Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fita, suna jin tsananin tsanar Shukura a ransu. Saboda tun da suka yi wayo, ba su taɓa ganin mahaifiyarsu tana kuka saboda ɓacin ran mahaifinsu ba. Alhaji Gambo aminin Daddy ne, garinsu ɗaya da shi. Kuma duk gwagwarmayar rayuwa kusan tare suka yi, kowa ya san sirrin kowa. Kuma duka su biyun suna ba wa junansu shawarwari, haka idan wata matsala ta iyali ce. Matar wannan tana iya kiran wannan ta yi masa ƙorafi domin a gyara. Hajiya Karima kiransa ta yi, bayan sun gaisa take sanar da shi duk abin da ya faru. Ko kaɗan bai ji daɗi ba, don dama tun da Alhaji ya ɗauko maganar auren Shukura, da ya bincika ya ji yanayin tarbiyyar gidansu Shukura sam auren bai kwanta masa ba. Don kafin a yi ya sha ba shi shawara, a kan ya haƙura da ita ya nemi wata. Haƙuri ya ba ta sosai, sannan ya ce ta bari zuwa dare zai zo gidan domin su tattauna gabaɗaya. Tun da suka gama Alhaji Gambo ya kira Daddy, ya ce masa zai shigo bayan sallar magriba. A yanayin muryar Daddy da ya ji sam kamar bai yi murna da zuwansa ba, ya yi mamaki matuƙa. Saboda koda a fushi yake bai cika nuna masa fushinsa ba. Bayan sallar Isha'i, Alhaji Gambo ne ya yi fakin a ƙofar gidan Daddy. Waya ya ciro ya kira shi ya sanar da shi, babu jimawa Daddy ya fita suka suka gaisa babu yabo babu fallasa sannan suka shiga. A falonsa na saukar baƙi suka zauna, Alhaji Gambo ya dube shi ya ce. "Wata magana ce fa tafe da ni, ɗazu Hajiya Karima ta kira ni. Amma kafin nan ka kira ta tukunna sai mu tatattauma gabaɗaya." Nan take Daddy ya haɗe fuska ya ce. "Dole sai ta zo? Duk abin da za mu faɗa mu yi mana." Shiru Alhaji Gambo ya yi, ya ɗan haɗe fuska ya ce. "Ka ga malam ka kira ta mu yi magana, ka san ni dai ba baƙon gidan nan ba ne. Idan ba za ka kira ta ba, zan leƙa na ce su Haidar su yi mata magana." Guntun tsaki Daddy ya yi ya fice, bayan wani lokaci sai ga shi sun dawo yana gaba Hajiya Karima tana biye da shi. Gaisawa suka fara yi, sannan Alhaji Gambo ya wassafa duk maganar da suka yi da ita, sannan ya ɗora da cewa. "A gaskiya ka ba ni mamaki Alhaji Umaru, yanzu kai ko wani ne ka ji zai yi wa iyalinsa haka ba za ka tsawatar masa ba?" "Dakata Gambo don Allah, wannan sabgar iyalina ce. Ban ce ka tsoma bakinka a ciki ba, wallahi sai ta fitar da kajin nan tun da Shukura ba ta son warinsu. Idan kuma rabuwarmu ta zaɓa, a yanzu sai na rubuta mata takardarta ta kama gabanta." Yana gama maganar ya wuce fuu har zai fita, sai ya sake waigowa ya ce. "Kuma daga yau babu kai babu sake shiga duk wata magana ta iyalina, kai ma idan har ka ce za ka bi wani ra'ayin ba na Shukura ba, a shirye nake da na datse duk wata alaƙa da ke tsakanina da kai." Daga haka ya saka kai ya fice. Daga Mommy har Alhaji Gambo jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, saboda ɓacin rai sai kawai ta fashe da kuka. GIDAN HAFIZ "Za ki buɗe baki ki yi mini magana, ko sai ranki ya ɓaci?" Hafiz ya buga wa Amina tsawa a zafafe, hawaye ta shiga yi baki yana rawa ta ce. "Wallahi... ban... san yadda aka yi ba, wallahi ban san komai game da wannan layar ba." Furzar da iska mai zafi Hafiz ya yi, zuciyarsa tana tafasa ya matsa kusa da ita kamar zai tsinka mata mari. Da