya ji an ce Alhaji Idi Naira ya yi ƙarar Malam Shehu zai ɓata masa suna.
Mai Yasin tun da ya saka 'Yar gwal a idonsa soyayyarta ta dawo masa sabuwa fil a ransa, haka a ɓangare ɗaya kishinta ya mamaye shi, yana jin tsanar Ɗanladi a ransa don dai kawai yana shakkarsa ne. Yana daga ɗakinsa ya hango ta, ta nufi banɗaki da buta a hannu shi ma ya yi zaraf ya ɗauki buta ya rufa mata baya. Tana shiga banɗaki za ta turo ƙofa ta ji mutum yana ƙoƙarin turowa, suna haɗa ido ta saki murmushi irin na 'yan bariki ta ce.
"Mai Yasin namu, ashe a wannan lungun ka lafe?"
Mai Yasin ya riƙo hannunta ya ce, "Ga ni kuwa kin gani, wai dama 'Yar gwal za ki iya auren wani namijin ba ni ba?"
'Lallai wannan gafalallan tsohon naka wasa ne.' Ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce.
"Ka da ka sake kallona a matsayin matar aure, saboda wannan auren nawa shi da babu duk ɗaya. 'Yar gwal ta auri Ɗanladi ne domin ta yi masa tatsar mai, idan ta kwashe albarkar aljihunsa sai ta ƙara gaba."
"Sai da ke 'Yar kunama!"
Mai Yasin ya yi maganar yana dariya, sannan ya yi ƙasa da murya ya ce. "Yanzu ni ya za ki yi da ni?"
"A'a ka ji da tsohuwar da ka samu, idan fa muka bari suka san alaƙarmu na rantse da Allah ni da kai sai dai mu yi biyu-babu. Kawai mu cigaba da sabgarmu, kowa ya wawuri abin da ya wawura ko a fakaice ma dinga haɗuwa."
Guntun tsaki Mai Yasin ya ja, ya ce. "Wa yake ta wata tsohuwa? Ƙila dai a rashinki yau na waiwayi haƙƙina a wurinta."
'Yar gwal ta saki dariya, sannan ta ce ya yi maza ya tafi don kada wani ya gansu.
Bayan 'Yar gwal ta koma a tsakar gida ta ci karo da Laraba tana 'yar carafke, tana shiga ta ɗebo wankin rigunan mama da ɗan kamfai ta wurga mata a fuska. Tsaminsu haɗe da warin man bilicin ɗin da 'Yar gwal take shafawa ya bigi Laraba, ta ture su tana yamutsa fuska.
"Ke! Wanke mini su yanzu, ina son su fita sosai." Da mamki Laraba take kallon ta.
"Ko ba za ki wanke ba? Kika zubo mini ido irin na marasa tarbiyya kina kallo."
Laraba ta tashi ta ɗaga wani wargajejen ɗan kamfai, sai kawai ta tuntsire da dariya. Tun tana dariya a tsaye har ta tsugunna, ta janyo wata warɓeɓiyar rigar mama ta ɗago ta ta sake kwanciya tana dariya.
"Don uwarki dariya ma za ki yi mini? Wato ni za ki mayar 'yar iska?"
Laraba ta tsagaita da dariya tana ɗan tsuke fuska ta furta. "Kambu... Kada ki sake zagin uwata tana ƙasa, ki zagi kowa nawa ban ta uwata wallahi. Ehe, ba dole mutum ya yi dariya ba wannan ai ya isa na yi hijabi da shi."
"Rashin kunya za ki yi mini?" 'Yar gwal ta ƙarasa gaban Laraba a fusace. Laraba ta juya mata baya tana ɗago ɗankwalinta gaba ta ce.
"Faɗa wa ƙeya ɗankwali ya ba ki amsa 'yan mata."
Laraba tana juyowa 'Yar gwal ta wanke ta da mari, a hargitse Laraba ta ɗago za ta yi magana Ɗanladi ya ƙarasa yana faɗin.
