sa cikin Mai Yasin ya kaɗa, wani zazzafan gumi ya yanko masa. Ya ƙarasa gaban Yaya Inu ya riƙo hannunsa da ke karkarwa ya ce, "A'a Inusa ka bar mini komai a hannuna, ka san dai kamar yadda na faɗa muku zafin aikina ne ya sa ake kira na da Mai Yasin. To ni zan..."
Kallon da Yaya Inu ya shiga wurga masa ne ya sa shi katse kalamansa, don yadda ya ga yana kallonsa har sai da ya sa shi tsarguwa.
"Ka bar mini komai a hannuna, ni na san irin shige da ficen da nake yi a wurin malamai, don haka zan ji da shi."
Jiki a sanyaye kamar zakaran da ya shuri wuƙa, Mai Yasin ya ja jiki gefe. Yaya Inu ya fice yana muzurai, babu jimawa kowa ya watse.
Ganin duk irin gudun da Mai gari yake fallawa su Mahmud ba su daina bin sa ba, ya sa shi ɓarkewa da kuka yana gudu yana waigensu. Ba shi ya tsaya ba sai da ya ƙarasa tukubar tsiren Mai daban-daban, yana shiga rumfar a guje ya yi bayan su Haladu da ke zaune a kan benci. Zumbur! Suka miƙe, cikin damuwa Sallau ya ce.
"Subhanallah! Ranka shi daɗe lafiya kuwa? Me yake faruwa daga kai sai gajeren wando?" Kafin Mai gari ya bayar da amsa su Mahmud suka ƙarasa cikin runfar, ganinsu ya sa bakin Mai gari ya shiga karkarwa hannu yana rawa ya nuna su ya ce.
"Su... ne, wallahi ba... mutane ba ne. Ku taimaka..."
Bai ƙarasa maganar ba ya yanke jiki ya faɗi, cikin su Mahmud ya sake kaɗawa don Mudassir tuni ya fara hawaye, ya dubi Mahmud ya ce.
"Mahmud ka janyo mana masifa muna zaune ƙalau."
Sai ya sake ɓarkewa da kuka, hawayen da Mahmud yake riƙewa ne ya ɓalle haɗe da wanke fuskarsa lokaci ɗaya. Sun juya za su fita da sauri Mai daban-daban ya danƙo wuyan rigarsu yana faɗin.
"Billahillazi la'ilaha'illahuwa sai kun tsallaka mai gari, kai babu wanda fa zai bar wurin har sai mai gari ya dawo hayyacinsa." Su Mahmud suka yi tsilli-tsilli ƙirjinsu yana bugawa.
"Wallahi a ɗaure su har sai ranka shi daɗe ya dawo hayyacinsa, idan ba haka ba sai sun tsallaka shi, dubi idon munafuka sun yi kama da baƙaƙen mayu. Wai ma ku su waye a garin nan!" Daga ƙarshe Sallau ya wurga musu tambaya.
Daga Mahmud har Mudassir aka rasa mai magana, ba su yi aune ba Mai daban-daban ya fiszo wata ƙatuwar igiyar da yake ɗaure damin itace, shi da Haladu suka shiga ɗaure Mahmud da Mudassir.
"Wallahi mu baƙi ne kuma ɗalibai, don Allah ku kunce mu. Wallahi ba mu yi gadon maita ba."
Madassir ya faɗa murya tana rawa. Babu wanda ya kula shi, sai da suka ɗaure su tsaf sannan suka shiga yayyafa wa Mai gari ruwa.
"Wallahi matuƙar ranka shi daɗe ya mutu gabaɗaya sai mun ƙone ku."
Mai daban-daban ya furta, ganin sun gama juye ruwan buta guda a kan Mai gari ba tare da ya motsa ba. Mahmud da Mudassir kusan lokaci ɗaya suka kallo wutar tukubar naman Mai daban-daban, kamar haɗin baki sai kawai suka ɓarke da kuka; bayan zuciya ta gama raya musu Mai gari zai iya mutuwa tun da sun ga bai motsa ba.
Dukan ƙirjin Mai gari aka fara yi ana shafa masa ruwa a fuska, sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya. Ya buɗe idanunsa a hankali yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya.
"Su waye ku? Mu ne ko kuma su ɗin ne?"
Mai gari ya faɗa yana raba idanu kamar ƙosan sadaka.
"Allah Ya taimake ka Mai daban-daban ne, sannu ya jikin naka?"