sauri Amina ta ja da baya cikin matsanaacin tsoro, don ta gama saddaƙar da Hafiz hannu zai kai jikinta. Rai a ɓace ya nuna ta da yatsa ya ce. "Uwargidana, kuma uwar 'ya'ya ko hanyar gidan malamai ba ta sani ba, haka kawai ina zamana lafiya da matata za ki haukata mini ita. Shi ya sa kullum take yin abu kamar na mai shafar aljanu, ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni. Wallahi idan na sake ganin makamancin wannan shirmen sai ranki ya yi mugun ɓaci. Saboda mugun hali ki zo ki samu mace a ɗakinta kina ƙoƙarin illatata, ba zan juri ki zo ki hargitsa mini gida ba." Hafiz ya juya ya fita, kai tsaye kicin ya shiga ya ɗauko ashana ya fita da layar ya ƙona a waje. Duk abin da yake faruwa Bikisu tana daga ɗaki tana ji, zuciyarta fes don haka ta cigaba da harkokinta hankali kwance. Tun daga wannan ranar Bilkisu ta warware tas, ta daina duk wani makircin nesanta kanta da Hafiz. Wannan ya sake tabbatar wa da Hafiz zarginsa na Amina ce ta yi wa Bilkisu asiri, dalilin haka ya ƙara tsaurara tsattsamar alaƙa tsakaninsa da Amina. Suka koma irin zaman cin kunamar ƙadangare, don Amina wani haushin Hafiz take ji a kan abin da ya yi mata. Shi ma kuma haushinta yake ji, don haka ya koma kwanan falo. A kullum idan a ɗakinta yake zai ɗauko filo ya fito falo ya kwanta, saboda idan ya kwanta a kan gadon ma sai dai Amina ta juya masa baya. A wannan kwanakin Bilkisu sai nannan take da Hafiz kamar ta haɗiye shi, haka shi ma yake ba ta kulawa; saboda yadda ya ga ta saki jiki da shi saɓanin tun lokacin da ya auri Amina. Watarana Hafiz yana ɗakin Amina, har ya yi shirin zuwa kasuwa sai ya shiga ɗakin Bilkisu don ya yi mata sallama. Yana shiga bisa tsautsayi hannunta da manja ya kife masa a gaban riga, a kan dole ya shiga uwar ɗakinta ya cire kayan jikinsa ya ɗaura towel. Da yake Bilkisu ta ɗora ruwan wanka, sai ta ce bari ta juye masa ya sake yin wanka tun da duk jikinsa ya ɓaci. Sai da Bilkisu ta shiga uwar ɗaki ta ɗauro zani, sannan ta je ta juye masa ruwan a banɗaki. Hafiz ne ya shiga banɗaki cikin sauri, saboda ya yi rana bai fita da wuri ba. Bilkisu tana ganin haka ta yi zaraf ta fito tsakar gida, sai da ta je bakin ƙofar ɗakin Amina ta yi ƙasa da murya yadda Hafiz ba zai ji ba ta ce. "Ban da abin Abban Sayyid ka ce ba ka gajiya da ni saboda Allah, tun da dai ba kwanana ba ne ai sai ka bari sai ka dawo nan ɗin tun da ba guduwa zan yi ba. Ga shi haka kawai za ka saka ni jiƙa kaina ban shirya ba." Da ta tabbatar da Amina ta ji abin da ta faɗa, sai ta ce. "Koda yake bari na zo na taya ka, tun da shi ma sunna ne." Ta nufi ƙofar banɗakin tana gimtse dariyar mugunta, tana zuwa cikin sanɗa ta tsaya a ƙofar banɗakin. Saboda ta san ko kaɗan Hafiz ba zai bari ta shiga su yi wanka tare ba, tun da ba ranar girkinta ba ne. Tana jin motsin zai fito ta ce. "Idan ka gama Abban Sayyid ba ni bokitin ni ma zan yi wanka."Ajiye mata ya yi, sai ya wuce ya shiga ɗakin Amina ya sauya kaya ba tare da ya tanka mata ba. Tana ganin ya saka wasu kayan ya fita, ta shiga uwar ɗaki ta fashe da kuka. Sai da ta yi mai isarta sannan ta share hawayenta, ta kwanta tana jin gabaɗaya zaman gidan ya ishe ta. Uwa-uba ga laulayin da take fama da shi, don a