"Kin yi mini daidai sanyin zuciyata, wato har yanzu kina nan da iskancinki ko Laraba? Maza wuce ki kwashe su ki wanke kada ranki ya ɓaci." Idon Laraba ya yi ja saboda ɓacin rai, ta harari 'Yar gwal a hankali ta ce.
"Allah Ya isa ban yafe..."
Tun ba ta gama magana ba, kamar haɗin baki Ɗanladi da 'Yar gwal suka make bakinta, nan take bakin ya fashe amma a dole ta kwashe kayan, ta fara wanki saboda yadda Ɗanladi ya ciro belt zai zane ta da shi. Sai da ta yi wa kayan ruwa kusan huɗu kowanne 'Yar gwal tana cewa bai wanku ba, sai a na biyar sannan suka bar Laraba ta fara shanya a lokacin har an fara kiran sallar isha'i.
Jin shirun Laraba ya yi yawa ya sa Inno ta fito daga sashenta, tana zuwa harabar ta ci karo da ita tana shanyar kaya su Ɗanladi suna tsaye a kanta.
"Laraba me kike yi haka da daren nan?"
Murya tana rawa Laraba ta ce, "Wanki."
Inno ta ƙanƙance ido ta ce, "Mene ne wannan kamar ɗan diras? Ke wuce ciki mu je."
Da sauri Laraba ta saki na hannunta ta wuce ciki, Inno ta dubi Ɗanladi rai a ɓace ta ce.
"Ba baiwa aka sayo muku ba, tun da ba ka da mutumci haka matarka ma ba ta gaji arziki ba wallahi ba za ku mori Laraba. Mun kwana a gida ɗaya, amma ban da mutumci da za ku zo ku gaishe ni." Inno ta wuce sashenta a zafafe.
Ran Laraba ya ɓaci sosai, ita kanta ta san a banza ma tana dafa mutum da ruwan jikinsa har ya nuna, ballantana sun taɓo ta da kansu. Don haka ta ci alwashin yadda suka azabtar da ita sai ta rama.
Tun da dare ya fara yi Laraba ta fara zarya, tana saka da warwarar abin da za ta aikata, tana wucewa ta ga 'Yar gwal a ƙofar ɗaki tana dama kunun gyaɗa. Da sauri ta faɗa ɗakin Inno, a can drower madubi ta buɗe ta ciro wani maganin hawan jinin Inno, mai saka bacci ta ɓallo guda takwas. A ƙa'ida Inno ɗaya take sha a wuni guda, kuma a hakan ma bacci yake saka ta sosai. Bayan jininta ya sauka ne aka sauya mata wani, don haka ta daina shansa. A cikin ƙaramar farar leda ta zuba su ta ɗebi ruwa kaɗan ta zuba, sai da ya narke sannan ta fita cikin sa'a kuwa ta ga 'Yar gwal ta shiga ɗaki. Da sauri ta matse maganin a cikin jug ɗin kunun, ta juya cikin sauri ta bar wurin. Tana laɓe a bakin ƙofar Inno tana leƙe ta ƙofa, ta ji lokacin da 'Yar gwal ta ɗauka ta shiga ɗaki. Zuciyar Laraba ƙal da haye katifa ta kwanta, tana shirya irin muguntar da za ta yi musu. A fili ta saki dariya, Inno ta wurga mata harara sannan ta ɗauki furar Mai Yasin ta nufi ɗakinsa.