Mai daban-daban ya furta yana tallafo Mai gari. Tashi ya yi zaune ya sake kallonsu, sai a lokacin komai ya shiga dawo masa.
"Mai daban-daban ni kaɗai kuka gani, ko kun ga wani jinsin bayan ni?"
Mai gari ya tambaya a firgice.
"Allah Ya taimake ka kai kaɗai ka fara shigowa, sai kuma waɗancen matasan."
Ya faɗa yana nuna masa su Mahmud, da fuskarsu ta kumbure suntum saboda kuka.
A zabure Mai gari ya miƙe jikinsa yana rawa, gudun kada ya sake fita da gudu ya sa su Haladu suka dafe kafaɗunsa.
A madadin Mai gari ya yi musu bayani sai ya fashe da kuka, yana cusa kansa a cikin jinkinsu. Cikin tashin hankali ya ce.
"Wallahi ba mutane ba ne, aljanun Laraba ne daga hukumar kare haƙƙin aljanu ta faɗin duniya." A razane suka dubi su Mahmud, Mai daban-daban ya bugi ƙirjinsa sannan ya zaro wani kwalli a aljihu ya saka a idonsa. Ya kalli su Mahmud na wani lokaci ya ce.
"Waɗannan yaran mutane ne, domin babu wani aljani da ya isa ya yi mini kurari. Sa'a kuka ci na ji an ambaci sunan Laraba da tuni na sheƙa kurwarku ƙiyama." Mahmud ya ƙanƙame Muddasir ƙirjinsa yana bugawa.
"Kai uban me ya kai ku razana Mai gari."
Ya wurga musu tambaya yana zare ido.
"Dama wannan ne..."
Da sauri Mahmud ya katse Mudassir da yake son tona masa asiri, ya kwashe abin da ya faru tsakaninsu da Mai gari na aiken yaro da suka yi, don a yi musu sallama da shi su gabatar da kansu a wurinsa. Kunyar duniya ta lulluɓe Mai gari musamman da ya gan shi a yashe da gajeren wando, ya dubi Haladu cikin tsare gida da borin kunya ya ce.
"Kai Haladu, a suturta mu ba ma son raini. Muna buƙatar babbar rigarku, wane irin iskanci ne za a gan mu a haka; kuma a ƙyale mu tsirara ana ƙare wa surarmu kallo?" Haladu ya gimtse dariyarsa, ganin yadda Mai gari yake cijewa yana haɗe rai, ya ciro babbar rigarsa ya miƙa masa. Mai gari ya dubi Mai daban-daban ya ce.
"Ku kuma sai mun buƙaci hula za a ba mu saboda rashin girmama na gaba?" Tun bai gama magana ba, ya ciro hular kansa ya miƙa masa. Bayan ya saka ya dubi Sallau cikin kurari ya ce. "Ba tun yau ba, muka lura kuna da jiji da kai. Idan ba ku kwaɓo takalmanku ba, za mu yanke muku hukuncin noman gonar bayan gidanmu." Da sauri Sallau, ya sunkuya ya ce. "Tuba nake ranka shi daɗe." Daga haka ya miƙa masa takalmansa. Mai gari ya dubi su Mahmud yana baza babbar riga ya ce.
"A kunce su yanzu, kuma su same mu a ƙofar fada idan Allah Ya kaimu."
Daga haka ya yi gaba, har ya fara tafiya borin kunya ya sa sake juyowa ya ce.
"Kai Haladu za a bi bayanmu ana yi mana kirari, ko sai mun tura ku birni gidan yari!"
Da sauri Haladu ya koma gefen Mai gari, yana tafe a gefensa yana yi masa kirari. Shi kuma yana tafe cikin ƙasaita kamar ba zai tata ƙasa ba.
Mai daban-daban ya kunce su Mahmud, suka fito daga runfar jiki a sanyaye kamar marayun zakaru, suka nufi hanyar gidan da suka sauka.
Washegari
A hankali yake bubbuga ƙofar sashen Inno, kusan minti ɗaya yana tsaye ba tare da an buɗe ba. Inno ce ta ƙarasa tana faɗin, "Waye haka zai ɓalle mini ƙofa? Saboda Allah mutum bai gina mini ba, da farar safiya ya nemi karya mini ita..."
Ba ta ƙarasa maganar ba ta cire sakatar, ganin Fadil a tsaye ya sa Inno ta ɗan ƙanƙance ido ta kalle shi tana faɗin.