wannan lokacin ko abincin kirki ba ta ci. Bilkisu tana fitowa daga wanka ta shige ɗaki, sai da ta shirya tsaf sannan ta ɗauko wayarta ta kira Lami mai wanki. Tana ji an ɗauka ta yi ƙasa da murya ta ce. "Yawwa Lami na haɗa kayan wankin namu, ki aiko yaro ya zo ya ɗauka. Da nawa da na yara gabaɗaya set goma sha biyar ne, yawwa akwai kuma na Abban Sayyid za ki gansu daban. Su kuma sai ki ba wa Babansu Bala (Mijin Lami) ya wanke ya goge. Idan an gama sai a yi mini lissafi zan bayar da kuɗin." Amsa mata Lami ta yi sannan ta katse wayar, da sauri ta matsa bakin ƙofa. Sai ta latsa ainahin ringing ɗin wayarta ta ware volum, sai da ya yi na ɗan sakanni sannan ta kashe. Sai ta kai shi kunne a zuwan kiranta aka yi ta ce. "Hello Abban Sayyid, ka yi mantuwa ne?" Sai ta yi shiru kamar wacce ake yi wa magana ta sake cewa. "Kai Abban Sayyid yanzu bayan kuɗin makarantar yara da aka ƙara ga hidimar gida har da wanki? To shi kenan, bari na karɓo na wajen nata, Allah Ya ƙara buɗi Habibi." Sai ta yi ƙasa da murya kamar mai kukan gaske ta ce. "Haƙiƙa samun miji kamarka sai an tona Zauji, Allah Ya kula mini da kai." Daga haka sai Bilkisu ta ƙarasa ƙofar ɗakin Amina ta yi sallama, jin ta amsa sai ta ce. "Abban Sayyid ya ce ki haɗo kayansa na ɗakinki za a kai wanki." A sanyaye Amina ta amsa mata, sannan ta shiga ɗaki ta haɗo kayan wankin Hafiz ta kawo mata. Sai da ta karɓa ta ɗan yamutsa fuska ta ce. "Ni kam ko ba kya jin daɗi ne Auntyn yara? Na ga tun safe kina ɗaki." Murmushin yaƙe Amina ta yi ta ce. "Ba na jin daɗi ne shi ya sa." Bilkisu ta rausayar da kai alamun tausayi ta ce. "Ayya sannu, dama kin san fa sai an rabu ake jin daɗin jiki. Ni na yi mamaki ma, da Abban Sayyid yake fita ba tare da ya yi miki share-sharen ɗaki ba, don lokacin cikin Sayyid hatta moping sai ya yi mini yake fita." Wani zafi Amina ta ji a ranta, tana ayyana wato ita da yake ya daina sonta ko gyaran gado bai taɓa yi mata ba. Bilkisu ta saci kallon Amina a fakaice sannan ta ce. "Kodayake bari na dinga rage miki wasu ayyukan, ai ban san ba ki da lafiya ba." Tana faɗar haka ta fice, sannan ta ɗebo kayan wankinta ta fito da su tsakar gida ta ɗauki waya ta kara a kunne bayan wani lokaci ta ce. "Hello, Abban Sayyid." Shiru ta yi sai ta sake cewa. "Ashe Amina ba ta jin daɗi tun safe, na ce ko na karɓi kayanta a haɗa da namu a kai wankin? Tun da ka ga kayana da na su Sayyada ba su da yawa." A wannan karon ma shiru ta sake yi, sai bayan wani lokaci tace. "A'a don girman Allah ka yi haƙuri, ya za a yi ka ce ka rantse ba za a haɗa da nata ba. Don Allah kada ka yi haka ba za ta ji daɗi..." "Don Allah ki daina yi masa magiya Aunty, tun da bai yi niyya ba ai shi kenan. Wanki ai ba zai kashe ni ba." Amina ta furta cikin zafin zuciya, don a wannan karon ta gagara riƙe ɓacin ranta. Girgiza kai Bilkisu ta yi ta ce. "Haba ta ina za a yi haka, to ai kuwa nawa ma sai dai a bar shi gaskiya." Jim ta yi kamar mai sauraren abin da yake faɗa, sai ta ce. "To shi kenan, ka yi haƙuri zan bayar da su. Wai dama don kada ta ji babu daɗi ne ya sa na yi maganar, amma tun da maganar kayan na ta ya ɓata maka rai ka yi haƙuri." Bilkisu tana sauke wayar sai ga Habibu ɗan gidan Lami ya yi sallama, kayanta da na Hafiz ta haɗa ta ƙulle ta ɗaura masa a kansa. Amina tana shiga ɗaki, ta ɗauko hijabinta ta zura sannan ta rufe ƙofarta ta fice ko sallama ba ta yi wa Bilkisu ba. Tana jin zuciyarta na zafi, don yadda ta fita daga gidan ta ci alwashin ba za ta koma ba sai dai Hafiz ya kai mata takardar sakinta. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA TARA ALL NATURAL PRODUCT💃🏻 Tsumi Tsumin tighten Tsumin Sanyi Tsumin basir Tsumin 3in1 Kazar Amare yan mata. Kazar Amare zawarawa. Kazar Masu haihuwa. Kazar 3in1 Kazar uwargida ko amarya da suke son burge oga. Gumbar dabino. Gumbar kwakwa. Gumbar Madara. Garin dahuwar kaza. Garin dahuwar ciccibi. Garin dahuwar hanta. Garin dahuwar kwai. Garin dahuwar kifi. Garin hakin maye na sha da Madara ko nono. Ingantaccen tsumin maganin sanyi, wanda aka samo daga masunta masu kamun kifi,bayan maganin infection yana magance sanyin da aka sha a ruwa ko a tiles ko irin sanyin nan mai kumbura jikin mutum. Bugu da kari ana iya ba yara kanana masu fama da mura ko tari, haka akan dace idan yaro yana fitsarin kwance aka bashi in sha Allah yana dainawa. 09065730652 A tuntuɓi lambarmu. *** Bilkisu tana kwance a ɗaki ta ji fitar Amina, da sauri ta fito tsakar gida don ta sake tabbatar da zarginta. Ƙofarta ta gani a garƙame da kwaɗo, kuma ta san duk rashin daɗin zaman da suke yi da ita idan za ta fita sai ta yi mata sallama. Wannan ya sa ta sake tabbatar da zanginta na Amina yaji ta yi. Cikin tsananin farin ciki ta koma ɗaki ta haye kan gado, wayar Hafiz ta kira don ta bigi cikinsa tana jin ya ɗauka ta ce. "Yawwa na manta ban tamabaye ka ba, me za a dafa ne. Saboda na ga Auntyn yara ta yi bacci, kuma ka ga ba a tashe ta ba." Har cikin zuciyarsa ya ji daɗi, musamman da a kullum yake sake ganin sauƙin kan Bilkisu. Cike da farinciki ya ce. "Da ma kafin na fita na ga yanayin jikinta nata kamar ba ƙwari, ko doya da miya ma kika yi ta isa." Murmushi Bilkisu ta yi ta ce. "An gama ranka shi daɗe." Har ta kashe sai ta yi farat ta sake kira, yana ɗauka ta ce. "Na ce dama ɗazu na bayar da wankin kayanka da namu, ina jin zuwa gobe ma za kawo su." Ɗan jim Hafiz ya yi, kafin ya yi magana ta ce. "Dama bayan fitarka Yaya ya turo mini kuɗi, ka san ya sayar da gonarsa kwanaki." Sai a lokacin Hafiz ya ce. "Ma Shaa Allah, godiya nake Habibty." Lumshe ido ta yi, tana jin soyayyar Hafiz har cikin ranta. Sai da suka yi sallama a fili ta ce. "Haka kawai ina zaune ƙalau da mijina wata shegiya ta zo ta addabi rayuwata. 'Yan iska macizai da ba sa ramin kansu, don bala'i kowacce yarinya da ta yi kwantai sai dai ta ce mijin wata ne zaɓinta. In Shaa Allahu yadda kika fita kin fita kenan, ban da neman masifa da fitina ki je ki nemi naki mijin mana." Bilkisu ta ƙarasa maganar cikin ƙwafa. AMINA Amina tana tafe a hanya tana hawaye, bakin titi ta ƙarasa ta tari adaidaita sahu ta wuce unguwarsu. Tuno halin mahaifinta da ta yi ya sa ta yi saurin daidaita fuskarta, don ta san idan har ya ji dalilin zuwanta gida sai ranta ya ɓaci. Don haka tana shiga gidan ta saki fuskarta kamar babu wani abu da yake damunta, sai bayan sun gama gaisawa mahaifiyarta ta ce. "Aminatu ke ce da ranar nan haka?" Gyaɗa kai Amina ta yi, ta