Saboda Laraba ta taki mugunta haka ta zauna tunkur, har kusan ƙarfe ɗayan dare. Sai da ta fito cikin sanɗa zuwa ƙofar ɗakin Mai Yasin, ta kasa kunne ta ji munsharin Inno da Mai yasin sannan ta saɗaɗa ta fice daga sashensu ta isa ɗakin Ɗanladi. A yadda ta fahimta sun jima da yin bacci, don lokacin da ta ɗaga labulen ɗakin a ƙasa ta gansu sun ɓingire suna bacci, 'Yar gwal tana jingine da bango da kofin kunnu a hannunta. Sai da Laraba ta saka ɗankwali ta rufe fuskarta, sannan ta ɗauki sauran kunun ta juye mata a fuskar. Wani tunani ne ya faɗo mata ta fita da sauri, ta ɗauko jarkar ruwa irin ta 'yan-ga-ruwa ta tuttule musu ruwan gabaɗaya a ɗakin. Ta janyo galan ɗin man gyaɗarsu ta sheƙa a ƙafafuwan 'Yar gwala da Ɗanladi, ta kai jarkar man ta saƙala mata a hannu. A hankali ta lalallaɓa ta ja ƙafar Ɗabladi sai ta ji ya tafi yaraf, daga shi da ma sai gajeren wando da singlet. Ta ɗauko ƙaton omonsu ta zazzage masa a jiki zuwa fuska, har ta je za ta fita ta hango belt ɗinsa da sauri ta ɗauka ta fara zabga musu ɗaya bayan ɗaya. Sai da ta ga sun fara motsi sannan ta fice daga ɗakin da sauri, ta nufi ɗakin Inno. Tana zuwa ta shige bargo ta kwanta tana dariyar ƙeta, babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita.
Mai Yasin tun da ya sha fura suna hira da Inno ya ga bacci ya ɗauke ta, bai tashe ba don shi ma ba son tafiyarta ɗakinta yake ba. Yana gama shan furar babu jimawa shi ma bacci ya ɗauke shi, ba shi ya farka ba sai kusan uku saura na dare. Inno cikin bacci ta fara jin alamun ana lalubar mamanta, da yake bacci ya sha kanta cikin magagi ta ce.
"Laraba wani wulaƙanci ne kike ji da shi haka?"
Shiru Mai Yasin ya yi ya ci gaba da sabgar gabansa, Inno ta gyara kwanciyarta jin har lokacin ba a daina lalubarta ba, kuma har lokacin idonta a rufe yake da sauran bacci a kanta ta furta.
"Laraba zan ci mutumcinki fa."
Mai Yasin ya kashe murya, shi a dole yana son lallamar Inno don kar ta ba shi matsala ya ce, "Wannan Ɗanlami ne ba Laraba Innota." Firgigit Inno ta yi ta ware idonta, a rikice ta ce. "Malam mene ne haka?" Mai Yasin ya kashe mata ido ɗaya ya ce, "Haba Innoniyata, kamar wata 'yar sha uku duk kin firgice. Sharuɗɗan aure ne fa nake son cikawa." Inno tana shirin ture Mai Yasin ya murɗe 'yan hannuwanta, ta yi mamaki matuƙa yadda ta ji ta kasa kataɓus. Don ba ta taɓa tsammanin yana da ƙwari haka ba, Inno babu yadda ta iya haka ta zubawa sarautar Allah ido. Tun tana tsine wa Mai Yasin a zuciyarta har ta fito fili, don shi da ita sun yi yarjejeniyar auren ɗauko mini buta suka yi.
In Shaa Allahu wannan shi ne shafi na biyun ƙarshe, gobe zan gama free pages.
Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
*GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd
Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻
SHAFI NA SHA UKU
Inno har gari ya waye ban da hawaye babu abin da take yi, da ta kalli Mai Yasin ban da kallon tsana babu abin da yake wurga masa. Shi kuma Mai Yasin ban da juyi a katifa babu abin da yake yi, saboda wani bacci da ya samu mai cike da kwanciyar hankali. Jin shasshekar kukan Inno ce ta farkar da shi, ya ɗago cike da shauƙi ya ce.