"Wane ne haka kamar Iro?"
Fadil ya saki murmushi don ya fahimci Inno rikici take ji, shi kuma ba zai biye mata ba.
"Eh shi ne."
Ya ba ta amsa yana gegarewa ta gefe ya wuce ciki.
"Kai boka ni fa na gaji da ganinka a sashena, ita waccen figigiyar matar taka ban isa ta zo ta gaishe ni ba kenan? Kullum sai dai ka ɗebo doro ka shigo mini gida."
Fadil bai tanka mata har ya shiga ya zauna, kasancewar ranar weekend ce ta sa koda da ya ga Laraba tana bacci bai tanka wa Inno ba.
"Ina kwana Inno?"
Ya furta mata.
"Lafiya ƙalau boka ya mugun halin matarka? Don ni dai ba zan ce ga abin da ta yi mini na laifi ba, amma wallahi yadda take kwaɓe fuska kamar kunu kullum babu fara'a, ya sa nake mata kallon mai mugun hali." Ido ya zuba mata yana kallo, ya saki murmushin gefen baki saboda idan ba ka san halin Inno ba, sai ta ɓa ta maka rai a banza.
"Inno wata magana na ji, a gaskiya ba zan lamunci ki yi zaman aure da mutumin da ba a tantance jininsa ba."
Tun da ya fara magana take kallonsa a gwasale, sai da ya gama ta ce.
"Ubanka Iro ma haka ya gan ni ya ƙyale ni, wallahi bokan turai ka shiga taitayinka tun ban yi maka iyaka da ɓangarena ba."
Hannu ya saka a aljihu ya ɗebo wasu kuɗi masu kauri ya miƙa mata. Ino ta karɓa tana zuba kabbara.
"Allahu akbar kabiran, wato boka ni fa inda kake burge ni kenan. Akwai ka da kyauta har ka fi uwarka miƙa hannu, dama ba zan saka Iro ba don babu abin da ubanka yake ba ni." Dariya sosai Fadil ya yi, musamman da ya kalli gwangwanayen madarar da ke kan firjinta, ya tuna gorin da Inno ta yi masa ta ce mahaifinsa ne ya kai mata. Yana shirin yin magana ta ce.
"Ka ga idon nan, tun jiya yake yi mini rawa. Ni dama na san ko dai kuɗi zan samu ko kuma baƙi zan yi." Haɓa ya riƙe yana kallon Inno ya ce.
"Kenan saboda fatar idonki tana rawa sai ki samu kuɗi ko ki yi baƙi? Inno me ya sa har yanzu ba za ki watsar da camfe-camfen nan ba? A kimiyance fa ba haka abin yake ba, babu dalili da zai sa don fatar idonki tana rawa ki samu kuɗi duk camfi ne. Kuma dama duk abin da ka camfa shi, za ka ga yana tabbata kamar yadda tsafi yake gaskiyar mai shi."
Inno ta yi kicin-kicin da fuska ta ce, "Kana nufin ƙarya nake kenan? To ba ubanka Iro ba, ko yayan uban Inusa bai isa ya karyata ni ba, ku da komai na ku sai kun sako iyayi da tsurfar ƙaryace-ƙaryacan yahudawa."
Fadil ya ɗan girgiza kai ya ce, "Allah da gaske Inno duk camfi ne, a kimiyance fa wasu dalilai ne suke haddasa haka. Har ka ji tsokar jikin mutum, ko wani sashe na jikinsa yana rawa wato (twitching) a kimiyance mu ce nervous ticks. Dehydration, wato bushewar jiki da ƙarancin ruwa a jikin mutum yana haifar da haka. Akwai yawan shan abubuwa masu ɗauke da caffiene , wasu a ɓangare ci ko sha zuwa yawaita shan magunguna hana zugi barkatai, ba tare da shawarar likita ba. Musamman magungunan da za ki ji ana kira da ciwo goma, ko ciwo takwas. Haka idan sinadarin ƙara ƙarfin ƙashi wato vitamin D, da vitamin E na rage dattin jiki zuwa calcium suka yi ƙaranci, duk zai iya janyo wani sashe na jiki ya dinga rawa. Akwai kuma rawar hannu, da za ka ji haka kawai hannunki yana rawa. (Neurological disorder) Ana iya gadon rawar hannu, kamar idan iyaye da kakannin suna yi. Shi ma kuma, akwai wanda wani dalili yake saka haka."