ce. "Ai zuwa na yi na kwana biyu Umma, saboda ba na iya komai a gidan. Idan na warware sai na koma gida, don wallahi wani lokacin kamar zan faɗi saboda juwa." Shiru mahaifiyarta ta yi sai kuma ta ce. "Yanzu don ba ki da lafiya sai shi kuma Hafiz ɗin ya bar ki ki taho gida?" A ɗan duburburce Amina ta ce, "Na'am, eh shi ya ce na zo." Kallon tsaf mahaifiyarta ta yi mata ta fahimci tana cikin damuwa. Ganin irin kallon da take mata na tuhuma ya sa ta miƙe za ta fita, mahaifiyarta ta ce. "Amina me yake damunki?" Nan take idonta ya ciko da ƙwalla ta fara hawaye, sai da ta share hawayen ta ce. "Umma wai dama haka ake shan wahala? Wallahi ko ruwan shayi na sha ba ya zama." Ta faɗi haka, don a wannan lokacin ba ta son duk wani abu da zai sa a kira Hafiz gidansu har a yi musu sasanci. Ajiyar zuciya mahaifiyarta ta yi ta ce. "Ai dama tun da abu ya zo ga ma'iya sai Allah, marar kunya fita ki ba ni wuri." Amina ta yi murmushi, hira suka cigaba da yi da 'yan'uwanta. Duk sai ta ji damuwar da take ciki ta yaye, kuma wani abu da ya ba ta mamaki yadda ta zage ta ci abinci sosai saɓanin tana gida HAFIZ Sai bayan sallar Isha'i Hafiz ya dawo gida, bai yi mamakin rashin fitowar Amina ta tarbe shi ba. Saboda tun da suka yi faɗa ta daina zuwa taro shi idan ya shigo gidan. Kai tsaye ɗakin Amina ya ƙarasa yana zuwa ya yi turus, saboda ganin ƙwadon da ya yi. Bakin ƙofar Bilkisu ya ƙarasa, ta yi luf kamar wacce ta fara bacci. Sai da ya kira sunanta har sau uku sannan ta tashi tana murtsika ido, a yamutse ta ƙarasa bakin ƙofar ta ce. "Sannu da zuwa." "Yawwa sannu, ya yaran ya kike?" Hafiz ya tambaye ta, amsa masa ta yi ya sake cewa. "Ina Amina ta tafi? Na ga ƙofarta a rufe." Nan take ta sauya fuska cikin alamun mamaki ta ce, "Au wai dama ba ka san ta fita ba?" Ran Hafiz ya fara ɓaci, ganin haka ya sa Bilkis ta cigaba da cewa. "Ai ina jin ko azahar ba a yi ba ta fita, ni kuma dama ba ta yi mini sallama ba. Ka ga ba zan kawo ba ta fita babu izininka ba." Ƙwafa Hafiz ya yi ya ce. "Ya yi mata kyau." Daga haka sai ya wuce uwar ɗakinta, kaya ya sauya ya buƙaci da ta zubo masa abinci. Jikin Bilkisu har rawa yake ta fita cikin kwarkwasa ta haɗa masa kayan abinci ta dire a gabansa. Gani ta yi ya miƙe ya fita, ta yi jim tana nazari sai kuma ta taɓe baki. A can ƙofar gida wayar Amina Hafiz ya kira, har ta katse ba ta ɗauka ba. A hakan ya sake danne zuciyarsa ya sake kiranta, sai a lokacin ya ji ta ɗauka. "Da izinin wa kika fita daga gidana?" Hafiz ya wurga mata tambaya a fusace, cikin ɓacin rai Amina ta ce. "Da ka bi ni ta lallami ma, don ba zan dawo gidanka ba sai dai ka aiko mini takardata. Ka ga sai ka je can ka cigaba da rayuwa da 'yar gwal, tun da kai ba adalin namiji ba ne." A wannan karon zuciyar Hafiz har tafasa take yi, ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Haka kika zaɓa?" Cikin zafin zuciya da ganin Hafiz bai damu da tafiyarta gida ba ta ce. "Eh, ka kawo mini takardata ko na cigaba da samun farinciki a wurin iyayena. A wuni ɗaya da na yi a gidanmu, har na manta da duk wata cusgunawa da kake yi mini. Ka ga sai na yi rayuwa cikin salama da kwanciyar hankali." Hafiz bai tanka mata ba, ya saki ƙwafa haɗe da kashe wayar. Cikin gida