"Innota! Haba Innota, me ya sa kike son ɗaga mini hankali da farar safiya haka? Maimakon ki zo na ninke ki a bargo, mu cigaba da baccin cikar fariciki amma sai ki ɓa ta ranki a banza. Ko me na yi miki ai soyayya ce, haba Innaniyota!" Inno ta share hawaye, a hankali Mai Yasin ya dinga fasa mata kai yana yabonta tare da nuna mata zallar soyayya. Saboda ya lura da abin da Inno ta fi so, ya kuma fi saurin sace zuciyarta da shi. Nan take ta saki jikinta, sannan ta miƙe za ta fita da sauri ya ce.
"Inno me za ki fita ki yi, kina fama da kanki?"
Inno ta jingina da jikin ƙofa ta ce, "Abin kari zan haɗa mana..."
"Allah Ya sawaƙe ki fita ki haɗa kayan abinci, da kanki kina fama da ɗanyan jiki."
Murmushi Inno ta saki har cikin ranta ta ji daɗin kulawar da yake ba ta.
"Bari ki ga na je wurin Sule mai shayi, na kaso mana dubu biyar ɗin nan."
Da sauri Inno ta ce, "Malam dubu biyar fa?"
Cike da son nuna burga Malam Ya ce, "Dubu biyar ɗin banza, ni duk yawan kuɗi ba kin fiye mini su ba Innota." Kan Inno ya ƙara girma, za ta fara magana wayar ta ta fara ringing. Malam ne ya miƙa mata, sai da ta ɗauka ta kai kunnenta sannan ta gane muryar aminiyarta ce, kasancewar sabuwar wayar da Fadil ya sauya mata, ba a iya saving da shaidar mota ko jirgi da a baya ake yi mata.
"Assalamu Alaikum, Hajiya Goggo barka da safiya."
Daga can ɓangaren Goggo ta ce, "Wa alaikissalam, barka dai amarsu. Inno ga mu nan a tasha yanzu motarmu za ta taso."
Cike da farinciki Inno ta ce, "Kai amma dai gaskiya kin yi mini bazata, Allah Ya kawo mini ke lafiya."
Goggo ta amsa da Amin sannan ta furta, "To agaida mana angonmu kafin mu zo, don na ji muryarki ta sauya amarci ya karɓe ki tsohuwar nan."
Inno da Goggo suka saki dariya lokaci ɗaya, daga haka suka yi sallama. Ba tun yau ba Mai Yasin yake jin labarin Goggo a wurin Inno, a lokacin aurensu ma ta so zuwa wani jikanta ya rasu don haka ta ɗaga zuwan sai daga ba ya.
Tun bayan fitar Laraba sama-sama suka dinga yunƙurin buɗe idonsu, amma fatar idanunsu ta yi wani irin nauyi don haka suka gagara buɗewa. Sai dai wasu abubuwan da suka faru gani suke yi kamar a cikin mafarki ne. Ɗanladi da 'Yar gwal ba su suka farka ba, sai kusan ƙarfe tara na safe. Ɗanladi ne ya fara farkawa ya ji jikinsa duk ya yi tsami, a hankali ya buɗe idonsa ya ci karo da ɗakin ya yi jaga-jaga. Ransa ne ya ɓaci da ya ci karo da mai ya yi luntsum a tsakar ɗakin, ga jarkar man a hannun 'Yar gwal ta yi share-share a ƙasa tana munshari. A fusace ya ƙarasa wurin da take yashe, ya tsinka mata mari wanda ya sa ta miƙe tsaye a gigice.
"Tsabar iskanci dama ba ki daina shaye-shayen da na hana ki ba? Dubi irin rashin mutumcin da kika yi mana?"
Da mamaki 'Yar gwal take bin jikinta da ɗakin da kallo, ta dafe kumatu ta ce. "Ni ka mara?"
A harzuƙe Ɗanlami ya ce, "An mare ki ko za ki rama? Da yake har lokacin maganin bai gama sakin ta, ta yi luuu da idanu ta furta. "Wallahi ba ka mari banza ba sai na rama."