Inno ta shiga tafa hannu a tsorace ta ce, "Wallahi ni dai a kaf zuri'ar dangin uwata da ubana babu maye ko mayya. Don haka babu ta inda Iro zai gaji maita, ballantana ya haifo maye sai dai ko a can dangin uwarka. Ni kake cewa ban da bitamin a jikina boka? An ya a makarantar da ka yi karatun likitancin nan, ba su sayar maka da maita ba?"
Yadda ya ga Inno ta tsorata ne, ya tabbatar masa da gaske take faɗar maganganun har cikin zuciyarta. Ya saka hannu ya dafe kai ya ce.
"Haba Inno don Allah ki fahimce ni, ni fa ba haka nake nufi ba. Ina yi miki bayanin abin da yake kawo motsin wani sashe na jiki ne, kamar yadda kika ce fatar idonki tana rawa."
Shiru ta yi tana kallonsa a gwasale, ganin haka ya sa Fadil ya cigaba. "Inno har yawan rashin hutu ko wadataccan bacci yana haifar da haka, haka fargaba ko damuwa duk suna cikin abin da yake janyowa. A ɓangare ɗaya, yawan zuƙar taba da shan giya duk yana daga cikin abubuwan, da za su iya saka wani sashe na jiki ya dinga motsi, kamar ki ji hannu, ido ko tsokar cinya tana motsi. Idan kina son gujewa haka, sai dai ki kiyaye waɗannan abubuwan da na lissafa, yawaita shan ruwa, samun hutu da bacci da yawan cin kayan marmari. Masu zuƙar taba kuma, muna ba su shawarar guje wa zuƙar taba da shan giya, haɗe da takatsantsan wurin shan magunguna masu ɗauke da caffeine. Idan kuma matsalar ta ta'azzara sai mutum ya wuce asibiti, domin ya ga likita."
A fusace Inno ta wawauro muhuci ya raɗa wa Fadil ta ce, "Fice ka ba ni wuri, mutumin banza da wofi. Yanzu ni kake zama ka cewa ina shan giya, giya fa boka..."
Sai kawai Inno ta ɓarke da kuka, Fadil ya fice yana shafa kafaɗa don dukan ba ƙaramin shigarsa ya yi ba.
Tun daga ɗaki su Hansatu, suka fara jin yadda Yaya Inu yake wurgo ƙullin kaya da kwanukansu tsakar gida. Kusan lokaci ɗaya Hansatu da su Indo suka yi carko-carko, a ƙofar ɗakin suna kallonsa.
"Mai gida Lafiya wai? Dubu yadda kake jefo mana kaya tsakar gida."
Hansatu ta faɗa tana tattarawa kayan wankinta. A daidai lokacin Yaya Inu ya sake wurgo wata tukunya da farantin Indo suka fashe lokaci ɗaya.
Ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi, ta kwashe cikin masifa ta ce." Malam mene ne haka muna magana ka yi shiru?"
Yaya Inu ya tako yana kallonsu a wulaƙance haɗe da yamutsa fuska kamar ya ga kashi, ya dafa ƙofar ɗakin ya yi bake-bake ya ce.
"Gabaɗayanku ku kwashe mini wannan tarkacen haukan, saboda gobe za a ɗaura mini aure. Kuma a yanzu ne na san zan yi aure, zan auri farincikina mai faranta mini rai. Wacce ta san mutumci da ƙimar aure, tun a yanzu ta fara shagwaɓa ni tana lailaya ni. Wallahi idan ta zo duk wacce ta koya mata ƙazanta da mugun hali sai na ci mutumcinta. Saboda a kullum idan na kalli ku fuskokinku kama kuke yi mini da sumammun birirrika." Da sauri Hansatu ta saka hannu ta rufe bakinta saboda mamaki da ɓacin rai.
"Mai gida cin zarafin naka har ya kai ka kira mu da birrai?" Hansatu ta faɗa a zafafe.
Indo tana shirin yin magana, suka ji muryar Abu ta shigo gidan tana faɗin.
"Yawwa Goggo, mun zo a daidai ma ga shi nan yana gida."
Ɓata rai Yaya Inu ya yi yana ƙanƙance ido ya ce, "Bayan na warware igiyar aurena da ke, uwar me ya kawo ki gidana da farar safiya Abu?" Abu ba ta tanka masa ba, tana zuwa ta ɗaga hijabi ta miƙa masa jaririya.