ya shiga ya zauna a gaban a binci ya zura masa ido, Bilkisu ta lura da yanayin da yake ciki don haka ta ce. "Abban Sayyid ko wani abu ne yake damunka?" Girgiza mata kai ya yi, ya ɗauki cokali ɗaya na abinci ya saka a baki. Haka kawai ya ji abincin ya yi masa ɗaci, murya a dakushe ya ce. "Ɗauke na ƙoshi." Marairaice murya Bilkisu ta yi ta ce. "Abban Sayyid ko yanzu ban isa na ji damuwarka ba ne? Kyakkyawar fuskar da ke faranta mini zuciya ta alamta mini damuwa ta yi kwance male-male a samanta. Da za ka sanar da ni, wataƙila da sai na samu ƙwarin gwiwar faranta mata har ta manta wani kaso, daga cikin damuwar koda ba zan yaye maka duka ba." Shiru ta ga ya yi, alamar saƙon da take turawa ya fara ringajayar zuciyarsa. Ta matsa kusa fa shi har suna jin numfashin juna, saƙalo hannunsa ta yi cikin nata ta cigaba da cewa. "A da ban san kalar wannan fuskar a jikin surarka ba sadaukina, ba ka saba mini da fushinka ba. Don haka ne ma ganinka a cikin wannan yanayin ya fara azabtar da gangar jiki da ruhina. Don Allah koda za ka yi fushi, ka dinga tuna akwai hallitun da suke zagaye a ƙasan zuciyarka. Ka sani, ni na sani duk duniya idan ka cire su Inna. Nida Amina ne na biyu da ke ƙaunarka, haka kuma ni da ita ne muke durƙushe a ƙarƙashin inuwarka. Don Allah ka sassauta fushinka ko na ji daɗi a raina." Har cikin zuciyarsa yake jin soyayyar Bilikisu, saboda tana da baiwar iya tsara magana. Don haka ya ji kaso casa'in da damuwar da yake ciki ta tafi, ya janyo ta ya manna a ƙirjinsa ya ce. "Sautari idan na shiga wani yanayi, na kan ji ɗaci da tururi a cikin raina. Zuciyata ta kan dugunzuma, har wani lokacin na gagara sarrafa ta. Sai dai samunki a duniyata, yana gusar da dubban abubuwan da ke bazanar nakasta zuciyata. Ina matuƙar ƙaunarki Billyna, Allah Ya yi miki albarka." Cike da so Bilkisu ta sun baci gefen bakinsa ta ce. "Ka gama mini komai a duniya gwarzona." Ɗan sauya fuska ta yi cikin damuwa ta ce. "Amma ban sani ba ko ka samu layi Auntyn yara kuwa? Na kira ta bayan fitarka ba ta ɗauka ba." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Na kira ta, sai dai har yanzu ina mamaki sauyin halin Amina. A da zan iya bugar ƙirji a gaban duniya na yabi kyawun hali da ɗabi'arta, amma a yanzu ta fara ba ni tsoro. Ki ta ya ni da addu'a Allah Ya zaɓa mini abin da ya fi zama alheri." Wani sanyi ta ji a cikin ranta, ta lumshe ido cikin jimamin ƙarya ta ce. "Amin Ya Rabbi, ka san dama wani zubin sai zama ya yi zama ake gane halin mutum. To amma ina ta tafi?" "Gidansu ta tafi." Daga haka Hafiz ya miƙe ya nufi ɗakin yara. Haska su ya yi ɗaya bayan ɗaya, ya gansu suna bacci sannan ya koma ɗaki. Tun a wannan ranar Hafiz ya saka wa zuciyarsa ba zai je gidansu Amina don ya yi bikonta ba, tun da ba faɗa suka yi ba kuma ba wani laifi ya yi mata ba. Duk da yadda yake jin soyayyarta tana addabar zuciyarsa. Haka ita ma ta ci alwashin ba za ta dawo ba, duk da a kullum sai ta ji kewa da soyayyar mijinta. A wannan zaman da suke yi har suka shafe kwana goma a haka, ganin kwanaki suna tafiya ya sa mahaifiyar Amina ta matsa mata da maganar komawa. A ranar ne ta fito ta sanar da su dalilin zuwanta gida, daga mahaifinta har mahaifiyarta

Chapter 7 of 35