"Ashe kuwa zan yi miki ɓarin makauniya, tsabar rashin mutumci in saka sama da dubu goma sha na sayi jarkar mai ki rubar a ƙasa. Wallahi yau sai kin gane ke ƙaramar ƙwaya kike sha." A zabure 'Yar gwal ta miƙe tsaye tana kaɗa ƙugu ta ce, "Ƙwayar ma ai mataki-mataki ce, billahillazi sai na nuna maka ko a gidan giya akwai babba. Kai ba wani shege fa." Daga haka ta cakumi wuyan Ɗanladi, ganin haka ya sake ɓa ta ransa don haka ya shiga kai mata duka ita ma tana ramawa. Kasancewar ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba, ya sa 'Yar gwal ta fara laushi. Wannan ya sa, ta ɗauki wani burugali a bayan ƙofa ta ranƙwala masa a goshi, nan take goshinsa ya yi wani tsororo ya kumbure suntum. Azaba ta sa Ɗanladi ya kai mata naushi a ba ki, sai ga bakin 'Yar gwal ya fashe har haƙorinta ɗaya na gaba ya faɗo. Kafin wani lokaci tuni bakin ya kumbure sai sheƙi yake yi. Sai da suka jigatu don kansu sannan suka faɗi gefe, ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba. 'Yar gwal ta fara tattara kayanta tana kuka, hakan ya sa jikin Ɗanladi ya yi sanyi. Ya tsugunna a gefenta cikin tattausan lafazi ya furta. "Me kike yi haka 'Yar gwal?"
Ba ta tanka masa ba, ta cika akwatinta, ta fizgi mayafi ko wanke fuskarta ba ta yi ba saboda ɓacin rai za ta fita. Da sauri ya janyo ta, ta faɗo jikinsa ya ce. "Haba 'Yar gwal, don Allah ki yi haƙuri kin san dai ba zan iya rabuwa da ke ba. Wallahi ɓacin ran abin da kika yi mini ne ya sa haka, ke ma kin san ba ki kyauta ba." Har a ranta ta ji daɗi saboda ita ma dama ba ta yi niyyar tafiyar ba, ta yi hakan ne don ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Ta janye hannunsa fuska a haɗe ta ce, "To ai gara na ba ka wuri tun da hakan shi ya fiye maka, da ka dinga tuhuma ta a kan abin da ba ni da masaniya."
Shiru ya yi yana nazari, don shi ma a iya saninsa dai 'Yar gwal ta daɗe ba ta shaye-shaye, kuma ko ta bugu ba ta irin wannan ɓarnar.
"Yar gwal jiya bayan mun sha kunu me ya faru?"
Ba ta ba shi amsa ba, ta taɓe baki. Wani irin tsoro ya kama shi, don ya ga jikinsa da na 'Yar gwal duk sun yi ruɗu-ruɗu.
"An ya ɗakin nan babu aljanu kuwa?"
Ya yi tambayar cikinsa yana kaɗawa, 'Yar gwal ta ce, "Ah to gidanku ne dai, ka fi kowa sanin yadda yake ai." Ɗaladi ya jima yana rarrashin 'Yar gwal, daga ƙarshe dai ta haƙura. Shi da kansa ya shiga gyaran ɗakin, don 'Yar gwal cewa ta yi ba za ta taɓa komai ba.
Washegari tun da farar safiya Zuly matashin kai ta dokowa Yaya Inu waya, cike da kissa take yi masa kalaman tausasawa domin tana son sake karɓar kuɗi a wurinsa. Yaya Inu duk damuwar da yake ciki lokaci ɗaya ta yaye, ya miƙe a hankali ya saka wata jallabiyyarsa ya fice. Ƙofar gidansu Zuly ya ƙarasa, ya kai mata dubu goma sha biyar kamar yadda ta buƙata. Ta kashe masa ido ta ce, "Yanzu fa nan da awa biyu zuwa uku na zama taka. A gaskiya duk macen da ta yi sa'ar samunka ta yi dacen miji." Yaya Inu ya saki murmushi ya ce, "Waɗannan kalaman na ki suna sake birkita ni Zulyta. Yanzu dai bari na wuce gida na sallami waɗancan mutanen, na fara shirin tafiya ɗaurin aure." Zuly ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Tun yanzu baby?" Yaya Inu cikin tausasa lafazi ya ce, "Sai yadda kika ce." Zuly ta yi wani far da ido ta ce.