Ba Yaya Inu ba, hatta su Indo zaro ido waje suka yi suna kallon yanayin kalar jaririyar.
"Ke mene ne wannan? Kuma waye uban wannan abin?"
Yaya Inu ya furta yana janye jiki cike da ƙyanƙyami.
"Kai ne ubanta, kuma a haka ta zo duniya." Ganin kamar Yaya Inu ba zai karɓa ba, ya sa ta dire masa jaririyar a ƙasa.
Kwana biyu na yi nisan zango, bayan na ɗanyi rashin lafiya sai kuma muka shiga biki. Na gode sosai da kulawarku, Allah Ya bar zumunci.
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[01/01, 19:10] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd
Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻
SHAFI NA GOMA
A zabure Yaya Inu, ya buga tsalle ya dira a gaban Abu da Goggonta da suke shirin fita. Goggo ta haɗe rai ta ce, "Kai Inusa, ka ba mu hanya mu wuce. Ciki ne dai Allah Ya raba ta da shi lafiya, don haka muka kawo maka abarka."
Yaya Inu saka hannuwa biyu, ya yi bake-bake a bakin ƙofar ya ce, "Ku je ina? Don Allah Goggo kada ki shiga gonata, saboda akwai ragowar mutumcinki a idona." Ya waiga wurin Abu ya ce.
"Wallahi tun muna mu biyu, ki gaggauta ɗauke wancen abin daga cikin gidan nan!"
Abu tana shirin magana Indo ta saki shewa har da guɗa tana buga cinya.
"Ahayye! Allah na gode maka, ai dama Allah ba azzalumin bawa ba ne sai bawan da ya zalinci kansa. Yau ga shi muna ji muna gani, satar kwana da karya dokar Ubangiji ta bayyana a fili mun gani." Indo ta ƙarasa maganar tana sakin dariyar izgilanci.
Hansatu ma dariyar take yi ta isa gaban Yaya Inu tana kallonsa a watse ta ce, "Yanzu don Allah mai gida ba ka ji kunyar abin da kuka haifo ba? Ke yanzu Abu ba ki ji kunyar iyayenki da sauran danginku ba? Tirƙashi! Yau ake yin ta a gidan nan, abin da muke hange a nesa ya zo kusa da mu. Yanzu mai gida jarabar taka har ta kai ka dinga kusantar Abu tana jinin al'ada?"
Yaya Inu da ya gama zuwa wuya a zafafe ya ce, "A gidan uwar wa kika ga na kusance ta tana jini? Ko kin ɗauka ban san hukuncin addini ba."
Su Indo suka kwashe da dariya kusan lokaci ɗaya, Hansatu ta kalli wurin da jaririyar take kwance tana mutsu-mutsu ta ce.
"Ga shaida can mun gani, ko ba zabiya ta haifa maka ba. Ai an yi walƙiya mun ganku, duk munafuncin da kuke yi ashe Allah zai tona muku asiri ba ku sani ba. Ba ni kaɗai ba, kowa ya san sai an kusanci mace tana jinin al'ada ake haihuwar zabiya."
Abin duniya goma da ashirin ya haɗe wa Yaya Inu, ya haɗiyi yawu mai ɗaci kamar zai yi kuka ya ce.
"Billahillazi la'ilaha'ilahuwa ban taɓa aikata wannan ɗanyan aikin ba. Ni fa shi ya sa nake tantama, magana ta Allah a ce duk dangina babu zabiya sai yanzu zan haife ta. Wallahi tun ban kai ku wurin hukuma ba, Abu ki ɗauke yarinyar nan ki kai ta wurin ubanta. Da ma ni da ke babu kare bin damo." Hankalin Abu ya tashi, saboda babu abin da yake ɗaga mata hankali irin ta yi ido biyu da ɗansanda. Duk da tana da gaskiya, amma haka gumi ya shiga karyo mata, ta ƙarasa ta ɗauki jaririyar cikin ƙarfin hali da barazana ta ce.
"Au haka ka ce ko? To kafin ka kai mu wurin hukuma, ni da kai na zan fara kai ƙararka. Ka san dai ko lokacin 'yan matancin na kai ne mutumin da nake kulawa. Don haka babu wani uban yarinyar nan, idan ba kai ba. Ai na sha faɗa maka ka daina satar kwana kana kirana turakarka amma sai ka ce ba haka ba. Ka dinga koɗa ni kana ce mini matar so, ni kuma ina jin daɗi domin na ɓa ta ran su Indo nake biye maka. Sai yanzu za ka ce ba ka san zancen ba, za ka yi bayani a gaban ƙuliya." Tana gama faɗar haka ta yi waje fuu! A fusace.