"Ni na isa, Allah Ya taimake ka aje ayi yadda ya dace. Don na fi son mijina ya zama adali."
Yaya Inu sai da ya yi da gaske sannan ya tafi daga wurin Zuly, yana tafiya ta wuce gidan Hajiya zuma mai magungunan mata. Ta kai mata dubu biyar cikon kuɗin magungunan da take bin ta. Saboda ba ƙaramin haɗi ta yi mata ba, don ta ci alwashin kafin ta fito daga gidan Yaya Inu sai ta tatike shi tsaf, domin ba da niyyar zama ta je ba. Don haka ta je aka saka mata inplan, don ma kada ta ɗauki ciki.
Tun da hantsi ya yi suka ga shiru Mai gari bai fito ba, Azeema ce ta shiga ɗakin saboda dama girkinta ne. A zaune ta samu Mai gari ya haɗa kai da gwiwa yana hawaye, hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba. Jiki a sanyaye ta zauna kusa da shi ta ce, "Ranka shi daɗe lafiya? Me yake faruwa da kai a farar safiyar nan kake kuka?"
Mai gari ya ja majina yana sharce hawaye, ya saka hannu ya dafe saitin zuciyarsa da yake bugawa da sauri ya ce. "Azeem ina cikin wani yanayi mara musaltuwa, zuciyata tana cike da muradin da ban san lissafin da mutane za su lissafa a kaina ba."
Azeema ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Tun shekaran jiya na fara lura da sauyinka ranka shi daɗe, amma na yi maka tambayar duniya ka ce mini babu komai. Mene ne a zuciyarka da yake damunka?"
Kai tsaye Mai gari ya ce, "So ne, so ne yake nuƙurƙusar zuciyata kuma ban san a lokacin da ya yi mini kamun kazar kuku ba. Yanzu haka na takure kaina a ɗakina ne, saboda kada na fita fada zuciyata ta fisge ta zuwa gidansu."
"Wace ce ita?"
Ta wurga masa tambaya.
"Laraba ce Azeema, wallahi zuciyata har wani tartsatsi take a kanta."
A razane Azeema ta ce, "Laraba tsidigu dai? Eh lallai dole ka ce jarabta. Ranka shi daɗe ko dai mafarki kika yi, ka rasa wacce za ka so sai waccan sheɗaniya hatsabibiyar yarinyar Lara..." Ba ta gama magana ba, Mai gari ya gwaɓe mata ba ki ya fashe.
"Kada ki sake danga ta mini Laraba da shaiɗanu, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci."
Tsoro ne ya kama Azeema, jikinta a sanyaye ta fice daga ɗakin domin ba ta tantama akwai ciwon da ya samu mijin nasu.
Kamar yadda suka tsayar da magana, a washegari Baba Ibrahim da Baba Sale har da Ɗan Bishir suka sake komawa police station.
"Alhaji na yi mamaki ƙwarai da na ji an ce case ɗin naka ne? Me ya yi zafi haka?" Baba Ibrahim ya tambayi Alhaji Idi Naira.
Alhaji ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Wani zance ne ya fara yawo a cikin garin nan, wai ina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki Dr, ni kuma a iya sanina ba ni da ita. Da na bi diddigin maganar, sai aka ce an samo zancen daga wurin Malam Shehu, don haka na kawo shi ƙara. Sai bayan na zo na ci karo da Bala wanzan a nan , ni kuma ba zan laminta ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 35