Hansatu ta gyaran ɗaurin ɗan kwalinta, irin ɗaurin ture ka ga tsiya ta ce.
"Kai yau Allah na gode maka da ka nuna mini wannan rana. Ayyiriri! Shagali wan dina. Ai gara da ta tafi da 'yarta don wallahi ba zan riƙe gayyar tsinuwa ba, yarinya an same ta a tsine ta rayu a ciki cikin tsinuwa sannan a ce za a dire mana ita. Haka kawai muna zaune a kawo mana annoba cikin zuri'a ta kwashe mana albarkatun cikin gida."
Daga haka ta wuce cikin ɗakinta, su Indo ma haka. Yaya Inu jiki a sanyaye ya nufi ɗakinsa yana nazarin baƙin cikin da Zainab ta dasa masa. A ɓangare ɗaya yana fargabar abin da zai je ya dawo, saboda shi dai ya san bai taɓa kusantar mace tana jini ba, satar kwana dai kam ya san yana yi babu adadi musamman idan mace ta ɓata masa rai. Don ya rama abin da ta yu masa sai ya kira wata macen da ba girkinta ba, musamman Abu ta kwana a ɗakin. Babban tashin hankalinsa, ya yi mata barazana da hukuma kamar yanda ya san tana tsoron 'yansanda amma ya lura ko a jikinta.
Zaune yake ya yi shiru yana kallon Ɗan Bishir da jijiyoyin jikinsa suka gama yin laushi, ya ja riga ya share hawayensa. Yana jin ina ma yana da ikon dawo da ciwon shalelensa kansa, da tuni ya dawo da shi.
"Mai gida zaman nan naka fa ba zai kai mu ba, a ce yanzu tun da aka yi wa yaron nan shayi ba za ka fita kasuwa ba. Ita zara fa ba ta barin dami, don Allah ka tashi ga magungunanka can na haɗa maka su." Baba Sale ya ja majina ya ce, "Haka ne Uwale, amma gani nake idan na fita kamar wani abu zai faru da shi. Ban taɓa ganin kaciyar da ta lalace haka ba, ki duba fa ki ga yadda take yin ruwa. Yaron nan duk kuzarinsa ga shi nan ba shi da kataɓus."
Ita kanta Uwale ƙarfin hali take yi, don tana nuna rauninta ta san abin da mijin na ta zai yi sai ya fi haka, don haka ta shanye hawayen idonta ta ce. "Haka ne, amma ko ka zauna ɗin ma abin da Allah Ya ƙaddara shi zai faru. Shi kuma idan mun ga ba ta daina ruwa ba, sai mu sake kiran wanzan mu yi masa bayani. Tun da maganin wurinka ma bai sa ta ƙame ba."
A sanyaye Baba Sale ya miƙe ya shiga ɗaki, ya ɗauko wani ƙaton buhu da ke cike da magunguna. Ya ƙarasa gaban Ɗan Bishir ya ce, "Ɗan Bishiriri ni zan fita nema."
Ɗan Bishiri da ya yi lugub, saboda yadda yake jin jiki ya kalle shi da shanyayyun idanunsa ba tare da ya amsa masa ba. Da ƙyar Baba Sale ya iya ɗaga ƙafarsa ya fita Uwale tana biye da shi. Suna fita Fadil yana fitowa bayan sun gaisa ya wuce ya shiga motarsa da ke gefensu.
"Au Mai gida na manta ba ka bayar da maganin Shamsiyya ba, kada sai ka tafi ta aiko."
Uwale ta furta.
Buhun ya buɗe ya ɗebo wasu matsakaitan magunguna a cikin jarkoki guda huɗu, sannan ya ɗauko wata ƙaramar roba mai ɗauke da man shafawa na magani ya miƙa mata. Ya ɗago jarkokin guda biyu, ya nuna mata wurin da aka yi bayanin maganin a jikin takardar.
"Wannan ki ce mata sai ta ci abinci za ta sha, maganin sanyin mara ne. Kuma sau biyu ake sha safe da yamma, duk lokacin da za ta sha murfi biyu za ta sha saboda yana da ƙarfi sosai."
Ya sake ɗauko ragowar roba biyun da yake ba iri ɗaya da waɗancan ba ne ya ce.
"Wannan kuma idan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 35